2017/07/06

huduba 13 SHAWWAL 1438H ta Huzaifiy daidai 07 julaye 2017M











HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 13/SHAWWAL/1438H
daidai da 07/JULAYE/ 2017M




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEIKH ALIYU BN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
Nm,,
Shehin Malami wato: Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: mn,,, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO

"Yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai", "kuma yabon nasa ne a ta farko (duniya) da ta qarshe (lahira), kuma hukunci nasa ne, kuma zuwa gare shi za a mayar da ku" [Qasas: 70],  
Ya halitta halittu, ba a kan wani misali ba da ya gabata, kuma ya qaddara qaddarori da iliminSa da kuma qudurarSa, kuma sunnarSa ta shuxe, kuma nufinSa ya zartu, kuma kalmarSa ta xaukaka, Tsarki ya tabbata ga Ubangijina; "Ba a tambayarSa kan abinda ke aikatawa, su ne ake tambayarsu" [Anbiya'i: 23].
            Ina yabo ga Ubangijina, kuma ina gode masa akan ni'imominSa gaba xaya,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya, sai Allah shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, mulki nasa ne, kuma yabo nasa ne, kuma ya xaukaka ga barin abinda su ke masa shirka.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, Wanda aka tayar da shi, domin ya zama rahama ga talikai.
Ya Allah! ka yi salati, da sallama ga bawanka kuma manzonka; Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa, waxanda su ka shiryu da shiriyarsa.

Bayan haka:
Ku bi Allah ta'alah da taqawa; saboda taqawar Allah ita ce dalilin sa'ada a duniya, da samun rabo a lahira, domin babu wanda zai samu sa'ada idan ba masu taqawa ba, kuma babu wanda zai yi hasara face bijirarru.

Ya ku, Bayin Allah… !!!
Mafi alherin abinda mutum ya samar shi ne, AIKI NA KWARAI, wanda UbangijinSa, zai yarda da mutum saboda aikin, sai ya samu sa'ida da shi a duniyarsa, ya kuma rabauta da shi a cikin dukkan halin da ya samu kansa, ya kuma samu daraja maxaukakiya da shi a lahira, sai a xora shi bisa ga matsayin da Allah ya rubuta masa samunsa.
Kuma idan Allah ya sauqaqe wa bawa ibada, kuma ya masa baiwar yin ikhlasi a cikin aikin, kuma ya datar da shi da bin shiriyar Annabi, da riqo da Sunnah, to haqiqa Allah -Mabuwayi da xaukaka- ya karrama shi da mafi girman abin karramawa, kuma ya masa baiwa da mafi girman abin nema, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Lallai ne Allah yana bada duniya ga wanda Allahn ke so, da wanda baya so, sai dai kuma baya bada addini sai ga wanda ya ke so".
Kuma Allah ta'alah yana cewa: "Lallai ne Allah yana karvar aiki ne daga masu taqawa" [Ma'ida: 27].
            Kuma wajibi ne akan bawa, ya tsayu wajen gode wa karramawar da Allah ya masa na aikata xa'a, ta hanyar dawwamar da daidaituwa akan addini, saboda duk wanda ya dawwama akan tsayuwa a bisa addini, shi ne zai rabauta da alkhairori, kuma ya tsira daga abubuwa masu halakarwa, Allah ta'alah yana cewa: "Lallai waxannan da su ka ce, Ubangijinmu shi ne Allah, sannan su ka daidaitu, Mala'iku na sassauka akansu (a lokacin saukar ajalinsu, suna cewa:) Kada ku ji tsoro, kuma kada ku yi baqin ciki, kuma ku yi bushara da aljannah, wadda kuka kasance ana muku wa'adi da ita" [Fussilat: 30].
Kuma an karvo daga Sufyan xan Abdullahi, ya ce: Na ce ya Manzon Allah! Ka gaya mini wani zance a cikin musulunci, wanda ba zan tambayi wani ba, idan ba kai ba? Ya ce: "Ka ce: Na yi imani da Allah, sa'annan ka daidaitu". Muslim ya ruwaito shi.
            Ayyuka kyawawan da Allah ke karrama wanda ya nufa daga cikin bayinSa, dole sai an yi aikin KIYAYE SU, ta hanyar nisantar ababen da za su vata su, na ayyukan savo da zunubai, ko su ke tauye ladansu; na laifuka, da zalunci, Allah ta'alah yana cewa: "Ya ku waxanda su ka yi imani, ku yi xa'a wa Allah, da ManzonSa, kuma kada ku vata ayyukanku" [Muhammadu: 33].

            Sai ka yi qoqari –Ya kai musulmi- ka kasance a yau, ka fi alkhairi akan jiyanka, kuma ka kasance a gobenka ka fi alkhairi akan yau xinka.
            kuma duk wanda ya yaqi kansa wajen ayyukan xa'oi, ya kuma yaqi kansa wajen nisantar abubuwa na haram, sai Allah ya taimake shi, ya kuma shiryar da shi zuwa ga tafarki madaidaici, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma waxannan da su ka yi jihadin neman yardarmu, lallai za mu shiryar da su ga hanyoyinmu, kuma lallai Allah yana tare da masu kyautatawa" [Ankabut: 69].
            Yau (wato a duniya) ake tsere, gobe (kiyama) kuma, yini ne na raba kyautukan waxanda su ka yi rigaye.

