A IRIN WANNAN WATA NA SHA'ABAN !
(في مثل هذا الشهر -شعبان-)
Watan Sha'abana, shine wata na takwas
daga cikin watannin shekarar hijira. Kuma a cikinsa ababe dayawa na tarihi na-musamman,
suka auku,
A SHEKARA TA 2 BAYAN HIJIRA Allah ya farlanta
azumin watan Ramadana akan musulmai, sai hakan ya mayar da azumi ya zama daya
daga cikin rukunan guda biyar wadanda aka gina musulunci akansu.
A CIKIN SHA'ABAN NA SHEKARA TA 3
BAYAN HIJIRA Aka haifi Alhasan bn Aliyu –Allah ya kara yarda akansu-; wato
jikan Manzon Allah –sallal lahu alaihi wa sallama-, kuma daya daga jagorori
biyu na samarin Aljannah.
A RANAR BIYAR GA WATAN SHA'ABAN, A SHEKARAR
HIJIRA TA BIYAR Aka haifi Alhusaini bn Aliyu –Allah ya kara yarda a gare su-; wato
jikan Manzon Allah –sallal lahu alaihi wa sallama-, kuma daya daga jagorori
biyu na samarin Aljannah.
KUMA A WATAN SHA'ABAN NA SHEKARA TA
BIYAR KO KUMA SHIDA BAYAN HIJIRA Labarin azamar wasu mushirkai kan yakar Manzon
Allah –sallal lahu alaihi wa sallama- ya iske shi, wanda hakan yazama sababin
yakin da ke kira da YAKIN BANIL MUSDALIK kuma a wannan yakin Musulmai suka ci
nasara akan mushirkai.
KUMA A WATAN SHA'ABAN NA SHEKARA TA
CASA'IN DA HUDU (94), AKA HAIFI IMAM LAISU BN SA'AD BN ABDURRAHMAN ALFAHMIY
ALMISRIY, wato babban malamin hadisi, masanin ilimin fikihu mahardaci.
KUMA A 25 NA WATAN SHA'ABAN TA
SHEKARA TA 625 daga hijira, aka haifi babban malamin fikihu na mazhabar
ImamAs-Shafi'iy, Wato, Takiyyudden Muhammadu bn Aliyu bn WAhab, wanda aka
sanshi da lakabin Ibnu-dakik Al-id, ma'abucin wallafe-wallafe sanannu, da kuma
tarihi abin yabo.
A KUMA RANAR 12 GA WATAN SHA'ABAN NA
SHEKARA TA 672 ta hijira, ya rasu a garin Damaskas, Malamin da yayi zurfi cikin
ilimin harshen larabci, da sanin fiskoki mabanbanta da ake karanta Kur'ani da
su; wato ilimin kiraa-at, wanda shine Imam Ibnu-Malik, ma'abucin shahararrun wallafe-wallafe,
daga cikinsu Alfiyyar Ibnu-Malik.
Watan Sha'aban wata ne da
aka haifi jigajigan Maluma da manyan mutane.
No comments:
Post a Comment