WASSU
DAGA CIKIN ZANCEN ADALAI KAN SAHABIN NAN; KHALIFA MU'AWUYA (r a)
مِن أقوال المُنْصفين في الصحابي الخليفة
معاوية t
Wallafar
As sheikh
Abdul-Muhsinil bn Hamad Al-Abbad Albadr
Fassarar
Abubakar Hamza
Zakariya
Abubuwan da ke
cikin Littafin
Gabatarwa………………………………………………………….
Dalilin zaban
Mu'awuya ya zama abin zance koma bayan waninsa
daga Sahabbai …………………………………………………......
Wassu daga cikin
zancen magabata kan Sahabbai:
1-
Fadin Imamud
Dahawi…………………………………………..
2-
Zancen mai sharhin
Dahawiyya…………………………………
3-
Maganan
Bagawi………………………………………………….
4-
Maganan
Shaukani…………………………………………………
5-
Maganan
Nawawiy………………………………………………..
6-
Fadin Ibnu Umar a tafsirin fadin
Allah ﴿ للفقراء المهاجرين﴾ ………….
7-
Maganan Imam
Ahmad;………………………………………….
8-
Zancen Imamus sabuniy;
…………………………………………
9-
Fadin Shekhul Islam ibnu
taimiyyata……………………………….
10-
Maganan Shehi Yahya bn Abibakar
al'amiri alyamani……..
11-
Maganan Abil Muzaffaris
sam'ani………………………….
12-
Maganar Imam Ahmad da Maimuni ya
ciro………………..
13-
Fadin Abi zur'atur
razi…………………………………….
14-
Zancen Alhafiz Ibnu Kasir………………………………….
15-
Zancen Alhafiz Ibnu
Hajar………………………………….
Wassu daga
Maganan Adalai kan Mu'awuya:
1.
Maganan Muwaffag Ibnu
kudamata…………………………….
2.
zancen mai sharhin
Dahawiyya……………………………………
3.
Maganan
Zahabi…………………………………………………..
4.
Maganan Imamu
Ahmad………………………………………….
5.
maganan Umar bn Abdil
aziz…………………………………….
6.
Maganan Abi zur'atur
razi……………………………………….
7.
Amsar Imamu Ahmad kana bin day a
faru tsakanin Aliyu da Mu'awuyatu (r
a)…………………………………......................
8.
Fadin Ibnul
Mubaraak…………………………………………...
9.
Fadin Fadlu bn
Ziyad…………………………….……………….
10.
Foron Umar bn Abdul aziz ga
Mutumin
da ya zagi Mu'awuyata……………………………………………
11.
Fadin Abu taubata arrabi'u bn
Nafi'i al-halabi………………..
- Bukahari
babi ya kulla don ambaton Mu'awuyatu……………..
- hadisi
cikin Sahihu Muslim kan falalar Mu'awuyatu…………
- Maganan
Nawawi kan sharhin hadisin………………………….
- Fadin
Ibnu khasir a tafsirin ﴿ ومن قتل مظلوماً﴾ ……………………
-
Fadin Hafiz Ibnu hajar cewa( Falalan Ansaar Waninsu zai yi
tarayya da su; ): ………………………………………………
- Fadin
Imam As-sharif Muhammad bn Ibrahim bnul Murtada
Kan cewa kin Ali ( r a) abin sani kawai ya
zama alamar munafirci
ne a farkon musulunci ne ; saboda…………………………….
-
Maganan Zahabi wajen amintuwar dan bidi'a ( wato:
a ce: shi (ثقة) ne );
……………………………………………..
-
Maganganun Ibnu Taimiyyata kan Mu'awuyatu da kuma abin da ya faru tsakanin
Sahabbai;……………………………………………
-
Dunkulen abin day a wajabta a kulle/ a kudure kan abin day a gudana tsakanin
Sahabbai lokaci fitina…………………………………
GABATARWA
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah
Ubangijin Halittu, Mai rahama Mai jin kai, Mai mulkin Ranar sakamako, Kai kadai
kawai Mu ke bautawa, Kuma kai kadai Mu ke neman taimako, Ka shiryad da mu hanya
madaidaiciya, Hanyar wadanda ka yi ni'ima a gare su ba wadanda ka yi fushi
akansu ba, kuma ba batattu ba.
Ya Allah ka yi yabo wa (Annabi) Muhammadu,
da kuma Iyalan (Annabi) Muhammadu, kamar
yadda ka yabi ( Annabi) Ibrahima da kuma Iyalen (Annabi) Ibrahim, Lallai kai
abun yabo ne Mai daukaka. Ya Allah ka yi albarka wa (Annabi) Muhammadu da
Iyalen (Annabi) Muhammadu, kamar yadda ka yi albarka wa (Annabi) Ibrahima da
Iyalen (Annabi) Ibrahima, Lallai kai abun yabo ne Mai daukaka. Ya Allah ka kara
yarda da Sahabbai gaba daya, da ma Wadanda su ka bisu da kyautatawa zuwa Ranar
sakamako, ka hada da mu da baiwarka da karamcinka, Ya mafificin masu rahama, (
Ya Ubangijinmu! Ka gafarta mana mu da 'Yan Uwanmu da su ka rigaye da Imani,
Kuma kada ka sanya hassadan Wadanda su ka yi Imani cikin Zuciyarmu, Ya
ubangijinmu Lallai kai Mai tausasawa ne Mai rahama).
Bayan haka:
Ya ku 'Yan Uwana Masu karamci! wannan wani
zance ne kan Mu'awuya ibn Abi Sufyan – Allah ya yarda da su – wanda ya Kunshi
wassu daga cikin zancen Sashen Adilai a kansa, ( A nan ) Banso in yi Magana kan
Dangantakansa, Rayuwarsa, da Hadisinsa (da ya ruwaito daga Manzon Allah) da
kuma duk abin da ya ke da alaka da shi ba, kawai akalar zancen za ta kasance ne
a wani bangare ayyananne; Shi ne Maganan Adalai a kansa; Wanda su ne Allah ya
datar da su Su ka bi tafarki madaidaici kansa, kuma Su ka fadi abin day a dace
da shi, kuma abin da ya dace da matsayinsa, sannan basu auka cikin abin da wassu
su ka auka ba; wanda datarwan Allah bai gamu da su ba, sai ya zamo abin da
Kubutansu da Tsiransu da Rabautarsu ba kasance daga wajensu ba.
Shi dai Mu'awuya bn Abi Sufyan daya daga
cikin Sahabban da Allah ya karrama su da abotar Annabinsa Muhammad (S A W); Don
haka duk kan abin da ya dace ace akan Sahabbai da ke da alaka da Falalarsu a
gabadayance, da abin da ya Wajaba ( Na hakkinsu akan Mutane) gaba daya To
Mu'awuya ( r a) zai shiga cikin haka. Sannan (Malamai) Su na da magana da kebe
shi na abin day a dace a siffanta shi da shi kuma a fada akansa (Allah ya yarda
da shi kuma ya yardad da shi wa Mutane). ( Shi kuma) abin da zan fada a kansa
bani da komi cikinsa sai Kokarin tattara shi daga Littafai, wanda Masu su Sun
yi kokari: Wajen hidima wa Sunnar Annabi ( s a w), da kuma bayanin abin da ya
Wajaba (na hakkin) Sahabbai (r anhum).
Don haka zan zo da Magana kan Sahabbai gaba
daya; wanda Mu'awuya bn Abi Sufyan ya shiga ciki, Sannan Sai na zo da maganan
da ta kebanci Mu'awuya (R A).
DALILI DA YASA
NA ZABI LECCA KAN MU'AWUYA (R A)
Ta yuwu Wani ya yi tambaya; Ya ce: Meyasa ka
zabi Mu'awuya bn Abi Sufyan ka ware shi da Lecca ka kuma bar Waninsa?
Amsa kan haka: Shi ne; Daya daga cikin
Magabata ( Salaf) - Shi ne; Abu Taubatil Halabiy – Ya fadi wata Magana da ta
shahara daga gare shi :
قال أبو توبة الحلبي:
((
إن معاوية بن أبي سفيان
سترٌ لأصحاب رسول الله صلى الله عليه وسلم؛ فمن كشف الستر اجترأ على ما وراءه )).
Ma'ana: " Lallai
shi Mu'awuya bn Abiy Sufyan Labule ne da ya suturce Sahabban Manzon Allah (s a w);
Duk Mutumin da ya yaye wannan Labulen kuwa to ba makawa zai shiga abin da ke
bayansa". Kenan Duk Mutumin da ke Magana kan Mu'awuya (r a), sannan ya ke
feke Ido ya fadi maganan da bata dace da shi ba, To zai masa sauki kuma ya yi
kan Waninsa; ( Kai!) kuma al'amarin bai kasance zai takaita a kansa ba! A'a!
hasali ma! zai kai ya yi Magana kan Wanda ya fi shi alkhairi, wanda ya fi shi
falala, Kai! Har kan fiyayyen Hallita bayan Annabawa da manzanni; Abubakar
Siddiq, sannan Umar ibnul khaddab, sannan Usman ibn affan, sannan Aliyu ibn Abi
Dalib (R Anhum wa ardahum) (Hakan kuwa duka ya samu! Wal Lahul Musta'an!) Haka
kuma wassun wadannan na daga Sahabbai suma korafe-korafe ya samu akansu; a
hakikan gaskiya; ( Duk) abin day a samu na maganganu da ya dace da su To su
(sahabban (Allah ya yarda da su kuma ya yardad da su)) Sun cancanci hakan, Shi
kuma wanda ya fadi maganar ya fadi abin a yabe shi. Shi yasa ma Wadannan
Magabatan da su ka yi Magana kan wadancan zababbun – Allah ya yarda da su kuma
ya yardad da su – Ambatonsu be gushe ba yana kan rasan Mutane, Ana kuma
ambaton: Maganansu mai kyau, kuma ana nema musu rahamar ( Allah), sannan ana
yabonsu; saboda; Sun Tsayu kana bin day a wajaba akansu na ( Hakkokin) Sahabban
Manzon Allah ( s a w) kuma Allah ya kara da Sahabbai gaba daya.
Amma wanda ya yi Magana a kansu da maganan
da bata dace da su ba; To alal hakika bai cutar da su ba, sai dai ma cutar da
kansa da ya yi; Bayani kan wannan shi ne: Su dai Sahabbai (r anhum wa ardahum)
Sun isa zuwa ga abinda su ka gabatar (aikata), kuma hakika sun gabatar da
alkhairi mai yawa, don sun gabatar da manyan ayyuka ne da su ka yi su tare da
Manzon Allah ( s a w), Don haka wanda ke Magana kansu da abin da be dace da sub
a a hakikance ba cutar da sub a, hasali ma cutar da kansa ya ke yi, Su kuwa
hakan yakan zama kari ne ga kyawawansu ( bayan mutuwarsu), kuma daguwa ne ga
darajarsu; saboda Idan ya yi Magana kansu ba tare da hakki ba To sai a dibi
daga kyawawan mai maganan a basu – idan yana da kyawawan fa kenan – su kuwa sai
hakan ya zama daguwar darajarsu, alhalin kuwa suna kubutattu daga sukan mai
suka, kuma dai Haushin Karnuka ai baya cutar da Gajimare!
