2016/04/22

MATSALOLIN MASU DA'AWA (من مشكلات الدعاة)



MATSALOLIN MASU DA'AWA

Babin farko:

Babi na biyu:

Babi na uku:

Babi na fudu:

Babi na biyar:











Babin farko: Sakaci wajen biyayya wa Allah; wannan kuma na bayyana cikin fuskoki masu zuwa:

1.   Kauracewa ma maganan Allah ( Al-qur'ani ) / da kuma raunin tunani cikin ayoyin Allah ( da ya saukar da kuma na halitta ).
2.   Raunin ibada ( kamar raunin jin tsoron Allah, da kiyaye hakkokinsa, tare da raunin kankan da kai wa Allah).
3.   Son duniya tare da manta lahira ( yana kuma daga cikin hakan: Jiran sakayya kan aikinsa anan gidan duniya – ko daga Allah ko kuma daga Mutane - .
4.   Sakaci wajen cin naman mutane ( giba ) da annamimanci da karya da kuma gani.
5.   Aiki ya saba wa Magana.
6.   Tsayuwa da yin aiyukan alkhairi ( aikin Allah ) don sha'awa da burgewa da kuma shi ne aikina, ba don bauta wa Allah bad a kuma neman kusanci zuwa gare shi.


Babi na biyu: Matsalolin zuci:

1.   Karancin damuwa da aiyukan ( ibadun ) zuci;
2.   KKKaikashewan zuciya.
3.   Da'awar ( jin da riya cewa ) yana da Ikhlasi.
4.   Munana zato wa 'yan 'uwansa.
5.   Tsoro da faduwar gaba ( tare da jin cewa bai kai komi ba ).
6.   Shu'umci ( ganin abu da idon hagu ).
7.   Hassada da kiyayya.
8.   Yanke kauna.
9.   Son zuciya ( da bin hakan ).

Babi na uku: Matsaloli ga zati ( kai ):

1.   Ji da kai da kuma ganin aiki.
2.   Yawan tsumuwa da kuma saurin fushi.
3.   Son bayyana da kuma son shugabanci.
4.   Son yabo da jawo shi tare da jin dadinsa, wadda hakan ya hada da: Kwadayin bayyanar da aiki, da son yin hidima wa mutane a bayyane, tare da kaiwa makura ( wuce gona da iri ) wajen fito da abubuwan bayyane.
5.   Raina kai tare da nuna gazawa wajen daukan nauyace – nauyace ( ga wadda ya cancanci hakan ).
6.   Rashin himmatuwa da bukatocinsa da su ka kebance shi ( kona kai da haskaka wa wassu kamar fitila ).
7.   Kafuwa kan kuskure; da kuma rashin ikrari da shi, tare da rataya sakacin ko kuskuren ga waninsa, hadi da kawo sabbuba ( na karya da na gaskiya ) ga kura – kurai tare da kubutar da kai daga gare su.
8.   Neman daukar fansa wa kai.
9.   Gabatar da maslahar kai da kai akan maslahar al'umma.
10.                Kambama abubuwa da kuma maida karami babba ( maida allura garma).
11.                Rasa yi wa kai hisabi da kuma manta aibubbukan rai.
12.                Kai – komo a gu guda da kuma rashin bunkasa abubuwa.
13.                Dogaro ga wassu da mimmike kafa.
14.                Rowa.
15.                Sakaci da shubuhohi.
16.                Buyan danganta falala ga ma'abotansa.
17.                Yawan zance akan kai.
18.                Jafa'i da karancin tawadu'I ( kankan - da – kai ).
19.                Yawan kokawa.
20.                Hiran dare.

Babi na fudu: Matsalolin alakoki:

1.    Cutar da iyaye da kuma yanke zumunta.
2.    Kuncin kirji wajen dauke mutane / kaushin hali da kuma tsanani, tare da kama mutane kan kuskure ko zamewan kafa.
3.    Alfahari da matsayi ko danganta ko gari.
4.    Rashin aje mutane a matsayinsu da kuma tawaye wa mutane abubuwansu!
5.    Zari da daukan abun da ya fi karfin …
6.    Ko – oho da iyalai da barin tarbiyyarsu da kuma yi musu nasiha.
7.    Karancin hidima wa iyalan gida.

Babi na biyar: Matsaloli cikin manhaji ( salon tafiya da da'awa ):

1.   Shanbe society da kuma rashin lura da damammaki da ya ke da su da da guraben alkhairorinsa.
2.    Wuce gona – da – iri wajen yabo ko zargi.
3.    Kuncin fahimta da karancinsa wajen fahimtar wannan addinin.
4.    Ta'assubanci da kuma kishiyantar ta'asubanci da ta'asubancin irinsa.
5.    Amincewa da kowani mutum, da kuma rashin bin diddigin abubuwa.
6.    yawan sukan sauran mutune da ke kaiwa zuwa ga: tsarkake kai, da kuma kawar da kai ga barin sauraron mai nasiha da kuma yin tunatarwa kan barin aibuka.
7.    Kambama barna da kuma ma'abotansa.
8.    Ko – oho wajen bin tsari.
9.    Karkasa mutane da kuma sanya su aji – aji; ( wani ace mai tsanani ne wajin bin addini, wani kuma mai sako – sako ne wajen wajin riko da shi … ).
10.                Soyayya da kiyayya kan wata kungiya ko wata jama'a.
11.                Bawa da'awa kasheshshun lokuta.
12.                Karanta Istikhara ( bawa Allah zabi ), da kuma shawartar mutane.
13.                Kwadayin neman kubuta daga duk kan halittu.
14.                Rashin damuwa da matsalolin al'umma.
15.                Rashin bin diddigi.

 رابعاً: تسرب الطاقة

1.    Son jayayya da musu.
2.    Karancin himma; haka na bayyana cikin:
·         Yawan barci da yawan cin abinci.
·         Cewa: da sannu – da sannu.
·         Fadada, da kuma sakaci cikin huldodi.
·         Da kuma shagaltuwa da abin da aka fi ga barin abin da ya fi.
·         Da kuma wuce gona – da – iri cikin hutu da kuma fita shan iska da bude ido.
3.   Almubazzaranci.
4.    Rashin bin abubuwa cikin tsanaki, da rashin juriya tare da karancin hakuri, tare da nuna gazawa a lokacin faruwar kowace musiba.
5.   Gaggawan neman sakamakon aiyuka.
6.   'Yar table cikin aiyuka da rashin tabbata cikin abu guda.
7.   Gaggawa wajen daukar matsaya da mataki.
8.    Raunin ilimin da yawa - yawan masu da'awa su ke fitarwa, tare da jinkiri kafin fitar da shi, tare da rashin bin tsari cikin yawa – yawan programs.
9.    Yawan tunani cikin al'amuran duniya da kuma tsoron gaba a rayuwa.
10.       Gwada kai da wadanda basu cin nasara cikin al'amura ba ( tare da jin wai gwanda ni akansu ).


Dr. Yahya bn Ibrahim Al – yahya
www.Daiba.ogn

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...