2016/04/22

FALALAR AHLULBAITI A WURIN AHLUSSUNNAH





فضلُ أهلِ البيت وعلوُّ مكانتِهم عند أهل السنة والجماعة


Falalar Ahlul Baiti, da kuma Daukakuwar Matsayinsu a wajen Ahlus Sunna Wal Jama'a












Wallafar
Abdul Muhsin Bn Hamad Al Abba-d Albadr












Fassarar
Abubakar Hamza




Abubuwan da ke ciki:

Gabatarwa.................................................................................................................


Fasalin farko: Su wanene Ahlul baiti?................................................................


Fasali na biyu: dunkulen akidar Ahlus sunna wal jama'a kan Ahlul baiti..............................................................


Fasali na uku:Falalar Ahlul baiti cikin Qur'ani;..............................................................


Fasali na hudu: Falalan Ahlul baiti cikin sunna mai tsarki;..............................................................


Fasali na biyar: Daukakan matsayin Ahlul baiti a wajen Sahabbai da wadanda su ka bi su da kyautatawa;..............................................................


Fasali na shida: Yabon wassu Maluma ga jama'a daga cikin Sahabbai Ahlul baiti;..............................................................


Fasali na bakwai: Yabon wassu Maluma ga jama'a daga cikin Sahabbai mata ( Ahlul baiti)..............................................................


Fasali na takwas: Yabon wassu Maluma ga jama'a daga cikin Tabiai da wassunsu Ahlul baiti..............................................................


Fasali na tara: 'Yar aune tsakanin akidar Ahlus sunna da wassunsu kan Ahlul baiti!..............................................................


Fasali na goma: Haramcin danganta kai - ba tare da hakki ba - zuwa ga Ahlul baiti..............................................................


  Yabo da godiya sun tabbata ga Allah; muna gode masa, kuma muna neman taimakonsa, da neman gafararsa, muna kuma neman tsarin Allah daga sharrin kayukanmu da kuma munanan aiyukanmu; duk wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, wadda kuma ya batar to babu mai shiryad da shi, Ina kuma shaidawa ba wadda ya cancanci a bauta masa sai Allah; shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, ina kuma shaidawa annabi Muhammadu bawansa ne manzonsa ne, yabon Allah da tsirarsa tare da albarkarsa su tabbata a kansa, da kuma iyalansa da sahabbansa, da wadda ya bi turbarsa, ya kuma shiriya da shiriyarwarsa har ranar sakamako.
bayan haka:
saboda muhimmancin bayanin matsayin iyalan gidan Annabi ( s a w) a wajen Sahabbai da wadanda su ka bi su da kyautatawa; na yi Lecca a kan topic din a Hool din lecca a Jami'ar musulunci da ke nan Madina - kafin shekara sha shida - To wai don ganin fa'idar ta game, na ga ya dace na rubuta wata takkaicecciyar mata-shiya (panpalet) a kan topic din; Na kuma yi mata take da:


فضلُ أهلِ البيت وعلوُّ مكانتِهم عند أهل السنة والجماعة


Na kuma kasa Littafin zuwa fasali goma; kamar haka:
Fasalin farko: Su wanene Ahlul baiti?
Fasali na biyu: dunkulen akidar Ahlus sunna wal jama'a kan Ahlul baiti
Fasali na uku:Falalar Ahlul baiti cikin Qur'ani
Fasali na hudu: Falalan Ahlul baiti cikin sunna mai tsarki
Fasali na biyar: Daukakan matsayin Ahlul baiti a wajen Sahabbai da wadanda su ka bi su da kyautatawa
Fasali na shida: Yabon wassu Maluma ga jama'a daga cikin Sahabbai Ahlul baiti
Fasali na bakwai: Yabon wassu Maluma ga jama'a daga cikin Sahabbai mata ( Ahlul baiti)
Fasali na takwas: Yabon wassu Maluma ga jama'a daga cikin Tabiai da wassunsu Ahlul baiti
Fasali na tara: 'Yar aune tsakanin akidar Ahlus sunna da wassunsu kan Ahlul baiti!
Fasali na goma: Haramcin danganta kai - ba tare da hakki ba - zuwa ga Ahlul baiti



Marubuci
1 / Rabiyus sani / 1422h







FASALIN FARKO:

SU WANENE KAM AHLUL BAITI?

  Inganceccen zance kan abin nufi da " Alu baitin " Annabi ( s a w ) su ne: Wadanda ya haramta su ci zakka; wadanda su ne:
1- Matansa.
2- da zurriyarsa.
3- da kuma dukkan musulmi da musulma cikin 'yayan Abdul muddalib; wadanda su ne 'Ya'yan Hashim bn Abdi manaf; Ibnu Hazmin yana cewa - (a shafi 14) cikin Jamharatu ansabil arab - : (( An haifa aifa wa Hashim bn Abdi manaf: Shaibat; wanda shi ne Abdul muddalib, yana da daukaka kuma shi ne tushe, sannan Hashim bai kasance yana da baya ba ( Haula da 'Ya'ya) sai ta hanyar Abdul muddalib kawai.
 ( Dangane da 'Yayan Abdul muddalib; ka yi dubi zuwa ga p14 -15 cikin Jamharatu ansabil arab na Ibnu Hazmin, da kuma Attabyin fi ansabil kurashiyyin na Ibnu kudamata; p76, da kuma Minhajus sunna na Ibnu taimiyyata; vol: 7 / 304 -305, tare da Fathul bariy na Ibnu Hajar, vol: 7 / 78 -79 ).

 Dalili da ke nuna shigan 'Yayan Baffanunsa cikin Iyalan gidansa ( Ahlu baitihi) Shi ne: abin da Muslim ya ruwaito a sahihinsa ( 1072) daga Abdul muddalib bn Rabi'ata bnul Harith bn Abdul muddalib lallai shi ya tafi shi da Fadal bn Abbas zuwa ga Manzon Allah ( s a w ) su na neman ya basu aikin karbo zakka da sarrafata ... domin su samu dukiyar da za su yi aure da shi, sai ya ce musu:

" إنَّ الصدقة لا تنبغي لآل محمدٍ؛ إنما هي أوساخٌ الناس "

Ma'ana: " Lallai ita zakka bata halatta ga Iyalan Muhammad; abin sani kawai ita daudar Mutane ne " Sannan sai Annabi ( s a w ) ya yi umarni da a musu aure kuma a bada sadakinsunsu daga Khumusi.

Hakika wassu ma'abota ilimi - daga cikinsu akwai shafi'i da Ahmad - sun riskar da 'Ya'yan Muddalib bn Abdi manaf wajen haramta musu sadaka da 'Ya'yan Hashim; saboda tarayyarsu da su wajen basu Khumusi khumusi; saboda Hadisin da Bukhari ya ruwaito cikin sahihinsa ( 3140) daga Jubairu ibnu Mud' im ( r a ); wanda a cikinsa an bayyana cewa lallai bayarwan da Annabi ( s a w ) ya yi wa 'Ya'yan Hashim da 'Ya'yan Almud dalib ya kuma bar 'Yan uwansu; 'Ya'yan Abdi shams, da 'Ya'yan Naufal; saboda 'Ya'yan Hashim da 'Ya'yan Almud dalib abu guda ne.

Amma dalili kan shigan Matansa ( Allah ya kara yarda da su) cikin Iyalansa ( s a w ); to shi ne fadin Allah mai girma da 'daukaka:

               ﭽﭾ  ﭿ             ﮅﮆ                                 

Ma'ana: " Kuma ku zauna a dakunanku (gidajenku), haka kuma kada ku yi fice irin fitan Jahiliyyar farko, ku tsaida salla, kuma ku bada zakka, ku yi biyayya wa Allah da Manzonsa, abin sani kawai Allah na nufin ya kawar da dauda ne daga gare ku ya ku mutanen wannan gidan kuma ya tsarkake ku tsarkakewa * ku kuma tuna abin da a ke karantawa a cikin dakunanaku na ayoyin Allah da hikima ( hadisi), Lallai Allah mai tausasawa ne kuma mai bada labari ".

Wannan ayar tana yin nuni kan shigansu ( matansa cikin Alin gidansa); kuma shigansu dinma dole ne; saboda zubin ayoyin da ke kafinta da na bayanta (Ubangiji) na zance da su; wannan kuma ba zai yi karo da abin da ya zo cikin sahihi Muslim ba ( 2424) daga A'ishatu ( r a ) lallai ta ce: Annabi ( s a w ) ya fita cikin wata safiya alhalin yana sanye da tufa mai zanen abin hawan rakumi da aka yi shi da gashi baki; sai Hassan bn Aliyu ya zo; sai ya shigar da shi ta ciki, sai Husaini ma ya zo sai ya shiga, sannan sai Fadimatu ta zo sai ya shigar da ita,sannan sai Aliyu ya zo; sai ya shigar da shi, sannan ya ce:

                               

saboda ayar ta yi nuni kan shigansu; saboda zance cikin duk ayoyin da su  ke yi, amman shigan Aliyu da Fadimatu da Hassan da Husaini ( r a ) cikin ayar to wannan hadisin ne ya yi nuni zuwa gare shi. kuma kebewar da Annabi ( s a w ) ya yi wa wadannan fudun - cikin wannan hadisin - abin sani kawai na nuni ne kan karin kusantakansu da shi fiye da sauran danginsa.
Kwatankwacin nunin wannan ayar kan shigar da Matan Annabi ( s a w ) cikin iyalansa, da kuma nunin hadisin A'ishatu ( r a ) da ya gabata kan shigar da Aliyu da Fadimatu da kuma Hassan da Husaini ( r a ) cikin Iyalan gidansa, kwatankwacin wannan shi ne klwatankwacin nunin  fadin Allah:

                 

da ke nuna abin da ake nuni da shi shi ne: Masallacin Kuba'a, tare kuma da nunin sunna cikin hadisin da Muslim ya ruwaito shi cikin sahihinsa( 1398) cewa abin da ake nufi da masallin da aka assasa shi a kan tak'wa shi ne: masallacinsa ( s a w)

(wannan kamancecceniyar Shekhul Islam bn taimiyyata ya ambace ta cikin mata-shiya da ya yi kan Falalar Ahlul baiti da kuma hakkokinsu ( p20 -21).

Matansa ( s a w ) sun shiga karkashin lafazin:


(الآل)؛
saboda fadinsa ( s a w ):

 " إنَّ الصدقة لا تحلُّ لمحمدٍ ولا لآل محمدٍ؛ "

Ma'ana: " sadaka bata halatta ga Muhammad da iyalan Muhammad " dadin - dadawa kuma lallai su ana ba su daga khumusi, haka kuma abin da Ibnu abiy shaibata ya ruwaito cikin Musannaf dinsa ( vol: 3 / p214) da sanadi ingatacce daga Ibnu abiy mulaikata: Lallai Khalid bn Sa'id ya tura wa A'ishata Saniyar zakka sai ta dawo da ita, ta kuma ce:

 (( إنَّا آل محمدٍ r لا تحل لنا الصدقة ))

Ma'ana: " Mu Iyalan Muhammadu zakka bata halatta mana"

Daga cikin abin da Ibnul kayyim ya ambata cikin littafinsa ( Jala'ul afham, p331 - 333) lokacin da ke ambato hujjojin  masu shigar da matansa ( s a w ) cikin Iyalan gidansa; fadinsa: " Wadannan sun ce: Abin da ya shigar da mata cikin (Iyalai ); musamman Iyalan Annabi ( s a w) saboda kamantuwansau da ( Danganta) wajen rashin yankewa;
1- saboda su matansa ( s a w ) haduwansu da shi ba zai taba yankewa ba,
2- kuma waninsa haramun ne a gare shi ya aure su - a rayuwar Annabi ( s a w ) ko bayan rasuwarsa -,
3- dadin - dadawa su matansa ne a duniya da lahira;
don haka alakar da ta ke tsakaninsu da Annabi (s a w) ta tsaye ne tsayuwar Danganta, kuma Annabi ( s a w ) ya nassanta kan yi musu salati - a lokacin yi masa salati -; shi yasa inganceccen magana - kuma shi ne maganan Imamu Ahmad - Lallai cin zakka haramun ne su ma akansu; saboda kasancewarta daudar Mutane; Allah kuma ya kiyaye Manzonsa da Iyalensa ga barin dukkan daudar 'Yan - adam.
Yau ga abun mamaki! yaya matan Annabi ( s a w ) za su shiga cikin fadinsa:

 " اللهم اجعل رزق آل محمدٍ قوتاً "

Ma'ana: " Ya Allah ka sanya arzikin Muhammadu: bukatarsu ( abincinsu) "
da kuma fadinsa akan abin Layya:

" اللهم هذا عن محمد وآل محمد"

Ma'ana: " Ya Allah ka karbi wannan ga Muhammad da Iyalan Muhammad! "
da kuma fadin A'ishatu ( r a ):

" ما شبع آل رسول الله r من خبز برٍّ "

Ma'ana: " Iyalan Manzon Allah ba su taba koshi ba da biredin alkama "
da kuma fadin mai sallah:

" اللهم صلِّ على محمد وعلى آل محمد"

Ma'ana: " ya Allah ka yi yabo wa Muhammad da kuma iyalan Muhammad "

amma ba za kuma shi giga cikin fadinsa:

" إنَّ الصدقة لا تحل لمحمد ولا لآل محمد"

" Lallai sadaka bata halatta ga Muhammad da kuma Iyalan Muhammad "!! tare da cewa kuwa daudar Mutane ce; ai kuwa Matan Manzon Allah su su ka fi cancantar a kare su daga ita, da kuma nisantar ta?!
To da za a ce: Da zakka ta haramta musu to ko da ta haramta wa bayinsu da su ka 'yanta su; kamar yadda yayin da ta zama haramun ga banu Hashim sai ta zama haramun ga 'yantattun bayinsu; Ga shi ya tabbata cikin Bukhari da Muslim Lallai Bariratu an mata sadakan nama; sai ta cinye shi, kuma Annabi ( s a w ) bai haramta shi ba;alhalin ita kuma 'yancacciyar baiwar A'isha ce.
To sai a ce: Wannan shi ne shubuhar ( dalilin) wanda ya halatta ta ga Matan Annabi ( s a w )
Amma amsar wannan shubuhar ita ce: Lallai haramcin sadaka ga Matan Annabi ( s a w ) ba asali ne ba, kai dai hakan na bin haramcinta ( sadakan ) ne a gare shi ( s a w ); saboda ai sadakar halal ne su amfana da ita kafin saduwasu (aurensu) da shi; don haka su ba asali ba ne wajen wannan haramcin, Shi kuma haramcinta ga 'yancaccen bawa reshe ne na na haramcita ga shugabansa; don haka yayin da haramcin ( sadaka) ya zama asali ga Banu Hashim sai hakan ya zama yayi naso kuma ya bi-bi-yi 'yantattun bayinsu, Yayin da kuma haramcinta ga matan Annabi ( s a w ) reshen haramcinta ne a gare shi sai hakan bai yi karfin ya bi-bi-yi 'yantattun bayinsu ba; saboda kasancewarsu reshen reshe.

su ka ce: ga shi Allah madaukaki ya ce:

                        ﯵﯶ    وساق الآيات إلى قوله تعالى:                     ﮚﮛ      

ya karanto ayoyin nan, sannan ya ce: " sai su ka shiga cikin Ahlul baiti; saboda zancen gaba dayansa cikin jerin ambatojnsu ne; don haka ne ma baya halatta a fitar da su cikin wani abu daga cikijhnsa. Wallahu a'alam ".

Amma dalili kan haramcin sadaka ga 'yantattun bayin Banu Hashim shi ne abin da Abu dawud ya ruwaito cikin sunsn dinsa (1650) da tirmiziy (657) da Nasa'i (2611) da sanadi ingacecce - lafazin kuma na Abu dawud ne - daga Abu rafi'i ( r a ) Lallai Annabi ( s a w ) Lallai Annabi ( s a w ) ya tura wani daga Banu makhzumin aikin zakka, sai ya ce wa Abu rafi'i: Ka aboce ni ( ka raka ni); don kai ma ka samu daga zakkan, Sai ya ce masa: Sai na je wajen Manzon Allah ( s a w ) na tambaye shi, sai ya zo masa ya kuma tambaye shin; Sai Annabi ( s a w ):

 " مولى القوم من أنفسهم، وإنا لا تحل لنا الصدقة "

Ma'ana: " 'yanceccen bawan Mutane na daga kayukansu ( saboda ya na daukar hukuncinsu); Mu kuma zakka bata halatta mana ".




FASALI NA BIYU:

DUNKULEN AKIDAR AHLUS SUNNA WAL JAMA'A KAN AHLUL BAITI:


  Akidar Ahlus sunna wal jama'a tsaka-tsaki ne tsakanin wuce gona-da-iri da kuma gajertawa wajen bada hakkoki a dukkan nin mas'alolin akida; daga ciki kuwa akwai: Akidarsu kan iyalan gidan Manzon Allah ( s a w ); sun kasance su kan so su kuma jibinci dukkan musulmi da musulma daga tsatson Abdil muddalib, haka kuma matayen Annabi ( s a w ) gaba ki dayansu; suna son gaba daya, suna kuma yaba musu, sannan suna saukar da su matsayinsu da su ka cancance shi da adalci, ba,da son zuciya ko kakale ba, Kuma sun san falalan wanda Allah ya hada masa daukakar imani da daukakar danganta; don haka duk wadda ya kasance daga cikin ahlul baiti na cikin sahabban Manzon Allah to su kan so shi saboda;
1- imaninsa da takawarsa.
2- da kuma abotarsa da Manzon Allah ( s a w ).
3- sannan don kusancinsa da shi.
amma in ba sahabi ba ne kuma to su kan so shi saboda;
1- imaninsa da tsoron Allansa!
2- da kuma kusancinsa da manzon Allah ( s a w ).
kuma sun gudure cewa daukakar danganta na bin daukakar imani ne; wannan ya hukunta duk wanda Allah ya hada masa biyun to hakika ya hada masa kyawawan abu biyu, wanda kuma bai datar da shi da imani ba to daukakar dantaka ba zai amfanar da shi da komai ba; Allah yana cewa:

            ﮅﮆ   

Ma'ana: " Lallai mafi karamcinku ( girmanku) a wajen Allah shi ne: mafi takawanku ( wadda yafi tsoron Allah), Annabi ( s a w ) ya ce a karshen hadisi dogo da Muslim ya ruwaito shi cikin sahihinsa ( 2699) daga Abu hurairata ( r a ):

 " من بطَّأ به عملُه لم يسرِع به نسبُه"

Ma'ana: " Duk wadda aikinsa ya yi saibi da shi to dangantansa ba zai gaggautar da shi ba "
Ibnu Rajab - Allah ya yi masa rahama - ya fada a sharhin wannan hadisin cikin littafinsa Jami'ul ulumi wal hikam (p308) - " Ma'anarsa: shi dai aiki shi ke kai ya isar da Mutum darajar Lahira kamar yadda Allah ya madaukaki ya ce:

      ﭔﭕ     

Ma'ana: " Kowa yana da daraja ne gwargwadon aikinsa" don haka duk wadda aikinsa ya yi saibin ya isar da shi matakai madaukaka a wajen Allah madaukaki, to dangantarsa ba zai yi sauri da shi ya isar da shi wadannan darajojin ba; domin Allah madaukaki ya rataya sakamako ne a kan aiki ba a kan danganta ba, kamar yadda ya ke cewa:


                              

Ma'ana: " Idan aka yi busa cikin kaho ( busan farko ko na biyu) to a wannan yinin kam babu dangantaka tsakaninsu, kuma ba za su tambayi juna ba ". Hakika Allah madaukaki ya yi umurni da gaugawan neman gafararsa da rahamarsa da aiyuka, kamar yadda ya ce:

