2018/09/26

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI صلى الله عليه وسلم JUMA'A, 18Muharram1440H daidai da 28Satumba 2018M للثببيتي












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 18/Muharram/1440H
daidai da 28/Satumba/ 2018M



LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH ABDULBARIY BN AWWADH AL-SUBAITIY





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
KA CE: LALLAI SALLATA
قل إنّ صلاتي
Shehin Malami wato: Abdulbariy bn Awwadh Al-Subaitiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: KA CE: LALLAI SALLATA, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan abinda ke tafe, Ya ce:

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya karrama jinsin Mutum; sai ya sanya shi ya zama khalifa a bayan kasa, ina yin yabo a gare shi Subhanahu kuma ina gode masa, akan ni'imar imani da falala.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya, wanda yin bauta a gare shi itace manufar samar da halitta.
Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa, ya tsawatar daga dabi'ar zage-zage da munanan halaye.
Allah yay i Karin salati a gare shi, da kuma iyalanSa da sahabbanSa, ma'abuta kyawawan zukata.
Bayan haka:
Ina yin wasici a gare ku da ni kaina da takawar Allah, Allah Ta'alah yana cewa:

"Ka ce: lallai ne sallata, da yankena-yankena, da rayuwata, da mutuwata, na Allah ne Ubangijin talikai * bashi da abokin tarayya, kuma da aikata hakan aka umurce ni, kuma ni ne farkon masu sallamawa", [An'am: 162-163].
Wannan aya mai karamci, ta zana hadafi da aiki da manufar wannan rayuwa, wanda kuma shine kasancewar Musulmi, da rayuwarsa da mutuwarsa, na Allah ne Ubangijin talikai, na Allah ne Mamallakin ranar sakamako, wanda ya halitta mu, kuma yake azurta mu,  kuma ya bamu kyautar wannan rayuwar.

Tilawar wannan ayar, da yin fadakarwa akanta, da yin tunani a cikin ma'anarta, yana rayar da fahimtoci masu girma, kuma yana jaddada ma'anoni masu tsada, wadanda ya wajaba kada su buya, ko su yi nisa ga kwakwale, ko su bace ta hanyar  fadawa cikin da'irar gafala da mantuwa, wanda kuma su ne: Ya kasance sallar Bawa, da yanke-yankensa, da rayuwarsa da mutuwarsa ga Allah ne, kuma ya kankan-da-kai cikin dukkan sha'anoninsa ga wanda ya halitta shi, kuma yake azurta shi, yake juya lamarinsa. Kuma Bawa a cikin dukkan lamuransa ya fiskanci ko ya nufi fiskar Allah da ikhlasi; har ya zama babu wani abin da Murum yake nufa idan ba Allah ba;
Kuma Mai nufin samun yardar UbangijinSa baya yin magana sai domin UbangijinSa, baya yin wani aiki sai domin UbangijinSa, a darensa da yininsa, da safiyarsa da maraicensa, saboda dukkansu na Allah ne shi kadai bashi da abokin tarayya.

Ayar tana tunatarwa kan samar da matsayi mafi daukaka, wanda shine yin bauta cikin dukkan abinda Musulmi ke aikatawa ko ya bari; yana mai imani da Allah, yana mai tsarkake niyya a gare shi, yana mai son Allah, yana shauki ko begensa, yana mai tsoronsa, yana fatan samun falalarsa, yana mai cin halal, da barin cin haram, da biyayyar iyaye, da sada zumunci, da kyautatawa makwabta, da kyautata halayya, da runtse idanu, da sanya hijabi, da da'awa zuwa ga Allah, da umurni da kyakkyawa, da hani ga mummuna.
Kuma idan bautar Allah ta samu gindin zama a cikin zuciya, to sai Mutum ya 'yantu daga yin bauta ga wanin Allah.

Fadinsa: "Ka ce: lallai ne sallata, da yanke-yankena", [An'am: 162-163].
"قل إنّ صلاتي".
Ginshiki ne na abubuwan da Bawa yake kusantar Ubangijinsa; Majibincinsa Mabuwayi da daukaka da shi; domi ginshikin ibadodin da suka fi girma shine/ Yin farillan da Allah ya wajabta su ga bayinSa.
Wanda kuma yake neman lada mai yawa, to sai ya karfafi yin farillansa da ibadodin nafilfili da sunnoni, kuma da aikata hakan Mutum zai samu soyayyar Allah, sai ruhinsa ta samu daukaka, ransa kuma ta tsarkaka, Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama-: "Lallai ne Allah yana cewa: Wanda ya yi adawa da waliyyina, hakika  ina shelanta yaki da shi, Kuma Bawana bai kusance ni da wani abu wanda yafi soyuwa a gare ni ba, fiye da abinda na farlanta akansa…
Kuma ba zai gushe yana kusantata da nafilfili ba, har sai na so shi, kuma idan na so shi sai in kasance jinsa da yake ji da shi, da ganinsa wanda yake gani da shi, da hannunsa wanda yake damka da shi, da kafarsa wanda yake tafiya da ita, kuma idan ya roke ni tabbas zan bashi, idan kuma ya nemi tsarina to lallai ne zan tsare shi", Bukhariy ya ruwaito.

