HADISAI ARBA'IN KAN
SALLAH
أربعون حديثا تتعلق بالصلاة
TATTARAWAR
DA TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم
الله الرحمن الرحيم
والصلاة
والسلام على أشرف المرسلين، وعلى آله وصحبه أجمعين، أما بعد:
ورد عن عُمَرَ بْن الْخَطَّابِ رضي الله تعالى عنه قال: سَمِعْتُ رَسُولَ
اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، يَقُولُ: «إِنَّمَا الأَعْمَالُ بِالنِّيَّاتِ، وَإِنَّمَا لكل امْرِئٍ
مَا نَوَى، فَمَنْ كَانَتْ هِجْرَتُهُ إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ فَهِجْرَتُهُ
إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ، وَمَنْ كَانَتْ هِجْرَتُه لدُنْيَا يُصِيبُهَا، أَوِ
امْرَأَةٍ يَنْكِحُهَا فَهِجْرَتُهُ إِلَى مَا هَاجَرَ إِلَيْهِ». رواه
البخاريّ، ومسلم([1]).
An karvo
daga Umar xan Alkhaxxabi (r.a) yace: Na ji Manzon Allah (s.a.w) yana cewa:
"Dukkan aiyuka su kan inganta tare da niyya, kuma lallai kowane mutum
yana samun sakamakon abinda yayi niyya; Wanda hijirarsa ta kasance saboda Allah
ne da ManzonSa to sakamakon hijirarsa tana ga Allah da Manzonsa. Wanda kuma
hijirarsa ta kasance saboda wata duniya ce da zai same ta, ko saboda wata matar
da zai aure ta, to sakamakon hijirarsa yana ga abin da yayi hijira dominsa. Bukhariy
[lamba: 1], da Muslim [lamba: 1907] suka ruwaito shi.
الأول:
بيان أنّ إقام الصلاة من الخمس التي بني عليها الإسلام
عَنِ عبد الله بْن عمر رضي الله عنهما، قَالَ: سمعتُ رَسُول اللَّهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يقول: «بُنِيَ
الْإِسْلَامُ عَلَى خَمْسٍ، شَهَادَةِ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَأَنَّ
مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ، وَإِقَامِ الصَّلَاةِ، وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ،
وَصَوْمِ شَهْرِ رَمَضَانَ، وَحَجَّ الْبَيْتِ». رواه البخاري ومسلم.
NA XAYA: TSAYAR DA SALLA NA CIKIN GINSHIQAI
BIYAR DA AKA GINA MUSULUNCI AKANSU
An ruwaito daga Abdullahi xan Umar (r.a) yace:
Naji Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "An gina musulunci akan abubuwa
guda biyar; Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Muhammadu
manzon Allah, da tsayar da salla, da bada zakka, da yin hajjin wannan xakin, da
azumin watan ramadana".
Bukhariyy [8] da Muslim [16] suka ruwaito shi.
الثاني: بيان أنّ الصلاة عمود الإسلام، وأن إقامتها من أسباب
دخول الجنة
عَنْ مُعَاذِ بْنِ جَبَلٍ رضي الله عنه قال: قلت يا رسول الله أَخْبِرْنِي
بِعَمَلٍ يُدْخِلُنِي الْجَنَّةَ، وَيُبَاعِدُنِي مِنَ النَّارِ؟ قَالَ: "لَقَدْ سَأَلْتَ عَنْ عَظِيمٍ، وَإِنَّهُ لَيَسِيرٌ
عَلَى مَنْ يَسَّرَهُ اللهُ عَلَيْهِ، تَعْبُدُ اللهَ وَلَا تُشْرِكُ بِهِ
شَيْئًا، وَتُقِيمُ الصَّلَاةَ، وَتُؤْتِي الزَّكَاةَ، وَتَصُومُ رَمَضَانَ،
وَتَحُجُّ الْبَيْتَ"
ثُمَّ قَالَ: "أَلَا
أَدُلُّكَ عَلَى أَبْوَابِ الْخَيْرِ؟ الصَّوْمُ جُنَّةٌ، وَالصَّدَقَةُ تُطْفِئُ
الْخَطِيئَةَ كما يطفئ الماء النار، وَصَلَاةُ الرَّجُلِ فِي جَوْفِ اللَّيْلِ
" ثُمَّ تلا: {تَتَجَافَى جُنُوبُهُمْ عَنِ الْمَضَاجِعِ} حَتَّى بَلَغَ، {يَعْمَلُونَ} [السجدة:
17] ثُمَّ قَالَ: "أَلَا
أُخْبِرُكَ بِرَأْسِ الْأَمْرِ وَعَمُودِهِ وَذُرْوَةِ سَنَامِهِ؟"
فَقُلْتُ: بَلَى يَا رَسُولَ اللهِ. قَالَ: "رَأْسُ
الْأَمْرِ الْإِسْلَامُ وَعَمُودُهُ الصَّلَاةُ، وَذِرْوَةُ سَنَامِهِ الْجِهَادُ" ... الحديث رواه الترمذي وقال: حديث حسن صحيح.
NA BIYU: SALLA ITACE FILAR DA TA
DOGARE MUSULUNCI, KUMA TSAYAR DA ITA SABABI NE NA SHIGA ALJANNA
An
ruwaito daga Mu’azu xan Jabal (R.A) yace: Nace ya Manzon Allah bani labarin
wani aiki da zai shigar da ni aljanna, kuma ya nisantar da ni daga shiga wuta,
sai ya ce: Haqiqa ka yi tambaya game da abu mai girma, saidai abu ne mai sauqi
ga wanda Allah ya sauqaqe shi a gare shi; ka bauta wa Allah ba tare da ka haxa
shi da wani ba, kuma ka tsayar da Sallah, kuma ka bada zakka, kuma ka azumci
Ramadan, sannan ka ziyarci xakin Allah.
Sannan
sai yace: Shin ba zan shiryar da kai qofofin alheri ba? Azumi garkuwa ne,
sadaka kuma tana shafe kurakurai kamar yadda ruwa ke kashe wuta. haka sallar
mutum a cikin yankin dare. Sannan ya karanta faxin Allah: (Gefen jikinsu yana
nisantar gurin kwanciyar su…) har ya kai inda Allah yake cewa: ‘ya ‘amaluun.
Sannan sai yace: Ba zan ba ka labari dangane
da, kan wannan al’amarin ba, da ginshiqansa, da qololuwar tozonsa? Sai nace:
Eh. Sai yace: Kan wannan lamarin shine: Musulunci. Ginshiqinsa kuwa sallah.
Qololuwar tozonsa kuma shine: Jihadi”. … . Tirmiziy ya
ruwaito shi [ 2616] kuma yace: Hadisi ne
mai kyau ingantacce.
الثالث: في الدعوة إلى الشهادتين
وشرائع الإسلام
عَن
عبد الله بن عباس أَنَّ مُعَاذًا قَالَ: بَعَثَنِي رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: «إِنَّكَ
تَأْتِي قَوْمًا مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ، فَادْعُهُمْ إِلَى شَهَادَةِ أَنَّ لَا
إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَأَنِّي رَسُولُ اللهِ، فَإِنْ هُمْ أَطَاعُوا لِذَلِكَ،
فَأَعْلِمْهُمْ أَنَّ اللهَ افْتَرَضَ عَلَيْهِمْ خَمْسَ صَلَوَاتٍ فِي كُلِّ
يَوْمٍ وَلَيْلَةٍ، فَإِنْ هُمْ أَطَاعُوا لِذَلِكَ، فَأَعْلِمْهُمْ أَنَّ اللهَ
افْتَرَضَ عَلَيْهِمْ صَدَقَةً تُؤْخَذُ مِنْ أَغْنِيَائِهِمْ فَتُرَدُّ فِي
فُقَرَائِهِمْ ...»، متفق عليه.
NA UKU : KIRAN MUTANE ZUWA GA
SALLA BAYAN TAUHIDI…
An ruwaito
daga Abdullahi xan Abbas (r.a) Lallai Mu’azu xan Jabal (R.A) yace: Manzon Allah
ya tura ni Yaman, Sai yace: "Lallai kai z aka je wajen wasu mutane
na Ahlul-kitabi, Sai ka kira su zuwa ga kalmar La ilaha illal lahu, Muhammadur
rasulul lahi, Idan har suka yi maka biyayya akan haka, Sai ka ilmantar da su
cewa lallai Allah ya farlanta salloli guda biyar akansu cikin kowani yini da
dare, Idan suka yi biyayya akan haka, to ka ilmantar da su cewa lallai Allah ya
farlanta zakka akansu; wanda ake xaukanta daga mawadatansu, a mayar da ita zuwa
ga faqiransu", … Bukhariy [1496 da 4347] da Muslim
[19] suka ruwaito shi..
الرابع:
فرض خمس صلوات في كل يوم وليلة
عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله
عنه، قَالَ: بَيْنَمَا نَحْنُ جُلُوسٌ مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
فِي المَسْجِدِ، دَخَلَ رَجُلٌ عَلَى جَمَلٍ فَقَالَ لِلنَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ: إِنِّي سَائِلُكَ فَمُشَدِّدٌ عَلَيْكَ فِي المَسْأَلَةِ، فَلاَ تَجِدْ
عَلَيَّ فِي نَفْسِكَ؟ فَقَالَ: «سَلْ عَمَّا بَدَا لَكَ» فَقَالَ: أَسْأَلُكَ بِرَبِّكَ وَرَبِّ مَنْ قَبْلَكَ، آللَّهُ أَرْسَلَكَ
إِلَى النَّاسِ كُلِّهِمْ؟ فَقَالَ: «اللَّهُمَّ نَعَمْ». قَالَ: أَنْشُدُكَ بِاللَّهِ، آللَّهُ أَمَرَكَ أَنْ نُصَلِّيَ الصَّلَوَاتِ
الخَمْسَ فِي اليَوْمِ وَاللَّيْلَةِ؟ قَالَ: «اللَّهُمَّ نَعَمْ». ... وفي آخر القصة قَالَ الرَّجُلُ: آمَنْتُ
بِمَا جِئْتَ بِهِ، وَأَنَا رَسُولُ مَنْ وَرَائِي مِنْ قَوْمِي، وَأَنَا ضِمَامُ بْنُ
ثَعْلَبَةَ. متفق عليه.
NA HUXU : ALLAH YA FARLANTA
SALLOLI BIYAR NE CIKIN DARE DA YINI
An ruwaito daga Anas xan Malik (r.a) ya ce:
Wata rana muna zaune tare da Annabi (s.a.w) a cikin masallaci, sai wani mutum
akan raqumi ya shigo, sannan yace wa Annabi (s.a.w): Lallai ni zan yi tambayoyi
a gare ka, kuma zan tsananta maka tambaya, kada ka ji haushina a cikin ranka?
Sai yace: Ka tambayi duk abinda ka so. Sai yace: Ina tambayarka kuma
ina haxa ka da Ubangijinka da Ubangijin waxanda suke gabaninka, Shin Allah ne
ya turo ka zuwa ga mutane gabaxaya? Sai yace: Allahumma, Na'am. Sai
yace: Ina haxa ka da Allah, Shin Allah ne ya umurce mu da mu yi salloli guda
biyar a cikin yini da dare? Yace: Allahumma Na'am. … har qarshen qissar, inda Mutumin yake cewa:
Nayi Imani da abinda ka zo da shi. Kuma zan isar da shi ga mutanena da suke
bayana. Kuma nine Dimam xan Sa'alabah". Bukhariy [63] da Muslim [12] suka
ruwaito shi.
الخامس والسادس: محو
الخطايا وتكفير السيئات من فضل الصلوات الخمس
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه، قال، سمعت رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: "أَرَأَيْتُمْ
لَوْ أَنَّ نَهْرًا بِبَابِ أَحَدِكُمْ يَغْتَسِلُ مِنْهُ كُلَّ يَوْمٍ خَمْسَ مَرَّاتٍ؛
هَلْ يَبْقَى مِنْ دَرَنِهِ شَىْءٌ؟ قَالُوا: لاَ يَبْقَى مِنْ دَرَنِهِ شَىْءٌ.
قَالَ: فَذَلِكَ مَثَلُ الصَّلَوَاتِ الْخَمْسِ يَمْحُو اللَّهُ بِهِنَّ الْخَطَايَا" ([2]).
NA BIYAR DA NA SHIDA: KANKARE KURA-KURAI NA
DAGA CIKIN FALALAR SALLOLI BIYAR
An ruwaito daga Abu-Hurairah (r.a) ya ce:
Na ji Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: (Ku bani labari; Da wani kogi zai
kasance a qofar xayanku; yana yin wanka a cikinsa a kullum sau biyar; shin wani
abu na dauxa zai saura tare da shi? Sai su ka ce: Babu wani abu na dauxarsa da
zai saura! Sai ya ce: To haka misalin salloli biyar su ke –ga bawa-; Allah na
share masa laifukansa da su). Bukhariy [lamba: 528], da Muslim [lamba: 667]
suka ruwaito shi.
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: "الصَّلَـوَاتُ
الْخَمْسُ، وَالْـجُـمُعَةُ إِلَى الْجُـمُـعَةِ، ورمضـان إلى رمضـان: مكفِّرات لِمَا
بَيْنَهُمَا مَا اجْـتـنبَت الْكَبَائِر"([3]).
An ruwaito daga Abu-hurairah (r.a) daga Annabi
(s.a.w) ya ce: (Salloli guda biyar, da kuma juma'a zuwa wata juma'ar, da azumin
ramadana zuwa wani ramadan: masu kankare qananan zunuban da su ka kasance a
tsakaninsu ne; matuqar an nisanci manyan-manyan laifuka",
Muslim ya ruwaito shi (233).
السابع: كيف فرضت الصلوات في يوم المعراج وبيان أنها خمس في الفعل
عن ابن حَزْمٍ وَأَنَس رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قالا، قَالَ رسول الله
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّم: ففَرَضَ اللَّهُ عَلَيَّ خَمْسِينَ صَلاَةً،
فَرَجَعْتُ بِذَلِكَ حَتَّى أَمُرَّ بِمُوسَى، فَقَالَ مُوسَى: مَا الَّذِي فَرَضَ
عَلَى أُمَّتِكَ؟ قُلْتُ: فَرَضَ عَلَيْهِمْ خَمْسِينَ صَلاَةً، قَالَ: فَرَاجِعْ
رَبَّكَ، فَإِنَّ أُمَّتَكَ لاَ تُطِيقُ ذَلِكَ، فَرَجَعْتُ فَرَاجَعْتُ رَبِّي فَوَضَعَ
شَطْرَهَا، فَرَجَعْتُ إِلَى مُوسَى، فَقَالَ رَاجِعْ رَبَّكَ: فَذَكَرَ مِثْلَهُ،
فَوَضَعَ شَطْرَهَا، فَرَجَعْتُ إِلَى مُوسَى فَأَخْبَرْتُهُ فَقَالَ: رَاجِعْ
رَبَّكَ، فَإِنَّ أُمَّتَكَ لاَ تُطِيقُ ذَلِكَ، فَرَجَعْتُ فَرَاجَعْتُ رَبِّي،
فَقَالَ: هِيَ خَمْسٌ وَهِيَ خَمْسُونَ، لاَ يُبَدَّلُ القَوْلُ لَدَيَّ،
فَرَجَعْتُ إِلَى مُوسَى، فَقَالَ رَاجِعْ رَبَّكَ، فَقُلْتُ: قَدِ اسْتَحْيَيْتُ
مِنْ رَبِّي([4]).
NA BAKWAI: YADDA AKA FARLANTA
SALLOLI BIYAR A DAREN MI'IRAJI
An ruwaito daga Anas (r.a), ya ce: Manzon
Allah (s.a.w) yana cewa: "… Sai Allah ya farlanta min salloli
hamsin, Sai na tafo da sallolin har sai da na zo shige saman da annabi Musa
yake, Sai yace: Me aka farlanta wa al'ummarka? Na ce: Ya farlanta musu salloli
guda hamsin. Ya ce: Sai ka koma zuwa ga Ubangijinka, domin al'ummarka ba za ta
iya aikata haka ba, Sai na koma wa Ubangijina sai ya xauke rabin sallolin, Sai
na koma zuwa ga annabi Musa, sai ya ce: Ka koma wa Ubangijinka, domin
al'ummarka ba za ta iya haka ba, Sai na
koma wa Ubangijina sai ya sake xauke rabin hakan, Sai na koma zuwa ga annabi
Musa na bashi labari, sai ya ce: Al'ummarka ba za ta iya haka ba, Sai na koma wa Ubangijina sai ya ce: Su guda
biyar ne, amma kuma hamsin ne –ta fiskar lada-, Ba a canza magana a wurina. Sai
na koma zuwa ga annabi Musa, sai ya ce: Ka koma wa Ubangijinka, Sai na ce:
Lallai na ji kunyar Ubangijina", Bukhariy
ya ruwaito shi (349) da Muslim (163) ([5]).