                                                    ﭧﭨ                                                       ﭿ            

Ma'ana: " Kuma ku yi gaugawa zuwa ga wata gafara daga ubangijinku da wata aljanna da fadinta shi ne fadin sammai da kassai, da aka tanada ta ga masu tsoron Allah * wadanda su ke ciyarwa cikin saukin rayuwa da kunci ( kowani hali), masu kuma hadiye fushi ( kamewa daga gare shi ), masu afuwa wa Mutane ... " sannan ya ce:

          ﯿ                                                                      

 Ma'ana: " Lallai wadanda su ka kasance dangane da tsoron Ubangijinsu masu tsoro ne * wadanda su ka kasance dangane da ayoyin Ubangijinsu ( ayoyinsa na halittunsa da su ke nuna kadaitakarsa, da ayoyinsa wadanda su ne umurninsa da haninsa) su ka kasance masu imani * kuma wadanda su ka kasance dangane da Ubangijinsu basa hada shi da waninsa ( basa shirka ) * kuma su ne wadanda su ke bada abin da su ke bayarwa ( na sadaka da zakka da sauran aiyuka) alhalin zukatansu su na tsorace, lallai su zuwa ga ubangijinsu za su koma * to irin wadannan su na gaugawa cikin alkhairori, su din nan kuma zuwa gare su masu rigaye ne " 
sannan sai ya ambaci dalilai da ke kwadaitarwa kan aiyukan kwarai, da cewa samun kusaci da Annabi ( s a w ) kawai yana kasancewa ne da takawa da kuma aikin kwarai, sannan sai ya rufe da hadisin Amru bn Al' aas ( r a ) cikin sahihul Bukhari ( 5990) da sahihu Muslim (215), ya ce: " Hujja kan duk abin da ya gabata shi ne abin da ya zo cikin Bukhari da Muslim daga Amru bn Al' aas lallai shi ya ji Annabi ( s a w ) ya na cewa:

" إن آل فلانٍ ليسوا لي بأولياء، وإنما وليِّي الله وصالحُ المؤمنين "

Ma'ana: " Lallai Iyalan wane ba masoya na ba ne, abin sani kawai; Masoyi na shi ne: Allah da kuma salihan muminai " kaga yana nuni cewa soyayyarsa ba a samunta da dangantaka ko da kuma ya yi kusaci, kawai dai ana samunta ne da imani da aiki na kwarai; don haka; Duk wadda ya kasance ya fi cikar imani da aiki to ya fi zama cikakken masoyinsa; dai dai ne: yana da dangantaka na kusa da shi, ko ba shi da ita; Shi ya sa wani ya ke cewa:


لعمرُك ما الإنسانُ إلا بدينه 
  فلا تترك التقوى اتكالاً على النسَب

لقد رفع الإسلامُ سلمانَ فارسٍ 
  وقد وضع الشركُ النسيبَ أبا لهب


Ma'ana: Mutum ba komai ba ne sai da addininsa; a kan haka: kada ka bar biyayya wai don dogararka da danganta;
shin ba ka san! Musulunci ya daukaka Salmanul farisiy ba ne, kamar kuma yadda shirka ya kaskantar da 'dan dangi: Abu lahabi ".



FASALI NA UKU:

FALALAR AHLUL BAITI CIKIN QUR'ANI

  Allah madaukaki da buwaya yana cewa:

                                                                                                                             ﯵﯶ                                                          ﭦﭧ                                              ﭽﭾ  ﭿ             ﮅﮆ                                                      ﮚﮛ                        .

Ma'ana: " Ya kai wannan Annabi! ka gaya wa Matanka in kun kasance ku na nufin rayuwar duniya da kawarta to ku zo na jiyar da ku dadi, na kuma sake ku shika mai kyau * idan kuma kun kasance kuna nufin Allah ne da Manzonsa da gidan lahira to Allah ya yi tanadi wa mai kyautatawa daga cikinku lada mai girma * ya ku matan wannan Annabin duk wadda ta zo da alfasha mabayyaniya daga cikinku to za a ninka mata azaba ninki biyu; haka kuwa mai sauki ne a wajen Allah * amma wacce ta yi biyayya wa Allah da Manzonsa kuma ta aikata aiki mai kyau to za mu bata ladanta kashi biyu, kuma mun mata tanadin arziki mai karamci ( a cikin gidan aljanna tare da manzon Allah) * Ya ku matan wannan Annabin ku fa ba dadai ku ke da sauran mata ba idan ku ka kiyaye dokoki Allah; don haka kada ku yi kan-kan da murya; sai wadda akwai cutar sha'awa a zuciyarsa ya yi kwadayi, ku dai ku fadi magana sananne (wanda ba fitina cikinsa) * kuma ku zauna cikin gidajenku kada ku yi fita irin ta jahiliyyar farko, kuma ku tsayar da salla, ku bada zakka, ku yi biyayya wa Allah da Manzonsa, Allah na nufin ya kawar mu ku da dauda ( Shedan da shirka da kuma dukkan sabo) ya ku Mutanen wannan gidan, ya kuma tsarkake ku tsarkakewa * kuma ku tuna abin da a ke karantawa a cikin dakunanku na ayoyin Allah da hikima ( Hadisai), Lallai Allah ya kasance mai taushi ne mai bada labari "
Fadinsa:

                              

Na nuni kan falalar Dangin Annabi ( s a w ), wanda su ne sadaka ta haramta a gare su, na gaba-gaba daga cikinsu kuma su ne: Matansa da zurriyarsa - kamar yadda bayanin hakan ya gabata.

Ayoyin kuma su na nuni kan wassu falalolin matan Annabi ( s a w ):
Na farkonsu: Kasancewansu an su zabi tsakanin nufan rayuwar duniya da kawarta, da kuma zaban Allah da Manzonsa da gidan lahira Sai su ka zabi Allah da Manzonsa da gidan Lahiran, Allah ya kara musu yarda kuma ya yardar da su.

daga cikin dalilai kan falalarsu = fadin Allah madaukaki:

  ﯟﯠ     

Ma'ana: " kuma Matansa iyayensu ne "

kaga a nan ya siffanta su da cewa su iyayen Muminai ne.

Amma fadinsa mai girma da daukaka:

                        ﭣﭤ   

Ma'ana: " Ka ce bana tambayanku lada ( kan da'awata da duk alkhairi da na ke isar mu ku ) sai ku so ni saboda dangantakana da ku ( wato: in zan rasa amsawarku ga da'awata to bai kamata na rasa soyayyarku ba; saboda ni danginku ne! ya ku kuraishawa!!)

( ayar da ta gabata) Inganceccen ma'ananta shi ne: Dukkan kabilun kuraishawa - kamar yadda hakan ya zo cikn sahihul Bukhari ( 4818) daga Abdullahi bn Abbasin ( r a ); Bukhari ya ce:
Muhammadu bn Bash-shar ya ban labari, ya ce:
Muhammadu bn Ja'afar ya ban labari, ya ce:
Shu'ubatu ya ban labari, ya ce:
daga Abdul malik bn Maisarata shya ce: Na ji 'Dawuus ya ruwaito daga Ibnu Abbas
Lallai shi an tambaye shi kan fadin Allah:

      ﭣﭤ 

Sa'idu bn Jubair ya ce: Makusanta: iyalan Annabi ( s a w ), Sai Ibnu Abbas ya ce: ka yi gaugawa; domin Annabi ( s a w ) babu wani gida ( kabila ) daga cikin gidajen Kuraisahawa face yana da danganta a cikinsu, Sai Ibnu Abbas ya ce: (ma'anar ayar)  Sai dai ku sadar da abin da ke tsakani na da tsakaninku na dangantaka.
Ibnu Kasir ya ce - a tafsirinsa ga ayar -: " Kace - Ya kai Muhammad! - ga wadannan mushirkan kafiran Kuraishawa: Ba zan tambaye wani dukiya ba da za ku ban shi kan wannan isar da manzoncin da kuma nasihata gare ku, kawai dai; Ina nema daga gare ku ku kame sharrinku daga gare ni, kuma ku kale ni na isar da manzancin ubangijina; in ba ku taimake ni ba to kar ku cutar da ni; saboda abin da ke tsakanina da tsakaninku na dangantaka ". sannan sai ya kawo maganan Ibnu Abbas da ya gabata.
Amma kebancewan da 'Yan bidi'a su ka yi wa ( Kurbah ) da cewa su ne kawai: Fadimatu da Aliyu da zurriyarsu to wannan bai inganta ba;
1- saboda ayar a Makka ta sauka, amma auren Aliyu da Fadimatu ( r a ) kuma a Madina, Ibnu Kasir yana cewa: " Wai ace kuma ayar ta sauka a Madina ne to wannan (ingancinsa ) ya yi nisa ; saboda saukarta a Makka,
2- kuma a wannan lokacin Fadimatu bata da 'Ya'ya kwata-kwata; saboda ai bata yi aure da Aliyu ba sai bayan yakin badar da a ka yi a shekara ta biyu da hijira, Kai dai gaskiya shi ne: a fassara ayar da abin da Malamin al'umma, ma-fassarin Qur'ani Abdullahi bn Abbas ( r a ) ya fassara ta da shi, kamar yadda Bukhari ya ruwaito ". sannan sai ya ambaci dalilai da su ke nuna Falalan Iyalan gidan Manzon Allah ( s a w ) daga hadisan Annabi ( s a w ) da kuma maganganun Abubakar da Umar ( r a ).





FASALI NA HUDU:

FALALAN AHLUL BAITI CIKIN SUNNA MA-TSARKAKIYA ( HADISAN ANNABI S A W )

  Muslim ya ruwaito cikin sahihinsa ( 2276) daga Wasilatu bn Al-aska'a ( r a ) lallai shi ya ce: Na ji Manzon Allah ( s a w ) yana cewa:

 " إنَّ الله اصطفى كنانة من ولد إسماعيل، واصطفى قريشاً من كنانة، واصطفى من قريشٍ بني هاشم، واصطفاني من بني هاشم "

Ma'ana" Lallai Allah ya zabi Kinanat daga 'Ya'yan Annabi Isma'il, ya kuma zabi Kuraishawa daga Kinanat, haka kuma ya zabi Banu Hashim daga daga Kuraishawa, sannan ya zabe ni daga Kuraishawa "
Kuma Muslim ya ruwaito cikin sahihinsa ( 2424 ) daga A'ishatu ( r a ) lallai ta ce: Manzon Allah ( s a w ) ya fita a wata safiya yana sanye da mayafi mai zane - zane da aka yi shi da bakin gashi; Sai Hassan bn Aliyu ya shigo sai ya shigar da shi cikinsa ( mayafin ), sannan sai Husaini ya zo sai ya shiga tare da shi, sannan sai Fadimatu ta zo sai ya shigar da ita, sannan sai Aliyu ya zo sai ya shigar da shi, sannan ya ce:

                                [الأحزاب: ٣٣]

 Ma'ana: " Abin sani kawai Allah na nufin ya kawar mu ku da dauda ne ( shedan da shirka ) ya ku mutanen wannan gidan, kuma ya tsarkake ku tsarkakewa ".
Muslim ya sake ruwaitowa ( 2404 ) daga hadisin Sa'ad bn Abiy Wakkas ( r a ) lallai shi ya ce: " yayin da wannar ayar ta sauka:

               [آل عمران: ٦١]

 Sai Annabi ( s a w ) ya kira Aliyu da Fadima da Hassan da Husaini; sa'anan ya ce:

" اللهم هؤلاء أهل بيتي "

Ma'ana: " Ya Allah wadannan iyalan gidana ne ".
Kuma Muslim ya sake ruwaitowa cikin sahihinsa ( 2408 ) da sanadinsa daga Yazeed bn Hayyan, lallai shi ya ce: Na tafi - ni - da Husain bn Sabrata da Umar bn Muslim zuwa ga Zaid bn Arkam; yayin da mu ka zauna a wajensa; sai husain ya ce masa:

 (( لقد لقيت - يا زيد! - خيراً كثيراً؛ رأيت رسول الله r، وسمعت حديثَه، وغزوت معه، وصلَّيت خلفه، لقد لقيت ـ يا زيد! - خيراً كثيراً؛ حدِّثْنا - يا زيد! - ما سمعتَه من رسول الله r )).

Ma'ana: Ya Zaid! Hakika ka hadu da alkhari mai yawa; kaga Manzon Allah ( s a w ), kuma ka ji maganansa, kuma ka yi yaki da shi, haka kuma ka yi sallah a bayansa, Zaidu! Hakika ka gamu da alkhari mai yawa; to ka bamu labarin abin da ka ji daga Manzon Allah ( s a w ) ya kai zaidu!
Sai ya ce: ya 'dan 'dan uwana! Wallahi! Shekaruna sun yi yawa, kuma zamanina ya tsufa, na kuma manta sashen abin da na rike daga MAnzon Allah ( s a w ); don haka: abin da na baku labari ku karba, abin da kuma ban baku ba to kada ku kallafa min baku shi, sannan ya ce: Manzon Allah ( s a w ) ya tashi a cikinmu yana mai khuduba a wajen wani ruwa da ake kira Khum - tsakanin Makka da Madina - sai ya yi godiya wa Allah ya kuma yaba masa, ya kuma yi wa'azi ya tunatar, sannan ya ce:

 " أما بعد! آلا أيها الناس! فإنما أنا بشرٌ يوشك أن يأتي رسول ربي فأجيب، وأنا تاركٌ فيكم ثقلين؛ أولهما: كتاب الله؛ فيه الهدى والنور؛ فخذوا بكتاب الله واستمسكوا به )، فحثَّ على كتاب الله ورغَّب فيه، ثم قال: ( وأهل بيتي، أذكركم الله في أهل بيتي، أذكركم الله في أهل بيتي، أذكركم الله في أهل بيتي "

Ma'ana: " Bayan haka! Ya ku mutane ku saurara! sakawai ni Mutum ne; ya yi kusa kuma Manzon Ubangijina ya zo min sai na amsa ( wato: yana nufin mai daukar rai ); sannan Ni zan bar mu ku da nauyayaan abu biyu; na farkonsu: Littafin Allah; cikinsa akwai shiriya da haske; don haka! ku dau littafin Allah kuma ku yi riko da shi " ya kwadaitar kan littafin Allah sannan ya ce: " da kuma iyalan gidana; Ina tunatar da ku Allah kan iyalan gidana! Ina tunatar da ku Allah kan iyalan gidana!! Ina tunatar da ku Allah kan iyalan gidana!!! "
Sai Husain ya ce masa: Su wanene Iyalan gidansa? - ya kai Zaidu! - Shin Matansa basa cikin Iyaln gidansa?
Sai ya ce: Matansa suna daga cikin Iyalan gidansa, sai dai Iyalen gidansa su ne wadanda aka haramta musu sadaka bayansa, sai ya ce: Wanene su? sai ya ce: Su ne Iyalan Aliyu, da Iyalan Akilu, da Iyalan Ja'afaru, da Iyalan Abbas, sai ya ce: Duk wadannan an hana su cin sadaka? Sai ya ce: na'am.

A wani lafazi: Sai mu ka ce: Su wanene Ahlu baitihi? Matansa? Sai ya ce: A'a! Na rantse da Allah!! Mace ta kan kasance tare da Mutum wani lokaci daga zamani sannan sai ya sake ta; sai ta koma wajen Babanta da Mutanenta! Iyaln gidansa: su ne Tushensa da kuma masu cin gadonsa da ta'asibi; wadanda aka haramta musu sadaka bayansa ".

Anan zan yi fadakarwa kan wassu al'amura:
Na farko: Lallai ambaton Aliyu da Fadimatu da 'Ya'yansu guda biyu cikin hadisin Mayafi da kuma hadisin Mubahala ( rantsuwa tare da tsinuwa ) da su ka gabata ba sa nuni kan takaituwan Ahlul baiti a kansu, kai dai kawai suna nuni ne cewa su ne na gaba - gaba cikin iyalensa, kuma su ne su ka fi cancantan su shiga cikin lafazin ( Ahlul baiti ); wannan kuma ishara akansa ta gabata.
Na biyu: Ambaton Zaidu ( r a ) Alu Akilu da Alu Aliyyu da Alu Ja'afar da Alul Abbas ba ya nuni cewa su ne kawai sadaka ta haramta a kansu koma bayan wassunsu; saboda ai ta haramta ga kowani musulmi da musulma na daga 'Ya'yan Abdul muddalib, kuma hadisin Abdul muddalib bn rabi'ata bn Alharith bn Abdul muddalib da ke cikin sahihu Muslim ya gabata; wanda a cikinsa ( akwai ) gamewar hakan ga 'Ya'yan Rabi'atu bn Alharith bn Abdul muddalib.
Na uku: Dalili daga Qur'ani da hadisi da ke nuna kasancewar matan Annabi ( s a w ) suna cikin iyalan gidansa, da bayanin suma sadaka ta haramta musu = ya gabata, Amma abin da ya zo cikin maganan Zaidu ( r a ) da ya gafata na shigar da su cikin Iyalan a riwayar farko, da kuma rashin shigar da su cikin riwaya ta biyu; to abin lura dai shi ne riwayar farko, amma abin da ya ambatan na rashin shigan na su abin sani kawai zai dace ne da sauran mata banda matansa ( s a w ); Amma matansa ( r a ) to lallai saduwansu da shi kamar danganta ne; saboda saduwansu da shi ba zai taba daguwa ba, kuma su matansa ne a duniya da lahira - kamar yadda bayani kan haka ya gabata cikin maganan Ibnul Kayyim - ( r a).
Na hudu: Lallai ahlus sunna wal jama'a su su ka fi kowa rabauta wajen aiki da wasiyyar Annabi ( s a w ) dangane da iyalan gidansa - wanda ya zo cikin wannan hadisin -; saboda suna sonsu gaba daya kuma suna jibintarsu, tare da ajiye kowa a matsayinsa da su ka cancanceta da adalci, amma wassunsu = hakika Ibnu taimiyya cikin majmu'u fatawa-hu ( 4 / 419 ) ya ce: " Wadanda su ka fi nisa ga barin wannar wasiyyar su ne: Rafida ( 'Yan shi'a ); saboda su na gaba da Abbas da zurriyarsa, kai suna gaba ma da mafi yawan Ahlul baitin kuma suna taimakon kafirai a kansu "

Da kuma hadisin:

 " كل سببٍ ونسبٍ منقطعٌ يوم القيامة إلا سببي ونسبي "

Ma'ana: " Dukkan wata alaka da danganta za ta yanke ranar tashin kiyama sai dai alaka da ni da danganta da ni " - Ash sheikh Albani ( r a ) ya ambace shi cikin As silsilatus sahihatu ( 2036 ) ya kuma jingina shi zuwa ga Ibnu Abbas da Umar da Ibnu Umar da Almiswar bn Makhramata ( r a ), sannan ya ambaci wanda ya fitar da hadisin daga gare su, ya ce: " Dunguln magana dai! Hadisin ya inganta da hanyoyinsa. Wal=lahu a'alam. ". ya zo a wassu hanyoyin cewa wannan hadisin shi ya sanya Umar ( r a ) ya yi kwadayin auren Ummu kulthum bintu ('Yar) Aliyu daga Fadimatu 9 Allah ya kara yarda a daukacinsu gaba dayansu ).

