GABANIN 'DANKA YA SHIGA MAKARANTA
(قبل
أن يدخل ولدك المدرسة)
Tarjamar
Abubakar Hamza
Neman Makaranta mai kyau, da Malamai zaka-kurai, da kayayyakin
Makaranta, lamura ne da iyaye ke bincike akansu, domin shirin shigar da
'yayansu ga Makaratu.
Saidai wadannan ababen duk da muhimmancinsu, ba za su isar ba, su kadai,
wajen sauke nauyin abinda ya wajaba na tarbiyyar Yara. Saboda tarbiyyar Yara ta
fiskar halayyansu da 'dabi'unsu amana ce, da daukanta a farkon fari ke wuyan
Uwa da Uba, a cikin gida, domin
"Namiji a cikin gidansa
mai kiyo ne, kuma shi abin tambaya ne kan abinda akabashi kiyo. Kuma itama Mace
a cikin gidan mijinta mai kiyo ce, kuma ita abar tambaya ce akan abinda aka
bata kiyo", Bukhariy da Muslim. Wannan ya nuna, bada kulawa ga
'ya'ya ya kan fara ne tun suna kanana, gabanin a shigar da su Makarantu; Ta
hanyar
shuka ma'anonin tsoron Allah da girmama shi a
cikin zukatansu,
da karantar da su Alkur'ani mai karamci,
da wasu daga cikin hadisan Annabi –sallal Lahu
alaihi wa sallama-,
da tarbiyyantar da su akan ladduban Musulunci,
a cikin lamuran ci da sha, da ladduban barci da kuma tasowa daga gare shi, da
makamantansu.
Da nuna musu muhimmancin yin salla akan
lokacinta, ta hanyar Mahaifi ya bada misali abin koyi, da gamammen kwadaitarwa,
Haka kuma jiyar da su kissoshin musulunci da
tarbiyya, wadanda za su shuka manyan fahimtoci a zukatan yara, su kuma bunkasar
da bangarorin alkhairi da gyaruwan halaye a tattare da su.
Kuma
rawan da iyaye ke takawa ta tarbiyya, bata karewa, wai domin 'ya'yansu sun
shiga makarantu, a'a, bal, za su kara da lamarin fadakar da 'ya'yan kan girmama
da karrama malumansu,
Da karfafa su kan zaben abokai natsattsu
wajen dabi'unsu da halayensu,
Da bibiyar ababen da suke daukowa daga
Makaranta; na darrusa da nau'ukan tunani,
Da basu damar yin wasa, wanda zai tafi tare
da bukatar yaro, da kuma yawa ko karancin shekarunsu, tare da zaba musu nau'ukan
wasanni masu amfani, da nisatar da su irin wasannin da suke zaburar da yaro kan
keta, da munanan dabi'u.
Ayyukan
iyaye biyu -kenan- suna da girma, kuma wajibin da ke kansu babba ne,
Ibnul-kayyim –Allah yay i masa rahama- yana cewa:
"BABU
ABINDA KE BATA TARBIYYAR 'YA'YA, FIYE DA GAFALA DA KO-OHON IYAYE DA KYALE
YARAN, KUMA SAU DAYAWA UBA YANA HARAMTA WA 'DANSA ALHERIN DUNIYA DA LAHIRA,,,
KUMA DUKKAN WANNAN YANA DAGA ABABEN DA SAKACIN IYAYE KAN HAKKOKIN ALLAH DA
TOZARTA SU, DA JUYA BAYANSU GA ABINDA ALLAH YA WAJABTA SHI AKAN IYAYE; NA NEMAN
ILIMI MAI AMFANI DA YIN AIKI NA-KWARAI KE HAIFARWA" (Tuhfatul
Maudud: 240).
No comments:
Post a Comment