2015/04/09

SAKO ZUWA GA MA'AIKATA





TA YAYA MA AIKACI ZAI SAUKE AMANA?!

(كيف يؤدِّي الموظَّفُ الأمانةَ)
 (Hanyoyin da ma'aikaci zai bi wajen sauke nauyin dake kansa!)












NA

AS-SHEIKH ABDUL-MUHSIN BN HAMD AL-ABBAD
Allah ya kara datar da shi, ya kuma taimake shi









Fassarar:
Abubakar Hamza





ABUBUWAN DA SUKE CIKIN LITTAFIN

SHAFI
Abubuwan da suke cikin littafin
2
Gabatarwa
3
AYOYI MASU KARAMCI DA SUKE MAGANA KAN SAUKE AMANA
3


HADISAI DAGA MANZON ALLAH ( S A W ) KAN BADA AMANA
5


MA'AIKACI YAYI AIKINSA DA KWAZO DA KUMA IKHLASI, ZA A BASHI LADANSA A DUNIYA DA LAHIRA:
7


KIYAYE LOKACIN DA AKA KEBE MA AIKI DON AIKATA ABINDA ZAI BUNKASA AIKIN:
8


ABIN LURA WAJEN ZABEN MAI KWADAGO DA MA'AIKATA
9


MANYAN MA'AIKATA ABIN KOYI NE = WAJEN KWAZO KO KASALA GA KANANANSU
11


MU'AMALANTAR MA'AIKACI GA WANINSA DA IRIN ABINDA YAKE SON A MU'AMALANCE SHI DA SHI
12


MA'AIKACI YA GABATAR DA WANDA YA RIGA ZUWA SAI WANDA KE BIYE, DAGA MABUKATA (MAZOWA WURINSA)
14


SIFFANTUWAR MA'AIKACI DA SIFFAR KAMEWA TARE DA KUBUTA KO BARIN CIN RASHAWA, DA NIISANTAR KARBAR KYAUTA
15







بسم الله الرحمن الرحيم
            Malam a farkon littafinsa –bayan yayi bismillah– Sai yace:
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai, Yabo da aminci cikakku guda biyu sun tabbata ga shugaban Manzanni kuma jagoran masu tsoron Allah, Annabinmu Muhammad da kuma Iyalansa da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.                              Bayan haka:
Wannan takarda ce karama da na rubuta don yin nasiha wa ma'aikata; da fatan su sauke tare da aiwatar da abinda aka rataya a wuyansa na aiki ta fiskar da ta dace, Lallai na rubuta ta da fatan ma'aikatan su amfana da ita, haka; don ta taimake su wajen gyara niyyarsu, da kuma kokari cikin aikinsu da kuma tsayuwa wajen aikata wajibinsu.
Ina kuma rokon Allah ta'alah aikata daidai da dacewa, gare mu gaba daya.


AYOYI MASU KARAMCI DA SUKE MAGANA KAN SAUKE AMANA:
Daga cikin ayoyin da suke magana kan sauke/ kiyaye amana da barin ha'inci:
}إنَّ الله يأمرُكم أنْ تُؤدُّا الأمانات إلى أهلها وإذا حكمتم بين الناس أنْ تحكموا بالعدل إنَّ الله نعمّا يعِظكم به إنَّ الله كان سميعًا بصيرًا{النساء: ٥٨
Ma'ana: "Lallai Allah yana umurtarku da ku bada amanoni  zuwa ga ma'abotansu, kuma idan za kuyi hukunci tsakanin mutane ku yi hukunci da adalci, lallai Allah madalla da abinda yake muku umurni da shi, lallai Allah ya kasance mai ji ne mai gani" [Nisa'i: 58].
Ibn kasir ya fada a tafsirinsa: (Allah) madaukaki ya bada labarin cewa lallai shi yayi umarnin bada amanoni zuwa ga ma'abotansu, ya zo cikin hadisin Alhasan bn samurah lallai manzon Allah (s.a.w) yace:
((أدِّ الأمانة إلى مَن ائتمنك، ولا تخنْ مَن خانك)).
 Ma'ana: ka mayar da amana zuwa ga wanda ya baka amana, kuma kada ka ha'inci wanda ya ha'inceka''. Imamu Ahmad da ma'abota littafin "sunan" ne suka ruwaito shi.
Wannan kuma ya game dukkan amanoni na wajibi akan mutum na daga hakkokin Allah  mai girma da daukaka akan bayinsa; na sallah da zakka da azumi da kaffarori da kuma bakance, da wassun haka, daga cikin abinda Allah ya bawa mutum amana, kuma bayi basa tsinkaya akansa (ganinsa).
Da kuma    hakkokin bayi sashinsu zuwa ga sashe; kamar jingina da wassunsa wadanda mutane ke bada amanarsa ba tare da sun tsinkayar da shaidu ba akan haka;
Sai Allah mai girma da daukaka ya yi umurni da a bada shi, duk kuma wanda bai aikata haka ba a duniya to za'a dauka daga wajensa ranar kiyama".
  
