ZIKIRIN SAFIYA DA MARAICE([1])
(1)
An karbo
daga Abu-hurairah (ra) daga annabi (saw) ya ce: "Duk wanda ya fada –a
lokacin day a wayi gari, da lokacin da ya yi yammaci-: SUBHANAL LAHI WABI
HAMDIHI sau dari, Wani mutum a ranar kiyamah ba zai zo da fiye da abin da
wannan ya zo da shi ba Sai dai mutumin da ya fadi kamar yadda ya fada, ko ya yi
kari akan nasa"([2]), Muslim ya rawaito shi.
(2)
An karbo
daga Ibnu-mas'ud (ra) ya ce: Annabin Allah (saw) ya kasance idan ya yi
yammaci ya kan ce:
«أَمْسَيْنَا وَأَمْسَى الْمُلْكُ
لِلَّهِ، وَالْحَمْدُ لِلَّهِ، لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ
لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ، وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُـــــوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ،
رَبِّ أَسْأَلُكَ خَيْرَ مَا فِي هَذِهِ اللَّيْلَةِ وَخَيْرَ مَا بَعْدَهَا،
وَأَعُـــــوذُ بِكَ مِنْ شَــــــــــــرِّ مَا فِي هَذِهِ اللَّيْلَةِ وَشَرِّ
مَا بَعْدَهَا، رَبِّ أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْكَسَلِ وَسُوءِ الْكِبَرِ، رَبِّ
أَعُوذُ بِكَ مِنْ عَذَابٍ فِي النَّارِ وَعَذَابٍ فِي الْقَبْرِ».
Ma'ana: "Mun yi yammaci,
kuma mulki shima ya yi yammaci mallakin Allah, kuma yabo ma na Allah ne, babu
wanda ya cancanci bauta sai Allah, shi kadai ya ke bashi da abokan tarayya,
mulki nasa ne, yabo nasa ne, kuma lallai shi mai iko ne akan komai, Ubangijina
ina rokonka alherin wannan dare da alherin abin da ke bayansa, kuma ina neman
ka da tsare ni daga sharrin wannan dare da sharrin wadanda su ke bayansa,
Ubangijina ina neman tsarinka daga kasala, da mummunan tsufa, Ubangijina ina
neman tsarinka daga azaba a cikin wuta, da azaba a cikin kabari".
In kuma ya wayi gari sai ya fadi hakan, yana mai canza
lafazin:
«أَصْبَحْنَا وَأَصْبَحَ
الْمُلْكُ لِلَّهِ».
Ma'ana: "Mun wayi gari,
kuma mulki shima ya wayi gari mallakin Allah"([3]), Muslim ne ya rawaito shi.
(3)
An karbo
daga Shaddad bn Aus (ra) daga annabi (saw): "Jagora cikin dangogin
laffuzan neman gafara (istigfari) da nau'ukansa, shi ne, ka ce:
«اللَّهُمَّ أَنْتَ رَبِّي لاَ
إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ، خَلَقْتَنِي وَأَنَا عَبْدُكَ، وَأَنَا عَلَى عَهْدِكَ
وَوَعْدِكَ مَا اسْــتَـطَعْتُ، أَعُـــــــوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا صَنَعْتُ،
أَبُوءُ لَكَ بِنِعْمَتِكَ عَلَيَّ، وَأَبُوءُ بِذَنْبِي؛ اغْفِرْ لِي فَإِنَّهُ
لاَ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلاَّ أَنْتَ».
Ma'ana: "Ya Allah kai ne
ubangijina babu abun bauta da gaskiya sai kai, kai ne ka halicce ni, ni kuma
bawanka ne, kuma ina kan alkawarinka gwargwadon ikona, Ina neman tsarinka daga
sharrin abun da na aikata, ina tabbatar maka da ni'imominka a kaina, ina kuma
mai tabbatar da zunubaina; ka gafarta min; lallai babu mai gafarta zunubai in
ba kai ba". Annabi (saw) ya ce:
«وَمَنْ قَالَهَا مِنَ النَّهَارِ مُوقِنًا بِهَا
فَمَاتَ مِنْ يَوْمِهِ قَبْلَ أَنْ يُمْسِيَ فَهُوَ مِنْ أَهْلِ الْجَنَّةِ،
وَمَنْ قَالَهَا مِنَ اللَّيْلِ وَهْوَ مُوقِنٌ بِهَا فَمَاتَ قَبْلَ أَنْ
يُصْبِحَ فَهْوَ مِنْ أَهْلِ الْجَنَّةِ».
