HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
صلى الله عليه وسلم
JUMA'A, 22/RAJAB/1437H
Daidai da
29/Afrilu/2016M
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI ALIYU XAN ABDURRAHMAN AL-HUZAIFIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
YIN SHIRI GA MUTUWA
Shehin Malami wato: Aliyu
xan Abdurrahman Alhuzaifiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai
taken: YIN SHIRI GA MUTUWA, Wanda kuma ya tattauna a cikinta, akan mutuwa da
kasancewarta maqura ko gaya ga kowace halitta, kuma qarshen kowani rayayye, yana
mai bayyana HANYOYIN DA MUTUM ZAI BI YA SHIRYA MATA na kyawawan aiyuka, kuma mafi
girma daga cikin hanyoyin shine: TABBATAR DA TAUHIDI ga Allah ta'alah, kamar
yadda ya bayyana sabuban samun kyakkyawan qarshe, da kuma na mummunan qarshe.
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Godiya ta tabbata ga Allah Rayayye Tsayayye
wanda baya mutuwa, Ma'abucin mulki da iko, da buwaya, da girma; Ina yin godiya wa ubangijina, kuma ina yin
yabo a gare shi, ina tuba zuwa gare shi, ina kuma neman gafararSa.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai
Allah; shi kaxai yake bashi da abokan tarayya, Mai tankwasa bayinSa, Wanda yake aikata abinda ya nufa,
kuma yake hukunta abinda ya so.
Ina kuma shaidawa lallai annabinmu kuma
shugabanmu Muhammadu; bawanSa ne kuma manzonSa.
Ya Allah ka yi daxin salati da sallama da
albarka ga bawanka kuma manzonka annabi Muhammadu zavavve, da kuma ga iyalansa da sahabbansa waxanda
suke kan miqaqqiyar turba.
Bayan haka:
Ku kiyaye dokokin Allah ta'alah da taqawa, ta
hanyar neman yardarSa, da nisantar sava masa, saboda taqawar Allah itace
sababin gyaruwar halayenku a cikin rayuwarku, kuma ita ce tanadi ko shiri don
fiskantar abinda yake gabanku, na ababen da kuke tsoro, ko kuke kiyayarsu. Kuma
taqawa ita ce garkuwa ko kariya daga ababe masu halakarwa, kuma da ita ne Allah
yayi alkawarin bada aljannoni.
Ya ku bayin Allah!
Kowani Mutum yana yin aiki a cikin wannan
rayuwar don samun amfaninsa, da gyara lamuransa, da samun ababen rayuwarsa;
Daga cikin Mutane akwai wanda
yake gyara addininsa, tare da gyara duniyarsa, irin waxannan sune Allah ta'alah
ya ba su abu mai kyau a gidan duniya, a gidan lahira shima ya ba su mai kyau,
kuma ya kare su daga azabar wuta.
Daga cikinsu kuma akwai wanda ya ke yin
aiki don duniya, sai kuma ya tozarta rabonsa a lahira, su kuma irin waxannan
sune waxannan da suke jin daxi (a duniya), kuma suke ci, kamar yadda dabbobi ke
ci, kuma Wuta ce mazauni a gare su.
Kuma kowace NIYYA da AIKI suna da wani lokaci
da zasu qare; ba za su wuce shi ba, Allah ta'alah yana cewa:
"Kuma lallai ne, makoma (da qarewar lamura)
izuwa ga Ubangijinka kawai su ke!" [Najm: 42].
Tsarki
ya tabbata ga Ubangijin da ya sanya wani aiki ga kowace Rai, kuma ya sanya wa
kowace Rai niyya da nufi, ta hanyar halitta wa kowani Mutum nufi da azama; har
ya zama kowace rai tana yin aikinta idan ta nufe shi, ko ta ga dama, tana kuma
barin yin aiki a lokacin da taga dama.
