AKIDAR AHLUS SUNNA WAL JAMA'A KAN
SAHABBAI MASU KARIMCI – Allah ya kara yarda da su kuma ya yardad da su –
( KUDURIN AHLUS SUNNA KAN SAHABBAI)
(عقيدة أهل السنة والجماعة في الصحابة الكرام
y
وأرضاهم)
NA
Ash-sheikh
Abdul Muhsin bn Hamd Al-abba-d Albadr
Fassarar
Abubakar Hamza
Abubuwan da ke ciki;.
Dalilai
daga Qur'ani da Hadisi
kan Falalar Sahabbai da kuma
girman matsayinsu;………………………….
Sahabbai dukkansu Adalai ne; …………….
Akidar
Ahlus Sunna kan Sahabbai ( r a);
–
A dunkule -; ………………………………..
WASSU
DAGA CIKIN MAGANGANUN MAGABATA KAN SAHABBAI:
Maganan Al'Imamu'd 'Dahawiy; …………….
Maganan Ibn Abiy Zaid Al-kairawaniy; ……..
Maganan Imamu Ahmad; …………………..
Maganan Imam Abiy Usman As-sabuniy;..
Maganan Shekhul Islam Ibn Taimiyyata; ……..
Sukan Sahabbai Sukan Qur'ani da Hadisi ne;.
Sukan Sahabbai baya cutar da su, Cutuwan na
dawowa ne kan Wanda ya yi sukan;………
بسم الله الرحمن الرحيم
Gabatarwa
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Yabo da tsira da albarka su kara
tabbata ga Bawansa kuma Manzonsa Annabinmu Muhammadu, da kuma Iyalansa da
Sahabbansa.
Bayan haka:
Yana daga cikin rahamar Allah ga Bayinsa da kuma falalarsa akansu;
Tayarwansa da Manzon a cikinsu daga kayukansu, don ya isar da sakon
Ubangijinsu, ya kuma shiryad da su zuwa ga duk kana bin da zai amfanar da su,
ya kuma tsawatar da su kan duk abin da zai cutar da su, Hakika wannan Manzo ya
tsayu kana abin da aka turo shi da shi yadda ya kamata; ta yadda ya nusar da al'umarsa kan duk kan
alkhairi, ya kuma hane ta duk kan sharri, ya kuma yi nasiha iyaka nasiha. Hakika
Allah ya zabi Wassu Mutane don Abokantakansa da kuma kamar Shari'a daga
wajensa, wanda sun e mafifitan wannan al'ummar da ita ce Mafificiyar al'ummai,
Sai ya daukake su da abotar Annnabinsa ( s a w), Ya kuma kebe su – a rayuwar
Duniya – da yin dubi zuwa gare shi, da kuma sauraron maganansa daga Bakinsa
madaukaki, Wannan kuma falalar Allah ne da ke bada ita ga wanda ya ga dama,
Allah shi ne ma'abocin falala mai girma.
Dalilai
daga Al'qur'ani da Hadisai kan falalar Sahabbai da kuma girman matsayinsu
Hakika Sahabbai sun isar wa Manzon Allah ( s a w) abin da Allah ya turo
shi da shi na daga haske da shiriya akan mafificiyar Fuska, kuma cikakkiya( ta
yadda ya dace); Sai ya zamo su na da lada mai girma; saboda abotarsu da Manzon
Allah ( s a w) da kuma Jihadinsu tare da shi kuma don Allah, da kuma ayyukansu
masu girma wajen yada wannan Musuluncin, kuma su na da kwatankwacin Ladan
Wadanda su ka zo bayansu; saboda kasancewarsu 'Yan tsakani tsakaninsu da
tsakanin Manzon Allah ( s a w) Ai [duk wanda ya yi kira zuwa ga wata shiriya To
ya na da lada kwatankwacin ladan Wanda ya bi shi, ba tare da ya tawaye mu su
ladansu da komai ba] Muslim ne ya ruwaito a cikin Sahihinsa.
Hakika
Allah ya yabe su cikin Littafinsa mabuwayi, kuma Manzon Allah ( s a w) ya yaba
musu cikin Sunnarsa matsarkakiya, Wannan kuma ya ishe su Falala da Daukaka.
Allah ya na cewa:
﴿وَالسَّابِقُونَ الْأَوَّلُونَ مِنَ الْمُهَاجِرِينَ
وَالْأَنْصَارِ وَالَّذِينَ اتَّبَعُوهُمْ بِإِحْسَانٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا
عَنْهُ وَأَعَدَّ لَهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي تَحْتَهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا
أَبَدًا ذَلِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ﴾ (100)
Ma'ana:
"
Wadanda su ka yi rigaye na Farko daga cikin MUHAJIRINA (wadanda su ka yi
Hijira) da kuma ANSAAR (Mataimakan Manzon Allah s a w da kuma Wadanda su ka yi
hijira) da wanda su ka bi su da kyautatawa; Allah ya yarda da su kuma Suma sun
yarda da shi, kuma ya tanada mu su Aljannoni da koramai ke gudana a karkashinsu,
su na masu dawwama a cikinsu, Wannan shi ne Falala mai girma".