Ma'ana: "Duk wanda ya
karanta zikirin nan da rana yana mai samun yakini da shi sai ya mutu a cikin
yininsa gabanin ya yi yammaci to lallai yana daga cikin yan aljannah, wanda
kuma ya fade shi a cikin dare alhalin yana da yakini da shi sai ya mutu gabanin
ya wayi gari to lallai shi dan aljannah ne"([4]). Bukhariy ya rawaito shi.
(4)
An karbo
daga Abdullahi bn Habib (ra) daga babansa, lallai shi ya ce: "Mun fita a
cikin wani dare da ruwa ke sauka, tare da duhu mai tsanani muna neman annabi
(saw) domin ya mana sallah, sai mu ka riske shi, Sai ya ce: Shin kun yi sallah?
sai ban ce komai ba, sai ya ce: ka ce? Sai bance komai ba, sai ya ce: ka ce?
Sai ban ce komai ba, sai ya ce: ka ce? Sai ban ce komai ba, Sai na ce ya manzon
Allah me zan ce? Sai ya ce:
«قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ وَالْمُعَوِّذَتَيْنِ
حِينَ تُمْسِي، وَحِينَ تُصْبِحُ، ثَلَاثَ مَرَّاتٍ تَكْفِيكَ مِنْ كُلِّ شَيْءٍ».
'KUL HUWALLAHU
AHAD, DA FALAKI, DA NASI' ka karaanta su lokacin da ka
yi yammaci da lokacin da ka wayi gari, sau uku uku = Sun isar maka daga kowani
abu"([5]). Abu-dawud da At-tirmiziy su ka rawaito shi, da An-nasa'iy da
isnadi mai kyau (hasan).
(5)
An karbo
daga Abu-hurairah (ra) lallai Abubakar as-siddik (ra) ya ce: Ya ma'aikin Allah!
Ka umurce ni da wassu kalmomi da zan rika fadansu idan na wayi gari, da idan na
yi yammaci, sai ya ce: "Ka ce:
«اللَّهُمَّ فَاطِرَ
السَّمَوَاتِ وَالْأَرْضِ، عَالِمَ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ، رَبَّ كُلِّ شَيْءٍ
وَمَلِـــــيكَهُ، أَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْــــــتَ، أَعُوذُ بِكَ
مِنْ شَرِّ نَفْسِي، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ الشَّيْطَانِ وَشِرْكِهِ، وَأَنْ
أَقْتَرِفَ عَلَى نَفْسِي سُوءًا، أَوْ أَجُـــــــرَّهُ إِلَى مُسْلِمٍ». قَالَ: «قُلْها إِذَا أَصْبَحْتَ، وَإِذَا
أَمْسَيْتَ، وَإِذَا أَخَذْتَ مَضْجَعَكَ».
Ma'ana: "Ya Allah kai ne
wanda ya kagi halittar sammai bakwai da kassai, masanin abin da ke boye da na
bayyane, ubangijin kowani abu mai kuma mullakarsa, Ina shaidawa babu abun bauta
da gaskiya sai kai, ina kuma neman tsarinka da sharrin kaina, da kuma sharrin
shedan da shirkarsa, ka kuma tsare ni kada na kasassabo ma kaina mummuna, ko na
jawo shi ga wani musulmi" ([6]).
Annabi (saw) ya ce: "Ka
fadi wannan zikirin idan ka wayi gari, da kuma idan ka yi yammaci, da kuma idan
ka kwanta a makwancinka" ([7]).
Imam Ahmad da Abu-dawud da
At-tirmiziy da An-nasa'iy da Bukhariy a cikin "al'adabul mufrad" su
ka rawaito shi da isnadi mai inganci (sahih). Wannan lafazin na Ahmad ne da
Bukhariy.