Kuma Imamu Ahmad ya ruwaito a cikin musnad=dinsa ( 5 / 374 ) daga Abdur razzak ya samo daga Ma'amar, daga Ibnu dawuss, daga Abubakar bn Muhammad bn Amru bn Hazmin daga wani Mutum daga cikin sahabban Annabi ( s a w ), daga Annabi ( s a w ) lallai shi ya kasance yana cewa:

" اللهم صلِّ على محمدٍ، وعلى آل بيته، وعلى أزواجه وذريته، كما صليت على آل إبراهيم إنك حميدٌ مجيدٌ، وبارك على محمدٍ، وعلى آل بيته، وعلى أزواجه وذريته، كما باركت على آل إبراهيم إنك حميدٌ مجيدٌ "

 Ma'ana: " Ya Allah! Ka kara yabo wa ( annabi ) Muhammadu, da iyalan gidansa da matansa da zuriyyarsa, kamar yadda ka yi yabo ga iyalan ( annabi ) Ibrahim; lallai kai abun yabo ne mai girma, kuma ka yi albarka wa ( annabi ) Muhammad da kuma iyalan gidansa, da matansa da zurriyarsa, kamar yadda ka yi albarka wa iyalan ( annabi ) Ibrahim; lallai kai abun yabo ne mai girma.

Ibnu Dawuss y ace: Mahaifina ya kasance yana fadan kwatankwacin wannan.

 Mazajen isnadin da ke kasan Sahabin Bukhari da Muslim da ma'abota sunan guda hudu ( Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah ) sun fitar da hadisinsu.
 Albani ya fada a cikin siffar sallan Annabi ( s a w )…  cewa: " Ahmad da 'Dahawiy sun ruwaito shi da sanadi ingancecce ".

  Amma ambaton salati wa wadannan Matan da zuriyar ( Matan Annabi s a w da zuriyarsa ) to kuma shi ma ya tabbata cikin Bukhari da Muslim daga hadisin Abu Humaid as sa'idiy ( r a ).
 Sai dai ( hadisin ) baya nuna takaituwan Ahlul baiti kan Matan da zurriyar kawai; abin sani dai sani dai kawai na tabbatuwan shigansu ( cikin Ahlul baiti ) da kuma rashin fitarsu.
 Amma ambaton Matansa da zuriyarsa da aka yi bayan ( lafazin ) Ahlul baiti ( wadda ya game su …) cikin hadisin da ya gabata, tare da yin ADAFINSU akansa  to wannan na daga cikin ambaton takaiceccen abu bayan ambaton ( lafazi ) mai fadi ( da ya kunshi ta kaiceccen; don kara bawa takaiceccen muhummanci ).  Ibnul Kayyim yana cewa bayan ya ambaci wani hadisin da aka ambaci: Ahlul bai, da kuma wadannan Matan da zurriyar – amma akwai maganganun Malalai kan ingancin sanadinsa - : " sai ya ambaci mata da zurriya da kuma iyalai kuma ya  hada su, abin sani kawai ya bayyana su karara ne don ya bayyana cewa su din nan ( mata da zurriyar ) su su ka fi cancantar shiga cikin – lafazin – ( Al aal ), kuma ba za su taba fita daga cikinsa ba, kuma su ne wadanda su ka fi cancantan wadanda su ka shiga cikinsa, wannan kuma kamar irinsa ne ( da yawa ) ADAFUL KHAS ALAL AMM, WA AKSIHI ( wato: ambaton kuntaceccen lafazi bayan ambaton mai fadin da kuntaceccen ya ke cikinsa don kara nuna muhimmacin kebanceccen[1]. Amma kishiyan haka kuma shi ne: A fara ambaton kebanceccen lafazin sannan a bi bayansa da mai fadi! ); ana yin haka ne ( ambaton kebanceccen bayan lafazi mai fadin )don nuna daukakan kebanceccen, da kuma kebance shi da ambato daga cikin sauran nau'insa; saboda kasancewarsa shi ya fi sauran nau'in cancantan shiga cikin wannan nau'in " ( Jala'ul afhaam: shafi na 338 ).

  ( Annbi s a w) ya ce:
 " إنَّ الصدقة لا تنبغي لآل محمدٍ، إنما هي أوساخ الناس "

  " Lallai sadaka bata halatta ga iyalan Muhammadu; abin sani dai ita daudar Mutane ne " Muslim ne ya ruwaito shi daga hadisin Abdul muddalib bn rabi'ata ( 1072 ) kamar yadda ya gabata.


FASALI NA BIYAR:

DAUKAKAN MATSAYIN AHLUL BAITI A WAJEN SAHABBAI DA WADANDA SU KA BI SU DA KYAUTATAWA

  Abubakar as siddiq ( r a ):

Bukhari ya ruwaito cikin sahihinsa ( 3712 )cewa Lallai Abubakar ( r a ) ya ce wa Aliyu ( r a ):

 (( والذي نفسي بيده لقرابة رسول الله r أحبُّ إليَّ أنْ أصل من قرابتي ))

 Ma'ana: " Na rantse da wadda raina ya ke hanunsa! Wallahi dangin Manzon Allah ( s a w ) su su ka fi soyuwa a wajena da na sadar fiye dad angina"

 Kuma Bukhari ya sake ruwaitowa cikin sahihinsa ( 3713 ) daga Ibn Umar ( r a ), daga Abubakar ( r a ) ya ce:

 (( ارقُبُوا محمداً r في أهل بيته ))  

 Ma'ana: " Ku kiyaye Muhammad ( s a w ) cikin iyalan gidansa ".
 Ibnu Hajar ya ce a sharhinsa: " ( Abubakar ya fadi wannan ne)  yana mai zance da Mutane kuma yana musu wasiyya da shi, Abin da ake nufi kuma da
المراقبة للشيء:
Shi ne: kiyaye shi, ( Abubakar kenan ) yana cewa: ku kiyaye shi ( s a w ) kuma ku lura da shi a cikinsu; don haka; kada ku cutar da su kuma kada ku munana musu ".

Yazo a cikin sahihul Bukhari ( 3542 ) daga Ukbatu bn Al-harith ( r a ) lallai ya ce:

 (( صلَّى أبو بكر ( t ) العصر، ثم خرج يمشي، فرأى الحسنَ يلعب مع الصبيان، فحمله على عاتقه، وقال:
بأبي شبيهٌ بالنبي

لا شبيهٌ بعلي
 وعليٌّ يضحك ))

 Ma'ana: " Abubakar ( r a ) ya yi  sallan la'asar sannan sai ya fita yana tafiya, sai yaga Al hasan yana wasa da yara, sai ya dauke shi akan kafadarsa ya kuma ce: Ina fansanka da Babana! ( wannan ) ya yi kama da Annabi, be kuma yi kama da Aliyu ba, Aliyu kuma ( yana ji ) yana dariya ".

Ibnu Hajar a sharhinsa ya ce: "fadinsa:
( بأبي )
Akwai wani abin da aka goge, ana kaddara shi da
 (أُفْدِيه )
 Ma'ana: Ina fansansa da Babana!.
Ya kuma ce:
 (( وفي هذا الحديث فضلُ أبي بكر ومحبتُه لقرابة النبيٍّ  r ))

 Ma'ana: cikin wannan hadisin akwai falalar Abubakar, da kuma sonsa ga dangin Annabi ( s a w ) ".

 Umar bn Al khaddaabi da kuma Uthman bn Affan ( r a ):

 Bukhari ya ruwaito cikin sahihinsa ( 1010 ), da ( 3710 ) daga Anas ( r a ) ya ce:

 (( إنَّ عمر بن الخطاب كان إذا قُحِطوا استسقى بالعباس بن عبد المطلب، فقال: اللهم إنا كنا نتوسَّل بنيِّنا  r فتسقينا، وإنا نتوسَّل إليك بعمِّ نبيِّنا فاسقنا، قال: فيُسقَون )).

 Ma'ana: " Lallai Umar bn Al khaddab ya kasance idan aka musu fari yak an nemi shayarwa da addu'an Abbas bn Abdul muddalib, sai ya ce: Ya Allah! Lallai mum un kasance muna tawassuli ( neman tsani da kamun kafa ) da addu'ar Annabinmu ( s a w ), Sai ka shayar dam u ( kamar yadda ya faru a kisser Balaraben kauye ranar Juma'a da yadda ya nemi Annabi s a w ya roki Allah ya saukar da ruwa!, cikin kissa sananniya ) to ( yanzu kuma ) lallai muna nema tsani da addu'ar baffan Annabinmu! ( ya Allah! ) ka shayar da mu! Sai ya ce: Sai a shayar da sun! ( ruwa ya sauko )

 Abin da ake nufi da tsanin da Umar ( r a ) ya nema da Abbas ( r a )  shi ne: neman tsani ne da addu'arsa kamar yadda bayanin hakan ya zo abayyane karara cikin wassu riwayoyin, kuma Al hafiz ( Ibnu Hajar ) ya ambace su a sharhin hadisin a KITABU LISTISKA'I a fathul bari.

  Zabin kuma da Umar ( r a ) ya yi wa Abbas ( r a ) don ya yi tsani da addu'ansa to hakan ya kasance ne saboda kusacinsa da Manzon Allah ( s a w ); shi yasa ma y ace a cikin tawassulin nasa:

 ((وإنا نتوسَّل إليك بعمِّ نبيِّنا  ))

  Be ce: da Abbas ba! Sai ya ce kuma lallai mu muna neman kusaci zuwa gareka da addu'ar BAFFAN ANNABINMU!

 Kuma dai sananne ne Lallai Aliyu ( r a ) ya fi Abbas falala da daukaka, kuma yana cikin dangin ( makusantan ) Manzon Allah ( s a w ), Sai dai Abbas kuma ya fi shi kusanci, kuma da Annabi ( s a w ) za a gaji dukiyansa to da Abbas shi za a gabatar cikin haka; saboda fadin Manzon Allah ( s a w ):

  " ألحِْقوا الفرائضَ بأهلها، فما أبقت الفرائض فلأَوْلى رجلٍ ذكر "

  Ma'ana: " Ku riskar da gado[2] zuwa ga ma'abotanta ( masu ita ), abin da ya saura – bayan an cire rabon masu rabo -  to  sai a bada shi ga mafi kusa kuma namiji " Bukhari da Muslim ne su ka ruwaito shi. Ya zo kuma cikin Sahihul Bukhari da sahihu Muslim daga cikin hadisin Abu Huraira = fadin Manzon Allah ( s a w ) wa Umar kan Baffansa Abbas:

  " أما علمتَ أنَّ عمَّ الرجل صنوُ أبيه "

  Ma'ana: " Shin ba ka sani ban e; Lallai Baffan Mutum kwatankwacin babansa bane?
    A cikin tafsirin ibn kasir ga ayoyin shura lallai umar bn kaddab yace wa Abbas (r.a) :

  (( والله! لَإسلامُك يوم أسلمتَ كان أحبَّ إليَّ من إسلام الخطاب لو أسلم؛ لأنَّ إسلامك كان أحبَّ إلى رسول الله r من إسلام الخطاب))

 Ma'ana: " Wallahi!! Lallai musuluntarka  a ranar da ka musulunta ya fi soyuwa a gare ni fiye da musuluntar Khaddabi day a musulunta!!; saboda musuluntarka ya fi soyuwa a wajen Manzon Allah ( s a w ) fiye da musuluntar Khaddabi " Ibnu Sa'ad cikin littafin Dabakaat ( 4 / 22, 30 ).

 A cikin littafin Iqtidha'us siradis mukhalafati ashabul jahim ( 1 / 446 ) na shaikhul islam Ibn taimiyya ( r ahimahul lah ):
" Lallai Umar ( r a ) yayin day a sanya rigistan kyauta ya rubuta mutune ne gwargwadon dangantakansu; sai ya farad a mafi kusacin dagantaka da Manzon Allah ( s a w ) sai wadda ke biye da shi,… day a kamala larabawa sai kuma ya shiga cikin ajamawa, haka register =n ya kasance a zamanin Khalifofi shiryeeyyu, da kuma sauran Khalifofin umawiyya da 'Ya'yan Abbas ( abbasiyyawa), sannan daga baya abun ya canza ".
 Kuma ya sake cewa ( 1 / 453 ):  " Ka yi dubi zuwa ga Umar bn Al khaddabi ( r a ) yayin day a sanya register; kuma aka ce da shi: Amirul mu'uminina ya farad a kansa! Sai y ace:

 (( لا؛ ولكن ضعوا عمر حيث وضعه الله! ))

 A'a; ku dai ku sa Umar in da Allah ya sanya shi " Sai ya fara da iyalan gidan Manzon Allah ( s a w ), sannan sai wadanda su ke biye da su, har aka iso layinsa cikin Banu adiyyin; wadda su na daga karshe karshe ne cikin cikkunan kuraishawa.

 Kuma ya gabata cikin ( FALALAR AHLUL BAITI DAGA HADISAI) hadisin:

" كلُّ سببٍ ونسَبٍ منقطعٌ يوم القيامة إلا سببي ونسَبي "

 Ma'ana: " Dukkan wata alaka da kuma dangantaka mai yankewa ne ranar tashin kiyama sai dai alaka da ni ko dangantaka ta " Wadda wannan shi ya tunkuda Umar ( r a ) zuwa ga neman auren Ummu kulthuum bint Aliyu. Albaniy a cikin silsilatus sahihatu karkashin lamba ( 2036 ) ya ambaci hanyoyin wannan hadisin daga Umar ( r a ).

  Kuma sananne ne dukkan Khalifofi shiryeyyu guda hudu ( r a ) surkan Manzon Allah ne ( s a w );  Abubakar da Umar ( r a ) sun samu Karin daukaka da auren Annabi ( s a w) 'ya'yansu: A'ishatu da Hafsatu. Usman kuma da Aliyu ( r a ) sun samu Karin daukaka saboda auren 'ya'yan Manzon Allah ( s a w ); Usman ( r a ) ya auri Rukayya, bayan rasuwarta kuma ya auri 'yar' uwarta Ummu Kulthuum; shi ya sa ma ake ce masa: Zun nuuraini, Aliyu ( r a ) kuma ya auri Fadimatu ( r a ).
Ya zo cikin siyaru a'alamin nubala'i na Zahabi da tahzibut tahzibi na Ibnu Hajar cikin tarjamar Abbas: " Lallai shi Abbas idan ya zo shige Umar ko UThman alhali suna kana bin hawa sai su sauka har sai ya shige su; don girmama baffan Manzon Allah ( s a w ) ".


UMAR BN ABDIL' AZIZ ( rahimahul lah ):

Ya zo cikin 'Dabakaat din Ibnu Sa'ad ( 5 / 333 ) da ( 5 / 387 – 388 ) da sanadinsa zuwa ga Fadimatu bint Aliyu bn abiy 'Dalib Lallai Umar bn Abdil'aziz y ace mata: " Yak e 'Yar Aliyu! Wallahi!!  A doron kasa babu mutanen wani gida da su ka fi soyuwa a wajena fiye da ku, kuma wallahi ku ku ka fi soyuwa a wajena fiye da iyalan gidana".

ABUBAKAR IBN ABIY SHAIBATA ( rahimahul lah ):

  Ya zo cikin tahzibul kamali na Mizziy cikin tarjamar Aliyu bn Al husain; Abubakar ibnu abiy Shaibata ya ce: " Mafi ingancin sanadi gaba daya shi ne: Zuhuri ya karbo daga Aliyu bn Alhusain daga babansa daga Aliyu ".

SHAIKHUL ISLAM IBNU TAIMIYATA ( rahimahul lah ):

  Ibnutaimiyyat ( rahimahul lah ) ya ce a cikin akidatul wasidiyyatu: " Kuma  suna son ( yana nufin: Ahlus sunnati wal jama'ati )  Iyalan gidan Manzon Allah ( s a w ) kuma suna jibintarsu, kuma suna kiyaye wasiyyar da Manzon Allah ( s a w ) ya yi a kansu ta yadda ya ce -  a ranar da su ka huta a rijiyar da ta ke Khum ( Gadir Kuum):

   " أُذكِّركم الله في أهل بيتي! "

 Ma'ana: Ina tunatar da ku Allah kan iyalan gidana! ",
  Sannan ya ce dangane da Abbas – alhalin ( Abbas ya koka masa cewa lallai wassu daga cikin kuraishawa sun a musu jafai'i ( basa basu hakkinsu :

 " والذي نفسي بيده! لا يؤمنون حتى يحبُّوكم لله ولقرابتي "

 " Na rantse da wadda raina ke hanunsa! Wallahi imaninsu ba zai cika ba har sai sun so ku don Allah da kuma kusaci da ni ".
 Ya ce:

 " إنَّ الله اصطفى من بني إسماعيل كنانة، واصطفى من كنانة قريشاً، واصطفى من قريشٍ بني هاشم، واصطفاني من بني هاشم "

 Ma'ana: " Lallai Allah ya zabi kinanata daga cikin 'ya'yan Isma'il, ya zabi kuraishawa dag cikin kinana, ya kuma zabi banu Hashim daga cikin kuraishawa, sannan ya zabe ni daga cikin banu Hashim ".
 Sannan sun a jibintar matan Manzon Allah ( s a w ) uwayen mu'uminai, sun kuma yi imani da cewa su matansa ne a lahira; musamman Khadija ( r a ); uwar mafi yawan 'ya'yansa, sannan farkon wadda ya yi imani da shi kuma ya karfafe shi kan a'amarinsa, dama ta kasance tana da matsayi madaukaki a wajensa.da kuma mai yawan gaskiya 'yar mai yawan gaskiya ( A'ishatu bint Abubakar r a ) wacce Annabi ( s a  w) ya fada a kanta:

 " وفضل عائشة على النساء كفضل الثريد على سائر الطعام "

 Ma'ana: " Kuma fifikon A'isha kan mata kamar fifikon sarid[3] ne akan sauran abinci ". Kuma suna bara'a ( kubutuwa da kauracewa ) irin hanyar 'Yan shi'a da su ke kin sahabbai kuma su ke zaginsu, da kuma irin hanyar Nasibawa[4] da su ke cutar da Ahlul baiti da Magana ko da aiki ".

  Ya sake cewa kuma a cikin littafinsa alwasiyyatul kubra, kamar yadda yak e cikin majmu'ul fatawansa ( 3 / 407 – 408 ): " Haka kuma iyalan gidan Manzon Allah ( s a w )!; suna da hakkokin day a zama dole a lura da su; saboda Allah ya sanya musu rabo daga Khumusi da kuma Fai'u[5], sannan ya yi umurni da a musu salati tare da Manzon Allah ( s a w ); ya ce:


 " قولوا: اللهم صلِّ على محمدٍ، وعلى آل محمدٍ، كما صليت على آل إبراهيم إنك حميدٌ مجيدٌ، وبارك على محمدٍ، وعلى آل محمدٍ، كما باركت على آل إبراهيم إنك حميدٌ مجيدٌ "

  Su ko iyalan Muhammad ( s a w ) su ne wadanda aka hana su cin sadaka; haka Shafi'i da Ahmad bn Hanbal da wassunsu daga cikin maluma ( rahimahumul lah ) su ka fada; saboda Annabi ( s a w ) ya ce:

 " إنَّ الصدقة لا تنيغي لمحمدٍ ولا لآل محمدٍ "

  Ma'ana: " Lallai ita sadaka bata halalta wa Muhammad haka kuma ga iyalan Muhammad ". Allah madaukaki ya fada cikin littafinsa:

                               

 Ma'ana: " abin sani kawai: Lallai Allah na nufin ya tafiyar muku da dauda ne yak u mutanen wannan gidan! Kuma ya tsarkake ku tsarkakewa "; sannan Allah ya haramta musu sadaka ne saboda kasancewarta daudar mutane ".

  Sannan ya kuma fada a cikin MAJMU'UL FATAAWA ( 28 /  491 ): " Haka kuma iyalan gidan Manzon Allah ( s a w ) wajibi ne a so su kuma a jibince su sannan a kiyaye kuma a lura musu da hakkinsu ".