FALALAR SAHABBAI
( R A)
Allah ( s w) yayin da ya turo Manzonsa
Muhammad ( s a w), kuma ya cike Manzonci da shi, ya kuma sanya Manzoncinsa ( s
a w); Cikakke, da ya game ( komai) kuma Madawwami har zuwa Allah ya gaje kasa
da ma wadanda su ke kanta, To Allah ( s w) ya kebe shi da Sahabbai da ya zabe
su don abotansa, kuma Allah ya nufi su kasance a zamaninsa sai kuwa su ka
kasancen, kuma su ka tsayu wajen aikata duk abin da su ke da iko akansa na
kokari cikin Jihadi tare da shi kan hanyar Allah, da kuma yada Sunnarsa, da
karban abin da ya zo da shi – yabo da aminci su kara tabbata a kansa – Sai su
ka zamo su neواسطةtsakanin Manzon (s a w) da wadanda
su ka zo bayansu. Don haka; Duk wanda ya soke su abin sani kawai yana suka ne
ga 'Yan tsakani da suka kulle tsakanin Musulmai da Manzon Allah ( s a w), kaga
kuwa mai sukansu na yin hakan ne ga magami mai karfin da ya kulla mutane da Manzonsu
( s a w).
Suna kuma da wata kebebbiya da ta kebe su; Ita
ce: Lallai su an zabe su don Abotar Manzon Allah (S A W), Allah kuma ya daukaka
su a wannan Gidan Duniyar suka yi dubi zuwa ga ( Fiskar Fiyayyen Hallitu S A W
), wanda haka bai samu ba ga Wani In ba su ba, ( Allah ya yarda da su kuma ya
yardad da su), kuma Allah ( S W) ya kara Daukaka su Su ka ji Maganan Manzo daga
Bakinsa madaukaki ( Yabo da amincin Allah su kara tabbata a gare shi); (
Sahabbai) su ka karbo wannan alkhairin, da wannan hasken, da wannan shiriyar,
sannan su ka mika shi ga wadanda su ka zo bayansu; don haka; Duk Mutumin day a
zo bayansu, Su na da مِنةٌ a kansa, kuma suna
da Falala a kansa; saboda Wannan shiriya da wannan Haske da wannan alkhairin
day a kasance musu bai kasance ba sai ta hanyar Wadancan Mutanen alkhairi ( R
Anhum wa ardahum), kuma hakika ya tabbata daga Manzon Allah ( S A W) lallai shi
ya ce:
[ من دعا إلى هدىً كان له من الأجر مثل أجور من تبـِعَه لا ينقص
ذلك من أجورهم شيئاً، ومن دعا إلى ضلالةٍ كان عليه من الإثم مثل آثام من تبـِعَه
لا ينقص من آثامهم شيئاً ]
Ma'ana: [ Duk
wanda ya yi kira zuwa ga wata shiriya, To yana kwatankwacin ladan wanda ya
bishi, ba tare da an tawaye musu ladansu da komai ba, haka kuma; Wanda ya yi
kira zuwa ga wata Bata To akwai Kwatankwacin zunubin Wadanda su ka bi shi
akansa, ( hakan kuma) ba zai zunubinsu da komai ba] Don haka Wannan Hadisi madaukaki ( Sahabban
Annabi ( S A W) Su na da rabo mai tsoka na daga Abin da ke hukuntawa, saboda;
Su din nan Su ne su ka karbo wannan Shiriyar da wannan Hasken daga Manzon Allah
( S A W ) Su ka kuma mika shi zuwa ga wanda su ke bayansu; Shi ya sa Duk
Mutumin day a amfana daga gare shi ( Wato: Musulunci da Shiriya) To suna da
irin Ladan da Shi zai samu, har zuwa Allah ya gaje Kasa da abin da ke kanta.
Kafinsu kuma ( Wato: Sahabban) Manzon Allah (S
A W) Wanda ya zo da wannan alkhairin da kuma wannan Shiriyar, Duk Mutumin day a
shiriya ya kuma Shiga Addinin Allah, ya aikata mai kyau, To Allah zai saka wa
Manzonsa ( S A W) da kwatankwacin abin day a saka wa Wancan Ma'aikacin, ba tare
da ya rage wa Ma'aikacin komi ga Ladansaba, saboda; Manzon Allah shi ya kira
Mutane zuwa ga wannan Shiriyar; Don haka; Yana da kwatankwacin Ladan Duk Wanda
ya amfana da wani alkhairi ta sababinsa ( Yabon Allah da amincinsa Su kara
tabbata a gare shi), Sahabbansa kuma; Suma sun a da rabo mai tsoka na Ladan;
saboda Su su ka karbi wannan shiriyar (daga wajensa) kuma Su ka mika tag a
Wadanda su ka tafo bayansu, Don Su ne su ka Tara Qur'ani(جمع القرآن),kuma Su ne; Su
ka Haddace shi, Kuma Su ne Su ka mika shi zuwa ga na bayansu, Kuma Su ne Su ka
karbo Sunnar Manzon Allah ( S A W), kuma Su ka mika ta zuwa ga na bayansu, Sai
ya zama Su na da Lada mai yawa, mai girma, sannan Sun samu rabo mai tsoka na
Addu'ar da Manzon Allah ( S A W) cikin Inganceccen Hadisin day a ce a cikinsa:
[ Allah ya haskaka Mutumin day a ji maganata kuma ya kiyaye ta, ya kuma isar da
ita kamar yadda ya ji ta…]. To su Wadannan (Sahabban) Su ne su ka ji daga gare
shi kai tsaye, ba tare da Sha-maki ba/ tafinta ( 'Dan tsakani), Wannan kuma
wani kebebben abu ne da su kawai su ka kebanta da shi, Waninsu bai yi tarayya
da su cikinsa ba, ( Allah ya kara yarda da su kuma ya yardad da su).
Kenan; Wadannan Mutanen alkhairin, wadannan
Magabata (Sahabban Manzon Allah S A W) Su ne Kulli mai karfi da ya kulle mu da
Manzon Allah ( S A W); Don haka; Duk wanda ya soki wannan kullin To hakika ya
yanke Madanganciya da ta dangantar da
tsakaninsa da tsakanin Manzon Allah ( S A W), Wannan kuwa shi ne makura ta bata
da tabewa! Allah ka tsare mu!
WASSU DAGA CIKIN
ZANCEN MAGABATA KAN SAHABBAI ( R ANHUM)
Bayan haka zan karanto mu ku wani daga cikin
abin da Magabatan wannan al'umman suka fada kan Sahabban Manzon Allah ( S A W)
gaba dayansu, wanda Mu'awuya ( R A) ya shiga cikinsu, sai kuma na biyo bayansa
da abin da su ka fada kansa shi kadai dinsa;
1.
Dahawiy ya na fadi cikin Shahararriyar
Akidarsa ya na cewa:
" ونحبّ أصحاب رسول الله صلى الله عليه وسلّم ولا نفرط في حبّ أحدٍ منهم ولا
نتبرّأ منهم، ونبغض من يبغضهم، وبغير الخير يذكرهم، ولا نذكرهم إلا بخيرٍ، وحبّهم
دينٌ وإيمانٌ وإحسانٌ، وبغضُهم كفرٌ ونفاقٌ وطغيانٌ".
Ma'ana: "
Muna son Sahabban Manzon Allah ( S A W), kuma wuce Gona-da-iri cikin son Wani
daga cikinsu, kuma bama barranta daga
Wani daga cikinsu, kuma Mu na kin mai kinsu,
Mai ambatonsu ba da alkhairi ba, Ba ma kuma ambatonsu sai da
alkhairi, kuma son su Addini ne da Imani
da Ihsan, kinsu kuma Kafirci ne da Munafurci da ketare Iyaka".
2.
Mai sharhin Dahawiyya yana cewa:
" فمن أضلّ ممن يكون في قلبه غلٌّ على خيارِ المؤمنين، وساداتِ أولياء الله
تعالى بعد النبيين، بلْ قد فضلهم اليهودُ والنصارى بخصلةٍ؛ قيل لليهود: من خير أهل ملّتكم؟ قالوا أصحاب موسى. وقيل للنصارى: من خير أهل ملّتكم؟ فقالوا: أصحاب عيسى. وقيل للرافضة: من شرّ أهل ملّتكم؟ فقالوا: أصحاب محمدٍ، ولم
يستثنوا منهم إلا القليل، وفيمن سبوهم من هو خيرٌ ممن استثنوهم بأضعاف مضاعفة".
Ma'ana: "
Ai babu wanda yafi 'bata fiye da wadda yak e kasancewa a cikin zuciyarsa;
Hassada ga zababbun muminai, kuma shugabannin Waliyan Allah bayan Annabawa, (
Irin wannan Mutanen ) Yahudawa da Kirista ma sun fi su da sifa 'daya; saboda an
ce wa Yahudawa: Wanene mafi alkhairin daga cikin ma'abota addininku? Sai su ka
ce: Sahabbn Musa.
An ce wa Kirista; Wanene mafi alkhairin daga
cikin ma'abota addininku? Sai su ka ce: Abokan Isa.
Sai a ka ce wa 'Yan shi'a; Wanene mafi sharri
daga ma'abota addininku? Sai su ka ce: Abokan Muhammad; bas u kuma toge kowa
daga cikinsu ba sai ka'dan. Daga cikin wanda su ka zaga akwai wadda ya fi wanda
su ka toge da ninkin-ba-ninkiya ".
3.
Bagawiy a cikin sharhin Sunna ya na cewa:
" قال مالكٌ: من يبغض أحداً من أصحاب
رسول الله صلى الله عليه وسلم، وكان في قلبِه عليه غلٌ فليس له حقٌ في فيء
المسلمين، ثم قرأ قوله سبحانه وتعالى: ( ما أفاء الله على رسوله
من أهل القرى فلله وللرسول ولذي القربى) إلى قوله: ( والذين جاءوا من بعدهم يقولون ربنا غافر لنا
ولإخواننا الذين سبقونا بالإيمان)الآية. وذكِر بين يديه رجلٌ ينتقص أصحاب رسول الله صلى الله
عليه وسلم فقرأ مالكٌ هذه الآية ( محمد رسول الله والذين
معه أشداء على الكفار) إلى قوله: ( ليغيظ بهم الكفار). ثم قال: من أصبح من الناس في
قلبه غلٌ على أحدٍ من أصحاب النبيّ صلى الله عليه وسلم فقد أصابتْه هذه الآية.