Fadinsa: "Ka ce: lallai ne sallata, da yanke-yankena", [An'am: 162].
"ونسكي".
Ya nuna cewa lallai yanka domin Allah yana cikin manyan ibadodin da suka fi girma, kuma don haka ne Allah Ta'alah ya gwama ambaton ibadar yanka tare  da sallah a cikin fadinSa: "Saboda haka, ka yi sallah ga Ubangijinka, kuma ka soke (wato, rakumi)" [Kausar: 2].
Kuma wannan ibada ta yanka, lallai tana da gaya da manufofi, wanda aka shar'anta a cikin kowace shari'a; saboda Allah yana son ibadar yanka, kuma tana da yawan amfani.
Yanka domin Allah Ta'alah yana daga cikin ginshikan imani, kuma lamari ne daga cikin lamuran da tauhidin baya yake bayyanarwa, kuma yanka baya halatta a cikin Musulunci a gabatar da shi, face ga Ubangijin talikai.
Kuma dabbar da aka yanka tana zuwa a ranar Kiyama cikin fatarta da gashinta da kofatonta da dukkan abinda ke tattare da ita, a cikin ma'aunin Bawa, idan har yankan ya kasance domin Allah, ba domin wani abin da ba Allah ba; saboda ba a yin yanka domin gunki, ko bishiya, ko kabari ko waliyyi, kawai ana yin yanka ne domin Allah (سبحانه وتعالى) cikin tsarkin niyya da tauhidi.

Kuma yana daga cikin shirki ga Allah, gabatar da ibadodi da yanke-yanken dabbobin yanka, ba domin Allah Ta'alah ba, Aliyu –Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya gaya min kalmomi hudu: "Allah ya la'anci wanda ya yi yanka ga wanin Allah, Allah ya la'anci wanda ya tsine wa iyayensa, Allah ya la'anci wanda ya bada mafaka ga mai bidi'a, Allah ya la'anci wanda ya canza alamomin kasa", Muslim ya ruwaito shi.

Fadinsa: "da rayuwata, da mutuwata, na Allah ne Ubangijin talikai", [An'am: 162].
"ومحياي ومماتي لله رب العالمين".
Rayuwa ga Allah Ubangijin talikai, itace rayuwa akan addininSa da shari'arSa, da umurninSa da haninSa, a cikin dakikokinta, da bacin ranta da farin cikinta, da darenta da yininta, da kuma dukkan abinda ke cikinta na tsayuwa da zama, da motsawa da natsuwa, da barci da farkawa, da saye da sayarwa, da abinci da abin sha, da koyo da koyarwa, da kwadago da aiki, dukkan wannan, da waninsa, na Allah ne Ubangijin talikai.

Asara dukkan hasara, tana cikin ace Musulmi ya mance da wadannan ma'anonin, ya kuma manta da UbangijinSa, har ya wayi gari a dimauci cikin tafiyarsa, gafalalle daga hadafinsa da manufarsa a cikin rayuwa, sai ya yi shirki wa abin bautarSa Makadaici da UbangijinSa Mafi girma, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma kada ku kasance kamar wadanda suka manta Allah, sai ya mantar da su kayukansu" [Hashr: 19].


Musulmi yana da abin bauta ne guda daya, shine Allah, Mamallakin mulki, wanda ya nufi Mutum ya 'yantu daga dukkan ababen bauta, idan ba Allahn ba, kuma ya nufi rayuwar Bawa ta kasance da ayyukansa da mayar da lamuransa, zuwa gare shi; ba zuwa ga wanin Allah ba; sai ya rayu domin Allah, kuma cikin biyayyar Allah, "Kuma tsarki ya tabbata ga Allah, a lokacin da kuke shiga maraice, da lokacin da kuke shiga safiya * kuma godiya tasa ce, a cikin sammai da kasa, da kuma lokacin zawali" [Rum: 16-17].

Wannan rayuwar idan muka yi ta domin Allah, kuma daidai da ababen da suke yardar da shi, kuma muka so abinda Allah yake so, muka ki abinda Allahn yake ki, muka rika rayar da zukata da ambaton Allah, to lallai tabbas zata kasance rayuwa ce mai dadi da walwala, Allah Ta'alah ya ce: "Wadanda suka yi imani, sai zukatansu suka natsu da ambaton Allah, to lallai da ambaton Allah ne zukata ke samun natsuwa" [Ra'ad: 28].

Wannan kuma shine halin Musulmi a koyaushe, wato, lokaci ba zai shige alhalin yana nesa da UbangijinSa, da zikirinSa, da bautarSa ba, don haka Musulmi yake sallah, yake azumi, yake hajji, yake fitar da zakkar dukiyarsa, yake auna dukkan ayyukansa da ma'aunin shari'a da imani.

Kuma rayuwa ta kan kasance ta Allah ne Ubangijin talikai, idan aka yi amfani da lokacinta wajen aikin ginawa da bunkasawa, da kuma yin aiki da hankali wajen rayar da Duniya, da sana'a da noma, da gyara rayuwar al'ummai, da tabbatar da aminci da walwala, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma a lokacin da Ibrahimu ya ce: Ya Ubangijina! Ka sanya wannan gari (na Makkah) amintacce, ka azurta mutanensa, daga 'ya'yan itace, wanda ya yi imani daga cikinsu, da Allah da ranar lahira. Allah ya ce: wanda ya kafirta ma ina jiyar da shi dadi kadan, sa'annan kuma in tilasta shi zuwa ga azabar Wuta, kuma makomar ta munana", [Bakara: 126].


Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Mai rahama mai jin-kai. Mamallakin ranar sakamako.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, abin bautar nafarko da na karshe.
Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, majibinci masu takawa.
Allah ya yi dadin salati a gare shi da iyalansa da sahabbansa gaba daya.

Bayan haka:
Ina yin wasiyya a gare ku, da ni da bin dokokin Allah, Allah Ta'alah ya ce: "Ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah iyakar takawarsa kuma kada ku mutu face kuna Musulmai ", [Ali-imrana: 102].

