2015/10/23

HUDUBAR MADINA TA juma a 10 muharram 1437h daidai da 23 10 2015m ta Alhuzaifiy






HUXUBAR MASALLACIN ANNABI (r)
JUMA'A, 10/MUHARRAM/1437h




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI ALIYU XAN ABDURRAHMAN AL-HUZAIFIY







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
Godiya ta tabbata ga Allah Mai rahama Mai jin qai; Mai ilimi Mai hikima, Ma'abocin falala mai girma,        Ina yin godiya wa Ubangina kuma ina yin yabo a gare shi,     Ina kuma tuba zuwa gare shi ina kuma neman gafararSa,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, Ma'abocin al'arshi mai karamci,   
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu annabi Muhammadu bawanSa ne kuma manzonsa ne;    Ma'abocin halayya masu girma,    Ya Allah ka yi qarin salati da sallama ga bawanka kuma manzonka annabi Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa, masu kira zuwa ga Allah da kuma shiryarwa zuwa ga hanya madaidaiciya.

Bayan haka:
Ku kiyaye dokokin Allah ta hanyar yin aiki da abubuwan da suke yardar da shi, da kuma qaurace wa abubuwan da ya haramta;       domin ku rabauta da samun yardarSa da kuma ni'imomin aljannoninSa,      sannan ku samu tsira daga fushinSa da kuma uqobobinSa,

Ya ku musulmai…
Lallai Ubangijinmu mabuwayi da xaukaka ya yawaita qofofin alkhairi, da kuma hanyoyin aiyuka kyawawa,     a matsayin falala da rahama da kuma kyauta daga ma'abocin buwaya da xaukaka;      domin musulmi ya shiga kowace qofa ta alkhairori,       ya kuma bi kowace hanya daga cikin hanyoyin biyayya;      sai Allah ya gyara duniyarSa,     ya kuma xaukaka shi zuwa ga darajoji a lahirarSa;       Sai shi kuma Allah (سبحانه) ya karrama shi ta hanyar bashi rayuwa daddaxa, da kuma rabauta a cikin rayuwarsa,      daga qarshe sai ya samu ni'ima tabbatacciya, da kuma yardar Ubangiji, bayan mutuwarsa.  Allah (تعالى) yana cewa:
"Sai ku yi tsere zuwa ga aiyukan alkhairi. Kuma duk inda kuka kasance Allah zai zo da ku gabaxaya, Lallai Allah akan komai mai iko ne" [Baqarah: 148].
Kuma Allah (سبحانه) yana cewa -a dangane da annabawansa; waxanda sune abin koyi ga mutane (Allah yayi qarin salati da sallama a gare su gabaxaya):
"Lallai su, Sun kasance suna yin tsere cikin aiyukan alkhairi, Kuma suna yin bauta a gare mu akan kwaxayi da fargaba, kuma sun kasance a gare mu masu tsoro ne" [Anbiya'i: 90].
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace wa sahabinsa Mu'azu (رضي الله عنه):
"Shin ba zan shiryar da kai zuwa ga qofofin alheri ba? Azumi garkuwa ne, Sadaka kuma tana shafe kurakurai kamar yadda ruwa ke kashe wuta. haka Sallar mutum a cikin yankin dare. Sannan sai Annabi ya karanta faxin Allah: (Gefen jikinsu yana nisantar gurin kwanciyarsu, suna roqon Ubangijinsu cikin fargabar tsoro da kwaxayi, kuma daga cikin abinda muka azurta su suna ciyarwa. Kuma rai bata san abinda aka voye a gare ta na sanyin ido ba, sakamakon abinda suka kasance suke aikatawa). Sa'annan yace: Ba zan ba ka labari dangane da, kan wannan lamarin ba, da ginshiqansa, da qololuwar tozonsa?
Sai nace: Eh, ka bani labari ya Manzon Allah!
Sai yace: Kan wannan lamarin shine: Musulunci.
Ginshiqinsa kuwa sallah.
Qololuwar tozonsa kuma shine: Jihadi fiysabillah. 
Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma ya inganta shi.