            HASARA wacce babu wani abu da ke tsayuwa a matsayin canjinta, da KARAYAR da bata warkewa, da TAVEWAR da babu sa'ida a tare da ita,  ita ce LALACEWAN AYYUKA, bayan kyawunsu, da KOMAWA BAYA bayan DAIDAITUWA.
            Saboda shexan yana jiran mutum a madakata, kuma ya zauna masa akan kowace turbar alkhairi, domin ya kange shi daga aikata alkhairin, kuma domin ya vata ayyukansa nagari, da abinda (a kullum) ya ke qawata masa na shubuhohi da bidi'oi da sha'awowi, Allah ta'alah ya faxa, dangane da adawar Shexan: "Sa'annan zan je musu daga gaba gare su, da baya gare su, da kuma daga jihohin bayansu, da jihohin hagunsu, kuma ba za ka sami mafi yawansu suna masu godiya ba" [A'araf: 17].

            Sai dai kuma qofofin alkhairi suna dayawa, hanyoyin samun falaloli da gafara suma suna da faxi, kuma rahamar Allah ta dabaibaye halittu, kuma a cike, kuma babu mai halaka a wurin Allah, face halakakken da babu alkhairi a tare da shi.
            Kuma lallai ibadodi, da ayyukan samun falaloli suna nan a kowani wata, bal a kowace rana.
            Kuma Ubangiji yana gode wa bayinSa akan aikinsu kaxan, sai ya sakanta musu da sakamako mai tarin yawa, Allah ta'alah yana cewa: "Lallai Allah ba ya zaluncin gwargwadon nauyin zarra, idan ta kasance alheri ce, sai ya rivanyata, kuma ya kawo daga wurinsa lada mai yawa" [Nisa'i: 40].
            Kuma yana daga cikin QOFOFIN ALKHAIRI MASU GIRMA, da amfani mai gamammen fa'ida, kuma yana daga cikin qofofin biyayya wanda tasirinsu ke tsawaita, alkhairinsa ke da faxi:        BIYA WA MUTANEN DA AKE BIN BASHI BASHINSU, DA TAIMAKA MUSU WAJEN SAUKE HAQQOQIN WAJIBIN DA SUKA XORU AKANSU, kana mai neman abinda ke wurin Allah na sakamako mai girma, musamman kuma waxanda aka kurkukunce su, daga cikin mutanen da su ka gaza wajen biyan basukan da ke wuyansu, waxannan da su ke jiran wanda zai tsamo su, daga cikin ma'abuta jin-qai, da kyautatawa, saboda sun yi kama da waxanda ruwa ya haxiye wanda su ka cancanci a kama hannunsu, zuwa gavar tsira, waxanda lokutan idi da lokutan farin cikin mutane ke shuxe musu alhalin suna cikin kurkuku, saboda basuka, alhalin sun dulmuya cikin vacin ran tunanin basuka. Abinda kuma ya fi hakan girma, shi ne tunaninsu ga waxanda ke bayansu, (na 'ya'ya) waxanda su ke tsorace musu tozarta, ga kuma tarin buqatu.
            Ma'abuta musulunci su ne ma'abuta jin-qai da kyautatawa.
            Kuma lallai a cikin dukiyar mawadata ta zakka () da sadakoki, akwai abinda ya xoru akan buqatun mabuqata.
            Kuma yana da sauqi, a iya kaiwa ga xaixaikun waxannan mabuqatan waxanda su ke kulle a kurkuku, saboda basuka, ta hanyar shugabannin gidajen kurkukun, domin a biya masu basukan bashin da su ke bi, ta hanyar yaqini, tare da baiwa mutanen da ake bi bashi, abinda za su ciyar da iyalansa, na tsawon lokacin da zasu fara aiki, a bayansa.
            Kuma abu ne mai sauqi, bibiyan mabuqata domin warware musu buqatunsu, a kowani birni da gari, domin taimaka musu a lokutan buqatuwansu, Allah kuma yana cewa: "Kuma duk abinda ku ka ciyar daga wani abu, to shi ne zai musanya shi, kuma shi ne mafificin masu azurtawa" [Saba'i: 39].
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Sadaka bata tauye wata dukiya".
            Kuma albishir wanda ya fi duniya da abinda ke cikinta alkhairi ta tabbata ga wanda aka datar da shi, wajen yin irin wannan aikin, da kuma mutumin da ya buxe irin wannan qofar ta taimako, kuma ya lazimce ta, albishir, wanda ya zo a cikin faxin Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم): "Wanda ya kwaranye baqin ciki ga mumini, daga cikin baqin cikin duniya, Allah zai kwaranye masa baqin ciki, daga cikin baqin cikin lahira, kuma duk wanda ya sauqaqe wa mutumin da ke cikin qunci, Allah zai sauqaqe masa a duniya da lahira, kuma duk wanda ya rufa asirin musulmi, Allah zai rufa masa asirinsa a duniya da lahira, Allah yana taimakon bawa, matuqar bawan yana cikin taimakon xan'uwansa", Muslim ya ruwaito shi.
Kalmar "kurbatun" a cikin hadisin, tana nufin tsanani mai girma, wanda ke aukar da ma'abucinsa, cikin baqin ciki.
Shi kuma baqin cikin yinin qiyama, wanda ke kasancewa a gabanin shiga aljannah, dukkansu suna da girma, ga kuma tarin yawa. Kuma yana daga cikinsu: Abinda Bukhariy da Muslim su ka ruwaito daga hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه) ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Mutane za su yi gumi, a yinin qiyama, har sai guminsu ya tafi a bayan qasa, na tsawon zira'i saba'in, kuma zai musu linzami, har sai ya kai ga kunnuwansu".
Kuma an ruwaito daga Uqbah bn Amir (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) lallai ya ce: "Kowani mutum yana qarqashin inuwar sadakarsa ne, har a yi hukunci a tsakanin mutane", Hadisi ne ingantacce, Ahmad ya rawaito shi.
            Allah ta'alah yana cewa: "Kuma ku yi gaggawa zuwa ga neman gafarar Ubangijinku, da wata aljannah, wadda faxinta daidai da sammai da qasa ya ke, an yi tattalinta domin masu taqawa * Waxannan da su ke ciyarwa a cikin sauqi da tsanani, kuma su ke masu haxiyewar fushi, kuma masu yafe wa mutane, kuma Allah yana son masu kyautatawa" [Ali-imraan: 133-134].

Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUXUBA TA BIYU
            Yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, Mai yawan azurtawa, ma'abucin tsananin qarfi,
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, Mai gaskiya, Amintacce,

Ya Allah ka qara salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa, da sahabbansa, har zuwa ranar sakamako.

Bayan haka … !!
Ku yi taqawar Allah, iyakar taqawa, domin duk wanda ya yi taqawar Allah, sai ya sanya shi cikin majivintarsa, kuma duk wanda Allah ya jivince su, to sai ya kiyaye su, a duniyarsu da lahiransu.

Ya ku Bayin Allah … !!
Ku sani lallai manufar musulunci ita ce: Mutum ya kyautata wa ransa, da kuma kyautatawa halittu,
Amma KYAUTATA WA RAI to, ta kan tabbatu ne, ta hanyar TABBATAR DA TAUHIDI GA UBANGIJI Mabuwayi da xaukaka, da tsayuwan bawa da AIKATA NAU'UKAN IBADODI, cikin son Allah, da qanqan-da-kai da rusunawa da miqa-wuya, da NISANTAR ABUBUWAN HARAMUN, Allah yaan cewa: "Kuma bayin Mai rahama su ne waxanda ke yin tafiya akan kasa da sauki, kuma idan jahilai suka yi musu magana sai su ce salama (a zauna lafiya) * kuma waxanda su ke kwana suna masu sujjada da tsayi a wurin Ubangijinsu * kuma waxanda su ke cewa ya Ubangijinmu ka karkatar da azabar jahannama daga gare mu, lallai ne azabarta ta kasance mai dawwama * lallai ne jahannama ta munana ta zama wurin tabbata da mazauni * kuma waxanda su ke, idan sun ciyar basu yin varna kuma basu yin kwauro kuma (ciyarwarsu) sai ta kasance a tsakanin wancan da tsakaitawa * kuma waxanda basu kiran wani Ubangiji tare da Allah, kuma basu kashe rai wanda Allah ya haramta face da haqqi, kuma basu yin zina, kuma wanda ya aikata wancan zai gamu da laifuffuka * za a rivanya masa azaba ranar qiyama, kuma ya tabbata cikinta yana wulaqantacce * sai wanda ya tuba, yayi imani, kuma ya aikata aiki na kwarai, to waxancan Allah yana musanyan miyagun ayyukansu da masu kyau, Allah ya kasance Mai gafara Mai jin qai" [Furqan: 63-70]

Amma shi kuma KYAUTATA WA HALITTU to, ta kan kasance, da NA'UKAN KYAUTATAWA, na ciyarwar wajibi ko ta mustahabbi, ko karantarwa, ko jurewa da shanyewa da haquri, da kamewa daga cutarwa, da makamncin haka, Annabi (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Halittu iyalan Allah ne, kuma halittar da ta fi soyuwa a wurin Allah, ita ce, wanda ta fi amfanar da iyalanSa".
Ma'anar "iyali" a cikin hadisin, shi ne, Allah ke xaukar nauyinsu.