 IBNUL KAYYIM ( rahimahul lah ):

  Ibnul kayyim ya ce – alhalin yana yin bayanin dalilai da sabbuban da yasa Mutane ke karbar gurbaceccen tafsiri - : " Sababi na uku: Shi ne mai fassaran ya jingina fassaran nasa zuwa ga wani mai girman matsayi, wadda kuma ambatonsa ya tashi cikin gwarzontaka na daga masu hankali, ko iyalan gidan Annabi ( s a w ), ko wadda ya ke da yabo mai kyau cikin al'umma, ya ke kuma da harshen gaskiya, Sai ya yi kwalliya wa maganan nasa ( da jingina shi zuwa ga irin wannan Mutumin ) a cikin zuciyar JAHILAI; domin yana daga cikin sha'anin Mutane: Girmama maganan wadda yak e da matsayi mai girma cikin zuciyarsu, har ma za su iya gabatar da maganan nasa akan maganan Allah da Manzonsa, kuma su ce: Shi ya fi mu sanin Allah!

Da wannan hanyar ne 'Yan shi'a da Isma'iliyya da Nusairiyya su ka isa zuwa ga: tallen barnar da su ke kai, da kuma tafsirorinsu; yayin da su ka jingina su zuwa ga iyalan gidan Manzon Allah ( s a w ); wannan kuma ya kasance ne yayin  da su ka san dukkan musulmai sun hadu kan son su da girmama su; Sai su ka jingina zuwa gare su kuma su ka bayyana: soyayyarsu da kuma girmama su da ambaton falalansu; ta yadda mai sauraronsu zai ga kamar su din nan masoyansu ne, sannan su ka yi tallen barnarsu ta hanyar  jingina ta zuwa gare su.

La'ilaha illal lah!! Nawa-nawa daga munafurci da kuma keta haddi da bidi'a ta tallatu a duniya da wannan sababin – alhala su kuma basu da alaka da ita!!!
 Idan ka lura da wannan sababin za ka ga shi ked a rinjaye kan yawa – yawan zukata; don basu da wani abu face kyautata zato ga wadda ya yi fadi Magana, ba tare da hujja daga Allah ba da ke musu jagora zuwa ga haka; wannan kuma sun gado shi ne kwanza da kwarkwatarsa daga wadanda su ka bijire wa addinin manzanni saboda ya musu karo da abin da iyaye da magabata ke kai! Kuma wannan shi ne sha'anindukkan mai taklidi ( mabiyi ) ga wadda yak e girmama shi cikin abin day a saba wa gaskiya!! Har tashin kiyama " MUKHTASARUS SAWA'IKIL MURSALATI ( 1 / 90 ).

 AL HAFIZ IBNU KASIR ( rahimahul lah ):

Ibnu kasir a tafsirinsa na ayar shura – bayan ya bayyana inganceccen zance kan tafsirinta da cewa abin da ake nufi da:
القُربَى

 Shi ne: cikkunan ( kabilan ) kuraishawa ( gaba dayansu ) kamar yadda ya zo cikin tafsirin Ibnu Abbas ga ayar a cikin sahihul Bukhari – ya ce - rahimahul lah -: " Ba za mu musa wasici da aka yi kan Ahlul baiti ba! Da kuma umurni kan kan kyautata musu, da girmama su da karrama su; saboda su daga zurriya ne mai tsarki, daga kuma mafi daukakan gida da ak yi abayan kasa wajen alfahari da matsayi da dangantaka, musamman ma; idan su ka kasance masu bin sunnar Annabi ingancecciya mabayyaniya kamr yadda magabatansu su ka kasance, kamar Abbas da 'ya'yansa, da Aliyu da  iyalan gidansa da zurriyarsa, Allah ya kara yarda da su gaba daya ".
 Bayan kawo asari[6] guda biyu daga Abubakar ( r a ), sannan asari daya daga Umar ( r a )  na nuna girman Ahlul baiti da kuma bayanin daukakan matsayinsu, sai ya ce:  " Halin dattawan nan biyu ( Abubakar da Umar ) shi ne ya zama dole ga kowani Mulum ya zama kamar haka, shi ya sa su ka zama mafi daukakan mu'uminai bayan Annabawa da Manzanni, Allah ya kara musu yarda tare sauran sahabbai gaba daya ".

 AL HAFIZ IBNU HAJAR ( rahimahul lah ):

 Ibnu hajar ya fada a FATHUL BARIY ( 3 / 11 ) a wani hadisin da a cikin sanadinsa akwai: " Aliyu bn Husain daga Husaini bn Aliyu daga Aliyu bn Abiy Dalib ( r a ) " ya ce: " Wannan yana daga cikin mafi ingancin sanadi, kuma shi ne mafi daukakan tarjamomi da ke zuwa da: ( wane ) ya ruwaito daga babansa daga kakansa ".

 SHAIKHUL ISLAM MUHAMMADU BN ABDIL WAHHAB ( rahimahul lah ):

 Amma shaikhul islam Muhammadu bn Abdil wahhab ( rahimahul lah ) to yana da 'ya'ya maza shida, mace daya; sun e: Abdullahi da Aliyu da Hasan da Husaini da Ibrahim da Abdul' aziz da Fadimatu, dukkansu sun a dauke da sunan Ahlul baiti in banda Abdul' aziz; domin Abdullahi da Ibrahim 'ya'yan Annabi ne ( s a w ), sauran kuma: Aliyu da Fadimatu da Hasan da Husaini; surkinsa ( s a w ) da 'yarsa da jikokinsa.

 Zaban sunayen 'yan'yansa da sunayen wadannan na nuna sonsa ga iyalan gidan Annabi ( s a w ) da kuma girmama su da ya ke yi, wadannan sunayen kuma sun maimaitu ( da yawa ) cikin jikokinsa!.

 A karshen wannan fasalin na ke cewa: Hakika Allah ya azurta ni da 'ya'ya maza da 'ya'ya mata; wadanda na sanya mu su sunan: Aliyu da Al hasan da Al husain da kuma Fadimatu, da kuma sunan bakwai daga cikin uwayen mu'uminai. Su kuma wadanda da na sanya sunansu ( wa 'ya'yana ) hakika sun hada tsakanin kasancewarsu: Sahabbai kuma dangi ( Annabi s a w ).

  Ina gode wa Allah da ya min ni'imar son sahabban Manzon Allah ( s a w ) da kuma iyalan gidansa, kuma ina rokon Allah day a dawwamar min da wannan ni'imar, kuma ya kiyaye min zuciyata daga ki ( da hassada ) ga daya daga cikinsu, harshena kuma daga ambatonsu da abin da bai dace ba:
                                                  

 " Ya Ubangijinmu ka gafarta mu da 'yan 'uwanmu; wadanda su ka rigaye mu da imani, kuma kada ka sanya hassadar wadanda su ka yi imani cikin zuciyarmu, ya Ubangijinmu lallai kai mai tausasawa ne mai rahama ".


FASALI NA SHIDA:

YABON WASSU MALUMA GA JAMA'A DAGA CIKIN SAHABBAI AHLUL BAITI

  BAFFAN MANZON ALLAH ( S A W ) AL ABBAS BN ABDIL MUDDALIB ( r a ):

Zahabiy ya fada cikin SIYARU A'ALAMIN NUBALA'I ( 2 / 79 – 80 ):           " Ya kasance daga cikin mafi tsayin mazaje, kuma daga cikin mafi kyawunsu sura, haka kuma yana daga cikin wadanda suka fi kwarjinikuma yana daga cikin wadanda suka fi  bayyanannan sauti,tare da hakuri mai yawa da shugabanci… Azzubairu bn Bakkar  ya ce: ''Abbas yana da wani tufa day a tanada ga funtun ( wadda ba shi da tufa ) na bani Hashim,  kuma yana da akwashi day a tanada don mayunwatansu, haka kuma yana da ankwa don wawayensu, sannan ya kasance yana tsare ( hakkin ) makwabci ( ya kuma kiyaye ), ya kan kuma bada dukiya, haka yak an bayar da kyauta ga wadda ya shiga tsanani da musifa ".

 Amma fadinsa:
 (( منظرة ))
 A ( littafin )tarikhi ibni Asakir ya zo ne:
 (( مقطرة ))
 Wadda shi ne: abin da a ke daure wadda ya ketare iyaka kuma ya yi zalunci ( ankwa ) (ka yi dubi zuwa ga hashiyar SIYAR ).

 BAFFAN MANZON ALLAH ( S A W ) HAMZA BN ABDIL MUDDALIB ( r a ):

 Ibnu Abdil barri ya fada a cikin AL ' ISTIY' AB ( 1 / 270 a hasiyar AL' ISABATU): " Hamzatu bn Abdil muddalib bn Hashim, Baffan Annabi  ( yabo da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ), ya kasance ana ce da shi: Zakin Allah, da kuma: Zakin Manzon Allah ( s a w ), ana masa alkunya da : Abu umarata da kuma Abu ya'ala ".
 Zahabiy yana fada akansa: " shi ne shugaba, gwarzo, zaki, zakin Allah, Abu Umarata kuma Ya'ala, bakuraishe, bahashime, mutumin makka sannan madina, wadda ya halarci badar ( badariyyu), kuma wadda ya yi shahada, baffan Manzon Allah ( s a w ), kuma dan' uwansa na daga shayarwa " ( 1 / 172 ).

AMIRUL MU'UMININA ALIYU BN ABIY DALIB ( r a ):

Muslim ya ruwaito cikin sahihinsa ( 276 ) da sanadinsa zuwa ga Shuraih bn Hani'i Lallai shi ya ce: " Na zo wajen A'ishatu ( r a ) ina tambayanta kan shafa a khuffi, sai ta  ce: Ina horonka da Ibn abiy Dalib ka je ka tambaye shi; saboda shi ya kasance yana tafiya tare da Manzon Allah ( s a w ), Sai mu ka tambaye shi, sai ya ce: Manzon Allah ( s a w ) ya sanya kwanaki da dararensu ga matafiyi, ya kuma sanya yini da dare ga mazaunin gida ". A wata riwayarsa ta ce: " Ka je wajen Aliyu; saboda ya fi ni sanin wannan, Sai na zo wajen Aliyu, sai ya ambata daga Manzon Allah ( s a w ) kwatankwacin ( hadisin day a gabata ).
 Ibnu Abdil barri ( rahimahul lahu ) ya fada cikin AL ' ISTIY' AB ( 3 / 51 a hasiyar AL 'SABATU): " Ahmad bn Hanbal Isma'il bn Ishaka al kaadiy sun ce: Ba a ruwaito falalan wani sahabi ba da sanadi ingancecce kamar yadda aka  ruwaito falalolin Aliyu bn Abiy Dalib, haka kuma Ahmad bn Shu'aib bn Aliyu an nasa'iy ( ya fada ).

 Ya kuma sake cewa ( 3 / 47 ): " An tambayi Al hasan bn Abil Hasan albasariy kan Aliyu bn Abiy Dalib ( r a )?
 Sai ya ce: " Aliyu ya kasance – wallahi! – kibiya ne da baya kuskurewa daga cikin kibon Allah ga makiyansa, kuma rabbanin wannan al'umman ne ( shi ne: wadda ke tarbiyyantar da Mutane kan kananan ilimi kafin manyansu, kuma wadda ya hada tsakanin ilimi da aiki da shi ), kuma shi ne ma'abucin falalarta, kuma ma'abocin rigayenta ( cikin musulunci ), kuma ma'abocin kusacinta zuwa ga Manzon Allah ( s a w ), be kasance barci ban e kan al 'amarin Allah, kamar yadda bai kasance abun zargi ba cikin addinin Allah, haka kuma shi ba barawon dukiyar Allah ba ne. Ya bawa alqur'ani karfinsa sai rabauta daga gare shi ( qur'anin ) da wani irin dausyi mai 'ya'ya! Wannan shi ne Aliyu bn Abiy Dalib ya kai wawa!!! ".

 Ya kuma sake cewa ( 3 / 52 ): " Asammu ya ruwaito daga Abbas adduriy daga Yahya bn Ma'in lallai shi ya ce: Mafi alkhairi wannan al ummar bayan Annabinta: Abubakar da Umar sannan sai Uthman sannan sai Aliyu, wannan shi ne akidarmu! Kuma shi ne maganan Limamanmu!! ".

 Ya kuma sake cewa ( 3 / 65 ): Abu Ahmaiz Zubairiy da waninsa sun ruwaito daga Malik bn Migwal daga Ukail daga Sha'abiy lallai ya ce: Alkamatu ya ce mini: Shin ka san misalign Aliyu cikin wannan al'ummar? Na ce: menene misalinsa? Ya ce: misalinsa shi ne misalign Isa; wassu sun so shi har su ka halaka cikin sonsa, wassu kuma su ka ki shi har su ka halaka cikin kinsa ".
 Abin da Alkamatu yak e nufi da wadanda ya kamanta da su su ne: Yahudu da nasara, su kuma wadanda ya kamantan su ne: Khawarijawa da Shi'a.

 Ya kuma sa ke cewa ( 3 / 33 ): " Kuma sun yi ijma'i cewa ya yi sallah yana mai fiskantar alkibla biyu, kuma ya yi hijira, sannan ya halarci badar da Hudaibiyyat da sauran yakuka kuma lallai shi ya yi kwazo da bajinta a Badar da Uhud da Khandak da Khaibara bajinta mai girma, kuma lallai shi ya wadatar a wadannan yakukan kuma ya a cikinsu a matsaya mai karimci, kuma tutar Manzon Allah ta kasance a hanunsa a guri da yawa, kai! Ranar badar ta kasance a hanunsa duk da cewa akwai sabani a kan haka, Yayin da aka kasha Mus'ab bn Umair ranar ( yakin ) Uhud kuma tuta ya kasance a hanunsa gabanin haka Sai Manzon Allah ( s a w ) ya mika shi zuwa ga Aliyu ( r a ).
 Ibnu taimiyyat ( rahimahul lah ) ya fada a cikin minhajus sunna ( 6 / 178 ): " Kuma Aliyu ( r a ) basu gushe ba – yana nufin Abubakar da Umar – su na masu karrama shi matukar karramawa da kowace hanya, suna masu gabatar da shi, kai dama sauran Banu Hashim wajen kyauta a kan wassunsu, kamar yadda su ke fifita shi su kuma gabatar da shi wajen martaba da alfarma da so da jibinta da yabo da girmamawa, kamar yadda su ke aikatawa da sauran, sannan sun a fifita shi da abin da Allah mabuwayi da daukaka ya fifita shi a kan wadda ba kwatankwacinsa ba, kuma kwata – kwata ba an san sun taba fadan wata kalma mummuna ( ta batanci ) da su ka yi ba a kan Aliyu, kai! Haka kuma ( ba a kiyaye musu wannan ba ) a kan wani daga cikin Banu Hashim " zuwa fadinsa: "  haka kuma Aliyu ( r a ) hakika ya zo ta hanyoyi mutawatirai daga wajensa na sonsa wa su ( Abubakar da Umar ) da kuma jibintar al'amarinsu da girmamasu da gabatar da su akan dukkan al'umma, ( ya tabbata daga gare shi ) tabbatar da za a iya sanin halinsa kan haka, kuma shi ma ba a san wata kalma day a fada ta munanawa akansu ba, ko wai shi ya fi cancantar shugabanci fiye da sub a; wannan kuma sananne ne ga duk wadda ya san labaru ( al aasar ) da su ka tabbata, kuma mutawatirai a wajen masu ilimi d agama garin mutane, da kuma wadanda aka ciro su da labarum amintattu ".

 Ya kuma sake cewa: ( 6 / 18 ): " amma Aliyu ( r a ) Ahlus sunna sun a sonsa kuma suna jibintar al'amarinsa, kuma su na shaidawa cewa yana cikin Khalifofo shiryeyyu, kuma yana cikin limamaimasu shiryarwa ".

 Ibnu Hajar ( rahimahul lah ) ya ce a cikin TAKRIB: " Aliyu bn Abiy Dalib bn Abdil muddalib bn Hashim bahashime, ( wadda ake masa lakabi da ): haidara, kuma shi ne: baban turbaya, baban Hasan da Husaini, dan baffan Manzon Allah ( s a w ), kuma mijin 'yarsa, kuma na daga cikin wadanda su ka yi rigaye na farko ( wajen shiga wannan musuluncin ) kai! Malamai ndayawa sun ma fifita kasancewarsa shi ne farkon wadda ya musulunta; don haka; shi ne wadda ya riga larabawa, kuma 'dayan mutum goma ne da aka musu albishir da aljanna, ya rasu a Ramadan a shekara ta arba'in (40); kuma shi ne mafificin rayayyu a bayan kasa na 'yan adam a lokacin da ijma'in Ahlus sunna, kuma ( ya rasu ) yana da shekara shittin da uku (63) ga zancen da ya fi rinjaye "

 Aliyu bn Abiy Dalib ( r a ) yana da 'ya'ya goma sha biyar (15) maza, da kuma goma sha takwas (18) mata, Al'amiriy ya ambata hakan a cikin ARRIYADUL MUSTADABATU FI JUMLATI  MAN RAWA FIS SAHIHAINI MINAS SAHABA ( a shafi: 180 ), sannan ya ambace su, ya kuma ambaci uwayensu, sannan ya ce: " amma zurriya da ga 'ya'yan Aliyu ya kasance kawai daga Alhasan ne da Alhusaini da Muhammad da Umar da kuma Al'abbas ".

JIKAN MANZON ALLAH ( S A W ) AL HASAN BN ALIYU BN ABIY DALIB ( r a ):

  Ibnu Abdil barri ( rahimahul lahu ) ya fada a cikin AL'ISTIY'AB ( 1 / 369 a hasiyar AL'ISABATU): " Hadisai ingantattu daga Annabi ( s a w ) sun yi tawatur[7] kan lallai ya ce  akan Al hasan bn Aliyu ( r a ):


 " إنَّ ابني هذا سيِّدٌ، وعسى الله أنْ يُبقيَه حتى يُصلح به بين فئتين عظيمتين من المسلمين "

  Ma'ana: " Lallai 'dana wannan shugaba ne, kuma da sannu Allah zai wanzar da shi don ya daidaita ( sulhu ) bangarori guda biyu masu girma na daga musulmai " Jama'a ce ( dayawa ) na daga sahabbai su ka ruwaito shi. Ya zo cikin hadisin Abu bakrata cikin haka lallai ( Annabi s a w ) ya ce:

 " وأنه ريحانتي من الدنيا "

 Ma'ana: " Kuma lallai shi arzikina ne ( dan lelena kuma abun shanshana na) daga duniya ".  Babu kuma wadda ya fi shugabanci fiye da wadda Manzon Allah ( s a w ) ya masa lakabi da " shugaba " kuma ya kasance – Allah ya kara masa rahama – mai yawan hakuri ne, mai kuma tsentseni ( gudu wa shubuha ), sannan madaukaki; tsentseninsa ne da kuma daukakarsa su ka kira shi zuwa ga barin mulki da duniya, yana kuma mai kwadayin abin da ke wajen Allah; kuma hakika ya ce:

 (( والله! ما أحببتُ ـ منذ علمتُ ما ينفعني ويضرُّني ـ أنْ ألِيَ أمرَ أمةِ محمدٍ r على أن يُهراق في ذلك محجمة دمٍ ))

 Ma'ana: " Na rantse da Allah! Ban taba son na jagoranci al'amarin al'ummar Annabi Muhammadu ( s a w ) akan a zubar da kaho ( daya ) na jinni ba, - tun da na san abin da zai amfanar da ni da kuma abin da zai cutar da ni ( ma'ana: na yi hankali ) - . Kuma ya kasance cikin wadanda su ka yi gaugawa wajen taimakon Uthman ( rahimahul lah ) da kuma kare shi ( daga wadanda su ka zo kasha shi ) ".
ZAHABIY ya fada akansa a cikin ( littafinsa ) siyar ( 3 / 245 - 246 ): " Shi ne wannan shugaban kuma jagora, dan lelen Manzon Allah ( s a w ), kuma jikansa ( ta wajen 'yarsa ), kuma shugaban samarin gidan aljanna! Shi ne kuma Abu Muhammad, bakuraishe, bahashime, mutumin madina, kuma shahidi ".
 Ya kuma sake cewa ( 3 / 253 ): " Hakika wannan shugaban ya kasance jagora ne, kuma ( Mutum ) mai kyau, mai hankali, kuma nitsetstse kamemme ( kammalelle mai nauyin kima ), mai yawan kyauta, wadda ake yawan yabonsa, mai yawan alkhairi, mai riko da addini kuma mai tsentseni, ma'abocin kunya, kuma mai girman sha'ani ".
 Ibnu Kasir yana fada akansa a cikin ALBIDAYATU WAN NIHAYATU ( 11 / 192 – 193 ): " Hakika ( Abubakar ) as siddiqu ya kasance yana daukaka shi kuma yana girmama shi, yana kuma masa kyauta, sannan yana fansarsa ( da iyayensa )! Haka kuma Umar bn Alkhaddab ( r a ) ", ( ya kawo asarin kyautar Umar ( r a ) lokacin day a yi register ) sannan ya ce: " haka kuma Uthman bn Affan;  shi ma ya kasance yana kyauta ( ya kuma karrama ) Al hasan da Al husain, sannan yana sonsu, Shi ma Al hasan bn Aliyu ya kasance yana wajensa – alhali Uthman yana tsare a ranar da aka kewaye masa gida kuma aka kasha shi – yana wajensa kuma yana rataye da tokobi don yak are Uthman da shi; Sai Uthman ya jiye masa tsoro;kuma ya rantse cewa sai ya koma gidansu; ( Uthman ) ya yi haka ne don ya dadada wa zuciyar Aliyu, sannan kuma yana tsorace ( Al hasan kar a cutar da shi), Allah ya kara yarda da su ".