Allah Ma'daukaki ya ce:
﴿ مُحَمَّدٌ
رَسُولُ اللَّهِ وَالَّذِينَ مَعَهُ أَشِدَّاءُ عَلَى الْكُفَّارِ رُحَمَاءُ بَيْنَهُمْ
تَرَاهُمْ رُكَّعًا سُجَّدًا يَبْتَغُونَ فَضْلًا مِنَ اللَّهِ وَرِضْوَانًا سِيمَاهُمْ
فِي وُجُوهِهِمْ مِنْ أَثَرِ السُّجُودِ ذَلِكَ مَثَلُهُمْ فِي التَّوْرَاةِ وَمَثَلُهُمْ
فِي الْإِنْجِيلِ كَزَرْعٍ أَخْرَجَ شَطْأَهُ فَآَزَرَهُ فَاسْتَغْلَظَ فَاسْتَوَى
عَلَى سُوقِهِ يُعْجِبُ الزُّرَّاعَ لِيَغِيظَ بِهِمُ الْكُفَّارَ وَعَدَ اللَّهُ الَّذِينَ
آَمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ مِنْهُمْ مَغْفِرَةً وَأَجْرًا عَظِيمًا﴾ (29)
Ma'ana:
" Muhammadu Manzon Allah ne, Wanda ke tare da shi kuma Masu tsanani
ne akan Kafirai, Masu rahama a tsakaninsu, zaka gansu suna masu Ruku'I,
Sujjada, Suna neman Falala daga Ubangijinsu da kuma Yarda, Alamarsu na fuskarsu
na gurbin Sujjada, Wannan shi ne misalinsu cikin At taura, Misalinsu kuma cikin
Injila: Kamar Shuka ne day a fitar da tofonsa na farko sannan yayi karfi ya
kuma yi kauri, ya daidaita kan Kafafunsa, yana burge Manoma don ( Allah) ya
bakanta wa kafirai da su, (Wannan shi ne misalinsu cikin Injila) Allah yayi
alkawari ga wadanda su ka yi Imani kuma suka yi aiki na kwarai da wata Irin
gafara da kuma lada mai girma".
Cikin Fadinsa – mai girma da daukaka – kan Sahabbai masu karamci
) ليَغيظَ بهمُ الكفارَ(
" Don Allah ya bakanta wa Kafirai da su"; Akwai; Hukunci mai
hatsari, da kashedi mafi girma, da kuma Narkon ( Azaba) mai tsanani da radadi
ga Mutumin da Sahabbai Manzon Allah (s a w) su ke bakanta ma sa zuciya, ko ya
zama a zuciyarsa akwai Hassada a kansu.
Allah
Ma'daukaki ya ce:
﴿ لا يَسْتَوِي
مِنْكُمْ مَنْ أَنْفَقَ مِنْ قَبْلِ الْفَتْحِ وَقَاتَلَ أُولَئِكَ أَعْظَمُ دَرَجَةً
مِنَ الَّذِينَ أَنْفَقُوا مِنْ بَعْدُ وَقَاتَلُوا وَكُلًّا وَعَدَ اللَّهُ الْحُسْنَى
وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ﴾ (10)
Ma'ana:
Baza
su yi dadai ba daga cikinku: Wandanda su ka ciyar kafin FATH ( Sulhul
Hudaibiyya da ya auku a shekara ta shida) kuma su ka yi Yaki, Wadannan Sun fi
girman daraja fiye da Wadanda su ka
ciyar bayansa kuma su ka yi Yaki, Amma dukkansu Allah ya musu alkawarin
Aljanna, Kuma Allah dangane da abin da ku ke aikatawa; Mai bada Labari
ne".
Allah
Ma'daukaki ya ce:
وقال تعالى في بيان
مصارف الفيء: ﴿ لِلْفُقَرَاءِ الْمُهَاجِرِينَ الَّذِينَ أُخْرِجُوا مِنْ دِيَارِهِمْ
وَأَمْوَالِهِمْ يَبْتَغُونَ فَضْلًا مِنَ اللَّهِ وَرِضْوَانًا وَيَنْصُرُونَ اللَّهَ
وَرَسُولَهُ أُولَئِكَ هُمُ الصَّادِقُونَ * وَالَّذِينَ تَبَوَّءُوا الدَّارَ وَالْإِيمَانَ
مِنْ قَبْلِهِمْ يُحِبُّونَ مَنْ هَاجَرَ إِلَيْهِمْ وَلَا يَجِدُونَ فِي صُدُورِهِمْ
حَاجَةً مِمَّا أُوتُوا وَيُؤْثِرُونَ عَلَى أَنْفُسِهِمْ وَلَوْ كَانَ بِهِمْ خَصَاصَةٌ
وَمَنْ يُوقَ شُحَّ نَفْسِهِ فَأُولَئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ * وَالَّذِينَ جَاءُوا مِنْ بَعْدِهِمْ يَقُولُونَ
رَبَّنَا اغْفِرْ لَنَا وَلِإِخْوَانِنَا الَّذِينَ سَبَقُونَا بِالْإِيمَانِ وَلَا
تَجْعَلْ فِي قُلُوبِنَا غِلًّا لِلَّذِينَ آَمَنُوا رَبَّنَا إِنَّكَ رَءُوفٌ رَحِيمٌ﴾ (8-10)
Allah ya ce yana
mai bayanin Wadanda su ka cancanci Alfai'u ( Ma'ana: Dukiyar da kafiran yaki su
ka gudu su ka bari ba tare da an gwabza da su ba)
ya ce:
(Shi
wannan dukiyan) " Na Wadannan talakawa masu Kauran da aka fitar da su daga
Gidaddajinsu da Dukiyoyinsu Suna masu neman Falala daga Ubangijinsu da kuma
yardam Suna masu taimakon Allah da Manzonsa, Wadannan su ne Masu Gaskiya * Da
Wadanda suka Tanadi Gida da Imani kafinsu, Su ke son Wanda ya yi Hijira zuwa
gare su, Kuma bas a jin Hassada cikin Zuciyan kan abin da su ka bayar, Kuma
suna fifita (waninsu) akan kansu koda kuwa suna da bukata, ( Ai) Duk wanda aka
kare shi daga Rowan kansa To Wadannan Su ne suka rabauta * da wadanda su ka zo
bayansu su ke cewa: Ya Ubangijinmu ka gafarta mana (mu) da 'Yan' uwanmu da su
ka rigaye mu da Imani, Kuma kada ka sanya hassadan wadanda su ka yi Imani cikin
Zuciyarmu, Ya Ubangijinmu Lallai kai mai tausayi ne mai rahama".