Ma'ana: " Malik ya ce: Duk wadda ya ki ( Mutum)
'daya daga cikin Sahabban Manzon Allah ( s a w) kuma ya zama a cikin zuciyarsa
akwai yi masa hassada; To ba shi da wani hakki cikin Fai'in Musulmai ( wato:
dukiyan da Kafirai su ka gudu su ka bar mu su, ba tare da sun yi ba-ta-kashi
ba) sannan ya karanta fa'din Allah ma'daukaki: " Dukiyar da Allah ya bawa
Manzonsa na daga 'Yan alkaryu; to na Allah ne da Manzonsa da kuma makusata da
Marayu da Miskinai da kuma 'Yan hanya ( hakan kuma ya kasance ne ) don kar ya
zama maciya ce tsakanin Mawadata a cikinku …zuwa fadinsa: " Na talakawa
masu kaura da a ka fitar da su daga gidajensu da dukiyansu… da kuma wadanda su
ka tanadi Gida da imani gabaninsu … zuwa fa'dinsa: " da wadanda su ka zo
bayansu su ke cewa: ya Ubangijinmu ka gafarta mana (mu) da 'Yan' uwanmu da su
ka rigaye mu da imani, Kuma kada ka sanya hassadan wadanda su ka yi imani cikin
zuciyarmu, ya Ubangijinmu lallai kai mai tausayi ne mai rahama". Kuma an
ambaci wani Mutumi a gabansa (Malik) ya kasance ya na 'bata ga Sahabban Manzon
Allah ( s a w); Sai malik ya karanta wannan ayar: " Muhammadu Manzon Allah
ne, Wanda ke tare da shi kuma Masu tsanani ne akan Kafirai, Masu rahama a
tsakaninsu, zaka gansu suna masu Ruku'I, Sujjada, Suna neman Falala daga
Ubangijinsu da kuma Yarda, Alamarsu na fuskarsu na gurbin Sujjada, Wannan shi
ne misalinsu cikin At taura, Misalinsu kuma cikin Injila: Kamar Shuka ne da ya
fitar da tofonsa na farko sannan ya yi karfi ya kuma yi kauri, ya daidaita kan
Kafafunsa, ya na burge Manoma don ( Allah) ya bakanta wa kafirai da su, …"
har zuwa fadinsa: " .. don ( Allah) ya bakanta wa kafirai da su"
sannan ya ce: " Duk wanda ya wayi gari daga cikin Mutane a zuciyarsa akwai
hassada ga 'daya daga Sahabban Annabi ( s a w); to wannan ayar ta same
shi".
4.
Shaukaniy yana fadi a tafsirin fadin Allah
madaukaki:
﴿ والذين جاءوا من بعدهم
يقولون ربنا غافر لنا ولإخواننا الذين سبقونا بالإيمان ولا تجعل في قلوبن غلاً
للذين ءامنوا ربنا إنك رؤوف رحيم ﴾
Ya ce – bayan ya fassara" Wa'danda
su ka zo bayansu" Ya na nufin: bayan Muhajruna da Ansaar; kuma su ne:
Wa'danda su ka bi su da kyautatawa = har zuwa ranar sakamako" Ya ce:
" Allah da tsarki ya tabbata masa ya umurce su baya da nema gafara ga
Muhajirun da kuma Ansaar da su nema daga Allah da tsarki ya tabbata masa = ya
cire kyashi da kiyayyar wa'danda su ked a imani gaba-'daya; wanda ko za su fara
shiga cikin wannan su ne: Sahabbai; saboda su ne: ma'daukakan Muminai, kuma
saboda jerin ayoyin a kansu a ke Magana; Don haka duk wadda bai nemi gafara wa
Sahabbai ba a gaba-'dayance, ya kuma ki neman yardan Allah a gare su; To ya
saba wa abin da Allah ya umurce shi da shi cikin wannan ayar.
In kuwa ya ji
hassadan su a zuciyarsa; To wannan fizga ne ya fizge shi daga She'dan, sannan
rabo mai gima na sabon Allah da kiyayyar Waliyyansa kuma zababbun Al'umman
Annabinsa ( s a w) ya auku a kansa, Sannan kofar tabewa ce ta bu'du a gare shi;
wadda zai bi ta ya fa'da Wutar Jahannama – matukar bai dawo da kansa ba;
ta hanyar fakewa zuwa ga Allah ma'daukaki da neman agajinsa kan ya cire abin
day a kwankwasa zuciyarsa da hassada ga mafi alkhairin Karni, kuma fiyeyyun
wannan Al'umma 'daukaka.
In abun nasa
ya wuce abin day a ke ji na hassada = ya kai zuwa ga zagin Wani daga cikinsu;
to hakika ya jawu zuwa She'dan da Linzami, ya kuma fa'da cikin fushin Allah.
Shi kuwa
wannan cutar wanda a ke samunsa da shi shi ne: wadda a ka jarrabe shi da Malami
'dan shi'a, ko kuma ya aboci wani daga cikin
abokan gaban mafi alkhairin wannan Al'ummar;
wa'danda She'dan ya yi wasa da su, kuma ya kawata mu su kare-reyi da a
ka kirkiro, da kissoshin karya, da kuma shiftan Gizo (
والخرافات الموضوعة) , da kuma kawar da su ga barin Littafin Allah da 'barna bat a zuwa
masa ta gaba gare shi da kuma bayansa, da sunnar Manzon Allah ( s a w) da tai
so mud a riwayoyin manyan Limamai na kowani zamani daga zamanuka; sai kuwa su
ka 'bata da shiriya, su ka canji asara mai girma dad a riba mai yawa, haka-haka
She'dan jefeffe kuma wanda ya yi nisa daga rahama bai gushe ba ya na 'daukan su
daga mataki zuwa mataki, haka daga martaba zuwa martaba har said a su ka zama
makiyan Littafin Allah, da kuma sunnar Manzonsa (s a w), da kuma mafi alherin
al'ummarsa ( r a) da kuma salihan bayinsa, da sauran Muminai, Su ka yi kuma
watsi da farillan Allah, su ka nisaci ( kaurace wa) alamomin addininn nan, su
ka kuma tafi iya tafiya don kaidi wa Musulunci da ma'abotansa, sannan su ka
jefin wannan addinin da ma'abotansa da kowani dutse da foge. Allah kuma a
bayansu ( da ma aiyukansu) ya na mai kewaye da su ".
Wannan shi ne
abin da Shaukani – allah ya masa rahama
– ya fada a wajen tafsirin wannar ayar, sannan ya ce: " Hakim ya fito da
(wannan Asarin) kuma ya inganta shi, haka kuma Ibn Mardawaihi daga Sa'ad bn
Abiy Wakkas ( r a) Lallai ya ce:
(( الناس
على ثلاث منازل قد مضت منهم منزلتان، وبقيت منزلةٌ، فأحْسنُ ما أنتم كائِنون عليه أن
تكونوا بهذه المنزلة التي بقيت ثم قرأ ﴿ والذين جاؤوا من بعدهم يقولون ربنا اغفر لنا
ولإخواننا الذين سبقونا بالإيمان﴾الآية ))
Ma'ana: " Mutane
mataki uku ne, mataki biyu daga ciki sun wuce, 'daya kuma ya saura; ( don haka)
abin da ya fi kyau ku kasance a kansa shi ne ku kasance a kan wannan mataki da
ya saura; sanna ya karanta: " wadanda su ka zo bayansu su ke cewa: ya
Ubangijinmu ka gafarta mana (mu) da 'Yan' uwanmu da su ka rigaye mu da imani
…" zuwa karshen ayar.
Sannan Abdu
bn Humaid ya fito da ( wannan asarin ), da kuma Ibnul Munzir, da Ibnu Abiy
Hatim, da Ibnul Anbariy cikin ( Al-Masa-hif), da Ib Mardawaihi daga A'isha ( r
a) Lallai ta ce:
(( أُمِرُوا أن يستغفروا لأصحابِ النبيِّ r؛ فسبُّوهُم،
ثم قرأت هذه الآية ﴿ والذين جاؤوا من بعدهم﴾.
Ma'ana:
" An
umurce su da su nemi gafara ga Sahabban Manzon Allah ( s a w) Sai su ka zage
su" sannan ta karanta ayar ".
Na ce ( Mai
Magana: Sheikh Abdul Muhsin): Muslim ma ya ruwaito wannan asarin a karshen
Sahihinsa ba tare da karanta ayar ba.
5.
Nawawiy ya ce a cikin Sharhinsa:
" Kadiy ya ce: Abin da ke bayyana shi ne: Lallai ( A'isha) ta fa'di
maganantan nan ne lokacin da ta ji Mutanen Misra su ke fa'dan abin da su ka
fa'da a kan Usman ( r a), da kuma Mutanen Shaam; ya yin da su ka fa'di abin da
su ka fa'da a kan Aliyu ( r a), da kuma Khawarijawa ( Mutanen garin Harura); ya
yin da su ke fa'dan abin da su ke fa'da kan duka ".
Amma umarni da neman gafara da aka yi wanda ta yi
nuni zuwa gare shi; shi ne fa'din Allah:
﴿ والذين جاؤوا
من بعدهم يقولون ربنا اغفر لنا ولإخواننا الذين سبقونا بالإيمان﴾
Kuma da wannan
Malik ya kafa hujja da cewa babu hakkin Fai'u ( dukiyan da kafirai su ka gudu
su ka bari, Musulmai kuma su ka tattara, ba kuma tare da an yi ba-ta-kashi ko
an zubar da Jini ba) ga Mutumin day a zagi Sahabbai ( Allah ya kara yarda da
su); saboda Allah ta'ala ya sanya ta ne kawai ga wanda su ka zo bayansu daga
cikin wa'danda su k enema mu su gafara. Allah ta'ala shi ne masani".
6.
Kuma Ibnu Mardawaihi ya ruwaito
daga Ibnu Umar ( Allah ya kara mu su yarda da su) Lallai shi ya ji wani Mutum –
alhalin ya na fa'din abin bai dace ba kan sashin Muhajirun; Sai ya karanta
masa:
) لِلْفُقَرَاءِ الْمُهَاجِرِينَ
الَّذِينَ أُخْرِجُوا مِنْ دِيَارِهِمْ وَأَمْوَالِهِمْ يَبْتَغُونَ فَضْلًا مِنَ اللَّهِ
وَرِضْوَانًا وَيَنْصُرُونَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ أُولَئِكَ هُمُ الصَّادِقُونَ
(
Sannan ya ce
masa: Wa'dannan su ne: Muhajirun; Shin kai kana cikinsu? Sai ya ce: A'a! Sannan
ya karanta masa:
﴿ وَالَّذِينَ تَبَوَّءُوا الدَّارَ وَالْإِيمَانَ
مِنْ قَبْلِهِمْ يُحِبُّونَ مَنْ هَاجَرَ إِلَيْهِمْ وَلَا يَجِدُونَ فِي صُدُورِهِمْ
حَاجَةً مِمَّا أُوتُوا وَيُؤْثِرُونَ عَلَى أَنْفُسِهِمْ وَلَوْ كَانَ بِهِمْ خَصَاصَةٌ
وَمَنْ يُوقَ شُحَّ نَفْسِهِ فَأُولَئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ﴾
Sannan ya ce:
Wa'dannan kuma su ne: Al-ansaar; Shin kana cikinsu? Sai ya ce: A'a! Sannan ya
karanta masa:
﴿ وَالَّذِينَ
جَاءُوا مِنْ بَعْدِهِمْ يَقُولُونَ رَبَّنَا اغْفِرْ لَنَا وَلِإِخْوَانِنَا الَّذِينَ
سَبَقُونَا بِالْإِيمَانِ وَلَا تَجْعَلْ فِي قُلُوبِنَا غِلًّا لِلَّذِينَ آَمَنُوا
رَبَّنَا إِنَّكَ رَءُوفٌ رَحِيمٌ ﴾
Sannan ya ce: To ka shiga cikin wa'dannan? Sai ya
ce: Ina fata! Sai ya ce masa: Baya cikin wa'dannan wanda ya ke zagin wa'dancan ".
7.
Imamu Ahmad ya na fada a cikin Littafinsa –
As- sunna:
(( ومن السنة: ذكرُ محاسنِ
أصحاب رسول الله r كلِّهم
أجمعين، والكفُّ عن الذي جرى بينهم؛ فمنْ سبّ أصحابَ رسول الله r أو واحداً منهم فهو مبتدعٌ رافضيٌّ، حبُّهم سنةٌ، والدعاءُ لهم
قربةٌ، والاقتداءُ بهم وسيلةٌ، والأخذُ بآثارهم فضِيلةٌٌ)).
