2018/05/15

AZUMI AKAN WA YAKE WAJABA?

AZUMI AKAN WA YAKE WAJABA?
10. Azumi yana wajaba ne, akan kowane Musulmi, balagagge, mai hankali, mazaunim gari (ba mai bulaguro ba), mai ikon zartar da shi, wanda ya kubuta da ababen da suke hana azumin, kamar haila da jinin haifuwa.
11. Ana umartar karamin yaro da yin azumi, tun daga shekaru bakwai, idan har zai iya azumin, Kuma wasu ma'abuta ilimi sun ce, za a iya dukansa idan ya kai shekaru goma; sai bai yi azumin ba, kamar lamarin sallah.
12. Idan kafiri ya musulunta, ko karamin yaro ya balaga, ko mahaukaci ya warke, a tsakiyan yinin azumi, to wajibi ne akan wadannan su kame bakunansu daga cin abinci, ga abinda ya rage na wannan yinin. Sai dai ba wajibi ba ne, su yi ramukon kwanakin da suka gabaci haka; na wannan watan.
13Mahaukaci an dauke alkalami akansa. Amma idan ya kasance yana yin haukan ne, cikin wani lokaci, sai kuma ya warke a wasu kwanakin, to wajibi ne akansa ya yi azumin kwanakin da yake da lafiyar hankali, banda kwanakin da yake cikin hauka. Kuma mai farfadiya misalin irin wannan ne cikin hukunci.
14. Wanda ya mutu, a tsakiyan watan azumi, to babu komai akansa, ko ga waliyansa, na azumtar kwanakin da suka rage a karshen wannan watan.
15. Wanda ya jahilci wajabcin azumi a cikin Ramadhana, ko ya jahilci haramcin cin abinci ga mai azumi, ko jima'i, to jamhurin malamai da suka fi yawa sun tafi akan bashi uzuri, idan kamarsa za a iya masa uzuri. Amma wanda ya kasance a tsakiyar al'ummar Musulmai, kuma zai iya yin tambaya ko ya koya, to wannan kam bashi da wani uzuri.

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...