 JIKAN MANZON ALLAH  ( S A W ) ALHUSAIN BN ALIYU BN ABIY 'DALIB ( r a ):

 Ibnu Abdil barri ( rahimahul lah )ya fada cikin AL ISTIY' AB ( 1 / 377 a hashiyar Al' isabatu ): " Kuma Al husan ya kasance mai girma ne, mai riko da addini; mai yawan azumi da salla da kuma hajji ( na nafila ) ".
 Ibnu taimiya ya ce – kamar yadda ya ke cikin majmu'ul fatawa ( 4 / 511 ) -: " Alhusain ( r a ) Allah madaukaki ya karrama shi da yin shahada a wannan yinin – yinin ashura -, ya kuma wulakanta [8] wadda ya kashe shi ko wadda ya taimaka wajen kashe shi ko ya yarda da kashe shin ( da kasha shin ), kuma dai yana da abin koyi mai kyau da wadnda su ka riaye shi daga shahidai; domin shi da dan 'uwansa su ne shugabannin samarin gidan aljanna. Kuma sun kasance sun samu tarbiyarsu ne cikin daukakar musulunci; shi ya sa ba su samu ( ladan ) hijira da kuma ( ladan ) hakuri kan cutarwa kan bin Allah ba; kamar yadda ( sauran ) iyalan gidansa su ka samu ba; sai Allah madaukaki ya karrama su da yin shahada don ya cika musu kyautarsu, kuma ya daga darajarsu. Kashe shi kuma musiba ce, Allah kuma ( s w t ) ya shar'anta fadin: INNA LIL LAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN yayin musiba da fadinsa:

                                                             ﭾﭿ          

 Ma'ana: " Kuma ka yi albishir ga masu hakuri * wadanda idan musiba ta same su su kan ce: Lallai mu daga Allah mu ke, kuma zuwa gare shi za mu koma * wadancan su na da wassu irin yabo daga wajen Ubangijinsu, da wata irin rahama, kuma wadancan su ne shiryeyyu "
 Zahabiy ( rahimahul lah ) yana fadi akansa a cikin siyar ( 3 / 280 ): " ( Al husaini shi ne ) wannan shugaban madaukaki, cikakke, jinkan Manzon Allah ( s a w ) - ta wajen 'yarsa – kuma lelensa daga duniya, kuma masoyinsa, baban Abdullah; Al husain bn Amiril mu'uminai; baban Al hasan Aliyu bn Abiy 'Dalib bn Abdul muddalib bn Hashim, Ibn Abdi manaf bn Kusaiy, bakuraishe, bahashime! ".
 Ibnu Kasir ( rahimahul lah ) ya fada a cikin ALBIDAYATU WAN NIHAYATU ( 11 / 476 ): " Abin nufi dai! Lallai shi Alhusain ya yi zamani da Manzon Allah ( s a w ) kuma ya aboce shi har ya rasu yana mai yarda da shi, sai dai shi ya kasance yaro ne, sannan ( Abubakar ) as siddiqu ya kasance yana masa kyauta kuma yana girmama shi, haka kuma Umar da Uthman, sannan ya aboci babansa ya kuma ruwaito hadisi daga wajensa, kamar yadda ya kasance tare da shi a dukkan yakusansa; - a ( yakin ) Jamal da As siffin -, kuma ya kasance abun girmamawa ne abun darajawa ".


 'DAN BAFFAN MANZON ALLAH ( S A W ) ABDULLAHI BN ABBAS ( r a ):

 Bukhari ya ruwaito a cikin sahihinsa ( 4970 ) daga ( Abdullahi ) ibn Abbas ( r a ) ya ce:

 ((كَانَ عُمَرُ يُدْخِلُنِي مَعَ أَشْيَاخِ بَدْرٍ، فَكَأَنَّ بَعْضَهُمْ وَجَدَ فِي نَفْسِه،ِ فَقَالَ: لِمَ تُدْخِلُ هَذَا مَعَنَا وَلَنَا أَبْنَاءٌ مِثْلُهُ؟ فَقَالَ عُمَرُ: إِنَّهُ مَنْ قَدْ عَلِمْتُمْ، فَدَعَاهُ ذَاتَ يَوْمٍ فَأَدْخَلَهُ مَعَهُمْ فَمَا رُئِيتُ أَنَّهُ دَعَانِي يَوْمَئِذٍ إِلَّا لِيُرِيَهُمْ قَالَ مَا تَقُولُونَ فِي قَوْلِ اللَّهِ تَعَالَى:             فَقَالَ بَعْضُهُمْ: أُمِرْنَا أَنْ نَحْمَدَ اللَّهَ وَنَسْتَغْفِرَهُ إِذَا نُصِرْنَا وَفُتِحَ عَلَيْنَا، وَسَكَتَ بَعْضُهُمْ فَلَمْ يَقُلْ شَيْئًا، فَقَالَ لِي: أَكَذَاكَ تَقُولُ يَا ابْنَ عَبَّاسٍ؟ فَقُلْتُ: لَا، قَال:َ فَمَا تَقُولُ؟ قُلْتُ: هُوَ أَجَلُ رَسُولِ اللَّهِ r  أَعْلَمَهُ لَهُ؛ قَالَ:           وَذَلِكَ عَلَامَةُ أَجَلِكَ؛ ﭿ       ﮂﮃ                فَقَالَ عُمَرُ: مَا أَعْلَمُ مِنْهَا إِلَّا مَا تَقُولُ )).

 Ma'ana: " Umar ya kasance ya kan shigar da ni tare da dattawan badar; to sai ya zama kamr sashinsu bai ji dadi ba a ransa; har ma ya ce: Don me ka ke shigo da wannan tare da mu alhali muna da yara kwatankwacinsa? Sai Umar ya ce: Lallai shi fa shi ne wadda ku ka riga ku ka sani! Sai ya kira shi wata rana ya kuma shigar da shi cikinsu! – ( Ibnu Abbas ya ce: ) banga cewa ya kira ni ba a wannan yinin sai don ya nuna musu ( matsayi na ), Sai ya ce: Me za ku ce kan fadin Allah madaukaki: ( Idan taimakon Allah ya zo da cin nasara)? Sai sashinsu ya ce: An umurce mu da mu gode wa Allah kuma mu nemi gafararsa idan aka taimake mu kuma aka mana budi! Wassu kuma su ka yi shiru ba su ce komai ba, Sai ya ce min: Kai ma haka za ka ce ya kai Ibnu Abbas? Sai na ce: A'a! Sai ya ce: To me za ka ce? Sai na ce: Ajalin Manzon Allah ne ya sanar da shi; ya ce: ( Idan nasarar Allah ta zo da budi ) to wannan ita ce alamar ajalinka; do haka; (  sai ka yi tasbihi da godewa Ubangijinka, kuma ka nemi gafararsa; lallai shi ya kasance mai yawan karbar tuba ne ), Sai Umar ya ce: Ban san wani abu daga gareta ba ( suratun nasr ) sai abin da ka ke fadan ".

 Ya zo cikin DABAKAT na Ibnu Sa'ad ( 2 / 369 ) daga Sa'ad bn Abiy Wakkas ( r a ) lallai shi ya ce:

 (( ما رأيتُ أحضرَ فهماً، ولا ألبَّ لُبـاًّ، ولا أكثر علماً، ولا أوسع حِلماً من ابن عباس، ولقد رأيتُ عمر بنَ الخطاب يدعوه للمعضلات ))

 Ma'ana: " Ban ga mai kaifin ( saurin ) fahimta ba, mai kuma cikar hankali ba, da yawan ilimi tare da yawan hakuri kamr Ibnu Abbas, kuma hakika na ga Umar bn Alkhaddab yana kiransa don warware matsaloli ( na ilimi ).

 Ya zo kuma a cikinsa ( dabakat 2 / 370 ) daga 'Dalhatu bn Ubaidul lah ( r a ) Lallai shi ya ce:

 (( لقد أعطي ابن عباس فهما ولقنا وعلما، ما كنت أرى عمر بن الخطاب يقدم عليه أحدا ))

Ma'ana: " Hakika an bawa Ibnu Abbas saurin fahimta da hazaka da kuma ilimi; ( saboda haka ); ban ga Umar bn Alkhaddab yana fifita wani ba akansa ".


 Ya zo kuma a cikinsa ( dabakat 2 / 370 ) daga Jabir bn Abdullahi ( r a ) lallai shi ya ce yayin da ( labarin ) mutuwar Ibnu Abbas ya zo masa – ya dauki dayan hanunsa ya buga wa 'dayan – ya ce:

 (( مات أعلم الناس، وأحلم الناس، ولقد أصيبت به هذه الأمة مصيبة لا ترتق!))

 Ma'ana: " Mafi ilimin mutane, kuma mafi haurin mutane ya rasu, kuma hakika an jarrabi wannan al'ummar da rashinsa jarabawan da ba zai toshe ba ".


Ya zo kuma a cikinsa daga Abubakar bn Muhammad bn Amru bn Hazm lallai ya ce: Yayin da Ibn Abbas ya rasu; Rafi'u bn Khadij ya ce:

 (( مات اليوم من كان يحتاج إليه مَنْ بين المشرق والمغرب في العلم ))

 Ma'ana: " Wadda duk wanda ke tsakanin gabar da yamma na bukatar sa a ilimi ya rasu yau! ".

 Ya zo cikin ISTIY'AB na Ibnu Abdul barri ( 2 / 34 – 345 ): daga Mujahid lallai shi ya ce: " Ban taba jin fatawa ba fiye da ta Ibnu Abbas; sai dai mai fadi ya ce: Manzon Allah ya ce! ( to wannan kam ya fi maganan kowa! ), kuma an ruwaito kwatankwacin wannan daga Alkasim bn Muhammad ".

 Ibnu Kasir ( rahimahul lah ) ya ce a cikin ALBIDAYATU WAN NIHAYATU ( 12 / 88 ): " Kuma ya tabbata dag Umar bn Alkhaddabi ( r a ) lallai shi ya kasance yak an zaunad da Ibnu Abbas tare da shehunen sahabbai, kuma ya ce:

 (( نِعْمَ ترجمانُ القرآن عبد الله بن عباس ))

 Ma'ana: " madalla! Da masanin fassarar alqur'ani: Abdullahi bn Abbas ". ya kasance idan kuma ya fiskanto sai Umar ( r a ) ya ce:

 (( جاء فتى الكهول، وذو اللسان السَّؤل، والقلبِ العَقول )).

 Ma'ana: " Saurayi dattijo ya zo, ma'abucin harshe mai yawan tambaya, da kuma zuciya mai yawan fahimta! ".

 'DAN BAFFAN MANZON ALLAH ( S A W ) JA'AFAR BN ABIY 'DALIB ( r a ):

 Ya zo cikin sahihul Bukhari ( 3708 ) daga hadisin Abu Huaira ( r a ), a cikinsa:

 (( وَكَانَ أَخْيَرَ النَّاسِ لِلْمِسْكِينِ جَعْفَرُ بْنُ أَبِي طَالِبٍ كَانَ يَنْقَلِبُ بِنَا فَيُطْعِمُنَا مَا كَانَ فِي بَيْتِهِ حَتَّى إِنْ كَانَ لَيُخْرِجُ إِلَيْنَا الْعُكَّةَ الَّتِي لَيْسَ فِيهَا شَيْءٌ فَنَشُقُّهَا فَنَلْعَقُ مَا فِيهَا ))

  Ma'ana:  " Ja'afar bn Abiy 'Dalib ya kasance shi ne mafi alherin mutane ga miskinai; kuma ya kasance yak an tafi da mu, sai ya ciyar da mu abin da ke gidansa; har ma ya kasance yana fitar mana da jakar fata ( da ake sa mai ko zuma ) wadda ba komai a cikinta; sai mu tsaga ta kuma mu lashe abin da ke cikinta ".

 Alhafiz ibn Hajar ya fada a sharhin hadisin ( a cikin Fat' hul bari 7 / 76 ): " wannan takaicewa da ya zo cikin hadisin ( wato fadinsa: mafi alkhairin mutane ga miskinai ), da shi za a fassara abin da ya zo a sake ( a cikin hadisi mai zuwa ); wadda ya zo daga Ikrimatu daga Abu Huraira ( r a ), lallai ya ce:

 (( ما احتذى النِّعال، ولا ركِبَ المطايا بعد رسول الله r أفضل من جعفر بن أبي طالب ))

 Ma'ana: " Babu wadda ya saka takalmi, ko ya hau abin hawa in banda Manzon Allah ( s a w) fiye da Ja'afar bn Abiy 'Dalib ".  Tirmizi da Hakim ne su ka ruwaito shi da sanadi mai inganci ".

 Zahabi a cikin SIYAR ( 1 / 206 ) na fadi akansa: " ( Ja'afar ) shi ne wannan shugaban nan, wadda ya yi shahada, mai girman sha'ani, gwarzon masu jihadi ( kuma tutar su ), baban Abdullahi, 'dan Baffan Manzon Allah ( s a w ) Abdu Manaaf bn Abdul muddalib bn Hashim bn Abdu Manaaf bn Kusayyi, bahashime, 'dan 'uwan Aliyu bn Abiy 'Dalib, shi kuma ya fi Aliyu girma da shekara goma. Ya yi hijira guda biyu ( hijiran farko da na biyu zuwa Habasha ), sannan ya yi hijira daga Habashan zuwa Madina; ya iske ( samu )musulmai lokacin su na Khaibara bayan karbe ta, ya kuma zauna a Madina watanni sannan sai Manzon Allah ( s a w ) ya shugabantar da shi ga rundunar yakan Mu'uta ta bangaren Karak; sai ya yi shahada. Hakika Manzon Allah ( s a w ) ya yi farin cikin zuwansa ( isowarsa Madina ), kamar yadda – Wallahi! – ya yi bakin cikin rasuwansa!!".

 Ya zo cikin TAKRIB na Ibnu Hajar  lallai ya ce: " Ja'afar bn Abiy 'Dalib, bahashime, baban mikinai, ma'abocin fukafuki biyu, kuma sahabi mai girma, 'dan Baffan Manzon Allah ( s a w ), ya yi shahada a yakin mu'uta a shekara ta takwas da hijira, an ambace shi cikin Bukhari da Muslim ba tare da an ruwaito daga gare shi ba ".
Kuma an ce masa ma'abocin fukafuki biyu ne; saboda an canza masa a madadin hanayensa da aka gutsure a yakin mu'uta da fukafukai guda biyu da ya ke furkawa da su tare da Mala'iku; ya zo cikin sahihul Bukhari ( 3709 ) da sanadinsa zuwa ga Sha'abi: Lallai Ibnu Umar ( r a ) ya kasance idan ya yi sallama wa 'dan Ja'afar sai ya ce:

 (( السلام عليك يا ابنَ ذي الجناحَين ))

 Ma'ana: " Aminci ya tabbata ga 'dan ma'abocin fukafuki guda biyu ".
 Alhafiz ya fada cikin sharhin hadisin: " Kamar yana nuni ne zuwa ga hadisin Abdullahi bn Ja'afar, lallai shi ya ce: Manzon Allah ( s a w ) ya ce min:

 " هنيئاً لك؛ أبوك مع الملائكة في السماء! "

 Ma'ana: '' Lalenka! Babanka yana furkawa da Mala'iku a cikin sama!! ". 'Dabarani ne ya ruwaito shi da sanadi mai kyau ".
 Sannan ya ambaci wassu hanyoyi na daban daga Abu Huraira da Aliyu da Ibnu  Abbas (r a), kuma ya ce a wata hanya daga Ibnu Abbas:

 " إن جعفر يطير مع جبريل وميكائيل، له جناحان؛ عوَّضه الله من يديه "

 Ma'ana: " Lallai Ja'afar yana furkawa tare da Jibril da Mika'il; yana da fukafuki guda biyu da Allah ya musanya masa a madadin hannayensa " kuma ya ce: sanadin wannan mai kyau ne.".

 DAN BAFFAN MANZON ALLAH ( S A W ) ABDULLAHI  BN JA'AFAR (r a ):

 Ya zo cikin sahihu Muslim ( 2428 ) daga Abdullahi bn Ja'afar lallai shi y ace:

 (( كان رسول الله r إذا قدم من سفر تُلُقِّي بصبيان أهل بيته، قال: وإنه قدم من سفر فسُبق بي إليه، فحملني بين يديه، ثم جيء بأحد ابنَيْ فاطمة فأردفه خلفه، فأُدخلنا المدينة ثلاثةً على دابةٍ ))

 Ma'ana: " Manzon Allah ( s a w ) ya kasance idan ya dawo daga tafiya sai a fiskance shi da yaran Ahlul baiti, sai ya ce: kuma lallai shi ya dawo daga wata tafiya sai aka riga zuwa da ni wajensa sai ya dauke ni a gaba gare shi, sannan sai a ka zo da dayan yayan Fadima sai ya goye shi a bayansa, sai ya ce: sai mu ka shiga Madina mu uku akan dabba ".
 Zahabi ( rahimahul lah ) yana fada akansa a cikin SIYAR ( 3 / 456 ): " ( Shi Abdullahi shi ne ) wannan shugaban nan, kuma malami, baban Ja'afar, bakuraishe, kuma bahashime, shi ne wadda aka haife shi a Habasha, kuma magidanci a Madina, mai kyauta dan mai kyauta ma'abocin fukafukai biyu, sannan kuma shi sahabi ne ( ya abokanci Annabi s a w yana yaro! ), kuma  ya ruwaito daga gare shi, ana kirga shi cikin kananan sahabbai, babansa ya yi shahada a ranar Mu'uta, sai manzon Allah ( s a w ) ya rene shi, kuma ya tashi a gabansa ".
 Kuma ya sake cewa: " Kuma ya kasance mai girman sha'ani ne, mai karrama (girmama) mutane kuma mai yawan kyauta, ya kuma cancanci shugabanci! ''.
 Ya zo cikin ARRIYADU ALMUSTADABATU na Al'amiri ( p: 205 ): "  Aban bn Uthman shi ya masa sallah ( lokacin da ya rasu ) ya kasance shi ne kuma gwamnan Madina a wannan lokacin, sannan Abanu ya dauki makararsa alhalin hawayensa yana gangara, yana kuma cewa: ka kasance – wallahi! – alkhairi ne babu sharri a cikinka, kuma ka kasance – wallahi!! – madaukaki, mai girma, mai kuma biyayya ".