Da kuma saboda fadinsa madaukaki:
}يا أيُّها الذين ءامنوا لا تخونوا الله والرسول وتخونوا ءماناتكم وأنتم تعلمون{ [ الأنفال: ٢٧ ].
  Ma'ana: "Ya ku wadanda suka yi imani kada ku ha'inci Allah da wannan Manzon, kuma ku ha'inci amanoninku alhalin kuna sani" [Anfaal: 27].
Ibn kasir yace: Shi kuma ha'incin ya game dukkan zunubai; manyansu da kananansu, wadanda suka takaita (ga mutum) da wadanda suka tsallake shi zuwa ga waninsa, Aliyu bn Abiy Dalhatu yace daga ibn Abbas (r.a):
 "وتخونوا أماناتكم ": الأمانة التي ائتمن الله عليها العباد".
Ma'ana sai ku ha'inci amanoninku" na nufin: amanonin da Allah ya nemi bayi su bayar, wato : farillai, yana cewa kada ku ha'inci =kada ku warware su.
A wata riwayar kuma ya ce:
 "لا تخونوا الله والرسول" يقول: يترك سنته وارتكاب معصيته".
 Ma'ana: kada ku ha'inci Allah da wannan Manzon) da barin sunnoninsa da kuma fadawa cikin sabonsa"
Da kuma fadin (Allah) Madaukaki:
}إنَّا عرضنا الأمانة على السماوات والأرض والجبال فأبَيْنَ أنْ يحمِلنَها وأشفقنَ منها وحملها الإنسان إنَّه كان ظلوماً جهولاً{ [ الأحزاب: ٧٢ ]
Ma'ana: (Lallai mune muka bijiro da amana ga sammai da kassai da duwatsu sai suka ki daukarta, suka kuma tsorata daga gareta, Sai shi kuma mutum ya dauke ta, lallai shi ya kasance mai yawan zalunci ne, mai yawan jahilci"[Ahzaab: 72].
Ibn-kasir yace- bayan ya ambaci zantuttukan maluma da maganganunsu kan tafsirin "amana"; Wanda daga cikinsu akwai:
1- Biyayya da da'a
2-Farillai
3-Addini
4-Haddi mabanbanta.                                                                                                                                       
 Sai yace: " Duk kan wadannan maganganu wani baya goge wani; saboda dukkansu sun yi ittifaki, kuma suna komawa zuwa ga taklifi da karbar umarni da hani tare da sharadinsa;- wanda shine: Duk kuma wanda ya tsayu wajen haka to za'a bashi lada akai. Idan kuma ya bar hakan a hora shi; Sai mutum ya karbe shi -tare da rauninsa da jahilcinsa da zaluncinsa; In banda  wanda Allah ya datar da shi, Allah ne kawai abin taimako).
Da kuma fadin Allah madaukaki:
}والذين هم لأماناتهم وعهدِهم راعون{. [ المؤمنون: 8]
Ma'ana: sune wadanda dangane da amanoninsu da alkawarinsu masu lura ne" [Muminuna: 8].
Ibn-kasir yana cewa :"In an basu amana basa ha'inta, idan akayi alkawari dasu kuma basa sabawa, wannan kuma shine siffofin muminai; kamar yadda ya zo cikin hadisi ingantacce:
"آية المنافق ثلاث: إذا حدَّث كذب, وإذا وعد أخلف, وإذا ائتمن خان" وفي رواية: إذا حدث كذب, وإذا عاهد غدر, وإذا خاصم فجر".
Ma'ana: alamomin munafuki guda uku ne: idan yayi zance sai yayi karya, idan yayi alkawari kuma sai ya saba, sannan idan aka bashi amana sai yayi ha'inci''.
A wata riwayar kuma: "Idan yayi magana sai yayi karya, idan yayi alkawari kuma sai ya ki cikawa, haka kuma idan yayi kusuma (fada sai aka raba su) sai ya fajirce".



HADISAI DAGA MANZON ALLAH ( S A W ) KAN BADA AMANA
         Daga cikin hadisai daga Manzon Allah ( s a w ) kan kiyaye amana, da kuma hani kan tozartata:

Na daya: Daga Abu-hurairah (r a) Lallai yace:
"بينما النبي r في مجلس يحدث القوم, جاءه أعرابي فقال: متى الساعة؟ فمضى رسول الله r يحدث, فقال بعض القوم: سمع ما قال فكره ما قال, وقال بعضهم: بل لم يسمع, حتى إذا قضى حديثه, قال: أين أُراه السائل عن الساعة؟ قال: ها أنا يا رسول الله, قال: فإذا ضُيّعت الأمانة فانتظر الساعة, قال: إضاعتها؟ قال إذا وسد الأمر إلى غير أهله فانتظر الساعة" رواه البخاري. (59).
 Ma'ana: "Wata rana Annabi (s a w) yana wani majlisi yana bada hadisi wa mutane sai wani balaraben kauye ya zo; yace: Yaushe ne tashin kiyama?! Sai Manzon Allah (s a w)  ya ci gaba da bada hadisinsa; Sai wassu daga cikin mutanen suka ce: ya ji abinda ya fada sai kuma ya kyamace shi (ya ki), Wassun kuma suka ce: a'a; annabi bai ji ba.
Bayan ya gama hadisinsa sai yace: '' Ina zan ga mai tambaya kan lokacin kiyama!?
Sai yace: Gani nan ya Manzon Allah! Sai yace: Idan aka tozarta amana to ka jira tashin kiyama!
Sai yace: yaya ne tozartata?
Sai yace: Idan aka jingina al'amari na shugabanci zuwa ga wanda  bai dace  da shi ba to ka jira kiyama''. Bukhari ne ya ruwaito shi (59)

Na biyu: Daga Abu Hurairah (r.a) Lallai shi yace: Manzon Allah (s a w) yace:
"أدِّ الأمانة إلى من ائتمنك, ولا تخُن مَن خانك".
Ma'ana: ka mayar da amana zuwa ga wanda ya baka ita, kuma kada ka ha'inci wanda ya ha'inceka'' Abu Da'uda ne ya ruwaito shi (3535) da Tirmiziy (1264) kuma yace: hadisi ne  حسن غريب [Duba/ As-silsilatus sahihatu na Albani (lamba: 424)].

Na Uku: Daga Anas (r.a) yace: Annabi ( s a w ) yace:
"أول ما تفقدون من دينكم: الأمانة, و آخره: الصلاة".
Ma'ana: "Farkon abinda zaku rasa daga addininku shine: AMANA, na karshensa kuma sallah". [Khara'idiy ne ya ruwaito shi cikin makarimul akhlak (28), Duba littafin/ as-silsilatus sahihah na Albaniy (lamba: 1739)].

Na hudu: Daga Abu hurairah (r.a) daga Annabi (s a w) lallai yace:
"آية المنافق ثلاث: إذا حدث كذب, وإذا وعد أخلف, وإذا ائتمن خان".
Ma'ana: alamomin munafuki guda uku ne: (1) Idan yayi zance sai yayi karya (2) Idan yayi alkawari sai ya karya (3) Idan aka bashi amana kuma sai yayi ha'inci". Bukhariy (33) da Muslim (107) ne suka ruwaito shi.