Wadannan Ayoyi uku ne daga Suratul Hashr; Ta farko daga cikinsu tana
Magana kan Al Muhajirun (Wadanda suka yi hijira daga Makka zuwa Madina don
taimakon Musulunci da Manzon Allah, su ka bar Dukiyansu da Iyalensu), Ta biyun
kuma kan ANSAAR (wato: Mataimaka 'Yan Madina da su ka tarbi sannan su ka sauki
wadanda su ka yi hijira tare da Manzon Allah), Ta ukun kuma; Kan Wadanda su ka
zo bayan Al-Muhajirun da Ansar su na masu nema musu gafara; masu rokon Allah kar
ya sanya hassadar Wadanda su ka yi Imani cikin zuciyarsu. Bayan Wadannan kaso uku kuma ba wani abu sai
tabewa, da kuma fadawa Tarkon Shedan. Shi ya sa A'isha ( r a) ta ce wa Urwatu bn
Zubairin dangane da wadannan tababbun:
((
أُمِروا أن يستغفروا لأصحاب رسول اللهr فسبـّوهم))
Ma'ana:
" An umurce su da su nemi gafara ga Sahabban Manzon Allah ( s a w)
Sai su ka zage su" Muslim ne ya ruwaito a karshe - karshen Sahihinsa.
Nawawiy ya ce – a sharhinsa – bayan ya ambaci ayan Hashr –ma'ana: ayan
karshe cikin ukun da su ka gabata:
" Da wannan ne Malik ya kafa hujja
cewa: Babu rabo cikin Fai'u (dukiyar da aka samu ba tare da an zubar da jinni
ba saboda tsoratar Kafirai da guduwarsu) babu rabo ga Mutumin day a zagi
Sahabbai ( Allah ya kara yarda da su); saboda Allah ya sanya shi ne kawai ga
Mutumin day a zo bayansu daga cikin masu nema musu gafara".
Ibn kasir – Allah ya yi masa rahama – a tafsirinsa ga ayar ace:
" Abin da Imamu malik ya cira daga
Wannan aya mai madaukakiya na cewa: 'Dan Shi'a da ke zagin Sahabbai ba shi da
rabo cikin Fai'u saboda; Bai rashin Siffantuwansa da abin da Allah ya yaba wa
Wadannan da shi cikin Fadinsa:
)يَقُولُونَ رَبَّنَا اغْفِرْ لَنَا وَلِإِخْوَانِنَا الَّذِينَ
سَبَقُونَا بِالْإِيمَانِ وَلَا تَجْعَلْ فِي قُلُوبِنَا غِلًّا لِلَّذِينَ آَمَنُوا
رَبَّنَا إِنَّكَ رَءُوفٌ رَحِيمٌ (10) (
" Su ke cewa: Ya Ubangijinmu ka gafarta mana (mu) da 'Yan 'uwanmu
da su ka rigaye mu da Imani, Kuma kada ka sanya hassadan wadanda su ka yi Imani
cikin Zuciyarmu, Ya Ubangijinmu Lallai kai mai tausayi ne mai rahama".
Manzon Allah ( s a w) ya ce:
[خيرُ الناسِ قرْني، ثم الذين
يلُونهم، ثم الذين يلُونهم ]
Ma'ana: [ Mafi alherin Mutane su ne Karni na,
Sannan sai Wadanda ke biye da su, Sannan sai Wadanda ke biye da su ], Bukhari
da Muslim da wassunsu su ka ruwaito shi daga hadisin Imrana bn Husaini da
Abdullahi bn Mas'udin (Radiyal Lahu anhuma). Kuma Muslim ya ruwaito daga
Hadisin Abu Hurairata ( Allah ya kara masa yarda) da Lafazin:
[ خير أمتي القرن الذي بعثت فيهم، ثم الذين
يلونهم، ثم الذين يلونهم]، والله أعلم ذكر الثالث أم لا.
Kuma Muslim ya sa ke ruwaito shi daga Hadisin A'isha ( Allah ya kara
mata yarda), ta ce: " Wani Mutum ya tambayi Annabi ( s a w) Wadan ne
Mutane su ka fi alkhairi? Sai ya ce:
[ القرن الذي أنا فيه، ثم الثاني، ثم الثالث]
Ma'ana:
[
Karnin da Ni na ke ciki, Sai kuma na biyu, Sai na uku].