Saidai kuma nufin Allah da ganin damansa suna
sama da kowani nufi ko ganin dama, Allah ta'alah yana cewa:
"Lallai ba za ku so (aukuwar wani lamari,
sai kuma ya aukun kamar yadda kuka nufe shi ba) face idan Allah Ubangiji
halittu ya yarda (kuma ya nufa)" [Takwir: 29].
Saboda haka, Duk abinda Allah ya nufa; ya kan
kasance, Wanda kuma bai nufi aukuwarsa ba to lallai baya kasancewa.
ITA
KUMA MUTUWA iyaka ce ga kowani halittan da yake doron qasa, kuma mutuwa
ita ce qarshen kowani mai rai a cikin wannan duniyar, Kuma lallai Allah ya
rubuta mutuwa har ga Mala'iku; Jibrila
da Mika'iyla, da Israfiyla (عليهم السلام)
–duka za su mutu-, Kuma shima Mala'ikan mutuwa (da xaukar rai) zai mutu; Allah
ta'alah yana cewa:
"Dukkan wanda yake kan qasa mai qarewa ne *
Kuma fuskar Ubangijinka Mai girman jalala da karimci ita ce take wanzuwa"
[Rahman: 26-27].
Kuma
mutuwa ita ce qarshen rayuwar duniya, kuma ita ce farkon rayuwar lahira; saboda
Da mutuwa ne, jin daxin da ke cikin rayuwar duniya ke yankewa, sai wanda ya
mutu ya gane wa kansa bayan mutuwa; ko dai ni'ima mai girma, ko kuma azaba mai
raxaxi.
Kuma
ita mutuwa aya ce daga cikin ayoyin Allah, masu nuni akan: ikon Allah mabuwayi
da xaukaka, da rinjayenSa ga halittunSa, Allah ta'alah yana cewa:
"Kuma (Allah) shine Mai rinjaye bisa ga
bayinSa, kuma yana aikan masu tsaro akanku, har idan mutuwa ta je wa xayanku,
sai manzanninmu su karvi ransa alhali, su ba su yin sakaci"
[An'am: 61].
Kuma
mutuwa adalci ne, daga Allah; wanda dukkan halittu suke daidaituwa a cikinta,
Allah ta'alah yana cewa:
"Dukkan Rai mai xanxanar mutuwa ne, sa'annan
izuwa gare mu ake mayar da ku" [Ankabut: 57].
Kuma
mutuwa tana yanke duk wani jin daxi, tana kuma qarar wa jiki kowani motsi, kuma
tana rarraba jama'a, tana katange mutum daga aikata ababen da ya saba aikata su,
Allah ya kevanta da kashewa tare da rayarwa, Yana cewa:
"Kuma (Allah) shine wanda yake rayarwa, kuma
yake matarwa, kuma a gare shi ne savawar dare da yini suke, Shin, ba za ku
hankalta ba" [Mu'uminun: 80].
Ita
Mutuwa Mai gadi, baya hana zuwanta, kuma Masu bada tsaro basa tunkuxe ta, kuma
dukiya bata wadatarwa, ko ta hana ta, haka 'ya'ya ko abokai. Qarami baya tsira daga mutuwa haka
babba. Ko kuma mawadaci ko faqiri. Ko mai girma ko qasqantacce, Allah ta'alah
yana cewa:
"Inda duk kuka kasance, mutuwa za ta riske
ku, ko da kuwa kun kasance ne a cikin benaye da aka inganta su" [Nisa'i:
78]. Kuma Allah ta'alah yana cewa:
"Ka ce: Lallai mutuwar nan da kuke gudu daga
gare ta, to lallai ne ita mai haxuwa da ku, ce, sa'annan a mayar da ku zuwa ga
masanin fake da bayyane, domin ya ba ku labari ga abinda kuka kasance kuna
aikatawa" [Jumu'a: 8].
Kuma
mutuwa tana zuwa kwatsam, idan ajalinta ya zo, Allah ta'alah yana cewa:
"Kuma Allah ba zai jinkirta wa wata rai ba
idan ajalinta ya zo, Kuma Allah Masani ne ga abinda suke aikatawa"
[Tagabun: 11].