Ma'ana:
" Yana daga cikin Sunna; Ambaton kyawawan
Sahabban Manzon Allah ( s a w) dukkansu gaba 'dayansu, Da kuma kamewa kan abin
da ya gudana a tsakaninsu; Don Duk Wanda ya zagi Sahabban Manzon Allah ( s a w)
ko 'Daya daga cikinsu to 'Dan bidi'a ne, 'Dan Shi'a. Sonsu Sunna ne, Yi musu
addu'a kuma kusantar Ubangiji ne, Koyi da su kuma tafarki ne da kusanci, Aiki
kuma da Hadisansu falala ne ". Ya
sake cewa kuma:
(( لا يجوز لأحدٍ أنْ يذكرَ شيئاً من مساويهم، ولا يطعنَ على أحدٍ
منهم؛ فمن فعل ذلك فقد وجَب على السلطانِ تأديبُه وعقوبتُه، وليس له أنْ يعفوَ
عنه، بل يعاقبُه، ثم يستَتِيبُه؛ فإنْ تاب قَبِل منه، وإنْ لم يتُبْ أعاد عليه العُقوبَةَ،
وخلّده في الحَبْس حتى يتوبَ ويُراجعَ )).
Ma'ana:
" Bai halatta ga wani ba; ya ambaci wani
abu na munanansu, ko ya soki wani daga cikinsu; duk wanda ya aikata haka; to ya
zama dole ga Shugaba ya ladabtar da shi, ya kuma masa horo, bashi = kuma da
daman ya yafe masa, ya masa horo sannan ya nemi tubansa; in ya tuba; ( Alhamdu
lil lah, to) ya karba daga wajensa, in kuma ya ki ya tuba Sai ya sake yi masa
Horon, ya kuma tabbatar da shi a rufe har ya tuba ya dawo".
8. Imam
Abu Uthman As-sabuniy ya fa'da a cikin littafinsa: Akidar maga-bata da ma'abota
hadisi:
(( ويرَوْن الكفَّ عما شجَر
بين أصحاب رسول الله r، وتطهيرَ
الألسنةِِ عن ذكر ما يتضّمن عَيْباً لهم، أو نقصاً فيهم، ويرَون الترحُّم على جميعِهم،
والموالاةَ لكافتهم)).
Ma'ana:
" ( Su Ahlus Sunnah) su na ga ( wajibcin)
kamewa dangane da abin da ya faru a tsakanin Sahabban Manzon Allah ( s a w), da
kuma tsarkake harasa ga barin ambaton abin da ya ke kunsan aibi a gare su ko
nakasa cikinsu, Kuma su na ga neman rahamar Allah ga 'Daukacinsu gaba 'dayansu,
da kuma so da taimako ga dukkansu".
9. Shekhul
Islam ibn taimiyyata a cikin littafinsa (Akidatul wa-sidiyyat) ya ce:
" Kuma ya na daga cikin Ginshikan Ahlus Sunnah wal Jama'a: Kubutuwan Zuciyansu da Harasansu ga Sahabban
Manzon Allah ( s a w); kamar yadda Allah ya siffanta su cikin fadinsa:
) والذين جاءوا
مِنْ بَعْدِهِمْ يَقُولُونَ رَبَّنَا اغْفِرْ لَنَا وَلِإِخْوَانِنَا الَّذِينَ
سَبَقُونَا بِالْإِيمَانِ وَلَا تَجْعَلْ فِي قُلُوبِنَا غِلًّا لِلَّذِينَ
آَمَنُوا رَبَّنَا إِنَّكَ رَءُوفٌ رَحِيمٌ( (10)
Ma'ana: " da
wadanda su ka zo bayansu su ke cewa: Ya Ubangijinmu ka gafarta mana (mu) da
'Yan' uwanmu da su ka rigaye mud a Imani, Kuma kada ka sanya hassadan wadanda
su ka yi Imani cikin Zuciyarmu, Ya Ubangijinmu Lallai kai mai tausayi ne mai
rahama".
Kuma biyayya wa Manzon Allah cikin
fadinsa:
[لا تسبّوا أصحابي؛ فو
الذي نفسي بيده لو أنفق أحدُكم مثلَ أحدٍ ذهباً ما بلغ مُدّ أحدِهم ولا نصِيْفَه]
Ma'ana:
" Kada
ku zagi Sahabbaina; Na fa rantse da wanda raina ya ke hanunsa da 'Dayanku zai
ciyar da kwatankwacin (Dutsen) Uhudu na Zinari, to da bai kai Mudun 'Dayansu
ba, koma rabi".
Zuwa fa'dinsa: " Kuma su na barranta daga
hanyar 'Yan shi'a; da ke kin Sahabbai, ke kuma zaginsu, da kuma hanyar
(Nasiba); wadanda ke cutar da Ahlul Baiti da fadi ko da aiki. Sannan su na
kamewa dangane da abin da ya gudana tsakanin Sahabbai; Su kuma ce: Wadannan
Lallai Wadannan Abubuwan da aka kawo mana na fadin munanansu: Daga ciki akwai
abin da Karya ne, daa ciki kuma akwai abin da aka kara a ciki, aka kuma rage,
daga aka jirkita shi ya bar fiskarsa. Ingancecce kuwa daga ciki; Su abun a musu
uzuri ne a cikinsa; saboda ko dai ya zama sun yi kokari ( Ijtihadi) su ka kuma
dace, ko sun yi kokari sannan su ka kuskure. Sannan du da haka su ( Ahlus
sunnah) ba su kudurta cewa: kowani 'daya daga cikin Sahabbai ma'asumi( wanda aka
kare shi) ne ga barin manyan laifi ko kanana ba; hasali ma (su Sahabbai) mai
yuwuwa ne a gare su su yi zunubi a dunkule, Amma dai su na rigaye (cikin duk
aiyuka) da kuma falala da zai wajabta gafarta musu abin da ya faru daga wajensu
– in ya farun – har ma za'a gafarta musu munanan da baza a gafarta ma Wadanda
su ka zo bayansu ba; saboda su na da kyawawan da ke goge munana wanda na
bayansu basu da su; saboda ya tabbata daga Manzon Allah (s a w) cewa su ne:
mafificin karni, kuma mudun 'Dayansu idan ya yi sadaka da shi ya fi Dutsen
Uhudu na zinari daga Wadanda su ke bayansu. Sannan idan ya zama an samu wani
zunubi daga 'daya daga cikinsu To zai zama ya tuba daga gare shi, ko kuma ya
aikata kyawawa da za su goge masa shi, ko kuma an gafarta masa saboda falalar
rigayensa, ko da ceton (Annabi) Muhammad
( s a w); wanda su su ka fi Mutane cancantar ceton nasa, ko kuma an jarrabe shi
da wata jarabawa a Duniya wanda za'a kankare masa shi da shi. (Idan wannan fa
shi ne halinsu ga zunubai da ake da tabbacinsa; To yaya kuma dangane da abin da
su ka kasance a cikin masu: Ijtihadi; wanda in sun dace su na da lada biyu, in
kuma su ka kuskure su na da lada 'daya, Shi kuma kuskuren an yafe!.
Sannan gwargwadon abin da ake ki daga aikin
sashensu kadan ne kuma bacecce ne a gefen falalan Mutanen da kyawawansu; na
daga Imani da Allah, da Manzonsa, da kuma jihadi a kan tafarkinsa, da hijira,
da taimakonsu, da kuma ilmi mai amfani, da aiki managarci (mai kyau).
Kuma duk
wanda ya yi dubi cikin tarihin Mutanen da ilimi da basira, da kuma abin da
Allah ya yi musu baiwa da shi na falala To zai sani yanke cewa: Su ne mafi
alherin Halittu bayan Annabawa, ba a yi kamar su ba kuma ba za ayi ba, kuma su
ne zababbu wannan al'ummar; wacce ita ce mafi alkhairin al'ummai kuma mafi
daukaka da daraja a wajen Allah ".
10.
As-sheikh Yahya bn Abibakar al-amiriy
alyamaniy ya ce a cikin littafinsa; Ar-riyadul musta'dabatu fi man lahu riwayatun
fis sahihaini minas Sahabati:
(( وينبغي لكلّ صيّنٍ
متديّنٍ مسامحةُ الصحابة فيما صدر بينهم من التشاجُرِ، والاعتذار عن مخطئهم, وطلب
المخارج الحسنة لهم, وتسليم صحة إجماع ما أجممعوا عليه علي ما علموه؛ فهم أعلم
بالحال، والحاضر يرى ما لا يرى الغائب، وطريقة العارفين الاعتذار عن المعايب،
وطريقة المنافقين تتبع المثالب. وإذا كان اللازم من طريقة الدين ستر عورات
المسلمين، فكيف الظن بصحابة خاتم النبيين مع اعتبار قوله: [ لا تسبوا أحداً من
أصحابي ] وقوله: [ من حسن إسلام المرء تركه ما لا يعنيه ]، هذه طريقة صُلحاء السلف
وما سواها مهاوٍ وتلفٌ )).
Ma'ana: " Ya
dace da duk Mutumin day a kiyaye kansa mai addini; Yin rangwame ( da uzuri) wa
Sahabbai kana bin day a faru a tsakaninsu na kace-nace, da kuma yin uzuri ga
wanda ya yi kuskure daga cikinsu, tare da neman kyawawan mafita a gare su, da
kuma sallamawa kan ingancin abin da su ka ha'du ( Ijma'i) a kansa tare da
kasancewarsu sun san abin da ya faru; don su su ka fi sanin abin da ya faru, Shi
ko wanda ya halarci abu ai ya ga abin da wanda bay a nan bai gani ba. Salo da
hanyar masana shi ne; Uzuri kan aibuka, yayin da hanyar Munafukai kuma it ace;
Bibiyan kura-kurai. Kuma tunda ya zama dole – a Musulunce – suturce da boye
al'auran Musulmai; to me ka ke zato kuma dangane Sahabban cika makon Annabawa!!!
Ga shi ko y ace: (( Kada ku zagi Sahabbaina!)) da kuma fa'dinsa: (( Yana daga kyan
Musulcin Mutum; Barinsa abin da bai shafe shi ba )). Wannan kuma ita ce hanyar
salihan Magabata. Abin da ba haka kuma
sukurkucewa ne da lalacewa " .
11.
Ibnu Hajar ya ciro a cikin Fathul bariy daga Abil Muzaffar As-sam'aniy Lallai shi ya
ce:
(( التعرُّض إلى جانب الصحابة علامةٌ على خذلانِ
فاعلِه، بل هو بدعةٌ وضلالةٌ))
Ma'ana: "
Taba Sahabbai alama ce da ke nuna tabewan mai aikata ta, dadin-dadawa kuma
bidi'a ce bata".
12.
Maimuniy ya ce:
(( قال لي أحمد بنُ حنبل: يا أبا الحسن! إذا رأيت
رجلاً يذكُر أحداً من الصحابة بسوءٍ فاتهمهُ على الإسلام ))
Ma'ana: "
Ahmad bn Hanbal ya ce min: Ya kai Baban Hasan!
Idan kaga Mutum ya na ambaton 'Daya daga cikin Sahabbai da mummuna to ka
tuhumce shi kan Musulunci ".
13.