الثامن: الفرض خمس صلوات والتطوع مطلوب
2678 - عَنْ
طَلْحَة بْن عُبَيْدِ اللَّهِ رضي الله عنه، قال: جَاءَ رَجُلٌ إِلَى رَسُولِ
اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَإِذَا هُوَ يَسْأَلُهُ عَنِ
الإِسْلاَمِ، فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «خَمْسُ صَلَوَاتٍ فِي اليَوْمِ
وَاللَّيْلَةِ»، فَقَالَ: هَلْ عَلَيَّ غَيْرُهَا؟ قَالَ: «لاَ، إِلَّا أَنْ
تَطَّوَّعَ» فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «وَصِيَامُ
شَهْرِ رَمَضَانَ»، قَالَ: هَلْ عَلَيَّ غَيْرُهُ؟ قَالَ: «لاَ، إِلَّا أَنْ
تَطَّوَّعَ»، قَالَ: وَذَكَرَ لَهُ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ الزَّكَاةَ، ... الحديث
متفق عليه([6]).
NA TAKWAS: SALLOLIN FARILLA
BIYAR NE, SAIDAI ANA SON YIN NAFILFILI
An ruwaito daga Xalhah xan
Ubaidullahi (r.a) yace: Wani Mutum ya zo zuwa ga Manzon Allah (s.a.w) sai ya
tambaye shi kan musulunci, Sai Manzon Allah (s.a.w) yace masa: "Salloli biyar ne
cikin yini da dare, Sai mai tambayar ya ce: Shin akwai wasu a kaina? Sai ya ce:
A'a;
saidai idan za ka yi sallar taxawwu'iy –ta nafila-. Sai Manon Allah
(s.a.w) ya sake cewa: Da azumtar watan ramadhana, Sai mai
tambayar ya ce: Shin akwai wasu aumin a kaina? Sai ya ce: A'a; saidai idan
za ka yi na taxawwu'iy –nafila- . Ya ce: Sai Manzon Allah
(s.a.w) ya ambata masa zakka…. Bukhariy (46, da 2678) da Muslim (11) suka
ruwaito shi .
التاسع: إنما تجب الصلاة على البالغ العاقل
عَنْ عَلِيٍّ رضي الله عنه، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ قَالَ: "رُفِعَ
الْقَلَمُ عَنْ ثَلاثَةٍ: عَنِ النَّائِمِ حَتَّى يَسْتَيْقِظَ، وَعَنِ
الْمَجْنُونِ حَتَّى يفيق، وعَنِ الصَّغِيرِ حَتَّى يَبْلُغَ"([7]).
NA TARA: SALLA TANA WAJABA NE
AKAN BALIGI MAI HANKALI
An ruwaito daga Aliyu (r.a), daga Annabi
(s.a.w) lallai shi ya ce: "An xauke alqalami akan mutane guda uku;
Ga mai barci har sai ya tashi, da kuma mahaukaci har sai ya wartsake, da
qaramin yaro har sai ya balaga).
العاشر متى يؤمر الأولاد بالصلاة ومتى يضربون
عليها؟
عَنْ عَمْرِو بْنِ
شُعَيْبٍ، عَنْ أَبِيهِ، عَنْ جَدِّهِ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "مُرُوا أَوْلادَكُمْ بِالصَّلاةِ
لسَبْعٍ، وَاضْرِبُوهُمْ عَلَيْهَا لعَشْرٍ، وَفَرِّقُوا بَيْنَهُمْ فِي الْمَضَاجِعِ"([8]).
NA GOMA: LOKACIN DA AKE UMURTAR
YARA DA YIN SALLA, DA LOKACIN DA ZA A DAKE SU AKANTA
An
ruwaito daga Amru xan Shu'aibu, daga Babansa, daga Kakansa (r.a), yace: Manzon
Allah (s.a.w) yace: "Ku umurci yaranku da yin sallah; alhalin suna 'yan
shekaru bakwai, kuma ku yi musu duka akan barinta matuqar sun kai shekaru goma.
Sannan ku rabe tsakaninsu a wuraren kwanciya).
الطهر من الحيض ودم النفساء من شروط
صحة الصلاة والصوم
عَنْ أَبِي سَعِيدٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ الخُدْرِيِّ، قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ: «أَلَيْسَ
إِذَا حَاضَتْ لَمْ تُصَلِّ وَلَمْ تَصُمْ؟ فَذَلِكَ نُقْصَانُ دِينِهَا»([9]).
TSARKAKA DAGA HAILA DA JININ
NIFASI SUNA CIKIN SHARUXAN INGANCIN SALLAH DA AZUMI
An ruwaito daga Abu-Sa'id Alkhudriy (r.a) ya
ce: Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Shin mace ba ta kasance, idan ta
yi haila ba ta sallah kuma ba ta azumi ba? To wannan na daga tawayar addininta!".
وعَنْ مُعَاذَةَ، قَالَتْ: سَأَلْتُ عَائِشَةَ فَقُلْتُ: مَا بَالُ
الْحَائِضِ تَقْضِي الصَّوْمَ،
وَلَا تَقْضِي الصَّلَاةَ. فَقَالَتْ: أَحَرُورِيَّةٌ أَنْتِ؟ قُلْتُ: لَسْتُ
بِحَرُورِيَّةٍ، وَلَكِنِّي أَسْأَلُ. قَالَتْ: «كَانَ يُصِيبُنَا ذَلِكَ، فَنُؤْمَرُ بِقَضَاءِ
الصَّوْمِ، وَلَا نُؤْمَرُ بِقَضَاءِ الصَّلَاةِ»([10]).
Kuma an ruwaito daga Mu'azatu, tace: Na
tambayi A'isha, Na ce: Me yasa Mace mai haila ta ke biyan azumi, amma bata yin
ramukon sallah? Sai ta ce: Ke daga matattarar khawarijawa; Harura'u, ki ke? Sai
nace: Ni ba daga garin Harura'u nake ba, saidai ina yin tambaya ne kawai, Sai
ta ce: "Hakan ya
kasance ya kan same mu; sai a umurce mu da yin ramukon azumi, amma ba a
umurtarmu da mu rama sallah".
الحادي عشر: منزلة الصلاة في الإسلام وكفر تاركها
عَنْ بُرَيْدَةَ رضي الله عنه، قَالَ: قَالَ رَسُولُ
اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «الْعَهْدُ الَّذِي بَيْنَنَا وَبَيْنَهُمُ الصَّلاَةُ،
فَمَنْ تَرَكَهَا فَقَدْ كَفَر»، رواه الترمذي وابن ماجه، وقال الترمذي: حسن صحيح([11]).
NA GOMA DA SHA XAYA: MATSAYIN
SALLA A MUSULUNCI DA HUKUNCIN WANDA YA QI YINTA
An ruwaito daga Buraidah (r.a) yace: Manzon
Allah (s.aw) yace: "Alkawarin da ke tsakaninmu da
tsakaninsu –munafikai- shi ne: Yin sallah; duk wanda ya bar yinta to ya kafirta),
Tirmiziy (2621) da Ibnu-Majah (1079) suka ruwaito shi, kuma Tirmiziy yace:
Hadisin mai kyau ne ingantacce.
وعَنْ جَابِرٍ رضي الله عنه، أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى
اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: بَيْنَ الكُفْرِ وَالإِيمَانِ تَرْكُ
الصَّلاَةِ.
وعنهُ رضي الله عنه، قَالَ: بَيْنَ العَبْدِ وَبَيْنَ الشِّرْكِ أَوِ
الكُفْرِ تَرْكُ الصَّلاَةِ. رواهما
الترمذي، وقال: هذا حديث حَسَنٌ صَحِيحٌ.
An ruwaito daga Jabir (r.a), daga Annabi
(s.a.w) yace: "Tsakanin Imani da kafirci shine barin salla".
Kuma an sake ruwaitowa daga Jabir, yace:
"Tsakanin bawa da shirka, ko kafirci shine barin salla".
Tirmiziy ya ruwaito su (2618, 2619), kuma
yace: Hadisi ne mai kyau ingantacce.
وبسند الترمذي إلى عَبْدِ اللهِ بْنِ شَقِيقٍ العُقَيْلِيِّ، قَالَ: كَانَ أَصْحَابُ مُحَمَّدٍ صَلَّى اللَّهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لاَ يَرَوْنَ شَيْئًا مِنَ الأَعْمَالِ تَرْكُهُ كُفْرٌ غَيْرَ
الصَّلاَةِ. رواه الترمذي.
Kuma ya zo daga Abdullahi xan Shaqiq, yace:
"Sahabban annabi Muhammadu sun kasance basa ganin barin wani aiki
kafirci ne in banda salla". Tirmiziy ya ruwaito shi (2622).
الثاني عشر: أوقات الصلاة
عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ عَمْرٍو رضي الله عنه، أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: "وَقْتُ
الظُّهْرِ إِذَا زَالَتِ الشَّمْسُ وَكَانَ ظِلُّ الرَّجُلِ كَطُولِهِ مَا لَمْ يَحْضُرِ
الْعَصْرُ، وَوَقْتُ الْعَصْرِ مَا لَمْ تَصْفَرَّ الشَّمْسُ، وَوَقْتُ صَلاةِ الْمَغْرِبِ
مَا لَمْ يَغِبِ الشَّفَقُ، وَوَقْتُ صَلاةِ الْعِشَاءِ إِلَى نِصْفِ اللَّيْلِ الأَوْسَطِ،
وَوَقْتُ صَلاةِ الصُّبْحِ مِنْ طُلُوعِ الْفَجْرِ مَا لَمْ تَطْلُعِ الشَّمْس"، رواه مسلم([12]).
An ruwaito daga Abdullahi xan Amru (r.a),
lallai Manon Allah (s.a.w), yace: "Lokacin sallar azahar shi ne idan rana
ta gota daga tsakiyar sama; inuwar mutum ya zamto kamar tsayinsa, matuqar
lokacin la'asar bai shiga ba. Shi kuma lokacin la'asar matuqar rana ba ta yi
fatsi-fatsi ba. Lokacin sallar magriba kuma matuqar "shafaqi" bai
vace ba. Shi kuma lokacin sallar ishah har zuwa tsakiyar rabin dare. Lokacin
sallar asuba kuma tun daga vullar alfijir; matuqar rana bata fito ba",
Muslim ya ruwaito shi (612).
الثالث عشر: استحباب الإبراد بالظهر في شدة الحر
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: "إِذَا اشْتَدَّ الْحَرُّ
فَأَبْرِدُوا بِالصَّلاةِ؛ فَإِنَّ شِدَّةَ الْحَرِّ مِنْ فَيْحِ جَهَنَّمَ"([13]).
NA SHA UKU: JINKIRTA SALLAR
AZAHAR A LOKACIN TSANANIN AFI
An ruwaito daga Abu-hurairah (r.a), daga
Annabi (s.a.w), ya ce: "Idan zafin rana ya yi tsanani to ku
sanyaya sallah –ma'ana: ku jinkirtata har sai duniya ta yi sanyi-; saboda
tsananin zafin rana yana daga tiririn wutar jahannama",
Bukhariy (533) da Muslim (615) suka ruwaito shi.
الرابع
عشر: إثم من تفوته صلاة العصر
عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عُمَرَ، أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: "مَنْ فَاتَتْهُ الْعَصْرُ،
فَكَأَنَّمَا وُتِرَ أَهْلَهُ وَمَالَه" رواه
البخاري ومسلم([14]).
NA SHA HUXU DA SHA BIYAR: ZUNUBIN
WANDA LA'ASAR TA FITA BAI YI BA
Daga Abdullahi xan Umar (r.a), lallai Manzon
Allah (s.a.w) yace: "Duk mutumin da sallar la'asar ta kufce masa; to kai
kace an wawashe iyalensa ne da dukiyarsa –ya rasa su baki-xaya-", Bukhariy
(552) da Muslim (626) suka ruwaito shi.
وعَنْ بُرَيْدَةَ رضي الله عنه قَالَ لأصحابه فِي يَوْمٍ ذِي غَيْمٍ:
بَكِّرُوا بِصَلاَةِ العَصْرِ، فَإِنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ قَالَ: "مَنْ
تَرَكَ صَلاةَ الْعَصْرِ فقد حبِطَ عَمَلُهُ"([15]).
Daga Buraidah (r.a) lallai shi yace wa
abokansa, a wani yinin da aka yi hazo, Ku yi sallar la'asar a farkon lokacinta,
saboda Annabi (s.a.w) yace: "Duk mutumin da ya bar sallar la'asar;
bai yi ta ba; to haqiqa aikinsa ya ruguje", Bukhariy ya ruwaito
shi (553).
السادس عشر: وقت صلاة المغرب
عن أبي أيوب رضي
الله عنه، قال: قال رَسُول اللَّهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّم: "لاَ
تَزَالُ أُمَّتِي بِخَيْرٍ، أَوْ عَلَى الْفِطْرَةِ مَا لَمْ يُؤَخِّرُوا الْمَغْرِبَ
إِلَى أَنْ تَشْتَبِكَ النُّجُومُ؟" رواه أبو داود([16]).
NA SHA SHIDA: LOKACIN MAGRIBA
Daga Abu-Ayyub (r.a) yace: Manon Allah (s.a.w)
yace: "Al'ummata ba za ta gushe tana cikin alheri ba matuqar basu jinkirta sallar magriba i zuwa taurari sashinsu ya shiga cikin sashi ba", Abu-Dawud ya ruwaito shi
(418).
السابع عشر: استحباب تأخير صلاة العشاء
عَنْ أبي بَرْزَةَ الْأَسْلَمِيّ رضي الله عنه، قال: «أنّ
رَسُول اللهِ r كان يَكْرَهُ النَّوْمَ قَبْلَ
الْعِشَاء، وَالْحَدِيثَ بَعْدَهَا»، متفق عليه([17]).
NA SHA BAKWAI: JINKIRTA LOKACIN ISHA
Daga Abu-barzatah Al-aslamiy (r.a) "Lallai Manzon
Allah (s.a.w) ya kasance yana qin ayi barci kafin sallar isha, da kuma hira
bayanta", Bukhariy (568) ya ruwaito shi da Muslim (647).
الثامن
عشر: فضل الصلاة على وقتها وبيان أنها أحبّ الأعمال إلى الله تعالى
عن عَبْدِ اللهِ بن مسعود رضي الله عنه قَالَ:
سَأَلْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: أَيُّ الْأَعْمَالِ
أَحَبُّ إِلَى اللهِ؟ قَالَ: «الصَّلَاةُ عَلَى وَقْتِهَا» قُلْتُ: ثُمَّ أَيٌّ؟ قَالَ: «ثُمَّ بِرُّ الْوَالِدَيْنِ» قُلْتُ: ثُمَّ أَيٌّ؟ قَالَ: «ثُمَّ الْجِهَادُ فِي سَبِيلِ اللهِ»، رواه البخاري ومسلم([18]).
NA SHA TAKWAS: FALALAR YIN SALLA
AKAN LOKACINTA
An ruwaito daga Abdullahi xan Mas'ud (r.a),
yace: Na tambayi Manon Allah (s.a.w) cewa: Wane aiki ya fi soyuwa a wajen
Allah? Sai ya ce: "Yin sallah akan
lokacinta", Nace: Sa'annan sai wane? Yace: Sa'annan sai
biyayya wa iyaye. Nace: Sa'annan sai wane? Yace: Sai jihadi
fiysabillah, Bukhariy (527, da 5970) ya ruwaito shi da Muslim (85).
التاسع
عشر: الطهور من شروط قبول الصلاة
عن ابْنَ عُمَرَ رضي الله عنه قَالَ: قال رَسُول اللهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قال: "لا يقْبَلُ اللهُ صَلاة بِغَيْرِ
طُهُورٍ"([19]).