MA'AIKACI YAYI AIKINSA DA KWAZO DA KUMA IKHLASI, ZA A BASHI LADANSA A DUNIYA DA LAHIRA:
Idan ma'aikaci ya tsayu wajen yin aikinsa da kwazo, yana kuma fatan ladan Allah, to sai ya kubutar da wuyansa, sannan ya cancanci ladan aikin (Albashi ko waninsa) a nan gidan duniya, sannan kuma ya rabauta da lada a gidan lahira.
Kuma hakika nassoshin shari'a sun zo suna nuni cewa lallai lada kan abinda mutum ke aikatawa na aiyuka kawai ya kan kasance ne idan aka nemi ladansa kuma aka nufi Allah da neman ganin fuskarsa da aiki; Allah mai girma da daukaka yana cewa:
 }لا خير في كثيرٍ من نجواهم إلا من أمر بصدقة أو معروفٍ أو إصلاحٍ بين الناس ومن يفعل ذلك ابتغاء مرضاة الله فسوف نؤتيه أجرًا عظيمًا{ [ النساء: ١١٤].
Ma'ana: "Babu alkhairi cikin dayawa daga ganawarsu sai dai wanda yayi umarni da sadaka, ko yin aiki da abu mai kyau, ko sulhu a tsakanin mutane, duk wanda ya aikata haka yana mai neman yardar Allah to da sannu zamu bashi lada mai girma" [Nisa'i: 114].
Kuma Bukhariy  (55) da Muslim (1002) sun ruwaito daga Abu mas'ud (r.a) lallai Manzon Allah (s a w) yace:
 "إذا أنفق الرجل على أهله يحتسبها فهو له صدقة".
Ma'ana: "Idan mutum ya ciyar da iyalansa- alhalin yana neman lada akan haka- to wannan din sadaka ne a gare shi".
Kuma  Annabi (s a w) yace wa Sa'ad bn Abiy-wakkas:
"ولستَ تنفق نفقة تبتغى بها وجه الله إلا أُجِرتَ بها, حتى اللقمة تجعلها في في امرئتِك".
 Ma'ana: "Ba za ka ciyar da wata ciyarwa ba kana mai neman fiskar Allah da ita, face an baka lada akanta, kai! Har loma da zaka sanya a bakin matarka'' Bukhari (5354) da Muslim (1628) ne suka ruwaito shi.
Wadannan nassoshin sun yi nuni cewa lallai musulmi idan ya bayar da abinda ke kansa na wajibin bayi a kansa to wuyansa ya kubuta, kuma sa'annan abin sani kawai zai samu lada ne (a wajen Allah) idan ya nemi ladan (ya kuma yi ikhlasi) kuma ya nemi fiskar Allah (Tsarki da daukaka sun tabbata a gare shi).

KIYAYE LOKACIN DA AKA KEBE MA AIKI DON AIKATA ABINDA ZAI BUNKASA AIKIN:
Ya zama wajibi (dole) ga dukkan ma'aikaci (aikin hukuma da waninsa) ya cike dukkan lokaci da aka kebe masa; kar yayi wassu al'amura na daban ba aikin da ya zama dole ya aikata a cikinsa ba, kamar kuma yadda ba zai cike lokacin ko sashensa ba da wani abinda maslaharsa ce kawai (ba na aiki ba), ko maslahar waninsa idan ta zama bata da alaka da aikin; saboda lokacin aikin ba mallakar ma'aikaci ba ne; kai dai lokacin mallakin aikin da aka karbi kudi don aikata shi ne.
Hakika As-sheiku Almu'ammar bn Aliyu Albagdadiy (wanda ya rasu a shekarar hijira 507) yayi nasiha wa Nizamal mulki Alwazir wa'azi mai ratsa jiki mai amfani, daga cikin abinda ya fada a farkonta "Sananne ne -ya kai sadrul islam- lallai dayan wadanda ake jagorantarsu (wadanda ba shugabanni ba) suna da zabi cikin masu nufo su da masu zuwa musu; (ta yadda) idan sun so sai su sadar, idan kuma sun so sai su yanke, Sai dai kuma duk wanda ya tufata da shugabanci, to shi kam bashi da zabi kan wanda ya nufo shi da wanda ya zo masa; saboda duk wanda ya zama shugaban wassu halittu, to shi fa hakika kamar dan-kwadago ne, saboda ya sayar da lokacinsa ya kuma karbi kudinsa; don haka; Babu wani abu da ya rage masa a yininsa da zai sarrafa shi cikin zabinsa, kai! Bashi da damar yin sallar nafila ko ya shiga wajen yin i'itikafi …; saboda wancan nafila ne, wancan kuma farilla ne dole".
Daga cikinta kuma akwai fadinsa- alhali yana masa wa'azi -:
"فاعمُر قبرَك كما عمَرتَ قصرَك".
 Ma'ana: kuma ka raya kabarinka kamar yadda ka raya  benin gidanka", [Duba zailu dabakatil hanabilah (1/107)].
Kuma lallai kamar yadda mutum ke kwadayin ya karbi ladansa (ko albashinsa) a cike ba nakasu, sannan baya so a tauye masa wani abu daga ciki; to haka kuma ya zama dole akansa kada ya tauye komai na lokacin aiki wajen sarrafa shi ba'a abinda zai zama maslahar aikin ba. Kuma hakika Allah ta'alah ya zargi masu tauye ababen awu da ma'aunai wadanda ke neman hakkokinsu a cike, sannan su tauye hakkokin wassunsu Yace:
} ويلٌ للمطففين * الذين اكتالوا على الناس يستَوفون * وإذا كالوهم أو وزنوهم يُخسرون * آلا يظنُّ أولئك أنَّهم مبعوثون * ليومٍ عظيم * يوم يقوم الناس لربِّ العالمين { [ المطففين: 1 – 6 ]  
Ma'ana: ''kwarin azaba ta tabbata ga masu tauyewa, wadanda idan suka auna daga mutane suke neman cikawa, kuma idan suka auna musu, ko suka gwada musu (wato a sikeli) suke tauyewa, shin wadancan kam basu da tabbacin cewa lallai su abun tayarwa ne, ga wani yini mai girma, yinin da mutane zasu tsaya gaba ga ubangijin halittu?! [Mudaffifina: 1-6].