Kuma
mutuwa ba ta neman izinin wani idan ba ga annabawa ba, Su annabawa kam, mutuwa
ta neman izininsu saboda matsayinsu a wurin Allah (عليهم الصلاة والسلام), wannan ya sanya mutuwa
ta nemi izinin kowani xaya daga cikinsu, Ya zo cikin hadisi cewa:
"Babu wani Annabi face Allah ya
bashi zavi tsakanin dawwama a duniya, sa'annan aljannah, ko kuma mutuwa, amma sai
ya zavi mutuwa".
Allah
ta'alah ya nufi cewa xan-adam ya fice daga duniya ta hanyar mutuwa, domin ya
yanke dukan alaqoqinsa da ita; har ya zamo babu wani gashi guda xaya a jikinsa
da zai so duniya; matuqar ya kasance mumini, Hadisi ya zo daga Anas (رضي الله عنه) lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Babu wani da yake da wani matsayi a
wurin Allah, da zai so ya sake dawowa duniya, a bashi duk abin da suke doron
qasa, saidai wanda yayi mutuwar shahada; yana fatan ya komo duniya, don a sake
kashe shi sau goma, saboda abinda yake gani na karamomi",
Bukhariy ya ruwaito shi, da Muslim.
Kuma
ita mutuwa musiba ce, wanda babu makawa kan aukuwarta, kuma zogi ne wanda babu wani
mutum da zai iya sifanta shi; saboda tsananinsa; Domin Rai ne ake zare shi daga
magudanan jini da tsoka da jijiya.
Kuma duk wani zogi mai tsanani to bai kai
zogin da mutuwa take da shi ba, Hadisi ya zo daga A'isha (رضي الله
عنها) ta ce: Na ga Manzon Allah (صلى الله
عليه وسلم) a lokacin mutuwa, a wurinsa akwai kofi
wanda a cikinsa akwai ruwa, yana tsoma ko shigar da hannunsa a cikin kofin,
sa'annan sai ya shashshafi fiskarsa da ruwan, Sai kuma ya ce:
"Ya Allah ka taimake ni akan magagin
mutuwa, da mayen da ke cikin mutuwa", Tirmiziy ya ruwaito shi.
A wasu riwayoyin kuma: "Lallai
mutuwa tana da maye".
Wani mutum ya ce wa mahaifinsa a lokacin da
yake cikin halin fitan rai: Ka sifanta min zogin mutuwa don xaukar izina? Sai
ya ce: Ya kai xana! Kamar wata qaya ce mai lankwasa a ke janta a cikin
cikina, kuma kai ka ce numfashi nake yi daga qofa ko kafar allura.
Kuma an ce wa wani wanda yake cikin yanayi ko
halin fitar rai, Yaya kake ji? Sai ya ce: Kai ka ce: Babbar wuqa ce mai
lankwasa take ta kai-komo a cikin cikina.
Wani kuma an ce masa, Yaya raxaxin mutuwa yake?
Sai ya ce: Kai ka ce, wuta ce take ruruwa a cikin cikina.
Kuma duk wanda ya dawwamar da ambaton mutuwa
to zuciyarsa ta kan yi taushi, aikinsa da halinsa kuma su kan gyaru. Kuma ba
zai samu kwarin guiwar aikata savon Allah ba, kuma ba zai tozartar da farillai
ba, kuma duniya da qawarta ba za ta ruxe shi ba, kuma –a koyaushe- zai kasance ne
cikin begen Ubangijinsa, da aljannonin ni'ima.
Shi kuma mutumin da ya mance da lamarin mutuwa
sai zuciyarsa ta qaiqashe, sai kuma ya karkata zuwa ga duniya, aikinsa kuma sai
ya yi muni, burinsa kuma ya yi tsayi.
Don haka; Tuna lamarin mutuwa shine mafi
girman wa'azozi, saboda hadisi ya zo daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"أكثروا من
ذكر هاذم اللذات".