(6)
An karbo
daga Usman bn Affan (saw) ya ce: Manzon Allah (saw) ya ce: "Babu wani bawa
da zai ce –a cikin safiyar kowani yini, da kuma yammacin kowani dare-:
«بِسْمِ اللهِ الَّذِي لاَ
يَضُرُّ مَعَ اسْمِهِ شَيْءٌ فِي الأَرْضِ وَلاَ فِي السَّمَاءِ، وَهُوَ
السَّمِيعُ الْعَلِيمُ».
Ma'ana: "Da sunan Allah
wanda wani abu a cikin kasa ko a cikin sama ba ya cutarwa in an ambaci sunansa,
Shi mai ji ne masani". Ya karanta shi sau uku, = Ba zai aikata haka ba Sai
wani abu ya cutar da shi([8]). Imam Ahmad da Tirmiziy da Ibnu-majah su ka rawaito shi.
Tirmiziy ya ce: hadisi ne mai kyau ingantacce (hasan sahih), lamarin kuma kamar
yadda ya fada ne.
(7)
An karbo
daga Sauban mai hidima ga annabi (saw) lallai manzon Allah (saw) ya ce:
"Babu wani bawa musulmi da zai ce –a lokacin da ya wayi gari da a lokacin
da ya yi yammaci- sau uku:
«رَضِيتُ بِاللَّهِ رَبًّا،
وَبِالإِسْلاَمِ دِينًا، وَبِمُحَمَّدٍ نَبِيًّا».
Ma'ana: "Na yarda da
Allah a matsayin ubangiji, da musulunci a matsayin addini, da Muhammadu a
matsayin annabi" = in ya fadi haka face ya zama hakki akan Allah ta'alah
ya yardar da shi a ranar tashin kiyamah"([9]).
Imam Ahmad da Abu-dawud da
Ibnu-majah su ka rawaito shi da isnadi mai kyau (hasan). Wannan lafazin Ahmad
ne, sai dai kuma bai ambaci "Sauban" ba, Amma shi kuma Tirmiziy ya
ambace shi da sunansa a riwayarsa. Kuma An-nasa'iy shima ya ambace shi a cikin
littafinsa mai suna "amalul yaumi wallailah" ya kuma ambace shi ne da
lafazin Ahmad.
(8)
Ya zo a
cikin "sahihu Muslim" daga Abu-sa'id alkhudriy (ra) lallai annabi
(saw) ya ce:
«مَنْ
قَالَ: رَضِيتُ بِاللَّهِ رَبًّا، وَبِالْإِسْلَامِ دِينًا،
وَبِمُحَمَّدٍ رَسُولًا، وَجَبَتْ لَهُ الْجَنَّةُ».
Ma'ana: "Duk wanda ya
ce: Na yarda da Allah a matsayin ubangiji, da musulunci a matsayin addini, da
Muhammadu a matsayin annabi = lallai aljannah ta tabbata a gare shi"([10]).
(9)
Kuma dai
Muslim ya sake rawaitowa a cikin "sahihinsa" daga Abbas bn
Abdulmuddalib (ra) lallai annabi (saw) ya ce:
«ذَاقَ طَعْمَ الإِيمَانِ مَنْ
رَضِيَ بِاللَّهِ رَبًّا، وَبِالإِسْلامِ دِينًا، وَبِمُحَمَّدٍ نَبِيًّا».
Ma'ana: "Ya samu
dandanon imani; wanda ya yarda da Allah a matsayin ubangiji, da musulunci a
matsayin addini, da Muhammadu a matsayin manzo"([11]).
(10)
An samo
daga Anas (ra) lallai annabi (saw) ya ce: "Duk wanda ya fada a lokacin da
ya wayi gari, ko a lokacin da ya yi yammaci:
«اللَّهُمَّ إِنِّي أَصْبَحْتُ
أُشْهِدُكَ وَأُشْهِدُ حَمَلَةَ عَرْشِكَ وَمَلَائِكَتَكَ، وَجَمِيعَ خَـــلْقِكَ
أَنَّـــكَ أَنْـــــــــــــتَ اللَّهُ لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ، وَأَنَّ
مُحَمَّدًا عَبْدُكَ وَرَسُولُك».