Ya zo cikin Bukhari da Muslim daga Abu Sa'id
Alkuduriy ( r a) ya ce: Manzon Allah ( s a w) ya ce:
[
يأتي على الناس زمانٌ فيغزوا فئامٌ من الناس فيقال: هل فيكم من صاحب رسول الله r؟ فيقولون: نعم؛ فيفتح لهم، ثم يأتي على الناس زمان فيغزو فئام من الناس
فيقال: هل فيكم من صاحَب أصحابَ رسولِ الله r؟
فيقولون: نعم؛ فيفتح لهم، ثم يأتي على الناس زمان فيغزو فئام من الناس فيقال: هل فيكم
من صاحب من صاحب أصحاب رسول الله r؟ فيقولون: نعم؛ فيفتح لهم]
Ma'ana:
" Wani Lokaci zai zo wa Mutane, Sai
Wassu Jama'a daga Mutane su je yaki, Sai a ce musu; Shin cikinku akwai Wanda ya
Aboci Manzon Allah ( s a w)? Sai su ce: E; Sai a musu Budi ( su ci nasara),
Sannan wani lokaci zai zo wa Mutane, Sai Wassu Jama'a daga cikin Mutane su yi
yaki, sai a ce musu; Shin cikinku akwai Wanda ya Aboci Wanda ya Aboci Manzon
Allah ( s a w)?, Sai su ce: E; Sai kuwa a yi musu budi, Sannan Wani lokaci zai
zo wa Mutane, sai Wassu Jama'a daga cikin Mutane su tafi Yaki, sai a ce musu;
Shin a cikinku akwai Wanda ya Aboci Wanda ya Aboci Wanda ya aboci Manzon Allah
( s a w)? Sai Su ce, E; Sai kuwa a yi musu budin"
Ibn Badda ya ruwaito da Inganceccen Sanadi – kamar
yadda ya zo cikin Minhajus Sunna na Ibn Taimiyya – daga Ibn Abbasin ( r anhuma)
Lalle shi ya ce:
(( لا تسبّوا أصحاب محمدٍ r فلمقامُ
أحدهم ساعةً ـ يعني: مع رسول الله صلى الله صلى الله – خيرٌ من عمل أحدِكم أربعين
سنةً)) وفي رواية وكيعٍ: (( خيرٌ من عمل
أحدِكم عمره)).
Ma'ana:
" Kada ku zagi Sahabban ( Annabi)
Muhammadu ( s a w); don tsayuwan Dayansu 'dan wani Lokaci – yana nufin:
Tare da Manzon Allah ( s a w) – Ya fi alkhairi fiye da aikin 'Dayanku
shekara arba'in" a riwayar Waki'u kuma: " Ya fi aikin 'Dayanku
rayuwarsa".
Yayin da Sa'id bn Zaid ( r a) Ya ambaci Mutum
goma (10) da aka musu albishir da Aljanna Sai ya ce:
(( والله لمشهد رجلٍ منهم مع رسول الله r يغبر
فيه وجهُه خيرٌ من عمل أحدكم ولو عُمّر عُمْرَ نوحٍ))
Ma'ana:
"
Wallahi! Halartan 'Daya daga cikinsu Yaki tare da Manzon Allah ( s a w) wanda Fiskarsa
zai yi kura ciknsa To ya fi aikin 'Dayanku koda an rayar da shi kwatankwacin
rayuwar Nuh ( a s) " Abu Da'uda da Tirmiziy ne su ka ruwaito shi.
An samo daga Jabir ( r a) Ya ce: an ce wa
A'isha;
(( إنّ أناساً يتناولون أصحاب النبيّ r حتى أبا
بكرٍ وعمر؛ فقالت: " ما تعجبون من هذا؟ انقطع عنهم العملُ فأحبّ اللهُ أنْ لا
ينقطع عنهم الأجر))
Ma'ana:
" Lalle Wassu Mutane su na Magana kan
Sahabban Annabi (s a w); kai har kan Abubakar da Umar, Sai t ace: Me ku ke
mamaki daga wannan? Aiki ya yanke musu Sai Allah kuma ya so kar lada ya yanke
musu" Ibn Asir ya ambato shi cikin Jami'ul Usul.
Abin da ke kara fito da wannan fili kuwa Fadin
Manzon Allah ( s a w) cikin Inganceccen Hadisi:
[ إنّ المُفْلِس من أمّتي يأتي يومَ القيامة بصلاةٍ، وصيامٍ،
وزكاةٍ، ويأتي وقد شتم هذا، وقذف هذا، وأكل مال هذا، وسفك دم هذا، وضرب هذا، فيعطى
هذا من حسناته، وهذا من حسناته، فإنْ فنيتْ حسناتُه قبل أنْ يقضي ما عليه أُخذ من
خطاياهم فطُرحتْ عليه ثم طُرح في النار]
Ma'ana:
" …Ai fallasheshshe kam daga al'ummata
Shi ne Wanda zai zo ranar kiyama da Salla, da Azumi, da Zakka, Sai ya zo alhali
ya zagi Wannan, ya yi kazafi ma Wannan, ya ci dukiyan Wannan, ya zubar
da Jinin Wannan, ya doki Wannan, Sai a bawa Wannan daga kyawawansa, Wannan daga
kyawawansa, Idan kyawawan nasa su ka kare kafin y agama biyan abin da ke kansa;
Sai a dauki kurakurensu sai a dora a kansa, Sannan a jefa shi cikin Wuta"
Kuma Bukhari ya ruwaito a cikin sahihinsa daga
Abu sa'id Al khudriy ( r a) Lalle shi ya ce: Manzon Allah ( s a w) ya ce:
[ لا
تسبُّوا أصحابي فلوْ أنّ أحدكم أنفق مثل أحدٍ ذهباً ما بلغ مُدّ أحدهم ولا نصِيْفَهُ]
Ma'ana:
" Kada ku zagi Sahabbaina! Da 'Daya daga
cikinku zai ciyar da kwatankwacin ( Dutsen) Uhdu da zinari To da bai kai Mudun
'Dayansu ba; koma rabi"
Muslim kuma ya rawito cikin Sahihinsa daga Abu
Hurairata ( r a) Lallai ya ce: Manzon Allah ( s a w) ya ce:
[ لا تسبُّوا أصحابي؛ فو الذي نفسي بيده لو
أنفق أحدكم مثل أحدٍ ذهباً ما أدرك مُدّ أحدهم ولا نصيفه]
Ma'ana:
" Kada ku zagi Sahabbaina; Na fa rantse
da Wanda Raina ya ke hanunsa Da 'Dayanku zai ciyar da Kwatankwacin ( Dutsen)
Uhdu na Zinari, To da bai riski Mudun 'Dayansu ba, koma rabi".
