2018/08/31

HAKKIN ALLAH DA HAKKOKIN IYAYE Huzaifiy 20 zulhijja 1439H الحقوق الواجبة












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 20/ZULHIJJAH/1439H
daidai da 31/AUGUST/ 2018M




LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH ALIYU BN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
HAKKOKI NA WAJIBI
(HAKKIN ALLAH DA NA IYAYE BIYU)
Shehin Malami wato: Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: HAKKOKI NA WAJIBI, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO

Yabo ya tabbata ga Allah; wanda ya yi falala ga bayinsa; sai ya yi bayanin HAKKOKIN da su ke kansu DA WAJIBAI, kuma ya yarje musu aiyuka masu kyau, ya kuma sanya musu kin munanan ayyuka, ya yi alkawarin alkhairori ga salihan bayi,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya, sai Allah shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya, Mai amsa addu'oi,
kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawansa ne Manzonsa, Wanda aka karfafe shi da mu'ujizozi.
Allah ka yi dadin salati, da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka; Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa, masu taimakon addinin Allah, da jihadi da kuma hujjoji bayyanannu,

Bayan haka:
Ku bi Allah da takawa; kada ku tozarta farillanSa, kuma kada ku ketare dokokinSa, kuma lallai wanda ya yi takawa, ya samu babban rabo, wanda kuma ya bi son zuciya ya tabe,

Ya ku, Bayin Allah… !!!
Ku sani
Lallai ayyukan bayi, sakamakonsu nasu ne, ukubar ayyukan kuma akansu ne, saboda biyayyar bawa bata amfanar da Allah, kuma aikata sabo baya cutar da Allah, Allah (تعالى) ya ce: "Wanda ya aikata aikin kwarai, to, domin kansa ne,  wanda kuma ya munana, to, a kansa. Sa'annan zuwa ga Ubangijinku za a mayar da ku" [Jasiya: 15].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Wanda ya aikata mummunan aiki, ba za a sakanta masa ba, face da kwatankwacinsa, wanda kuma ya aikata aiki na kwarai, daga namiji ko mace, alhali yana mumini, to wadannan za su shiga Aljanna, ana ciyar da su a cikinta, ba da lissafi ba" [Gafir: 40].
Kuma Allah Mabuwayi da daukaka a cikin hadisin kudusi ya ce: "Lallai ku, ba za ku kai ga cutar da ni ba, balle ku cutar da ni, kuma ba za ku kai ga amfanar da ni ba, balle ku amfanar da ni, Ya ku bayina! Lallai wadannan ayyukanku ne, na ke kididdige muku su, sa'annan sai in cika muku sakamakonsu, saboda haka; Wanda ya samu alheri to ya gode wa Allah, wanda kuma ya samu akasin haka, to kada ya zargi kowa, face kansa", Muslim ya ruwaito shi, daga hadisin Abu-zarrin |(رضي الله عنه).

Lallai sauke HAKKOKIN DA SUKA WAJABA AKAN BAWA, Amfaninsu –a karshen lamari- yana komawa ne ga bawa mukallafi (mai hankali balagagge), ta hanyar bashi sakamakonsa a duniya da lahira, kamar yadda Allah (تعالى) ya ke cewa: "Kuma duk wanda ya aikata, ayyukan kwarai, alhalin yana mumini, to babu musu ga aikinsa, kuma Mu a gare shi, masu rubutawa ne" [Anbiya'i: 94].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Lallai wadanda su ka yi imani, kuma suka aikata ayyukan kwarai, lallai ne Mu, ba za Mu tozartar da ladan wanda ya kyautata aikinsa ba" [Kahf: 30].

        Kuma lallai sakaci, wajen sauke sashin HAKKOKIN DA SUKA WAJABTA GA BAWA (mai hankali, balagagge), ko tozarta hakkokin gabadaya da barin sauke su, cutar da ke cikin hakan da ukubarsa, yana komawa ne ga mutumin da ya tozarta irin hakkokin da addini ya shar'anta;
saboda idan Mutum ya tozarta HAKKOKIN UBANGIJIN TALIKAI, to, bai cutar da kowa ba, face kansa, a Duniya da Lahira, domin Allah, Mawadaci ne daga barin talikai, Allah (تعالى) yana cewa: "Idan ku ka kafirta, to lallai Allah Wadatacce ne ga barinku, kuma bashi yarda da kafirci (butulci) ga bayinSa, idan kuma kuka yi godiya zai yarda da godiyar, a gare ku" [Zumar: 7].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Ya ku, Mutane! Ku ne masu bukata zuwa ga Allah, shi kuma Allah shine Mawadaci Abin godiya" [Faxir: 15].
Kuma Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: "Ga ku, Ya ku wadannan! Ana kiranku, domin ku ciyar ga tafarkin Allah, amma daga cikinku akwai mai yin rowa, kuma wanda ya yi rowa, to hakika yana yin rowar ne ga kansa" [Muhammadu: 38].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kuma wanda ya aikata zunubi, to lallai yana tsirfarsa ne a kan kansa, kuma Allah ya kasance Masani Mai hikima" [Nisa'i: 111].

