HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 08/RAJAB/1437H
daidai da 15/ Afrilu/ 2016M
LIMAMI MAI HUXUBA
DR. SALAH XAN MUHAMMADU ALBUDAIR
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
HATSARIN YIN TA'ADDANCI GA
DUKIYAR GADO
Shehin Malami wato: Salah
xan Muhammadu Albudair –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken:
Hatsarin yin ta'addacin ga kayan gado, Wanda kuma ya tattauna a cikinta, kan haramcin
cin dukiyar gado, da hatsarin aikata haka, musamman kuma waxanda Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya
tsawatar kan cinye dukiyarsu; wato: Mace, da Maraya, yana mai bayyana munin
wannan aikin, da kuma uqubar da aka tanada akan wanda ya aikata shi, a Lahira.
HUXUBAR FARKO
Godiya ta tabbata ga Allah, Ina gode masa akan
shiriyar da yayi mana, da kuma inuwantar da mu da yayi da mafificin inuwa, kuma
ina neman tsarinsa wajen bada haqqoqi daga xabi'ar jinkiri ko karkatar da haqqi.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi
da abokin tarayya; shaidawar da nake fatan samun tsira daga hanyar ma'abuta
vata da karkata, kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu
bawansa ne kuma manzonsa, wanda yake cewa:
"Duk wanda
ya mutu ya bar wata dukiya ko wani haqqi to na iyalansa ne, Wanda kuma ya bar
wata wahala ko bashi to wannan wahalar, ko biyan bashin suna kaina".
Allah yayi salati da
sallama a gare shi, da kuma iyalansa da sahabbansa; mafi alherin qabila da zamani
da Mutane.
Bayan haka:
Ya ku Musulmai!!
Ku kiyaye dokokin Allah
cikin kai-komo, kuma ku riqa kiyayarSa cikin abinda ya voye da wanda ya
bayyana,kuma ku yi bauta a gare shi, yadda ya cancanci a yi masa bauta, a yammaci
dana safiya. "Kuma ku bi dokokin Allah da taqawa, kuma ku sani lallai Allah yana tare
da masu taqawa".
Ya ku Musulmai!!
Duniya xan jin daxi ne, Duk wanda kwaxayinsa da zalamar ta ya
dabaibaye shi To faxuwarsa a cikinta tayi kusa, Kuma wanda ya zura idanunsa ga
abinda ba nasa ba Sai hasara da tavewa suyi sauri zuwa gare shi, sai kuma baqin
ciki da vacin rai su lazimce shi.
Kuma LAHIRA ita tafi soyuwa
a wurin ma'abuta imani fiye da kowani abu mai darajar qima wanda ke ratayuwa da
zuci, kuma ita tafi xaukaka akan kowani abinda ba ita ba, kuma ita tafi girma
akan kowani abu mai kyau.
Shi kuma rabiyar kayan da aka mutu aka bari
(kayan gado) Shari'a ce saukakkiya (daga Allah), kuma rabo ne na adalci.
Duk wanda kuma amanarsa ta lalace, Ha'incinsa ya bayyana,
har yake yin rantsuwa akan munafurci da yaudara, kuma warware alkawarinsa ya
bayyana, da hiyanarsa da makircinsa = To, sai ya munana rabiyar riba, ya kuma
ha'inci abokin kasuwancinsa, ya xauki rabonsa, sa'annan yayi kwaxayin rabon
waninsa, har ya zama, bai bar wa abokin kasuwarsa daidai da "kan yatsa"
ko kamar "taqi guda" ba. Haka ba zai bar masa wajen zama ko wurin
hawa ba, ko kuma wurin qailula ko wata hanya, ko wata dama, ko kuma wata dukiya
ba,
Idan aka ce za a tattauna
tare da shi sai ya qulle mutum a
cikin ransa, idan kuma zaman lissafi aka ce za a yi To sai ya gudu, idan kuma aka nemi wani haqqi a wurinsa sai yayi xagawa, ya gudu; wurin da wani ba zai ganshi ba, yana mai yin ha'inci, da zarar haqqi, da makirci da yin wayo, "Kuma lallai ne, dayawa daga abokan hulxa" [Sad: 24] –kamar: masu lazimtar juna da makusanta da abokai, da masu tarayya cikin kasuwanci- "Sashinsu lallai yana zambatar sashi, Saidai waxanda suka yi imani, kuma suka aikata aiyukan kwarai, kuma su kaxan ne kwarai" [Sad: 24].
