HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 17/Ramadhana/1439H
daidai da 01/Yuni/ 2018M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH ABDULLAHI BN ABDURRAHMAN ALBU'AIJAN
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
DARARE GOMAN KARSHEN RAMADANA
SUNE MAFI FALALAN LOKATAI, WANDA YIN BAUTA A CIKINSU SHINE MAFI GIRMAN BAUTA
Shehin Malami wato:
Abdullahi bn Abdurrahman Albu'aijan –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai
taken:
DARARE
GOMAN KARSHEN RAMADANA SUNE MAFI FALALAN LOKATAI, WANDA YIN BAUTA A CIKINSU
SHINE MAFI GIRMAN BAUTA, Wanda
kuma a cikinta ya tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah;
wanda ya sanya hanya ga wanda ya nemi tuba zuwa gare shi.
Wanda kuma ya mayar da
lamura gare shi, ya ke sanya masa matabbata da mafi kyan wurin kailula.
Wanda kuma ya rayu cikin
bautar Allah, ya kan sanya masa inuwa mai matabbaciyar lumshi; Don haka; wanda
ya so, sai ya riki hanyar kirki zuwa ga UbangijinSa.
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya, sai Allah; shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya, ina mai
girmama shi, kuma ina darajanta shi.
kuma ina shaidawa lallai
annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa, madalla da shi jagora kuma mai nusar da
mutane hanya,
Allah ka yi karin salati a
gare shi, da iyalanSa da sahabbanSa, da sallamar amintarwa mai tarin yawa.
Bayan haka:
Ina yin wasiyya a gare ku -Ya
ku bayin Allah- da ni kai-na, da jin tsoron Allah Mabuwayi da daukaka,
domin babu samun jin dadi da sa'ida sai ta hanyar takawar Allah, kuma ba a samun
babban rabo sai ta hanyar da'a ga Allah Majibinci.
Sannan ku sani, Lallai da'a
ko biyayyar Allah shine mafi alherin abinda aka ribata kuma aka aikata, samun
yardarSa kuma, shine mafi alherin abinda aka ribata kuma abin nema, ita kuma
Aljannah an kewaye ta da ababe masu wahala, Wuta kuma, an kewaye ta abinda Rai
ke sha'awa. Kuma lallai za a cika ladan kwadagonku
ne a gare ku, a ranar Kiyama; kuma duk wanda aka nisantar da shi daga Wuta, sai
aka shigar da shi Aljannah to hakika ya samu babban rabo.
Ya ku masu azumi!!!
Allah ya karbi ayyukanku na
'da'a, kuma ya gyara halayenku (Amin), kuma ina rokonsa ya muku dace cikin
abinda ya rage na wannan watan, kuma ya rubuta muku tabbatuwa akan biyayya a gare
shi, a sauran kwanaki na rayuwa.
Ya ku taron
Musulmai!!!
Ku ribaci lokaci iyakar
ribata, ku yi gaggawan aikin alheri kuna masu sauri da rigaggeniya, saboda
watanku mai karamci ya dau hanyarsa ta raguwa da tafiya, kuma dararensa da
yininsa sun dau hanyar karewa da gushewa, Sai ku riski abinda ya rage daga
cikinsa ta hanyar aikata kyawawan ayyuka, kuma ku yi gaggawan tuba zuwa ga
Ma'abucin girma da buwaya, Ya kaiton masu sakaci! Ya asarar tababbu batattu!! Ya
musibar gafalallu!!!
Domin Manzon Allah –sallal
Lahu alaihi wa sallama- ya hau minbari sai ya ce: Amin!
Amin!! Amin!!! Yayin da ya sauka, sai aka tambaye akan haka, sai ya ce: mala'ika
Jibrilu ne ya zo min sai ya ce: Hancinsa ya bugi turbaya; Wanda ya riski watan
Ramadana, sai ba a gafarta masa ba; har ya shiga wuta, kuma Allah ya nisanta
shi daga rahama! Ka ce: Amin! Sai na ce: Amin!
Kuma hancinsa ya
bugi turbaya; Wanda ya riski iyayensa biyu, ko kuma daya, sai bai musu biyayya
ba, har ya mutu ya shiga wuta, Kuma Allah ya nisanta shi daga rahama, Ka ce:
Amin, sai na ce: Amin!!