Ma'ana: "Ku yawaita ambaton
mai yanke jin daxi; wato mutuwa", Tirmiziy ya ruwaito shi,
da Nasa'iy, Kuma Ibnu-Hibbana ya inganta shi.
Ma'anan hadisin kuma shine: (A riqa tuna ko
ambaton) mai yanke jin daxi, mai gusar da shi.
An ruwaito daga Ubaiyyu xan Ka'ab (رضي الله عنه) ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance, idan xaya bisa ukun ( 1/3
) dare ya tafi sai ya tashi, Yana cewa:
"Ya ku mutane! Ku tashi ku ambaci
Allah! Busa mai girgiza ta yi kusan zuwa (wato: busan farko), Me biye mata kuma
tana biye (wato busan qaho na biyu), Mutuwa da abinda ke cikinta, suna zuwa",
Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma ya ce: Hadisi ne mai kyau.
An ruwaito daga Abud-darda'i (رضي الله عنه) yace:
"Mutuwa ta isa ta zama mai wa'azi,
Zamani kuma, ya zama mai raba jama'a, Yau kuna cikin gidaje, gobe kuma a cikin
qaburbura", Ibnu-Asakir ya ruwaito shi.
Rabauta
cikakkiyar rabauta, da yin dace cikakken yin dace, da samu rabo cikakke, Yana
nan ne cikin yin shiri ko tanadi ga mutuwa, saboda kasancewar mutuwa ita ce farkon
qofar shiga aljannah, ko kuma ita ce farkon qofar shiga wuta.
Shi
kuma tanadi ga mutuwa yana kasancewa ne, da TABBATAR DA TAUHIDI
ga Allah Ubangijin talikai, ta hanyar bautar Allah; ba tare da an haxa shi da
komai ba, da kuma nisantar nau'ukan shirka gabaxayansu, An ruwaito daga Anas (رضي الله عنه) ya ce: Na ji Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"Ya kai xan Adam! da ace zaka zo min
da kamar cikin qasa da zunubai, sa'annan ka gamu da ni, ba tare da ka haxa ni
da kowa ba, ni kuma zan zo maka da wata gafara, kamar cikin qasa”,
Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma yace hadisi ne mai kyau.
Tanadi ga mutuwa yana kasancewa ta hanyar TSARE
DOKOKIN ALLAH da FARILLAI , Allah ta'alah yana cewa:
"Da masu kiyaye dokokin Allah, kuma ka bada
bushara ga muminai"[Tauba: 112].
Tanadi
ga mutuwa yana kasancewa ta hanyar NISANTAR MANYA-MANYAN ZUNUBAI DA SAVO,
Allah ta'alah yana cewa:
"Idan kuka nisanci manyan laifukan da aka
hane ku aikata su, to za mu kankare munanan aiyukanku daga gare ku, kuma za mu
shigar da ku mashiga ta karimci" [Nisa'i: 31].
Tanadi ga mutuwa yana kasancewa ta hanyar
BADA HAQQOQIN HALITTU DA KUMA QIN TOZARTA SU, KO JINKIRTA BAYAR DA SU: Saboda
haqqin Allah, mai yiwuwa ne ya yafe abinda yake qasa da shirka. Amma haqqoqin
halittu, to su kam Allah (تعالى) baya
yafe su, sai ta hanyar xaukar haqqin daga wanda ya yi zalunci, da bayar da
haqqin ga wanda aka zalunta.
Tanadi ga mutuwa yana kasancewa ta hanyar
RUBUTA WASIYYA, da kuma kada mutum ya yi sakaci kan haka.
Tanadi ga mutuwa yana kasancewa ta hanyar
Mutum ya kasance YANA SHIRYE KAN ZUWAN MUTUWA
a kowani lokaci, wannan ne kuma yasa yayin da faxin Allah ta'alah, ya
sauka:
"فمَن يُرد
الله أن يهديه يشرح صدره للإسلام".