KUMA YANA DAGA CIKIN QOFOFIN ALKHAIRORI, DA HANYOYIN KYAWAWAN AIYUKA DA XA'O'I, KUMA YANA DAGA CIKIN SABBUBAN SHAFE MUNANAN AIYUKA: NEMAN GAFARA; Saboda neman gafara sunnar Annabawa da Manzanni ne (عليهم الصلاة والسلام), Allah (تعالى) yana cewa a dangane da iyayen 'yan-adam; guda biyu (wato: annabi Adam da Hauwa'u) Allah ya yi salati mai yawa da rahama da qarin albarka a gare su:
"Suka ce: Ya Ubangijinmu! Mun zalunci kayukanmu, Idan baka gafarta mana, ka yi rahama a gare mu ba, zamu kasance daga cikin masu hasara" [A'araf: 23].
Kuma Allah yana cewa a dangane da annabi Nuhu (عليه السلام)
"Ya Ubangijina! Ka gafarta mini, da iyayena guda biyu, da wanda ya shiga gidana yana mumini, da kuma muminai maza da muminai mata" [Nuh:   28].
Kuma Allah mabuwayi da xaukaka yana faxa dangane da Ibrahimu alkhalil (عليه السلام):
"Ya Ubangijinmu! Ka gafarta mini, da iyayena biyu, da kuma muminai, a ranar da hisabi yake tsayawa" [Ibrahim: 41].
Kuma Allah yana cewa dangane da annabi Musa (عليه السلام):
"Ya Ubangijina! Ka yi gafara a gare ni, ni da xan'uwana, kuma ka shigar da mu cikin rahamarka; lallai kai ne mafi rahamar masu rahama" [A'araf: 151].
Kuma Allah (تعالى) yana cewa:
"Sai annabi Dawuda ya tabbata cewa: Lallai jarrabarsa muka yi, sai ya nemi gafarar Ubangijinsa, ya kuma faxi yana mai sujjada, ya kuma mayar da lamari zuwa ga Allah" [Sad: 24].
Allah (تعالى) yana cewa, a inda yake umurtar annabinSa (صلى الله عليه وسلم) da cewa:
"Ka sani, Lallai babu wanda ya cancanci bauta sai Allah, kuma ka nemi gafarar zunubanka, da kuma wa muminai maza da muminai mata" [Muhammadu: 19].

            KUMA YANA DAGA SHIRIYAR MANZONMU (صلى الله عليه وسلم): YAWAITA NEMAN GAFARA, tare da cewa Allah ta'alah ya gafarta masa abinda ya gabata na zunubansa, da abinda ya jinkirta;    Ya zo daga Xan Umar (رضي الله عنهما) yace:
"Mun kasance muna qidaya wa Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) a majalisa guda xaya, sau xari: RABBI IGFIR LIY WA TUB ALAYYA; INNAKA ANTAT TAWWABUR RAHIM.
Ma'ana: Ya Ubangijina! Ka gafarta mini, ka karvi tuba ta, lallai kai mai yawan karvar tuba ne, Mai rahama". Abu dawud ya ruwaito shi, da Tirmiziy, kuma yace: Hadisi ne mai kyau ingantacce.
Kuma an ruwaito daga A'ishah (رضي الله عنها) lallai ta ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance gabanin mutuwansa yana yawaita faxin: SUBHANALLAHI, WA BI HAMDIHI, ASTAGFIRULLAHA WA ATUBU ILAIHI.  
Ma'ana: Tsarki ya tabbata ga Allah, tare da gode masa, Ina neman gafarar Allah, ina kuma yin tuba zuwa gare shi. Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
An ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه) yace:
"Ban ga wani mutumin da yafi Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yawaita faxin ASTAG FIRUL LAHA WA ATUBU ILAIHI". Ma'ana: Ina neman gafarar Allah, kuma ina tuba zuwa gare shi. Annasa'iy ya ruwaito shi.

Kuma Annabi |(صلى الله وسلم) ya kasance bayan yin sallamar fita daga sallah ya kan ce: Astagfirul laha, Astagfirul laha, Astagfirul laha, har sau uku. Muslim ya ruwaito shi, daga hadisin Sauban (رضي الله عنه). Sa'annan daga bisani sai ya faxi zikirorin da aka shar'anta faxinsu a bayan sallolin farilla.

