SUNA TILAWAR KUR'ANI HAKIKANIN TILAWARSA
(يتلونه
حق تلاوته)
Tarjamar
Abubakar Hamza
Alkur'ani, taska ne da ya cika da falaloli da alkhairori.
Kuma domin samun fa'idodin wannan taskar babu makawa, sai an yi amfani
da mabudansa.
Wanda sune, LADDUBAN TILAWARSA
DAGA CIKIN WADANNAN LADDUBAN akwai: Tsarkake niyya ga Allah Ta'alah,
saboda Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya bada labarin cewa
lallai: daga cikin na-farko-farkon wadanda za a iza wutar sa'ira da su, a
ranar Kiyama, akwai makaranci ko mahaddacin Alkur'ani, za a ce masa: Ka haddace
Alkur'ani ne, domin a ce: Shi mai hadda ne. Muslim ya ruwaito.
Kuma DAGA CIKINSU: Akwai yin asiwaki da tsarkaka daga karamin kari
(hadasi), da fiskantar alkibla.
Kuma a lokacin fara karatun, zai nemi tsarin Allah daga Shedan;
((فإذا قرأت القرآن فاستعذ
بالله من الشيطان الرجيم))
[النحل: 98].
Ma'ana: "Kuma idan zaka karanta
Alkur'ani, sai ka nemi tsarin Allah daga Shedan jefaffe daga Rahama"
[Nahl: 98].
Kuma zai yi karatu ko tartilin Alkur'ani ne cikin tsanaki, da kokarin
bayyanar da harrufansa, karatun, Abdullahi bn Abbas ya kasance yana cewa:
((لأنْ أقرأ سورة أُرتلها، أحبّ إليَّ مِن
أنْ أقرأ القرآن كلَّه))، رواه أبو داود عن ابن عباس.
Ma'ana: "Na
karanta sura daya cikin tsanaki da tartili, lallai shi yafi soyuwa a wurina
fiye da na karanta Alkur'ani gaba dayansa". Abu-dawud ya
ruwaito shi, daga Ibnu-Abbas.
Kuma Mustahabbi ne, a rika kyautata sauti, a yayin karatun Alkur'ani,
saboda Annabi –صلى الله عليه وسلم- yana cewa:
((زيِّنوا القرآنَ بأصواتكم))، رواه أبو داود،
وصححه الألباني.
Ma'ana: "Ku
kawata Kur'ani da sautinku", Abu-dawud ya ruwaito shi, Albaniy
ya inganta shi.
Idan kuma ya bi ta kan ayar Rahama, sai ya
nemi Allah daga falalarSa, idan kuma ya biyo ta kan ayar azaba, sai ya nemi
tsarin Allah, daga wannan azaban.
Kuma
mustahabbi ne, mutane su rika haduwa wajen karatun Alkur'ani, da kai-komo kan
ma'anoninsa, da yin darasunsa, saboda fadin Annabi –صلى الله عليه
وسلم-:
"ما اجتمع قوم في بيت من بيوت
الله يتلون كتاب الله ويتدارسونه بينهم إلا نزلت عليهم السكينة، وغشيتهم الرحمة،
وحفَّتهم الملائكة، وذكرهم الله فيمن عنده"، رواه مسلم.
Ma'ana: "Lallai
Mutane ba za su hadu a cikin daki daga cikin dakunan Allah, suna tilawar
Alkur'ani ba, suna yin darasunsa a tsakaninsu, face natsuwa ta sauka akansu,
kuma rahama ta lullube su, kuma Mala'iku sun kewaye su, kuma sai Allah ya
ambace su ga wadanda suke wurinsa", Muslim.
No comments:
Post a Comment