Irin wannan Musulmi wanda ke mayar da rayuwarsa gaba dayanta ga Allah: ya kan zama kamar ruwan sama, duk wurin da ya sauka sai ya amfanar, wato, zai rika raya kyakkyawar fata a cikin zukata, ya rika karfafar aminta da Allah, yana yada jin-kai da tausayi a cikin rayuwa, yana barbaza alkhairi, yana ciyar da miskinai, yana tsayuwa akan sha'anonin raunanan Mutane da Marayu da Marasa lafiya, Allah Ta'alah ya ce:  "Kuma wanda ya rayar da wata rai, to lallai kamar ya raya Mutane ne gaba daya", [Ma'idah: 32].
Kuma duk wanda rayuwarsa ta kasance domin Allah, to ba zai jira sakamako ko godiya daga wanin Allah ba, zai cigaba da ayyukansa, ta yadda ba zai iya dakatar da shi ba; wanda ya yi ranga-ranga ga hanya, ko ya ke musa alherinsa ko ya ki godiya a gare shi,
Kamar harshen 'dayansu yana fadin: "suna cewa: Lallai ne mu, muna ciyar da ku ne domin newan yardar Allah, bamu nufin samun wani sakamako daga gare ku, kuma bamu nufin godiya * Lallai ne mu, muna tsoro daga Ubangijinmu wani yini mai gintsewa mai murtukewa * Sai Allah ya tsare musu sharrin wannan yinin, kuma ya hada musu annurin fiska da farin ciki * kuma ya saka musu -saboda hakurin da suka yi- da Aljannah, da tufafin alharir", [Insan: 9-12].

Sai ku yi salati –Ya ku bayin Allah- ga Manzon shiriya, saboda Ubangijinku ya umurce ku da aikata hakan, a cikin littafinsa a inda y ace: "Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati ga annabi Muhammadu da kuma iyalan annabi Muhammadu, kamar yadda ka yi salati ga annabi Ibrahima, da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai abin godiya ne mai girma.
Ya Allah! Ka yi albarka ga annabi Muhammadu da iyalan annabi Muhammadu, kamar yadda ka yi albarka ga annabi Ibrahima, da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai abin godiya ne mai girma.
Kuma ya Allah, ka yarda da khalifofi guda hudu masu shiryarwa, Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu, da sauran sahabbai da iyalan Annabi masu karamci, ka hada mu da su da afuwarka da baiwarka da kyautatawarka Ya mafi jin-kan masu jin-kai!
Ya Allah ka daukaka musulunci da Musulmai



2018/09/14

kawa'idul arba'a


                                                                                        
Bismillahir Rahmanir Rahim
Lallai yabo na Allah ne, muna gode masa, muna neman taimakonSa, kuma neman gafararSa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kayukanmu da munanan ayyukanmu, wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi, wanda kuma ya batar babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne ManzonSa. Bayan haka:
Matashiya a gabanin sharhi

 






LITTAFIN ALKAWA'IDUL ARBA'I shine littafi na biyu, da ake karanta su a cikin jerin littatafan da aka jeranta su ga dalibin ilimi (MUTUN DALIBIL ILMI). Yin sharhin wannan littafin ya ginu ne, akan sabbuba dayawa, daga cikinsu:
:
                                                                                                          
                                                                                                  
Saboda koyi da Magabata na kwarai
Saboda littafin Kawa'idul arba'i kamar takaicewan littafin KashfusShubuhat ne

Saboda nasihar da Malumanmu suka yi a gare mu (kan bashi muhimmanci).
.
La facilidad
Saboda a cikin littafin akwai yaye shubuhohin Mushirkan zamaninmu namu.

Za mu fara sharhin Kawa'idul Arba'i ne gabanin fara sharshin KashfusShubuhat; domin kada wata shubuha ta makale a zuciyar Dalibin ilimi.
 






ABUBUWAN DA SUKE CIKIN LITTAFIN KAWA'IDUL ARBA'I
Ana kasa wannan littafin zuwa kashi uku, kamar haka:


2.Muhimmancin karanta ilimin Tauhidi


3.Sai ka'idodi guda hudu (4)

1.Gabatarwa (sabuban jin dadi da walwala).

















                                                                                                           

Na daya: Gabatarwa (sabuban jin dadi da walwala)
Domin koyi da Maluman da suka gabace shi, da magabatan kwarai; wadanda cikin al'adarsu akwai bude littatafansu da sunan Allah. (Bismillah).

(1)SABABIN DA YA SANYA MAWALLAFIN YA FARI LITTAFINSA DA "BISMILLAH"


Domin koyi da littafin Allah, da Annabawa عليهم السلام.
Domin neman albarkar farawa da sunan Allah Mai-karamci.
Bismillahir Rahmanir Rahim
(1) Ina rokon Allah Mai karamci, Ubangijin Al'arshi mai girma, ya jibinci lamuranka, a nan duniya, da lahira (2). Kuma ya sanya ka zamo mai albarka a duk inda ka kasance (3).
(2) Bayan bismillah, sai Shehin –Allah ya yi masa gafara- ya fara littafinsa, da yin addu'a ga dalibin ilimi, kamar yadda ya saba. Wannan kuma dalili ne kauna da son da yake yi ga daliban ilimi, ta hanyar roka musu ya basu kowane alheri.
(3) Waliyyan Allah sune suka hada tsakanin imani da takawa, Sheikhul Islam Ibnu-Taimiyyah –Allah yay i rahama a gare shi- ya ce: "Wanda ya kasance mumini mai takawa, to shi waliyyin Allah ne". dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: {LALLAI NE MASOYAN ALLAH, BABU WANI TSORO AKANSU, KUMA BA ZA SU KASANCE CIKIN BAKIN CIKI BA}. [Yunus: 62-63].
 


















ALBARKA: Ita ce, bunkasar abu, da karuwarsa.
NEMAN ALBARKA: Yana nufin, neman bunkasarsa, da karuwarsa.
MAI ALBARKA: Shine, wanda ake amfana da shi a duk inda ya safka.