        Hakkin Ubangiji, wanda ya wajaba a bashi kiyayewa, shine TAUHIDI, Kuma hakika Allah ya yi mafi girman alkawari akansa, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma an kusantar da Aljanna ga masu takawa, ba da nisa ba * Wannan shine abinda ake yi muku wa'adi da shi, ga dukkan mai yawan komawa ga Allah, mai kiyaye (umurninsa)" [Kaf: 31-32].

Kuma duk wanda ya tozarta HAKKIN ALLAH Mabuwayi da daukaka, ta hanyar SHIRKA  a gare shi, da rikon wasu koma bayan Allah a tsakani, yana yin bauta a gare su, ko yana rokonsu, neman yaye cuta, da baqin ciki, ko biyan buqata, kuma yana tawakkali a gare su, to lallai ya tabe, kuma ya yi hasara, kuma aikinsa ya ruguje, kuma Allah ba zai karba masa farilla ba, ko fansa, kuma za a ce masa, ka shiga wuta tare da masu shiga, Saidai idan ya tuba daga aikata shirka, saboda ya zo cikin hadisi, cewa: Za a fadawa Mutum, daga cikin 'yan wuta, cewa: "Da abinda ke cikin duniya naka ne, shin za ka fanshi kanka da shi, daga shiga wuta? Sai ya ce: E, sai a ce masa: Ai an umurce ka da abinda ya fi hakan sauki, cewa kada ka yi shirka wa Allah", Bukhariy ya ruwaito shi.

        Ku saurara!
        Lallai yana daga sakayyar kyakkyawa aikata kyakkyawa a bayanta, Allah Ta'alah ya ce:
"Kuma wadannan da suka nemi shiryuwa, Allah yana kara musu shiriyarsu, kuma ya basu sakamakon takawarsu" [Muhammadu: 17].

        Kuma ku saurara!
        Kuma yana daga ukubar mummunan aiki, aikata mummuna a bayansa, Allah Subhanahu yana cewa: "A cikin zukatansu akwai cuta, sai Allah ya kara musu wata cutar" [Bakara: 10].

        Kuma ku saurara!
        Lallai wanda ya tsira da SALLOLINSA BIYAR to, hakika ya tsira da yininsa.
        Wanda kuma ya tsira da JUMA'ARSA to, lallai ya tsira da satinsa.
        Wanda kuma ya tsira da AZUMIN RAMADAN nasa to, hakika ya rabauta da shekararsa.
        Wanda kuma ya bada ZAKKAR DUKIYARSA, sai Allah ya kiyaye masa dukiyarsa, kuma ya sanya masa albarka a cikinsa.
        Wanda ya tsira da HAJJINSA, to, hakika ya tsira da rayuwarsa gaba dayanta.
        Wanda kuma ya kiyaye TAUHIDI, To lallai Allah ya lamunce masa shiga Aljannah.

Idan kuma Mukallafi (mai hankali balagagge) ya tozarta HAKKOKI, wato, ya ki bayar da hakkokin bayin Allah na wajibi akansa, to hakika ya haramtawa kansa lada, a Duniya da Lahira. Idan kuma ya yi sakaci wajen bada sashensu, to lallai za a haramta masa alherori ne, gwargwadon sakacin da ya yi, wajen bada hakkokin halittun Allah.
        Kuma rayuwa tafiya ta ke yi, da abinda Mutum ke samu na tsanani ko wadaci, da hanawa ko baiwa, kuma ba za ta tsayawa ba, akan yadda 'Dan'adam ke samun hakkokinsa na wajibi, wadanda suke wajen Mutane ba, Saidai kuma (idan aka cinye masa su) to a wurin Allah ne masu husuma za su hadu, sai Ya baiwa wanda aka zalunta hakkinsa, daga Mutumin da ya zalunce shi, ya kuma tozarta hakkinsa, Ya zo daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), ya ce: "Lallai tabbas, za ku mayar da hakkoki ga Ma'abutansu, a ranar kiyama, har sai an dauki fansa ga akuyar da bata da kafo, daga akuya mai kaho", Muslim ya ruwaito shi.