NA GOMA SHA TARA: TSARKI YANA
DAGA CIKIN SHARRUXAN KARVAR SALLA
An ruwaito daga Abdullahi xan Umar (r.a) yace,
Manzon Allah (s.a.w) yace: "Allah ba ya
karvar sallah ba tare da tsarki ba", Muslim (224).
حديث التنزه من البول
عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي
الله عنهما, قال: قال رسول الله صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "تَنَزَّهُوا عن الْبَوْلِ؛ فَإِنَّ عَامَّةَ عَذَابِ
الْقَبْرِ مِنه"([20]).
Daga
Abdullahi xan Abbas (r.a) yace, Manon Allah (s.a.w) yace : "Ku tsarkaka daga fitsari; saboda yawancin azabar kabari
daga gare shi ne –rashin tsarkaka daga fitsari-".
حديث غسل الثوب الذي أصابه دم حيض
والصلاة فيه
عَنْ أَسْمَاءَ رضي الله عنها، قَالَتْ: جَاءَتِ
امْرَأَةٌ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَتْ: أَرَأَيْتَ
إِحْدَانَا تَحِيضُ فِي الثَّوْبِ، كَيْفَ تَصْنَعُ؟ قَالَ: "تَحُتّهُ، ثُمَّ تَقْرُصُهُ بِالْمَاءِ، ثُمَّ تَنْضَحْهُ، ثُمَّ تُصَلِّي فِيه"([21]).
An ruwaito daga Asma'u (r.a) tace: Wata mata
ta zo wajen Annabi (s.a.w) sai tace: Xayarmu idan ta yi haila a jikin wani
tufa, yaya zata yi? Sai ya ce: "Za ta kankare
shi da xan tsinke ko dutse, sa'annan ta cuccuxa shi da faratu da kuma geffan
yatsu cuccuxawa mai tsanani, sa'annan ta karkaxe shi, sannan ta yi sallah da tufanta).
Hadisin
mala'ika Jibrilu –AS- lokacin da ya limanci Annabi (r) a salloli guda biyar, sa'annan ya ce:
Ma'ana:
(Tsakanin waxannan lokutan guda biyu shi ne lokacin).
الحديث
العشرون: ستر العورة من شروط قبول الصلاة
عَنْ جَابِر بْن عَبْدِ اللَّهِ رضي الله عنه، قَالَ: قال رسول الله صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "إِذَا صَلَّيْتَ في ثَوْب
وَاحِد؛ فَإِنْ كَانَ وَاسِعًا فَالْتَحِفْ بِهِ، وَإِنْ كَانَ ضَيِّقًا فَاتَّزِرْ
بِه"([23]).
An ruwaito daga Jabir (r.a) yace: Nace, Manzon
Allah (s.a.w) yace: "Idan kana sallah da tufa xaya; in ya kasance mai
yalwa ne to sai ka lulluva da shi, in kuma mai qunci ne to sai ka xaura shi a
matsayin (izari –zani-)''.
حديث لباس المسلمة في الصلاة
وعَنْ عَائِشَةَ، عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
قَالَ: "لا يقْبَلُ اللهُ صَلاة حَائِضٍ
إِلا بِخِمَارٍ"([24]).
An ruwaito daga A'ishah (r.a), daga Manzon
Allah (s.a.w), yace: "Allah baya karvar sallar mace baliga –wacce ta kai
ta yi hailah- Sai ta sanya khimar –ta rufe kai-".
حديث الأذان مثنى مثنى والإقامة واحدة إلا قد قامت الصلاة:
عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه، قَالَ: «لَمَّا كَثُرَ النَّاسُ»
قَالَ: «ذَكَرُوا أَنْ يَعْلَمُوا وَقْتَ الصَّلاَةِ بِشَيْءٍ يَعْرِفُونَهُ،
فَذَكَرُوا أَنْ يُورُوا نَارًا، أَوْ يَضْرِبُوا نَاقُوسًا فَأُمِرَ بِلاَلٌ أَنْ يَشْفَعَ الأَذَانَ، وَأَنْ
يُوتِرَ الإِقَامَةَ، إِلاَّ الإِقَامَة»([25]).
KIRAN SALLA SAU BIBBIYU, IQAMA
SAU XAXXAYA, IN BANDA "QAD QAMATIS SALAH"
DagaAnas xan Malik (r.a) yace, A lokacin da Musulmai suka yi yawa,
Yace: Sai suka ambaci yadda zasu riqa gane shigan lokacin sallah da wani abinda
suka san shi, sai suka ambaci su riqa kunna wuta, ko su buga qararrawa, To sai
aka "umarci Bilal da ya maimata lafazin
kiran sallah sau bibbiyu, ya kuma xayanta laffuzan iqamah; saidai (qad-qaamatis
salatu)".
كيفية الآذان
عَنْ أَبِي مَحْذُورَةَ رضي الله عنه، قَالَ: قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ
عَلِّمْنِي سُنَّةَ الْأَذَانِ؟، قَالَ: فَمَسَحَ مُقَدَّمَ رَأْسِي، وَقَالَ: "تَقُولُ: اللَّهُ أَكْبَرُ اللَّهُ أَكْبَرُ،
اللَّهُ أَكْبَرُ اللَّهُ أَكْبَرُ، تَرْفَعُ بِهَا صَوْتَكَ، ثُمَّ تَقُولُ:
أَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، أَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا
اللَّهُ، أَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ، أَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا
رَسُولُ اللَّهِ، تَخْفِضُ بِهَا صَوْتَكَ، ثُمَّ تَرْفَعُ صَوْتَكَ
بِالشَّهَادَةِ، أَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، أَشْهَدُ أَنْ لَا
إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، أَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ، أَشْهَدُ
أَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ، حَيَّ عَلَى الصَّلَاةِ، حَيَّ عَلَى
الصَّلَاةِ، حَيَّ عَلَى الْفَلَاحِ، حَيَّ عَلَى الْفَلَاحِ، فَإِنْ كَانَ
صَلَاةُ الصُّبْحِ قُلْتَ: الصَّلَاةُ خَيْرٌ مِنَ النَّوْمِ، الصَّلَاةُ خَيْرٌ
مِنَ النَّوْمِ، اللَّهُ أَكْبَرُ اللَّهُ أَكْبَرُ، لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ"([26]).
HADISIN SIFAR KIRAN SALLAH
An ruwaito daga Abu-Mahzurah (r.a), yace:
Nace: Ya Ma'aikin Allah! Ka sanar da ni yadda kiran salla take? Yace: Sai ya
shafi kaina ta gaba, Ya kuma ce: Ka ce: "ALLAHU
AKBAR ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, kana mai xaga sautinka, Sannan
ka ce: ASH-HADU AN LA ILAHA ILLAL LAHU, ASH-HADU AN LA ILAHA ILLAL LAHU,
ASH-HADU ANNA MUHAMMADAN RASULUL LAHI, ASH-HADU ANNA MUHAMMADAN RASULUL LAHI,
HAYYA ALAS SALAH, HAYYA ALAS SALAH, HAYYA ALAL FALAH, HAYYA ALAL FALAH, Idan kuma
a kiran sallar asuba ne, ka ce: ASSALATU KHAIRUN MINAN NAUM, ASSALATU LHAIRUN
MINAN NAUM (wato: Sallah ita tafi alkhairi akan barci), ALLAHU AKBAR ALLAHU
AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU".
ما يقال عند الأذان وبعده
عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ عَمْرِو بْنِ الْعَاصِ رضي الله عنه، أَنَّهُ
سَمِعَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «إِذَا سَمِعْتُمُ الْمُؤَذِّنَ، فَقُولُوا مِثْلَ مَا
يَقُولُ ثُمَّ صَلُّوا عَلَيَّ، فَإِنَّهُ مَنْ صَلَّى عَلَيَّ صَلَاةً صَلَّى
الله عَلَيْهِ بِهَا عَشْرًا، ثُمَّ سَلُوا اللهَ لِيَ الْوَسِيلَةَ، فَإِنَّهَا
مَنْزِلَةٌ فِي الْجَنَّةِ، لَا تَنْبَغِي إِلَّا لِعَبْدٍ مِنْ عِبَادِ اللهِ،
وَأَرْجُو أَنْ أَكُونَ أَنَا هُوَ، فَمَنْ سَأَلَ لِي الْوَسِيلَةَ حَلَّتْ لَهُ
الشَّفَاعَةُ»([27]).
ABINDA AKE FAXA A LOKACIN KIRAN
SALLA DA BAYANSA
An ruwaito daga Abdullahi xan Amru xan As
(r.a), Lallai shi ya ji Annabi (s.a.w) yana cewa: "Idan kuka ji
kiran sallah, To sai ku faxi kwatankwacin abinda mai kiran ya ke faxa, Sa'annan
ku yi salati a gare ni, saboda duk wanda ya yi min salati guda xaya Allah zai
masa guda goma da ita, sa'annan ku roqa mini wasila; saboda ita wani matsayi ne
a cikin aljanna, wanda baya dacewa sai ga wani bawa daga cikin bayin Allah,
kuma ina fatan na kasance nine shi, Kuma duk wanda ya roqa min wasila to cetona
ya tabbata a gare shi".
وعَنْ عُمَرَ بْنِ الْخَطَّابِ رضي الله عنه، قَالَ:
قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "إِذَا قَالَ الْمُؤَذِّنُ: اللهُ أَكْبَرُ اللهُ
أَكْبَرُ، فَقَالَ أَحَدُكُمْ: اللهُ أَكْبَرُ اللهُ أَكْبَرُ، ثُمَّ قَالَ:
أَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، قَالَ: أَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا
اللهُ، ثُمَّ قَالَ: أَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ قَالَ: أَشْهَدُ
أَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ، ثُمَّ قَالَ: حَيَّ عَلَى الصَّلَاةِ، قَالَ: لَا
حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللهِ، ثُمَّ قَالَ: حَيَّ عَلَى الْفَلَاحِ،
قَالَ: لَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللهِ، ثُمَّ قَالَ: اللهُ أَكْبَرُ
اللهُ أَكْبَرُ، قَالَ: اللهُ أَكْبَرُ اللهُ أَكْبَرُ، ثُمَّ قَالَ: لَا إِلَهَ
إِلَّا اللهُ، قَالَ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ مِنْ قَلْبِهِ دَخَلَ الْجَنَّةَ"،
رواه مسلم([28]).
An ruwaito daga Umar xan Khaxxab (r.a) yace:
Manzon Allah (s.a.w) yace: "Idan mai kiran salla yace: ALLAHU AKBAR
ALLAHU AKBAR, Sai xayanku shima yace: ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, Sa'annan yace:
ASH-HADU AN LA ILAHA ILLAL LAHU, Sai yace: ASH-HADU AN LA ILAHA ILLAL LAHU,
Sa'annan yace: ASH-HADU ANNA MUHAMMADAN RASULUL LAHI, Sai yace: ASH-HADU ANNA
MUHAMMADAN RASULUL LAHI, Sa'annan yace: HAYYA ALAS SALAH, Sai yace: LA HAULA
WALA QUWWATA ILLA BILLAHI, Sa'annan yace: HAYYA ALAL FALAH, Sai yace: LA HAULA
WALA QUWWATA ILLA BILLAHI, Sa'annan yace: ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, Sai yace:
ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, Sa'annan yace: LA ILAHA ILLAL LAHU, Sai yace: LA
ILAHA ILLAL LAHU, daga cikin zuciyarsa, To ya shiga aljannah", Muslim ya
ruwaito shi (385).
وعَنْ سَعْدِ بْنِ أَبِي وَقَّاصٍ رضي الله عنه، عَنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهُ قَالَ: «من قَالَ حِينَ يَسْمَعُ الْمُؤَذِّنَ أَشْهَدُ أَنْ
لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ
وَرَسُولُهُ، رَضِيتُ بِاللهِ رَبًّا وَبِمُحَمَّدٍ رَسُولًا،
وَبِالْإِسْلَامِ دِينًا: غُفِرَ لَهُ ذَنْبُهُ»([29]).
An ruwaito daga Sa'ad xan Abiy-Waqqas (r.a),
daga Manzon Allah (s.a.w), lallai shi yace: "Wanda ya faxa
–a lokacin da ya ji mai kiran sallah-: ASH-HADU AN LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU
LA SHARIKA LAHU, WA ANNA MUHAMMADAN ABDUHU WA RASULUHU, RADIYTU BILLAHI RABBAN,
WA BI MUHAMMADIN RASULAN, WA BIL ISLAMI DIYNAN: To an gafarta masa zunubansa",
Muslim ya ruwaito shi (386).
وعَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ رضي الله عنه: أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ قَالَ: "مَنْ قَالَ حِينَ يَسْمَعُ النِّدَاءَ: "اللَّهُمَّ
رَبَّ هَذِهِ الدَّعْوَةِ التَّامَّةِ، وَالصَّلاةِ الْقَائِمَةِ، آتِ مُحَمَّدًا الْوَسِيلَةَ
وَالْفَضِيلَةَ، وَابْعَثْهُ مَقَامًا مَحْمُودًا الَّذِي وَعَدْتَه: حَلَّتْ لَهُ شَفَاعَتِي يَوْمَ القِيَامَةِ"([30]).
"ALLAHUMMA RABBA HAZIHID DA'AWATIT
TAMMAH, WAS SALATIL QA'IMAH ATI MUHAMMADAN ALWASILATA WAL FADIYLAH, WAB AS,HU
MAQAMAN MAHMUDAN ALLAZIY WA'ADDATAH".
An ruwaito daga Jabir xan Abdullahi (r.a),
lallai Manzon Allah (s.a.w) yace: "Duk
wanda yace –a lokacin jin kiran salla-:Ya Allah! Ubangijin wannan kira
cikakke, da kuma sallar da za a tsayar; Ka bawa annabi Muhammadu wasila
–matsayi na musamman a wajenka- da kuma falala, ka kuma tayar da shi; tare da
bashi matsayi abun yabo da ka yi masa alkawari: Cetona
ya tabbata a kansa, ranar qiyama".
عَن أبي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه، قَالَ: قَامَ
أَعْرَابِيٌّ فَبَالَ فِي المَسْجِدِ، فَتَنَاوَلَهُ النَّاسُ، فَقَالَ لَهُمُ
النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «دَعُوهُ وَهَرِيقُوا عَلَى بَوْلِهِ سَجْلًا مِنْ
مَاءٍ، أَوْ ذَنُوبًا مِنْ مَاءٍ، فَإِنَّمَا بُعِثْتُمْ مُيَسِّرِينَ، وَلَمْ
تُبْعَثُوا مُعَسِّرِينَ»([31]).
Daga Abu_Hurairah (r.a) yace: Wani balaraben
qauye yayi fitsari a cikin masallaci, sai mutane suka tsawatar masa da magana,
Sai Annabi yace musu: "Ku kyale
shi, sai ku kwarara wa fitsarinsa guga xaya babba; na ruwa, domin an turo ku ne
don sauqaqawa, kuma ba a turo ku don quntatawa ba",
Bukhariy ya ruwaito shi (22).