DAGA CIKIN SAHABBAN MANZON ALLAH ( S A W ) WADANDA SU AHLUL BAITINSA NE:

Abu Sufyan da Naufal da Rabi'atu da kuma Abidatu 'ya'yan Alharith bn Abdil muddalib.

Da Abdil Muddalib bn Rabi'ata bn Al harith bn Abdil Muddalib.

Da Al harith da Almugiratu 'ya'yan Naufal bn Al harith bn Abdil Muddalib.

Da Ja'afar da kuma Abdullah 'ya'yan Abu Sufyan bn Al harith bn Abdil Muddalib.

Da Mu'attib da kuma Utbatu 'ya'yan Abu lahab Abdul uzza bn Abdil muddalib.

Da kuma Fadl da Ubaidullahi 'ya'yan Al abbas bn Abdil muddalib.


FASALI NA BAKWAI:

YABON WASSU MALUMA GA JAMA'A DAGA CIKIN SAHABBAI MATA ( AHLUL BAITI)

  'YAR MANZON ALLAH ( S A W ) FADIMATU ( r a ):

  Daga A'isha uwar mu'uminai ( r a ) lallai ta ce:

 (( ما رأيتُ أحداً أشبه سمْتاً ودلاًّ وهدْياً برسول الله في قيامها وقعودها من فاطمة بنت رسول الله r ... ))

 Ma'ana: " Ban ga wadda ya fi kama da Manzon Allah ( s a w ) cikin kyan misali wajen kankan da kai ga Allah da … da kyan hali da taushin zance, da kuma shiriya, cikin tsayuwanta da zamanta fiye da Fadimatu 'yar Manzon Allah ( s a w ) ".  Abu Dawud ( 5217 ) ne da Tirmiziy ( 3872 ) su ka ruwaito shi da sanadi mai kyau.

 Abu Nu'aim a cikin AL HILYATU ( 2 / 39 ) ya ce:

 (( ومن ناسكات الأصفياء، وصفيات الأتقياء فاطمة رضي الله تعالى عنها. السيدة البتول، البضعة الشبيهة بالرسول، ألوط أولاده بقلبه لصوقاً، وأولهم بعد وفاته به لحوقاً، كانت عن الدنيا ومتعتها عازفة، وبغوامض عيوب الدنيا وآفاتها عارفة )).

 Ma'ana: " Kuma daga cikin masu bauta zababbu, da kuma tatattun masu tsoron Allah: Fadimatu ( r a ), shugaba da ta yanke ga barin komai zuwa ga bautar Allah , tsokar ( Manzon Allah s a w ), wacce ta yi kama da Manzo, wacce zuciyarsa yafi ratayuwa da sonta cikin 'ya'yansa, kuma ita ce farkon wadda ya riske shi bayan rasuwarsa, kuma ta kasance dangane da duniya da jin dadinta mai kawar da kai ne ( gudun duniya ), kuma ta kasance dangane da aibukan duniya da basu shahara ba da kuma matsalolinta masaniya ce ".

 Zahabiy ( rahimahul lahu ) ya ce a cikin SIYAR ( 2 / 118 -119 ): " Ita ce shugaban matan duniya a zamaninta, tsokan annabci, wacce ta fito ta bangaren zabebbe, ( ta kasance ana mata alkunya da ) ummu abiha, 'yar shugaban halittu; Manzon Allah ( s a w ), baban Kasim Muhammadu bn Abdil lah bn Abdil muddalib bn Hashim bn Abdi manaf, bakuraishe, bahashime, uwar Alhasan da Alhusaini '.
 Ya kuma sake cewa: " Hakika kuma Annabi ( s a w ) yana sonta kuma yana karrama ta, haka kuma yana sirri da ita, darajojinta da falalolinta suna da yawa, kuma ta kasance mai hakuri ce, mai riko da addini, mai alkhairi ce, kamemmiya, mai wadatar zuci ( adila kuma yajejjiya ), mai kuma godiya wa Allah ".

 Ibnu Kasir ( rahimahul lahu ) ya cewa a cikin ALBIDAYATU WAN NIHAYATU ( 9 / 485 ): " Kuma ana mata alkunya da: ummu abiyha! " ya ce: " Kuma ita ce karama daga cikin 'ya'yansa mata; a maganan da ta fi shahara, kuma babu wadda ya rage a bayansa ( daga cikin 'ya'yansa ) in banda ita; don haka ne ma ladanta ya girmama; saboda an jarrabe ta da rashinsa ( alaihis salatu wassalam ).


UWAR MU'UMINAI KHADIJA BINT KHUWAILID ( r a ):

 Zahabi yana fada a cikin SIYAR ( 2 / 109 – 110 ): " ( Khadija ) ita ce: uwar mu'uminai, kuma shugaban matan duniya a zamaninta,… uwar 'ya'yan Manzon Allah ( s a w ); in banda Ibrahim, kuma ita ce farkon wadda ta yi imani da shi; kuma ta gaskata shi kafin kowa, ……………….,    … abubuwan yabonta da  aiyukanta masu kyau su na da yawa, kuma ita tana daga cikin wadanda su ka cika daga mata, ta kasance mai hankali ce, kuma madaukakiya mai addini, kamemmemiya kuma mai kyauta, tana dag cikin 'yan aljanna, Annabi ( s a w ) ya kasance yana yaba mata, kuma yana fifita ta akan sauran iyayen mu'uminai, kuma yana kai makura wajen girmama ta, … Yana kuma daga cikin karamar ta:
  1. Manzon Allah ( s a w ) bai auri mata ba kafin ta,
  2. Sannan ya haifi yara da dama tare da ita,
  3. Kamar yadda bai auri wata a kanta ba, haka kuma bai riki baiwa ba, har zuwa rasuwarta; kuma lallai ya ji ciwon rasa ta; saboda ita ta kasance abokin zama ne da a ke madalla da shi, … kuma hakika allah ya umurce shi da ya mata albishir da wani irin gida a cikin aljanna mai kan lu'ulu'i, babu ihu cikinsa, kuma ba a gaji ba wajen emansa ".

 Daga cikin abin da Ibnul ya fada a cikin JALA'UL AF HAM ( p: 349 ) Lallai yana daga cikin abubuwan da ta kebanta da su: lallai Allah ya aiko mata da sallama tare da Jibrilu ( a s ), kuma ya ce:

 (( وهذه لعمر الله! خاصةٌ لم تكن لسواها ))

 Ma'ana: " Na rantse da Allah! Wannan kuwa wani abu ne da ta kebanta da shi; be kasance wa watanta tab a " .
 Kafin nan kuma ya ce: " Daga cikinsu ( Na nufin daga cikin abubuwan da ta kebanta da su: ) Lallai ita ce mafi alkhairin matan wannan al'umma, amma an yi sabani wajen fifita ta akan A'isha( r a ) ya zuwa ga zance uku [9] : na ukun shi ne: tsayawa ga barin fifita daya akan daya, Na tambayi malaminmu Ibnu Taimiya - rahamar Allah ta tabbata akansa? – Sai ya ce: Kowacce ta kebanta da wani abun da ta kebanta da shi; Amma Khadija; tasirinta ya kasance ne a farkon musulunci, kuma ta kasance tana rarrashin Manzon Allah ( s a w ) kuma tana tabbatar da shi, tana nitsar da shi, kuma don shi tana bada dukiyar ta; sai ta riski ( ladan ) farkon musulunci, sannan ta jure cutarwa in dai akan Allah ne madaukaki, da Manzonsa ( s a w ); sai ya zama taimakonta wa Manzon ya kasance ne a mafi girman lokutan bukata; wannan yasa ta ke ( ladan ) taimako da kuma sadaukarwa; wadda watanta bata da shi. A'isha kuma ( r a ) tasirinta ya kasance ne a karshen musulunci; wannan ya sat a ked a ( wani kaso ) na fahimtar addini da kuma isar da shi, da kuma amfanuwan 'ya'yanta da abin da ta basu na ilimi; wadda hakan bai kasance ga watanta ba; wannan shi ne ma'anar maganarsa! ".

UWAR MU'UMINAI A'ISHA ( r a ):

 Zahabiy na fada a kanta a cikin SIYAR ( 2 / 140 ): " … Kuma Annabi ( s a w ) bai auri budurwa ba in banda ita, kamar yadda bai so wata mata ba irin sonta, kuma ni ban san wata ba cikin al'ummar Annabi Muhammadu – kai! A cikin mata ma daukacinsu ( gaba dayansu ) – ban san wata matar da ta fit a ilimi ba ".
 A cikin SIYAR din kuma du ( 2 / 181 ) ya zo daga Aliyu bn Al'akmar, lallai shi ya ce: " Masruku ya kasance idan idan zai bada hadisi daga A'isha ya kan ce:

 (( حدثتْني الصدِّيقة بنتُ الصدِّيق، حبيبةُ حبيب الله، المبرَّأةُ من فوق سبع سموات فلم أكذِّبها ))

 Ma'ana: " Me gaskiya 'yar mai gaskiya, masoyiyar masoyin Allah, wacce aka kubutar da ita ( ga barin abin da ka jefe tad a shi na zina! ) daga saman sammai bakwai ce ta ban labari; Ni kuwa b azan karyata ta ba ".

 Ibnul Kayyim a cikin JALA'UL AF HAM ( p: 351 – 355 ) ya ambaci tarin abubuwan da ta kebanta da shi; dunkulensu:
  1. "  Lallai it ace mafi soyuwan mutane ga Manzon Allah ( s a w ),
  2. Kuma lallai shi bai taba auren budurwa ba in banda ita,
  3. kuma wahayi ya kasance yana sauko masa alhali yana cikin mayafinta,
  4. kuma yayin da ayoyin bada zabi wa matansa su ka sauko masa ya fara ne da ita; ya bata zabin; sai ta zabi Allah da Manzonsa, sai sauran matan nasa su ka yi koyi da ita,
  5. kuma lallai Allah ya kubutar da ita daga abin da ma'abota babban karya su ka jefe tad a shi; kuma ya saukar da wahayi da ake karanta shi a mihrabobin musulmai da kuma sallolinsu har zuwa tashin kiyama don uzurinta da kubutar da ita,
  6. kuma ya mata shaida cewa ita tana daga cikin tsarkaka,
  7. kuma ya mata alkawari da wata irin gafara da kuma arziki mai karamci;

 Amma duk da wannan matsayi madaukaki ta kasance tana kaskantar da kanta ga Allah; har ma ta ce:

 (( ولشأنِي في نفسي أهون من أنْ يُنَزِّل الله فيَّ قرآناً يُتلى!! ))

 Ma'ana: " Kuma hakika sha'anina a karan kaina bai kai Allah ya saukar da Alqur'ani da ake karantawa a kaina ba!! ".
  1. kuma lallai manyan sahabbai ( r a ) sun kasance idan wani abu na addini ya daure musu kai sun kasance su kan nemi fatawarta; sai kuma su samu iliminsa a wajenta,
  2. kuma lallai Manzon Allah ( s a w ) ya rasu ne a dakinta, kuma a rananta, sannan a tsakanin wuyanta da kirjinta, kuma an bunne shi a 'dakinta,
  3. kuma lallai Mala'ika ya nuna photonta wa Annabi ( s a w ) a jikin wani guntun alhariri mai kyau fari - kafin ya aure ta, sai ya ce:

 " إنْ يكنْ هذا من عند الله يُمضِه! "

 Ma'ana: " in hakan ( mafarkin ) ya zama daga allah ne to zai zartar da shi ".
  1.  kuma lallai mutane sun kasance suna kardadon ranar da Manzon Allah ( s a w ) yak e dakinta don su kai kyautarsu; sai sub a shi kyautar abin da ya fi so a a kuma dakin mafi soyuwan matansa a wajensa ( Allah ya kara yarda da su gaba daya ) ".

 UWAR MU'UMINAI SAUDATU BINT ZAM'ATA ( r a ):

 Zahabiy ( rahimahul lahu ) yana fada a cikin SIYAR ( 2 / 265 – 266 ): " ( Saudatu ) Ita ce: farkon wacce Annabi ( s a w ) ya aure ta bayan Khadija ( r a ), kuma ta kadaita da shi kimanin shekara uku ko fiye, har kuma ya tara da A'isha ( r a ), ta kasance shugaba ce, mai girma kuma madaukakiya, mai jiki … it ace wadda ta bada kyautar yininta ga A'isha ( r a ); don kula da zuciyar Manzon Allah ( s a w ), …
 Ibnul Kayyim J rahimahul lahu – ya ce a cikin JALA'UL AF HAMI ( p: 350 ): " … Kuma ta manyanta a wajensa, sai ya nufi sake ta; sai ta kyautar da yininta ga A'isha ( r a ); sai ya rike ta; wannan kuma yana daga abubuwan da ta kebanta da su; cewa: ta fifita masoyiyar manzon Allah ( s a w ) da ranar ta, tana mai neman kusanta zuwa ga Manzon Allah ( s a w ), da kuma sonsa, da kuma fifita kasancewarta tare da shi; Manzon Allah ( s a w ) ya kasance yana raba ( kwana ) wa matansa, baya kuma rabawa da ita; alhali ta yarda da hakan, tana mai fifita yardan Manzon Allah ( s a w ) – Allah ya kara yarda da ita – ".

UWAR MU'UMINAI HAFSAT BINT UMAR BN ALKHADDAB ( r a ):

 Zahabiy yana fada a cikin SIYAR ( 2 / 227 ): " ( Hafsat ita ce ) Sitirar ( Manzon Allah s a w ) madaukakiya, 'yar Amirul mu'uminina Abu Hafs Umaru bn Alkhaddab, Annabi ( s a w ) ya aure ta bayan karewar iddar ta da ta yi wa Khunais bn Huzafata As sahamiy – 'daya daga cikin wadanda su ka yi hijira – a shekara ta uku na hijira. A'isha ( r a ) ta ce: Ita ce wacce ta kasance ta ke tsere da ni daga cikin matan Annabi ( s a w ) '.


UWAR MU'UMINAI UMMU SALAMATA HINDU BINT ABIY UMAYYATA ( r a ):

 Zahabiy ya fada a cikin SIYAR ( 2 / 201 – 203 ): " ( Ummu salamata ita ce ): Shugaba, wacce ta kai matuka wajen suturta kai!, kuma matsarkakiya, … kuma tana cikin matan farko da su ka yi hijira, … kuma ta kasance ana kidaya ta daga cikin maluma mata na sahabbai ''.
 Yahya bn Abiy bakar  Al' aamiriy yana cewa a cikin ARRIYADUL MUSTADABATU ( p: 324 ); " Kuma ta kasance madaukakiya ce mai yawan hakuri, kuma it ace ta yi nuni wa Manzon Allah "( s a w ) ranar ( sulhun ) Al hudaibiyya – da ya aske kansa kuma ya soke abun hadayarsa -, kuma tag a ( mala'ika ) Jibrilu a surar Dihyatu ( r a ) ".


UWAR MU'UMINAI ZAINAB BINT KHUZAIMATA ALHILALIYYATA ( r a ):

  Zahabiy ya ambata a cikin SIYAR ( 2 / 218 ) cewa ana mata kirari da: Uwar miskinai; saboda yawan kyautatawanta.
 Ibnul Kayyim ya fada a cikin JALA'UL AF HAM ( p: 376 ) cewa: " Kuma ta kasance ana kiranta uwar miskinai; saboda ciyarwanta ga miskinai, kuma ta kasance bat a zauna ( dade ) a wajen Manzon Allah ( s a w ) said an kadan; wata biyu ko uku, ta kuma rasu – Allah ya kara mata yarda! ".


UWAR MU'UMINAI JUWAIRIYYA BINT ALHARITH ( r a ):

  Ita ce uwar mu'uminai, kuma matar shugaban Manzanni, wannan kuma ya ishe ta falala da daukaka; Ibnul Kayyim yana fada a cikin JALA'UL AF HAM ( p: 376 – 377 ): " Kuma it ace musulmai su ka 'yanta iyalan gida 'dari bakwai bayi saboda ita; su ka kuma ce: surikan Manzon Allah ( s a w )!; wannaan kuma na daga albarkanta wa mutanenta! – Allah ya kara yarda da ita!! ".


UWAR MU'UMINAI SAFIYYA BINT HUYAYYI ( r a ):

  Ya zo cikin JAMI'UT TIRMIZIY ( 3894 ) da sanadi ingancecce daga hadisin Anas ( r a ): Lallai Annabi ( s a w ) ya ce mata:

 " إنَّكِ لابنَةُ نبيٍّ، وإنَّ عمَّكِ لنبيٌّ، وإنَّكِ لتحتَ نبيٍّ "

 Ma'ana: " Lallai ke 'yar Annabi ne, kuma baffanki Annabi ne, kuma lallai ke a karkashin Annabi ki ke ".
 Zahabiy yana fadi a cikin SIYAR ( 2 / 232 ): " Kuma ta kasance madaukakiya ce mai hankali, ma abociya danganta da kyau da kuma addini – Allah ya kara mata yarda " .
 Ya kuma sake fada ( 2 / 235 ) cewa: " Safiyyatu ta kasance ma'abociya hakuri ne da nitsuwa ''.
 Ibnul Kayyim a cikin JALA'UL AF HAM ( p: 377 ) yana cewa: " Manzon Allah ( s a w ) ya auri Safiyya bint Huyayyin ( kuma ) tana daga cikin 'ya'yan Haruna bn Imran 'dan 'uwan Musa – a s - ".
 Ya kuma sake cewa: " Yana daga cikin abubuwan da ta kebanta da su; Lallai  Manzon Allah ( s a w ) ya 'yanta ta kuma ya sanya 'yanta tan shi ne sadakinta; Anas ( r a ) ya ce:

 (( أمهرها نفسها ))

 Ma'ana: " Ya bata sadakin kanta! "
 Hakan sai ya zama sunna ga al'umma har zuwa tashin alkiyama; cewa ya halatta mutum ya sanya 'yantawarsa ga baiwarsa sadakinta; sai ta zama matarsa, kamar yadda Imamu Ahmad - rahimahul lahu -  ya fada ".


UWAR MU'UMINAI UMMU HABIBA RAMLATU BINT ABIY SUFYAN ( r a ):

  Zahabiy na fada a cikin SIYAR ( 2 / 218 ): " ( Ummu Habiba ita ce ): " shugaba wacce ta kai matuka wajen lulluba ".
 Ya kuma sake cewa ( 2 / 222 ): " Hakika Ummu Habiba ( r a ) ya kasance tana da alfarma da daukaka; musamman lokacin daular 'dan 'uwanta, kuma saboda matsayinsa a wajenta aka masa lakabi da: baffan mu'uminai ''.

 Ibnu Kasir ya ce a cikin ALBIDAYATU WAN NIHAYATU ( 11 / 166 ): " Hakika ta kasance daga cikin shugabanin iyayen muminai, kuma daga cikin masu yawan bauta, masu tsentseni – Allah ya kara yarda da ita – ".


UWAR MU'UMINAI MAIMUNA BINT ALHARITH ( r a ):
 
A cikin SIYAR ( 2 / 244 ): ya zo daga A'isha ( r a ) Lallai ta ce:

 (( أما إنَّها من أتقانا لله، وأوصلنا للرحم )).