Ma'ana: "Ya Allah lallai
ni na wayi gari ina shaida maka, kuma ina shaida ma mala'ikun da su ke dauke da
al'arshinka, da mala'ikunka, da sauran halittunka gabadaya cewa: Lallai kai ne
Allah wanda babu abun bauta da gaskiya sai kai, kuma lallai Muhammadu bawanka
ne kuma manzonka ne"([12]). Wanda ya fadi haka Allah zai yanta daya bisa hudunsa (1/4)
daga wuta, Wanda kuma ya fade shi sau biyu Allah zai yanta rabinsa ne, wanda kuma
ya fada sau uku to shi kuma Allah zai yanta uku bias hudunsa (3/4)
daga wuta, In kuma ya fade shi sau hudu to Allah zai yanta shi gabadayansa daga
wuta". Abu-dawud ya rawaito shi da isnadi mai kyau (hasan). Da
An-nasa'iy a cikin littafinsa
"amalul yaumi wallailah", da Isnadi hasan, Lafazinsa kuma shi ne:
«مَنْ قَالَ حِينَ يُصْبِحُ: اللَّهُمَّ إِنِّي أَصْبَحْتُ أُشْهِدُكَ وَأُشْهِدُ حَمَلَةَ عَرْشِكَ،
وَمَلَائِكَتَكَ وَجَمِيعَ خَــــلْقِكَ، أَنَّــكَ أَنْتَ اللَّهُ لَا إِلَهَ
إِلَّا أَنْتَ، وَحْدَكَ لَا شَرِيكَ لَكَ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُكَ
وَرَسُولُكَ، أَعْتَقَ اللَّهُ رُبُعَهُ
ذَلِكَ الْيَوْمَ مِــــــنَ النَّارِ، فَإِنْ قَالَ أَرْبَعَ مَرَّاتٍ أَعْتَقَهُ
اللَّهُ ذَلِكَ الْيَوْمَ مِنَ النَّارِ».
Ma'ana: "Duk wanda ya
fada a lokacin da ya wayi gari: Ya Allah lallai ni na wayi gari ina
shaida maka, kuma ina shaida ma mala'ikun da su ke dauke da al'arshinka, da
mala'ikunka, da sauran halittunka gabadaya cewa: Lallai kai ne Allah wanda babu
abun bauta da gaskiya sai kai; kai daya ka ke baka da abokin tarayya. kuma
lallai Muhammadu bawanka ne kuma manzonka. = Allah zai yanta daya bisa hudunsa
(1/4) a wannan yinin daga wuta, In kuma ya fade shi sau
hudu to Allah zai yanta shi a wannan yinin gabadayansa daga wuta"([13]).
(11)
An rawaito
daga Abdullahi bn Gannam (ra) lallai manzon Allah (saw) ya ce: "Duk wanda
ya fada a lokacin da ya wayi gari cewa:
«اللَّهُمَّ مَا أَصْبَحَ بِي
مِنْ نِعْمَةٍ فَمِنْكَ وَحْدَكَ، لاَ شَرِيكَ لَكَ، فَلَكَ الْحَمْدُ، وَلَكَ
الشُّكْرُ، فَقَدْ أَدَّى شُكْرَ يَوْمِهِ،
وَمَنْ قَالَ مِثْلَ ذَلِكَ حِينَ
يُمْسِي فَقَدْ أَدَّى شُكْرَ لَيْلَتِهِ».
Ma'ana: "Ya Allah babu
wata ni'ima da ta wayi gari tare da ni, face ta kasance daga wurinka ne; kai
dayanka baka da abokin tarayya; dukkan godiya taka ne. duk wanda ya fadi wannan
a wannan lokaci to hakika ya yi godiyarsa ta wannan yini, in kuma ya fada
kwatankwacin hakan a lokacin day a yi yammaci to hakika ya yi godiyar darensa
gabadayansa"([14]).
Abu-dawud ya rawaito shi da
An-nasa'iy a cikin littafin "amalul yaumi wallailati" da isnadi mai
kyau (hasan), kuma wannan lafazinsa ne, sai dai kuma shi bai ambaci lafazin
"a lokacin da ya yi yammaci" ba, kuma Ibnu-hibban ya rawaito shi da
lafazin An-nasa'iy daga hadisin abdullahi bn Abbas (ra).
