2016/04/12

HADISIN SIFAR SALLAH TUN DAGA ALWALA HAR ZUWA SALLAMEWA (حديث صفة الصلاة من الوضوء إلى التسليم)

حديث صفة الصلاة من الوضوء إلى التسليم
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: أَنَّ رَجُلًا دَخَلَ المَسْجِدَ، وَرَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ جَالِسٌ فِي نَاحِيَةِ المَسْجِدِ، فَصَلَّى ثُمَّ جَاءَ فَسَلَّمَ عَلَيْهِ، فَقَالَ لَهُ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «وَعَلَيْكَ السَّلاَمُ، ارْجِعْ فَصَلِّ فَإِنَّكَ لَمْ تُصَلِّ» فَرَجَعَ فَصَلَّى، ثُمَّ جَاءَ فَسَلَّمَ عَلَى رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَرَدَّ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ السَّلَامَ قَالَ: «ارْجِعْ فَصَلِّ فَإِنَّكَ لَمْ تُصَلِّ» فَرَجَعَ الرَّجُلُ فَصَلَّى كَمَا كَانَ صَلَّى، ثُمَّ جَاءَ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَسَلَّمَ عَلَيْهِ فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «وَعَلَيْكَ السَّلَامُ» ثُمَّ قَالَ: «ارْجِعْ فَصَلِّ فَإِنَّكَ لَمْ تُصَلِّ» حَتَّى فَعَلَ ذَلِكَ ثَلَاثَ مَرَّاتٍ. فَقَالَ الرَّجُلُ: وَالَّذِي بَعَثَكَ بِالْحَقِّ مَا أُحْسِنُ غَيْرَ هَذَا فعَلِّمْنِي، قَالَ: «إِذَا قُمْتَ إِلَى الصَّلاَةِ فَأَسْبِغِ الوُضُوءَ، ثُمَّ اسْتَقْبِلِ القِبْلَةَ فَكَبِّرْ، ثُمَّ اقْرَأْ بِمَا تَيَسَّرَ مَعَكَ مِنَ القُرْآنِ، ثُمَّ ارْكَعْ حَتَّى تَطْمَئِنَّ رَاكِعًا، ثُمَّ ارْفَعْ حَتَّى تَسْتَوِيَ قَائِمًا، ثُمَّ اسْجُدْ حَتَّى تَطْمَئِنَّ سَاجِدًا، ثُمَّ ارْفَعْ حَتَّى تَطْمَئِنَّ جَالِسًا، ثُمَّ اسْجُدْ حَتَّى تَطْمَئِنَّ سَاجِدًا، ثُمَّ ارْفَعْ حَتَّى تَطْمَئِنَّ جَالِسًا، ثُمَّ افْعَلْ ذَلِكَ فِي صَلاَتِكَ كُلِّهَا»([1]).
HADISIN SIFAR SALLAH TUN DAGA ALWALA HAR ZUWA SALLAMEWA
Daga Abu-Hurairah (r.a), Lallai Wani Mutum ya shiga masallaci, alhalin Manzon Allah (s.a.w) yana cikin wani vangare na masallacin, sai yayi salla, sa'annan ya zo ya yi sallama a gare shi, Sai Manzon Allah (s.a.w) ya ce masa: "WA ALAIKAS SALAM, Koma ka yi salla; kai baka yi salla ba, Sai ya koma ya yi sallah, Sannan ya zo yayi sallama wa Manzon Allah (s.a.w), Sai Manzon Allah (s.a.w) ya amsa masa sallama, sai kuma yace: Ka koma ka yi salla, lallai kai baka yi salla ba, Sai mutumin ya koma yayi salla kamar yadda yayi salla, Sa'annan ya zo zuwa ga Annabi (s.a.w) sai yayi sallama a gare shi, sai Manzon Allah (s.a.w) yace: WA ALAIKAS SALAM, Sai kuma yace: Koma ka yi salla, lallai kai baka yi salla ba", har sai da ya aikata haka, sau uku. Daga nan sai Mutumin yace: Na rantse da wanda ya turo ka da gaskiya, Ban iya wanda ta fi wannan kyau ba, Ka karantar da ni? Sai Manzon Allah (s.a.w) yace: "Idan ka tashi i zuwa ga sallah to ka kyautata alwala, sa'annan ka fiskanci alqibla, ka yi kabbara, Daga nan sai ka karanta abinda ya sauwaqa na alqur'ani, Sa'annan ka yi ruku'i har sai ka nitsu a cikin ruku'i, Sa'annan sai ka xago har sai ka daidaita a tsaye, Sa'annan ka yi sujjada har sai ka nitsu cikin sujjada, Sa'annan sai ka xago har sai ka daidaita a zaune, Sa'annan ka yi sujjada har sai ka nitsu a cikin sujjada, Sa'annan sai ka xago har sai ka nitsu a zaune. Sa'annan sai ka aikata haka a cikin sallarka gabaxayanta", Bukhariy ya ruwaito shi (lamba:  757, da 793, da 6251, da 6667) da Muslim (lamba:  397).



([1]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba:  757, da 793, da 6251, da 6667 ), da Muslim (lamba:  397).  

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...