            Ya ku Bayin Allah… !!!
            "Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa Annabi Muhammadu, ……………………………

,,,          ,,,          ,,,

2017/07/05

HADISAI ARBA'IN KAN KYAWAWAN HALAYE DA MUNANA أربعون حديثا في محاسن الأخلاق ومساوئها

مذكرة أحاديث محاسن الأخلاق ومساوئها
بسم الله والصلاة والسلام على عبد الله ورسوله نبينا محمد الذي وصفه ربه بقوله: {وَإِنَّكَ لَعَلَى خُلُقٍ عَظِيمٍ} [القلم: 4]، وعلى آله وصحبه والتابعين، أما بعد:
فهذه طائفة من أحاديث محاسن الأخلاق ومساوئها، تم الاكتفاء بأربعين منها من بين ثلاثمائة حديث احتواها كتاب: المنتخب من أحاديث الآداب والأخلاق، وسميت بالأربعين في الأخلاق، عسى الله أن يجعل فيها النفع العميم، إنه جواد كريم.
وحُسن الخلُق كما قال بعضهم، هو: بذل الندى وكفّ الأذى وطلاقة الوجه. وإليك الأحاديث:
الحديث الأول: عَنْ أَنَسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَحْسَنَ النَّاسِ خُلُقًا، وَكَانَ لِي أَخٌ يُقَالُ لَهُ أَبُو عُمَيْرٍ -قَالَ: أَحْسِبُهُ- فَطِيمًا، وَكَانَ إِذَا جَاءَ قَالَ: «يَا أَبَا عُمَيْرٍ، مَا فَعَلَ النُّغَيْرُ» نُغَرٌ كَانَ يَلْعَبُ بِهِ. [البخاري، 6203، ومسلم، 2310].
الحديث الثاني: عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا، قَالَ: "لَمْ يَكُنِ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَاحِشًا وَلاَ مُتَفَحِّشًا، وَكَانَ يَقُولُ: «إِنَّ مِنْ خِيَارِكُمْ أَحْسَنَكُمْ أَخْلاَقًا». [البخاري، 3559، ومسلم، 2321].
الحديث الثالث: عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَكْمَلُ الْمُؤْمِنِينَ إِيمَانًا أَحْسَنُهُمْ خُلُقًا». [أبو داود، 4682، والترمذي، 1162، وقال: حسن صحيح].
الحديث الرابع: عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «الْإِيمَانُ بِضْعٌ وَسَبْعُونَ -أَوْ بِضْعٌ وَسِتُّونَ- شُعْبَةً، فَأَفْضَلُهَا قَوْلُ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَأَدْنَاهَا إِمَاطَةُ الْأَذَى عَنِ الطَّرِيقِ، وَالْحَيَاءُ شُعْبَةٌ مِنَ الْإِيمَانِ». [البخاري، 9، ومسلم، 35].
الحديث الخامس: عَنْ أَبِي ذَرٍّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: قَالَ لِيَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا تَحْقِرَنَّ مِنَ الْمَعْرُوفِ شَيْئًا، وَلَوْ أَنْ تَلْقَى أَخَاكَ بِوَجْهٍ طَلْقٍ». [مسلم، 2626].
الحديث السادس: عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُما، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لِلْأَشَجِّ؛ أَشَجِّ عَبْدِ الْقَيْسِ: "إِنَّ فِيكَ خَصْلَتَيْنِ يُحِبُّهُمَا اللهُ: الْحِلْمُ، وَالْأَنَاةُ". [مسلم، 17].
الحديث السابع: عَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْها، أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «يَا عَائِشَةُ إِنَّ اللهَ رَفِيقٌ يُحِبُّ الرِّفْقَ، وَيُعْطِي عَلَى الرِّفْقِ مَا لَا يُعْطِي عَلَى الْعُنْفِ، وَمَا لَا يُعْطِي عَلَى مَا سِوَاهُ». [مسلم، 2593].
الحديث الثامن: عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: «يَسِّرُوا وَلاَ تُعَسِّرُوا، وَبَشِّرُوا، وَلاَ تُنَفِّرُوا». [البخاري، 69، ومسلم، 1734].
الحديث التاسع: عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: كُنْتُ أَمْشِي مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَعَلَيْهِ بُرْدٌ نَجْرَانِيٌّ غَلِيظُ الحَاشِيَةِ، فَأَدْرَكَهُ أَعْرَابِيٌّ فَجَذَبَهُ جَذْبَةً شَدِيدَةً، حَتَّى نَظَرْتُ إِلَى صَفْحَةِ عَاتِقِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَدْ أَثَّرَتْ بِهِ حَاشِيَةُ الرِّدَاءِ مِنْ شِدَّةِ جَذْبَتِهِ، ثُمَّ قَالَ: مُرْ لِي مِنْ مَالِ اللَّهِ الَّذِي عِنْدَكَ، فَالْتَفَتَ إِلَيْهِ فَضَحِكَ، ثُمَّ «أَمَرَ لَهُ بِعَطَاءٍ». [البخاري، 5809، ومسلم، 1057].