cikin ransa, idan kuma zaman lissafi aka ce za a yi To sai ya gudu, idan kuma aka nemi wani haqqi a wurinsa sai yayi xagawa, ya gudu; wurin da wani ba zai ganshi ba, yana mai yin ha'inci, da zarar haqqi, da makirci da yin wayo, "Kuma lallai ne, dayawa daga abokan hulxa" [Sad: 24] –kamar: masu lazimtar juna da makusanta da abokai, da masu tarayya cikin kasuwanci- "Sashinsu lallai yana zambatar sashi, Saidai waxanda suka yi imani, kuma suka aikata aiyukan kwarai, kuma su kaxan ne kwarai" [Sad: 24].
Kuma mafi sharri daga cikin Mutane shine wanda idan yayi
kwaxayi Sai yayi sata, idan kuma ya qoshi Sai ya yi
fasiqanci, Idan kuma ya buqaci wani abu Sai ya wawure, idan kuma wadaci ya samu to Sai yayi alfasha,
fasiqanci, Idan kuma ya buqaci wani abu Sai ya wawure, idan kuma wadaci ya samu to Sai yayi alfasha,
KUMA
YANA DAGA CIKIN GAGGAWA CIKIN ZALUNCI: Cinye wa magada kayan gado, Allah mabuwayi cikin
xaukakarsa yana cewa:
"Kuma kuna cin
dukiyar gado, ci na tarawa" [Fajr: 19].
kalmar "TURAS" a
cikin/
(وتأكلون التراث
أكلا لما).
Shine GADO, Shi kuma
"LAMMU": Daga, tara abu ne. Wannan kuma shine ta'addanci a cikin
kayan gado, ta hanyar Mutum ya cinye rabonsa na gado, da gadon waninsa.
Kuma duk Mutumin da ya shirya wayo don ya sarayar da
kason wasu magada da abinda aka yanka musu (na gado), ko ya caccanza rabon wasu
da haqqoqinsu, ko ya yi zalunci wajen raba gado, ya nisanci adalci cikin
karkasa shi, ko ya yanke wani magajin daga rabonsa na gado, ko ya killace
dukiyar gado, ya kuma voye tushenta da kuma xaixaikunta, tare da voye takardun da suke tabbatar da
mallakar kayan gado, ko ya taqaitu shi kaxai da jujjuya dukiyar gado, kuma ya
so kaxaituwa wajen amfana da ita, ko kuma
ya sanya magaji janyewa daga rabonsa, ko yarda tare da karvar sashin haqqinsa =
To, (mai irin waxancan sifofin) haqiqa, ya qetare hukuncin Allah da rabiyarSa
da iyakokinSa, Allah mabuwayi cikin xaukakarSa a qarshen ayoyin rabon gado, a
cikin suratun Nisa'i = yana cewa:
"Waxancan iyakoki ne
na Allah" [Nisa'i: 13] –ma'ana: waxannan kashe-kashe, da rabo; sune
dokokin Allah-, "Kuma duk wanda ya yi xa'a wa Allah da manzonSa –ma'ana:
bai yi qari wa wasu daga cikin magada ba, kuma bai tauye wa sashi ba, ta hanyar
shirya wayo. Kuma ya bar magada kan abinda Allah ya hukunta ko ya raba, to zai
shigar da shi aljannoni waxanda qoramu suke gudana daga qarqashinsu, suna masu
dawwama a cikinsu. Kuma wannan shine rabo mai girma * Wanda kuma ya sava wa
Allah da ManzonSa kuma ya qetare iyakokinSa –ta hanyar yin cuta cikin
rabiyar gado- zai shigar da shi wata wuta, yana mai dawwama a cikinta, kuma
yana da azaba mai walaqantarwa" [Nisa'i: 13-14].
Kuma a cikin adalci akwai
sada zumunci da qaunar juna da haxin kai
# A cikin zalunci kuma, akwai
savani, da rabuwar kai, da xaixaicewa, Da kuma qiyayyar juna, da yin faxa, da
jayayya, akan kayan duniya xan kaxan, wanda bai-kai-ya-kawo ba.