Ma'ana: "Duk wanda Allah
yayi nufin ya shiryar da shi sai ya buxa qirjinsa domin musulunci" [An'am:
125] Sai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya
ce:
"Haske ne Allah ya ke jefa shi a
cikin zuciya", (Sahabbai) sai suka ce: Menene alamar wannan ya
Ma'aikin Allah? Sai ya ce:
"Mayar da lamari zuwa gidan dawwama
(wato: lahira), da nisantar gidan ruxi (duniya), da
kuma yin shiri ga mutuwa, gabanin saukanta".
Kuma
samun rabo ko rabauta shine, Mai mutuwa a cike masa rayuwarsa da aikin
alkhairi, saboda Ya zo cikin hadisi cewa: "Aiyuka suna
kyau ne da abinda aka cike su da shi".
Kuma ya zo daga Mu'azu (رضي الله عنه) ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya
ce:
"Wanda qarshen maganarsa ita ce:
Kalmar LA ILAHA ILLAL LAHU, Ya shiga aljannah", Abu-Dawud ya
ruwaito shi da Alhakim da isnadi ingantacce.
Kuma
yana daga cikin ababen da yin aiki da su sunna ne mai qarfi: LAQQANA WA mutumin
da yake kan yanayi na mutuwa kalmar shahada (لا إله
إلا الله), cikin tausasawa, ta hanyar mutum ya riqa
ambaton wannan Kalmar; don mai mutuwan ya tuna ta, amma kada ya takura masa;
saboda yana cikin musiba da baqin ciki mai tsanani, An ruwaito daga Abu-Sa'id
Alkudriy (رضي الله عنه) ya ce: Manzon
Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Ku laqqana wa mamatanku kalmar LA
ILA ILLAL LAHU", Muslim ya ruwaito shi.
Rashin
rabo kuma da tavewa suna nan ne cikin: Gafala da lamarin mutuwa da mancewa da
ita, da kuma barin yin tanadi don ita, da tsaurin ido wajen aikata savo da
zunubai, da tozarta tauhidin Ubangiji mabuwayi da xaukaka, da qetare iyaka, da
yin zalunci ta hanyar zubar da jini na haram, da cin dukiya ta haram, da
tozarta haqqoqin halittu, da lumewa ko aukawa cikin ababen sha'awa da jin daxi;
waxanda aka haramta, har mutuwa ta sauka wa mutum, a lokacin da nadama ba za ta
yi amfani ba, kuma ba za a jinkirta ajali ba, Allah ta'alah yana cewa:
"Har idan mutuwa ta je wa xayansu, sai ya
ce: Ya Ubangijina, Ka mayar da ni (duniya) * Tsammanina zan aikata aiki na
kwarai cikin abinda na bari, Kayya! Lallai ne ita kalma ce, da yake faxinta,
alhali kuwa a baya gare su akwai wani shamaki har ranar da za a tayar da su" [Muminun:
99-100].
Kuma
a yinin qiyama bayyanar da hasara, da nadama suna qara girma, Allah ta'alah
yana cewa:
"Kuma ku bi mafi kyan abinda aka saukar zuwa
gare ku daga Ubangijinku, a gabanin azaba ta zo muku bisa kwatsam, alhali ba ku
sani ba * Sai wata rai ta ce, Ya kaitona (nadamata) akan abinda na yi sakaci ta
vangaren Allah, kuma lallai na kasance daga masu izgili * Ko kuma, ka da rai ta
ce: Da Allah ya shiryar da ni, da na kasance daga masu taqawa * Ko kuma kada
rai ta ce: a lokacin da take ganin azaba, Da ace ina da wata damar komawa
(duniya) domin in kasance daga Masu kyautatawa * Na'am, lallai ne ayoyina sun
je maka, sai ka qaryata, kuma ka yi girman kai, kuma ka kasance daga kafirai"
[Zumar:55-59].