Kuma lallai NEMAN GAFARA Xabi'ar salihai ne, kuma aiki ne na mutane masu biyayya, da taqawa, kuma alama ce ta muminan mutane,    Allah (تعالى) yana cewa:
"Ya Ubangijinmu! Ka gafarta mana zunubanmu, kuma ka kankare mana munanan aiyukanmu, kuma ka xauki rayukanmu tare da masu yin biyayya" [Ali-imrana: 193].
Kuma Allah (تعالى) yana cewa:
"Waxanda suke cewa: Ya Ubangijinmu! Lallai mu mun yi Imani; sai ka gafarta mana zunubanmu, kuma ka katange mu daga azabar wuta   *   Masu haquri, da masu gaskiya, da masu qanqan da kai, da masu ciyarwa, da masu yin istigfari a lokutan asuba" [Ali-imrana: 16-17].
Alhasan yace: Sun yi ta sallah har zuwa lokacin sahur, sannan suka fiskanci ibadar neman gafara.
Kuma Allah (تعالى) yana cewa:
"Sune kuma Waxanda, idan suka aikata wata alfasha, ko suka zalunci kayukansu su kan tuna Allah; sai su nemi gafarar zunubansu, Kuma wanene zai gafarta zunubai idan ba Allah ba, kuma basa dogewa akan abinda suke aikatawa, alhalin suna sane" [Ali-imrana: 135].
Ibnu-rajab yace: ((Shi kuma neman gafara daga zunubai shine: Neman lulluve su.    kuma lallai bawa yana da matuqar buqata zuwa ga hakan; saboda ko-yaushe ya kan yi kuskure cikin dare da rana. Kuma lallai ambaton TUBA DA NEMAN GAFARA ya maimaitu a cikin alqur'ani, da kuma yin umurni da su, da kwaxaitarwa zuwa gare su)). … Maganarsa ta qare.

            Kuma lallai NEMAN GAFARA DAGA Ubangiji mabuwayi da xaukaka Allah ta'alah yayi alkawari da cewa zai amsa, kuma zai yi gafara.

            Kuma lallai an shar'anta cewa Bawa ya riqa neman gafara a kan zunubi aiyananne, sananne; saboda faxin Annabi (صلى الله عليه وسلم):
"Lallai bawana ya aikata wani zunubi, Sannan yace: Ya Ubangijina, lallai ni na aikata wani zunubi; sai ka gafarta mini shi, Sai Allah yace: Bawana lallai ya san cewa  yana da Ubangijin da yake  gafarta zunubai, ya kuma tafiyar da shi, to lallai na gafarta wa Bawana", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi daga hadisin  Abu-hurairah (رضي الله عنه).

            Kamar yadda shari'a ta zo da cewa: Bawa ya riqa neman gafara, a sake ba qaidi; sai yace: Ya Ubangijina! ka gafarta min, kuma kayi mini rahama. Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma ka ce: Ya Ubangijina! Ka yi gafara kuma ka yi rahama, domin kai ne mafi alherin masu rahama" [Mu'uminuna: 118].
Kuma lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana sanar da mutumin da ya musulunta da cewa ya riqa yin addu'a da waxannan kalmomin :
"Ya Allah ka yi gafara a gare ni, ka yi mini rahama, ka shiryar da ni, ka bani lafiya, ka azurta ni", Muslim ya ruwaito shi daga hadisin Xariq xan Ashyam (Allah ya qara yarda a gare shi).

            Kamar yadda aka shar'anta: Bawa ya riqa nema daga Ubangijinsa cewa ya gafarta masa zunubansa gabaxayansu; waxanda ya san su da waxanda bai sansu ba; wannan kuma saboda zunubai dayawa babu wanda ya sansu sai Allah, kuma lallai bawa za a kama shi akansu;    Ya zo daga Abu-Musa al'ash'ariy (رضي الله عنه) daga Annabi(صلى الله عليه وسلم) lallai shi ya kasance yana yin addu'a da wannan addu'ar:
"Ya Allah! Ka gafarta min kurakuraina da jahilcina, da qetare iyakana cikin lamari, da abinda kai ne ka fini saninsa. Ya Allah! Ka gafarta mini gaskena da wasana, da kuskurena da gangancina, kuma dukkan haka, akwai shi a wurina. Ya Allah! Ka gafarta mini abinda na gabatar da wanda na jinkirta, da abinda na voye da abinda na bayyanar, da abinda kai ne ka fi ni saninsa, kai ne Mai gabatarwa, kuma kai ne Mai jinkirtarwa, kuma lallai kai akan kowani abu mai iko ne", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Da kuma saboda faxin Annabi (صلى الله عليه وسلم):
"Shirka a cikin wannan al'ummar tafi vuya fiye da tafiyar tururuwa, Sai Abubakar (رضي الله عنه) yace: To ta yaya za a kuvuta daga gare ta, ya Manzon Allah? Sai yace: Ka riqa cewa: Ya Allah ina neman ka tsare ni kan yin shirka a gare ka alhalin ina sane, Ina kuma neman gafararka daga zunubin da ban sani ba", Ibnu-Hibbana ya ruwaito shi, daga hadisin Abubakar, Da kuma Ahmad, daga hadisin Abu Musa.
An ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) lallai shi ya kasance yana yin addu'a:
"Ya Allah! Ka gafarta min zunubaina dukkansu; qananansu da manyansu, na kuskurensu dana gangancinsu, na sirrinsu dana bayyanansu, na farkonsu da na qarshensu", Muslim ya ruwaito shi, da Abu-dawud.
            Idan bawa ya roqiUbangijinSa gafarar zunubansa; waxanda ya sani daga cikinsu da waxanda bai sani ba, to lallai an datar da shi; dace mai girma.