حديث
صفة الصلاة من الوضوء إلى التسليم
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: أَنَّ
رَجُلًا دَخَلَ المَسْجِدَ، وَرَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
جَالِسٌ فِي نَاحِيَةِ المَسْجِدِ، فَصَلَّى ثُمَّ جَاءَ فَسَلَّمَ عَلَيْهِ،
فَقَالَ لَهُ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «وَعَلَيْكَ السَّلاَمُ، ارْجِعْ فَصَلِّ
فَإِنَّكَ لَمْ تُصَلِّ» فَرَجَعَ فَصَلَّى، ثُمَّ جَاءَ فَسَلَّمَ عَلَى رَسُولِ
اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَرَدَّ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ السَّلَامَ قَالَ: «ارْجِعْ فَصَلِّ فَإِنَّكَ لَمْ تُصَلِّ»
فَرَجَعَ الرَّجُلُ فَصَلَّى كَمَا كَانَ صَلَّى، ثُمَّ جَاءَ إِلَى النَّبِيِّ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَسَلَّمَ عَلَيْهِ فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «وَعَلَيْكَ السَّلَامُ» ثُمَّ قَالَ: «ارْجِعْ فَصَلِّ
فَإِنَّكَ لَمْ تُصَلِّ» حَتَّى فَعَلَ ذَلِكَ ثَلَاثَ مَرَّاتٍ. فَقَالَ
الرَّجُلُ: وَالَّذِي بَعَثَكَ بِالْحَقِّ مَا أُحْسِنُ غَيْرَ هَذَا فعَلِّمْنِي،
قَالَ:
«إِذَا قُمْتَ إِلَى الصَّلاَةِ فَأَسْبِغِ
الوُضُوءَ، ثُمَّ اسْتَقْبِلِ القِبْلَةَ فَكَبِّرْ، ثُمَّ اقْرَأْ بِمَا
تَيَسَّرَ مَعَكَ مِنَ القُرْآنِ، ثُمَّ ارْكَعْ حَتَّى تَطْمَئِنَّ رَاكِعًا،
ثُمَّ ارْفَعْ حَتَّى تَسْتَوِيَ قَائِمًا، ثُمَّ اسْجُدْ حَتَّى تَطْمَئِنَّ
سَاجِدًا، ثُمَّ ارْفَعْ حَتَّى تَطْمَئِنَّ جَالِسًا، ثُمَّ اسْجُدْ حَتَّى
تَطْمَئِنَّ سَاجِدًا، ثُمَّ ارْفَعْ حَتَّى تَطْمَئِنَّ جَالِسًا، ثُمَّ افْعَلْ
ذَلِكَ فِي صَلاَتِكَ كُلِّهَا»([32]).
HADISIN SIFAR SALLAH TUN DAGA
ALWALA, HAR ZUWA SALLAMEWA
Daga Abu-Hurairah (r.a), Lallai Wani Mutum ya
shiga masallaci, alhalin Manzon Allah (s.a.w) yana cikin wani vangare na
masallacin, sai yayi salla, sa'annan ya zo ya yi sallama a gare shi, Sai Manzon
Allah (s.a.w) ya ce masa: "WA ALAIKAS
SALAM, Koma ka yi salla; kai baka yi salla ba, Sai ya koma ya yi sallah, Sannan
ya zo yayi sallama wa Manzon Allah (s.a.w), Sai Manzon Allah (s.a.w) ya amsa
masa sallama, sai kuma yace: Ka koma ka yi salla, lallai kai baka yi salla ba,
Sai mutumin ya koma yayi salla kamar yadda yayi salla, Sa'annan ya zo zuwa ga
Annabi (s.a.w) sai yayi sallama a gare shi, sai Manzon Allah (s.a.w) yace: WA
ALAIKAS SALAM, Sai kuma yace: Koma ka yi salla, lallai kai baka yi salla
ba", har sai da ya aikata haka, sau uku. Daga nan sai Mutumin yace: Na
rantse da wanda ya turo ka da gaskiya, Ban iya wanda ta fi wannan kyau ba, Ka
karantar da ni? Sai Manzon Allah (s.a.w) yace:
"Idan ka tashi i zuwa ga sallah to ka kyautata
alwala, sa'annan ka fiskanci alqibla, ka yi kabbara, Daga nan sai ka karanta
abinda ya sauwaqa na alqur'ani, Sa'annan ka yi ruku'i har sai ka nitsu a cikin
ruku'i, Sa'annan sai ka xago har sai ka daidaita a tsaye, Sa'annan ka yi
sujjada har sai ka nitsu cikin sujjada, Sa'annan sai ka xago har sai ka
daidaita a zaune, Sa'annan ka yi sujjada har sai ka nitsu a cikin sujjada,
Sa'annan sai ka xago har sai ka nitsu a zaune.
Sa'annan sai ka aikata haka a cikin sallarka
gabaxayanta",
Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 757, da
793, da 6251, da 6667) da Muslim (lamba:
397).
صلاة
المريض مع الاستطاعة أم بدونها
عَنْ عِمْرَانَ بْنِ حُصَيْنٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: كَانَتْ بِي
بَوَاسِيرُ، فَسَأَلْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنِ الصَّلاَةِ،
فَقَالَ: «صَلِّ قَائِمًا، فَإِنْ لَمْ تَسْتَطِعْ فَقَاعِدًا،
فَإِنْ لَمْ تَسْتَطِعْ فَعَلَى جَنْبٍ»([33]).
SALLAR MARAS LAFIYA, A HALIN
IKO, KO RASHINSA
An ruwaito daga Imrana xan Husain (r.a), yace:
Ciyon basir ya kasance tare da ni, Sai na tambayi Annabi (s.a.w), Sai yace: "Ka yi sallah a
tsaye; idan ba zaka iya ba to ka yi a zaune, idan ba zaka iya ba to ka yi akan
kuivi".
حديث أجر صلاة القاعد والقائم
عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه، أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ خَرَجَ فَرَأَى أُنَاسًا يُصَلُّونَ قُعُودًا، فَقَالَ:
«صَلَاةُ الْقَاعِدِ عَلَى النِّصْفِ مِنْ
صَلَاةِ الْقَائِمِ»([34]).
LADAN SALLAR NA ZAUNE DA NA
TSAYE
An ruwaito daga Anas xan Maliku (r.a) yace:
Lallai Manzon Allah (s.a.w) ya fita sai ya ga wasu mutane suna yin sallah a
zaune, Sai ya ce: "Sallar Mutumin
da yake zaune ladanta rabin ta wanda ya yi sallarsa ne a tsaye".
ذكر مفتاح الصلاة وتحريمها وتحليلها
عَنْ علي بن أبي طالب رضي الله عنه، قَالَ: قَالَ
رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مِفْتَاحُ الصَّلَاةِ الطُّهُورُ،
وَتَحْرِيمُهَا التَّكْبِيرُ، وَتَحْلِيلُهَا
التَّسْلِيمُ» "تَحْرِيمُهَا التَّكْبِير، وتَحْلِيلُهَا التَّسْلِيمُ"([35]).
MABUXIN SALLAH DA HARAMARTA DA
SALLAMEWA DAGA GARE TA
An
ruwaito daga Aliyu (r.a), yace: Manzon Allah (s.a.w) yace: "Mabuxin sallah
shine tsarki, Haramar shiga cikinta kuma shine: Yin kabbarar harama, abin da ke
sanya a fita daga haramcinta kuma shi ne: sallama".
ركنية
قراءة الفاتحة في الصلاة
عَنْ عُبَادَةَ بْنِ الصَّامِتِ رضي الله عنه: أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لاَ صَلاَةَ لِمَنْ لَمْ يَقْرَأْ بِفَاتِحَةِ
الكِتَابِ» ([36]).
WAJABCIN KARATUN FATIHA A CIKIN SALLAH
An ruwaito daga Ubadah xan Samit (r.a), lallai
Manzon Allah (s.a.w) yace: "Babu sallah ga
wanda bai karanta fatiha ba".
السجود
على سبعة أعظم
عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«أُمِرْتُ أَنْ أَسْجُدَ عَلَى سَبْعَةِ أَعْظُمٍ: الْجَبْهَةِ -ثُمَّ أَشَارَ بِيَدِهِ إِلَى
أَنْفِهِ- وَالْيَدَيْنِ، وَالرُّكْبَتَيْنِ، وَأَطْرَافِ الْقَدَمَيْنِ»([37]).
YIN SUJJADA AKAN GAVVAI BAKWAI
An ruwaito daga Abdullahi xan Abbas (r.a),
daga Annabi (s.a.w) yace: "An umurce ni da
na yi sujjada akan gavvai bakwai; goshi –sai ya yi nuni i zuwa hancinsa-, da
tafuka biyu, da guiwowi biyu, da kuma kan 'yan yatsu".
فرضية التشهد
عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ مَسْعُودٍ رضي الله عنه، أَنَّهُ قَالَ: "كُنَّا نَقُولُ قَبْلَ أَنْ يُفْرَضَ عَلَيْنَا
التَّشَهُّدُ: السَّلاَمُ عَلَى اللَّهِ من عـباده، فَقَـالَ النـبـي r:
لا تَقُولُوا: السَّلامُ عَلَى اللَّه، وَلَكِنْ قُولُوا: التَّحِيَّاتُ للهِ"([38]).
WAJABCIN YIN TAHIYA A CIKIN
SALLAH
An ruwaito daga Abdullahi xan Mas'ud (r.a)
yace: "Mun kasance muna cewa –kafin a farlanta yin
tahiya-: Aminci ya tabbata ga Allah daga bayinsa. Sai Annabi -r- ya ce: Kada
ku ce: aminci ya tabbata ga Allah, sai dai ku ce: Gaisuwa duk na Allah ne".
صلوا كما
رأيتموني أُصلِّي
عَنْ أَبِي سُلَيْمَانَ مَالِكِ بْنِ الحُوَيْرِثِ
رضي الله عنه، قال: أَتَيْنَا إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
وَنَحْنُ شَبَبَةٌ مُتَقَارِبُونَ، فَأَقَمْنَا عِنْدَهُ عِشْرِينَ يَوْمًا
وَلَيْلَةً، وَكَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَحِيمًا
رَفِيقًا، فَلَمَّا ظَنَّ أَنَّا قَدِ
اشْتَهَيْنَا أَهْلَنَا - أَوْ قَدِ اشْتَقْنَا - سَأَلَنَا عَمَّنْ تَرَكْنَا
بَعْدَنَا، فَأَخْبَرْنَاهُ، قَالَ: «ارْجِعُوا إِلَى أَهْلِيكُمْ، فَأَقِيمُوا
فِيهِمْ وَعَلِّمُوهُمْ وَمُرُوهُمْ - وَذَكَرَ أَشْيَاءَ أَحْفَظُهَا أَوْ لاَ
أَحْفَظُهَا - وَصَلُّوا كَمَا رَأَيْتُمُونِي أُصَلِّي، فَإِذَا حَضَرَتِ
الصَّلاَةُ فَلْيُؤَذِّنْ لَكُمْ أَحَدُكُمْ، وَلْيَؤُمَّكُمْ أَكْبَرُكُمْ»([39]).
KU YI SALLAH KAMAR YADDA NAKE YI
An ruwaito daga Abu-Sulaiman Malik xan
Alhuwairis (r.a), yace: Mun zo zuwa ga Annabi (s.a.w) alhali Mu samari ne masu
kusanci shekaru, sai muka zauna a wurinsa tsawon yinin ashirin da dararensu,
kuma Manzon Allah (s.a.w) ya kasance mai jin qai ne mai tausasawa, yayin da
yayi zaton cewa lallai mun sha'awar iyalanmu –ko muna begensu- sai ya tambaye
mu, kan waxanda muka bari a bayanmu, sai muka bashi labari, Daga nan sai ya ce:
"Ku koma zuwa ga iyalanku, ku zauna a cikinsu, ku
karantar da su, kuna umurtarsu, -sai kuma ya ambaci abubuwa dayawa, na
kiyaye su ko ban hardace su ba, daga ciki ya ce:- kuma ku riqa yin sallah
kamar yadda ku ka ganni nake yin sallah. Kuma idan sallah ta zo sai xayanku
yayi muku kiran sallah, sai babbanku ya limance ku"
Bukhariy da Muslim.
مواضع التكبير في الصلاة، وذكر التسليمتين
عَنْ أبي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه، قال: «كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
إِذَا قَامَ إِلَى الصَّلَاةِ يُكَبِّرُ حِينَ يَقُومُ، ثُمَّ يُكَبِّرُ حِينَ
يَرْكَعُ» ثُمَّ يَقُولُ: «سَمِعَ اللهُ لِمَنْ حَمِدَهُ حِينَ
يَرْفَعُ صُلْبَهُ مِنَ الرُّكُوعِ» ثُمَّ يَقُولُ: وَهُوَ قَائِمٌ «رَبَّنَا وَلَكَ الْحَمْدُ، ثُمَّ
يُكَبِّرُ حِينَ يَهْوِي سَاجِدًا، ثُمَّ يُكَبِّرُ حِينَ يَرْفَعُ رَأْسَهُ،
ثُمَّ يُكَبِّرُ حِينَ يَسْجُدُ، ثُمَّ يُكَبِّرُ حِينَ يَرْفَعُ رَأْسَهُ، ثُمَّ
يَفْعَلُ مِثْلَ ذَلِكَ فِي الصَّلَاةِ كُلِّهَا حَتَّى يَقْضِيَهَا، وَيُكَبِّرُ
حِينَ يَقُومُ مِنَ الْمَثْنَى بَعْدَ الْجُلُوسِ» ثُمَّ يَقُولُ: أَبُو هُرَيْرَةَ «إِنِّي لَأَشْبَهُكُمْ صَلَاةً بِرَسُولِ اللهِ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ»([40]).
WURAREN YIN KABBARA A CIKIN
SALLAH DA BAYANIN SALLAMA BIYU
An ruwaito daga Abu-Hurairah (r.a), yace: "Manzon Allah –r- ya kasance
yana yin kabbara a lokacin da ya taso zuwa ga sallah, sa'annan ya yi kabbara a
lokacin da yake yin ruku'i, sa'annan ya ce: ''sami'al-lahu liman
hamidah" a lokacin da ke xago bayansa daga ruku'i, sa'annan ya ce
–alhalin yana tsaye cat-: rabbana wa lakal hamdu. Sa'annan yayi kabbara a
lokacin da yake tafiya sujjada. Sa'annan yayi kabbara a lokacin da yake xago
kansa. Sa'annan ya sake kabbara a lokacin da yake sake sujjada. Sa'annan yayi
kabbara a lokacin da yake xago kansa. Sa'annan ya aikata kamar haka a cikin
sallarsa gabaxayanta har ya kammala ta. Sai kuma yayi kabbara a lokacin da yake
xagowa daga raka'a ta biyu, bayan zaman tahiya. Sa'annan a wannan gavar sai
Abu-Hurairah yace: Lallai Nine na fi ku koyi da sallar Manzon Allah (s.a.w) ".
وعَنْ عَبْدِ اللَّهِ بن مسعود رضي الله عنه، قَالَ: "رَأَيْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُكَبِّرُ فِي كُلِّ خَفْضٍ وَرَفْعٍ، وَقِيَامٍ وَقُعُودٍ،
وَيُسَلِّمُ عَنْ يَمِينِهِ، وَعَنْ شِمَالِهِ: السَّلَامُ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَةُ
اللَّهِ، السَّلَامُ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَةُ اللَّهِ، حَتَّى يُرَى بَيَاضُ خَدِّهِ
"، وَرَأَيْتُ أَبَا بَكْرٍ وَعُمَرَ رَضِيَ
اللَّهُ عَنْهُمَا يَفْعَلَانِ ذَلِكَ" ([41]).
An ruwaito daga Abdullahi xan Mas'ud (r.a)
yace: "Naga Manzon
Allah (r) yana kabbara
a duk xagowa da sunkuyawa, da kuma tashi da zama. Kuma yana yin sallama ta dama
gare shi da ta haqu; cewa: ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAH, ASSALAMU ALAIKUM WA
RAHMATULLAHI, har sai an ga farin da ke kumatunsa. Kuma nag a Abubakar da Umar
–Allah ya qara yarda a gare su- suna aikata haka".
ذكر الائتمام بالإمام
عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه، أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَكِبَ فَرَسًا، فَصُرِعَ عَنْهُ فَجُحِشَ شِقُّهُ
الأَيْمَنُ، فَصَلَّى صَلاَةً مِنَ الصَّلَوَاتِ وَهُوَ قَاعِدٌ، فَصَلَّيْنَا
وَرَاءَهُ قُعُودًا، فَلَمَّا انْصَرَفَ قَالَ: "إِنَّمَا جُعِلَ الإِمَامُ لِيُؤْتَمَّ
بِهِ، فَإِذَا صَلَّى قَائِمًا، فَصَلُّوا قِيَامًا، فَإِذَا رَكَعَ، فَارْكَعُوا
وَإِذَا رَفَعَ، فَارْفَعُوا، وَإِذَا قَالَ: سَمِعَ اللَّهُ لِمَنْ حَمِدَهُ،
فَقُولُوا: رَبَّنَا وَلَكَ الحَمْدُ، وَإِذَا صَلَّى قَائِمًا، فَصَلُّوا
قِيَامًا، وَإِذَا صَلَّى جَالِسًا، فَصَلُّوا جُلُوسًا أَجْمَعُونَ".