ABIN LURA WAJEN ZABEN MAI KWADAGO DA MA'AIKATA:
Tushe wajen zaban kowane ma'aikaci (na hukuma ko waninsa) shine ya zama:
1.    Mai karfi
2.    amintacce;
 Saboda da karfi ne zai iya tsayuwa da aikin da ake nema daga wajensa, da amana ne kuma, zai yi shi ta fiskar da wuyarsa zata kubuta, kuma da amana ne zai iya ajiye abubuwa a gurabansu … Hakika Allah ya bada labarin daya daga cikin 'ya'yan mutumin garin Madyana, da kuma fadinta wa mahaifinta - yayin da (Annabi)  Musa  (a.s) ya shayar musu da dabbobinsu - :
} يا أبتِ استأجِرْهُ إنَّ خير من استأجرْت القويُّ الأمين { [ القصص: ٢٦ ]
Ma'ana: Ya babana! Ka nemi ya rika maka kwadago, lallai mafi alkhairin wanda ka nemi aikinsa shine: mai karfi, kuma amintacce" [Kasas: 26].
Sannan Allah yana cewa – dangane da ifritu daga cikin aljanu wanda ya baiyana wa (Annabi) sulaiman (a.s) shirinsa kan kawo al'arshin Bilkis-:
} أنا آتيك به قبل أنْ تقوم من مقامك إني عليه لقويٌّ أمين {[ النمل: ٣٩ ]
Ma'ana: "Ni zan zo maka da shi kafin ka tashi daga wajen zamanka, kuma lallai ni akansa (kawo al'arshin) lallai mai karfi ne kuma amintacce" [Naml: 39]; Ma'anar wannan shine: lallai shi (ifritu) ya hada tsakanin ikon daukar al'arshinta, da kuma halarto da shi, tare da: kiyaye shi da kawo shi da duk abinda ya kunsa (wannan kuma shine amana, a nan).
          Sannan Allah  ya bada labarin Yusuf (a.s) cewa lallai shi  ya ce ma wannan sarkin:
} قال اجعلني على خزائن الأرض إنِّي حفيظٌ عليم {[ يوسف: ٥٥ ]
Ma'ana: ''Ka sanya ni (jagora) kan taskokin kasa; lallai ni mai kiyayewa ne masani" [Yusuf: 55].
Kishiyan "karfi da amana" kuma sune "rauni da ha'inci"; wanda kuma sune tushe ko ginshiki wajen kin zaben (mutum) a matsayin ma'aikaci, kuma sune abubuwa na hakika da zasu halatta tobe (mutum) ko tsige ma'aikin daga (aiki). Wannan kuma shi dalilin da ya sanya Umar bn khaddab (r.a) ya nada Sa'ad bn Abiy-wakkas a matsayin gomna a garn Kufa, sannan aka samu wawayen cikinta suna sukansa, kuma suka kawo saransa wajen khalifa Umar (r.a); Sai (Umar) ya ga cewa maslaha tana hukunta ya tobe shi; saboda (1) tunkude fitina, (2)  kuma saboda kada wani daga cikinsu ya masa ta'addanci.
Sai dai Umar (r.a) a rashin lafiyan rasuwarsa ya aiyana mutane shida daga sahabban manzon Allah (s a w) da za a zabi khalifa daga cikinsu a bayansa kuma daga cikinsu din akwai  sa'ad bn Abiy-wakkas (r.a) sai kuma yaji tsoron kada wani yayi zaton cewa: tobewan da Umar (r.a) yayi wa (sa'ad r.a) daga gomnan garin Kufa (sababinsa shine) saboda rashin cancantarsa da wannan shugabanci; sai ya kore abun da za a iya zaton da fadinsa:
"فإنْ أصابت الإمرةُ سعدًا فهو ذاك, وإلا فليستعن به أيُّكم ما أُمِّر؛ فإني لم أعزِلْه عن عجَزٍ ولا خيانةٍ".
Ma'ana: "Idan shugabancin ya samu Sa'ad to shikenan, idan kuma a'a to duk wanda aka shugabantar ( a matsayin amirul mu'uminin ) ya nemi taimakonSa; saboda lallai ni ban tobe shi ba wai saboda gazawa, ko kuma ha'inci", Bukhariy ne [lamba: 3700] ya ruwaito shi.
 - Ya zo cikin sahihu Muslim [lamba: 1825] daga Abu-zarri (r.a) lallai yace:
"قلت لرسول الله! ألا تستعملني؟ قال: فضرب بيده عليّ منكبِي ثم قال: ((يا أبا ذر! إنك ضعيف وإنها أمانة, وإنها يوم القيامة خِزْيٌ وندامة, إلا مَن أخذها بحقها، وأدّى الذي عليه فيها)).
 Ma'ana: '' Nace wa Manzon Allah! Shin ba za ka ban aiki ba? Yace: Sai ya doki kafadata da hannunsa sannan yace: ya kai aba-zarrin! Lallai kai fa mai rauni ne, lallai kuma shi (aiki) amana ne, sannan kuma lallai shi (aikin) ranan tashin kiyama tabewa ne da nadama, sai dai wanda ya dauke shi da hakkinsa, sannan ya bada abinda ke kansa a cikinsa". Kuma lallai a cikin sahihu Muslim [lamba: 1826] daga Aba-zarrin (r.a) lallai Manzon Allah (s a w) yace:
((يا أبا ذر إني أراك ضعيفًا, وإني أحبُّ لك ما أحبُّ لنفسي, لا تأْمرَن علي اثنين, ولا توليَّن مالَ يتيم)).
 Ma'ana: '' Ya kai Abu zarrin lallai ni ina ga kai mai rauni ne, kuma lallai ina so maka abinda nake so wa kaina;! Kada ka zama shugaban mutane guda biyu, kuma kada ka jibinci dukiyar maraya".