Haka kuma ya ruwaito shi daga Hadisin Abiy
Sa'idin (din), Lafazinsa:
((
كان بين خالد بنِ الوليد
وبين
عبد الرحمن بن عوفٍ شيءٌ؛ فسبّه خالدٌ؛ فقال رسول الله r:
[لا تسبّوا أحداً من أصحابي؛ فإنّ أحدكم لو أنفق مثل أحدٍ ذهباً ما أدرك مُدّ
أحدهم ولا نصيفه]
Ma'ana:
" Wani abu ya kasance a tsakanin Khalid
bn Walid da Abdurrahman bn Auf; Sai khalid ya zage shi, Sai Annabi ya ce: Kada
ku zagi 'Daya daga cikin Sahabbaina! Domin 'Dayanku da zai ciyar da kamar (
Dutsen) Uhd na zinari, To da bai riski Mudun 'Dayansu ba, koma rabi".
To kaga kuwa! Idan Takobin Allah Khalidu bnul Walid
(سيف الله!) da Wassunsa Wadanda su ka
Musulunta bayan; HUDAIBIYYA Aikinsu da yawa ba zai zo dadai da Kadan daga
Abdurrahman bn Auf da Wassunsa Wadanda Musuluncinsu ya gabata ba – Tare da
cewa: Duk kan su Sun 'Daukaku ([1])
da Abotar Annabi ( s a w) - To kaga yaya
In an kwatanta Wanda bai samu 'Daukakar Abotan ba da Wadancan Mutanen kirki!? (
Sahabban Manzon Allah!) Lallai fa banbancin da ke tsakaninsu ba kusa ba!, kuma
tafiyar nesa take!!; Don Wutsiyar Rakumi ta yi nesa da Raba!!! Kamar yadda Sama
ta bakwai ta ke nesa da Kasa ta bakwai, Wannan kuma Falalan Allah ne da ke
bayar da ita ga Wanda ya nufa, Allah Shi ne Ma'abocin Falala Mai Girma.
WADANNAN SU NE SASHIN AYOYIN QUR'ANI DA
HADISAN ANNABI MA SU NUNI KAN FALALAN WADANCAN MUTANEN KIRKI, WANDA BA A YI
IRINSU BA ( A BAYA; IN KA TOGE; ANNABAWA) KUMA BA ZA A YI IRINSU BA, ALLAH YA
KARA YARDA DA SU.
Sahabbai
dukkansu Adalai ne
Sahabban
Manzon Allah ( s a w) duk kan su adalai ne; Saboda Allah ya Adaltar da su, haka
kuma yabon Manzon Allah ( s a w) day a yi akansu.
Nawawiy
ya ce: - a cikin TAKRIBIN DA SUYUDIY YA YI MASA SHARHI DA TADRIBUR RAWIY –
(( الصحابة كلهم عدولٌ، من
لابس الفتن وغيرُهم بإجماع من يُعتدّ بقوله))
Ma'ana:
" sahabbai duk kan su adalai ne,
Wanda ya yi fada daga cikinsu da Sauran, da IJMA'IN duk Wanda a ke lura da
maganansa".
Al
hafiz Ibn hajar ya ce – a cikin Isaba - :
(( اتفق أهلُ السنة على أنّ الجميع عدولٌ، ولم يخالف في ذلك إلا
شذوذٌ من المبتدعة))
Ma'ana:
" Ahlus Sunna sun hadu kan kasancewar Dukkan ( Sahabbai) Adalai ne,
Ba Wanda ya saba kan haka sai Wassu kadan daga cikin 'Yan bidi'a".
Don haka ne ma Rashin Sahabi a cikin jerin
Maruwaita ba ya cutar da Ingancin Hadisin; Idan Tabi'I ya ce:
(( عن رجلٍ صحب النبيّ r))
Ma'ana: Ya ji Hadisin daga Wani Mutum da ya yi
Abota da Annabi ( s a w) To hakan ba zai cutar da Hadisin day a ruwaito ba
wajen hana masa Inganci; saboda Jahiltar Wanene ( ya ruwaito shi) daa cikin
Sahabbai bay a cutarwa; saboda Dukkansu Adalai ne.