الحديث العاشر: عَنْ سُلَيْمَان بْنُ صُرَدٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: اسْتَبَّ رَجُلاَنِ عِنْدَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَنَحْنُ عِنْدَهُ جُلُوسٌ، وَأَحَدُهُمَا يَسُبُّ صَاحِبَهُ، مُغْضَبًا قَدِ احْمَرَّ وَجْهُهُ، فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "إِنِّي لَأَعْلَمُ كَلِمَةً، لَوْ قَالَهَا لَذَهَبَ عَنْهُ مَا يَجِدُ، لَوْ قَالَ: أَعُوذُ بِاللَّهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ " فَقَالُوا لِلرَّجُلِ: أَلاَ تَسْمَعُ مَا يَقُولُ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ؟ قَالَ: إِنِّي لَسْتُ بِمَجْنُونٍ. [البخاري، 6115، ومسلم، 2610].
الحادي عشر: عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، أَنَّ رَجُلًا قَالَ لِلنَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: أَوْصِنِي، قَالَ: «لاَ تَغْضَبْ» فَرَدَّدَ مِرَارًا، قَالَ: «لاَ تَغْضَبْ». [البخاري، 6116].
الثاني عشر: عَنْ عِيَاضِ بْنِ حِمَارٍ المُجَاشِعي رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: قَامَ فِينَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ذَاتَ يَوْمٍ خَطِيبًا، فَقَالَ: «إِنَّ اللهَ أَوْحَى إِلَيَّ أَنْ تَوَاضَعُوا حَتَّى لَا يَفْخَرَ أَحَدٌ عَلَى أَحَدٍ، وَلَا يَبْغِي أَحَدٌ عَلَى أَحَدٍ». [مسلم، 2865].
الثالث عشر: عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «كُلُّ سُلاَمَى مِنَ النَّاسِ عَلَيْهِ صَدَقَةٌ، كُلَّ يَوْمٍ تَطْلُعُ فِيهِ الشَّمْسُ، يَعْدِلُ بَيْنَ الِاثْنَيْنِ صَدَقَةٌ، وَيُعِينُ الرَّجُلَ عَلَى دَابَّتِهِ فَيَحْمِلُ عَلَيْهَا، أَوْ يَرْفَعُ عَلَيْهَا مَتَاعَهُ صَدَقَةٌ، وَالكَلِمَةُ الطَّيِّبَةُ صَدَقَةٌ، وَكُلُّ خُطْوَةٍ يَخْطُوهَا إِلَى الصَّلاَةِ صَدَقَةٌ، وَيُمِيطُ الأَذَى عَنِ الطَّرِيقِ صَدَقَةٌ». [البخاري، 2989، ومسلم، 1009].
الرابع عشر: عَنْ عَبْد اللَّهِ بْنَ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا، أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «المُسْلِمُ أَخُو المُسْلِمِ لاَ يَظْلِمُهُ وَلاَ يُسْلِمُهُ، وَمَنْ كَانَ فِي حَاجَةِ أَخِيهِ كَانَ اللَّهُ فِي حَاجَتِهِ، وَمَنْ فَرَّجَ عَنْ مُسْلِمٍ كُرْبَةً، فَرَّجَ اللَّهُ عَنْهُ كُرْبَةً مِنْ كُرُبَاتِ يَوْمِ القِيَامَةِ، وَمَنْ سَتَرَ مُسْلِمًا سَتَرَهُ اللَّهُ يَوْمَ القِيَامَةِ». [البخاري، 2442، ومسلم، 2580].
الخامس عشر: عَنْ ابْن عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُما أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «الْمُؤْمِنُ الَّذِي يُخَالِطُ النَّاسَ وَيَصْبِرُ عَلَى أَذَاهُمْ خَيْرٌ أَوْ أَفْضَلُ مِنَ الْمُؤْمِنِ الَّذِي لَا يُخَالِطُ النَّاسَ وَلَا يَصْبِرُ عَلَى أَذَاهُمْ». [الأدب المفرد، 393، وابن ماجه، 4032، وحسن إسناده ابن حجر].
السادس عشر: عَنْ أَبي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: "كُلُّ أُمَّتِي مُعَافًى إِلَّا المُجَاهِرِينَ، وَإِنَّ مِنَ المُجَاهَرَةِ أَنْ يَعْمَلَ الرَّجُلُ بِاللَّيْلِ عَمَلًا، ثُمَّ يُصْبِحَ وَقَدْ سَتَرَهُ اللَّهُ عَلَيْهِ، فَيَقُولَ: يَا فُلاَنُ، عَمِلْتُ البَارِحَةَ كَذَا وَكَذَا، وَقَدْ بَاتَ يَسْتُرُهُ رَبُّهُ، وَيُصْبِحُ يَكْشِفُ سِتْرَ اللَّهِ عَنْهُ". [البخاري، 6069، ومسلم، 2990].