MANYAN MA'AIKATA ABIN KOYI NE = WAJEN KWAZO KO KASALA GA KANANANSU:
Idan manyan ma'aikata suka tsayu wajen aikata abinda ya wajabta akansu cikakken tsayuwa to sai ma'aikata kanana mabiyansu su yi koyi dasu,  (kamar yadda kishiyan hakan shima daidai ne) kuma lallai kowane shugaba cikin wani aiki to za a tambaye shi kan kansa da wadanda yake shugabanta, kamar yadda Manzon Allah (s a w) yake cewa:
((كلكم راع ومسؤول عن رعية؛ فالأمير الذي على الناس فهو راعٍ عليهم وهو مسؤول عن رعيته, والرجل راع على أهل بيته وهو مسؤول عنهم, والمرأة راعية على أهل بيت بعلها وولده وهي مسؤولة عنهم, والعبد راعٍ على مال سيده وهو مسؤول عنه, ألا فكلكم راع, وكلكم مسؤول عن رعيته)).
Ma'ana: "Dukkan ku masu kiyo ne, kuma ababen tambaya kan abinda aka basu kiyo, shugaba da ke kan mutane mai kiyo ne a kansu kuma shi abun tambaya ne a kansu, Mutum mai kiyo ne ga iyalan gidansa, kuma shi abin tambaya ne a kansu, Bace mai kiyo ce kan gidan mijinta da yaransa kuma ita abar tambaya ce akansu, Bawa mai kiyo ne ga dukiyar shugabansa kuma shi abin tambaya ne akansa, Ku saurara!! Dukkan ku masu kiyo ne, kuma dukkan ku abun tambaya ne kan abinda aka baku kiyo", Bukhariy [lamba: 2554] da Muslim ne [lamba: 1829] suka ruwaito shi daga Abdullahi bn umar (r.a).
Don haka; Idan manyan ma'aikata suka kiyaye aiyukansu cikin lokuta, gabadaya Sai su zama abin koyi mai kyau ga wadanda suke karkashinsu,
Wani Mawaki yana cewa:
"وإنَّك إذْ ما نأت ما أنت آمِرٌ ...
به تلفِ مَن إياه تأمُر آتيا".
Ma'ana: "Kuma lallai kai idan ka aikata abinda kake umarni da shi, to za ka samu wanda kake masa umarni na zuwa da abinda kayi umarnin.
Ma'anar wannan shine: Idan har ka umarci waninka da ke kasa da kai cewa ya aikata wajibinsa,- sai kuma kayi rigaye wajen tsayuwanka da wannan wajibin- to zaka samu waninka yana mai amsa maka, kuma yana mai tsayuwa da abinda ka umurce shi.


MU'AMALANTAR MA'AIKACI GA WANINSA DA IRIN ABINDA YAKE SON A MU'AMALANCE SHI DA SHI:
          Ita nasiha sha'aninta a cikin musulunci yana da girma; shi yasa Manzon Allah yace:
((الدين النصيحة, قالوا: لِمَن يا رسول الله؟ قال: لله, ولكتابه, ولرسوله, ولأئمة المسلمين, وعامتهم)).
Ma'ana: "Addini shine nasiha, sai suka ce ga wa?- ya Manzon Allah- sai yace: Ga Allah, da littafinsa, da manzonsa, da kuma shugabannin musulmai da sauran musulmai'' Muslim [lamba: 55] ne ya ruwaito shi daga Abu-rukayyah Tamimu bn Aus Addariyyi (r.a). Shi kuma Jarir bn Abdullahi albajaliy (r.a) yace:
"بايعْتُ رسولَ الله r على إقام الصلاة, وإيتاء الزكاة, والنصح لكل مسلمٍ".
 Ma'ana: '' Nayi mubaya'a wa Manzon Allah (s a w) kan tsayar da sallah, da bada zakka, da kuma nasiha ga kowane musulmi'' Bukhari [lamba: 57] da Muslim [lamba: 56] suka ruwaito shi.
Kuma kamar yadda kowane ma'aikaci idan yana da bukata a wajen waninsa yake son waninsa ya mu'amalance shi mu'amala mai kyau to shima wajibi ne ya mu'amalanci waninsa da mu'amala mai kyau; Manzon Allah (s a w) yace:
((فمَن أحبَّ أن يُزحزح عن النار، ويدخل الجنة فلتأته منيّته وهو يؤمن بالله واليوم الآخر, وليأتِ إلى الناس الذي يُحبّ أنْ يؤتى إليه)).
Ma'ana:" Duk wanda yaso a kawar da shi ga barin wuta, a kuma shigar da shi aljanna to mutuwarsa ta zo masa alhalin yana mai imani da Allah da ranar karshe, ya kuma zo wa mutane da kwatankwacin abinda yake son a aikata masa" Muslim [lamba: 1844] ne ya ruwaito shi cikin hadisi dogo daga Abdullahi bn Umar (r.a). Ma'anan wannan shine: "Ka mu'amalanci mutane da irin abinda kake son su mu'amalance ka da shi.
Kuma Annabi (s a w)  yana cewa:
((لا يؤمن أحدكم حتى يحب لأخيه ما يحبّ لنفسه)).
Ma'ana: "Imanin dayanku baya cika har sai ya so wa dan uwansa abin da yake so wa kansa ''Bukhari (13) da muslim (45) ne suka ruwaito shi daga Anas (r.a)
Kuma hakika Allah ya zargi wanda ya ke mu'amalantar waninsa da sabanin abinda ya ke son a mu'amalance shi da shi cikin fadinsa madaukaki:
} ويلٌ للمطففين * الذين اكتالوا على الناس يستَوفون * وإذا كالوهم أو وزنوهم يُخسرون { [ المطففين: 1 – 3 ]  
Fassaran ayoyin ya gabata.
Manzon Allah ( s a w ) yana cewa:
"إنَّ الله عز وجل حرَّم عليكم عقوق الأمهات, ووأد البنات, ومنعًا وهات, وكره لكم ثلاثا: قيل وقال, وكثرة السؤال وإضاعة المال".
Ma'ana: "Lallai Allah mai girma da daukaka ya haramta muku kin biyayya wa iyaye, da bunne 'ya'ya mata, da kuma  hani da bani (rowa da kwadayi). Kuma ya kiye muku aikata abubuwa guda uku: jita-jita, da yawan tambaya  (ko tambayar kure) da kuma tozarta dukiya'' Bukhari [lamba: 2408] da Muslim [lamba: 593] ne suka ruwaito shi daga Almugirah bn shu'ubah (r.a).
A cikin wannan hadisin Annabi (s a w) ya zargi mutumin da ke tara dukiya mai hanawa; wanda yake karba, baya bayarwa;
Kuma hakika Allah ya tunatar da majibinta marayu da cewa sun kasance su kan ji tsoro ga kananan zurriyarsu- da (za a kaddara) su bar su, yace:
 } وليخشَ الذين لو تركوا من خلفِهم ذرِّيةً ضِعافًا خافوا عليهم فاليتقوا الله وليقولوا قولاً سديدًا { [ النساء: 9 ].
Ma'ana: "Su ji tsoro; Wadanda da sun bar zurriya masu rauni - a bayan rasuwarsu- za su kasance masu jiye musu tsoro (to irin wadannan mutanen da suke tsorace wa kananan 'ya'yansu tozarta a bayan rasuwarsu to su sani cewa: iyayen marayun nan suma gabanin rasuwarsu haka suke dangane da 'ya'yansu; don haka) su ji tsoron Allah  kuma su fadi magana da ta dace" [Nisa'i: 9].
Ma'anarta kuwa: kamar yadda su suke son a kyautata wa zurriyarsu masu rauni bayan rasuwarsu, to suma dole ne akansu su kyautata wa marayu da suke shugabantarsu.