Shi ya sa
Khadibul bagdadi ya ke cewa a cikin Littafinsa ( Alkifayat):
(( كلُّ حديثٍ اتصل إسنادُه بين من رواه وبين النبي r لم يَلْزم العمل به إلا بعد ثبوت عدالة
رجاله، ويجب النظرُ في أحوالهم سوى الصحابي الذي رفعَهُ إلى رسول الله r؛ لأن عدالة الصحابة ثابتةٌ معلومةٌ بتعديل
الله لهم، وإخبارُه عن طهارتهم، واختيارُه لهم في نصِّ القرآن)).
Ma'ana:
"Dukkan
Hadisin da Sanadinsa ( ma'ana: Jerin Mutanen da Su ka ruwaito shi Tun daga
Malami mai Littafi
har zuwa Annabi) ya sadu daga Wanda ya ruwaito shi har zuwa ga Annabi ( s a w)
To aiki da shi bai zama wajibi ba har sai bayan Tabbatuwan Adalcin Maruwaitansa,
kuma Wajibi ne a yi nazari kan Adalcinsu, ( Amma) banda Sahabin (da ya Jingina)
shi zuwa ga Manzon Allah ya kuma 'Daga shi zuwa gare shi; saboda Adalcin Sahabbai tabbacecce ne sananne; saboda Adaltar
da su da Allah ya yi, da kuma bada labarinsa kan tsarkinsu da ya yi, da kuma
zabansu da ya yi cikin Nassin Qur'ani)).
Sannan ya koro Ayoyi da Hadisai kan falalarsu,
sannan ya ce:
((على أنه لو لم يَرِدْ
من الله عزّ وجلّ ورسولِه فيهم شيءٌ مما ذكرناه لأوجبت الحالُ التي كانوا عليها من
الهجرة، والجهاد، والنصرة، وبذل المهجِ والأموال، وقتْلِ الآباءِ والأولاد،
والمناصحةِ في الدين، وقوّة الإيمان واليقين، = القطعَ على عدالتِهم، والاعتقادَ
لنـزاهتِهم، وأنهم أفضل من جميع المعدّلِين والمزكِّين؛ الذين يجِـيؤن من بعدهم أبدَ
الآبدين))
Ma'ana:
" ( kai!) Da abubuwan da mu ka ambata daga Allah mai girma da
'Daukaka da kuma manzonsa bai zo ba Kan ( yaba musu) To da halin da su ka
kasance a cikinsa na Hijira, da Jihadi, da Taimako, da bada Kai, da Dukiya, da
kasha Iyaye da Yara, da Nasiha wa juna cikin wannan addinin, da Karfin Imani da
Yakini, = ( da halin nan) ya sanya = Yankewa (cikin Zuci) kan adalcinsu, da
kuma kudurta Tsarkakuwansu …da kuma cewa su: Sun fi dukkan masu Adaltarwan da
masu bada Tazkiyyar ( ma'ana: masu cewa: Wane! Mutumin kirki ne, Tsarkakekke
ne) da su ke zuwa bayansu har abadin abadaye".
Sannan ya ruwaito da sanadinsa daga Abu
Zur'ata, Lallai shi ya ce:
((إذا رأيتَ الرجُلَ ينتقص
أحداً من أصحاب رسول الله r
فاعلمْ أنه زِنديقٌ؛ وذلك أنَّ الرسول r
عندنا حقٌّ، والقرآنَ حقٌّ، وإنما أدّى إلينا هذا القرآنَ والسننَ أصحابُ رسولِ
الله r،
وإنما يريدون أن يجرحوا شهودنا ليبطلوا الكتاب والسنة، والجرْح بهم أولى، وهم
زنادقة)).
Ma'ana:
" Idan kaga Mutum ya na ( taba) taba 'Daya daga cikin
Sahabban Manzon Allah da nakasa; To ka sani Lallai shi Zindiki ne ( ma'ana:
Munafiki); saboda Mu Manzon Allah a wajenmu gaskiya ne, kuma Qur'ani ma gaskiya
ne, kuma (ka sani) Wanda kawai ya kawo mana Wannan Qur'anin da Wadannan
Sunnonin su ne Sahabban Manzon Allah ( s a w), ( Sannan su kuma) abin da kawai
su ke nufi shi ne su soki SHAIDUNMU don su bata Littafi (Alqur'ani) da Sunnah,
To sukansu (su) shi ya fi, kuma su Zindikai ne (Munafukai).
Dunkulen
Akidar Ahlus-sunna Wal-Jama'a kan Sahabbai ( Allah ya kara yarda da su)
Mazhabar
Ahlus Sunna wal Jama'a kansu (Sahabbai) na tsakanin Geffa biyu na ( إفراط) ( ma'ana: Wuce Gona da iri) da kuma ( تفريط) ( ma'ana: Gajertawa wajen basu Hakkokinsu), (
kenan) na Tsakanin Wadanda ke wuce iyaka da Su ke 'Daga Wadanda su ke girmamawa
daga cikinsu zuwa ga abin da baya dacewa sai ga Allah ko kuma Manzanninsa,= da
kuma tsakanin Wadanda su ke gajartawa masu kin bada hakki wadanda su ke siffanta
su da nakasa su kuma zage su, Su Ahlus Sunnah na tsakanin Wa'dannan da
Wa'dannan ( الجفاة والغلاة), Su na son Sahabbai gaba 'daya, Sannan su
na ajiye su a matsaya da ta dace da su da adalci, (don haka) ba sa daga su zuwa
ga abin da basu cancanshi ba, kamar yadda kuma ba sa gajartawa kan abin da ya
dace da su, Harasunsu su na nan 'Danye da ambaton kyawansu da ya dace da su,
Zukatansu kuma suna raye da sonsu.