(12)
Abdullahi
bn Umar (ra) ya ce: "Annabi (saw) bai kasance yana barin fadin wadannan
addu'oi a lokacin da ya wayi gari, ko ya yi yammaci ba:
«اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ
الْعَافِيَةَ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ، اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ
الْعَفْوَ وَالْعَافِيَةَ فِي دِينِي وَدُنْيَايَ وَأَهْلِي وَمَالِي، اللَّهُمَّ اسْتُرْ
عَوْرَاتِي، وَآمِنْ رَوْعَاتِي، اللَّهُمَّ احْفَظْنِي مِنْ بَيْنِ يَدَيَّ،
وَمِنْ خَلْفِي، وَعَنْ يَمِينِي، وَعَنْ شِمَـــــــــــــــــــالِي، وَمِنْ
فَوْقِي، وَأَعُوذُ –بِعَظَمَتِكَ- أَنْ أُغْتَالَ مِنْ تَحْتِي».
Ma'ana: "Ya Allah ina
rokonka lafiya a duniya da lahira, Ya Allah lallai ni ina rokonka afuwa da
lafiya a addinina da duniyata da iyalaina da dukiyata, Ya Allah ka suturce min
al'aurata, ka amintar da tsorona, Ya Allah ka bani kariya ta gaba gare ni da
kuma ta bayana, da kuma ta damana da ta hagun dina, da ta samana, kuma ina
neman tsari –da girmanka- kan halaka ni ta kasana (ruftawar kasa ko
makamancinsa) ([15]).
Imam Ahmad a cikin musnad ya
rawaito shi, da Abu-dawud da An-nasa'iy da Ibnu-majah, kuma Al-hakim ya inganta
shi.
(13)
An rawaito
daga Abu-hurairah (ra) ya ce: manzon Allah (saw) ya ce:
«مَنْ قَالَ: لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ
وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ، وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ
شَيْءٍ قَدِيرٌ، مَنْ قَالَهَا عَشْرَ مَـرَّاتٍ
حِينَ يُـصْبِحُ، كُـــــتِبَ لَهُ بِهَا مِـــــــئَةُ حَسَنَةٍ، وَمُحِيَ عَنْهُ
بِهَا مِـــئَةُ سَـــــيِّئَةٍ، وَكَانَتْ لَهُ عَدْلَ رَقَــبَةٍ، وَحُـــــفِظَ
بِهَا يَوْمَــئِذٍ حَتَّى يُمْسِيَ، وَمَنْ قَالَ مِثْلَ ذَلِكَ حِينَ يُمْسِي،
كَانَ لَهُ مِثْلُ ذَلِكَ».
Ma'ana: "Duk wanda ya ce:
Babu wanda ya cancanci bauta sai Allah, shi kadai ya ke bashi da abokan
tarayya, mulki nasa ne, yabo nasa ne, kuma lallai shi mai iko ne akan komai=
Duk wanda ya fadi haka sau goma a lokacin da ya wayi gari, za a rubuta masa
kyawawa guda dari, a kuma goge masa munana guda dari, yana da ladan yanta baiwa
guda daya, za a kuma kiyaye shi a wannan yinin har ya yi yammaci. Wanda kuma ya
fadi kwatankwacin haka da yammaci to yana da kwatankwacin haka([16]).
Imam Ahmad ya rawaito shi a
cikin musnad da sanadi mai kyau (hasan).
(14)
Kuma an
sake rawaitowa daga gare shi (Allah ya kara yarda a gare shi) ya ce: annabi
(saw) ya ce:
«مَنْ قَالَ إِذَا أَمْسَى ثَلاَثَ مَرَّاتٍ: أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ، لَمْ تَضُرَّهُ حُمَةٌ تِلْكَ اللَّيْلَةَ».
Ma'ana: "Duk wanda ya
fada idan ya yi yammaci, sau uku: Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku,
daga sharrin abin da ya halitta, Abu mai dafi ba zai cutar da shi ba a wannan
daren"([17]).
Imam Ahmad da At-tirmiziy ne
su ka rawaito shi, da isnadi mai kyau (hasan). Abun da ake ce da shi (hummah)
da ya zo cikin hadisin shi ne: dafin dabbobi ma'abuta dafi, kamar kunama, da
maciji, da wassunsu.
(15)
Kuma
Muslim a cikin sahihinsa ya fitar daga Khaulah bint Hakim (ra), daga Annabi
(saw) lallai shi ya ce:
«مَنْ نَزَلَ
مَنْزِلًا، ثُمَّ قَالَ: أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ مِنْ
شَرِّ مَا خَلَقَ، لَمْ يَضُرَّهُ شَيْءٌ حَتَّى
يَرْتَحِلَ مِنْ مَنْزِلِهِ ذَلِكَ».