Khadibul Bagdadiy ya ruwaito a littafinsa – Alkifayatu – da sanadinsa zuwa ga
Abi zur'ata Ar-raziy Lalli shi ya ce:
((
إذا رأيتَ الرجُلَ ينتقص أحداً من أصحاب رسول الله r فاعلمْ
أنه زِنديقٌ؛ وذلك أنَّ الرسول r عندنا
حقٌّ، والقرآنَ حقٌّ، وإنما أدّى إلينا هذا القرآنَ والسننَ أصحابُ رسولِ الله r، وإنما يريدون أن يجرحوا شهودنا ليبطلوا الكتاب والسنة، والجرْح
بهم أولى، وهم زنادقة)).
Ma'ana:
" Idan kaga Mutum ya na ( taba) taba 'Daya
daga cikin Sahabban Manzon Allah da nakasa; To ka sani Lallai shi Zindiki ne (
ma'ana: Munafiki); saboda Mu Manzon Allah a wajenmu gaskiya ne, kuma Qur'ani ma
gaskiya ne, kuma (ka sani) Wanda kawai ya kawo mana Wannan Qur'anin da
Wadannan Sunnonin su ne Sahabban Manzon Allah ( s a w), ( Sannan su kuma) abin
da kawai su ke nufi shi ne su soki SHAIDUNMU don su bata Littafi (Alqur'ani) da
Sunnah, To sukansu (su) shi ya fi, kuma su Zindikai ne (Munafukai).
14.
Al-hafiz Ibnu kasir ( rahimahul Lahu) ya ce a cikin tafsirin fadin Allah mai
buwaya da daukaka:
﴿وَالسَّابِقُونَ الْأَوَّلُونَ مِنَ الْمُهَاجِرِينَ
وَالْأَنْصَارِ وَالَّذِينَ اتَّبَعُوهُمْ بِإِحْسَانٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا
عَنْهُ وَأَعَدَّ لَهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي تَحْتَهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا
أَبَدًا ذَلِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ﴾ (100)
Ya ce: " Hakika
Allah mai girma ya bayyana cewa Lallai shi ya yarda da wadanda su ka yi rigaye
na farko daga wadanda su ka yi hijira da kuma Mataimaka (
المهاجرون والأنصار) da kuma wadanda su ka bi su da
kyautatawa. Tabewar wanda ya ki su ko ya zage su, ko kuma ya ki ko ya zagi
sashensu; musamman ma Shugaban Sahabbai bayan Manzo ( s a w) kuma mafi
alkhairinsu mafi-fi-cinsu; Ina nufin: Mafi girman siddikai, babban khalifa
Abubakar ibn Abiy kuhafata; domin tababbiyar Jama'a na daga 'Yan shi'a sun a yin
gaba da mafi-ficin Sahabbai, kuma su na kinsu sun a kuma zaginsu. Mu na neman
tsarin Allah daga haka. Wannann ya nuna juyuwan kwakwalensu da kuma dawowan
zukatansu kai gurbin kafa, Ina wadannan su ka yi Imani da Qur'ani; yayin da su
ke zagin wadanda Allah ya yarda da su!
Amma Ahlus sunnah; to su kam su neman Allah ya
kara yarda da wadanda ya yarda da su, kuma su
na zagin wanda Allah da Manzonsa su ka zaga, haka kuma sun a soyayya da
wanda ke son Allah, kuma sun a gaba da wanda ke kin Allah, saboda su masu bi ne
ba masau kirkira ba, … shi ya sa su ka zama
rundunan Allah masu tsira, kuma bayinsa Muminai ".
15.
Ibnu Hajar Al'askalaniy ya ce:
(( واتفق أهل السنة على وجوب
منع الطعن على أحد من الصحابة بسبب ما وقع لهم من ذلك ولو عرف المحق منهم لأنهم لم
يقاتلوا في تلك الحروب الا عن اجتهاد وقد عفا الله تعالى عن المخطئ في الاجتهاد بل
ثبت أنه يؤجر أجرا واحدا وان المصيب يؤجر أجرين )).
Ma'ana: " Ahlus sunna sun hadu kan
wajabcin hana sukan daya daga cikin Sahabbai saboda abin day a faru tsakaninsu
na yakuka, koda ko an san mai gaskiyan daga cikinsu; saboda ba su yi yaki ba
sai sakamakon Ijtihadi; Allah kuma ya yi afuwa ga Mutumin da ya yi kuskure
cikin Ijtihadi, kai ya ma tabbata cewa za a ba shi lada 'daya, shi kuma wanda
ya dace: Lada biyu ".
DAGA CIKIN ZANCEN MASU ADALCI KAN MU'AWUYA ( R A)
Daga cikin zancen masu adalci kan mu'awuya bn
Abiy Sufyan ( r a), Ga shi kamar haka:
1.
Almuwaffak bn kudamatal Makdisiy ya ce a cikin
Lum'atul I'itikad:
(( ومعاوية خال المؤمنين، وكاتب وحْيِ الله،
وأحد خلفاء
المسلمين)).
Ma'ana: "
Mu'awuya kawun Muminai, kuma marubucin wahayin Allah, kuma daga cikin
khalifofin Musulmai ( r a).
2.
Mai sharhin 'Dahawiyya ya ce:
((وأول
ملوك المسلمين معاويةُ t وهو خيرُ ملوكِ المسلمين ))
Ma'ana: " Farkon Sarakunan Musulmai
shi ne; Mu'awuya ( r a), kuma shi ne mafi alherin khalifofin Musulmai ".
3.
Zahabi a cikin Siyaru a'alamin nubala'i ya ce:
(( أمير
المؤمنين، ملك الاسلام ))
Ma'ana: "
Shugaban Muminai, Sarkin Musulunci " .
4.
Baihaki ya ruwaito daga Imamu Ahmada Lallai
shi ya ce:
(( الخلفاء: أبو بكر وعمر وعثمان وعليٌّ. فقيل
له: فمعاويةُ. قال: لم يكن أحدٌ أحقَّ بالخلافة في زمان عليٍّ من عليٍّ، ورحِم
الله معاويةَ )).
Ma'ana: " Khalifofi su ne: Abubakar
da Umar da Uthman da Aliyu ( r a). Sai a ka ce masa: Yaya Mu'awuya ( r a)! Sai
ya ce: Babu wani da ya fi cancantan khalifanci a zamanin Aliyu ( r a) fiye da
Aliyu, Allah kuma ya yi rahama wa Mu'awuya ".
5.
Ibnu Abid-dunya ya ruwaito da
sanadinsa daga Umar bn Abdil'aziz Lallai shi ya ce:
(( رأيت رسول الله r في
المنام وأبو بكر وعمر جالسان عنده، فسلّمت عليه وجلستُ فبينا أنا جالسٌ أُتِيَ
بعليٍّ ومعاويةَ فأُدخِلا بيتاً وأُجيفَ الباب، وأنا أنظُرُ، فما كان بأسرعَ من أن
خرجَ عليٌّ وهو يقول: قُضِيَ لِي وربّ الكعبةَ! ثم ما كان بأسرعَ من أنْ خرج معاويةُ
وهو يقولُ: غُفِر لي وربِّ الكعبةَ )).
Ma'ana: " Na yi mafarkin Manzon
Allah ( s a w); a halin Abubakar da Umar su na zaune a wajensa, sai na masa
sallama kuma na zauna, ina nan ina zaune sai aka shigo da Aliyu da Mu'awuya, a
ka kuma shigar da su wani daki, sannan a ka kuma dawo da kofar ciki (rufe); ni
kuwa duk ina yin dubi, jim kadan sai Aliyu ya fito ya na cewa: Na rantse da
Ubangijin ka'aba! An min hukunci, nan-da-nan sai Mu'awuya shi ma ya fito ya na
cewa: Na rantse da Ubangijin ka'aba; an gafarta min ".
6.
Ibnu Asakir ya ruwaito daga Abiy zur'atar
raziy Lallai wani Mutum ya ce masa:
(( إنِّي أبْغَضُ معاويةَ!، فقال له: ولِمَ؟
قال: لأنّه قاتلَ عليّاً، فقال له أبو زرعةَ: ويحك! إنّ ربَّ معاويةَ رحيمٌ،
وخَصْمُ معاوية خصْمٌ كريمٌ، فأَيْش دُخُولُك أنتَ بينهما! رضِي الله تعالى عنهما
)).
Ma'ana: " Lallai ni ina kin Mu'awuya! Sai ya ce
masa: don me? Sai ya ce: saboda ya yi yaki da Aliyu, sai Abu zur'ata ya ce
masa: kaitonka! kaga Ubangijin Mu'awuya;
mai rahama ne, kuma abokin husumarsa Mutum ne mai karamci; to kai kuma me ya
shigar da kai tsakaninsu?! Allah shi kara musu yarda ".
7.
Kuma an tambayi Imamu Ahmad kan abin da ya
faru tsakanin Aliyu da Mu'awuya ( r a)! sai ya ce:
﴿ تلك أمةٌ قد خلتْ لها ما
كسبتْ ولكم ما كسبتم ولا تُسْئَلون عما كانوا يعملون ﴾ وكذلك قال غيرُ واحدٍ من
السلف.
Ma'ana: " Waccar Al'umma ce da ta
riga ta shige; aikinta nag are ta ( don haka za ta samu sakamakonsa), kuma
aiknku na gare ku ( …), kuma ku ba za a tambaye ku ba dangane da abin da su ka
kasance su ke aikatawa ba ". da yawa daga cikin magabata da wannan su ke
bada amsa.
8.
an tambayi Ibnul Mubarak kan Mu'awuya! Sai ya
ce:
(( ماذا أقول في رجلٍ قال رسول الله r: سمع اللهُ لمن حمِدهُ. فقال معاويةُ خلْفهُ: ربَّنا ولك الحمد )).
Ma'ana: " Me zan ce kan Mutumin da
Manzon Allah ( s a w) ya ce: Ubangiji ya amsa wa wanda ya gode masa / ya ji
wanda ya gode masa, Sai Mu'awuya ya fada a bayansa ( wato: a cikin sallah
kenan): Ya Ubangijinmu! Yabo da godiya naka ne kawai ".
Sananne ne ( سمِعَ ) Ma'ananta a nan
shi ne: ( استجابَ ) wato: ya amsa, Mu'awuya kuma ya samu wannan
falalar; wato: Yin Salla bayan Manzon Allah ( s a w); Manzon Allah ya ce:
Ubangiji ya amsa wa wanda ya yabe shi ( ya gode masa), Shi kuma Mu'awuya ( r a)
na daga cikin wadanda ke sallah bayansa sannan yana cewa: ya Ubangijinmu! Yabo
naka ne.
Sai aka ce
masa – Ibnul Mubarak -:
(( أيُّهما أفضل هو أو عمر بن عبد العزيز؟ فقال:
" لتُرابٌ في مَنْخِرَيْ معاويةَ مع رسول الله r خيرٌ
وأفضلُ من عمر بن عبد العزيز " )).
" Sai aka ce wa Ibnul Mubarak: To
wa yafi falala tsakaninsa ( Mu'awuya) da Umar bn Abdil'aziz?! Sai ya ce: Kura
day a taba hancin Mu'awuya tare da Manzon Allah s a w ( a wajen yaki) ya fi
alkhairi kuma ya fi Umar dan Abdil'aziz falala ".
9.
Kuma an tambayi Mu'afi bn Imran: Way a fi;
Mu'awuya ko Umar bn Abdil'aziz? Sai ya yi fushi sannan ya ce wa mai tambayan:
(( أتجعلُ رجُلاً من الصحابة مثلَ رجلٍ من
التابعين؛ معاويةُ صاحبُه، وصِهْرُه، وكاتبُه، وأمينُه على وحيِ الله )).