Shi kuma Mutum mai yawan ha'inci azzalumi a ko-yaushe ya
kan yi tsalle yayi gaggawa don cinye haqqoqin mace dana maraya (a cikin gado),
alhali, Manzon shiriya (صلى
الله عليه وسلم) yana cewa:
"Ya Allah! Lallai
ne ni ina sanya tava haqqin raunana guda biyu cikin qunci; wato: Mace da kuma
Maraya",
Ibnu-Majah ya ruwaito shi daga hadisin Abu-Hurairah (رضي الله عنه).
Kuma ma'anan kalmar
"Uharrij" a cikin hadisin, shine: Ina quntata wa Mutane wajen
tozartar da haqqin maraya da mace, kuma ina kausasawa akan haka, kuma ina
tsawatarwa, kuma ina riskar da qunci da zunubi ga duk wanda ya tozarta haqqin maraya
da mace.
Ya kai wanda ka samu damar xauke dukiyar gado cikin
sauqi, ,,,
Ya wanda ya mamaye kayan
gadon 'ya'ya mata, wanda kuma rauninsu ne, da yin shirunsu da kunyar da suke da
ita ya ruxe shi, ,,,
Ya wanda ya zauna akan
dukiyar gado ta zawarawa, da marayu, sai qarancin shekarunsu da rauninsu da
gajiyawar da suke da ita ya ruxe shi ,,,
Hannayenka biyu su halaka (تبت
يداك)!
Aikinka kuma ya lalace!! Tavewarka ta dawwama!!
Ta yaya ranka tayi maka
daxin ka mamaye dukiya da filaye da kaya, sai kuma ka jingina 'yan'uwanka da
danginka zuwa ga talauci da tozarta,,,
Ta yaya ranka tayi maka daxi; kan mallake riba da 'ya'yan itatuwa da
kuxaxen haya da gidaje, su kuma 'yan'uwanka ka fiskance su da qauracewa da
qiyayya da raini da wulaqanci;
Wanene ya halatta maka waxannan al'amura; qulla su da
warware su, da kuma shigi da fici a cikinsu?
Wanene kuma ya halatta maka
dukiyar da aka bari ta gado; riqe ta, da sake ta, haramta ta (ga wanda kake so)
da kuma ciyar da ita?
Bone ya tabbata maka (ويل لك), azaba ta tabbata a gare ka (ويل عليك),,, Kai ba komai ba ne, face mai tarayya da 'yan'uwansa cikin xinbin
masu tarayya, ko kuma mai cin gado daga cikin xinbin masu cin gado; Kana da
irin abinda suke da shi, kuma akanka akwai abinda ya xoru akansu,,,
Sai ka kiyaye dokokin
Mahaliccinka gabanin qasqanci da halaka su sauka a kanka,,,
Ka kuma xauki lamari da
linzaminsa da kuma tsarinsa, ,,,
Ka baiwa kowani mai haqqi
haqqinsa, da abinda ya cancanta
Kada kuma ka tsaya ko kayi
saivi ko jinkiri, ko sakaci, ,,,
Kuma kada ka jira, ko kayi
wasa, ,,, Saboda matsaloli ka iya bijirowa, ababen hanawa ka iya hanawa, ,,, Mutuwa
kuma tana zuwa kwatsam, ,,, Shi kuma Manzon shiriya (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"Ku raba
dukiya ga ma'abuta rabo cikin gado, akan tsarin da ya zo cikin littafin Allah, Duk
kuma abinda ya zama qari akan rabon masu rabo, to sai a miqa shi ga magaji
namiji wanda yafi kusanci da mamaci (daga cikin masu gado da nau'in da ake
kiransa: ta'asibi)" Muslim ya ruwaito shi.
Ya rabauta, wanda ya yi gaggawa zuwa aiki da daidai,
Tavewa kuma tana tabbata ga wanda amsa tambaya ta vuya a gare shi. Kuma tsira tana
tabbata ne kawai ga wanda ya tuba, ya nemi gafara, ya koma ga Allah! Kuma duk
wanda ya tuba ya mayar da lamuransa ga Allah, to lallai Allah shine Mai yawan
gafara Mai yawan karvar tuba.