 
Kuma ya sanya ka daga wadanda idan aka basu, sai su yi godiya (1).

Neman albarka, wanda aka shar'anta.
Neman albarka, wanda aka hana, Wannan kuma shine neman albarkar da shari'a bata tabbatar da shi ba, kuma irin wannan yana cikin nau'ukan karamar shirka.

NEMAN ALBARKA YANA KASUWA KASHI BIYU:
ALBARKAR DA AKA RISKO (DA HISSI), Misalin ilimi da addu'a, da makamantansu, saboda mutum ana iya samun albarkar iliminsa da da'awarsa zuwa ga alkhairi, sai a kira hakan da: albarka, saboda yadda muka samu alheri mai yawa daga wurinsa, kamar littafan Sheikhul Islam Ibnu-Taimiyyah da waninsa, daga cikin Maluman da Allah ya sanya albarka da alheri a cikinsu, kuma al'umma ta amfana da su.



ALBARKA TA SHARI'A: Misalin sallah a Masallaci Mai alfarma, ko Masallacin Annabi (SAW).


(1) Ni'ima jarabawa ce, saboda dalilai dayawa, daga cikinsu akwai fadinSa: "KUMA MUNA MUKU IBTILA'IN SHARRI DA ALHERI, A MATSAYIN JARRABAWA", Da fadinSa "YAYIN DA YA GANSHI A TABBACE A WURINSA, SAI YA CE: WANNAN YANA DAGA FALALAR UBANGIJINA, DOMIN YA JARRABE NI; SHIN ZAN BUTULCE NE, KO ZAN YI GODIYA, KUMA WANDA YA YI GODIYA TO HAKIKA YANA YIN GODIYAR NE AKANSA, WANDA KUMA YA BUTULCE, TO LALLAI UBANGIJINA MAWADACI NE MAI KARAMCI", Da fadinSa: "AMMA MUTUM, IDAN UBANGIJINSA YA JARRABE SHI, SAI YA KARRAMA SHI, YA MASA NI'IMA, TO SAI YA CE: UBANGIJINA YA KARRAMA NI".
Ya zo cikin hadisi: "Lallai wasu Mutane uku daga Banu-isra'ila, Allah ya yi nufin ya jarrabe su".
 





















   Rataya zuciya ga Allah, gabanin samuwar ni'imah            
Godiya wa Allah, bayan aukuwar ni'ima, Kuma wannan yana kasancewa, da dayan:


               
ZUCIYA

HARSHE
GABBAI
NI'IMA TANA RATAYA DA TAUHIDIN RUBUBIYYA (AIKIN ALLAH) DA KUMA TAUHIDIN ULUHIYYAH (AIKIN HALITTU)
KUMA GODIYA A GARE TA, YANA KASUWA KASHI BIYU:
:
Wannan nau'in kuma, yana neman bawa ya samar da kuduri da imani na yakini cewa lallai Mai bada ni'ima shine Allah SWT, don haka, ba zai rataya zuciyarsa ga wanin Allah ba, kuma ba zai nemi wani alheri ba, face daga Allah.
Kuma, kamar yadda Aljannah ana nemanta ne daga Allah SWT, saboda shine ya mallake ta, to haka arziki, ba zai yiwu a nemi shi ba, face daga Allah SWT.
"KUMA KAYI TAWAKKALI GA RAYAYYEN DA BAYA MUTUWA".
"LALLAI WADANDA KUKE BAUTA MUSU KOMA BAYAN ALLAH, BASU MALLAKA MUKU ARZIKI, SAI KU NEMI ARZIKI DAGA ALLAH" (Wato, ku nema daga Allah, ba daga waninsa zaku nemi arziki ba) "KUMA KU BAUTA MASA, KU YI GODIYA A GARE SHI".


Wannan kuma ta hanyar salwantar da ni'imar ta fiskar da zata yardar da Ubangijinmu Mabuwayi da daukaka akanmu. Tare da kara ayyukan da'a da nufin kusantarSa Mai tsarki da daukaka, da kuma nisantar ayyukan sabo, da nufin bin umarninSa.
Wannan kuma, ta hanyar yin zance kan ni'imar Allah, da yin godiya a gare shi, da yabonSa, da yin jinjina a gare shi SWT, saboda fadinSa Madaukaki: "KUMA AKAN NI'IMAR UBANGIJINKA, SAI KA BADA LABARI (da nufin godiya)".
Wannan yana kasancewa, ta hanyar gaskiyar imani da akida, da cikakken sallamawa, cewa Mai azurtawa Mai bada ni'ima shine Allah Subhanahu Wa Sa'alah, kuma lallai dukkan abinda ke tare da bawa na ni'ima, to daga wurin Allah ne SWT.



 

















(1)    Wannan kuma saboda hakuri wajibi ne, da ijma'in maluma.