        Kuma mafi garman HAKKOKI      bayan hakkin Allah, da ManzonSa, su ne HAKKOKIN IYAYE BIYU,
Kuma saboda girman hakkinsu ne, Allah ya gwama ambaton hakkokinsu da hakkinSa, a inda yake cewa: "Kuma Ubangijinka ya hukunta kada ku yi bauta ga kowa face Shi, kuma mahaifa biyu ku kyautata musu kyautatawa, ko da dayansu zai kai ga tsufa a wurinka, ko dukkansu biyun, to, kada ka tsawace su, kuma ka fada musu magana mai karimci * Kuma ka sassauta musu fikafikan tausasawa na rahama, kuma ka ce: Ya Ubangijina! Ka yi musu rahama, kamar yadda su ka yi renone ina karami" [Isra'i: 23-24].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kuma mun yi wasiyya ga Mutum, game da mahaifansa biyu; Uwarsa ta dauke shi, a cikin rauni a kan wani rauni, kuma yayensa a cikin shekaru biyu, (mu ka ce masa:) Ka gode mini da kuma mahaifanka biyu, Makoma zuwa gare Ni ne ta ke" [Lukman: 14].
        Kuma Allah ya girmama hakkin iyaye biyu ne, saboda Allah ya samar da kai ne; ya halitta ka ta hanyarsu; su biyu.
        Ita kuma Uwa ta samu mafi tsananin wahala, a matakan renon ciki, kuma ta yi kusan halaka a lokacin haihuwa, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma mun yi wasiyya ga Mutum, game da mahaifansa biyu; da kyautatawa, Uwarsa ta yi cikinsa da wahala, kuma ta haife shi da wahala" [Ahkaf: 15].
Kuma shayar da Mutum, aya ce daga cikin ayoyin Allah.
        Shi kuma Uba yana kulawa, yana tarbiyya, kuma yana yin aiki domin kawo abinci ga dansa.
        Kuma iyaye biyu suna neman magani ga cutukan 'ya'ya,
Kuma suna tashi cikin dare (su hana idanunsu barci) domin dansu ya yi barci,
Suna gajiyar da kansu domin dansu ya samu hutu,
Suna kuma wahalar ko takura wa kayukansu, domin su yalwata wa dansu,
Kuma suna jure wa kazantar yaro, domin ya ji dadi,
Kuma suna ilmantar da dansu, domin ya zama kamili, madaidaicin Mutum,
Kuma suna so dansu ya zamto ya fi su, ta kowace fiska,
        Don haka;
Kada ka yi mamaki –ya kai yaro- kan yawaitar wasiyyar da Allah (تعالى) ya yi, dangane da iyaye biyu,
kuma kada ka yi mamakin yawan narkon azabar da aka tanadar, ga Mutumin da ya ki yin biyayya ga iyayensa,
        Kuma "da" ba zai kai ga cikakken biyayya ga mahaifi ba, duk yadda ya yi kokarin ya kwatanta, sai a hali daya tak, Hadisi ya zo daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), lallai ya ce: "Da ba zai iya sakanta wa mahaifi ba, sai dai idan ya same shi a matsayin bawan da aka mallaka, sai ya saye shi, sannan ya 'yanta shi", Muslim ya ruwaito shi, da Abu-dawud da Tirmiziy.

Kuma iyaye biyu, kofofi ne biyu daga cikin kofofin Aljanna; wanda ya musu biyayya, zai shiga Aljanna, saboda ya zo daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) lallai ya ce: "Hancinsa ya turbudi kasa! Hancinsa ya bugi turbaya!! Hancinsa ya turbudi kasa!!! Sai aka ce wanene, ya Manzon Allah! Sai ya ce: Wanda ya riski iyayensa biyu da rai, a halin tsufa, ko daya daga cikinsu, sai bai shiga Aljanna ba", Muslim ya ruwaito shi.

Ya kai Musulmi!!!
Idan har iyayenka biyu, suka yarda da kai, to lallai Ubangijinka ya yarda da kai, Ya zo daga Abdullahi bn Amr (رضي الله عنهما), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Yardar Allah tana cikin yardar mahaifi, Fushin Allah kuma, yana cikin fushin mahaifi", Hadisi ne ingantacce, Tirmiziy ya ruwaito shi, da Alhakim, a cikin Almustadrak, kuma ya ce: hadisi ne ingantacce.