Ma'ana: "Duk wanda ya
sauka a wani masauki, sannan ya ce: Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku,
daga sharrin abin da ya halitta = Babu wani abu da zai cutar da shi har ya
kaura daga wannan masaukin nasa"([18]).
(16)
An karbo
daga Abdullahi bn Abdurrahman bn Abzah, daga mahaifinsa (ra) daga annabi (saw) lallai
shi ya kasance yana cewa idan ya wayi gari:
«أَصْبَحْنَا عَلَى فِطْرَةِ
الإِسْـــلاَمِ، وَعَلَى كَلِمَةِ الإِخْــــــلاَصِ، وَعَلَى دِينِ نَبِيِّنَا
مُحَمَّدٍ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وَعَلَى مِلَّةِ أَبِينَا
إِبْرَاهِيمَ حَنِيفًا مُسْلِمًا، وَمَا كَانَ مِنَ الْمُشْرِكِينَ».
Ma'ana: "Mun wayi gari
akan fidirar musulunci, da kalmar ikhlasi, da kuma addinin annabinmu Muhammadu
(saw), da tafarkin babanmu annabi Ibrahim mikakke, musulmi, kuma bai kasance
daga cikin mushirkai ba"([19]). Ahmad ne ya rawaito shi
a cikin "musnad" da isnadi mai inganci.
(17)
An karbo
daga Abdurrah bn Abiy-bakrah, lallai shi ya ce a mahaifinsa: Ya mahaifina
lallai ni ina jinka kana addu'a kowace safiya, ka ce:
«اللَّهُمَّ عَافِنِي فِي
بَدَنِي، اللَّهُمَّ عَافِنِي فِي سَمْعِي، اللَّهُمَّ عَافِنِي فِي بَصَرِي، لاَ
إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ، تُعِيدُهَا ثَلاَثًا حِــينَ تُصْبِحُ،
وَثَلاَثًا حِينَ تُمْسِي، وَتَقُولُ: اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ
مِنَ الْكُفْرِ وَالْفَقْرِ، اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُــــــــوذُ بِـــكَ مِـنْ
عَذَابِ الْقَبْرِ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْت، تُعِيدُهَا حِينَ تُصْبِحُ ثَلاَثًا، وَثَلاَثًا
حِينَ تُمْسِي، قَالَ: نَعَمْ يَا بُنَيَّ، إِنِّي سَــــمِــــعْتُ النَّبِيَّ
صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَدْعُو بِهِنَّ، فَأُحِبُّ أَنْ أَسْتَنَّ
بِسُنَّتِهِ» قَالَ: وَقَــــــــــــالَ رَسُـــــولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَـــلَّمَ: دَعَـــــــــــوَاتُ الْمَكْرُوبِ: «اللَّهُمَّ رَحْمَتَكَ أَرْجُو، فَلَا تَكِلْنِي إِلَى نَفْسِي طَرْفَةَ
عَيْنٍ، وَأَصْلِحْ لِي شَأْنِي كُلَّهُ، لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْــــتَ. فَأُحِبُّ
أَنْ أَسْتَنَّ بِسُنَّتِهِ».
(Ya Allah ka ban lafiya a jikina, Ya Allah
ka bani lafiya a jina, Ya Allah ka bani lafiya a ganina, Babu abun bauta da
gaskiya sai kai) Na ji kana maimata hakan har sau uku in ka wayi gari, da kuma
sau uku in ka yi yammaci, Sannan sai ka ce: Ya Allah lallai ni ina neman
tsarinka daga kafirci da talauci. Ya Allah lallai ni ina neman tsarinka daga
azabar kabari, babu bauta da gaskiya sai kai. Shima ka kan maimata shi har sau
uku in ka wayi gari, da kuma sau uku in ka yi yammaci, Sai ya ce: E, haka ne ya
kai dan karamin dana; lallai ni na ji annabi (saw) yana addu'a da su, sai na so
na yi koyi da wannan sunnar". Sannan ya ce: kuma manzon Allah (saw) ya ce:
"Addu'ar mutumin da ke cikin bakin ciki shi ne ya ce: Ya Allah rahamarka
na ke fata, kada ka dogarar da nig a kaina daidai da kyaftawar ido, ka gyara
mini sha'anina gabadayansa, Babu abun bauta da gaskiya sai kai. Sai na so na yi
koyi da sunnarsa"([20]).