MA'AIKACI YA GABATAR DA WANDA YA RIGA ZUWA SAI WANDA KE BIYE, DAGA MABUKATA (MAZOWA WURINSA):
Yana daga adalci kada ma'aikci ya jinkirta wanda ya riga daga cikin (mazowansa) masu bukata, ko kuma ya gabatar da wanda yayi jinkiri  (ya zo a karshe), (saboda adalci shine): gabatarwan ya kasance- a wajensa- gwargwadon rigaye, kuma cikin haka akwai hutu ga ma'aikacin tare da Mazowan nasa mabukata, Kuma hakika dalili ya zo cikin sunnar manzon Allah (s a w) a kan haka; Daga Abu Hurairata (r.a) lallai shi yace:
"بينما النبي r في مجلس يحدث القوم, جاءه أعرابيٌّ فقال: متى الساعة؟ فمضى رسول الله r يُحدِّث, فقال بعض القوم: سمِع ما قال فكره ما قال, وقال بعضهم: بل لم يسمع, حتى إذا قضى حديثَه قال: أين أُراه السائل عن الساعة؟ قال: ها أنا يا رسول الله, قال: فإذا ضُيِّعت الأمانةُ فانتظر الساعة قال: كيف إضاعتها؟ قال: إذا وُسِّد الأمر إلى غير أهله فانتظر الساعة".  
Fassaran hadisin ya gabata.
Bukhariy ne [lamba: 59] ya ruwaito shi.
Dalili daga wannan hadisin shine: lallai Manzon Allah (s a w) bai amsa wa mai tambaya kan tashin kiyama ba sai bayan gama bada hadisi ga wadanda suka rigaye shi.
Ibn-Hajar ya fada cikin sharhinsa: ''Daga (wannan hadisin) zamu koyi cewa: Daukar darrusa ya kan kasance ne gwargwadon rigaye, haka kuma (al'amarin) fatawowi da hukumomi da wassunsu'' (suma zasu kasance gwargwadon rigaye).
          Ya zo cikin tarjama ko tarihin Abu ja'afar muhammad bn Jarir Addabariy, a cikin LISANUL MIIZAAN na Hafiz ibn Hajar; fadinsa: ''Kuma ibn asakir ya fitar (da wannan maganar) daga Abiy-ma'abad Usman bn Ahmad Addainuriy, lallai yace: Na halarci majlisar Muh'd bn jarir Addabariy sai fadlu bn ja'afar bn alfura-at alwazir (minista) ya zo, sai dai kuma wani mutum ya riga shi, sai Dabariy yace wa wannan mutumin: shin ba za kayi karatu ba ne? Sai yayi nuni zuwa ga wannan ministan, sai dabariy yace masa idan layi ya zo kansa kada ka damu da (kogin) dijlat, ko furat.
Nace: (mai magana shine: Ibn-hajar) wannan yana cikin fa'idodin da wannan malami Ibn jarir ya bayar (lada'if) da kuma balagarsa, tare da rashin damuwarsa da 'yan duniya (masu kudi ko masu mulki).