Kuma biyayya wa iyaye biyu, shi ne:
-      Yin da'a a gare su, a cikin umurnin da babu sabon Allah a cikinsa,
-      Zartar da umurnin da iyayen biyu su ka bayar, da yin aiki da wasiyyar su,
-      Tausasa musu,
-      Shigar da farin ciki a zukatansu,
-      Yalwata musu ga ciyarwa,
-      Bada dukiya a gare su,
-      Jin kansu, da tausaya musu,
-      Shiga bacin rai, saboda bacin ransu,
-      Janyo abinda zai debe kewa a gare su,
-      'Da'a ko biyayya ga abokan iyayen biyu,
-      Sadar da zumuntar masoyansu,
-      Sada zumuncinsu,
-      Kamewa daga dukkan nau'ukan cutarwa a gare su,
-      Barin aikata dukkan abinda suka yi hani a kansa,
-      Son tsawon rayuwarsu,
-      Neman gafara a gare su a cikin rayuwarsu da bayan mutuwarsu.

Shi kuma BIJERA WA IYAYE KO RASHIN BIYAYYA a gare su (wato, Ukuk) shine abinda yake kishiyantar hakan gaba dayansa,
        Kuma lallai yawaitar bijire wa iyaye (wato,Ukuk) yana daga cikin alamomin Alkiyama, saboda ya zo cikin hadisi: "Lallai yana daga alamomin kiyama, ruwan sama ya yawaita, 'Da kuma ya zama sababin fushi (ga iyaye), ashararun Mutane kuma su yi mungun yaduwa, Mutanen kirki kuma su karanta mummunan karanci".

Yana daga manyan misalan bijire wa iyaye, Kai iyaye; su biyun, ko kuma daya daga cikinsu, gidan bada kulawa ga tsofi (masu shekaru dayawa), da fitar da su daga kulawar 'Dansu,  WAL IYAZU BILLAHI,
Kuma yana daga manyan misalan bijire wa iyaye, Yin girman kai a gare su, da ta'addanci akansu ta hanyar yin duka a gare su, ko yin wulakanci a gare su, da zaginsu, da hana su bukatar Duniya, Hadisi ya zo daga Abu-hurairah (رضي الله عنه) ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم): "Lallai Aljanna, ana samun kamshinta daga tafiyar shekaru dari biyar, kuma mai cutar (ko bijire) wa iyaye ba zai samu kamshinta ba", 'Dabaraniy ya ruwaito shi.
Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma ku bauta wa Allah, kuma kada ku hada wani da Shi, kuma ga mahaifa biyu ku kyautata musu, kuma ku kyautata ga ma'abucin zumunta, da marayu, da miskinai, da makwabci ma'abucin kusanta, da makwabci manisanci, da aboki a gefe, da dan hanya (matafiyi), da abinda hannunku na dama suka mallaka, Lallai ne Allah ba ya son wanda ya kasance mai takama mai yawan alfahari" [Nisa'i: 36].


Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Na fadi abinda ku ke ji, kuma ina neman gafarar Allah Mai girma ga Ni da KU da sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU
        Yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai,
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya, Mai tsananin karfi,
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawanSa ne ManzonSa, Mai gaskiya, Amintacce,

Ya Allah ka kara salati da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammadu, da iyalansa, da sahabbansa gaba daya.

Bayan haka … !!
Sai ku yi takawar Allah, iyakar takawa, kuma ku yi riko, a Musulunci da igiya mai karfi,

Ya ku Bayin Allah … !!
Lallai hakkokin iyaye biyu –tare da abinda ke cikin tsayuwar dansu wajen sauke su, na tarin lada mai girma, da albarka- to kuma, bada su yana daga manyan halayyar Musulunci, yana kuma nuna karamcin dabi'u, wadanda Mutumin da zuciyarsa ta yi kyau yake tsayuwa wajen bada su, kuma asalinsa ya kyautata, dabi'unsa suka tsarkaka,
Kuma lallai sakamakon kyautatawa shine kyautatawa,
Kyakkyawan abu kuma, duk wanda ya maka shi, to, hakkinsa shine a kula da shi, a yi masa sakayya,
Kuma abu mai kyau ana fiskantarsa ne da mai kyau irinsa,
Kuma babu mai bijire ga kyakkyawan abu, face mai yasassun halayya, maras mutunci, mai mummunar zuciya, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma kada ku manta da falalar da ta ke a tsakaninku, Lallai ne Allah ga abinda kuke aikatawa Mai gani ne" [Bakara: 237].

