ABABEN DA SUKA DACE A RIKA AIKATAWA
A WANNAN WATA MAI GIRMA
·
Samar da yanayi da shirya kai; domin yin ibadodi, da gaggawan tuba da
mayar da lamura ga Allah, da yin farin-cikin shigan watan azumi, da kyautata
ibadar azumi, da samun kushu'i da kan-kan-da-kai cikin sallolin tarawihi, da
nisantar raunin aiwatar da ibadodi a goman tsakiyan watan, da kirdadon dacewa
da daren Lailatul kadr, da yin sadaka, da i'itikafi,.
·
Babu laifi akan kalaman taya juna murnar shigowan watan azumi, saboda
Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya kasance yana yin bushara ga
SahabbanSa, kan zuwan watan azumi, ya kuma rika kwadaitar da su kan bada kulawa
ga wannan watan.
DAGA CIKIN HUKUNCE-HUKUNCEN AZUMI
6. DAGA CIKIN NAU'UKAN AZUMI; AKWAI
WANDA JERANTA SU WAJIBI NE; kamar azumin Ramadana, da yin azumin kaffarar kisan
kuskure, da azumin kaffarar zihari, da azumin kaffarar jima'i a cikin yinin azumi,
da wassunsu.
DAGA CIKIN AZUMI KUWA;
Akwai wadanda jerantawar ba wajibi ba
ne, kamar ramukon azumin Ramadana, da azumin kwanaki goma ga Mahajjacin da bai
samu damar yin hadaya ba, da makamantan wannan.
7. Azumin nafifili, suna tottoshe nakasar da ake samu
a cikin azumin farilla.
8. hani ya zo, kan kebance yinin Juma'a da azumi, da azumtar
yinin Asabat, idan ba na farilla ba, da azumtar kwanakin shekara (azumin
kullum-kullum), da hani kan wucel cikin azumi, kuma haramun ne yin azumin ranakun
idi guda biyu, da kwanakin bayan idin layya uku (na busar da naman layyah).
No comments:
Post a Comment