            Kuma bawa ya roqi Ubangijinsa gafarar zunubai cikin ikhlasi da naci da roqo mai tattare da qanqan-da kai yana qunsan TUBA DAGA ZUNUBAN, Shi kuma ROQON A DATAR DA MUTUM ZUWA GA TUBAN yana qunsan NEMAN GAFARAR; saboda haka, kowanne daga cikin ISTIGFAAR da TUBA idan aka ambace shi ba tare da xayanba to yana qunsan ma'anan xayan.  Idan kuma ambatonsu ya haxu a cikin nassoshin Qur'ani ko hadisi to Ma'anan: ISTIGFAARI sai ya zama: Neman shafe zunubi da gusar da alamarsa ko gurbin da ya bari, tare da bada kariya kan sharrin da ya gabata na zunubin, da kuma suturce shi. Ita kuma TUBA sai ma'ananta ya zama: Komawa zuwa ga Allah; ta hanyar barin aikata zunubai, da kuma kare bawa daga abinda ya ke tsoro; na munanan aiyukansa a rayuwar da yake fiskanta, tare da yin azama ko niyyar ba zai sake aikata zunubin ba.
Kuma lallai AyarAllah ta ambaci ISTIGFAARI da TUBA a haxe, a inda Allah yake cewa:
"Kuma ku nemi gafarar Ubangijinku, sa'annan ku tuba zuwa gare shi, zai jiyar da ku daxi jiyarwa mai kyau, zuwa ga wani lokaci ambatacce, kuma ya baiwa dukkan ma'abocin girma girmansa, Idan kuma kuka juya to lallai ni ina tsoron azabar yini mai girma akanku" [Hud: 3].
Da wassu ayoyin waxanda ba wannan ba.
Kuma lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Ya ku mutane! Ku tuba zuwa ga Ubangijinku, kuma ku nemi gafararSa; saboda Ni na kan tuba zuwa gare shi, ina kuma neman gafararSa; a kowani yini sau xari", Annasa'iy ne ya ruwaito shi, daga hadisin Al'agarri Almuzaniy (رضي الله عنه).

            Kuma lallai bawa yana da matsananciyar buqatar YIN ISTIGFAARI, a ko-da-yaushe,      musamman kuma a wannan zamanin saboda yawaitan ZUNUBAI da FITINTINU,    wannan kuma domin Allah ya datar da shi a rayuwarsa, da kuma bayan mutuwarsa, ya kuma gyara masa sha'aninsa.    Saboda yin istigfaari ya kan buxe qofofin alherori,   ya kuma tunkuxe sharrori da uqubobi.
            Kuma lallai itama al'ummar musulmai tana da matsananciyar buqata zuwa ga dawwama kan neman gafara; domin Allah ya yaye mata uqubobi da suka sauka a gare ta, ya kuma tunkuxe mata uqobobin da za su sake sauka a gare ta.
            Kuma babu wanda zai yi sakaci KAN NEMAN GAFARA sai wanda ya jahilci amfanoninsa da albarkokinsa,     saboda falolinsa sun zo dayawa a cikin ALQUR'ANI da SUNNAH; Allah (تعالى) yana cewa dangane da annabi Salihu (عليه السلام):
"Ya ku mutanena! Don me kuke gaggawan aikata mummuna gabanin kyakkyawa, Da dai kun nemi gafarar Allah; da tsammanin za a yi rahama a gare ku" [Naml: 46].   Saboda da yin istigfaari ne ake yin rahama ga al'ummah.
Kuma Allah (تعالى) yana faxa dangane da annabi Nuhu (عليه السلام):
"Sai nace: KU NEMI GAFARAR UBANGIJINKU lallai shi ya kasance mai yawan gafara   *    Zai saki ruwan sama akanku; mamako   *     kuma ya qarfafe ku da wata dukiya, da 'ya'ya, kuma ya sanya muku gonakai, kuma ya sanya muku koguna" [Nuh:10-12].
Kuma Allah (تعالى) yake faxi dangane da annabi Hudu (عليه السلام):
"Kuma, ya mutanena! Ku nemi gafarar Ubangijinku, sa'annan ku tuba zuwa gare shi; sai ya saki ruwan sama akanku, ya kuma qara muku wani qarfi akan qarfinku, Kuma kada ku juya baya kuna masu laifi" [Hudu: 52].
Allah (تعالى) yace:
"Allah bai kasance zai azabta su ba alhalin kana cikinsu, kuma Allah bai kasance mai azabta su ba; matuqar suna neman gafara" [Anfaal: 33].
Abu-Musa yake cewa (رضي الله عنه):
((Lallai wannan al'ummah a cikinku akwai abubuwan samun aminci guda biyu;   Amma dangane da wannan annabin –صلى الله عليه وسلم- to shi kam ya shuxe, Yayin da shi kuma NEMAN GAFARA zai ci gaba da wanzuwa a cikinku har zuwa tashin kiyama)).
            Don haka; Wannan al'ummar; Idan ta yawaita istigfaari = zai xauke mata musibun da suka sauka ko suka auku, sannan ya tunkuxe mata waxanda za su sauka a gaba;     saboda bala'i baya sauka sai idan an yi ZUNUBI,  kuma ba a yaye shi sai da yin TUBA da ISTIGFAARI,     An ruwaito daga Abdullahi xan Abbas (رضي الله عنهما) yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Duk wanda ya lazimci yin istigfaari Allah zai sanya masa mafita daga kowani qunci, da kuma yayewa daga kowani baqin ciki, ya kuma azurta shi ta yadda baya tsammani", Abu-dawud ya ruwaito shi.