        Kuma Allah (تعالى) yana cewa dangane da annabi Isah (عليه السلام): "Kuma Ni mai biyayya ne ga Uwata, kuma bai sanya ni mai kaushin zuciya, marashin alheri ba" [Maryam: 32].
        Kuma ya fada, dangane da annabi Yahya (عليه السلام): "Kuma mai biyayya ga mahaifansa biyu, kuma bai kasance mai girman kai, mai sabo ba" [Maryam: 14].
        Kuma Allah ya ce, dangane da shakiyyi marashin alkhairi: "Kuma wanda ya ce ga mahaifansa biyu, Tir gare ku, Shin kuna tsoratar da ni cewa za a fitar da ni daga kabari ne, alhali kuwa karnonan Mutane dayawa sun shude, a gabanina (basu komo ba), Kuma su (mahaifan) suna neman taimakon Allah, suna ce masa: Kaitonka! ka yi imani, domin alkawarin Allah gaskiya ne, ,,," [Ahqaf: 17].
        Kuma an ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) Lallai wani Mutum ya zo wurin Annabi (صلى الله عليه وسلم) sai ya ce: Ya Manzon Allah! WANENE A CIKIN MUTANE YAFI CANCANTAR KYAUTATA MU'AMALATA?
Sai ya ce: "Mahaifiyarka, sai mahaifiyarka, sai mahaifiyarka, sa'annan sai Mahaifinka, sa'annan sai wanda suke kusa da kai, sai wanda suke kusa da kai", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.

        Ya ku Bayin Allah… !!!
        "Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan Annabin, Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallamar aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa Annabi Muhammadu, ……………………………
,,,          ,,,          ,,,

2018/08/30

AMFANI DA DUKKAN DAMAMMAKI, DOMIN HIDIMAR BAKIN ALLAH; MAHAJJATA, DON SU YI TAFIYARSU TA HAJJI CIKIN SAUKI DA NATSUWA (تسخير كافة الإمكانات لضيوف الرحمن لتأدية رحلة الحج بيسر وطمأنينة)









AMFANI DA DUKKAN DAMAMMAKI, DOMIN HIDIMAR BAKIN ALLAH; MAHAJJATA, DON SU YI TAFIYARSU TA HAJJI CIKIN SAUKI DA NATSUWA
(تسخير كافة الإمكانات لضيوف الرحمن لتأدية رحلة الحج بيسر وطمأنينة)







Mai girma ministan hajji da umrah;
Dr. Muhammadu Salih bn Dahir Bintin
معالي وزير الحج والعمرة د. محمد صالح بن طاهر بنتن





Tarjamar
Abubakar Hamza Zakariyya


Ministirin hajji da umrah ta kasar Saudia
MA'AIKATA
Bayani ga 'yan jarida
SASHEN SADARWA
Amfani da dukkan damammaki domin hidimar bakin Allah; Mahajjata, don su yi tafiyarsu ta hajji cikin sauki da natsuwa
MAUDU'I
Cikin kasar Saudia da wajenta
YADAWA
06/ Zul-hijjah/1439h
RANA
Mai girma ministan hajji da umrah; Dr. Muhammadu Salih bn Dahir Bintin
MASU MAGANA