قَالَ أَبُو عَبْدِ اللَّهِ البخاري: قَالَ الحُمَيْدِيُّ: قَوْلُهُ:
«إِذَا صَلَّى جَالِسًا فَصَلُّوا جُلُوسًا» بهُوَ فِي مَرَضِهِ القَدِيمِ، ثُمَّ
صَلَّى بَعْدَ ذَلِكَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ جَالِسًا،
وَالنَّاسُ خَلْفَهُ قِيَامًا، لَمْ يَأْمُرْهُمْ بِالقُعُودِ، وَإِنَّمَا
يُؤْخَذُ بِالْآخِرِ فَالْآخِرِ، مِنْ فِعْلِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ
AN SANYA LIMAMI DON AYI KOYI DA
SHI
An ruwaito daga Anas xan Malik (r.a) lallai
Manzon Allah (s.a.w) ya hau wani doki sai yayi rauni a vangarensa na dama, sai
ya sallaci xaya daga cikin salloli alhalin yana zaune, sai muma muka yi salla a
bayansa a zaune, a yayin da ya idar da sallah sai ya ce: "Kawai an sanya
liman ne domin ayi koyi da shi, don haka idan yayi sallah a tsaye sai ku yi
sallah a tsaye, idan yayi ruku'i sai ku yi ruku'i, idan ya xago sai ku xago, Idan
kuma ya ce: sami'al-lahu liman hamidahu, to kuce: rabbana lakal hamdu. Idan ya
yi sallah a tsaye sai ku yi sallah a tsaye, idan kuma yayi sallah a zaune to sai
ku yi sallah a zaune gabaxaya". Abu-Abdullahi Albukhariy
yace: (Malamina) Alhumaidiy y ace: Faxinsa a cikin hadisin: " idan kuma yayi
sallah a zaune to sai ku yi sallah a zaune" hakan ya kasance ne,
a wani daxaxxen jinyarsa (s.a.w). Sa'annan sai Annabi (s.a.w) bayan haka wata
rana yayi sallah a zaune, mutane kuma suna bayansa suna biye da shi, amma sai
bai umurce su da zama ba, kuma a lamuran Manzon Allah (s.a.w) da aiyukansa abin
sani, kawai ana xaukar aikinsa na qarshe, na qarshe ne. .
Ka
yi
muraja'ar
zuwa
nan
الذكر في الركوع والرفع منه والسجود، واستحباب تطويل صلاة الليل
عَنْ حُذَيْفَةَ رضي الله عنه، قَالَ: صَلَّيْتُ مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ذَاتَ لَيْلَةٍ، فَافْتَتَحَ الْبَقَرَةَ، فَقُلْتُ:
يَرْكَعُ عِنْدَ الْمِائَةِ، ثُمَّ مَضَى، فَقُلْتُ: يُصَلِّي بِهَا فِي رَكْعَةٍ،
فَمَضَى، فَقُلْتُ: يَرْكَعُ بِهَا، ثُمَّ افْتَتَحَ النِّسَاءَ، فَقَرَأَهَا،
ثُمَّ افْتَتَحَ آلَ عِمْرَانَ، فَقَرَأَهَا، يَقْرَأُ مُتَرَسِّلًا، إِذَا مَرَّ
بِآيَةٍ فِيهَا تَسْبِيحٌ سَبَّحَ، وَإِذَا مَرَّ بِسُؤَالٍ سَأَلَ، وَإِذَا مَرَّ
بِتَعَوُّذٍ تَعَوَّذَ، ثُمَّ رَكَعَ، فَجَعَلَ يَقُولُ: «سُبْحَانَ رَبِّيَ الْعَظِيمِ»، فَكَانَ رُكُوعُهُ نَحْوًا مِنْ قِيَامِهِ، ثُمَّ
قَالَ: «سَمِعَ اللهُ
لِمَنْ حَمِدَهُ»، ثُمَّ قَامَ طَوِيلًا قَرِيبًا مِمَّا رَكَعَ،
ثُمَّ سَجَدَ، فَقَالَ: «سُبْحَانَ
رَبِّيَ الْأَعْلَى»، فَكَانَ
سُجُودُهُ قَرِيبًا مِنْ قِيَامِهِ"([43]).
ZIKIRIN RUKU'I DA BAYAN XAGOWA,
DANA SUJJADA, DA TSAWAITA SALLAR DARE TA NAFILA
An ruwaito daga Huzaifah (r.a), yace: ((Na yi
sallah tare da Annabi (s.a.w) a cikin wani dare, Sai ya buxe karatunsa da
karanta "suratul baqarah", Sai nace: Zai yi ruku'i idan ya kai aya ta
xari, sai ya wuce, Sai nace: Zai karanta wannan surar gabaxayanta a cikin
raka'a guda, Sai ya wuce. Sa'annan sai ya buxe "suratun Nisa'i" sai
ya karantata, Sa'annan sai ya buxe "suratu Ali-imran, sai ya karantata,
yana yin karatu a cikin tsanaki, kuma idan ya wuce ayar da a cikinta akwai yin
"tasbihi" sai ya yi tasbihi wa Allah, Idan kuma ya wuce ayar da a
cikinta akwai roqon Allah, sai ya roqe shi, ko kuma neman tsari sai ya nemi
tsarinsa. Sa'an nan sai ya yi ruku'i, kuma ya riqa cewa: "a cikin
ruku'insa: "subhana rabbiyal aziim", kuma ruku'insa
ya kasance kusa da tsawon karatunsa, Sannan yace: "Sami'al lahu liman
hamidah", Sannan ya yi dogon tsayuwa, kusa da tsawon ruku'insa.
Sa'annan ya yi sujjada, Sai ya ce: "Subhana rabbiyal a'alah", kuma
sujjadarsa tsawonta ya kasance kusa da tsayuwarsa na karatu)).
التشهد وتخيُّر الدعاء بعده
عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ مَسْعُودٍ رضي الله عنه، قَالَ: إِنَّ
مُحَمَّدًا صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عُلِّمَ فَوَاتِحَ الْخَيْرِ،
وَجَوَامِعَهُ، وَخَوَاتِمَهُ، فَقَالَ: "إِذَا قَعَدْتُمْ فِي كُلِّ رَكْعَتَيْنِ، فَقُولُوا:
التَّحِيَّاتُ لِلَّهِ، وَالصَّلَوَاتُ وَالطَّيِّبَاتُ، السَّلَامُ عَلَيْكَ
أَيُّهَا النَّبِيُّ وَرَحْمَةُ اللهِ وَبَرَكَاتُهُ، السَّلَامُ عَلَيْنَا
وَعَلَى عِبَادِ اللهِ الصَّالِحِينَ، أَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ،
وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ، ثُمَّ لِيَتَخَيَّرْ
أَحَدُكُمْ مِنَ الدُّعَاءِ أَعْجَبَهُ إِلَيْهِ، فَلْيَدْعُ بِهِ رَبَّهُ عَزَّ
وَجَلَّ"([44]).
YIN "TAHIYA" DA
ADDU'OIN BUQATU A BAYANTA
An ruwaito daga Abdullahi xan Mas'ud (r.a),
Yace: Lallai annabi Muhammadu (s.a.w) an ilmantar da shi mabuxan alkhairori, da
alkhairori masu gamewa, da na qarshensu, Sai yace: "Idan kuka zauna
a cikin kowaxanne raka'oi biyu to ku ce: attahiyatu lillahi, wassalawatu
waxxayibatu, Assalamu alaika ayyuhan nabiyyu, wa rahmatullahi wa barakatuhu,
Assalamu Alaina wa ala ibadillahis salihina, Ash-hadu an la ilaha illal lahu,
wa ash-hadu anna Muhammadan abduhu wa rasuluhu". Sai kuma Xayanku ya zavo
abinda ya burge shin a addu'a, sai ya roqi UbangijinSa mabuwayi da xaukaka da
shi".
إجمال صفة الصلاة
عَنْ رِفَاعَةَ بْنِ رَافِعٍ رضي الله عنه، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: «إِذَا أَنْتَ قُمْتَ فِي صَلَاتِكَ، فَكَبِّرِ اللَّهَ تَعَالَى، ثُمَّ
اقْرَأْ مَا تَيَسَّرَ عَلَيْكَ مِنَ الْقُرْآنِ» وَقَالَ فِيهِ: «فَإِذَا جَلَسْتَ فِي وَسَطِ الصَّلَاةِ
فَاطْمَئِنَّ، وَافْتَرِشْ فَخِذَكَ الْيُسْرَى ثُمَّ تَشَهَّدْ. ثُمَّ إِذَا
قُمْتَ فَمِثْلَ ذَلِكَ حَتَّى تَفْرُغَ مِنْ صَلَاتِكَ»([45]).
BAYANIN SALLAH A DUNQULE
An ruwaito daga daga Rifa'ah xan Rafi'I (r.a),
daga Annabi (s.a.w) yace: "Idan ka tashi a
cikin sallarka, sai ka yi kabbara wa Allah ta'alah (Allahu akbar), Sa'an nan
sai ka karanta abinda ya sauqaqa a gare ka na alqur'ani. Kuma ya faxa a
cikin hadisin: Kuma idan ka zauna a
tsakiyar sallah to sai ka nitsu, ka kuma shumfuxa cinyarka ta hagu
''iftirashi'' sai ka yi "tahiya". Sa'an nan idan ka tashi, sai aikata
kwatankwacin haka, hark a gama sallarka".
نسخ الكلام في الصلاة (1-3)
(ح1) عَنْ زَيْدِ بْنِ أَرْقَمَ رضي الله عنه، قَالَ: "كُنَّا نَتَكَلَّمُ فِي الصَّلاَةِ؛ يُكَلِّمُ
الرَّجُلُ صَاحِبَه وهو إِلَى جَانِبِهِ فِي الصَّلاَةِ حَتَّى نَـزَلَـتْ: ﭽ ﭖ ﭗ ﭘ ﭼ البقرة: ٢٣٨ فَأُمِرْنَا بِالسُّكُوتِ، وَنُهِينَا عَنِ الْكَلاَمِ"([46]).
SOKE HALACCIN YIN MAGANA A CIKIN
SALLAH (1-3)
An ruwaito daga Zaid xan Arqam (r.a), yace: "Mun kasance
muna yin magana a cikin sallah; Mutum ya kan yi magana da abokinsa da yake
gefensa a cikin sallah, sai faxin Allah ta'alah ya sauka: ''Kuma ku tsaya ga
Allah kuna masu shiru'' Sai aka umurce mu da yin shiru, aka kuma hane mu kan yin
magana".
(ح2) عَنْ مُعَاوِيَةَ بْنِ الْحَكَمِ السُّلَمِيِّ، قَالَ: بَيْنَا أَنَا
أُصَلِّي مَعَ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، إِذْ عَطَسَ رَجُلٌ
مِنَ الْقَوْمِ، فَقُلْتُ: يَرْحَمُكَ اللهُ فَرَمَانِي الْقَوْمُ
بِأَبْصَارِهِمْ، فَقُلْتُ: وَاثُكْلَ أُمِّيَاهْ، مَا شَأْنُكُمْ؟ تَنْظُرُونَ
إِلَيَّ، فَجَعَلُوا يَضْرِبُونَ بِأَيْدِيهِمْ عَلَى أَفْخَاذِهِمْ، فَلَمَّا
رَأَيْتُهُمْ يُصَمِّتُونَنِي لَكِنِّي سَكَتُّ، فَلَمَّا صَلَّى رَسُولُ اللهِ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَبِأَبِي هُوَ وَأُمِّي، مَا رَأَيْتُ
مُعَلِّمًا قَبْلَهُ وَلَا بَعْدَهُ أَحْسَنَ تَعْلِيمًا مِنْهُ، فَوَاللهِ، مَا
كَهَرَنِي وَلَا ضَرَبَنِي وَلَا شَتَمَنِي، قَالَ: «إِنَّ هَذِهِ الصَّلَاةَ لَا يَصْلُحُ فِيهَا
شَيْءٌ مِنْ كَلَامِ النَّاسِ، إِنَّمَا هُوَ التَّسْبِيحُ وَالتَّكْبِيرُ وَقِرَاءَةُ
الْقُرْآنِ»([47]).
An ruwaito daga Mu'awuya xan Alhakam Assulamiy
(r.a), yace: "Wata rana ina yin salla tare da Manzon Allah (s.a.w) sai wani daga
cikin mutane ya yi atishawa, Sai nace: YARHAMUKALLAHU, Sai waxannan Mutanen
suka jefe ni da idanunsu, Sai nace: Ya kaicon Uwata, Menene sha'aninku? Kuna ta
kallona! Sai suka fara dukan cinyoyinsu da hannayensu, A yayin da naga suna ta
neman sani na yi shiru, sai na yi shiru. Yayin da Manzon Allah (s.a.w) y agama
sallarsa, Ina bada fansarsa da Ubana da Uwata! Ban ga wani malami gabaninsa ko
bayansa da yafi shi kyawun hanyar karantarwa ba, Na rantse da Allah! Bai
tsawatar mini ba, kuma bai doke nib a, kuma bai zage ni ba, Kawai cewa yayi:
"Lallai ita sallah wani abu na maganan Mutane baya dacewa a cikinta, kasancewar
sallah tasbihi (faxin subhana rabbiyal a'alah ko azim) ne da takbiri (faxin
Allahu akbar), da karatun alqur'ani".
(ح3) عَنْ
عَبْدِ اللهِ بن مسعود رضي الله عنه، قَالَ: كُنَّا نُسَلِّمُ عَلَى رَسُولِ اللهِ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَهُوَ فِي الصَّلَاةِ، فَيَرُدُّ عَلَيْنَا،
فَلَمَّا رَجَعْنَا مِنْ عِنْدِ النَّجَاشِيِّ، سَلَّمْنَا عَلَيْهِ فَلَمْ
يَرُدَّ عَلَيْنَا، فَقُلْنَا: يَا رَسُولَ اللهِ كُنَّا نُسَلِّمُ عَلَيْكَ فِي
الصَّلَاةِ فَتَرُدُّ عَلَيْنَا، فَقَالَ: «إِنَّ فِي الصَّلَاةِ شُغْلًا»([48]).
An ruwaito daga Abdullahi xan Mas'ud (r.a),
yace: "Mun kasance muna yin sallama ga Manzon Allah (s.a.w) alhalin yana
cikin sallah, sai ya mayar mana da sallama, yayin da Muka dawo daga wajen sarki
Najashiy, sai muka yi sallama wa Manzon Allah amma sai bai amsa man aba, Sai
muka ce: Ya Ma'aikin Allah! Da mun kasance muna yin sallama a gare ka, alhalin
kana cikin sallah sai ka mayar mana, Sai ya ce: "Lallai cikin sallah
akwai aiyuka masu hana shalin duniya".
سترة المصلي وإثم المار بين يديه (1-2)
(ح1) عَنْ أَبِي ذَرٍّ رضي الله عمه، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِذَا
قَامَ أَحَدُكُمْ يُصَلِّي، فَإِنَّهُ يَسْتُرُهُ إِذَا كَانَ بَيْنَ يَدَيْهِ
مِثْلُ آخِرَةِ الرَّحْلِ، فَإِذَا لَمْ يَكُنْ بَيْنَ يَدَيْهِ مِثْلُ آخِرَةِ
الرَّحْلِ، فَإِنَّهُ يَقْطَعُ صَلَاتَهُ الْحِمَارُ، وَالْمَرْأَةُ، وَالْكَلْبُ
الْأَسْوَدُ» قُلْتُ: يَا أَبَا
ذَرٍّ، مَا بَالُ الْكَلْبِ الْأَسْوَدِ مِنَ الْكَلْبِ الْأَحْمَرِ مِنَ
الْكَلْبِ الْأَصْفَرِ؟ قَالَ: يَا ابْنَ أَخِي، سَأَلْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَمَا سَأَلْتَنِي فَقَالَ: «الْكَلْبُ الْأَسْوَدُ شَيْطَانٌ»([49]).
SUTURAR MAI SALLAH, DA ZUNUBIN
MAI SHIGEWA TA GABANSA
"Idan xayanku ya
tashi yana sallah, to lallai zai zama suturarsa idan akwai kimanin tuntun da ke
bayan sirdi, amma idan babu kwatankwacin abin da ke karshen sirdi to lallai
jaki da mace da kuma baqin kare idan su ka gifta za su yanke masa sallah".