 Ma'ana: " Ku saurara! Lallai ita ( Maimuna ) ta kasance daga cikin wadanda su ka fi mu tsoron Allah ( takawa ), kuma daga cikin wadanda su ka fi mu sada zumunci ".
 Zahabi ( 2 / 239 )na cewa: " Ta kasance daga cikin shugabannin mata ".


UWAR MU'UMINAI ZAINAB BINT JAHASH ( r a):
  Ya zo cikin sahihu Muslim ( 2442 ) cikin dogon hadisi daga A'isha ( r a ) Lallai ta ce:

 (( وَهِيَ الَّتِي كَانَتْ تُسَامِينِي مِنْهُنَّ فِي الْمَنْزِلَةِ عِنْدَ رَسُولِ اللَّهِ r وَلَمْ أَرَ امْرَأَةً قَطُّ خَيْرًا فِي الدِّينِ مِنْ زَيْنَبَ وَأَتْقَى لِلَّهِ وَأَصْدَقَ حَدِيثًا وَأَوْصَلَ لِلرَّحِمِ وَأَعْظَمَ صَدَقَةً وَأَشَدَّ ابْتِذَالًا لِنَفْسِهَا فِي الْعَمَلِ الَّذِي تَصَدَّقُ بِهِ وَتَقَرَّبُ بِهِ إِلَى اللَّهِ تَعَالَى مَا عَدَا سَوْرَةً مِنْ حِدَّةٍ كَانَتْ فِيهَا تُسْرِعُ مِنْهَا الْفَيْئَةَ )).

 Ma'ana: " kuma ita ce ( tana nufin: Zainab ) daga cikinsu ta ke tsere da ni wajen matsayi a wajen Manzon Allah ( s a w ), Kuma ban taba ganin wata mace ba wacce ta fi zainab alkhairi wajen addini, da kuma tsoron Allah, da gaskiyan zance, da sadar da zumunci, da yawan sadaka, tare da tsananin sadaukar da kai wajen aikin da ta ke yin sadaka da shi kuma ta ke kusantan Allah madaukaki da shi, ( tare da kamalar sifofi da ta ked a shi ) sai dai tana da zafin raid a saurin fushin da ta ke dawowa da sauri ta barshi ".

 Zahabiy ya fada a cikin SIYAR ( 2 / 211 ): " Sai Allah madaukaki ya aurar da ita da nassin littafinsa, ba tare da waliyyi da shaida ba; kuma ta kasance tana alfahari da hakan wa ( sauran ) uwayen mu'uminai; sai ta ce: Ku iyayenku ne su ka aurar da ku! Ni kuma Allah shi ya aurar da ni daga saman al'arshinsa " Wannan hadisin yana cikin sahihul Bukhari ( 7402 ).
 Ya kuma sake cewa ( 2 / 217 ): " Ta kasance saliha ce mai yawan azumi da yawan tsayuwan dare ( salla ), mai kuma yawan biyayya, ana kuma mata kirari da: Uwar miskinai! ".

BABAR MANZON ALLAH ( s a w ) SAFIYYA BINT ABDULMUDDALIB ( r a ):

  Zahabiy yana cewa a cikin SIYAR ( 2 / 169 ): " Safiiatu babar Manzon Allah ( s a w ), 'yar Abdul muddalib, bahashimiya, kuma ita 'yar uwar Hamza ne ( uwa daya, uba daya ), kuma ita ce uwar kebanceccen mataimakin Annabi ( s a w ): Azzubair ".
 Ya kuma sake cewa ( 1 / 270 ): " Magana mafi inganci shi ne: Babu wata daga cikin babanin Annabi ( s a w ) da ta musulunta in banda ita, kuma hakika ta yi bakin cikin rasuwar dan 'uwanta Hamza; amma sai ta yi hakuri kuma ta nemi lada, kuma tana cikin matan farko da su ka yi hijira ".

 DAGA CIKIN SAHABBAI MATA 'YAN AHLUL BAITI:

  'Ya'yansa mata ( s a w ); Zainab da Rukayya da kuma Ummu Kulsum.

 Da Ummu Kulsum da Zainab 'ya'yan Aliyu bn Abiy 'Dalib ( r a ), mahaifiyarsu kuma ita ce: Fadimatu.

 Da kuma Umamatu bint Abiy Al'aas bn Arrabi'I, Mahaifiyarta kuma ita ce: Zainab 'yar Manzon Allah ( s a w ), ita ce kuma Manzon Allah yak e daukanta a salla.

 Da kuma Ummu Hani'i bint Abiy 'Dalib bn Abdil muddalib.

 Da kuma Duba'atu da Ummul Hakam 'ya'yan Azzubairu bn Abdul Muddalib, Ambatonsu ya zo cikin wani hadisi da ke magana akansu; Abu Dawud ya ruwaito shi da lamba ( 2987 ), Ita kuma Duba'atu ita ce ma'abuciyar hadisin sa sharadin mahajjaci; wacce Manzon Allah ( s a w ) ya ce mata:

 " قولي: فإنْ حبسني حابسٌ فمحلِّي حيث حبستني "

 Ma'ana: " Ki ce: ( Ya Allah! ) In mai tsarewa ya tsare ni to wajen warware ( harama na ) shi ne gunda ka tsare ni!! ".

 Da Umamatu bint Hamza bn Abdul Muddalib.





FASALI NA TAKWAS:

YABON WASSU MALUMA GA JAMA'A DAGA CIKIN TABI'AI DA WASSUNSU AHLUL BAITI

  MUHAMMADU BN ALIYU BN ABIY 'DALIB ( WADDA YA SHAHARA DA: IBNUL HANAFIYYA – rahimahul lahu - ):

  Ibnu Hibban ya ce – a cikin ambaton amintattun tabi'ai -: " Kuma ya kasance daga cikin masu girman iyalan gidansu ".
 Ya zo cikin tarjamarsa a cikin TAHZIBUL KAMALI na Mizzi: " Ahmad bn Abdillahil Al' ijliy ya ce: Tabi'I ne amincecce, ya kasance mutum ne na gari … Ibrahim bn Abdillahi bn Aljunaid ya ce: Ba mu san wani ba da ya kawo hadisi da sanadin Aliyu daga Annabi ( s a w ) wajen yawa da inganci fiye da Muhammad bn Alhanafiyyat! ".

 A cikin SIYAR na Zahabiy ( 4 / 115 ) daga Isra'il daga Abdil 'a'ala ( shi ne: Ibn Amir ): " Lallai Muhammad bn Aliyu ya kasance ana masa alkunya da: Baban Kasim, kuma ya kasance mai tsentseni ne mai yawan ilimi ".
 Kuma ya sa ke cewa akansa ( 4 / 110 ): " Shi ne shugaba kuma limami, Abul Kasim kuma Abu Abdillah ".

 ALIYU BN ALHUSAIN BN ALIYU BN ABIY 'DALIB ( Rahimahul lahu! ):

  Ibnu Sa'ad na fada a cikin ADDABAKAT ( 5 / 222 ): " Aliyu bn Husain ya kasance amincecce ne, abun amincewa da shi, mai kuma yawan hadisi, madaukaki kuma mai tsentseni ".

 Ibnu Taimiya a cikin MINHAJUS SUNNAH ( 4 / 48 ) ya ce: " Amma Aliyu bn Alhusain to yana daga cikin manya – manyan tabi'ai, da kuma shugabanninsu; wajen ilimi da addini ".

 Ya zo cikin tarjamarsa a cikin TAHZIBUL KAMAL na Mizzi: " Sufyan bn Uyainat ya ce daga Zuhuri: Ban ga bakuraishen da ya fi Aliyu bn Alhusain falala ba ".
 Kuma an ruwaito ma'anarsa daga Abu Hazim, da Zaid bn Aslam, da Malik, da Yahya bn Sa'id Al 'ansariy – Allah ya musu rahama! –
 Ijliy ya ce: Aliyu bn Alhusain mutumin madina ne, tabi'I kuma amincecce.
 Zuhuriy ya ce: Aliyu bn Alhusain ya kasance cikin mafi daukakar iyalan gidansu, kuma mafi kyawunsu; biyayya, kuma mafi soyuwansu zuwa ga Marwan bn Alhakam da Abdullahi bn Marwan ".

 Zahabiy ya fada a cikin SIYAR ( 4 / 386 ): " Shi ne shugaba kuma limami, ( wadda ake masa lakabi da ) Zainul abidina, bahashime, kuma mutumin gidanAliyu, sannan mutumin garin Madina ".

 Ibnu Hajar ya fada a cikin TAKRIB cewa: " amincecce, kuma tabbacce, mai bauta mai kuma ilimi, madaukaki shahararre ".

 MUHAMMADU BN ALIYU BN ALHUSAIN BN ALIYU BN ABIY 'DALIB ( Rahimahul lahu! ):

  Yana daga cikin girmamawan Jabir bn Abdillah Al'an sariy ( r a ): Abin day a zo cikin sahihu Muslim ( 1218 )cikin sanadin hadisinsa mai tsayi da ke sifanta aikin hajjin ( Manzon Allah – s a w - ) daga hadisin Ja'afar bn Muhammad ( wadda shi ne Ibnu Aliyu bn Alhusain ), daga Babansa; Lallai y ace:

   (( دَخَلْنَا عَلَى جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ، فَسَأَلَ عَنْ الْقَوْمِ حَتَّى انْتَهَى إِلَيَّ، فَقُلْتُ: أَنَا مُحَمَّدُ بْنُ عَلِيِّ بْنِ حُسَيْنٍ، فَأَهْوَى بِيَدِهِ إِلَى رَأْسِي فَنَزَعَ زِرِّي الْأَعْلَى، ثُمَّ نَزَعَ زِرِّي الْأَسْفَلَ، ثُمَّ وَضَعَ كَفَّهُ بَيْنَ ثَدْيَيَّ وَأَنَا يَوْمَئِذٍ غُلَامٌ شَابٌّ، فَقَالَ: مَرْحَبًا بِكَ يَا ابْنَ أَخِي! سَلْ عَمَّا شِئْتَ ... فَقُلْتُ: أَخْبِرْنِي عَنْ حَجَّةِ رَسُولِ اللَّهِ r ))

 M a'ana: " Hakika mun shiga wa Jabir bn Abdillah [10] ; sai ya tambayi su wanene mutanen har ya iso kaina; sai na ce: Ni ne Muhammad bn Aliyu bn Alhusain, sai ya saukar da hanunsa zuwa ga kaina sannan ya cire maballi na na sama, sannan ya cire maballi na na kasa; sannan ya sanya tafinsa a tsakanin nonuwa na [11], Ni kuma a wannan lokacin yaro [12] ne saurayi, sai ya ce: Maraba da kai ya kai 'dan 'dan 'uwana!! ka yi tambaya kan abin da ka ke so, … sai na ce: Ka bani labarin aikin hajjin Manzon Allah ( s a w )?! " Sai ya ba shi labari da hadisinsa mai tsayin nan kan siffar aikin hajjin Annabi ( s a w )!

 Ibnu taimiyya y ace a cikin MINHAJUS SUNNA ( 4 / 50 ): " Haka kuma Abu Ja'afar Muhammad bn Aliyu yana daga cikin zababbun masu ili da addini, kuma an ce: abin sani kawai an masa lakabi da BAKIR ne; saboda ya tsaga ilimi ( kuma ya budo tushensa don ya yi kwari a cikinsa ), ba wai don sujjada ya tsaga goshinsa ba! ".

 Mizzi a cikin TAHZIBUL KAMALI ya fada a tarjamarsa: " Ijliy ya ce: Mutumin madina ne, tabi'I kuma amincecce, Ibnul Burki ya ce: Ya kasance malami ne mai girma ".

 Zahabi a cikin SIYAR ( 4 / 401 – 402 ) ya ce:" Shi ne shugaba kuma limami, baban Ja'afar Muhammad bn Aliyu bn Alhusain bn Aliyu, al'alawiy alfadimiy, mutumin Madina, 'dan ( gidan ) Zainul abiding … kuma ya kasance dayan wadanda su ka hada tsanin ilimi da kuma aiki, da shugabanci, da daukaka, da amintuwa, da nitsuwa tare da nauyin kima, kuma ya kasance ya cancanci khalifanci, kuma yana daya daga cikin Limamai goma da shi'a Imamiyya ta ke girmama su; kuma ta ke ma cewa su ma'asumai ne kuma sun san dukkan addini. Babu wani ma'asumi in banda Mala'iku da Annabawa, kuma kowani Mutum na dacewa kuma ya yi kuskure, a kuma dauka daga maganansa, kuma a bari; sai dai Annabi ( s a w ); shi kam ma'asumi ne kuma wadda ake karfafansa da wahayi. Abu Ja'afar ya shahara da lakabinsa BAKIR; wadda daga tsaga ilimi ne; ta yadda ya san asalinsa da ma abin day a buya a cikinsa. Hakika Abu Ja'afar ya kasance Limami ne, kuma mujtahidi [13] mai yawan karanta olittafin Allah, mai kuma girman sha'ani …".

 Ya kuma sake cewa ( p: 403 ): " Hakika Nasa'I da wassunsa sun kidaya shi daga cikin maluman tabi'ai da ke Madina, kuma duk hafizai sun hadu wajen kafa hujja da Abu Ja'afar ".

 JA'AFARU BN MUHAMMAD BN ALIYU BN ALHUSAIN BN ALIYU BN ABIY 'DALIB ( Rahimahul lahu ):

Al'imam Ibnu Taimiyya ya fada a cikin MINHAJUS SUNNA ( 4 / 52 – 53 ): " Ja'afarus sadiq ( r a ) na daga cikin zababbun masu ilimi da addini … Amru bn Abil Mikdam ya ce: " Na kasance idan na dubi Ja'afar bn Muhammad sai na smu yakinin cewa shi yana daga cikin ruwan Annabawa ( jinin annabta ) ".
 Ya kuma siffanta shi a cikin panpalet=dinsa da ya yi FALALAR AHLUL BAITI DA KUMA HAKKOKINSU ya ce ( p: 35 ): " Shehin maluman wannan al 'umman! ".

 Zahabiy a cikin SIYAR ( 6 / 255 ) ya ce: " Shi ne Limami kuma mai gaskiya, shehin Banu Hashim, baban Abdullahi, bakuraishe, bahashime, Al'alawiy, 'dan gidan annabta, mutumin Madina, sannan daya daga cikin manyan mutane ".
 Akansa da babansa ya ce: " Kuma sun kasance daga cikin manyan maluman madina ".

 A cikin TAZKIRATUL HAFFAZ ( 1 / 150 ) ya ce: " Shafi'I da Yahya bn Ma'in sun ce shi amincecce ne, an samo daga Abu Hanifata lallai ya ce: Ban ga wadda ya fi Ja'afar bn Muhammad malumta ba, Abu Hatim ya ce: Amincecce ne; ba a tambaya akan irinsa! ".

 ALIYU BN ABDILLAHI BN ABBAS ( Rahimahul lahu ):

  Ibnu Sa'ad a cikin ADDABAKAT ( 5 / 313 ) ya ce: " Kuma Aliyu bn Abdillahi bn Abbas ( r a ) ya kasance shi ne karami cikin 'ya'yan babansa, kuma shi ne mafi 'kyan bakuraishe a doron kasa, kuma mafi yawan sallah; shi ya sa ake masa lakabi da ASSAJJAD ( mai yawan sujjada ); saboda ibadarsa da kuma falalarsa ".
Ya kuma sake cewa ( p: 314 ): " Ya kasance amincecce ne, mai karancin hadisi ".

 Ya zo cikin TAHZIBUL KAMAL na Mizzi: " Ijliy da Abu Zur'ata sun ce: amincecce ne, Amru bn Aliyu ya ce: Ya kasance daga cikin zababbun mutane, Ibnu Hibban ya ambace shi cikin Amintattu " .

 Zahabiy a cikin SIYAR ( 5 / 252 ): " Shi ne shugaba, Abul Khala'if, kuma abu Muhammad, bahashime, mai yawan sallah, … ya kasance – Allah ya rahamshe shi – masani kuma mai aiki, mai girman jiki kuma mai kyau, mai tsayi kuma wadda ake jin kwar jininsa! ".


FASALI NA TARA:

'YAR AUNE TSAKANIN AKIDAR AHLUS SUNNA DA WASSUNSU KAN AHLUL BAITI!

  Ya bayyana daga abin da ya gabata; lallai akidar " Ahlus sunna wal jama'a " kan " Ahlu baitin nabiyyi " (iyalan gidan Annabi s a w ) tsaka-tsaki ne ( adalci ne ) tsakanin wuce gona-da-iri da kuma gajartawa wajen bada hakkoki, Kuma lallai su ( Ahlus sunna) suna son su ( Ahlul baiti) gaba daya, kuma suna jibintansu, basa kuma barin wani daga cikinsu, sannan basa wuce gona-da-iri kan wani. Kamar yadda kuma su ke son sahabbai gaba daya kuma su ke jibintansu; sai ya zama: sun hada son sahabbai da kuma dangi (n Manzon Allah s a w ); Wannan kuma sabanin wassunsu ma'abota son zuciya da ke wuce gona-da-iri kan wassu Ahlul baiti, sannan su yi wauta ( su bar ) dayawa daga Ahlul baitin da kuma sahabbai ( r a ).

  Daga cikin wuce gona – da – irinsu kan Limamai goma sha biyu na daga Ahlul baiti; - wadanda su ne: Aliyu da Al-hassan da Al-husain ( r a ) da kuma mutum tara daga cikin 'Yayan Al-husain – daga cikin haka: Abin da littafinsu  AL"USUL MINAL KAFI na Kulaini ya kunsa na Babuka ( Babi – babi) daga cikinsu:

 (( باب: أنَّ الأئمة عليهم السلام خلفاء الله عزَّ وجل في أرضه، وأبوابه التي منها يؤتى ))

Ma'ana: Babi: Lallai Limami ( a s ) sun e khalifofin Allah mabuwayi da daukaka a kasarsa, kuma su ne kofofinsa da ta wajensu kawai za a zo masa. (1/ 193).

 (( باب: أنَّ الأئمة عليهم السلام هم العلامات التي ذكرها عز وجل في كتابه ))

Ma'ana: Babi: Lallai su Limamai ( a s ) sun e alamomi da Allah ya ambace su a littafinsa ( 1 / 206). A wannan akwai hadisai guda uku daga cikin hadisansu wadda su ka kunshi fassarar fadinsa (Allah) madaukaki:

  ﭝﭞ           [النحل: ١٦]

Su na Cewa wai
(  النجم )
shi ne: Manzon Allah ( s a w ),

 su kuma Limamai su ne:
 (  العلامات ) .

 (( باب: أنَّ الأئمة عليهم السلام نور الله عز وجل ))

Ma'ana: Babi:  Lallai Limamai ( a s ) su ne hasken Allah mabuwayi da daukaka ( 1 / 194 ). ( Wannan babin ) ya kunshi wadansu hadisai daga cikin hadisansu, daga cikinsu akwai hadisin da ke isa zuwa ga Abu Abdullahi ( wadda shi ne: Ja'afarus saadiq ) da ke tafsirin fadin Allah mabuwayi da daukaka:

          

 Ya ce - kamar yadda su ke riyawa - :

     
 Mishkaat : Fadimatu ( a s ).
     
   
  Misbaah: Shi ne: Al hasan.

     
 Al misbaahu fi zujaajat: shi ne Al husain.


         

 Ma'ana: Fadimatu tauraro ce mai haski cikin matan duniya

        

 Yukadu min shajaratin: shi ne Annabi Ibrahim ( a s ).

           

 Ma'ana: " ( Annabi Ibrahim )ba bayahude ba kuma ba banasare ba!