Ma'ana: "
Shin za ka sanya Mutum daga cikin Sahabbai dadai da Mutum daga cikin Tabi'ai!
Mu'awuya fa Abokinsa ne ( Manzon Allah), kuma surkinsa ne, Marubucinsa, sannan
aminsa kan wahayin Allah ".
10.
Fadal bn Ziyad ya ce: Na ji baban
Abdullahi ( yana nufin Imam Ahmad) – an tambaye shi kan Mutumin da ya taba
Mu'awuya da Amru bnul As; Shi za a ce masa 'dan shi'a? Sai y ace:
(( إنه لم يجترئ عليهما إلا وله خبيئَةُ سوءٍ ؛
ما انتقص أحدٌ أحداً من الصحابة إلا وله داخلةُ سوءٍ )).
Ma'ana: "
Yadda al'amarin ya ke; Lallai bai mu su tsaurin ido face yana da wani mummunan
abu day a boye ( a zuciyarsa), ka sani; Babu wani da zai yi maganan nakasa kan
'daya daga cikin Sahabbai face akwai abin day a shiga zuciyarsa mummuna ".
11.
Ibnul Mubarak ya ji daga Muhammad
bn Muslim daga Ibrahim bn Maisara Lallai shi ya ce:
(( ما رأيت عمرَ بنَ عبد العزيز ضرب إنساناً
قطُّ إلا إنساناً شتم معاويةَ، فإنه ضربه أسواطاً ))
Ma'ana: "
Ban taba ganin Umar bn Abdil'aziz ya doki wani Mutum ba ( a rayuwa) sai Mutumin
day a zagi Mu'awuya; shi kam ( Umar) ya doke shi; bulali ( dorina).
12.
Abu taubata; Arrabi'u bn Nafi'il Halabiy ya
ce:
(( إن معاوية بن أبي سفيان سترٌ لأصحاب رسول
الله صلى الله عليه وسلم؛ فمن كشف الستر اجترأ على ما وراءه )).
Ma'ana: " Lallai Shi Mu'awuya bn Abiy Sufyan
Labule ne da ya suturce Sahabban Manzon Allah (s a w); Duk Mutumin da ya yaye
wannan Labulen kuwa to ba makawa zai shiga abin da ke bayansa ".
Wadancan
(maganganu) da su ka gabata yawancinsu na ciro sun e daga (Bidayatu wan
nihayatu) ([1]) na Ibnu kasir cikin tarjaman Mu'awuya.
Bukhari (
rahimahul lahu) ya kulla wani babi a cikin Littafin falalan Sahabbai cikin
Sahihinsa, ya ce:
بابٌ: ذكرُ معاوية t :
Babi kan ambaton Mu'awuya ( r a):
Sannan ya
kawo hadisai guda uku a karkashinsa:
Na farkonsu: Daga Ibnu Abiy Mulaikata; Lallai shi ya
ce:
(( أوتر
معاويةُ بعد العشاء بركعةٍ ... فأُتِيَ ابنُ عباسٍ فقال دَعْهُ فإنه صحِب رسول الله
r )).
Ma'ana: " Mu'awuya ya yi wutri da
raka'a daya bayan Sallan isha, … sai aka zo wa Ibnu Abbas ( aka kuma ba shi
labari); Sai ya ce: Kyale shi; Lallai shi ya aboci Manzon Allah ( s a w).
Na biyunsu: Daga Ibnu Abiy Mulaikata; an ce wa Ibnu
Abbas ( r a):
(( هل
لك في أمير المؤمنين معاوية؛ فإنه ما أوتر إلا بواحدةٍ ؟ قال أصاب؛ إنه فقيهٌ )).
" Me za ka ce kan Amiril Muminina
Mu'awuya; saboda shi ba ya wutri sai da (raka'a) 'daya? Sai ya ce: Ya yi dadai;
don shi mai ilmi ne ".
Na ukunsu:
Daga Mu'awuya ( r a), Lallai shi y ace:
((إنَّكُم
لتُصلُّون صلاةً لقد صحِبْنا النبيَّ r فما رأيناه يصلِّيها، ولقد نَهَى عنهما )) يعني: الركعتين بعد العصر.
Ma'ana: " Lallai ku kun a yin wata
irin sallah; hakika mun aboci Manzon Allah ( s a w) bam u ganshi ya na
sallatansu ba, Kai! Ya ma yi hani ne a kansu ". Yana nufin: rakao'i biyu
bayan la'asar.
Ibnu Hajar ya ce a cikin Sharhinsa: "
Bukhari ya ce: (ambaton Mu'awuya) a wannan tarjamar, bai ce ( falala ba …)
saboda; Falalar ba a ciran ta daga Hadisan day a ambato a babin; Sai dai kuma;
Shaidar Ibnu Abbasin a gare shi da cewa: ( Fakihi ne (Malami ne), Sahabi ne) na
nuni a kan falala mai yawa. Ibnu Abiy Asim ya yi Littafi kan falalarsa (
Mu'awuya), haka kuma Abu Umar (Yaron Sa'alab), da kuma Abubakar An-nak-kash,
Ibnul Jauziy – cikin Al-maudu'at – ya ambaci sashen Hadisan da su ka ambata;
sannan ya ruwaito daga Is'haka bn Rahuya, Lallai shi ya ce: " Babu wani Abu day a tabbata kan falalan Mu'awuya
" To wannan kuma shi ne dalilin kaucewar Bukhari ga barin fa'din: Falala);
wato: dogaro da abin da Malaminsa ya fa'da; amma kasancewarsa mai zurfin
tunani; ya ambato ya kuma ciro abin da zai doke kan 'Yan shi'a da shi ([2]) .
Ya zo cikin Sahihu Muslim Lallai Annabi ( s a
w) ya ce kan Mu'awuya:
{ لا أشبَعَ اللهُ بطَنَهُ }
Ma'ana:
" Kada Allah ya kosar da cikinsa! ".
Ya ruwaito ( wato: Muslim) da sanadinsa daga
Ibnu Abbas ( r a ) Lallai shi ya ce:
(( كنتُ ألعبُ مع الصبيان فجاءَ رسول الله
r فتواريتُ خلفَ بابٍ، قال: فجاء
فحطأَنِي حطَأةً، وقال: { اذهب وادع لي معاوية } قال: فجِئْتُ فقلت: هو يأكل، قال:
ثم قال لي: { اذهب فادْعُ لي معاويةَ } قال: فجئتُ فقلت: هو يأكل فقال: { لا أشبعَ
اللهُ بطنهُ }
Ma'ana:
" Na kasance ina wasa tare da Yara; sai Manzon Allah ( s a w) ya zo; sai
na buya a bayan kofa, Ya ce: Sai ya zo ya ( ma'ana: ya sadadado ) har ya doki
tsakanin kafaduna duka; sannan ya ce: ( Je ka kira min Mu'awuya), Ya ce: sai
(na je) na zo na ce: yana cin abinci, ya ce: Sannan ya ce min: ( Je ka kira min Mu'awuya), Ya
ce: sai (na je) na zo na ce: yana cin abinci, Sai ya ce: " Kada Allah ya
kosar da cikinsa! ".
Muslim ( rahimahul lahu) ya cike Hadisai da su
ka zo kan addu'an Annabi ( s a w) Ubangijinsa ya sanya duk abin da ya faru daga
wajensa na zagi da kuma addu'a ( mummuna) ga Mutumin da bai cancanceta ba,
Allah ya sanya shi ya zama masa tsarki da kuma lada da rahama; Misalin fadinsa:
{
تَرِبَتْ يمينك }.
Ma'ana:
" Damanka ya doki turbaya! ".
Da kuma fadinsa:
{
ثكلتك أمُّك }.
Ma'ana:
" Mamarka ta yi asararka! ".
Da fadinsa:
{ عقرى
حلقى}.
Ma'ana:
" Allah ya yi rauni a jikinta, sannan cuta ya kama Makogoronta ".
Da kuma fadinsa:
{ ولا كبِرَت سنُّك }.
Ma'ana: " kada shekarunki ya girma ( kar
Allah ya tsawaita rayuwarki) ".
( Musulim) ya ambato Hadisai da yawa a cikin
Sahihinsa. Daya daga cikinsu shi ne: wannan Hadisin, Kafinsa kuma ya kawo
Hadisin Anas bn Malik ( r a) ya ce: Ummu Sulaimin ta kasance tan a da Marainiya
– Ita kuma Ummu Sulaim Ita ce: Mahaifiyar Anas – Sai Manzon Allah ( s a w) ya
ganta ; Sai ya ce:
{أنت هيه؟ لقد كبِرتِ، لا كبِر سنُّك!}؛ فرجعت
اليتيمة إلى أُمّ سليم تبكي؛ فقالت أم سليم: مالك؟ يا بنية قالت الجارية دعا عليَّ
نبيُّ الله r أن لا يكبِرَ سنِّي؛ فالآن
لا يكبِر سنِّي أبداً / أو قالت: قرني؛ فخرجت أُم سُليمٍ مستعجلةً تلوث خمارَها حتى
لقيت رسول الله r، فقال لها رسول الله r: مالَكِ يا أُمَّ سُليمٍ؟! فقالت: يا نبيَّ الله
أدَعَوت على يتيمتي؟ قال: وما ذاكِ يا أُمَّ
سُليمٍ؟!
قالت: زعمت أنك دعوت أن لا يكبِر سنُّها،
ولا يكبِر قرنُها، قال: فضحك رسولُ الله r ثم قال: يا أُمَّ سُليمٍ! أما
تعلمين أن شرطي على ربِّي أنِّي اشترطت على ربي فقلت إنما أن بشر أرضى كما يرضى البشر
وأغضب كما يغضب البشر؛ فأيُّما أحدٍ دعوت عليه من أمتي بدعوةٍ ليس لها بأهلٍ أن تَجْعلها
له طهوراً وزكاةً وقربةً يقربه بها منه يوم القيامة}.
Ma'ana: " Ke ce! Hakika kin girma! To kar
( Allah ya sa) shekarunki ya girma", sai Marainiyar ta koma zuwa ga Ummu
Sulaimin tana kuka, Sai Ummu Sulaimin ta ce mata: me ya same ki ya ke 'Yata?
Sai yarinyar ta ce: ai Manzon Allah ne ( s a w) ya min addu'a kada shekaruna ya
girma; don haka yanzu shekaruna ba zai girma ba har abada! Sai Ummu Sulaimin ta
fita da gaggawa tana juya Khimar=dinta a kanta har ta sadu da Manzon Allah ( s
a w), sai Manzon Allah ( s a w) ya ce mata: me ya same ki yak e Ummu Sulaim?
Sai ta ce: ya Annabin Allah! Shin ka yi (mummunan) addu'a wa 'yar marainiyata?
Sai ya ce mata me ya faru yak e Ummu Sulaim? Sai ta ce: ta riya ne cewa ka mata
addu'a kan kada shekarunta ya yi tsayi! Sai Manzon Allah ( s a w) ya yi dariya
sannan ya ce: ya ke Ummu Sulaim shin ba ki sani ba ne lallai sharadina wa
ubangijina lallai ni na shardanta masa na ce: lallai ni mutum ne na kan yarda
kamar yadda mutum ke yarda, kuma na kan yi fushi kamar yadda mutum ke fushi;
don haka duk mutumin da na masa addu'a daga cikin al'ummata da wata addu'ar da
bai cancanceta ba, ka sanya masa ita ta zama: tsarkaka a gare shi da kuma
kusanci da za ka kusantar da shi zuwa gare ka da ita ranar kiyama".
