AZUMI RUKUNI NE
(ركن الصيام)
Azumi
shine rukuni na hudu daga cikin rukunnan Musulunci, saboda Manzon Allah –sallal
lahu alaihi wa sallama- ya ce:
"بٌني الإسلام على
خمس؛ -وذكر منها:- وصوم رمضان".
Ma'ana: "An gina musulunci akan ginshikai biyar; -daga cikinsu, sai ya
ambaci-, da azumin watan Ramadana" Bukhariy da Muslim.
Kuma azumin Ramadana yana wajaba ne,
akan: Dukkan musulmi, balagagge, mai hankali, mai iko, mazaunin gida (wand aba
matafiyi ba).
Kuma
shigowan watan Ramadana yana tabbata ne, ta hanyar ganin jinjirin wata da
kwayar ido, ko ta hanyar dube da na'urorin zamani, ko idan watan Sha'aban ya
cika kwanaki talatin, a halin rashin ganin jinjirin wata.
Kuma ba
a lura da lissafi irin na ilimin falaki.
Kuma
wajibi ne, a kwana da niyyar daukan azumi tun cikin dare. Kuma niyya guda daya
da aka yi ta a farkon wata, za ta isar, matukar ba a samu wani uzurin da ya
yanke ci-gaban aiki da ita ba, to a nan kam wajibi ne, a sake jaddada niyya.
Kuma
abinda azumi ke farlantawa shine/ kamewa daga ababn da suk karya azumi
(kamar ci da sha da biyan bukata), daga fudowar alfijir na gaskiya, har zuwa
faduwar rana.
Kuma duk wanda ya ci, ko ya sha, da
zaton rashin karewar dare, da rashin fudowar alfijir, ko kuma ya sha abin sha,
yana mai zaton rana ta fadi, Sai kuma kuskurensa ya bayyana masa, to azuminsa
ingantacce ne; saboda Annabi –sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce:
"إن الله وضع عن
أمتي الخطأ والنسيان وما استكرهوا عليه"، رواه ابن ماجه وصححه الألباني.
Ma'ana: "Lallai ne Allah ya daukee wa al'ummata abinda suka yi kuskure, da kuma
mantuwa, da abinda aka tilasta su akansa".
No comments:
Post a Comment