Mutane a lokacin da musibun duniya suka sauka akansu suna kasuwa kashi hudu:

Kuma idan aka masa ibtila'i sai ya yi hakuri (1)
 




Mai yin godiya
Mai yarda
Mai nuna bacin Rai
Mai hakuri
                                                                                               

1. NUNA BACIN RAI: a lokacin musiba haramun ne, kuma zunubi ne babba daga cikin manyan zunubai, kuma hakan ya kan kasance ko dai da:

Gabbai
Harshe
Zuciya
 



-          BACIN RAN ZUCIYA: Imam Ibnu-Kayyimil Jauziyyah, ya fadi maganar da ma'anarta shine, Lallai wasu mutane harshensu ba zai yi azarbabiyar fadin maganar bacin rai, Sai dai kuma zuciyarsu da take cikin kirjinsu, tana shaidar da hakan, ta yadda yake mummunan zato ga UbangijinSa, har yake fada a cikin zuciyarsa cewa, Ubangijina ya zalunce ni, Ubangijina ya haramta mini, Ubangijina ya hana ni, ... da makamancin haka, kuma a cikinsu akwai mai yin hakan a cikin zuciyarsa dayawa, wani kuma kadan. Sai ka bincika Ranka, shin ka kubuta daga wannan; domin idan ka zama ka kubuta, to lallai ka kubuta daga musiba mai girma.
-          NUNA BACIN RAI DA HARSHE: Wannan ya kan kasance ta hanyar ihu, shewan mutuwa, da kiran bone da bala'i da halaka, da tsinuwa da la'anta, da zage-zage.
-          NUNA BACIN RAI DA GABBAI: Wannan kuma ya kan kasance ta hanyar marin fiska, da yaga wuyar riga, da tuzge gashi.
2. HAKURI: Hukuncinsa wajibi ne, da ijma'in Maluma. Kuma wajibi ne mutum ya yi hakurin musibar da ta auku masa da zuciyarsa, da harshensa, da kuma gabbansa.
Imam Ahmad yana cewa: "Hakuri ambatonsa ya zo a cikin Alkur'ani, a kusan wurare casa'in, kuma shi wajibi ne, da ijma'in Maluman al'ummah. Kuma hakuri rabin imani ne, saboda imani ya rabu gida biyu, rabinsa hakuri, rabinsa godiya" [littafin MadarjisSalihina na Ibnul-Kayyim].
3. MATSAYIN YARDA: Hukuncin kaiwa matsayin yarda da musiba mustahabbi ne, kuma wannan martaba ce da tafi girma akan matsayin hakurtar da kai.
4. GODIYA: Hukuncin kaiwa matakin gode wa Allah ga musibu mustahabbi ne, kuma shine matakin da yafi sauran girma da cikar kamala.




,

 
Na biyu: Ka'idodi guda hudu
 

Bismillahir Rahmanir Rahim
Ka sani –Allah ya shiryar da kai ga aikin biyayya a gare shi-: Lallai Mikakken addini irin na annabi Ibrahima shine, ka bauta wa Allah, kana mai tsantsanta nufin addini a gare shi, kamar yadda Allah Ta'alah ya fada: "KUMA BAMU HALITTA MUTUM DA ALJAN BA SAI DON SU KADAICE NI DA BAUTA"(1).
Kuma idan ka san cewa, Allah ya halitta ka ne, domin bauta, to ka sani:
Lallai bauta bata zama bauta, sai an kadaita Allah da ita (Tauhidi), kamar yadda salla bata cin sunan sallah sai idan an yi ta da tsarki. Kuma idan shirka (nufin wani da ibada tare da Allah) ta shiga cikin bauta, sai ibadar ta lalace, kamar yadda hadasi idan ya shigar ma tsarki.
Kuma idan ka san cewa, lallai shirka idan ya cakuda da ibada, yak an lalata ta, ya rushe dukkan aiki, sai ma'abucinsa ya kasance daga masu dawwama a cikin wuta, a nan za ka san cewa lallai abinda yafi muhimmanci a gare ka, shine: Sanin hakan, da fatan Allah ya tsamar da kai daga wannan tarko, wanda shine shirka ga Allah, wanda yake magana akansa: "LALLAI ALLAH BAYA GAFARAR AYI MASA SHIRKA, AMMA YANA GAFARTA ABINDA BAI KAI HAKA BA, GA WANDA YA YI NUFI", [Nisa'i: 116].
Wannan kuma zai kasance ta hanyar sanin ka'idodi guda hudu, wadanda Allah Ta'alah ya ambace a cikin littafinSa:
KA'IDAR FARKO: Ka sani, lallai kafiran da Manzon Allah –sallal lahu alaihi wa sallama- ya yake su, suna masu tabbatar da cewa lallai Allah Ta'alah shine Mahalicci Mai jujjuya lamura, amma hakan bai shigar da su cikin musulunci ba, Dalili kuma akan wannan shine fadinSa Madaukaki: "KA CE: WANENE KE AZURTA KU DAGA SAMA DA KASA, KUMA WANENE YA MALLAKI JI DA GANI, KUMA WANENE KE FITAR DA RAYAYYE DAGA MATACCE, KUMA YAKE FITAR DA MATACCE DAGA RAYAYYE, KUMA YAKE JUJJUYA LAMARI, LALLAI ZA SU CE, ALLAH NE, KA CE: SHIN BA ZA KU YI TAKAWA BA"(2). 
(1) Mawallafin –Allah ya yi masa rahama- ya gaya mana, dalilin da ya sanya muke karanta Tauhidi.
(2) Kafiran da aka turo Annabi –S.A.W- a cikinsu, sun kasance basu jayayya, ko in ce, suna tabbatar da Tauhidin Rububiyya (wato, kadaitakar Allah cikin ayyukansa), tare da haka, Sai Manzon Allah –S.A.W- ya yake su; wannan kuma saboda husumar da take tsakaninsu da tsakanin Annabi –S.A.W- ta kasance ne, cikin Tauhidin Uluhiyyah (Kadaita Allah da ayyukan bayi); Don haka, duk wanda ya yi wani abu na ibada ga wanin Allah, to mushirki ne kafiri.   