(ح2) وعن أَبِي
جُهَيْمٍ رضي الله عنه قال، قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَوْ يَعْلَمُ الْمَارُّ بَيْنَ يَدَيِ الْمُصَلِّي
مَاذَا عَلَيْهِ، لَكَانَ أَنْ يَقِفَ أَرْبَعِينَ خَيْرًا لَهُ، مِنْ أَنْ
يَمُرَّ بَيْنَ يَدَيْهِ» قَالَ الراوي: "لَا أَدْرِي قَالَ: أَرْبَعِينَ يَوْمًا
أَوْ شَهْرًا أَوْ سَنَةً؟"([50]).
An ruwaito daga Abu-Huhaim (r.a), yace: Manzon
Allah (s.a.w) yace: "Da Mai shigewa ta gaban masallaci ya san abinda
yake kansa na zunubi, to da ya kasance ya tsaya arba'in shi yafi alheri a gare
shi akan ya shige ta gaba gar shi" Maruwaicin hadisin yace: Ban sani ba,
kwanaki arba'in ya faxa, ko watanni arba'in, ko shekaru arba'in.
حكم الالتفات في الصلاة
عَنْ عَائِشَةَ رضي الله عنها، قَالَتْ: سَأَلْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنِ الِالْتِفَاتِ فِي الصَّلاَةِ؟ فَقَالَ: «هُوَ اخْتِلاَسٌ يَخْتَلِسُهُ الشَّيْطَانُ
مِنْ صَلاَةِ العَبْدِ»([51]).
HUKUNCIN WAIGAWA A CIKIN SALLAH
An ruwaito daga A'isha (r.a), ta ce: Na
tambayi Manzon Allah akan waigawa a cikin sallah, sai ya ce:
"Waigawa wata Wafta ce da shexan ke wafta daga sallar bawa".
صحيح البخاري
759 - حَدَّثَنَا أَبُو نُعَيْمٍ، قَالَ: حَدَّثَنَا شَيْبَانُ، عَنْ يَحْيَى،
عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ أَبِي قَتَادَةَ، عَنْ أَبِيهِ، قَالَ: «كَانَ
النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقْرَأُ فِي الرَّكْعَتَيْنِ الأُولَيَيْنِ مِنْ
صَلاَةِ الظُّهْرِ بِفَاتِحَةِ الكِتَابِ، وَسُورَتَيْنِ يُطَوِّلُ فِي الأُولَى،
وَيُقَصِّرُ فِي الثَّانِيَةِ
وَيُسْمِعُ الآيَةَ أَحْيَانًا، وَكَانَ يَقْرَأُ فِي العَصْرِ بِفَاتِحَةِ
الكِتَابِ وَسُورَتَيْنِ، وَكَانَ يُطَوِّلُ فِي الأُولَى، وَكَانَ يُطَوِّلُ فِي
الرَّكْعَةِ الأُولَى مِنْ صَلاَةِ الصُّبْحِ، وَيُقَصِّرُ فِي الثَّانِيَةِ»
760 - حَدَّثَنَا عُمَرُ بْنُ حَفْصٍ، قَالَ: حَدَّثَنَا أَبِي، قَالَ:
حَدَّثَنَا الأَعْمَشُ، حَدَّثَنِي عُمَارَةُ، عَنْ أَبِي مَعْمَرٍ، قَالَ:
سَأَلْنَا خَبَّابًا أَكَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقْرَأُ فِي الظُّهْرِ وَالعَصْرِ؟
قَالَ: نَعَمْ، قُلْنَا: بِأَيِّ شَيْءٍ كُنْتُمْ تَعْرِفُونَ؟ قَالَ:
«بِاضْطِرَابِ لِحْيَتِهِ»
المصلي يناجي ربه
عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه، عَنِ النَّبِيِّ صلّى الله عليه
وسلم قَالَ: «اعْتَدِلُوا
فِي السُّجُودِ، وَلاَ يَبْسُطْ ذِرَاعَيْهِ كَالكَلْبِ، وَإِذَا بَزَقَ فَلاَ
يَبْزُقَنَّ بَيْنَ يَدَيْهِ، وَلاَ عَنْ يَمِينِهِ، فَإِنَّهُ يُنَاجِي رَبَّهُ» ([52]).
MAI SALLAH YANA GANAWA NE DA
UBANGIJINSA
An ruwaito daga Anas xan Malik (r.a), daga
Annabi (s.a.w), yace: "Ku daidaita a cikin sujjada, kada xayanku ya
shumfuxa zira'insa irin shumfuxawar kare, kuma idan zai yi kaki to kada ya
tofar da shi ta gaba gare shi, ko ta damansa, saboda yana yin ganawa ne da
UbangijinSa".
النهي عن الاختصار في الصلاة
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: "نَهَى
النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنْ يُصَلِّيَ الرَّجُلُ
مُخْتَصِرًا"([53]).
HANI KAN RIQE KWANKWASO A CIKIN
SALLAH
An ruwaito daga Abu-Hurairah (r.a) yace: (Annabi –s.a.w-
ya hana Mutum ya yi sallah yana riqe da kwankwaso).
Hadisin
Abu-hurairah -t-, yace:
"Annabi -r- ya hana a yi
''sadlu'' a cikin sallah, ya kuma yi hani kan mutum ya xaure bakinsa a cikinta).
"أَمَا
يَخْشَى أَحَدُكُمْ إِذَا رَفَـعَ رَأْسَـهُ قَبْلَ الإِمَـامِ، أَنْ يَجْـعَلَ اللَّهُ
رَأْسَـهُ رَأْسَ حِمَـارٍ، أَوْ يَـجْعَلَ صُـورَتَهُ صُـورَةَ حِـمَارٍ"([55]).
"Xayanku ba zai ji tsoron –idan
ya xaga kansa kafin liman- Allah ya sanya kansa ya zama kai irin na jaki ba, ko
kuma ya sanya xaukacin jikinsa ya zama irin jikin jaki!).
Hadisin
Abdullahi xan Abbas -t-, ya ce:
"أُمِرَ
النَّبِيُّ r أَنْ يَسْجُدَ عَلَى سَبْعَةِ
أَعْظُمٍ، وَلاَ يَكُفَّ ثَوْبه وَلاَ شَعَره" ([56]).
"An umurci Annabi -r- da yin
sujjada akan qasussuwa guda bakwai -gabbai-, kada kuma ya tare tufarsa da
gashinsa).
"Babu sallah idan abinci ya
halarto, haka kuma babu sallah alhalin bawa fitsari da bayan-gari sun matse shi).
"لَيَنْتَهِيَنَّ
أَقْوَامٌ يَرْفَعُونَ أَبْصَارَهُمْ إِلَى السَّمَاءِ فِي الصَّلاَةِ، أَوْ لَتُخْطَفَنَّ
أَبْصَارُهُمْ"([58]).
"Mutanen da su ke xaga ganinsu
can sama a cikin sallah, ko su hanu da aikata haka, ko kuma a kwafce ganin nasu".
"إِنَّ
اللَّهَ تعالى قَالَ: مَنْ عَادَى لِي وَلِيًّا فَقَدْ آذَنْتُهُ بِالْحَرْبِ، وَمَا
تَقَرَّبَ إِلَـيَّ عَـبْدِي بِشَـيْءٍ أَحَبَّ
إِلَيَّ مِمَّا افْتَرَضْتُ عَلَيْهِ، وَمَا يَزَالُ عَبْدِي يَـتَقَرَّبُ إِلَـيَّ
بِالنَّوَافِـلِ حَتَّى أُحِـبَّهُ" ([59]).
"Lallai Allah ta'alah ya ce:
Wanda ya yi adawa da masoyina –waliyyin Allah- to haqiqa ina masa shelar yaqi.
Bawana baya kusanta ta da wani abu da ya fi soyuwa a gare ni fiye da abin da na
farlanta akansa, kuma bawana ba zai gushe ba yana kusanta ta da nafilfili har
sai na so shi; …).
Hadisin Abu-hurairah -t-, daga Annabi (r), ya ce:
"إِنَّ
أَوَّلَ مَا يُحَاسَبُ بِهِ الْعَبْدُ الْـمُسْلِمُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ، الصَّـلاةُ
الْمَكْتُوبَةُ، فَإِنْ أَتَمَّهَا، وَإِلا قِيلَ: انْظُرُوا هَلْ لَهُ مِنْ تَـطَوُّعٍ
؟ فَـإِنْ كَانَ لَهُ تَطَـوُّعٌ أُكْـمِـلَـتِ الْفَـرِيـضَةُ مِنْ تَطَـوُّعِهِ ،
ثُمَّ يُفْعَلُ بِسَائِرِ الأَعْمَالِ الْمَفْرُوضَةِ مِثْلُ ذَلِكَ" ([60]).
"Lallai farkon abinda za a fara
hisabi wa bawa musulmi a ranar kiyama shi ne: sallah; idan ya cika ta to, Idan
kuma ba haka ba sai a ce: Ku duba shin bawana yana da ''taxawwu'i''? Idan ya
kasance yana da ''taxawwu'i'' sai a cikate farilla daga ''taxawwu'insa''.
Sa'annan sai a aikata kwatankwacin haka da sauran aiyuka na ''farilla'').
Abdullahi xan Umar -t-, cewa:
"حَفِظْتُ
عَنْ رَسُولِ اللَّهِ r رَكْعَتَيْنِ قَبْلَ الظُّهْرِ،
وَرَكْعَتَيْنِ بَعْدَ الظُّهْرِ، وَرَكْعَتَيْنِ بَعْدَ الْمَغْرِبِ، وَرَكْعَتَيْنِ
بَعْدَ الْعِشَاءِ، وَرَكْعَتَيْنِ قَبْلَ الْغَدَاة كَانَتْ سَاعَةً لا أدْخُلُ عَلَى
النَّبِيِّ r فِيهَا، فحَدَّثَتْنِي حَفْصَةُ
رضي الله عنها أَنَّهُ كَانَ إِذَا طَلَعَ الْفَجْرُ وأَذَّنَ الْمُؤَذِّنُ صَلَّى
رَكْعَتَيْن" ([61]).
"Na haddace daga Manzon Allah –r- cewa ya kan
yi raka'oi biyu kafin azahar, raka'oi biyu bayan azahar, da raka'oi biyu bayan
magrib, da raka'oi biyu bayan isha'i, da kuma raka'oi biyu kafin sallar asuba;
wannan lokacin lokaci ne da bana shiga wa annabi –r- a cikinsa;
Amma matarsa Hafsah -RA- ta ban labari cewa: idan alfijir ya keto, kana mai
kiran sallah ya yi kira; Annabi ya kan sallaci raka'a biyu".
"مَا
مِنْ عَبْدٍ مُسْلِمٍ يُصَلِّي لِلَّهِ تعالى كُلَّ يَوْمٍ ثِنْتَيْ عَشْرَةَ رَكْعَةً،
إِلا بَنَى اللهُ لَهُ بَيْتًا -أَوْ إِلا بُنِيَ لَهُ بَيْتٌ- فِي الْجَنَّةِ"([62]).
"Babu wani bawa musulmi da zai yi
sallah ga Allah ta'alah raka'oi goma sha biyu a cikin kowani yini; face Allah
ya gina masa gida –ko kuma an gina masa gida- a cikin aljanna).
A cikin hadisin Ummu-habibah –رضي
الله عنها-
wanda ambatonsa ya gabata:
"أَرْبَعًا
قَبْلَ الظُّهْرِ، وَرَكْعَتَيْنِ بَعْدَهَا، وَرَكْعَتَيْنِ بَعْدَ الْمَغْرِبِ،وَرَكْعَتَيْنِ
بَعْدَ العِشَاءِ،وَرَكْعَتَيْنِ قَبْلَ صَلاَةِ الْفَجْرِ" ([63]).
"raka'oi huxu kafin yin sallar
azahar, da raka'oi biyu bayan magriba, da raka'oi biyu bayan isha'i, da raka'oi
biyu kafin sallar asubah).
"Annabi -r- ya kasance ba
ya barin aiwatar da raka'oi huxu gabanin azahar).
''Raka'oi biyu da ake yi bayan fudowar
alfijir'' sun fi duniya da abinda ke cikinta alkhairi".
faxin A'ishah - رضي الله عنها-
dangane da waxannan rakao'in biyu:
Ma'ana: (Manzon Allah –r- a
rayuwarsa bai kasance yana barin aiwatar dasu ba har abada).
(Lallai Allah ''witri ne'' yana kuma son abu
''wutiri'').
(Ya
ku ma'abota alqur'ani ku yi witiri; saboda lallai
Allah ''witiri ne'' kuma yana son abu ''witiri'').
"إِنَّ
اللَّهَ أَمَدَّكُمْ بِصَلاَةٍ هِيَ خَيْرٌ لَكُمْ مِنْ حُمْرِ النَّعَمِ؛ صلاة الْوِتْرُ،
مَا بَيْنَ صلاة الْعِشَاءِ إِلَى طُلُوعِ الْفَجْرِ"([69]).
(Lallai Allah ya qarfafe
ku da wata sallah; wacce ta fi muku alkhairi fiye da jajayen raquma;
Ita ce sallar wutiri; tsakanin sallar ishah zuwa fudowar alfijir)
"صَلاةُ
اللَّيْلِ مَثْنَى مَثْنَى فَإِذَا خَشِيَ أَحَدُكُمُ الصُّبْحَ صَلَّى رَكْعَةً وَاحِدَةً
تُوتِرُ لَهُ مَا قَدْ صَلَّى"([70]).
: (Sallar dare raka'oi bibbiyu ce; Idan xayanku
ya ji tsoron asubah: sai ya sallaci raka'a guda xaya;
wacce za ta zame masa witiri ga abinda ya sallata).
Jabir -t- ya ruwaito,
lallai manzon Allah (r)
ya ce:
"مَنْ
خَافَ أَنْ لا يَقُومَ مِنْ آخِرِ اللَّيْلِ فَلْيُوتِرْ أَوَّلَهُ، وَمَنْ طَمِعَ
أَنْ يَقُومَ آخِرَهُ فَلْيُوتِرْ آخِرَ اللَّيْلِ، فَإِنَّ صَلاةَ آخِرِ اللَّيْلِ
مَشْهُودَةٌ، وَذَلِكَ أَفْضَلُ" ([71]).
"Duk wanda ya ji tsoron ba zai tashi
ba a qarshen dare to ya yi witirinsa a farkonsa, wanda kuma ya yi kwaxayin
zai tashi a qarshensa to ya yi witirinsa a qarshen
daren; saboda sallar qarshen dare mala'iku suna halartarta; wannan kuma shi ne ke da
fifiko).
: (Witiri raka'a xaya
ne a qarshen dare).
Hadisin Abdullahi xan
Umar -t- wanda ambatonsa ya gabata –a
kusa-:
: (.. Sai ya sallaci raka'a guda xaya;
wacce za ta zame masa witri ga dukkan abinda ya sallata).
Hadisin A'ishah - رضي الله عنها-,
cewa lallai Annabi (r)
ya kasance:
"يُصَلِّي
أَرْبَعًا، فَلاَ تَسْأَلْ عَنْ حُسْنِهِنَّ وَطُولِهِنَّ. ثُمَّ يُصَلِّي أَرْبَعًا،
فَلاَ تَسْأَلْ عَنْ حُسْنِهِنَّ وَطُولِهِنَّ. ثُمَّ يُصَلِّي ثَلاَثًا"([74]).
: (yana sallatar raka'oi huxu;
kada ka yi tambaya dangane da qyansu da tsawonsu,
sa'annan sai ya sallaci raka'oi guda huxu; kada ka
tambaya dangane da kyansu da tsawonsu, sa'annan sai ya sallaci raka'oi guda uku).
Abdullahi xan
Umar -t- ya kasance:
: (Ya kasance yana yin sallama bayan yin
raka'oi biyu; domin ya yi umurni kan wassu buqatunsa).
Hadisin
A'ishah - رضي الله عنها-,
ta ce:
: (Annabi -r- ya
kasance yana yin witiri da ''raka'oi guda uku'' baya zama sai a qarshensu).
Hadisin A'ishah - رضي الله عنها-, ta ce:
"كَانَ
رَسُولُ اللهِ r يُصَلِّي مِنَ اللَّيْلِ ثَلاثَ
عَشْرَةَ رَكْعَةً، يُوتِرُ مِنْ ذَلِكَ بِخَمْسٍ، لا يَجْلِسُ فِي شَيْءٍ إِلا فِي
آخِرِهَا"([77]).