السابع عشر: عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: «مَنْ دَعَا إِلَى هُدًى، كَانَ لَهُ مِنَ الْأَجْرِ مِثْلُ أُجُورِ مَنْ تَبِعَهُ، لَا يَنْقُصُ ذَلِكَ مِنْ أُجُورِهِمْ شَيْئًا، وَمَنْ دَعَا إِلَى ضَلَالَةٍ، كَانَ عَلَيْهِ مِنَ الْإِثْمِ مِثْلُ آثَامِ مَنْ تَبِعَهُ، لَا يَنْقُصُ ذَلِكَ مِنْ آثَامِهِمْ شَيْئًا». [مسلم، 2674].
الثامن عشر: عَنْ تَمِيمٍ الدَّارِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: «الدِّينُ النَّصِيحَةُ» قُلْنَا: لِمَنْ؟ قَالَ: «لِلَّهِ وَلِكِتَابِهِ وَلِرَسُولِهِ وَلِأَئِمَّةِ الْمُسْلِمِينَ وَعَامَّتِهِمْ». [مسلم، 55].
التاسع عشر: عَنِ ابْنِ مَسْعُودٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: سَمِعْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: "لاَ حَسَدَ إِلَّا فِي اثْنَتَيْنِ: رَجُلٍ آتَاهُ اللَّهُ مَالًا، فَسَلَّطَهُ عَلَى هَلَكَتِهِ فِي الحَقِّ، وَرَجُلٍ آتَاهُ اللَّهُ حِكْمَةً، فَهُوَ يَقْضِي بِهَا وَيُعَلِّمُهَا". [البخاري، 1409، ومسلم، 816].
الحديث العشرون: عَنْ أَبِي مُوسَى رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنَّ الأَشْعَرِيِّينَ إِذَا أَرْمَلُوا فِي الغَزْوِ، أَوْ قَلَّ طَعَامُ عِيَالِهِمْ بِالْمَدِينَةِ جَمَعُوا مَا كَانَ عِنْدَهُمْ فِي ثَوْبٍ وَاحِدٍ، ثُمَّ اقْتَسَمُوهُ بَيْنَهُمْ فِي إِنَاءٍ وَاحِدٍ بِالسَّوِيَّةِ، فَهُمْ مِنِّي وَأَنَا مِنْهُمْ». [البخاري، 2486، ومسلم، 2500].
الحادي والعشرون: عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُما أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: "أَرْبَعٌ مَنْ كُنَّ فِيهِ كَانَ مُنَافِقًا خَالِصًا، وَمَنْ كَانَتْ فِيهِ خَصْلَةٌ مِنْهُنَّ كَانَتْ فِيهِ خَصْلَةٌ مِنَ النِّفَاقِ حَتَّى يَدَعَهَا: إِذَا اؤْتُمِنَ خَانَ، وَإِذَا حَدَّثَ كَذَبَ، وَإِذَا عَاهَدَ غَدَرَ، وَإِذَا خَاصَمَ فَجَرَ". [البخاري، 34، ومسلم، 58].
الثاني والعشرون: عَنْ صُهَيْبٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «عَجَبًا لِأَمْرِ الْمُؤْمِنِ، إِنَّ أَمْرَهُ كُلَّهُ خَيْرٌ، وَلَيْسَ ذَاكَ لِأَحَدٍ إِلَّا لِلْمُؤْمِنِ، إِنْ أَصَابَتْهُ سَرَّاءُ شَكَرَ، فَكَانَ خَيْرًا لَهُ، وَإِنْ أَصَابَتْهُ ضَرَّاءُ، صَبَرَ فَكَانَ خَيْرًا لَهُ». [مسلم، 2999].
الثالث والعشرون: عَنْ عَبْدِ اللهِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «عَلَيْكُمْ بِالصِّدْقِ، فَإِنَّ الصِّدْقَ يَهْدِي إِلَى الْبِرِّ، وَإِنَّ الْبِرَّ يَهْدِي إِلَى الْجَنَّةِ، وَمَا يَزَالُ الرَّجُلُ يَصْدُقُ وَيَتَحَرَّى الصِّدْقَ حَتَّى يُكْتَبَ عِنْدَ اللهِ صِدِّيقًا، وَإِيَّاكُمْ وَالْكَذِبَ، فَإِنَّ الْكَذِبَ يَهْدِي إِلَى الْفُجُورِ، وَإِنَّ الْفُجُورَ يَهْدِي إِلَى النَّارِ، وَمَا يَزَالُ الرَّجُلُ يَكْذِبُ وَيَتَحَرَّى الْكَذِبَ حَتَّى يُكْتَبَ عِنْدَ اللهِ كَذَّابًا». [البخاري، 6094، ومسلم، 2607].
الرابع والعشرون: عَنْ حَكِيمِ بْنِ حِزَامٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "البَيِّعَانِ بِالخِيَارِ مَا لَمْ يَتَفَرَّقَا، فَإِنْ صَدَقَا وَبَيَّنَا بُورِكَ لَهُمَا فِي بَيْعِهِمَا، وَإِنْ كَتَمَا وَكَذَبَا مُحِقَتْ بَرَكَةُ بَيْعِهِمَا". [البخاري،2110، ومسلم، 1532].
