KA
KARANTA; SAI KA SAMU 'DAUKAKA
(اقرأ
واصعد)
Tarjamar
Abubakar Hamza
Zai kama hannunka domin ya daukaka ka zuwa ga matsayi mafi daukaka,
Zai tsaya tare da kai domin baka kariya, a lokacin kunci da tarin bakin-ciki,
Lallai wannan shine ALKUR'ANI, saboda ya zo a cikin hadisin da, Manzon
Allah –صلى الله عليه وسلم- ke cewa:
((يقال لصاحب القرآن إذا دخل الجنة: اقرأ واصعد، فيقرأ ويصعد بكل آية
درجة حتى يقرأ آخر شيء معه))،
رواه ابن ماجه، وصححه الألباني.
Ma'ana: "Za a
gaya wa mahaddacin Alkur'ani, idan ya shiga Aljannah: karanta, domin ka samu
daukaka, sai ya karanta, yana hawa daraja daya da kowace ayar da ya karanta ta,
har ya kai ga ayoyin karshe da suke tare da shi", Ibnu-Majah ya
ruwaito, kuma Albaniy ya inganta shi.
Kuma a lokacin da firgicin yinin kiyama da tsananin cikinsa za su zo, to
Kur'ani ba zai gudu ya kyale ma'abuta karanta shi ba; Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم– yana cewa:
((اقرؤوا القرآن فإنه يأتي يوم القيامة شفيعًا لأصحابه))، رواه مسلم [804].
Ma'ana: "Ku rika karanta Alkur'ani;
domin Kur'ani zai zo a ranar kiyama, yana neman ceto ga ma'abutansa",
Muslim [804].
Kuma Alkur'ani zai amfani ma'abucinsa, da kowane harafin da ke cikinsa,
saboda Kur'ani zai rika amfanarka yana daukaka darajarka a Duniya da Lahira,
saboda ya zo cikin hadisi; Annabi –صلى الله عليه
وسلم- yana cewa:
((مَن قرأ حرفًا من كتاب الله فله به حسنة، والحسنة بعشر أمثالها))، رواه الترمذي،
وصححه الألباني.
Ma'ana: "Wanda ya karanta harafi daya
daga littafin Allah, to yana da ladan kyakkyawa akansa, shi kuma kyakkyawa ana
ninninka shi da kwatankwacinsa", Tirmiziy ya ruwaito shi, Kuma
Albaniy ya inganta shi.
Wannan ya sanya ma'abucin Alkur'ani ya shiga cikin wadanda suka cancanci
a rika hassadar samun irin abinda yake wurinsu, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce:
((لا حسد إلا في اثنتين؛ رجلٍ آتاه الله القرآن، فهو يقوم به آناء الليل
وآناء النهار، ورجلٍ آتاه الله مالا فهو ينفقه آناء الليل وآناء النهار))، رواه مسلم [804].
Ma'ana: "Babu hassada sai cikin abubuwa
biyu; Mutumin da Allah ya bashi Alkur'ani, sai yake tsayuwa da shi, cikin dare,
da cikin yini. Da kuma Mutumin da Allah ya bashi tarin dukiya; sai yak e ciyar
da ita, cikin dare da cikin yini", Muslim ya ruwaito [804].
Don haka, sai ka kasance tare da wannan sahibi mai r8ike amanar abota,
kuma ka yi rayuwarka cikin inuwarsa, saboda kana cikin kasuwa ce mai riba, da
tijarar da babu asara a cikinta;
((إن الذين يتلون كتاب الله وأقاموا الصلاة وأنفقوا مما رزقناهم سِرًّا
وعلانية يرجون تجارة لن تبور))
[فاطر: 29].
Ma'ana: "Lallai ne wadanda ke karatun
littafin Allah, kuma suka tsayar da sallah, kuma suka ciyar daga abinda muka
azurta su da shi, a asirce da bayyane, suna fatan samun fatauci ne wand aba ya
yin tasgaro", [Fadir: 29].
No comments:
Post a Comment