SIFFANTUWAR MA'AIKACI DA SIFFAR KAMEWA TARE DA KUBUTA KO BARIN CIN RASHAWA, DA NIISANTAR KARBAR KYAUTA:
Wajibi ne kan kowane ma'aikaci ya kasance mai kamewa, ya kuma zamanto mai izza a ransa, mai wadatar zuci, tare da nisanta ko barin cin dukiyar mutane da barna, na daga abinda ake gabatar masa na rashawa ko da kuwa an kira shi: kyauta; saboda idan ya dauki dukiyar mutane ba tare da hakki ba to ya cinye ta ne  da barna; shi ko cin dukiya da barna na daga cikin sabbuban rashin karbar addu'a; Imam Muslim [lamba: 1015] ya ruwaito a cikin sahihinsa daga Abu-hurairah (r.a) lallai shi yace:
"أيها الناس! إن الله طيِّب لا يقبل إلا طيِّبًا, وإنَّ الله أمَر المؤمنين بما أمَر به المرسلين, فقال: (يا أيها الرسل كلوا من الطيبات واعملوا صالحا إني بما تعملون عليم) وقال: (يا أيها الذين ءامنوا كلوا من طيبات ما رزقناكم) ثم ذكر الرجل يطيل السفر, أشعث أغبر, يمد يديه إلى السماء : يا رب! يا رب!! ومطعمه حرام, ومشربه حرام, وملبسه حرام, وغذي بالحرام فأنى يستجاب لذلك!".
 Ma'ana: " Ya ku mutane lallai Allah mai tsarki ne, baya karbar aiki sai mai tsarki, kuma lallai Allah ya umurci muminai da irin abinda ya umurci manzanni da shi; yace ya ku wadannan manzanni ku ci daga dadada /tsarkaka kuma ku aikata mai kyau; lallai ni dangane da abinda kuke aikatawa masani ne" Sannan yace: "Ya ku wadanda su kayi imani ku ci daga dadadan abinda muka azurta ku" sannan sai ya ambaci wannan mutumin da ke tsawaita tafiya, mai yawan kullewar gashi, mai yawan kura, yana mika hannu zuwa ga sama; yana cewa: ya ubangiji! Ya ubangiji!! Alhalin abincinsa haramun ne, abin shansa haramun ne, tufarsa ta haramun ne, kuma an ciyar da shi daga haramun, to ta yaya za'a amsa ma wannan?!".
Daga cikin dalilai da suka fito fili wajen horarwa da kyamatarwa kan cin dukiya da barna, akwai hadisin da Bukhariy ya ruwaito cikin sahihinsa [da lamba: 7152] daga Jundub bn Abdullah (r.a), yace:
"إنَّ أول ما يُنتِن من الإنسان بطنُه فمَن استطاع أن لا يأكل إلا طيِّبًا فليفعل, ومَن استطاع أنْ لا يُحال بينه وبين الجنة بملء كفٍّ مِن دمٍ هراقه فليفعل".
Ma'ana: "Lallai farkon abinda zai fara wari daga jikin mutum shine: cikinsa; Don haka: duk wanda ya samu damar kada ya ci, sai abu mai tsarki to ya aikata, kuma duk wanda ya samu damar kada a shamakance tsakaninsa da tsakanin Aljanna da cikin tafin hannu na jini da ya zubar da shi, to ya aikata".
Da kuma abinda Bukhariy ya sake ruwaitowa [lamba: 2083] daga Abu-hurairah (r.a) daga Annabi ( s a w ) lallai yace:
"ليأتينَّ على الناس زمانٌ؛ لا يبالي المرءُ بما أخذ المال, أَمِن حلالٍ أم مِن حرامٍ".
Ma'ana: "Lallai wani lokaci zai zo wa mutane wanda mutum ba zai damu da mai  ya dau dukiya ba; shin daga halal ne ko daga haram ne!", A wajen wadannan -masu daukar, wadanda basu damu ba- lallai halal kawai shine: abin da ya fado a hannu, haka kuma haram shine: abinda bai iso zuwa ga hannun mutum ba, Yayin da shi kuma halal -a musulunci- shine abinda Allah da manzonsa (s a w) suka halatta, shi kuma haram : shine  abinda Allah da manzonsa suka haramta.
Hakika! Dalilai da suke hana ma'aikata karbar komai na dukiya sun zo daga sunnar Manzon Allah (s a w) koda kuwa an kira shi da suna: kyauta ne! Daga cikinsu; akwai hadisin Abu Humaid assa'adiy (r.a) lallai shi yace:
"استعمل رسول الله r رجلا من الأسد, يقال له: ابن اللتبية على الصدقة فلمّا قدِم قال: هذا لكم, وهذا لي؛ أهدي لي, قال: فقام رسول الله r على المنبر, فحمد الله وأثنى عليه, وقال: ما بال عامل؟! أبعثه فيقول: هذا لكم, وهذا أهدي لي؟! أفلا قعد في بيت أبيه أو في بيت أمه حتى ينظر أيهدى إليه أم لا ؟! والذي نفس محمد بيده! لا ينال أحد منكم منها شيئا إلا جاء به يوم القيامية يحمله على عنقه, بعير له رغاع, أو بقرة لها خوار, أو شاة تيعر, ثم رفع يديه حتى رأينا عفرتَى إبطيه, ثم قال: اللهم هل بلغت مرتين".
Ma'ana: "Manzon Allah (s a w)  ya aikatar da wani mutum daga (kabilar) asa-d kan zakka ana ce da shi ibn Lutbiyya, yayin da wannan mutum ya dawo sai yace: wannan naku ne, wannan kuma nawa ne an bani kyauta, sai yace: sai Manzon Allah ya tsaya akan minbari, ya gode wa Allah kuma ya yaba masa, sannan yace: me ya samu ma'aikaci da zan tura shi, amma sai yace: wannan naku ne wannan kuma an bani shi kyauta?! Me yasa ba zai zauna a gidan ubansa ko a gidan uwarsa don yaga za a masa kyautan ne ko kuma a'a?! Na rantse da wanda ran Muhammadu ke hannunsa ! Dayanku ba zai samu komi daga cikin kyautar ba face ya zo da shi a ranar tashin kiyama yana dauke da shi a wuyansa; Rakumi ne yana ta fitar da sauti (رغاع), ko kuma saniya ce tana kuka (خوار), ko akuya ce tana ta fitar da sauti (me, me, يعر). Sannan sai ya daga hannayensa don yin addu'a har sai da muka ga hasken hamatarsa, sannan yace: Ya Allah shin na isar? Ya maimaita wannan addu'ar har sau biyu. Bukhariy [lamba: 7174] da Muslim [lamba: 1832] suka ruwaito shi, wannan kuma lafazin Muslim ne.
Ya zo a cikin littafin sahihul Bukhari [lamba: 3073] da Muslim [lamba: 1831] –lafazin na Muslim ne,- daga Abu-hurairah (r.a) lallai yace:
"قام فينا رسول الله r ذات يوم, فذكر الغلول فعظّمه وعظم أمره, ثم قال: لا ألفين أحدكم يجيء يوم القيامة على رقبه بعير له رغاء يقول يا رسول الله! أغثني فأقول: لا أملك لك شيئا؛ قد أبلغتك.
لا ألفين أحدكم يجيء يوم القيامة على رقبته فرس له حمحمة, فيقول: يا رسول الله! أغثني فأقول: لا أملك لك شيئا, قد أبلغتك.
لا ألفين أحدكم يجيء يوم القيام على رقبته شاة لها ثغاء, يقول: يا رسول الله! أغثني فأقول: لا أملك لك شيئا, قد أبلغتك.
لا ألفين أحدكم يجيء يوم القيام على رقبته نفس لها صياح, فيقول يا رسول الله! أغثني, فأقول: لا أملك لك شيئا.
لا ألفين أحدكم يجيء يوم القيام على رقبته رقاع تخفق, فيقول: يا رسول الله! أغثني, فأقول: لا أملك لك شيئا, قد أبلغتك.
لا ألفين أحدكم يجيء يوم القيام على رقبته صامت, فيقول: يا رسول الله! أغثني, فأقول: لا أملك لك شيئا؛ قد أبلغتك".
 Ma'ana: "Manzon Allah ya tashi –wata rana– a cikin mu; ya ambaci daukar wani abu cikin ganima kafin a rabata (wato: gululi) sai ya nuna hatsarinsa sannan ya girmama lamarinsa, Sai kuma yace: Ba zan samu dayanku da zai zo ranar tashin kiyama yana dauke da rakumin da ke kuka a wuyansa, sai yace: ya Manzon Allah ka taimake ni, face nace da shi: babu abinda zan iya yi maka (bazan mallaka maka komai ba), kuma hakika na isar maka.
Kuma ba zan samu dayanku da zai zo ranan tashin kiyama yana dauke a wuyansa da dokin da ke yin haniniya, sai yace: ya Manzon Allah ka taimake ni face nace: bana iya mallaka maka komai; saboda na isar maka.
Ba zan samu dayanku da zai zo ranar tashin kiyama yana dauke a wuyansa da akuyar da take kuka ME, ME sai yace: ya Manzon Allah ka taimake ni! Face nace: ba zan mallaka maka komai ba; saboda na isar maka.
Ba zan samu dayanku ba da zai zo ranar tashin kiyama yana dauke a wuyansa da wata rai (mutum) da take ta IHU, sai yace: ya Manzon Allah ka taimake ni; face nace: bana iya mallaka maka komai; don hakika na riga na isar maka.
Ba zan samu dayanku da zai zo ranar tashin kiyama yana dauke a wuyansa da tufar da take kadawa, sai yace: ya Manzon Allah ka taimake ni, sai nace: ba zan iya mallaka maka komai ba; don na riga na isar maka.
Ba zan samu dayanku ba da zai zo ranar tashin kiyama na dauke a wuyansa da zinariya ko azurfa ba; sai yace: ya Manzon Allah ka taimake ni, face nace: ba wani abun da zan iya mallaka maka; saboda na riga na isar maka".
الرِّقاعُ
Da ya zo cikin hadisin shine: tufa, shi kuma:
الصامتُ
zinariya da azurfa.