            Kuma lallai KALMOMI DA AKA KIYAYE SU MASU ALBARKA na ISTIGFAARI sun zo daga Annabi (صلى الله عليه وسلم),     kuma lallai cikin faxin waxannan kalmomin akwai lada mai yawa;
            Yana daga cikinsu:
            Faxinsa (صلى الله عليه وسلم):
"Duk wanda ya faxI: ASTAGFIRUL LAHAL ALZIY LA ILAHA ILLA HUWAL HAYYAL QAYYUMA, WA ATUBU ILAIHI, Duk wanda ya faxi haka to an gafarta zunubansa, koda kuwa ya gudu a wurin yaqi". Abu-dawud da Tirmiziy suka ruwaito shi, da Hakim, kuma yace: hadisi ne ingantacce, akan sharaxin Bukhariy da Muslim.
An ruwaito daga Abu-Sa'id alkhudriy, daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), lallai yace:
"Duk wanda ya faxa a lokacin da ya tafo zuwa ga shumfuxinsa: ASTAGFIRUL LAHA ALLAZIY LA ILAHA ILLA HUWAL HAYYUL QAYYUMU, WA ATUBU ILAIHI, sau uku, to Allah zai gafarta zunubansa, koda sun kai kumfan teku", Tirmiziy ne ya ruwaito shi.
An ruwaito daga Ubadah xan As-samit (رضي الله عنه) yace: Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Duk wanda ya tashi daga barcinsa, a cikin dare' Sa'annan yace: LA ILAHA ILLAL LAHU, WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADIR, SUBHANAL LAHI, WALHAMDU LILLAHI, WA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR, ALLAHUMMAG FIR LIY, Sai yayi addu'a to an amsa masa, idan kuma ya tashi yayi sallah to an karvi sallarsa", Bukhariy ne ya ruwaito shi.
Ya zo cikin wani hadisin cewa:
"Duk wanda a gabanin ketowar alfijir xin juma'a yace: ASTAGFIRUL LAHAL ALZIY LA ILAHA ILLA HUWAL HAYYAL QAYYUMA, WA ATUBU ILAIHI, sau uku, an gafarta zunubansa koda sun kasance misalin kumfar teku ne".
Kuma an ruwaito daga Shaddad xau Aus (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Jagoran laffuzan neman gafara shine bawa yace: ALLAHUMMA ANTA RABBIY LA ILAHA ILLA ANTA; KHALAQTANIY, WA ANA ABDUKA, WA ANA ALA AHDIKA WA WA'ADIKA MASTAXA'ATU, A'UZU BIKA MIN SHARRI MA SANA'ATU, ABU'U LAKA BI NI'IMATIKA ALAYYA, WA ABU'U BI ZANBIY; FAGFIR LIY; FA INNAHU LA YAGFIRUZ ZUNUBA ILLA ANTA, Duk wanda ya faxi kalmomin nan cikin yini yana mai samun yaqini akansu sai ya mutu a wannan yinin nasa, gabanin yayi yammaci ya shiga aljannah. Wanda kuma ya faxe su cikin dare, alhalin yana da yaqini akansu sai ya mutu gabanin yayi yammaci to yana cikin 'yan aljannah", Bukhariy ya ruwaito shi.
An ruwaito daga Anas (رضي الله عنه) yace: Na ji Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: Allah (تعالى) yana cewa:
"Ya kai xan Adam! Da zunubanka za su cika sashen sama gabaxaya, sannan sai ka nemi gafarata sai in gafarta maka, ba zan damu ba!", Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma yace: hadisi ne mai kyau.