Ahmad ya rawaito shi, da
Bukhariy a cikin "Al-adabul mufrad, da Abu-dawud da An-nasa'iy da Isnadi
mai kyau (hasan).
Kuma an shar'anta ga dukkan
musulmi namiji ne ko mace, ya rika fada a cikin safiyar kowani yini:
LA'ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL
HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN KADIR, sau dari daya, don ya samu kariya daga
shedan na tsawon wannan yinin nasa har ya kai yammaci, saboda abun day a gabata
na hadisin Abu-hurairah (ra) wanda ya zo cikin sahihul Bukhariy da Muslim, daga
annabi (saw) lallai shi ya ce:
«مَنْ قَالَ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ
وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ
شَيْءٍ قَدِيرٌ، فِي يَوْمٍ مِائَةَ مَرَّةٍ،
كَانَتْ لَهُ عَدْلَ عَشْرِ رِقَابٍ، وَكُتِبَتْ لَهُ مِائَةُ حَسَنَةٍ،
وَمُحِيَتْ عَنْهُ مِائَةُ سَيِّئَةٍ، وَكَانَتْ لَهُ حِرْزًا مِنَ الشَّيْطَانِ،
يَوْمَهُ ذَلِكَ، حَتَّى يُمْسِيَ. وَلَمْ يَأْتِ أَحَدٌ أَفْضَلَ مِمَّا جَاءَ
بِهِ إِلَّا أَحَدٌ عَمِلَ أَكْثَرَ مِنْ ذَلِكَ، وَمَنْ قَالَ: سُبْحَانَ اللهِ وَبِحَمْدِهِ، فِي يَوْمٍ
مِائَةَ مَرَّةٍ حُطَّتْ خَطَايَاهُ وَلَوْ كَانَتْ مِثْلَ زَبَدِ الْبَحْرِ».
Ma'ana: "Duk wanda ya ce: Babu wanda ya
cancanci bauta sai Allah, shi kadai ya ke bashi da abokan tarayya, mulki nasa
ne, yabo nasa ne, kuma lallai shi mai iko ne akan komai= Duk wanda ya fadi haka
sau dari daya, zai samu ladan kwatankwacin yanta bayi goma, sai kuma a rubuta
masa kyawawa guda dari, a goge masa munana dari, kuma ya kasance kariya a gare
shi daga shaidan, tsawon yininsa har ya yi yammaci, Kuma babu wani mutum da zai
zo da abin da ya fi nasa sai mutumin da ya aikata fiye da yadda ya aikata. Kuma
duk wanda ya ce: SUBHANALLAHI WA BIHAMDIHI a cikin yini sau dari, za a kankare
masa kurakurensa koda sun kai kamar kumfar teku"([21]).
«وَأَنْ
أَقْتَرِفَ عَلَى نَفْسِي سُوءًا، أَوْ أَجُـــــــرَّهُ إِلَى مُسْلِمٍ»
Bata
cikin riwayar Abu-hurairah (ra), saboda ta zo ne a riwayar Abdullahi bn Amru bn
Al-aas, a kissar Abubakar siddik (ra), kuma Imam Ahmad ya fitar da ita a cikin
"musnad" din Abubakar, (1/14), da kuma "musnad" din
Ibnu-abil aas, (2/196).
([15])
Imam
Ahmad ya fitar da shi, (2/25), da Abu-dawud, (lamba: 5074), da Nasa'iy a amma a
takaice, (karshensa kawai, lamba: 5529), a cikin sunanul kubrah kuma
gabadayansa, (lamba: 10401), Ibnu-maajah shima ya rawaito shi a takaice (lamba:
4004), da Alhakim a cikin Mustadrak, (lamba: 1902), ya kuma inganta shi, Imam
Azzahabiy kuma ya masa muwafakah (1/699).
Malam muna godiya kwarai da gaske akan abubuwa masu mahimmanci da kuke ta kokarin fadakar damu ubangiji ya saka maku da alherin sa amin.
ReplyDelete