Kuma hancinsa ya
bugi turbaya, wato Wanda aka ambaci sunanka a wurinsa sai bai maka salati ba,
kuma Allah ya nisanta shi daga rahama, Ka ce: Amin, sai na ce: Amin!!!".
Ya ku taron
Musulmai!!!
Lallai ayyuka ana sakayya
ne akansu da abinda aka cike su da shi. Sai ku kara kokari, domin ba komai ba
ne watan Ramadana, face kwanaki kidayayyu.
Kuma lallai kwanaki goman
da suke gabanku sune mafificin lokatai, kuma lokuta na musamman don aikata alkhairi da yin
da'oi sune mafi girma, kuma su suka fi cancantar dacewa da yin kokarin bawa
cikin ayyukan kusanci ga Allah.
Kuma duk da cewa ayyukan
da'a a cikin sauran kwanakin wannan wata mai albarka suna da falala, sai dai a
cikin kwanaki gomansa na karshe sun fi girman falala, kuma matsayinsu yafi
daukaka, kuma sun fi lada mai gwabi.
Domin sune kwanaki goman da
ake goge tuntube a cikinsu, a kankare munana, ake amsa addu'oi, kuma don haka
ne "Annabi
–sallal Lahu alaihi wa sallama- ya kasance yake kara kokarin bauta a cikinsu
irin abinda baya yinsa a waninsu, Kuma ya kasance idan
wadannan goman suka shigo sai ya tamke kwarjallanSa, ya rika raya darenSa, yana
tayar da iyalanSa".
Sai ku bayyanar da
kwadayinku akan kwanakin, domin su ganima ce mai girma.
Kuma madalla da mutumin da
ya samu rabo a cikinsu, kuma ya ribaci alkhairin cikinsu da falalarsu.
Ya ku Bayin Allah …
!!!
A cikin kwanakin nan guda
goma, akwai wani dare wanda yafi watanni dubu alheri, Rahama da jin-kai suna
sauka a cikinsa, kuma ana amsa addu'oi,
ana kankare kura-kurai, ana gafarta laifuka, "Wanda ya tsayu a cikin wannan
daren (yana sallah) yana mai imani da neman lada, to an gafarta masa
abinda ya gabata daga zunubansa".
Wanda kuma ya yi sakaci a
lamarin wannan dare, sai aka haramta masa alkhairinsa, to shine abin zargi, marashin
rabo.
Lallai shi ne, daren Lailatul
kadr, abin neman mutane muminai, abin fatan samun salihai, burin masu
takawa, wanda a cikinsa ake rubuta daukacin ababen da aka kaddara, kuma a
cikinsa ake rarrabe kowani lamari da ake hukuntawa, Sai ku yi kwadayin tsayuwa
a cikinsa da salloli, kuma ku zage domin nemansa, ku kara kwazo kan bidar
dacewa da shi, kuma ku kankan-da-kai zuwa ga Allah a cikin wannan dare; saboda
wannan daren –Wallahi- ganima ce ta cikin ruwan sanyi, domin yin ibada a cikin
wannan dare yafi alheri akan ibadar watanni dubu.
Kuma ya dace, ga duk wanda
ya nemi dacewa da wannan daren, ya zamto ba a tabar da shi ba, domin Allah
Ma'abucin falala ne Mai girma; "Lallai Mu mun saukar da Kur'ani
a cikin daren Lailatul kadr * To me ya sanar da kai abinda ake cewa Lailatul
Kadari * Lailatul Kadari tafi alheri akan watanni dubu * Mala'iku da Ruhi (wato
Jibrilu) suna sauka a cikinsa da izinin Ubangijinsu, da kowane lamari * Aminci
ne wannan daren, har zuwa fitowan alfijir" [Kadr, 1-5].
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya sanya da'a a gare shi ta
zama hanyar samun yardarSa, kuma ya sanya yardarSa ta zama hanyar rabauta da
AljannarSa, kuma ya yi taufiki ga bayinsa muminai sai suka lazimci yin bauta a
gare shi, suka kaurace wa jin-dadinsu da sha'awowinsu, suka fifita neman
yardarSa.
