2018/05/20

YAYA 'DANKA ZAI HADDACE KUR'ANI (كيف تُحفِّظْ طفلك القرآن؟)








YAYA 'DANKA ZAI HADDACE KUR'ANI
(كيف تُحفِّظْ طفلك القرآن؟)









Tarjamar
Abubakar Hamza


Alkur'ani maganar Allah ne, kuma shine mafi alherin guzurin da Uba zai gabatar da shi ga 'Dansa, saboda kasancewarsa, hanyar SHIRIYA, da DAIDAITUWA AKAN ADDINI,
Allah Ta'alah yana cewa:
((إنّ هذا القرآن يهدي للتي هي أقومُ ويبشّر المؤمنين الذين يعملون الصالحات أنّ لهم أجرًا كبيرًا)) [الإسراء: 9].
Ma'na: "Lallai ne wannan Kur'ani yana shiryatarwa zuwa ga hanyar da tafi daidaita, kuma yana albishir ga muminai wadanda suke aikata kyawawan ayyuka, lallai suna da lada mai girma"

AKwai TUNANI DA HANYOYI wanda suke taimakon Mai tarbiyya, wajen kara kulla alakar kananan Yara da littafin Allah Ta'alah,

DAGA CIKINSU akwai: Yawaita karanta Alkur'ani a gaban idon yara, saboda bada abin koyi (kud-wa), yana daga cikin manyan hanyoyi kuma masu karfi, wajen gyaran halaye.

KARFAFA GUIWA: Ta hanyar karanto tare da sharhin ayoyi da hadisan da suke bayanin falalar karatun Alkur'ani da haddace shi.

YIN RIJISTA GA YARA A TSANGAYOYI KO MASALLATAI DA MAKARANTUN HADDAR KUR'ANI MAI GIRMA: domin wadannan makarantun suna sanya dalibi ya rika kokarin tsere tare da abokan karatunsa, kuma suna taimakonsa wajen inganta karatu da tajweed, kuma suna kara kulla alakarsa da Masallaci, da kuma zama da mutane nagari.

BAIWA YARO KISSOSHIN DA SUKA ZO A CIKIN ALKUR'ANI, ta hanya mai sauki, da jan-rai, saboda hikaya da kissa abun so ne ga Yara, kuma yana bada gudumawa wajen ratayuwar zukatunsu da Kur'ani, kamar yadda hakan ke kara bunkasa wa mutum yawan kalmomin harshe larabci da suka zo a cikin Alkur'ani.

KA BAIWA 'DANKA KYAUTAR ALKUR'ANI, saboda son mallakar abu, dabi'a ce, da za a iya amfana da ita ta fiska mai kyau, wanda hakan zai sanya Yaro ya rika son Kur'aninsa  da ya kebanta da mallakarsa, sai ya rika karanta shi, yana jujjuya shi yana bubbude shi duk lokacin da ya so.

KARFAFA GUIWAR YARO TA HANYAR BASHI KYAUTUKA, DA KUMA KARFAFA SHI KAN SHIGA MUSABAKA, domin yaro zai iya gaza yin hadda shi-kadansa, sai dai iya zama abokin gogayya mai karfi, kuma mai kyakkyawar hadda, idan lamarin ya kasance a cikin jama'a, musamman kuma idan aka tanadi wasu kyautuka.

AMFANI DA HANYOYIN ZAMANI YAYIN HADDA: saboda suna kosar da bukatun Yara na yin amfani da wadannan hanyoyi na ci-gaban zamani, wanda a mafi yawan lokaci ake aiki da su, ta wasu hanyoyin na-daban. Kuma abu ne mai kyau, ya zama suna da na'urorin rakodin din karatu, da sauraronsa, da hanyoyin sanin kura-kuran da suke cikin karatun mutum; Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce:

((مَن قرأ القرآن وتعلمه وعمِل وعمِل به: أُلبِسَ والداه يوم القيامة تاجًا مِن نورٍ، ضوؤه مثل ضوء الشمس، ويُكسى والداه حُلَّتان، لا تقوم لهما الدنيا، فيقولان: بِمَ كسينا هذا؟ فيُقال: بأخذ ولدكما القرآن)). رواه الحاكم، وحسَّنه الألباني في صحيح الترغيب والترهيب [1434].
Ma'ana: "Wanda ya karanta Alkur'ani, ya koye shi, ya yi aiki da shi: to lallai za a sanya wa iyayensa wani kambi na haske a ranar tashin Kiyama, Haskensa kamar hasken rana, kuma za a sanya wa iyayensa biyu tufafin alkebba biyu, wadanda Duniya gaba dayanta bata kai su kima ba. Sai su ce: Ta yaya aka tufatar da mu, wannan? sai ace musu: Saboda 'danku ya haddace Alkur'ani". Hakim ya fitar da shi, kuma Albani yace hadisi ne hasan, a cikin Sahih da da'if na Attargibi wat tarhibi [1434].

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...