الخامس والعشرون: عَنِ النُّعْمَانِ بْنِ بَشِيرٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُما، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "مَثَلُ الْمُؤْمِنِينَ فِي تَوَادِّهِمْ، وَتَرَاحُمِهِمْ، وَتَعَاطُفِهِمْ مَثَلُ الْجَسَدِ إِذَا اشْتَكَى مِنْهُ عُضْوٌ تَدَاعَى لَهُ سَائِرُ الْجَسَدِ بِالسَّهَرِ وَالْحُمَّى". [البخاري،6011، ومسلم، 2586].
السادس والعشرون: عَن أَبي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: "حَقُّ المُسْلِمِ عَلَى المُسْلِمِ خَمْسٌ: رَدُّ السَّلاَمِ، وَعِيَادَةُ المَرِيضِ، وَاتِّبَاعُ الجَنَائِزِ، وَإِجَابَةُ الدَّعْوَةِ، وَتَشْمِيتُ العَاطِسِ". [البخاري،1240، ومسلم، 1704].
السابع والعشرون: عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا، أَنَّ رَجُلًا سَأَلَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: أَيُّ الإِسْلاَمِ خَيْرٌ؟ قَالَ: «تُطْعِمُ الطَّعَامَ، وَتَقْرَأُ السَّلاَمَ عَلَى مَنْ عَرَفْتَ وَمَنْ لَمْ تَعْرِفْ». [البخاري، 12، ومسلم، 39]
الثامن والعشرون: عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا تَدْخُلُونَ الْجَنَّةَ حَتَّى تُؤْمِنُوا، وَلَا تُؤْمِنُوا حَتَّى تَحَابُّوا، أَوَلَا أَدُلُّكُمْ عَلَى شَيْءٍ إِذَا فَعَلْتُمُوهُ تَحَابَبْتُمْ؟ أَفْشُوا السَّلَامَ بَيْنَكُمْ». [مسلم، 54].
التاسع والعشرون: عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، أَنَّهُ سَمِعَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «إِنَّ الْعَبْدَ لَيَتَكَلَّمُ بِالْكَلِمَةِ، يَنْزِلُ بِهَا فِي النَّارِ أَبْعَدَ مَا بَيْنَ الْمَشْرِقِ وَالْمَغْرِبِ». [البخاري، 6477، ومسلم، 2988].
الحديث الثلاثون: عَنْ عَبْدِ اللهِ بن مسعود رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "إِنَّ الْمُؤْمِنَ لَيْسَ بِاللَّعَّانِ، وَلَا الطَّعَّانِ، وَلَا الْفَاحِشِ، وَلَا الْبَذِيءِ". [الترمذي، 1977، وأحمد، 3948، وقال الترمذي: حسن غريب].
الحادي والثلاثون: عَنْ عَبْدِ اللهِ بن مسعود رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «هَلَكَ الْمُتَنَطِّعُونَ» قَالَهَا ثَلَاثًا. [مسلم، 2670].
الثاني والثلاثون: عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: «أَتَدْرُونَ مَا الْغِيبَةُ؟» قَالُوا: اللهُ وَرَسُولُهُ أَعْلَمُ، قَالَ: «ذِكْرُكَ أَخَاكَ بِمَا يَكْرَهُ» قِيلَ أَفَرَأَيْتَ إِنْ كَانَ فِي أَخِي مَا أَقُولُ؟ قَالَ: «إِنْ كَانَ فِيهِ مَا تَقُولُ، فَقَدِ اغْتَبْتَهُ، وَإِنْ لَمْ يَكُنْ فِيهِ فَقَدْ بَهَتَّهُ». [مسلم، 2589].
الثالث والثلاثون: عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُما قَالَ: مَرَّ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلَى قَبْرَيْنِ فَقَالَ: «أَمَا إِنَّهُمَا لَيُعَذَّبَانِ وَمَا يُعَذَّبَانِ فِي كَبِيرٍ، أَمَّا أَحَدُهُمَا فَكَانَ يَمْشِي بِالنَّمِيمَةِ، وَأَمَّا الْآخَرُ فَكَانَ لَا يَسْتَتِرُ مِنْ بَوْلِهِ»، قَالَ فَدَعَا بِعَسِيبٍ رَطْبٍ فَشَقَّهُ بِاثْنَيْنِ ثُمَّ غَرَسَ عَلَى هَذَا وَاحِدًا وَعَلَى هَذَا وَاحِدًا ثُمَّ قَالَ: «لَعَلَّهُ أَنْ يُخَفَّفُ عَنْهُمَا مَا لَمْ يَيْبَسَا». [البخاري، 6052، ومسلم، 292].
الرابع والثلاثون: عَنْ أَبِي بَكْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَلاَ أُنَبِّئُكُمْ بِأَكْبَرِ الكَبَائِرِ؟» ثَلاَثًا، قَالُوا: بَلَى يَا رَسُولَ اللَّهِ، قَالَ: «الإِشْرَاكُ بِاللَّهِ، وَعُقُوقُ الوَالِدَيْنِ -وَجَلَسَ وَكَانَ مُتَّكِئًا فَقَالَ- أَلاَ وَقَوْلُ الزُّورِ»، قَالَ: فَمَا زَالَ يُكَرِّرُهَا حَتَّى قُلْنَا: لَيْتَهُ سَكَتَ. [البخاري، 2654، ومسلم، 87].