Daga cikinsu akwai hadisin Abu-humaid assa'adiy (r.a), lallai Manzon Allah (s a w) yace:
"هدايا العمال غُلولٌ".
Ma'ana: "kyautukan da ake baiwa ma'aikata gululi ne". Ahmad ne [lamba: 23601] da waninsa suka ruwaito shi. [Ka duba takhrijin hadisin cikin irwa'ul galili na Albaniy (2622)].
Wannan hadisin ma'anarsu daya da hadisin Abu-humaid assa'idiy (r.a) da ya gabata cikin kissar Ibnul lutbiyya da ta gabata.
Daga cikinsu akwai : hadisin Adiyyu bn umairah (r.a) lallai yace: na ji Manzon Allah (s a w) yana cewa:
"من استعملناه منكم على عمل فكتمَنا مخيطًا فما فوقه, كان غُلولاً يأتي به يوم القيامة".
Ma'ana: "Duk wanda muka bashi wani aiki daga cikinku sai ya boye mana koda gwargwadon allura ko abinda ke sama da shi to wannan gululi ne da zai zo dashi a ranar tashin kiyama", Abu-dawud [lamba: 2943] ne ya ruwaito shi da isnadi ingantacce, kuma Albaniy ya inganta shi.
Kuma ya zo a cikin "tarjamar" iyadhu bn Ganam (r.a) a cikin littafin sifatus safwati na ibnul-Jauziy (1/277) wanda kuma shi gomna ne da Umar ya nada a garin Hims, lallai shi yace: wa wassu daga cikin danginsa- a cikin wata kissa mai tsayi:
"فو الله! لأنْ أُشَقَّ بالمنشار أحبُّ إليَّ مِن أنْ أخون فِلسًا، أو أتعدى".
Ma'ana: "Na rantse da Allah! A tsaga ni da zarto kasha biyu shine yafi soyuwa a gare ni akan nayi ha'incin kwandala, ko na ketare iyakar aiki da dokokinsa (na yi ta'addanci).
Ibnul kayyim ya fada a cikin littafin "I'ilaamul muwakki'ina" (3/154) cikin dalilan (shari'a da suka haramta dukkan abinda zai kai zuwa ga buduwar anyar barna, wadanda ake musu lakabi da:   
(سدُّ الذرائع)
 (wato: toshe kofofin barna):
((الوجه الخامس والعشرون: أنّ الواليَ والقاضيَ والشافعَ ممنوعٌ مِن قبول الهدية، وهو أصل فساد العالم، وإسناد الأمر إلى غير أهله، وتولية الخونة والضعفاء والعاجزين([1])، وقد دخل بذلك من الفساد ما لا يحصيه إلا الله، وما ذاك إلا لأن قبول الهدية ممن لم تجر عادته بمهاداته ذريعة إلى قضاء حاجته، "وحبُّك الشيءَ يُعمِي و يُصِم"، فيقوم عنده شهوةٌ لقضاء حاجته مكافأة له، مقرونة بِشَرَهٍ، وإغماض عن كونه لا يصلح)).
Ma'ana: "Fiska na ashirin da biyar: lallai gomna (shugaba) da alkali da wanda zai yi shafa'a (ceto) an hana shi karbar wata kyauta, wannan kuma shine tushen lalacewar duniya da kuma jingina al'amari zuwa ga wanda bai cancance shi ba, tare da shugabantar da maha'inta da masu rauni da gajiyayyu. Kuma hakika barnan da ba wanda ya san adadinta sai Allah shi kadai ta shiga wa mutane ta wannan kofar (shugabanni da alkalai su karbi kyauta) dalili kuwa: lallai karbar kyautan mutumin da a al'adance baya baka kyauta; hanya ce da ya bude don neman shima a rika biya masa bukatarsa (Larabawa kuma suna cewa): (Sonka ga abu na makantar da kai ya kuma kurmantar). Daga nan sai sha'awar shima ya biya masa bukatunsa ya tsayu a cikin zuciyarsa, neman ya ga ya saka masa, da kuma kokarin saka shi cikin daula, tare da rintse idanu kan kasancewar la'alla wannan mutum bai cancanci hakan ba".

INA ROKON ALLAH MAI GIRMA DA DAUKAKA YA DATAR DA KOWANE MA'AIKACI DAGA CIKIN MUSULMAI KAN GABATAR DA AIKINSA TA FISKAR DA ZATA YARDAR DA ALLAH MAI YAWAN ALBARKA MADAUKAKI. SANNAN LADA DA KYAKKYAWAN KARSHE A DUNIYA DA LAHIRA YA DAWO MASA.
KUMA YABON ALLAH DA SALATINSA DA ALBARKARSA SU KARA TABBATA AKAN BAWANSA KUMA MANZONSA ANNABINMU MUHAMMADU, DA IYALANSA DA SAHABBANSA.



([1]) Haka lafazin ya zo a cikin littafin, Amma la'alla daidan shine:
((وأصل فساد العالم: إسناد الأمر إلى غير أهله، وتولية الخونة والضعفاء والعاجزين)).
Ma'ana: "Tushen lalacewar duniya ya fara ne daga: Jingana shugabanci ga wadanda basu cancance shi ba, da dora maha'inta shugabanci da mulki, ko kuma masu rauni, da gajiyayyu da ba za su iya yinsa ba".
Dalili kuwa akan wannan shine hadisin Abu-hurairah (r.a) daya gabata a kusa-kusa wanda a cikinsa Annabi (s a w) ya amsa wa mutumin da ya tambaye shi yaushe za a yi tashin kiyama? da fadinsa: Idan aka tozarta amana (shugabanci) to ka jira tashin kiyama, Sai yace: Yaya nene tozarta ya ke? Sai yace: Shine idan aka jingina al'amari na shugabanci zuwa ga wanda bai cancance shi ba; to ka jira kiyama".   

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...