            Kamar yadda kuma ake shar'anta neman GAFARAR ALLAH  a lokacin yin wata ibada ko bayan kammala ta; wannan kuma domin ta magance abinda ya kasance a cikin ibadar na tawaya ko naqasa, tare da nisantar da mutum daga ji-da kai, ko riya;    Allah (تعالى) yana cewa:
"Sa'annan ku tafo ta wurin da mutane suke gangarowa, kuma ku nemi gafarar Allah, lallai Allah Mai gafara ne Mai rahama" [Baqarah: 199].
Kuma Allah (سبحانه) yana cewa:
"Kuma ku tsayar da sallah, kuma ku bada zakka, ku bada rance wa Allah rance mai kyau,    kuma duk abinda kuka gabatar ga kayukanku na alkhairi za ku same shi a wurin Allah, zai kasance mafifici kuma zai fi girma ga sakamako, Kuma ku roqi Allah gafara; lallai Allah Mai gafara ne Mai rahama" [Muzammil: 20].
Sai Allah yayi umurnin a nemi gafararSa a lokacin da ake yin waxannan aiyukan xa'an, da kuma bayan kammala su.

            Haka kuma an shar'anta musulmi ya riqa neman gafara ga 'yan'uwansa muminai; maza da mata, da musulmai maza da msulmai mata, rayayyu daga cikinsu da waxanda suka mutu,    wannan kuma a matsayin kyautatawarsa ne a gare su, da bayyanar da soyayya, da lafiyar zuciya, tare da amfanar da musulmai, da kuma (tsoma baki) don neman cetonsu a wurin Allah;    Allah (تعالى) yana cewa:
"Da kuma waxanda suka zo a bayansu, suna cewa: Ya Ubangijinmu ka yi mana gafara, tare da 'yan'uwanmu da suka rigaye mu da Imani, kuma kada ka sanya wani qulli a cikin zukatanmu dangane da waxanda suka yi imani, Ya Ubangijinmu lallai kai Mai tausayi ne, Mai rahama" [Hahsri: 10].
An ruwaito daga Ubadah xan Assamit (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) lallai shi yace:
"Duk wanda ya nemi gafara ga muminai maza da muminai mata to lallai Allah zai rubuta masa lada a madadin kowani mumini namiji da mumina mace", Alhaisamiy yace: Isnadin wannan hadisin yana da kyau (jayyid).
Wannan kuma kamar nema musu gafara kenan a lokacin yin sallar janaza a gare su, da kuma nema musu gafara a maqabartai idan musulmi ya ziyarce su.
Hakan kuma koyi ne da Mala'ikun da suke xauke da al'arshi, da kuma sauran Mala'iku makusanta,   Allah yana cewa:
"Waxanda suke riqe da al'arshi, da waxanda suke kewayensa suna yin tasbihi da gode wa Ubangijinsu, kuma suna yin imani da shi, suna kuma neman gafarar Allah ga waxanda suka yi imani (suna cewa) Ya Ubangijinmu! Lallai ka yalwaci kowani abu da rahama da kuma ilimi; sai ka yi gafara ga waxanda suka tuba, suka kuma bi hanyarka, kuma ka kare su daga azabar wutar jahim" [Gafir: 7].  
Yin haka kuma yana daga cikin manyan haqqoqin muminai!

            Ya ku bayin Allah… !
            Ku amsawa umurnin Ubangijinku,    Allah yana cewa a cikin hadisin qudusiy:
"Ya ku bayina ! lallai ku, kuna yin laifi dare da rana, Ni kuma ina gafarta zunubai gabaxaya; sai ku nemi gafarata; zan gafarta muku", Muslim ya ruwaito shi daga hadisin Abi-zarrin.