KA'IDA TA BIYU: Lallai ne kafiran da Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya yake su suna cewa: Bamu roki ababen bautarmu muka fiskance su ba, sai domin neman kusanci, da kuma ceto. Shi kuma dalilin neman kusanci shine fadinSa Madaukaki: "WADANDA KUKA RIKA BAICINSA A MATSAYIN MAJIBINTA; SUNA CEWA: BA MU BAUTA MUSU, SAI DON SU KUSANTAR DA MU ZUWA GA ALLAH, KUSANCIN DARAJA, LALLAI ALLAH ZAI YI HUKUNCI A TSAKANINSU GA ABINDA SUKA KASANCE SUNA SABAWA A CIKINSA, LALLAI ALLAH BAYA SHIRYAR DA WANDA YAKE ME KARYA, MAI KAFIRCI" (1).
Dalilin neman ceton ababen bautarsu kuma shine, FadinSa Madaukaki:  "KUMA SUNA BAUTA WA BAICIN ALLAH, ABINDA BAYA CUTAR SU, KUMA BAYA AMFANINSU, KUMA SUNA CEWA: WADANNAN MACETANMU NE A WURIN ALLAH" [Yunus: 18].
Kuma ceto, nau'i biyu ne, ceton da aka kore, da ceton da aka tabbatar(2).


(1)               Ma'abuta shirki da kafirci suna kafa hujja, da cewar su basu roki ababen bautarsu na banza ba, koma bayan Allah, kuma basu fiskance su ba, sai don su kusantar da su, ga Allah, su cece su. Kuma da aikata hakan sun cancanci Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya kafirta su, sa'annan ya yake su.
(2)               Kalmar shafa'a: A harshen larabci, ta samu ne daga Tarawa, ko sanya abu  daya ya zama biyu (shafa'i).
A shari'a kuma: Shafa'ah, tana nufin zamowa tsani ga wani, wajen janyo masa amfani, ko tunkude masa wata cuta.





CETON DA AKA KORE: Shine ceton da ake nemansa daga wanin Allah, cikin abinda babu wanda ke iya yinsa sai Allah, Dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "YA KU WADANDA SUKA YI IMANI, KU CIYAR DAGA ABINDA MUKA AZURTA KU, GABANI WANI YINI YA ZO WANDA BABU CINIKI A CIKINSA, KUMA BABU ABUTA, KUMA BABU CETO, KUMA KAFIRAI SUNE AZZALUMAI" [Bakara: 254].
Shi kuma CETON DA AKA TABBATAR: Shine ake nemansa daga Allah, Shi kuma wanda aka karbi cetonsa an karfafa shi da karbar cetonsa, Wanda kuma za a karbi ceto akansa shine wanda Allah ya yarda da zancensa da ayyukansa –bayan ya bada izini-, kamar yadda Allah Ta'alah ya ce: "BABU WANDA ZAI YI CETO A WURINSA, FACE DA IZININSA" [Bakara: 255].
KA'IDA TA UKU (1): Lallai Annabi –sallal lahu alaihi wa sallama- ya bayyana ne, ga mutanen da suke a rarrabe cikin ibadodinsu; daga cikinsu akwai wanda ke bautar Mala'iku, daga cikinsu akwai wanda ke bautawa Annabawa da Salihai, daga cikinsu akwai ke bautawa bishiyoyi da duwatsu, daga cikinsu akwai wanda ke bautawa rana da wata, sai Manzon Allah –sallal lahu alaihi wa sallama- ya yake su, bai rabe wani daga cikinsu ba.
Dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "KUMA KU YAKE SU HAR WATA SHIRKA BAZA TA KASANCE BA, KUMA ADDINI DUKANSA YA KASANCE NA ALLAH" [Anfal: 39].
Kuma dalilin suna bautar rana shine fadinSa Madaukaki: "KUMA YANA DAGA AYOYINSA; DARE DA YINI, DA RANA DA WATA, KADA KU YI SUJADA GA RANA, KADA KU YI GA WATA, SAI KU YI SUJADA GA ALLAHN DA YA HALITTA SU, IDAN KUN KASANCE A GARE SHI KAWAI KUKE YIN BAUTA" [Fussilat: 37].
Kuma dalilin suna bautar Mala'iku shine fadinSa Madaukaki: "KUMA BAYA UMARTARKU, DA KU RIKI MALA'IKU DA ANNABAWA ABABEN BAUTAWA ..." har zuwa karshen ayar [Ali-imrana: 80].
(1)     Wannan ka'idar dalili ne, karara, a fili, wanda ke raddi ga wanda ke cewa: Lallai shirka, kawai tana kasancewa ne, cikin bautar sassaken gumaka. saboda, Dalilan shari'a sun zo akan gumakan, da sauran lalatattun ababen da ake bauta musu koma bayan Allah, a wancan zamanin, saboda Manzon Allah –sallal lahu alaihi wa sallama- bai rabe tsakaninsu ba, hasalima ya kirga su gaba dayansu a matsayin Dagutun da ake bauta musu koma bayan Allah, sai ya yake su ba tare da ya toge wasu ba; wannan kuma domin addini gaba dayansa ya kasance ya kebantu da Allah.