     

 Ma'ana: Ilimi ya yi kusa ya bulbulo ( fito ) daga gare ta.

          ﯬﯭ       ﯰﯱ 
  Nurun ala nur: Limami na fita daga gare ta ( Fatima ) bayan limami.

       

  Allah na shiryad da wadda yaga dama zuwa ga wadannan limaman! ".

 (( باب: أنَّ الآيات التي ذكرها الله عز وجل في كتابه هم الأئمة ))

 Ma'ana: Babi: Lallai ayoyin da Allah mabuwayi da daukaka ya ambace su a littafinsa su ne Limamai ( 1 / 207 ).  
 A wannan babin ya fassara fadin Allah mabuwayi da daukaka:

                     

 Ya fassara lafazin: (Al'aayaat) da ke cikin ayar da cewa: su ne: Limamai.
 Da kuma tafsirin fadinsa:

                    

 Ya fassara: ( Al aayaat ) da ke cikin ayar da: Wadanda aka mu su wasiyya da shugabanci da Imamanci gaba dayansu!!!
 Ma'ana wannan shi ne: Lallai ukuba da azaba da ta sauka wa iyalan fir'auna; sababinsa shi ne: karyatawarsu ga wadanda aka musu wasici wadanda su ne: Limamai!!

 (( باب: أنَّ أهل الذكر الذين أمر الله الخلق بسؤالهم هم الأئمة عليهم السلام ))

 Ma'ana: Babi: Lallai ( Ahluz zikri ) da Allah ya umurci halittu su tambaya ( matukar bas u da sani ) su ne: Limamai ( a s ) ( 1 / 216 ).

 (( باب: أنَّ القرآن يهدي للإمام ))

  Ma'ana: Babi: Lallai Qur'ani yana shiryarwa zuwa ga Imami ( 1 / 216 ).
 A wannan babin ya ambaci tafsirin fadin Allah mabuwayi da daukaka:

                  

 Ma'ana: " Lallai wanna Qur'anin yana shiryarwa zuwa ga abin da  ya fi  "  ya  fassara shi da cewa: Qur'ani na shiryarwa zuwa ga Imam!!
 Sannan a cikin babin ya kawo tafsirin fadin Allah mabuwayi da daukaka:

             

 (( باب: أنَّ النعمة التي ذكرها الله عز وجل في كتابه الأئمة عليهم السلام ))

 Ma'ana: Babi: Lallai ni'imar da Allah mabuwayi da daukaka a littafinsa ita ce: Limamai ( a s ) 1 / 217 ).
 A cikin wannan babin akwai tafsirin fadin Allah mabuwayi da daukaka:

                            
 Tare da riya cewa Aliyu ( r a ) ya ce: 

 (( نحن النعمة التي أنعم الله بها على عباده، وبنا يفوز من فاز يوم القيامة ))!!

 Ma'ana: " Mu ne ni'imar da Allah ya yi wa bayinsa, kuma da mu ne wadda ya tsira ya tsira ranar tashin alkiyama "
 Da kuma tafsirin fadin Allah mabuwayi da daukaka cikin suratur rahman:

           
 Ya ce:

 (( أبالنبيِّ أم بالوصيِّ تكذبان؟!!)).

 Ma'ana: " Yanzu wannan Annabin da wadda aka masa wasici ku ke karyata ".

 (( باب: عرض الأعمال على النبي صلى الله عليه وآله، والأئمة عليهم السلام ))

 Ma'ana: Babin: Bijiro da aiyuka wa Manzon Allah ( s a w ) da kuma Limamai ( a s ) ( 1 / 227 ).

 (( باب: أنَّ الأئمة عليهم السلام عندهم جميع الكتب التي نزلت من عند الله عز وجل، وأنهم يعرفونها على اختلاف ألسنتها ))

 Ma'ana: Babin: Lallai Limamai ( a s ) a wajensu akawai dukkan littafan da su ka sauka daga wajen Allah mabuwayi da daukaka, kuma lallai su sun san su ( littafan ) duk da banbancin harshensu ( yarensu) ( 1 / 227 ).

 (( باب: أنه لم يجمع القرآن كله إلا الأئمة عليهم السلام، وأنهم يعلمون عمه كله ))

 Ma'ana: Babin: " Lallai babu wadda ya tara Qur'ani ( da kiyaye shi – hardace shi - ) sai Limamai ( a s ), kuma lallai su suna da iliminsa gaba daya " ( 1 / 228 ).

 (( باب: أن الأئمة عليهم السلام يعلمون جميع العلوم التي خرجت إلى الملائكة والأنبياء والرسل عليهم السلام ))

 Ma'ana: Babin: Lallai Limamai ( a s ) sun san dukkan ilimin da ya fita zuwa ga Mala'ika da Annabawa da Manzanni ( a s ) ( 1 / 255 ).

 (( باب: أنَّ الأئمة عليهم السلام يعلمون متى يموتون، وأنهم لا يمون إلا باختيار منهم ))

 Ma'ana: Babin: Lallai Limamai ( a s ) sun san yaushe su ke mutuwa, kuma lallai basa mutuwa said a zabinsu ( 1 / 258 ).

 (( باب: أن الأئمة عليهم السلام يعلمون علم ما كان وما يكون، وأنَّه لا يخفى عليهم الشيءُ صلوات الله عليهم ))

 Ma'ana: Babin: Lallai Limamai ( a s ) sun san abin day a kasance da abin da ya ke kasancewa, kuma Lallai baa bin day a ke buya musu ( yabon Allah ya tabbata a gare su ) ( 1 / 260 ).

 (( باب: أنَّ الله عز وجل لم يعلّم نبيَّه علماً إلا أمره أنْ يعلِّمه أمير المؤمنين عليه السلام، وأنَّه كان شريكه في العلم ))

 Ma'ana: Babin: Lallai Allah mabuwayi da daukaka bai sanar da Annabinsa wani ilimi ba face ya umurce shi day a sanar da amirul mu'uminina ( Aliyu a s), kuma lallai shi ( Aliyu )ya kasance wadda ya yi tarayya da shi ( Annabi ) wajen ilimi ( 1 / 263 ).

 (( باب: أنَّه ليس شيء من الحق في  يد الناس إلا ما خرج من عند الأئمة عليهم السلام،  وأنَّ كلَّ شيءٍ لم يخرج من عندهم فهو باطلٌ ))

 Ma'ana: Babin Lallai babu wani abu da ke hanun Mutane na gaskiya face ya fita ne daga hanun Limamai, duk kuma abin da ba daga hanunsu ya fito ba to barna ne ( 1 / 399 ).

  Wadannan babuka sun kunshi hadisai daga cikin hadisansu, kuma an ciro su ne daga littafinsu bugegge da mabugar (Book shop din) Saduk a Dahran su ka watsa a shekara ta 1381h.
 Kuma suna daukan littafin cikin manyan littatafansu – in ma ba shi ne babbansu ba -, a mukaddamar (gabarawan) littafin kuma akwai yabo mai girma wa littafin da kuma mawallafinsa, Mutuwarsa kuma ya kasance ne a shekara ta 329h. shi kuma wannan abin da na ciro shi daga littafin misali ne daga wuce gona – da – irin magabatansu kan Limamai ( 12),
 Amma wuce gona – da – irin na karshensu kan Limaman to zai bayyana daga maganan daya daga cikin manyansu a wannan zamanin wadda shi ne Khumaini cikin Littafinsa  الحكومة الإسلامية shafi na 52, watsawar: Al-Maktabatul Islamiyyatul Kubra da ta ke Dahran)
 Yana cewa:


(( وثبوت الولاية والحاكمية للإمام (ع) لا تعني تجردَه عن منزلته التي هي له عند الله، ولا تجعله مثل من عداه من الحكام؛ فإنَّ للإمام مقاماً محموداً ودرجةً ساميةً وخلافةً تكوينيةً تخضع لولايتها وسيطرتها جميعُ ذرات هذا الكون، وإنَّ من ضروريات مذهبنا أنَّ لأئمتنا مقاماً لا يبلغه ملَكٌ مقرَّب، ولا نبيٌّ مرسَلٌ، وبموجب ما لدينا من الروايات والأحاديث فإنَّ الرسول الأعظم (ص) والأئمة (ع) كانوا قبل هذا العالم أنواراً؛ فجعلهم الله بعرشه مُحدقين، وجعل لهم من المنزلة والزلفى ما لا يعلمه إلا الله، وقد قال جبرائيل كما ورد في روايات المعراج: لو دنوت أنملة لاحترقتُ، وقد ورد عنهم (ع): إنَّ لنا مع اللهِ حالاتٍ لا يسعها ملكٌ مقرَّبٌ، ولا نبيٌّ مرسَلٌ ))!!!

  Ma'ana: " Kuma tabbatuwan wilaya da hakimiyya ga Imami ( a s ) baya nufin tobuwansa daga matsayinsa day a ked a shi a wajen Allah, kuma hakan ba zai sanya shi ya zama kamar waninsa ba daga cikin masu hukunci; saboda shi limami yana da wani matsayi abun yabo da kuma daraja madaukakiya da kuma kalifancin duniya wacce duk kwayar zarran duniyan nan na kankan da kai ga wannan khalifancin da mulkin. Kuma yana cikin lalurar  mazhabarmu ( ma'ana: abin da kudure shi cikin zuciya: wajibi ne): Lallai Imamanmu su na da wani irin matsayi da mala'ika makusanci ko annabi manzo ba zai isar masa ba. Kuma abin da ke wajenmu na riwayoyi da hadisai su ke hukuntawa shi ne: Lallai Manzo mafi girma ( s a w ) da kuma limamai ( a s ) sun kasance haske ne kafin wannan duniyar, Allah ya sanya su kewaye da al'arshinsa, sannan ya bas u matsayi da kusacin da wadda ya san shi sai Allah, hakika kuma Jibrilu ya fada kamar yadda ya zo cikin riwayoyin mi'iraji:
 " Da zan kara kusanci gwargwadon kan yatsa da na kone " ya kuma zo daga gare su ( Limamai a s ) cewa:
 " Lallai mu na da wassu halaye tare da Allah; Mala'ika makusanci ko annabi manzo ba ya isar musu " !!!

  Mutum ba zai ga ko ya ji irin wannan maganan ba face ba zai mallaki wani abu ba sai dai ya ce:

                        ﯶﯷ           [آل عمران: ٨].

  Ma'ana: "  Ya ubangijinmu kada ka karkatar da zuciyarmu bayan ka shiryad da mu, kuma ka mana baiwar wata rahama daga wajenka; lallai kai ne mai yawan baiwa ".

  Sannan duk wadda yak e da wata basira duk karancinta zai tabbatar kuma ya yanke cewa abin da ya gabatan nan daga gare su ( 'Yan shi'a) da makamantansa karya ne kuma kage ne da aka kaga was u wadannan limaman, kuma lallai su sun barranta daga masu wuce gona – da – iri a kansu tare da aikinsu (na wuce  gona – da – irin! ).



FASALI NA GOMA:
HARAMCIN DANGANTA KAI - BA TARE DA HAKKI BA - ZUWA GA AHLUL BAITI

  Mafi daukakan danganta; shi ne dangantakar Annabinmu Muhammadu ( s a w ), haka kuma mafi daukakan dangata kai; shi ne dangantawa zuwa gare shi ( s a w ) da kuma zuwa ga mutanen gidansa - matukar dangantawan ya inganta -.
hakika ( da'awar ) danganta kai zuwa ga wannan gida ( mai girma ) ya yi yawa cikin Larabawa dama Ajamawa; a kan haka: Duk wanda ya kasancena daga cikin mutanen wannan gidan kuma yana mumini to Allah ya hada masa tsakanin daukakar imani da kuma daukakar danganta, amma wanda kuma ya yi da'awar kasancewarsa cikin wannan gida ( dangi ) madaukaki alhali baya cikinsu to ya aikata haramun, kuma yana nuna koshi da abin da ba a bashi ba; ga shi kuwa Annabi ( s a w ) ya ce:

 " المتشبِّع بما لم يُعطَ كلابس ثوبَيْ زورٍ "

Ma'ana: " Wadda ke nuna koshi da abin da ba a bashi ba kamar mai saka tofofin karya ne " Muslim ne ya ruwaito shi cikin sahihinsa (2129) daga hadisin A'ishatu ( r a ). kuma haramcin dangantan mutum zuwa wanin danginsa ya zo cikin hadisai ingantattu; daga cikin haka: Hadisin Abu zarrin ( r a ) lallai shi ya ji Manzon Allah ( s a w ) yana cewa:

 " ليس من رجل ادعى لغير أبيه وهو يعلمه إلا كفر بالله، ومن ادعى قوماً ليس له فيهم نسبٌ فليتبوأ مقعده من النار "

Ma'ana: " Babu wani Mutum da zi yi da'awar wanin babansa - alhalin ya sanshi - face ya kafirce da da Allah, Duk kuma wanda ya yi da'awar Mutanen da ba shi da dangantaka cikinsu to ya tanadi makomnsa a wuta " Bukhari ( 3508 ) da Muslim ( 112 ) ne su ka ruwaito shi, wannan kuma lafazin Bukhari ne. A cikin Sahihul Bukhari ( 3509 ) daga hadisin Wasilatu bn Al-aska'a ( r a ), lallai shi ya ce: Manzon Allah ( s a w ) ya ce:

 " إنَّ من أعظم الفِرى أن يدَّعيَ الرجل إلى غير أبيه، أو يُريَ عينَه ما لم ترَ، أو يقول على رسول الله r ما لم يقل "

Ma'ana: " Lallai na daga cikin manya-manyan karya: Mutum ya yi da'awar ( Ubantakan) wanda ba ubansa ba, ko ya nuna wa idonsa abin da bata gani ba ( wato: a barci), ko ya kirkiri magana ya jingina wa Manzon Allah ( s a w ) - alhali bai fada ba - ".
A cikin - Majmu'u fatawa Shekhil Islam Ib Taimiyyat ( 31 / 93 ) - Lallai wakafi da aka tanada don Ahlul baiti / ko Ash-raf ( Sharifai ) ba wanda ya cancanci dauka daga gare shi sai wanda dangantakansa ya tabbata zuwa ga Ahlul baiti, Hakika an tambaye shi kan wakafin da aka yi wa Sharifai, ( ya kuma ce: Lallai su: AKARIBU ne), To su akaribun su ma sharifan ne ko ba Sharifai ba ne?, kuma shin ya halatta su dauki wani abu daga cikin wannan wakafin ko a'a?

Sai ya amsa da cewa: " Alhamdu lil lah! In wakafin ya zama ga Ahlul baiti ne ( iyalan gidan Annabi s a w ), ko ga sashen Ahlul baiti; kamar ( wadanda ake musu lakabi da) ALAWIYYUN, da FADIMIYYUNA ko ADDALIBIYYUN; wanda 'Ya'yan Ja'afar da 'Ya'yan Akilu sun shiga cikinsu, ko ga ABBASIYYUNA da makamancin haka, to ba wanda ya cancanci wani abu daga cikin wannan ( wakafin ) sai wanda dangantakansa ya ke ingancecce tabbacecce, Amma wanda ya yi da'awar yana cikinsu, ko kuma aka san baya cikinsu to bai cancanci ( komai ) daga cikin wannan wakafin ba, ko da kuwa ya yi da'awar yana cikinsun; kamar BANU ABDULLAHI BN MAIMUN ALKADDAH; saboda masana ilimin dangantaka da wassunsu sun san ba su da dangantaka ingancecciya ( da Annabi s a w ); wanda su ka yi shaida da haka kuwa su ne: Sashen maluman Fiqhu da Hadisi da (Ilmul ) kalam da masana danganta, Kai! takardun kotu da su ka tabbatar da hakan ( Al-mahaadir), wannan cikin manya-manyan littafan musulmai, kai wannan yana daga cikin abin da shahara a wajen maluma shaharar da ta kai a ce mata: MUTAWATIR.
Haka wanda ya yi wakafi ga Sharifai, to wannan lafazin - sharifai - sananne ne - a urfi - ba mai shiga cikinsa sai wadda dangantakansa zuwa ga Iyaln gidan Manzon Allah ( s a w ) ta tabbata (kuma ta inganta).
Amma in mai wakafi ya yi wakafi ga 'Ya'yan wane, ko dangin wane da makamancin haka, kuma a cikin ( lafazin ) wakafin babu abin da ya yi nuni cewa na iyalan gidan Annabi, sannan abin da aka bada shi wakafin mallakan wanda ya bada wakafin ne, ( to a irin wannan halin ) wakafinsa ya inganta ga zurriyar da ya ayyanan, Banu Hashim kuma basu shiga cikin wannan wakafin ba ".


A nan ne wannan matashiya ( panpalet) gajeruwa kan FALALAN AHLUL BAITI DA KUMA DAUKAKAR MATSAYINSU A WAJEN AHLUS SUNNA WAL JAMA"A ta zo karshe, Ina kuma rokon Allah datarwa zuwa ga abin da yardarsa ya ke cikinsa, da kuma fahimta cikin addininsa, da tabbata kan gaskiya; lallai Allah mai ji ne kuma mai amsawa, Allah kuma ya yi karin yabo da aminci da albarka ga Annabinmu Muhammadu, da Iyalansa da Sahabbansa gaba daya.




[1]  Daga cikin misalinsa:  Fadin Allah:
                           [لبقرة: ٩٨ ]
Kaga anan Allah ya yi Magana kan gaba da Jibrilu da Mika'ilu, - alhali kafin nan: ya yi magana kan gaba da Mala'iku gaba daya; wadda Jibrilu da Mika'ilu sashe ne daga cikin mala'iku.
[2]  A rabon gado akan fara bawa wadanda su ke da (faradi), sannan sai idan ya saura ne a ke bawa  masu (ta'asibi), in kuma bai saura ba sai su yi hakuri; duk da cewa; akwai wadanda su na ci da ( ta'asibin ) - kamar 'Da da 'dan 'da, da kuma Uba - wadanda basa faduwa a kowani hali. Masana ilimin rabon gado sun a cewa akan ci gado ne da dayan hali biyu: FARADI da TA'ASIBI kamar yadda hadisin da ya gabata ya nuna, kuma kamar yadda fadin Allah
                   ﯢﯣ     

 Ya ke nunawa.
[3]  " Sarid " wani nau'i ne na abinci????
[4]  " Nawasib " su ne???
[5]  " Khumusi " shi ne: ??? sannan shi kuma " Fai'u " shi ne???
[6]  " Asari " shi ne maganan Sahabi ko Tabi'I ko aikinsu.
[7]  " Hadisi mutawaturi " shi ne wadda adadi da yawa - wadda a al'adance ba za su hadu kan yin karya ba - su ka ruwaito shi, kuma a kowani set na masu riwaya an shardanta samun irin wannan adadin, sannan madogararsu wajen riwayar ya zama ji ne ko gani.
[8]  " Alkaramah " ta kan kasance ne kawai ga waliyyan Allah, yayin da ita kuwa " Al' ihanah " ta ke kasancewa ga wassunsu.
[9]  Maganan farko shi ne: Khadija ta fi A'isha, na biyun kuma A'isha ta fi Khadija.
[10]  Alhali a lokacin yana dattijo kuma makaho.
[11]  Ya yi haka ne saboda kasancewarsa yaro, kuma don ya debe masa kewa da wannan tausasawan nasa; dadin dadawa ga shi yana cikin iyalan gidan Manzon Allah ( s a w ).
[12]  Wannan shi ne sababin da ya sa ya masa haka; don da babba ne da ba zai yi kyau a cire masa aninin riga, sannan kuma a sa tafin hanu a tsakanin nonuwansa ba!.
[13] " Mujtahidi " shi ne wadda?????

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...