Sai ku fiskanci Ubangijinku da neman gafararSa, za ku ga karamcinSa da kyautarSa da falalarSa, da albarkokinSa, kuma za ku sami shafe aiyukanku munana, da xaukaka darajoji,      Hadisi y azo daga Abu-hurairah (رضي الله عنه) yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Na rantse da wanda raina yake hannunsa! Da ace bakwa yin zunubi to da Allah ta'alah ya tafiyar da ku, kuma da ya zo da wassu mutanen waxanda suke yin zunubi; sai suna neman gafarar Allah ta'alah sai ya gafarta musu", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma saboda kasancewarsa Allah maxaukaki Mai yalwar gafara ne, mai baiwa da kyauta da karamci, yana son a riqa neman gafararSa, ana roqonSa    Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma duk wanda ya aikata mummunan aiki, ko ya zalunci kansa, sa'annan sai ya nemi gafarar Allah, to lallai zai sami Allah Mai yawan gafara Mai rahama" [Nisa'i: 110].


            Allah yayi mini albarka Ni da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da mu da abinda ke cikinsa na ayoyi da tunatarwa mai hikima,      kuma ya amfanar da mu da shiriyar shugaban manzanni, da kuma maganganunsa miqaqqu,    Ina faxar maganata wannan, kuma ina neman gafarar Allah Mai girma Mai daraja wa Ni da Ku, da kuma sauran musulmai da muminai,     Ku nemi gafararSa; lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.


HUXUBA TA BIYU
            Godiya ta tabbata ga Allah, wanda yake gafarta zunubi, Mai karvar tuba, Mai kuma tsananin uquba, Ma'abocin ni'imomi, Babu abin bautawa da gaskiya sai shi, kuma zuwa gare shi makoma ta ke. Ina yin godiya wa Ubangijina, ina kuma yaba masa akan falalarSa mai girma,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokin tarayya,   Masani, Mai qudura. 
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shigabanmu Muhammadu bawan Allah ne kuma Manzonsa ne, mai bushara da gargaxi, kuma fitila mai haskakawa,  
            Ya Allah kayi salati da sallama da qarin albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa gabaxaya.

Bayan haka;;;
            Ku kiyaye dokokin Ubangijinku, kuma kuyi masa ikhlasin dukkan ibadodi, kuma ku nisanci kamunSa da azabarSa,

            Ya ku musulmai…
            Ku kiyayi fitintinu; saboda suna cutar da addini, da kuma duniya; wato suna halakar da bawa a lahira, su kuma gurvata yanayin rayuwa a duniya,
Kuma lallai wanda yayi rabo shine wanda aka nisantar da shi daga fitintinu,    
kuma lallai mafi girman fitina wajen muni ita ce: Wacce gaskiya da varna suka cakuxe wa mutum a cikinta, da kuma shiriya da vata, da kyakkyawa da mummuna, haka kuma halal da haram.
Kuma tabbas fitintinu masu yawa sun mamaye garurruka da kuma mutane, waxanda suka fitar da samarin musulmai daga wuraren tarbiyyarsu masu aminci, da kewayen da suke zaune a cikinsa mai tsari, da al'ummar da suke rayuwa a cikinta mai tausaya musu = zuwa ga vata, da vatacciyar aqida, da kuma bi, tare da son khawarijawan wannan zamanin;  sai su kuma KHAWRIJAWAN WANNAN ZAMANIN suka jagorance su zuwa ga/     KAFIRTA MUSULMAI,  da ZUBAR DA JINANEN HARAM (kisa), harma suka yi musu fatawar SU SHIGA YANAYIN DA ZA SU QONA KANSU DA KASHE KANSU, (والعياذ بالله),
Shin mutumin da yake (tayar da bomb); ya QONA KANSA yana zaton wai aikata hakan sababi ne na shiga aljannah???!!!

Shin bai san cewa duk wanda ya KASHE KANSA yana cikin wuta ba,    Shin be ji, ko ya karanta faxin Allah (تعالى) ba ne:
"Kuma kada ku kashe kayukanku; lallai Allah ya kasance mai yin rahama ne a gare ku    *     Kuma duk wanda ya aikata haka, yana mai qetare iyaka, da kuma zalunci, to da sannu zamu shigar da shi cikin wata wuta, kuma aikata haka, akan Allah mai sauqi ne" [Nisa'i: 29-30].
Kuma ya zo cikin hadisi cewa "Lallai wanda ya kashe kansa yana cikin wuta".
            Kuma wanda ya kashe MUSULMI yana zaton cewa kashe shin sababi ne na shiga aljannah???!!! 
Shin bai san cewa KASHE MUSULMI  yana dawwamar da ma'abocinsa, a cikin wuta ba? Shin kuma bai ji, ko ya karanta faxin Allah (تعالى) ba ne:
"Duk wanda ya kashe wani mumini da ganganci to sakamakonsa shine jahannama, yana mai dawwama a cikinta, kuma Allah ya yi fushi da shi, ya kuma yi tattalin azaba mai girma agare shi" [Nisa'i: 93].
Kuma shin faxin Annabi (صلى الله عليه وسلم) bai iske su ba ne, a inda yake cewa:
"Duk wanda ya kashe kafirin amana ba zai ji qamshin aljannah ba".