Ma'ana: (Annabi -r- ya
kasance yana yin sallar dare; raka'oi goma sha uku; yana yin ''witiri'' da
raka'oi biyar; baya zama a cikin wani abu daga cikinsu sai a qarshensu).
"كَانَ
رَسُولُ اللَّهِ r يُوتِرُ بِسَبْعٍ أَوْ بِخَمْسٍ،
لا يَفْصِلُ بَيْنَهُنَّ بِتَسْلِيمٍ وَلا كَلام"([78]).
Ma'ana: (Annabi -r- ya
kasance yana yin ''witiri'' da raka'oi bakwai ko biyar, baya rabe tsakaninsu da
sallama ko da magana).
Ma'ana: (Babu sallah bayan
sallar asubah har sai rana ta fudo).
Faxin Manzon Allah ga Amru
xan
Abasah -t-:
"صَلِّ
صَلاةَ الصُّبْحِ، ثُمَّ أَقْصِرْ عَنِ الصَّلاةِ حَتَّى تَطْلُعَ الشَّمْسُ؛ حَتَّى
تَرْتَفِعَ"([80]).
: (Ka yi sallar asubah, sa'annan sai ka
kame ga barin yin sallah; har rana ta fudo; kuma har ta xaukaka…).
Hadisin Uqbah xan
Aamir -t-:
"ثَلاثُ
سَاعَاتٍ كَانَ رَسُولُ اللهِ r يَنْهَانَا أَنْ نُصَلِّيَ
فِيهِنَّ، أَوْ أَنْ نَقْبُرَ فِيهِنَّ مَوْتَانَا: حِينَ تَطْلُعُ الشَّمْسُ بَازِغَةً
حَتَّى تَرْتَفِعَ، وَحِينَ يَقُومُ قَائِمُ الظَّهِيرَةِ حَتَّى تَزولَ الشَّمْسُ،
وَحِينَ تَتضَيَّفُ لِلْغُرُوبِ حَتَّى تَغْرُب"([81]).
: (Lokuta guda uku Manzon Allah –r- ya
kasance yana hana mu mu riqa yin sallah a cikinsu, ko kuma mu bunne mamatanmu a cikinsu:
lokacin da rana ta ke fudowa har sai ta xaukaka,
da kuma lokacin da rana ta ke takewa har sai ta yi zawali, da kuma lokacin da
ta karkata don faxuwa; har sai ta faxin).
"لا
صَلاةَ بَعْدَ الْفَجْرِ حَتَّى تَطْلُعَ الشَّمْس، ولا صَلاةَ بَعْدَ الْعَصْرِ حَتَّى تَغيبَ الشَّمْسُ"([82]).
: (Babu sallah bayan sallar asuba har sai
rana ta fudo, kuma babu sallah bayan sallar la'asar har sai rana ta fake).
Hadisin Amru xan
Abasah -t-:
"فَإِنَّهَا
–أي: الشمس- تَطْلُعُ حِينَ تَطْلُعُ بَيْنَ قَرْنَيْ شَيْطَانٍ، وَحِينَئِذٍ يَسْجُدُ
لَهَا الْكُفَّارُ، ... فَإِنَّهَا تَغْرُبُ بَيْنَ قَرْنَيْ شَيْطَانٍ، وَحِينَئِذٍ
يَسْجُدُ لَهَا الْكُفَّارُ"([83]).
: (Lallai rana ta kan fito lokacin
fitowarta tsakanin kafon Shexan guda biyu, a lokacin ne kuma kafirai suke yi mata sujjada …
Kuma lallai rana tana faduwa lokacin da ta ke faduwa a tsakanin kaho biyu na Shexan;
a wannan lokacin ne kafirai kuma suke yi mata sujjada).
"يَا
بَنِي عَبْدِ مَنَافٍ لاَ تَمْنَعُوا أَحَدًا طَافَ بِهَذَا الْبَيْتِ وَصَلَّى فيه
أَيَّة سَاعَةٍ شاء؛ مِنْ لَيْلٍ أَوْ نَهَار"([84]).
Ma'ana: (Ya
''baniy-abdi-manaf'' ka da ku hana wani mutum da ya yi xawafin
wannan xakin: ya yi sallah a kowani lokaci ya so; da dare ne ko da rana).
Ma'ana: (Duk wanda ya yi
barci bai yi wata sallah ba, ko ya manta ta: to ya sallace ta idan ya tunata).
"Sallar jam'i ta fi falala akan sallar
mutum shi kaxai, da daraja ashirin da bakwai).
"صَلاَةُ
الرَّجُلِ فِي الْجَمَاعَةِ تُضَعَّفُ عَلَى صَلاَتِهِ فِي بَـيْتِهِ وَفِي سُوقِهِ
خَمْسًا وَعِشْرِينَ ضِـعْفًا؛ وَذَلِكَ أَنَّهُ إِذَا تَـوَضَّأَ فَأَحْسَنَ الْـوُضُوءَ،
ثُمَّ خَرَجَ إِلَى الْـمَسْجِدِ لاَ يُـخْرِجُهُ إِلاَّ الـصَّـلاَةُ: لَمْ يَخْطُ
خَطْوَةً إِلاَّ رُفِعَتْ لَهُ بِهَا دَرَجَةٌ، وَحُطَّ عَنْهُ بِهَا خَطِيئَةٌ، فَإِذَا
صَلَّى لَمْ تَزَلِ الْـمَلاَئِكَـةُ تُصَلِّي عَلَيْهِ مَا دَامَ فِي مُصَلاَّه"([87]).
Ma'ana: (Sallar mutum a cikin
jama'a ana nin-ninkata a kan sallarsa a gidansa, da kuma a wajen kasuwancinsa:
ninki ashirin da biyar; saboda idan bawa ya yi alwala, ya kuma kyautata
alwalar, kana ya fita i zuwa masallaci; ba abinda ya fitar da shi sai sallar:
ba zai taka wani taku ba; face an xaga darajarsa
da ita, a kuma kankare masa kura-kurensa da ita, Idan kuma ya yi sallah: to
mala'iku ba za su gushe ba suna yi masa addu'a, matuqar
bai gushe ba a wurin sallarsa… -har qarshen
hadisin).
Abu-hurairah -t-, ya ce, Annabi (r) ya ce:
"أَثْقَلَ
الصَّلاةِ عَلَى الْـمُنَافِقِينَ صَلاةُ الْعِشَاءِ وَصَلاةُ الْفَجْرِ ، وَلَوْ يَعْلَمُونَ
مَا فِيهِمَا لأَتَـوْهُـمَا وَلَوْ حَبْوًا، ولَقَدْ هَمَمْتُ أَنْ آمُرَ بِالصَّلاةِ
فَـتُقَامَ، ثُمَّ آمُرَ رَجُلا يُصَلِّي بِالـنَّاسِ، ثُمَّ أَنْـطَـلِقَ مَعِي بِرِجَالٍ
مَعَهُمْ حُزُمُ من حَطَب إِلَى قَوْمٍ لا يشهدون الصَّلاة، فَأُحَرِّقَ عَلَيْهِمْ
بُيُوتَهُمْ بِالنَّار"([88]).
"Sallar da ta fi nauyi
akan munafikai sune sallar ishah da sallar asubah, da matune sun san abinda ke
cikinsu na lada da sun zo musu koda kuwa da ja-gindi ne, kuma haqiqa
na yi niyyar na yi umurni a tsayar da sallah, kana kuma na umurci wani ya
jagoranci mutane sallah, sa'annan na tafi –tare da wassu mazaje, a tare da su
akwai dami-damin itace- zuwa ga mutanen da basa halartar sallar jam'i; don na qona
gidajensu suna ciki da wuta".
"Shin kana jin kiran sallah? Sai ya
ce: E! Sai ya ce: to ka amsa!).
Da kuma faxinsa
(r):
"Duk wanda ya ji kiran sallah sai kuma
bai amsa ba, to ba shi da sallah; sai dai in yana da uzuri). Da kuma faxin
Abdullahi xan Mas'ud -t-:
"Kuma hakika na ganmu –yana nufin:
a zamanin sahabbai-; babu wanda ke qin halartarta –sallar jam'i a cikin jama'a-
sai munafiqi wanda aka san shi da munafurci".
"Kuma dakunansu shi ya fiye musu
alkhairi).
hadisin Abu-zarrin -t-, ya ce: Manzon
Allah (r)
ya ce:
"كَيْفَ
أَنْتَ إِذَا كَانَ عَلَيْكَ أُمَرَاءُ يُؤَخِّرُونَ الصَّلاةَ عَنْ وَقْتِهَا؟ أَوْ
يُمِيتُونَ الصَّلاةَ عَنْ وَقْتِهَا؟ قُلْتُ: فَمَا تَأْمُرُنِي؟ قَالَ: صَلِّ الصَّلاةَ
لِوَقْتِهَا، فَإِنْ أَدْرَكْتَهَا مَعَهُمْ، فَصَلِّ، فَإِنَّهَا لَكَ نَافِلَة"([93]).
"Yaya za ka yi idan ka kai
lokacin da shugabanni ke jinkirta sallah daga lokacinta? Ko kuma su ke kashe ta
-ma'ana: jinkirtata- daga lokacinta? Sai na ce: da me ka ke umurtata? Sai ya
ce: Ka yi sallah a lokacinta, idan kuma ka riske ta tare da su to sai ka sake
sallatarta; saboda za ta zame maka nafila".
"إِذَا
صَلَّيْتُمَا فِي رِحَالِكُمَا، ثُمَّ أَتَيْتُمَا مَسْجِدَ جَمَاعَةٍ، فَصَلِّيَا
مَعَهُمْ، فَإِنَّهُمَا لَكُمَا نَافِلَة"([94]).
"Idan har ku ka yi sallah a
masauqinku, sa'annan sai ku ka zo masallacin jama'a: to sai ku yi sallah tare
da su; za ta zame mu ku nafila".
Malik xan
Alhuwairis -t-:
"Idan sallah ta halarto, to sai
ku yi ''kiran-sallah" sa'annan ku yi ''iqama'', sai kuma babbanku a
shekaru ya limance ku".
adisin Abu-hurairah -t-:
"إِذَا
جِئْتُمْ إِلَى الصَّلاةِ وَنَحْنُ سُجُودٌ فَاسْجُدُوا، وَلا تَعُدُّوهَا شَيْئًا،
وَمَنْ أَدْرَكَ الرَّكْعَةَ فَقَدْ أَدْرَكَ الصَّلاة"([96]).
"Idan ku ka zo izuwa ga sallah
alhalin muna cikin sujjada; to sai ku yi sujjada, kuma kada ku kirga wannan a
wani abu, amma duk wanda ya riski raka'a to ya riski sallah".
Hadisin A'ishah - رضي الله عنها-:
"Babu sallah idan abinci ya
halarto, kuma babu sallah alhalin bawa fishari da bayan-gari sun matse shi".
Hadisin Abdullahi xan
Abbas -t-, daga Annabi (r), ya ce:
"مَنْ
سَمِعَ الْمُنَادِيَ فَلَمْ يَمْنَعْهُ مِنَ اتِّبَاعِهِ عُذْرٌ -قَالُوا: وَمَا الْـعُذْرُ؟
قَالَ: خَـوْفٌ أَوْ مَرَضٌ-: لَمْ تُقْبَلْ مِنْهُ الصَّلاةُ الَّتِي صَلَّى"([98]).
"Wanda ya ji mai kiran sallah,
sai kuma wani uzuri bai hana shi zuwa jam'i ba, -Sai sahabbai su ka ce: menene
uzurin? Sai ya ce: tsoro ko rashin lafiya-: To ba za a karva masa sallar da ya
sallata ba".
Hadisin Abdullahi xan
Umar -t-, ya ce:
"كَانَ
رَسُول r
يَأْمُرُ المُؤَذِّنَ إِذَا كَانَتْ لَيْلَةٌ ذَاتُ بَرْدٍ وَمَطَرٍ،
يَقُولُ: أَلاَ صَلُّوا فِي الرِّحَال"([99]).
(Manzon Allah –r-
ya kasance yana umurtar mai kiran sallah, a dare mai sanyi wacce aka yi ruwa,
ya ce: Ku yi sallah a masauqanku).
"Sallar mutum da wani mutum ya fiye
masa tsarki fiye da sallarsa shi kaxai…).
"Wanene zai yi sadaka ga wannan;
sai ya tashi ya yi sallah tare da shi. Sai wani daga cikin mutanen ya tashi,
sai ya yi sallah tare da wannan mutumin".
"Idan aka tsayar da sallah to
babu wata sallah sai ta farilla".
Ma'ana: (Shin kana yin sallar
asuba ne raka'oi huxu?!).
"يَؤُمُّ
الْقَوْمَ أَقْرَؤُهُمْ لِكِتَابِ اللهِ، فَإِنْ كَانُوا فِي الْقِرَاءَةِ سَوَاءً،
فَأَعْلَمُهُمْ بِالسُّنَّةِ، فَإِنْ كَانُوا فِي السُّنَّةِ سَوَاءً، فَأَقْدَمُهُمْ
هِجْرَةً، فَإِنْ كَانُوا فِي الْهِجْرَةِ سَوَاءً، فَأَقْدَمُهُمْ سِلْمًا"([104]).
Zai limanci mutane a cikin
sallah: Mutumin da ya fi su iya karatun alqur'ani,
in har su ka zama daidai wajen karatun; to sai wanda ya fi su sanin sunna
–hadisai-; in har kuma sun zama daidai wajen sanin sunna; to sai wanda ya riga
su yin hijira; idan kuma tare suka yi hijira; to wanda ya riga su shiga
Musulunci).
"Kada mutum ya limanci mutum a cikin
iyalensa, da kuma wurin da ke da iko akai –mulki-".
"Mutanen da suka jibintar da lamarinsu
ga mace ba za su tava samun tsira ba).
"ثَلاثَةٌ
لا تُرْفَعُ صَلاتُهُمْ فَوْقَ رُءُوسِهِمْ شِبْرًا: رَجُلٌ أَمَّ قَوْمًا وَهُمْ لَهُ
كَارِهُونَ"([107]).
"Sinfin mutane guda uku, ba a xaga
sallarsu a saman kayukankusu daidai da taqi xaya;
1- Mutumin da ya limanci mutane alhalin su suna qinsa
…-har qarshen hadisin-).
"أنَّ
جابرًا وجبَّارًا رضي الله عنهما وقفا؛ أحدهما عن يمينه r،
والآخر عن يساره، فأخذ بأيديهما حَتَّى أَقَامَهما خَلْفَه"([108]).
"Lallai ''Jabir da Jabbar –RA- sun
tsaya; xaya daga cikinsu ta dama da Manzon Allah –r-, xayan
kuma ta hagu da shi, Sai Annabi r
ya kama hannayensu, har ya tsayar da su a bayansa).
Faxin
Anas xan Malik -t- a yayin da Annabi (r) ya yi
sallah da su a cikin gidansu:
"…Sa'annan sai Manzon Allah –r- ya yi
limanci; sai mu kuma muka tsaya a bayansa, ya yi mana sallah).
Hadisin Anas xan
Malik -t-, ya ce:
Ma'ana: (Na yi sahu ni da
maraya a bayansa –r-,
Sai kuma tsohuwa ta tsaya a bayanmu).
"إِنَّمَا
جُعِلَ الإِمَامُ لِيُؤْتَمَّ بِهِ، فَإِذَا كَبَّرَ فَكَبِّرُوا، وَإِذَا رَكَعَ فَارْكَعُوا،
وَإِذَا قَالَ: سَمِعَ اللَّهُ لِمَنْ حَمِدَهُ، فَقُولُوا: رَبَّنَا لَكَ الحَمْدُ،
وَإِذَا سَجَدَ فَاسْجُدُوا"([111]).
"Lallai an sanya liman ne don ayi koyi
da shi; idan ya yi kabbara to sai ku yi kabbara, idan ya yi ruku'i kuma ku yi
ruku'i, idan ya ce: ''sami'a Allahu liman hamidahu'' sai ku ce: ''rabbana
walaka alhamdu, idan ya yi sujjada sai ku yi sujjada).
"Kada ku rigaye ni da ruku'i, ko kuma
da sujjada, ko wajen tashi).