الخامس والثلاثون: عَنْ أَبِي ذَرٍّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّهُ سَمِعَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «لاَ يَرْمِي رَجُلٌ رَجُلًا بِالفُسُوقِ، وَلاَ يَرْمِيهِ بِالكُفْرِ، إِلَّا ارْتَدَّتْ عَلَيْهِ، إِنْ لَمْ يَكُنْ صَاحِبُهُ كَذَلِكَ». [البخاري، 6045، ومسلم، 61].
السادس والثلاثون: عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "إِنَّ اللهَ يَرْضَى لَكُمْ ثَلَاثًا، وَيَكْرَهُ لَكُمْ ثَلَاثًا، فَيَرْضَى لَكُمْ: أَنْ تَعْبُدُوهُ، وَلَا تُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا، وَأَنْ تَعْتَصِمُوا بِحَبْلِ اللهِ جَمِيعًا وَلَا تَفَرَّقُوا، وَأَنْ تَنَاصَحُوا مَنْ وَلَّاهُ اللَّهُ أَمْرَكُمْ، وَيَكْرَهُ لَكُمْ: قِيلَ وَقَالَ، وَكَثْرَةَ السُّؤَالِ، وَإِضَاعَةِ الْمَالِ". [مسلم، 1715، وغيره].
السابع والثلاثون: عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «اجْتَنِبُوا السَّبْعَ المُوبِقَاتِ»، قَالُوا: يَا رَسُولَ اللَّهِ وَمَا هُنَّ؟ قَالَ: «الشِّرْكُ بِاللَّهِ، وَالسِّحْرُ، وَقَتْلُ النَّفْسِ الَّتِي حَرَّمَ اللَّهُ إِلَّا بِالحَقِّ، وَأَكْلُ الرِّبَا، وَأَكْلُ مَالِ اليَتِيمِ، وَالتَّوَلِّي يَوْمَ الزَّحْفِ، وَقَذْفُ المُحْصَنَاتِ المُؤْمِنَاتِ الغَافِلاَتِ». [البخاري، 2766، ومسلم، 89].
الثامن والثلاثون: عَنْ أُسَامَةَ بن زيد رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُما قال: سَمِعْتُ رَسُول اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، يَقُولُ: "يُجَاءُ بِالرَّجُلِ يَوْمَ القِيَامَةِ فَيُلْقَى فِي النَّارِ، فَتَنْدَلِقُ أَقْتَابُهُ فِي النَّارِ، فَيَدُورُ كَمَا يَدُورُ الحِمَارُ بِرَحَاهُ، فَيَجْتَمِعُ أَهْلُ النَّارِ عَلَيْهِ فَيَقُولُونَ: أَيْ فُلاَنُ مَا شَأْنُكَ؟ أَلَيْسَ كُنْتَ تَأْمُرُنَا بِالْمَعْرُوفِ وَتَنْهَانَا عَنِ المُنْكَرِ؟ قَالَ: كُنْتُ آمُرُكُمْ بِالْمَعْرُوفِ وَلاَ آتِيهِ، وَأَنْهَاكُمْ عَنِ المُنْكَرِ وَآتِيهِ". [البخاري، 3267، ومسلم، 2989].
التاسع والثلاثون: عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "قَالَ اللهُ تَبَارَكَ وَتَعَالَى: أَنَا أَغْنَى الشُّرَكَاءِ عَنِ الشِّرْكِ، مَنْ عَمِلَ عَمَلًا أَشْرَكَ فِيهِ مَعِي غَيْرِي، تَرَكْتُهُ وَشِرْكَهُ" [مسلم، 2985].
الحديث الأربعون: عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ كَانَتْ لَهُ مَظْلَمَةٌ لِأَخِيهِ مِنْ عِرْضِهِ أَوْ شَيْءٍ، فَلْيَتَحَلَّلْهُ مِنْهُ اليَوْمَ، قَبْلَ أَنْ لاَ يَكُونَ دِينَارٌ وَلاَ دِرْهَمٌ، إِنْ كَانَ لَهُ عَمَلٌ صَالِحٌ أُخِذَ مِنْهُ بِقَدْرِ مَظْلَمَتِهِ، وَإِنْ لَمْ تَكُنْ لَهُ حَسَنَاتٌ أُخِذَ مِنْ سَيِّئَاتِ صَاحِبِهِ فَحُمِلَ عَلَيْهِ». [البخاري، 2449].
الحادي والأربعون: عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِيَّاكُمْ وَالظَّنَّ، فَإِنَّ الظَّنَّ أَكْذَبُ الحَدِيثِ، وَلاَ تَحَسَّسُوا، وَلاَ تَجَسَّسُوا، وَلاَ تَنَاجَشُوا، وَلاَ تَحَاسَدُوا، وَلاَ تَبَاغَضُوا، وَلاَ تَدَابَرُوا، وَكُونُوا عِبَادَ اللَّهِ إِخْوَانًا». [البخاري، 6064، ومسلم، 2563].
الثاني والأربعون: عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنْ حَمَلَ عَلَيْنَا السِّلَاحَ فَلَيْسَ مِنَّا، وَمَنْ غَشَّنَا فَلَيْسَ مِنَّا». [مسلم، 101].
هذا ما تم اختياره. والحمد لله الذي بنعمته تتم الصالحات.
والصلاة والسلام على النبي الكريم، وعلى آله وصحبه والتابعين.

11/شوال/1438هـ الموافق/5/يوليو/2017م بالمدينة النبوية.

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...