Ina faxan abinda kuke
sauraro, kuma ina neman gafarar Allah, kuma sai ku nemi gafararSa; lallai shi
ya kasance ga Masu komawa gare shi Mai
yin gafara.
HUXUBA
TA BIYU
Godiya ta tabbata ga Allah
wanda ya fakar da Mutumin da ya nemi fakewa ga tausasawarSa. Kuma ina shaidawa
babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokin tarayya;
wanda ya bada waraka cikin ni'imarSa ga wanda ya xebe tsammanin samun waraka
daga cutarsa. Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu
bawansa ne kuma manzonsa, Salatin Allah da sallamarsa su qara tabbata a gare
shi, da iyalansa da sahabbansa, ma'adanan bin dokokin Allah, kuma
mavuvvugar kwanciyar hankali (da zaman
lafiya). Salatin da yake wanzuwa, da kuma sallamar da ba ta qarewa.
Bayana haka:
Ya ku Musulmai!!
Ku bi dokokin Allah; saboda
taqawar Allah itace mafi girman abin nema, kuma yin xa'a a gare shi shine mafi
xaukakar nasaba, "Ya ku waxanda suka yi Imani ku bi dokokin Allah iyakar
taqawarsa, kuma kada ku mutu face kuna musulmai" [Ali-imraan: 102].
Ya wanda ya ajiye mallakin da
aka killace su don Allah (na Bubusi), da dukiyar waqafai, da kuma ababen da
suke kawowa na riba, ,,,
Ya wanda ke jivintar
rabiyar sadakoki da dukiyar zakka da kayan da aka mutu aka bari, da dukiyoyi,
,,,
Ya wanda wata (mai kwanaki
30) bayan wani watan ke shuxewa, da wani lokaci na zamani, alhalin wannan
dukiyar tana cikin mulkinsa da damqarsa, kuma tana qarqashin kulawarsa, ,,,
A saboda me, kake riqe da dukiyar
a hannunka; kake wanzar da ita?
Ka rarraba dukiyar a wannan
yinin, ga waxanda suka cancance ta, idan ka kasance kana tsoron Allah, kuma kana
bin dokokinSa, saboda Kai za a tsayar da
kai a gaban Allah, kuma Mai haxuwa ne da shi,,,
Ka sanya sunnar Annabi (صلى الله عليه وسلم) –wacce zamu Ambato, a nan- ta zame maka
fitila kuma ginshiqi; domin an ruwaito daga Uqbah xan Alharis (رضي الله عنه) yace:
"Na yi
sallah a bayan Annabi (صلى الله عليه وسلم) a garin Madina, sallar la'asar, Sai ya
sallame, sa'an nan ya tashi cikin sauri, ya tsallake wuyan Mutane, zuwa xakin
sashin matanSa, Sai mutane suka tsorata da saurin da yayi, Sa'an nan ya fito
zuwa gare su, sai ya ga cewa sun yi mamakin irin saurin fitansa, sai yace: NA
TUNA WANI ZINARI NE (تبر) WANDA KE WURINMU DAGA CIKIN DUKIYAR
ZAKKA, sai na ji tsoron ya hana ni tsira, sai na yi umurnin a rarraba shi", Bukhariy ya ruwaito
shi [lamba: 1430].
A wata riwayar ta Bukhariy
"Na kasance na bar wani TIBRU a cikin gida daga cikin dukiyar
zakka, Sai na qi yay a kwana a wuri na".
Shi kuma TIBRU yanki ne na
zinari ko azurfa.
An ruwaito daga A'isha (رضي الله عنها) Tace:
"Jinyar Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) tayi
tsanani, alhalin a wurinsa akwai dinari guda bakwai, ko tara, Sai ya ce: Ya ke
A'isha? Ina labarin waxannan zinarin? Sai na ce: Suna wurina!, Sai ya ce: Ki yi
sadaka da su, Sai ta ce: Sai na shagalta da kula da lafiyarSa, Sa'an nan ya ce:
Ya A'isha! Ina labarin waxannan zinarin? Sai na ce: Suna wurina, Sai ya ce: Ki
zo min da su, Sai ta ce: Sai n azo da su, sai na sanya su cikin tafin hannunsa,
Sa'an nan ya ce: Menene zaton Muhammadu, da ya haxu da Allah, alhalin wannan
dukiyar tana wurinsa !", Ahmad ya ruwaito shi da Ibnu-Hibban.