To fa bayan wanna hadisin ne kai tsaye
Muslim(rahimahul Lah) ya kawo hadisin da Manzon Allah ( s a w) ya ce wa
Mu'awuya:
{ لا أشبَعَ اللهُ بطَنَهُ }
Ma'ana:
" Kada Allah ya kosar da cikinsa! ".
Wannan ko na nuna kyan aikin Muslim da kuma
kyan tsari day a yi wa Littafinsa ( sahih), wannan kuma ya bayu ne daga
kwalkwalalliyar fahimtarsa da kuma kyan iya cirar hukuncinsa (istinbadinsa). Nawawiy
ya ce a sharhinsa:
((
وقد فهم مسلمٌ رحمه الله من هذا الحديث أنَّ معاوية لم يكن مستحقاً للدعاء عليه؛
فلهذا أدخله في هذا الباب، وجعله غيرُه من مناقب معاوية)).
Ma'ana:
"Hakika Muslim – Allah ya rahamshe shi – ya fahimta daga wannan hadisin
cewa lallai Mu'awuya ( r a ) bai kasance daga cikin wadanda su ka cancanci a yi
a addu'a a kansu ba; don haka ne ma ya shigar da shi cikin wannan babin. Waninsa
kuma ya ma sanya shi daga cikin falalar Mu'awuya ( r a) ".
((وجعله
غيرُ مسلمٍٍ من مناقب معاوية)).
Saboda
a hakikance zai zama addu'a a ka masa.
Ibnu kasir ya fada a tafsiri fadin Allah madaukki:
﴿
ومن قُتل مظلوماً فقد جعلنا لولِّيه سلطاناً فلا يُسرف في القتل إنَّه كان
منصوراً﴾ [سورة الإسراء 33].
قال: ((وقد أخذ الحبر ابنُ عباس من عموم
هذه الاية الكريمة ولاية معاوية السلطنة أنه سيملك لأنه كان وليَّ عثمان، وقد قتل مظلوماً
t، وكان معاوية يطالب عليا t أن يُسلِّمه قتلته حتى يقتصَّ
منهم؛ لأنه أمويٌّ، وكان علي t يستمهله في الأمر حتى يتمكَّن
ويفعل ذلك، ويطلب عليٌّ من معاوية أن يُسلِّمه الشام؛ فيأبى معاويةُ ذلك حتى يُسلِّمه
القتلة، وأبى أن يبايع علياًّ هو وأهلُ الشام، ثم مع المطاولة تمكن معاوية، وصار الأمر
إليه كما قاله ابنُ عباسٍ، واستنبطه من هذه الاية الكريمة، وهذا من الأمر العجب)).
Ya
ce: " Hakika banban Malami Ibnu Abbas ( r a) ya cira daga abin da aya mai
karamci ta ke nunawa na ولاية معاوية السلطنة ya ciri cewa Mu'awuya zai jibinci
shugabanci kuma zai yi mulki; saboda kasancewarsa: WALIYYIN USMAN, ga shi kuma
an kasha shi yana wadda aka zalunta ( r a). mu'awuya ya kasance yana neman Aliyu
( r a) ya sallama masa wadanda su ka kashe Usman don ya daukar masa fansa;
saboda shi ba- umawiyye ne. Aliyu kuma (r a) ya kasance yana neman ya jira shi
har ya samu dama sai ya aikata hakan, Aliyun kuma yana neman ya sallama masa
Sham ( Siria); sai Mu'awuyan ya ki haka har sai an sallama masa wadanda su ka
yi kisan, ya kuma ki yin mubaya'a shi da kuma Mutanen sham. Sannan bayan dogon
lokaci Mu'awuya ya sama iko, al'amarin kuma ya zama a hanunsa. Kamar yadda Ibnu
Abbas ya fada, ya kuma cire shi daga wannan aya mai karamci. Wannan kuma daga
abubuwan mamaki.
A cikin Sahihul Bukhari daga Anas
(r a) lallai Annabi ( s a w) ya ce:
{ آية الإيمان حبُّ الأنصار، وآية النفاق بغض الأنصار}
Ma'ana:
" Alamar imani: son Mataimaka (Ansar), alamar munafurci kuma kin
Mataimakan"
Ibnu Hajar ya bayyana a cikin fathul bari cewa:
Lallai falalan Ansar=din nan, Waninsu zai yi tarayya da su a cikinsa matukar ya
yi tarayya da su cikin ma'anar da ta sa su ka samu wannan falalar; wadda ita
ce: Taimakonsu ga Manzon Allah ( s a w). sannan ya ce:
(( وقد ثبت في صحيح مسلم عن عليٍّ أن النبيَّ
r قال له: {لا يحبك إلا مؤمنٌ،
ولا يبغضك الا منافق}، وهذا جارٍ باطرادٍ في أعيان الصحابة ...إلى أن قال: قال صاحب
المفهم: وأما الحروب الواقعة بينهم فإن وقع من بعضهم بغضٌ فذاك من غير هذه الجهة، بل
للأمر الطاريء الذي اقتضى المخالفة؛ ولذلك لم يحكم بعضُهم على بعضٍ بالنفاق، وإنما
كان حالهم في ذلك حالَ المجتهدين في الأحكام للمصيب أجران، وللمخطئ أجرٌ واحدٌ والله
أعلم)).
Ma'ana:
" Ya tabbata cikin Sahihu Muslim daga Aliyu ( r a) lallai Annabi ( s a w)
ya ce masa: {Ba wadda ya ke son ka sai Mumini, ba kuma mai kinka sai Munafiki},
Wannan kuma na gudana ga daukacin Sahabbai Mai (Littafin) Mufhim ya ce: Amma yakuka da su
ka faru a tsakaninsu; to in kiyayya ya auku daga sashinsu to wannan ba zai
shiga nan ba, kai dai ya takaita ne ga wannan al'amarin day a bijiro wadda ya
hukunta wannan sabanin; don haka ne ma Sashinsu bai yi hukunci wa sashin ba da:
Munafirci. Kar ka dada kar ka rage! Shi ya sa halinsu cikin haka kamar halin
Malamai ne da su ke sabani cikin hukunce - hukunce; Wadda ya dace daga cikinsu
yana da: Lada biyu. Wanda kuma ya kuskure yana da: Lada daya. Allah shi ne
masani" ([3]) .
Sheikh Yahya bn Abibakar al-amiri al-yamani ya
fada cikin Littafinsa: الرياض المستطابة
a tarjamar Abi Musa al-ash'ariy ( r
a):
" As-sayyidul Imamush Sharif Muhammad bn
Ibrahim bn Murtada ya ciro cewa:
((
أنَّ بُغض عليٍّ إنما كان علامةً النفاق في أوَّل الإسلام؛ لأنَّه كان ثقيلاً على
المنافقين، ولذلك جاء في الأنصار أنَّ بغضهم علامةُ النفاق أيضاً، وحبُّهم وحبُّ
عليٍّ علامةُ الإيمان. واستدلَّ على ذلك بأنَّ الخوارج يبغضون علياًّ ويكفِّرونه
مع الإجماع على أنَّهم غيرُ منافقين، وإنْ كان ذنبهم عظيماً، ومروقهم من الإسلام
منصوصاً. والباطنيَّة يحبُّونه مع الإجماع على كفرهم، ثم كذلك الروافض يحبُّونه مع
ضلالتهم وفسوقهم. وعلى كلِّ حالٍ فلا يصدُر سبُّ أهل السوابق من الصحابة وتتبع
عوراتهم، والتنقيش والتفتيش عن مثالبهم عن ذي قلبٍ سليمٍ، ودينٍ مستقيمٍ. نسأل
الله العافية والسلامة)).
Ma'ana:
" Abin sani kawai lallai kin Aliyu ( r a) a farkon musulunci ya zama alama
ne na munafurci; saboda Aliyun ya kasance mai tsanani ne akan Munafikai; don
haka ne ma ( wato don tsanantawan Ansar ea Munafikai) ya zo cewa kin Ansar ma:
alama ce ta munafurci. Sonsu kuma da son Aliyu alamar Imani. Ya buga dalili
kuma da kasancewar Khawarijawa sun kasance suna kin Aliyu, kai suna ma kafirta shi, amma an yi
Ijma'i cewa su ba Munafikai ba ne([4]) duk da cewa zunubinsu yana da girma. Fitansu daga bin
musulunci kuma ya zo cikin hadisi. ( 'Yan shi'a) Badiniyya suna sonsa ( wato:
Aliyu), ga shi kuma an yi ijma'i([5]) cewa su kafirai
ne. haka kuma ( 'Yan Shi'a) Rafida suna sonsa([6]) ( kamar yadda su ka riya), tare da batansu da kuma
fasikancinsu. Ala kulli halin! Zagin wadanda su ked a gabaci daga Sahabbai ba
zai yiwu ba kuma ba zai kasance ba, da kuma bibiyan al'aurarsu, da kuma tono da
binciken kura kurensu daga Ma'abocin kubucecciyar zuciya, kuma Ma'abocin addini
mikakke. Muna rokon Allah lafiya da
kubuta" ([7]) .
Al hafizuz Zahabi ya ce a cikin
Littafinsa (ميزان الاعتدال):
Da za a ce: ta yaya 'Dan bidi'a zai zamo abin aminta da shi (
ثقة) ga shi kuwa shi amincecce (wajen Maluman hadisi) shi ne: 1-
Adali. 2- Mai kyan hadda.
To yaya za a yi 'Dan bidi'a ya zama Adali?
Amsa a nan shi ne: Ita bidi'a ta kasu kashi
biyu:
1) Akwai karamar bidi'a kamar taimakon Aliyu ( r
a) ba kuma tare da an wuce gona-da-iri, a kuma kuna cikin haka ba; (ta yadda
zai kai a ki Abubakar da Umar), Wannan na da yawa cikin Tabi'ai da kuma Tabi'ut
Tabi'ina, tare kuma da addini da wara'u (ma'ana: nisantan abin da a ke tsoron
cutarwansa a lahira) da gaskiya; irin wadannan da za a ki karbar hadisansu da
dayawa daga cikin hadisan Annabi ( s a w) sun tafi. Wannan kuma barna ne
mabayyaniya.
2) Sannan kuma sai babbar bidi'a kamar
bin addinin Rafida a cikensa, da kuma wuce gona-da-iri cikinsa, tare da sukar
Abubakar da Umar ( r a), da ma kiran Mutane zuga hakan. To irin wadannan kam ba
a kafa hujja da su kwata-kwata (ولا كرامة)
.
Sannan bana iya tuna Mutum daya daga cikin
wannan nau'in wadda a ke masa lakabi da (
صادق) ko
(مأمون) Wadannan
karya ce rigarsu ta ciki, Takiyya kuma da munafurci rigarsu ta waje. Ta yaya za
a karbi abin da wanda wannan ne halinsa ya ruwaito? Allah ya sawwake!
'Dan Shi'a da ya wuce gona da iri a zamanin
Magabata da kuma abin day a ke sananne a wajensu shi ne: Wanda ke Magana kan
Uthman da kuma Zubairu da 'Dalhatu da Mu'awuyatu, da kuma Jama'a da su ka yaki Aliyu ( r a) kuma su ka bijiro wa
zaginsu.