Kuma dalilin suna bautar Annabawa shine fadinSa Madaukaki: "KUMA A LOKACIN DA ALLAH YA CE: YA ISA 'DAN MARYAM! SHIN KAI NE KA CE WA MUTANE, KU RIKE NI, NI DA UWATA, ABUBUWAN BAUTAWA BIYU, BAICIN ALLAH? ISA YA CE: TSARKINKA YA TABBATA, BA YA KASANCEWA A GARE NI IN FADI ABINDA BANI DA WANI HAKKI A CIKINSA, IDAN NA KASANCE NA FADE SHI, TO LALLAI KA SAN SHI, DOMIN KA SAN ABINDA KE CIKIN RAINA, KUMA BANI SANIN ABINDA KE CIKIN RANKA, LALLAI NE KAI MASANIN ABUBUWAN DA SUKE FAKE NE" [Ma'ida: 116].
Kuma dalilin suna bautar Salihai shine fadinSa Madaukaki: "SUNE WADANCAN DA SUKE ROKO, SUKE NEMAN KUSANCI, WANENE A CIKINSU YAFI KUSANCI, KUMA SUNA FATAN RAHAMARSA, KUMA SUNA TSORON  AZABARSA" [Isra'i: 57].
Kuma dalilin suna bautar bishiyoyi da duwatsu shine fadinSa Madaukak: "SHIN BAKU GANIN GUNKIN LATA DA UZZAH *DA WANI GUNKIN WAI SHI MANATA NA UKUNSU" [Najm: 19-20].
Da hadisin Abu-Wakid Allaisiy –Allah ya kara yarda a gare shi-, ya ce: Mun fita tare da Annabi –sallal lahu alaihi wa sallama- zuwa Hunain, alhalin muna sabin ficewa daga kafirci. Alhalin mushirkai suna da bishiyar magarya wanda suke lazimtatrta, kuma suke rataya makamansu, suna kiran bishiyar da suna, ma'abuciya takkuban da ake ratayawa, sai muka shige ta jikin wannan bishiyar, sai muka ce: Ya Ma'aikin Allah! Muma ka sanya mana bishiyar ratayawa, kamar yadda mushirkai suke da bishiyar rataye tokobai... har karshen hadisin. 



KA'IDA TA HUDU: Lallai mushirkan zamaninmu sun fi munin shirka, akan mushirkan farko, saboda na farkon sukan yi shirki ne a halin walwala, sai su yi ikhlasi ga Allah a lokacin tsanani. Su kuma mushirkan zamaninmu shirkarsu a dawwame take; a halin wadaci da tsanani, Dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "KUMA IDAN SUKA SHIGA JIRGIN RUWA, SAI SU KIRAYI ALLAH, SUNA MASU TSARKAKE ADDINI A GARE SHI, TO A LOKACIN DA YA TSIRATAR DA SU ZUWA GA TUDUN KASA, SAI GASU SUNA SHIRKI" [Ankabut: 65],(1).
Allah shine Mafi sani.
Salatin Allah su kara tabbata ga annabi Muhammadu, da iyalanSa, da sahabbanSa, tare da sallama.

(1)    Mawallafin –Allah ya yi masa rahama- a cikin wannan ka'idar, ya bayyana girman hatsarin mushirkan wannan zamani; saboda sun fi tsananin shirki, akan mushirkan farko; saboda mushirkan zamaninmu suna yin shirka ne ga Allah a cikin tsanani da yanayin walwala, yayin da su kuma mushirkan farko su ke yin shirka a lokutan walwala, suke tuna Allah da kadaitakarSa, a lokacin tsanani.
Don haka; Idan har kafiran da aka turo Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- sun fi karancin shirka, sai kuma Allah ya kafirta su, To yaya lamarin zai kasance, kan wadannan da shirkansu dawwamamme ne; a cikin halin lafiya da cuta; kenan, sune suka fi cancantar zamowa kafirai.


LITTAFIN KAWA'IDUL ARBA'I; Wanda kamar takaicewa ne ga littafin KASHFUS-SHUBUHAT
MATASHIYA; a cikinta an kawo sabuban samun walwala
SABUBAN SAMUN WALWALA
Idan aka bashi sai ya yi godiya
Idan aka masa ibtila'i sai ya yi hakuri
NI'IMA IBTILA'I CE, Dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "KUMA MUNA JARABTARKU DA SHARRI DA KUMA ALHERI A MATSAYIN JARABAWA".
YANAYIN MUTANE LOKACIN SAUKAR MUSIBA
GODIYAR NI'IMAH
GODIYAR DA TA RATAYA DA TAUHIDIN RUBUBIYYA
WANDA TA RATAYA DA TAUHIDIN ULUHIYYAH
Neman Aljannah baya kasancewa sai daga Allah, saboda shine SWT ya mallake ta, to haka arziki shima, ba a nemansa, face daga Allah; don haka Babu makawa kan rataya zuciya ga Allah, ba ga waninsa ba.
YA YI GODIYA DA ZUCIYARSA:
Ta hanyar tabbatarwa cewa duk wani abinda ke tattare da shi na ni'ima, to daga Allah  ne; ba daga waninsa ba.
YA YI GODIYA DA HARSHENSA:
Ya ce: "WANNAN DAGA FALALAR UBANGIJINA NE, DOMIN YA JARRABE NI; ZAN YI GODIYA NE, KO ZAN BUTULCE".
YA YI GODIYA DA GABBANSA:
Ta hanyar sarrafa wannan ni'imomin cikin godiya wa mai bada ni'imomi. Kuma kowace ni'ima da yanayin yadda ake mata godiya; don haka godiyar ni'imar dukiya ita ce, shine ya ciyar da ita cikin biyayya ga Allah, godiyar ni'imar ilimi kuma ya rika bayar da shi, ga wanda ya yi tambaya da harshensa, ko kuma yake bukata.
MAI NUNA BACIN RAI: Hukuncinsa haramun ne, kuma daya daga manyan zunubai, har ma zai iya kaiwa zuwa ga karamar shirka, kuma lallai nuna bacin rai kan kasance, ko dai da; zuciya, ko da harshe, ko da gabbai.
MAI HAKURI: Hukuncin hakuri a yanayin musiba wajibi ne, da ijma'in Maluman al'ummah. Kuma zai yi hakurin ne da zuciyarsa, da harshensa, da kuma gabbansa. Kuma hakuri ya ci sunansa; domin dandana shi akwai daci, sai dai abinda ke haifarwa zakinsa yafi na zuma.