Amma abin daya inganta na abin da ya faru a tsakaninsu To su dinnan
MUJTAHIDAI ne ( masu kokarin neman gaskiya); Don haka ko su dace; sai ya zama
su na da ladan kokari, da kuma ladan dacewa, Ko su kuskure; Sai ya zamo su na
da ladan kokarinsu, Kuskurensu kuma an gafarta musu, Su kuma dama ba MA'ASUMAI
ba ne ( kamar Annabawa) ( A'a!) Su Mutane ne su na dacewa, sannan su na
kuskure; amma kayi mamakin yawan dacewansu in an kwatanta da na Wassunsu!,
Sannan ka yi mamakin karancin kuskurensu idan a ka kwatanta da kurakuren
Wassunsu!!, Sannan Su na da wani gafara da yarda daga Ubangijinsu!!!
Littatafan Ahlus Sunna cike su ke da bayanin Wannan tacecciyar Akida
kuma kuma kubucecciya kan hakkin Wadannan zababbu daga Mutane don Abotar
Shugaban Mutane ( s a w), Su kuma Allah ya kara musu yarda gaba daya.
Daga;
Zancen Malaman Ahlus- Sunna kan Sahabbai
1.
Daga cikin haka; Fadin dahawiy cikin Akidar
Ahlus sunna:
((ونحبُّ أصحابَ رسول الله r ،ولا نُفْرِطُ في حبّ أحدٍ منهم، ولا نتبرّأ
منهم، ونُبْغِض من يُبغِضهم، وبغير الخير يذكُرهم، ولا نذكُرهم إلا بخيرٍ، وحبُّهم
دينٌ وإيمانٌ وإحسانٌ، وبغضُهم كفرٌ ونفاقٌ وطغيانٌ)).
Ma'ana: "
Muna son Sahabban Manzon Allah ( S A W), kuma wuce Gona-da-iri cikin son Wani
daga cikinsu, kuma bama barranta daga
Wani daga cikinsu, kuma Mu na kin mai kinsu,
Mai ambatonsu ba da alkhairi ba, Ba ma kuma ambatonsu sai da
alkhairi, kuma son su Addini ne da Imani
da Ihsan, kinsu kuma Kafirci ne da Munafurci da ketare Iyaka".
2.
Fadin Ibn Abiy Zaid Alkairawaniy:
Ibn Abiy Zaid Alkairawaniy Ba- Malike ya fada
cikin Mukaddiman (gabatarwar) RISALARSA shahararriya, alhalin yana bayyana
akidar Ahlus Sunna:
(( وأنّ خيرَ القرونِ الذين رأَوا رسولَ الله
r،
وأفضلُ الصحابة؛ الخلفاءُ الرشدون المهديون: أبو بكر ثم عمر ثم عثمان ثم علي y أجمعين، وأنْ لا يُذْكرَ أحدٌ من صحابة رسول
الله r
إلا بأحسنِ ذكرٍ، والإمساك عن ما شجَر بينهم، وأنهم أحقّ الناس أنْ يُلتمس لهم
أحسنُ المخارج، ويُظنَّ بهم أحسنُ المذاهب))
Ma'ana:
" Kuma mafi alherin karni; Su ne Wadanda
su ka ga Manzon Allah ( s a w), Kuma Mafificin Sahabbai; Khalifofo shiryeyyu,
masu shiryarwa: Abubakar, sannan Umar, sannan Uthman, sannan Aliyu ( Allah ya kara yarda da su gaba dayansu), Kuma kada a
ambaci 'Daya daga Sahabban Manzon Allah ( s a w) Sai da mafi kyan ambato, Da
kuma kamewa kan abin da ya faru a tsakaninsu, Kuma su ne mafi cancantan Mutane
da a nema musu mafi kyan mafita, a kuma zata musu mafi kyan MAZHABOBI".
3.
Fadin Imamu Ahmad cikin Littafin ( AS SUNNAH):
(( ومن السنة: ذكرُ
محاسنِ أصحاب رسول الله r
كلِّهم أجمعين، والكفُّ عن الذي جرى بينهم؛ فمنْ سبّ أصحابَ رسول الله r أو واحداً منهم فهو مبتدعٌ رافضيٌّ، حبُّهم
سنةٌ، والدعاءُ لهم قربةٌ، والاقتداءُ بهم وسيلةٌ، والأخذُ بآثارهم فضيلةٌ)).
Ma'ana:
" Yana daga cikin Sunna; Ambaton kyawawan
Sahabban Manzon Allah ( s a w) dukkansu gaba 'dayansu, Da kuma kamewa kan abin
da ya gudana a tsakaninsu; Don Duk Wanda ya zagi Sahabban Manzon Allah ( s a w)
ko 'Daya daga cikinsu To 'Dan bidi'a ne, 'Dan Shi'a. Son su Sunna ne, Yi musu
addu'a kuma Kusantar Ubangiji ne, Koyi da su kuma tafarki ne da kusanci, Aiki
kuma da Hadisansu Falala ne" Ya
sake cewa kuma:
(( لا يجوز لأحدٍ أنْ يذكرَ شيئاً من مساويهم،
ولا يطعنَ على أحدٍ منهم؛ فمن فعل ذلك فقد وجب على السلطان تأديبُه وعقوبتُه، وليس
له أنْ يعفوَ عنه، بل يعاقبُه، ثم يستتيبه؛ فإنْ تاب قبل منه، وإنْ لم يتبْ أعاد
عليه العقوبة، وخلّده في الحبس حتى يتوب ويُراجع)).