Amma 'Dan Shi'a da ya wuce gona da iri a
zamaninmu da kuma abin day a ke sananne a wajenmu ( Urfinmu) shi ne: yak e
kafirta wa'dannan Manyan, kuma yak e barranta daga Abubakar da Umar ( r a);
Wannan kam 'Bacecce ne, Makaryaci " ([8])
Daga cikin Maluman hadisi da a ka siffanta su da Wani abu na Shi'anci –
Shi'anci akwai: Malamin Bukhari أبو نُعيمٍ الفضل بن
دُكين
Ibn Hajar ya fada a mukaddimar
Fathul Bari cewa: (( Yabo a kansa wajen hardarsa da kuma kawun zabensa ga
wadanda su ka cancanci a ruwaito musu ya yi yawa; sai kuma wassu Maluman sun yi
Magana kansa saboda Shi'anci – Shi'ancinsa, amma duk da haka ya inganta lallai
shi ya ce:
((
ماكتبتْ عليَّ الحفظةُ أنِّي سببت معاوية)).
Ma'ana:
Mala'iku masu kiyaye([9]) Mutum kuma marubuta aiyukansa ba su taba rubuta min cewa
ni na zagi Mu'awuya ba! (r a) ([10]) .
Daga cikinsu kuma a kwai:محمد
بن الفضل بن غزوان الكوفي
Ibnu Hajar ya ce: " Nace: Wanda ya ki
ruwaitowa daga wajensa abin sani ya tsaya ne saboda Shi'anci – Shi'ancinsa,
Ahmad bn Ali Al'abaar ya ce: Abu Hashim ya bamu labari Lallai shi ya ji ابن
الفضل ya na cewa:
((
رحم الله عثمانَ، ولا رحِم الله من لا يترحَّم عليه)). قال: ورأيت عليه آثار أهل
السنة والجماعة رحمه الله)).
Ma'ana: " Allah ya yi rahama wa Uthman,
kuma kada ya yi rahama ga Mutumin da baya nema masa rahama". Ya ce: kuma
nag a alamar Ahlus sunna wal jama'a tare da shi" ([11]) .
Shekhul Islam Ibnu taimiyyata ya ce:
(( Bai halatta ba: La'antar Wani daga cikin
Sahabban Annabi ( s a w) ko zaginsa; duk wanda kuma ya la'anci wani daga
cikinsu kamar Mu'awuyatu bn Abiy Sufyan da Amru bnul Aas da makamancinsu, ko kuma
wanda ya fi wadannan guda biyun kamar Abu Musal Al'ash'ariy, da Abu Hurairata
da wassunsu, ko kuma wadanda su ka fi wadannan gaba daya kamar kamar 'Dalhatu
bn Ubaidul Lah, da Zubairu bnul Awwam, da Uthman bn Affan, da Aliyu bn Abiy
'Dalib, da Abubakaris Siddik da Umar bnul Khaddab, ko A'ishatu ummul
Mu'umininam da wassun wadannan daga Sahabban Annabi ( s a w); to lallai shi ya
cancanci foro mai tsanani, da ittifakin Limaman addini . Maluma sun yi
sabani shin za a yi masa foron ne da kisa ko sai abin da ke kasa da kisa? )).
Ya sake
cewa: (( Wadanda su ka yi hijira da farkonsu har karshensu ba wani daga cikinsu
da wani ya tuhumce shi da munafurci, dukkansu Mu'uminai ne da a ka musu shaida
da imani)).
Ya sa
ke cewa: (( Amma Mu'awuyatu da wassunsa
da a ke musu lakabi da ( 'Dulaka'u) da su ka musulunta bayan fathu Makkah kamar
Ikrimatu bn Abi Jahl, da Harith bn Hisham, da Suhail bn Amr, da Safwan bn
Umayyata, da Abu Sufyan ibnul Harith bn Abdul muddalib, wadannan da wassunsu
daga wadanda musuluncisu ya yi kyau da ittifakin Musulmai, ba wani da a ka
tuhuma a cikinsu bayan haka da munafurci, Mu'awuya kuma Manzo ( s a w) ya nemi
ya zama marubucinsa tun musuluntarsa)).
Ya sa ke cewa: (( Yayin da Yazeed bn Abi Sufyan ya rasu a khalifancin
Umar ( r a) sai Umar ya bada gomna wad an uwansa Mu'awuya, Umar kuma ya kasance
cikin manyan Mutane wajen hangen nesa, kuma yana cikin wadanda su ka fi sanin
Mazaje, kuma cikin mafi tsayuwarsu da gaskiya, sannan cikin mafi saninsu da
shi)).
Ya sa ke cewa: (( Umar bai taba bada Gomna, kai haka Abubakar ma bai
taba dora wa Musulmai Munafiki ba, haka kuma bas u taba dora wa Mutane danginsu
ba, sannan in su ka yi abunsu don Allah to zargin mai zargi baya damunsu)).
Ya sa
ke cewa: (( Sananne ne lallai Mu'awuyatu da Amru bnul Aas ( r a) da wassunsu fitina
da ya kasance a tsakaninsu ya kasance; amma duk da haka babu wani day a tuhume
su – daga cikin masoyansu ne ko kuma daga abokan fadansu – da karya wa Annabi (
s a w); kai dukkan Malaman Sahabbai da Tabi'ai bayansu sun yi ittifaki a kan
cewa lallai wadannan masu gaskiya new a Manzon Allah ( s a w), kuma amintattu
ne abin amincewa da su kan abin da su ka ruwaito daga gare shi. Shi ko Munafiki
ba wanda a ke amincewa da shi ba ne ga Annabi ( s a w), mai masa karya ne, kuma
mai karyata shi)).
Ya sa
ke cewa: (( 'Daukacin Ahlus sunna wal Jama'a da limaman addini ba su kudure
isma([12]) ba ga wani daga
cikin Sahabbai, haka kuma dangi na kusa na Manzon Allah, haka kuma wadanda su
ka yi rigaye haka wassunsu, yadda abin yak e a wajensu shi ne: kowanne daga
wadanda su ka gabata zai iya yin zunubi. Allah kuma zai gafarta musu da tuba,
ya kuma daga darajarsu da ita, ko ya gafarta musu da kyawawa masu kankare
munana masu share su, ko da wanin haka na sabbuba)).
Ya sa ke cewa: (( Wannan fa ya kasance ne cikin zunubi ne na hakika!
Amma abin da su ka yi sabani cikinsa ( su ka yi Ijtihadi) to wani lokaci su kan
dace, wani lokacin kuma su kuskure; Idan su ka dace bayan ijtihadi sun a da
lada biyu, yayin da in su ka yi ijtihadi sai su ka yi kuskure kuma sun a da
lada a kan ijtihadinsu, kuskurensu kuma an gafarta)).
Ya sa ke cewa: (( Shi Mu'awuyatu ( r a) bai yi da'awar khalifanci ba,
kuma ba a masa mubaya'a akan ta ba lokacin da ya yaki Aliyu ( r a), sannan bai
yi yaki a kan wai shi khalifa ba ne, ko wai cewa shi cancanci khalifanci, su
kuma sun a tabbatar da shi kan haka, kai ya kasance ma ya tabbatar da haka ga
wanda ya tambaye shi, kuma be kasance ya na ga shi da sahabbansa su fari Aliyu
( r a) da Sahabbansa da yaki ba. Kai yayin da Aliyu ( r a) da Sahabbansa cewa
dole ne kan Mu'awuyatu da Sahabbansa su yi da'a da mubaya'a; don ba zai kasance
wa Musulmi ba sai khalifa guda daya, sannan su ( Mu'awuyatu da Jama'arsa) sun
fita daga da'arsa dab a su aikata wannan wajibinba, وهم
أهل شوكة ya ga zai yake su har sai sun sauke wannan wajibin, sai a
samu biyayya da Jama'a.
Mu'awuyatu ( r a) da Sahabbansa su ka ce: haka
din ba wajibi ba ne a kansu, ku idan a ka yake su to an zalunce su ne. su ka
ce: Saboda Uthman an kasha shi yana wanda a ka zalunce shi ne da ittifakin
Musulmai, kuma ga shi wadanda su ka kasha shin sun a cikin Sojojin Aliyu ( r a),
ga shi su na da rinjaye, kuma sun a da karfi)).
Ya sa ke cewa: (( sannan fadin Annabi s a w:
{
إنَّ عمارً تقتله الفئة الباغيةُ}
((
Lallai Ammar ( r a) wata jama'a ce da ta ki da'a ita za ta kasha shi))
Ba wai dalili ne karara da ke nuni cewa a na
nufin Mu'awuyatu ( r a) da Jama'arsa ne ba; saboda zai iya yiwuwa a nufi wannan
Jama'ar da ta hau kansa hart a kasha shi, wadda ita ce bangaren Soja, haka kuma
duk wanda ya yarda da kashe Ammaar ( r a) to hukuncinsa to irin hukuncinta ne.
kuma sananne ne a cikin sojojin akwai wanda bai yarda da kashe Ammar ba kamar
Abdullahi bn Amru bn Aas da waninsa, kai dukkan Mutane ma sun yi inkarin kashe
Ammar har Mu'awuyatu da Amru)) ([13]).
DUNKULEN ABIN DA YA WAJABTA A KUDURA SHI KAN ABIN DA YA
FARU TSAKANIN SAHABBAI NA FITINA
A dunkule! Fitinar da ta faru tsakanin Sahabbai ( radiyal lahu anhum) Ya
zama dole ya zama rabon mai hankali da gare ta shi ne: Kyakkyawan zato wa
Sahabbai masu karamci, da kuma kamewa ga barin magana kansu said a alkhairi, da
kuma neman yarda ga daukacinsu, da kuma jibintarsu tare da sonsu, da kuma ji na
yanke cewa su din nan cikin abin da su ka yi sabani sun a tsakanin lada daya ne
ko biyu.
Mai sharhin dahawiyya ya kyauta lokacin da ya
ce – bayan ya yi nuni zuwa ga abin day a faru tsakanin Aliyu da Mu'awuya - :
(( ونقول في الجميع بالحسنى: ﴿ ربَّنا اغفر لنا ذنوبنا ولإخواننا الذين
سبقونا بالإيمان ولا تجعل في قلوبنا غلاًّ للذين آمنوا ربنا إنك رؤفٌ رحيمٌ﴾.
Ma'ana:"
kuma za mu fadi mai kyau kan daukacinsu baki-dayansu; Ya Ubangijinmu ka gafarta
mana zunubanmu (mu) da wadanda su ka rigaye mud a imani, kuma kada ka sanya
hassadan wadanda su ka yi imani a zuciyarmu, ya Ubangijinmu lallai kai mai
tausayi ne mai rahama".
Sannan ya ce:
((
والفتَن التي كانت في أيامه ـ أي: أيام أمير المؤمنين عليّ t
ـ قد صان اللهُ عنها أيدينا، فنسأله سبحانه وتعالى أن يصون عنها ألسنتنا بمنِّه
وكرمه)).
Ma'ana: " Fitinonin da su ka faru a kwanakinsa –
yana nufin: kwanakin amirul mu'uminina Aliyu ( r a) – Ubangiji ya kare mana
hannayenmu daga gare su, to muna rokonsa da baiwarsa da kuma kyautarsa
madaukakin sarki day a kare mana harasanmu daga gare su.
والحمد لله ربِّ العالمين، وصلَّى الله وسلَّم
وبارك على خير خلقه، وأفضل رسله نبيِّنا محمد بن عبد الله، وعلى آله وأصحابه، ومن
تبعهم بإحسانٍ إلى يوم الدين.
والسلام عليكم ورحمة الله وبركاته.
No comments:
Post a Comment