KA'IDODI GUDA HUDU (القواعد الأربع)


Idan kuma ya yi zunubi sai ya tuba
Don me, muke karanta ilimin Tauhidi?
Da bayanin hatsarin shirka
KA'IDAR FARKO: Lallai kafiran da Manzon Allah –sallal lahu alaihi wa sallama- ya yake su, sun kasance suna tabbatar da Tauhidin Rububiyyah, sai dai basu kasance suna tabbatar da Tauhidin Uluhiyyah ba, sai ya zama hakan bai shigar da su cikin Musulunci ba.
KA'IDA TA BIYU: Lallai kafirai sun kasance suna bautar gumaka ne, domin su kusantar da su ga Allah, su cece su.
KA'IDA TA UKU: Lallai Annabi –sallal lahu alaihi wa sallama- ya bayyana ne ga mutanen da suke a rarrabe cikin yanayin bautarsu, sai bai ware wani shirkan akan wani ba (duka ya yi fatali da su).
KA'IDA TA HUDU: Lallai Mushirkan zamaninmu sun fi girman shirka akan mushirkan farko.
MAI YARDA: Hukuncin samun yarda ga musiba mustahabbi ne, kuma idan yardar bawa ga UbangijinSa ta cika, zai san cewa, Dukkan abinda ya same shi, to daga Allah ne, Duk kuma abinda Allah ya kaddara shi ga bawa to alheri ne.
MAI GODIYA: Gode wa Allah ga musibu shine matakin da yafi sauran girmar martaba, kuma shine abinda yafi soyuwa. Mai yinsa kuma yana kasancewa ne daga cikin bayin Allah masu godiya.
MIKAKKEN ADDINI (Haniyfiyyah): Addinin Annabi Ibrahim, Lallai Allah ya halitta ka, domin yin bauta a gare shi, ita kuma bauta ba a kiranta da suna ibada, sai tare da tauhidi, saboda shirka idan ta cakudu da ibada, sai ta lalata ta, ta kuma rushe dukkan ayyuka, sai ma'abucinta ya wayi gari daga masu dawwama a cikin wuta; don haka shirka ita ce mafi muhimmancin abinda ya wajaba ka sanshi.



JARABAWAR LITTAFIN KA'IDODI HUDU (KAWA'IDUL ARBA'I)
SUNANKA ..................................................................
YAWAN ABINDA KA HARDACE DAGA LITTAFIN "kitabut Tauhid".....................................
SHIN KA HADDACE LITTAFIN: KA'IDODI HUDU (القواعد الأربع) .............................................
AIKI
DALILINSA DAGA ALKUR'ANI KO HADISI
Ni'ima ibtila'i ne

Kafirai sun tabbatar wa Allah Rububiyya

Bautar alloli don neman su kusantar da mai yinsu ga Allah

Nau'in ceton da aka kore

Dalilin cewa kafirai suna bautar Rana da Wata

Dalilin suna yin bautar Mala'iku

Dalilin suna yin bautar Annabawa

Dalilin suna yin bautar Salihan Bayi

Dalilin suna bautar duwatsu da bishiyoyi

Mushirkan farko suna tsarkake tauhidi a lokacin tsanani, sai kuma su yi shirka a lokacin wadaci

Dalilin da ke kaiwa ga shirka





RUBUTA ABINDA KA SANI KAN ABUBUWAN DA SUKE TAFE:
Me ya sa muke karanta ilimin Tauhidi?
1.                                           2.
3.                                           4.
5.                                           6.                                           7.
8.                                           9.
Me ya sa muke karanta littafin ka'idodi hudu (القواعد الأربع)?
1.                                          
2.

LITTAFIN KA'IDODI HUDU ANA KASA SHI ZUWA KASHI
1.                          2.                        3.                                          
Littafin Ka'idodi hudu, kamar takaicewa ne ga littafin

Me ya sa ba za mu fara da karatun littafin Kashfus Shubuhat ba?

Alamomin samun walwala da jin dadi
1.                          2.                        3.                                          
Mikakken addini (Hnaiyfiyyah) shine:

Fa'idan karanta littafin ka'idodi hudu

Waliyyan Allah, sune
Sheikhul Islam Ibnu-Taimiyyah ya ce:
Dalili akan haka

Don me:
Godiya akan ni'ima tana kasancewa, da, tare da misali
1.
2.
3.
Ta yaya bawa zai rataya ga Ubangiji wajen neman ni'ima?

Halayen Mutane a lokacin saukar musiba, da hukuncinsu:
1.      .................,,, hukuncinsa,     kuma yana kasancewa ta .....      da             da

2.      .................,,, hukuncinsa,     kuma yana kasancewa ta .....      da             da
3.
4.
Ceto (shafa'ah) a harshen larabci:

Shafa'a a shari'ah:

Ceto yana kasuwa zuwa kashi:
1.
2.
Sharuddan ceto tabbatacce:
1.
2.
3.
Kuma tana kasuwa zuwa:
1.
2.
1-          Shi kuma ya kasu zuwa:             da               da
1.         Shi kuma ya kasu zuwa:             da               da

2.            Shi kuma ya kasu zuwa:             da               da
KA'IDAR FARKO:


KA'IDA TA BIYU:


KA'IDA TA UKU:


KA'IDA TA HUDU:


Hukuncin aikin da shirka ta shiga cikinsa
Dalili:


           


   1
Matashiya kan sabubban samun walwala
56
   2
Ka'idar Farko
60-61
3
Ka'ida ta Biyu
62-64
4
Ka'ida ta Uku
64-65
5
Ka'ida ta Hudu
66
6
Sharhin littafin a takaice a cikin jadwala
67-68
7
Jarabawa kan littafin ALKAWA'IDUL ARBA'I
69-72
8
Fihirisa (abinda ke cikin littafin).
73



TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...