Mai girma Ministan hajji da umrah
YIN AMFANI DA DUKKAN DAMAMMAKI, DOMIN HIDIMAR BAKIN ALLAH; MAHAJJATA, DON SU YI TAFIYARSU TA HAJJI CIKIN SAUKI DA NATSUWA
            Mai girma ministan hajji da umrah; wato Dr. Muhammadu bn Salih bn Dahir Bintin, ya bayyana cewa lallai bin yadda ayyukan suke gudana ko-da yaushe, da umurnin Mai hidimar harami biyu masu girma; Sarki Salman bn Abdul'aziz, da kuma Mai girma Na'ibin sarki, wato Yarima Muhammadu bn Salman bn Abdul'aziz, wanda shine Na'ibin shugaban majalisar ministoci, kuma ministan tsaro –Allah ya kiyaye su-, sun nuna cewa: A yi amfani da dukkan damammaki da kafatanin ma'aikata, domin hidima ga Bakin Allah, wadanda suka zo domin hajjin dakin Allah mai alfarma.  
            Kuma Mai girman ministan ya tabbatar cewa hukumarsa da sauran hukumomi sun yi cikakken shiri domin tarbar Bayin Mai rahama, wadanda suka fito daga sako daban-daban na Duniya, wadanda suke shiri a ranar lahdi mai zuwa (wato, ranar takwas ga watan zul hijjah) cewa za su sauka a mahada ta farko daga cikin wuraren bauta masu tsarki, domin su kwana a wurin da ake kira Minah, (Ministan) yana mai fatan su samu tafiyarsu ta imani, cike da natsuwa, don su sauke hajjinsu da ibadodinsu cikin dukkan sauki da natsuwa.
            Kuma minister Dr. Bintin ya ce: "Lallai ministirin hajji da umrah, da dukkan bangarorinta, suna yin aiki tukuru, tare da samun taimakon dukkan hukumomin da aka hada na hajji da umrah, wajen gabatar wa bakin Allah mafi kyan hidimomi, a lokacin tarbarsu a wuraren ibada masu tsarki (Minah, Muzdalifah, da Arfah), har zuwa lokacin da za su koma gidajensu suna masu riba da samun babbar ganima".
            Kuma Mai girma ministan hajji da umrah Dr. Bintin ya yi nuni cewa lallai hukumar hadimin harami guda biyu madaukaka, ta yi aiki dayawa daga mafi girman ayyukan fadada Masallatai wanda garurruka biyu masu tsarki suka taba samu a tarihin Musulunci, wanda kuma hakan shine ya kara yawan abinda Masallatan biyu zasu dauka na masu ibada, kuma ya baiwa Musulmai daga ko-ina suke a Duniya, damar yin ayyukansu na ibada cikin sauki da natsuwa.
            Kamar yadda masarautar Saudia ta yi manyan ayyukan raya kasa, a garin Makkah da Madina da wuraren bauta na Mina da Muzdalifa da Arfah, wanda suka zama cibiyoyin ayyukan hidimtawa masu tarin yawa, wanda kuma sun kunshi:
1.     Ayyukan fadada harami biyu masu daraja.
2.     Da kuma wuraren da aka ware, sannan aka gina mazaunan Mahajjata, a wuraren da suka fi muhimmanci (da ake kira mandika markaziyya), na garurrukan  Makkah da Madinatul munawwarah.
3.     Da samar da jirgin kasa a wuraren ibada masu daraja (Mina, Arfah, da Muzdalifah).
4.     Da kammala gadodi na wurin jifan shedan.
5.     Da hidimomi ta bangaren ababen daukan Mahajjata (kamar motoci), da hidimomin lafiya, da tsafta, da wasu makamantan haka, daga cikin hidimomi na wajibi ga masu hajji da umrah da masu ziyara.
6.     Da assasa ko samar da yanayin tarbar baki na zamani, wanda ke karfafa hidimomi da tsare-tsaren tattali ga ayyukan hajji da umrah.
            Kuma Mai girma ministan hajji, Dr. Bintin ya bayyana cewa, lallai manufar bunkasa Saudia mai taken shekarar 2030 ta shigar wa aikin hajji da umrah tsare-tsare na cigaba, wadanda babu irinsu a baya, ta yadda hukumar hajji ke yin aiki da sabon tsari, wanda ya ginu a kan barin tsarin nan na baya; mai yin aiki a wasu lokuta, zuwa ga aiki tukuru a tsawon shekara, da kuma aiki da takanoloji domin bunkasa ayyuka, da tabbatar da yin aikin da bai san rufa-rufa ba, da amfani da tsare-tsare don samar da ayyuka ingantattu, da aiki da ma'aunan gwada ci-gaban da ake samu, domin kara bunkasa damammaki ko kara adadinsu, da bunkasa gwanancewar ma'aikata, da kara kawo tsari ga hukumomin da suke ayyukan hajji da umrah, da irin tsare-tsaren da insha Allahu za su taimaka wajen tabbatuwan manufofin da ake son cin musu, zuwa shekarar 2030, tare da tafiya da tsarin kawo canji ga kasar gaba daya.
            Kuma lallai Mai girma ministan hajji da umrah, Dr. Muhammadu bn Salih bn Dahir Bintin ya kwadaitar da dukkanin Ma'aikatan hukumar hajji da umrah cewa su kara aiki da kwazo, domin cimma abinda hukumar Mai hidimar harami guda biyu madaukaka –حفظه الله- ta ke fatan gani.

## Labarin ya kare##   

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...