Allah yayi albarka wa Ni da Ku cikin alqur'ani
mai girma! Kuma ya amfanar da Ni da Ku da abinda ke cikinsa na ayoyi, da
tunatarwa mai hikima, kuma ya amfanar da mu da shiriyar shugaban Manzanni, da
maganganunsa miqaqqu.
Ina faxar Magana ta wannan, kuma ina neman
gafarar Allah, wa Ni da Ku, da sauran Musulmai; sai kuma ku nemi gafararSa;
saboda shi Mai yawan gafara ne, Mai jin qai.
HUXUBA TA BIYU
Godiya
ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, Mai mulki, Mai gaskiya, Mabayyani, yana
da hikima cikakkiya, da hujja; da ta kai maqura; Da yayi nufi; da ya shiryar da
ku gabaxaya. Ina yin godiya wa Ubangijina, ina yin yabo a gare shi, ina tuba
zuwa gare shi, kuma ina neman gafararSa,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai
Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya,
Mai qarfi, Mai girma.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma
shugabanmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa, Mai gaskiyar alkawari Amintacce.
Ya
Allah kayi qarin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa, da waxanda suka
bi su da kyautatawa (bi da bi) har zuwa ranar sakamako.
Bayan
haka!
Ku
kiyaye dokokin Allah iyakar kiyayewa, saboda
babu mai tsira face masu taqawa, kuma babu mai hasara sai masu sakaci
mavarnata.
Ya
ku musulmai…
Ku
kula da yin aiki da sabuban jawo kyakkyawar qarshe (حسن الخاتمة), ta hanyar tsayar da rukunannan musulunci
guda biyar, da nisantar nau'ukan savo, da dangogin zalunci.
Kuma
yana cikin manyan sabuban samun kyakkyawan qarshe a wajen mutuwa: DAWWAMA AKAN
ROQON ALLAH samun kyakkyawan qarshe, Allah mabuwayi da xaukaka yana cewa:
"Ku roqe ni zan amsa muku, lallai ne
waxannan da suke girman kai ga barin bauta a gare ni, za su shiga jahannama
suna qasqantattu" [Gafir: 60].
Kuma
addu'a shina abinda ya tattara alkhairi gabaxayansa, An ruwaito daga Annu'uman
xan Bashir (رضي الله عنهما), ya ce: Manzon
Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Addu'a shine bauta",
Abu-Dawud ya ruwaito shi da Tirmiziy, kuma ya ce: hadisi ne mai kyau
ingantacce.
Kuma ya zo cikin wani hadisi cewa:
"Duk wanda ya yawaita faxin addu'ar:
"اللهم أحْسِن
عاقبتَنا في الأمور كلها وأجرنا من خزي الدنيا وعذاب الآخرة".
Ma'ana:
"Ya Allah ka kyautata qarshenmu cikin lamura dukansu, kuma ka
tseratar da mu daga kunyar duniya da bala'inta, da kuma azabar lahira = TO
WANNAN MUTUMIN ZAI MUTU GABANIN BALA'I YA RISKE SHI".
Su
kuma SABUBAN DA SUKE JAWO MUMMUNAN QARSHE
a lokacin mutuwa sune: Tozarta haqqin Allah, da haqqoqin halittu, da
dogewa akan aikata manyan zunubai da laifuka, da yin sako-sako da lamarin
girman Allah, da karkata zuwa ga duniya, da mance gidan lahira
Bayin Allah!
"Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan annabin, ya ku
waxanda su ka yi imani ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Duk wanda ya yi salati guda xaya a gare ni, to Allah zai salati
a gare shi guda goma saboda shi".
Sai ku yi
salati, da sallama ga shugaban na farko da na qarshe, kuma jagoran manzanni.
Ya Allah! Ka yi salati wa annabi
Muhammadu da iyalan annabi Muhammadu kamar yadda ka yi salati wa annabi
Ibrahima da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai Abun godiya ne, Mai girma.
Ya Allah! Ka yi albarka wa annabi
Muhammadu da iyalan annabi Muhammadu kamar yadda ka yi albarka wa annabi
Ibrahima da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai Abun godiya ne, Mai girma.