Kuma an ruwaito daga
Ummu-salamah (رضي
الله عنها) ta ce:
"Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم)
ya shigo wurina, alhalin launin fiskarsa ya canza, sai na yi zaton hakan ya
kasance ne saboda wata jinyar da ke tare da shi, Sai nace: Yaya nake ganin
launin fiskarka ya canza? Sai ya ce: Saboda dinarori guda bakwai ne da suka zo
mana jiya, sai bamu raba su ba. Ga shim un yi yammaci alhalin suna qarqashin
shunfuxi",
Ahmad ya ruwaito shi da Ibnu-Hibban.
Dinari guda bakwai ne fiskar Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) take canzawa saboda yini guda ya wuce,
bai yi rabiyarsu ba; Sai ku ki bi
dokokin Allah –Ya ku Musulmai-, kuma ku fiskanci abinda zai fi tseratar da
rayukanku, wanda kuma shine abinda zai fi nisanta ku daga jinkirta haqqi, kuma
shi yafi yardar da Ubangiji, sa'an nan yafi goge zunubi da wuri, ,,
Sai ku yi salati da sallama ga Ahmad Mai shiriya, Mai
kuma ceton Mutane gabaxaya; saboda duk Mutumin da yayi masa salati guda xaya,
Allah ta'alah zai yi masa guda goma,
Ya Allah! Ka yi salati da sallama ga bawanka
annabi Muhammadu, Kuma ya Allah ka qara yarda da khalfofinsa guda huxu Ma'abuta
sunna abar bi, da sauran Iyalan gidansa da sahabbai. Ka haxa tare da Mu, ya Mai
karimci, ya Mai baiwa.
Ya Allah! Ka xaukaka musulunci da
musulmai,
Ya Allah! Ka xaukaka musulunci da
musulmai,
Ya Allah! Ka xaukaka musulunci da
musulmai.
Kuma ka qasqantar da shirka
da mushirkai, kuma ka sanya wannan qasar cikin aminci da zaman lafiya, da
sauran qasashen musulmai, ya Ubangijin talikai.
Ya Allah! Ka tunkuxe mana; Mu da qasashen
musulmai, sharruka da yaquka, da fitintinu, Ya Mai karimci.
Ya Allah! Ka gaggauta kawo mafita da nasara da
kuma tabbatuwa da bada iko a bayan qasa, ga 'yan'uwanmu musulmai, waxanda ake
neman raunata su; wato: Ahlus Sunnah waljama'ati, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah! Ka
taimake su, akan maqiya addini da Sunnah, ya Mai karimci.
Ya Allah! Ka datar da shugabanmu majibinci
lamuranmu; mai hidimar harami guda biyu zuwa ga abinda kake so, kuma ka yarda.
Kuma ka yi masa jagoranci zuwa ga aiki da biyayya, da bin dokoki (taqawa). Kuma
ka datar da shi, da masu na'ibtarsa guda biyu zuwa ga abinda a cikinsa akwai
buwayar musulunci da xaukakarsa, da kuma gyaruwar musulmai, Ya Ubangijin
talikai.
Ya Allah! Ka tsarkake masallacin Qudus daga dauxar
Yahudawa,
Ya Allah! Ka tsarkake masallacin
Qudus daga dauxar Yahudawa,
Ya Allah! Ka tsarkake masallacin
Qudus daga dauxar Yahudawa.
Ya Allah! Ka bada lafiya ga marasa lafiyan
cikinmu, ka kawo afuwa ga waxanda aka jarrabe su, a cikinmu, ka fitar da
fursunoninmu, kuma ka yi rahama ga mamatanmu,ka taimake mu akan wanda yayi gaba
da mu .
Ya Allah! Kada ka kunya ta mu a gaban wani, kuma
kada ka sanya wa wani kafiri ya zama yana da wata dama ko ni'ima akanmu.
Ya Allah! Ka sanya addu'armu ta zama wace aka ji
ta, kiranmu kuma wanda aka amsa. Ya Mai karimci, Ya Mai girma, Ya Mai jin qai!
No comments:
Post a Comment