Ya ku bayin Allah
!! …
Itikafi shine lazimtar Masallaci
domin yin ibada, da killace Rai daga sha'awowinta da jin-dadinta, da juya baya
ga duniya da fitinunta, da abubuwa masu shagaltawa da masu dauke hankali. Da debe
kewa ko kadaici ta hanyar ganawa da Allah -سبحانه-, da warewa gefe da ficewa daga jama'a da yanke huldodi, da barin
wargi da wasa, da yin hisabi ga Rai, da sabunta ko jaddada alkawari tare da
Allah, da kokarin tsarkake zuciya daga abinda ka iya makale mata na daudar da
take cikin wannan rayuwar.
Kuma Allah Ta'alah ya
shar'anta yin itikafi a cikin Masallatai, kuma ya yi umurnin a shirya
Masallatan domin haka, a inda yake cewa: "Kuma muka yi
alkawali zuwa ga Ibrahima da Isma'ila, da cewa: Ku tsarkake dakina, domin masu
dawafi, da masu itikafi, da masu ruku'i, masu sujada" [Bakara: 125].
Ya ku bayin
Allah…!!
Itikafi sunna ne, sai dai a cikin
watan Ramadana yafi zama abin so, a gomansa na-karshe kuma yafi kasancewa
abinda yafi karin karfi, saboda an ruwaito daga A'isha –Allah ya kara yarda a
gare ta- lallai ta ce: "Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya
kasance yana yin itikafin kwanaki goman karshen watan Ramadana, har Allah Mabuwayi
da daukaka ya masa wafati, sa'annan sai matansa suka yi itikafin a bayansu", Bukhariy da Muslim.
Kuma an ruwaito daga
Abdullahi bn Umar –Allah ya kara yarda a gare su- ya ce: "Manzon Allah –sallal
Lahu alaihi wa sallama- ya kasance yana yin itikafin kwanaki goman karshen
watan Ramadana".
Ya ku masu zuwa
dakunan Allah (Masallatai)!!!
Masallatai sune dakunan Allah a doron
kasa, Sai ku sane musu hakkokiknsu, ku ladabtu da laddubansu, kuma ku kiyaye wa
masallatai matsayinsu da falalolinsu, domin an gina su ne domin bauta, sai ku
yi aiki a cikinsu da ladabi da natsuwa, kuma kada ku rike su a matsayin wuraren
wargi da wasa ko kamar kasuwa, kuma kada ku cutar da Masallata a cikinsu da
masu itikafi, saboda cikin aikata hakan akwai hana su yin ibada, da kuma fitar
da su daga cikin natsuwarsu.
Ya ku Ma'abuta
itikafi!!!
Kun zo dakunan Allah ne da
nufin yin bauta, da yanke alakokin Duniya da fiskantar gidan Lahira, Sai ku
fiskanci Allah da zukata masu mayar da lamura gare shi, masu cike da tsoronsa,
kuma ku kankan da-kai zuwa gare shi tare da jin kaskanci, da rusunawa, da
karayar zuciya. Kuma ku kiyayi abubuwan da suke daddatse muku hanya, ku kiyayi
shagaltuwa da na'urorin komfiyutoci da wayan salula, da maganganun
kila-da-kala. Kuma ku kiyaye wa Masallatai alfarmominsu.
Ya ku Ma'abuta itikafi a
Masallacin Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم-!!!
Lallai ne babban ofishin
ofishin kulawa da Masallatan Harami Biyu sun yi ayyuka tukuru ababen
yabawa, wajen tarbanku, kuma sun shishshirya hawan ginin sama na Masallacin
Annabi –صلى الله عليه وسلم- sun tanade shi,
kuma sun kebance shi ga masu shiga itikafi. Kuma koyaushe suna cikin hidimarku,
sai ku taimaki ma'aikatanmu; ta hanyar yin aiki da dokoki da tsare-tsare, don
girmama Masallacin Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم-, kuna masu yin hidima da aikata haka ga wadanda suka bakunce
shi, masu taimakon bayin Allah akan ayyukan da'a, kuna masu fatan samun lada da
sakayya, masu aiki da shari'a, saboda Allah Ta'alah yana cewa:
"Kuma a lokacin da
muka iyakance wa Ibrahimu wurin daki, muka ce: Kada ka hada komai da Ni ga bauta,
kuma ka tsarkake dakina, domin masu dawafi da ma'abuta tsayuwar sallah, da masu
ruku'i da sujada",
[Haj: 26].
Allah! Ya karba muku irikafinku,
da sauran dangogin ayyukanku na da'a.
Ya Allah! Ka daukaka Musulunci da …
,,, ,,, ,,,