            Shin waxannan mutanen ba za su xauki darasi daga waxanda suka gabace su; cikin masu aiki irin nasu ba ne; waxanda suka qetare iyakokin Allah, sai suka yi nidama a lokacin da nadamar ba ta yi amfani ba a gare su ba!  Haka kuma waxanda suka rikitar da su, ko suka ruxe su, suma basu iya amfanar da su da komai ba;

Duk wanda ya ce maka: ka je ka qona kanka, to sai ka ce: masa: Saidai shi, ya je ya qona kansa; kuma lallai ba zai aika hakan ba har abada;    saboda yana son ya jefa ka cikin wuta, ne,  
ya kuma yaqi 'yan'uwanka musulmai, da kai,   
ya kuma kawar da amincin da mutane suke cikinsa, da kai,
ya yaxa rashin nistuwa a cikin jama'a, da kai,   
ya kawo varna ko yaxa ta, da kai,   
ya zubar da jinanen haram tare da kashe musulmai da kai,
Sannan ya sanya ka, ka fice daga cikin jama'ar musulmai, da kuma yin fito-na-fito da shugabanninsu,     alhalin kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"Duk Wanda ya fice daga biyayyar shugaba, ya kuma vangare ga jama'ar musulmai, sai ya mutu to ya mutu irin mutuwar jahiliyya. Kuma duk wanda ya yi yaqi qarqashin tutar da aka jahilta yana yin fushi akan qabilanci, ko yana kira zuwa ga a raya qabilanci ko yana taimakon qabilanci sai aka kashe shi to shima kisansa irin na jahiliyya ne. kuma duk wanda ya fice daga al'ummata; yana ta dukan nagari da fajirin wannan al'ummah da takobi, kuma baya nisantar muminanta, baya kuma cika alqawarin kafiran da aka basu amana, to baya tare da ni, kuma nima bana tare da shi", Muslim da Abu-dawud suka rawaito shi, daga hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه).
A wani hadisin "Na hore ku da zama cikin jama'ar musulmai,   Duk kuma wanda ya fanxare to ya tafi cikin wuta".

Bayin Allah,,,

"Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan annabin,   Ya ku waxanda suka yi Imani, ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].
Manzon Allah kuma (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Duk wanda yayi mini salati guda xaya to Allah zai yi masa salati guda goma ".
Sai ku yi salati da sallama ga shugaban mutanen farko da na qarshe, kuma shugaban manzanni;
Ya Allah! Ka yi salati wa annabi Muhammadu da iyalan annabi Muhammadu kamar yadda ka yi salati wa annabi Ibrahima da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai a cikin talikai, Abun godiya ne, Mai girma.
Ya Allah! Ka yi albarka wa annabi Muhammadu da iyalan annabi Muhammadu kamar yadda ka yi albarka wa annabi Ibrahima da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai a cikin talikai, Abun godiya ne, Mai girma.
Kuma ka yi musu sallama; tsiratarwa mai yawa.
Ya Allah! Ka yarda da sahabbai gabaxaya, da kuma khalifofi shiryayyu, kuma shugabanni masu shiryarwa; Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu, da sauran sahabban annabinka gabaxaya, da waxanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar qarshe,
Ya Allah! Ka yarda da mu tare da su, da baiwarka, da rahamarka ya mafi rahamar masu rahama.
Ya Allah! Ka xaukaka musulunci da musulmai, ka kuma qasqantar da kafirci da kafirai,
Ya Allah ! ka kashe bidi'oi har zuwa ranar tashi qiyama;  
Ya Allah! Ka dusar da wutar bidi'a; wacce ta ke cin karo da addininka, kuma take cin karo da shari'arka,
Ya Allah! Ka kashe bidi'oi, har zuwa tashin qiyama, lallai kai mai iko ne akan komai.
Ya Allah!
Ya Allah!
Ya Allah!  
       Addu'oi;;;;;;;;;;;;;;;;
            ;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;

            ;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...