Ya Allah! Ka yarda da sahabbai
gabaxaya, da kuma khalifofi shiryayyu, kuma shugabanni masu shiryarwa; Abubakar
da Umar da Usmanu da Aliyu, da sauran sahabban annabinka gabaxaya,
Ya Allah! Ka yarda da tabi'ai da
waxanda suka bi su da kyautatawa (bi da bi) har zuwa ranar qarshe,
Ya Allah! Ka yarda da mu tare da su,
da baiwarka, da rahamarka ya mafi rahamar masu rahama.
Ya Allah! Ka xaukaka musulunci da
musulmai (sau uku), ka kuma qasqantar da kafirci da kafirai, Ya Ubangijin
talikai.
Ya
Allah ! ka qasqantar da bidi'a da 'yan bidi'a har zuwa tashin
kiyama.
Ya
Allah ! ka sanya mu daga cikin waxanda suke yin riqo da sunnar Annabinka
Muhammadu (صلى الله عليه وسلم).
Ya
Allah ! ka sanya mu daga cikin masu riqo da littafinka, da kuma sunnar
Annabi (صلى الله عليه وسلم).
Ya
Allah! Lallai ne mu muna roqonka, da ka kyautata qarshemu cikin lamura
gabaxaya, kuma ku tseratar da mu daga wulaqancin duniya da bala'inta, da kuma
azabar lahira.
Ya
Allah! Lallai ne mu muna roqonka, da ka taimake akan magagi ko mayen da
yake cikin mutuwa, Ya Ubangijin talikai.
Ya
Allah! Lallai ne mu muna roqonka, da ka sanya qarshen rayuwarmu a nan
duniya shine ka yarda da mu, Ya Ma'abucin girman jalala da karramawa. Kuma ka
sanya mafi alherin yininmu ya zama shine ranar da za mu sadu da kai, Wa wanda
yafi masu karramawa girman karimci.
Ya
Allah ! Lallai mu muna roqonka aikata aikhairori, da barin aikata ababen
qi, da son miskinai, Ya Ubangijin talikai.
Ya
Allah! Ka nuna mana gaskiya a matsayin gaskiya, kuma ka azurta mu da binta,
kuma ka nuna mana qarya a matsayin qarya, ka azurta mu da nisantarta, kuma kada
ka sanya varna ta cakuxe mana da gaskiya; tsoron kar mu vata.
Ya
Allah! Ka gafarta mana abinda muka gabatar, da abinda muka jinkirta, da
abinda muka asirce, da abinda muka bayyana, da abinda kai ne kafi mu saninsa.
Ya Allah ! Lallai muna roqonka
aljanna da abinda ke kusantarwa zuwa gare ta na zance ko aiki, kuma muna neman
tsarinka daga wuta da abinda yake kaiwa zuwa gare ta; na zance ko aiki.
Ya Allah! Ka taimake mu akan
ambatonka da yin godiya a gare ka, da kyautata ibadarka, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah! Ka gafarta wa mamatanmu da
mamatan musulmai, Ya Allah! Ka gafarta wa mamatanmu da mamatan musulmai,
kuma ka yalwata musu kabarinsu akansu, kuma ka haskaka musu cikinsa, Ya
Ma'abucin girman jalala, da karramawa. Kuma ka tsare su daga azabar qabari, Ya
Mafi jin qan masu jin qai.
Ya Allah! Ya Mafi jin qan masu jin qai, Ya
Wanda yafi dukkan masu karramawa yin baiwa, Kada ka dogarar da mu ga
kanmu, koda daidai da kyaftawar ido.
Ya Allah! Ka gyara mana sha'anoninmu
gabaxayansu.
Ya Allah! Ka yaye baqin cikin masu baqin ciki daga
cikin musulmai, Ya Allah! ka biya bashi wa waxanda ake binsu bashi daga
cikin musulmai.