Abu-hurairah -t-, daga Annabi (r):
"أَمَا
يَخْشَى الذي يَرفَع رَأْسَهُ قَبْلَ الإِمَامِ أَنْ يُحوِّل اللَّهُ رَأْسَهُ رَأْسَ
حِمَارٍ؟"([113]).
Ma'ana: (Shin wanda ke xaga kansa
kafin xagowar liman ba zai ji tsoron cewa Allah zai rikixar da kansa i
zuwa kan jaki ba?).
"لِيَلِنِي
مِنْكُمْ أُولُو الأَحْلامِ وَالنُّهَى ثُمَّ الَّذِينَ يَلُونَهُمْ، ثُمَّ الَّذِينَ
يَلُونَهُم"([114]).
"Ma'abota kaifin hankali su zama a
bayana, Sai waxanda ke biye da su, sai waxanda
ke biye da su).
"تَقَدَّمُوا
فَأْتَمُّوا بِي، وَلْيَأْتَمَّ بِكُمْ مَنْ بَعْدَكُمْ، لا يَزَالُ قَـوْمٌ يَـتَأَخَّرُونَ
حَتَّى يُـؤَخِّرَهُمُ الله"([115]).
"Ku gabato ku yi koyi da ni, su kuma waxanda
suke bayanku suyi koyi da ku. Wassu mutane ba za su gushe ba suna yin baya-baya
har sai Allah ya mayar da su baya).
"لَوْ
يَعْلَمُ النَّاسُ مَا فِي النِّدَاءِ وَالصَّفِّ الأَوَّلِ، ثُمَّ لَمْ يَجِدُوا إِلا
أَنْ يَـسْتَهِمُوا عَلَيْهِ لاسْتَهَمُوا"([116]).
"Da mutane sun san abinda ke
cikin ''kiran sallah'', da sahun farko –na lada-, sa'annan basu samu damar
aiwatar da su ba sai ta hanyar quri'a to da sun yi quri'ar).
"خَيْرُ
صُفُوفِ الرِّجَالِ أَوَّلُهَا، وَشَرُّهَا آخِرُهَا، وَخَيْرُ صُفُوفِ الـنِّسَاءِ
آخِرُهَا، وَشَرُّهَا أَوَّلُهَا"([117]).
"Mafi alherin sahun maza na
farkonsu, mafi sharrinsu kuma na qarshensu, Mafi alherin sahun mata kuma shine na
qarshensu, mafi sharrinsu kuma na farkonsu".
"Ku daidaita sahunku; saboda
daidaita sahu na daga "cikar sallah").
Daga Anas xan
Malik -t-, lallai ya ce: An yi ''iqamah'',
sai Annabi (r)
ya fiskance mu da fiskarsa, kana ya ce:
"Ku daidaita sahu kuma ku manne da juna; saboda lallai ina
ganinku ta bayan bayana).
Anas -t- ya ce:
"Xayanmu ya
kasance yana manna kafaxarsa da kafaxar
sahibinsa, da kuma qafarsa da qafarsa).
"أَلا
تَصُفُّونَ كَمَا تَصُفُّ الْمَلائِكَةُ عِنْدَ رَبِّهَا؟ فَقُلْنَا يَا رَسُولَ اللهِ،
وَكَـيْفَ تَـصُفُّ الْـمَلائِكَةُ عِنْدَ رَبِّهَا؟ قَالَ: يُتِمُّونَ الصُّفُوفَ
الأُوَلَ وَيَتَرَاصُّونَ فِي الصَّفِّ"([121]).
"Shin baza ku yi sahu kamar yadda
mala'iku suke sahu a wajen Ubangijinsu ba? Sai mu ka ce: Ya ma'aikin Allah!
yaya mala'iku suke sahu a wajen Ubangijinsu? Sai ya ce: su kan cika sahu na
farko-farko, su kuma manne da juna a cikin sahu".
"Babu sallah ga mutum guda a bayan
sahu).
"Ka yi sallah a tsaye, idan ba za ka
iya ba; ka yi a zaune, idan kuma ba za ka iya to ka yi akan kuivi).
aga Abdullahi xan
Umar -t- ya ce:
"إِنِّي
صَـحِـبْتُ رَسُولَ اللهِ r فِي الـسَّفَرِ، فَـلَمْ يَـزِدْ
عَلَى رَكْعَتَيْنِ حَتَّى قَـبَضَـهُ اللهُ، وَصَحِبْتُ أَبَا بَكْرٍ، فَلَمْ يَزِدْ
عَلَى رَكْعَتَيْنِ حَتَّى قَبَضَهُ الله ..."([124]).
Ma'ana: (Na aboci Manzon
Allah –r-
a hali na tafiya, bai kasance yana qari akan
raka'oi biyu ba, har Allah ta'alah ya karvi
rayuwarsa. Na kuma aboci Abubakar –t-
shima bai kasance yana yin qari akan raka'oi
biyu ba a hali na tafiya, har Allah ya karvi
rayuwarsa…).
faxin Abdullahi xan
Abbas -t- yace:
"فَرَضَ
اللهُ الصَّلاةَ عَلَى لِسَانِ نَبِيِّكُمْ r
فِي الْحَضَرِ أَرْبَعًا، وَفِي السَّفَرِ رَكْعَتَيْن"([125]).
Ma'ana: (Allah ya wajabta
sallah, a ta harshen annabinku raka'oi huxu a halin
zaman gida, a yanayi na tafiya kuma raka'oi biyu …).
Ma'ana: (Duk wanda ya yi
barci bai yi wata sallah ba, ko ya manta ta: to ya sallace ta idan ya tunata).
hadisin Mu'azu -t- cewa lallai:
"أَنَّ
النَّبِيَّ r كَانَ فِي غَـزْوَةِ تَـبُوكَ
إِذَا ارْتَـحَلَ قَـبْلَ زَيْغِ الـشَّمْسِ أَخَّـرَ الظُّهْرَ حَتَّى يَجْمَعَهَا
إِلَى الْعَصْرِ يُصَلِّيهِمَا جَمِيعًا، وَإِذَا ارْتَـحَلَ بَعْدَ زَيْغِ الـشَّمْسِ
صَـلَّى الـظُّهْرَ وَالْـعَصْرَ جَـمِيعًا، ثُمَّ سَارَ وَكَانَ يَفْعَلُ مِثْلَ ذَلِكَ
فِي الْمَغْرِبِ وَالْعِشَاء" ([127]).
Ma'ana: (Lallai Annabi –r- ya
kasance a yaqin tabuka idan zai tafi kafin rana ta
karkata to sai ya jinkirta azahar don ya haxe ta da
sallar la'asar sai ya sallace su gabaxaya,
idan kuma zai tafi bayan rana ta gota ne to sai ya sallaci azahar da la'asar a
tare, sa'annan ya tafi. Kuma ya kasance yana aikata kwatankwacin haka a sallar
magrib da isha'i).
"جَمَعَ
رَسُولُ اللَّهِ r بَيْنَ الظُّهْرِ وَالْعَصْرِ،
وَالْمَغْرِبِ وَالْعِشَاءِ بِالْمَدِينَةِ مِنْ غَيْرِ خَوْفٍ، وَلا مَطَر".
Ma'ana: (Manzon Allah –r- ya haxe
sallolin azahar da la'asar, da kuma magrib da isha'i, a garin madina ba tare da
wani tsoro –yaqi- ko ruwan sama ba). A wata riwaya:
(Ba tare da wani tsoro ba, ko kuma tafiya).
Abdullahi xan
Abbas cewa me yasa ne manzon Allah (r)
ya haxe
sallolin? Sai yace:
"أَرَادَ أَنْ لا يُحْرِجَ
أُمَّتَه".
(ya haxe sallar ne
saboda kar ya sa al'ummarsa cikin qunci);
"Tafiya sallar juma'a wajibi ne akan
kowani baligi). Da kuma saboda faxinsa (r):
"لَيَنْتَهِيَنَّ
أَقْوَامٌ عَنْ وَدْعِهِمُ الْجُمُعَاتِ، أَوْ لَيَخْتِمَنَّ اللهُ عَلَى قُـلُوبِهِمْ،
ثُمَّ لَـيُكوننَّ مِنَ الـغَـافِلِين"([130]).
Wassu mutane su hanu kan
barin halartar juma'o'i, ko kuma Allah ya yi rufi akan zukatansu, sa'annan su
kasance daga cikin rafkanannu).
"الْجُمُعَةُ
حَقٌّ وَاجِبٌ عَلَى كُلِّ مُسْلِم فِي جَمَاعَةٍ إِلا أَرْبَعَةً: عَبْدٌ مَمْلُوكٌ،
أَوِ امْرَأَةٌ، أَوْ صَبِيٌّ، أَوْ مَرِيضٌ"([131]).
"Juma'a" haqqi
ne na wajibi akan kowani musulmi, ya yi ta a cikin jama'a, sai mutum huxu:
Bawa da ake mulkarsa, ko mace, ko yaro, ko maras lafiya).
Duk wanda ya riski raka'a xaya
daga sallah to haqiqa ya riski wannan sallar).
"إِذَا
خَطَبَ يَوْمَ الْجُمُعَةِ دَعَا فَأَشَارَ بِأُصْبُعِهِ وَأَمَّنَ النَّاسُ".
"Idan yana huxuba
sai ya yi addu'a, yana mai ishara da yatsarsa, mutane kuma suna cewa: aamin!).
Jabir xan
Samurah -t- ya ce:
"كَانَ
رَسُول اللَّهِ r يَخْطُبُ قَائِمًا، ثُمَّ يَجْلِسُ،
ثُمَّ يَقُومُ فَيَخْطُبُ قَائِمًا، فَمَنْ حَدَّثَكَ أَنَّهُ كَانَ يَخْطُبُ جَالِسًا
فَقَدْ كَذَب"([133]).
"Manzon Allah –r- ya
kasance yana yin huxuba a tsaye, sa'annan ya zauna, sa'annan ya tashi ya tsaya ya
sake huxuba, Duk wanda ya baka labarin cewa yana yin huxubarsa
ne a zaune to lallai ya yi qarya).
faxin Abdullahi xan
Umar -t-
"كَانَ
النَّبِيُّ r يَخْطُبُ الْخُطْبَتَيْنِ وَهُوَ
قَائِمٌ، وَكَانَ يَفْصِلُ بَيْنَهُمَا بِجُلُوسٍ"([134]).
"Annabi –r- ya
kasance yana yin huxuba guda biyu alhalin yana tsaye, ya kan kuma rabe tsakaninsu da
zama).
"إِنَّ
طُولَ صَلاةِ الرَّجُلِ، وَقِصَرَ خُطْبَتِهِ مَئِنَّةٌ مِنْ فِقْهِه، فَأَطِيلُوا
الصَّلاةَ، وَأَقْصِرُوا الْخُطْبَة"([135]).
Ma'ana: (Lallai tsawon sallar
mutum, da gajercin huxubarsa alama ce da take nuna zurfin
fahimtarsa; don haka ku tsawita sallah, kuma ku gajerta huxuba).
"مَنْ
تَكَلَّمَ يَوْمَ الْجُمُعَةِ وَالإِمَامُ يَخْطُبُ، فَهُوَ كَالْحِمَارِ يَحْمِلُ
أَسْفَارًا"([136]).
"Duk wanda ya yi magana a ranar juma'a
alhalin limami yana huxuba to kamar jaki ne da ke xauke
da laftun littatafa).
"Idan kace wa sahibinka: Yi shiru,
alhalin liman yana huxuba to lallai ka yi wargi).
"مَنِ
اغْتَسَلَ يَوْمَ الْجُمُعَةِ ... ثُمَّ رَاح فَلَمْ يُفَرِّقْ بَيْنَ اثْنَيْنِ فَصَلَّى
مَا كُتبَ اللَّهُ لَه... غُفِرَ لَهُ مَا بَيْنَهُ وَبَيْنَ الْجُمُعَةِ الأُخْرَى"([138]).
"Wanda ya yi wanka a ranar juma'a, …
sa'annan ya tafi salla, bai rabe tsakanin mutane biyu ba, ya kuma sallaci
abinda aka qaddara masa… an gafarta masa abinda ke tsakaninsa da juma'a ta
gaba).
"Duk wanda ya riski raka'a guda daga
juma'a to haqiqa ya riski wannan sallar).
"Ya kasance yana sallatar raka'oi biyu
bayan ya yi juma'a), An samu kuma cewa
Annabi (r)
ya ce:
"Idan Xayanku
ya sallaci juma'a to ya sallaci raka'oi huxu a
bayanta), a wata riwayah kuma:
"Duk wanda zai yi sallah daga cikinku
bayan juma'a to ya sallaci raka'oi huxu).
"مَنِ
اغْتَسَلَ يَوْمَ الجُمُعَةِ غُسْلَ الجَنَابَةِ ثُمَّ رَاحَ فَكَأَنَّمَا قَرَّبَ
بَـدَنَةً، وَمَـنْ رَاحَ فِي الـسَّاعَةِ الثَّانِيَةِ فَكَأَنَّمَا قَرَّبَ بَـقَرَةً،
وَمَنْ رَاحَ فِي السَّاعَةِ الثَّالِثَةِ فَـكَأَنَّمَا قَرَّبَ كَبْشًا أَقْـرَنَ،
وَمَنْ رَاحَ فِي السَّاعَةِ الرَّابِعَةِ فَكَأَنَّمَا قَرَّبَ دَجَاجَـةً، وَمَنْ
رَاحَ فِي الـسَّاعَةِ الخـَامِسَةِ فَكَأَنَّـمَا قَرَّبَ بَيْضَةً، فَإِذَا خَرَجَ
الإِمَامُ حَـضَرَتِ الـمَلاَئِكَةُ يَـسْتَمِعُونَ الـذِّكْر"([143]).
"Duk wanda ya yi wanka a ranar juma'a
wanka irin ta janaba; sannan ya tafi zuwa masallaci –a farkon lokaci- to kamar
ya bada sadakar raqumi ne, Wanda kuma ya je a lokaci na biyu to kamar ya yi sadaka
da saniya ne, Wanda ya tafi a lokaci na uku kamar ya bada sadakar rago mai qaho
ne, Wanda ya tafi a lokaci na huxu to kamar ya bada
sadakar kaza ne, Wanda kuma ya tafi a lokaci na biyar to kamar ya bada sadakar
kwai ne. Idan liman ya fito sai Mala'iku su halarto suna sauraron huxuba).
Da kuma saboda faxinsa:
"مَنْ
اغْتَسَلَ يَوْمَ الجُمُعَةِ وَغَـسَّلَ، وَبَـكَّرَ وَابْـتَكَرَ، وَدَنَا وَاسْتَمَعَ
وَأَنْصَتَ، كَانَ لَهُ بِكُلِّ خُطْوَةٍ
"Duk wanda ya yi wanka a ranar
juma'a, ya zama sababin wanka, ya yi sammako zuwa masallaci, ya kusanci liman
ya kuma yi sauraro ga huxuba, to duk
wani taku da yayi yana da ladan shekara; ladan azumtarta da tsayuwan dararen
cikinta".
([24]) Abu-dawud ya ruwaito shi (627), da
At-tirmiziy (375), da kuma
Ibnu-majah (655), Albaniy kuma ya
inganta shi a 'Irwa'ul galil" (lamba: 196).
ABINDA
AKE NUFI DA ''MAI HAILAH'' A CIKIN HADISIN SHINE: WACCE TA
KAI SHEKARUN BALAGA.
([42]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba:
789) da Muslim (lamba: 411).
([76]) An-nasa'iy ya ruwaito shi (lamba: 1698, 3/234), da Alhakim (1/304), da
Albaihakiy (3/28, kuma lafazin nasa ne), Alhakim ya inganta shi, ya ce yana kan
sharaxin Bukhari da
Muslim, kuma Az-zahabiy ya masa "muwafaqa", An-nawawiy ya ce: An-nasa'iy ya ruwaito shi da
sanadi mai kyau, da Albaihaqiy da sanadi ingantacce (''Almajmu'u'', 4/17-18).
"مَنْ سَمِعَ النِّدَاءَ فَلَمْ يُجِبْ، فَلا
صَلاةَ لَهُ إِلا مِنْ عُذْر".
Ma'ana:
(Duk wanda ya ji kiran sallah sai bai amsa ba, to bashi da sallah sai dai in
yana da uzuri (Irwa'u algali, 2/ 336-337).
No comments:
Post a Comment