Ya Allah! Ka bada waraka ga marasa
lafiyanmu da marasa lafiyan musulmai (sau uku), da rahamarka Ya Mafi jin qan
masu jin qai.
Ya Allah!
Ka tseratar da mu, kuma ka tseratar da zurriyarmu, daga Iblis da zurriyarsa, da
shaixanunsa da rundunarsa, da makircinsa Ya Ubangijin talikai (sau biyu),
lallai kai mai iko ne akan komai.
Ya Allah!
Ka tseratar da musulmai daga Iblis da zurriyarsa, da shaixanunsa Ya ma'abucin
girman jalala, da karramawa.
Ya Allah!
Lallai mu muna roqonka Ya Mafi jin qan masu jin qai, muna roqonka Ya Allah! Da
bada mafita wa musulmai daga kowani baqin ciki, Ya Allah! Ka haxa tsakanin
zukatansu, kuma ka daidaita su, ka shiryar da su hanyoyin shiriya, kuma ka
fitar da su daga duffai zuwa ga haske.
Ya Allah! Ka lalata kaidin maqiya
musulunci ya Ubangijin talikai, Ya Allah ka ruguza makircin maqiya
musulunci, Ya Ubangijin talikai, Ya Allah! Ruguza tsare-tsaren
maqiya musulunci; waxanda suke tsattsara su domin suyi kaidi wa musulunci da
musulmai, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah! Ka kiyaye qasashenmu daga
kowani mummuna, ko abun qi, lallai kai akan kowani abu mai iko ne.
Ya Allah! Ka saukar da aminci –Ya
Ubangijin talikai- da imani a qasashen musulmai.
Ya Allah! Ka xauke wa musulmai
fitintinu masu vatarwa.
Ya Allah! Ka xauke fitintinu masu
vatarwa wa musulmai, Ya mafi jin qan masu jin qai, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah! Ka ciyar mai jin yunwa daga
cikin musulmai, kuma ka tufatar da wanda ke cikin tsiraici, Ya Allah ka amintar
da wanda yake cikin tsoro daga cikinsu, ya mafi jin qan masu jin qai. Kuma kada
ka dogarar da su ga kayukansu koda daidai da kyaftawar ido.
Ya Allah! Ka yi taufiqin dace ga
Mai hidiman harami biyu, zuwa abinda kake so kuma ka yarda, Ya Allah ka datar
da shi zuwa ga shiriyarka, kuma ka sanya aikinsa cikin yardarka. Ya Allah ka
taimake shi akan kowani alheri. Ya Allah ka taimaki addininka da shi, Ya
Ubangijin talikai. Ya Allah ka azurta shi da lafiya, Ya Ubangijin talikai, kuma
ka taimake shi a lamuran addininsa da duniyarsa, Ya Ma'abucin girman jalala da
karramawa.
Ya Allah! Ka datar da masu na'ibtarsa
guda biyu, zuwa ga abinda kake so kuma yarda da shi, da kuma zuwa ga abinda
akwai alkhairi a cikinsa ga musulunci da musulmai, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah! Ka gafarta mana, lallai kai
ka kasance Mai yawan gafara, kuma ka saukar da ruwan sama akanmu, na mamako, Ya
Allah ka sanya mana albarka cikin abinda k aba mu.
Ya Allah! Lallai mu muna neman
tsarinka daga gushewar ni'imarka, da canzawar lafiyarka, da zuwan uqubarka
kwatsam, da kuma xaukacin abinda ke sa fushinka, Ya Mafi jin qan masu jin qai.
"Ya Ubangijinmu! Ka
bamu mai kyau a duniya, ka bamu mai kyau a lahira, kuma ka kare mu daga azabar
wuta"
[Baqarah:
201].
Ya ku bayin Allah!
"Lallai Allah yana yin umurni
da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha
da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah zai
riqa ambatonku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah
shine mafi girma, Lallai kuma Allah ya san abinda kuke aikatawa.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
………………….
No comments:
Post a Comment