Ma'ana:
" Bai halatta ga Wani ba ya ambaci wani
abu na munanansu, ko ya soki Wani daga cikinsu; Duk Wanda ya aikata haka To ya
zama dole ga Shugaba ya Ladabtar da shi, ya masa Horo, Bashi ( uma da daman ya
yafe masa, ya masa horo sannan ya nemi tubansa; In ya tuba; ya karba daga
Wajensa, In kuma ya ki ya tuba Sai ya sake yi masa Horon, ya kuma tabbatar da
shi a rufe har ya tuba ya dawo".
4. Fadin Al'Imam Abu Uthman Assabuniy:
Al'Imam Abu Uthman Assabuniy cikin Littafin (
Akidatus Salaf wa As-habul hadis) ya ce:
((
ويرَوْن الكفَّ عما شجَر بين أصحاب رسول الله r،
وتطهيرَ الألسنةِِ عن ذكر ما يتضّمن عَيْباً لهم، أو نقصاً فيهم، ويرَون الترحُّم
على جميعِهم، والموالاةَ لكافتهم)).
Ma'ana:
" ( Su Ahlus Sunnah) Su na ga (
Wajibcin) kamewa dangane da abin da ya faru a tsakanin Sahabban Manzon Allah (
s a w), da kuma tsarkake Harasa ga barin ambaton abin da ya ke kunsan aibi a
gare su ko nakasa cikinsu, Kuma su na ga neman rahamar Allah ga 'Daukacinsu
gaba 'dayansu, da kuma So da taimako ga dukkansu".
5.
Fadin Shekhul Islam Ibn Taimiyyata:
Shekhul Islam Ibn Taimiyyata a cikin
Littafinsa (Akidatul Wasidiyyat) ya ce:
" Kuma ya na daga cikin Ginshikan
Ahlus Sunnah wal Jama'a: Kubutuwan
Zuciyansu da Harasansu ga Sahabban Manzon Allah ( s a w); kamar yadda Allah ya
siffanta su cikin fadinsa:
)
والذين جاءوا مِنْ بَعْدِهِمْ
يَقُولُونَ رَبَّنَا اغْفِرْ لَنَا وَلِإِخْوَانِنَا الَّذِينَ سَبَقُونَا
بِالْإِيمَانِ وَلَا تَجْعَلْ فِي قُلُوبِنَا غِلًّا لِلَّذِينَ آَمَنُوا رَبَّنَا
إِنَّكَ رَءُوفٌ رَحِيمٌ( (10)
Ma'ana: " Da wadanda su ka
zo bayansu su ke cewa: Ya Ubangijinmu ka gafarta mana (mu) da 'Yan' uwanmu da
su ka rigaye mud a Imani, Kuma kada ka sanya hassadan wadanda su ka yi Imani
cikin Zuciyarmu, Ya Ubangijinmu Lallai kai mai tausayi ne mai rahama".
Kuma biyayya wa Manzon Allah cikin
fadinsa:
[لا
تسبّوا أصحابي؛ فو الذي نفسي بيده لو أنفق أحدُكم مثلَ أحدٍ ذهباً ما بلغ مُدّ أحدِهم
ولا نصِيْفَه]
Ma'ana:
" Kada ku zagi Sahabbaina; Na fa rantse
da Wanda Raina ya ke hanunsa Da 'Dayanku zai ciyar da Kwatankwacin (Dutsen)
Uhdu na Zinari, To da bai kai Mudun 'Dayansu ba, koma rabi". Kuma suna
karbar abin da ya zo musu daga Alqur'ani da kuma Sunnah da Ijma'i na falalansu
da martabobinsu, kuma su na fifita Wanda ya ciyar kafin (Fat-hu) – wanda shi
ne: Sulhul Hudaibiyya – ya kuma yi yaki, Sannan su na gabatar da Wa'danda su ka
yi hijira akan Mataimaka (Mutanen Madina), Kuma sun yi Imani cewa Allah ya ce
wa ma'abota (yakin) Badr – alhali sun kasance Su 'Dari uku ne da goma sha wani
abu - :
[
اعمَلُوا ما شِئْتم فقدْ غفرتُ لكم]
Ma'ana: " Ku aikata abin da ku ka so; Na
gafarta muku".
Haka kuma:
[ لا
يدخل النارَ أحدٌ بايع تحت الشجرةِ]
Ma'ana: " Ba zai
shiga Wuta ba; ( Mutum) 'Daya da ya yi mubaya'a karkashin wannan Bishiyar;
Kamar yadda Annabi ( s a w) ya bada labari.
Kai! Allah ya ma yarda da su, Suma sun yarda da shi, Sun kasance fiye da dubu
da 'Dari hudu. Sannan su na shaidawa da aljanna ga Wanda Manzon Allah ( s a w)
ya shaida masa da shi; kamar Mutane goman nan, da Sabit bn Kais bn Sham-mas da
Wassunsu. Kuma sun tabbatar sun gamsu da abin da ya zo ta hanyayo da yawa (mutawatir)
daga Amiril Mu'uminina Aliyu bn Abiy 'Dalib ( Allah ya kara masa yarda) da
Waninsa na cewa: Mafi alherin Wannan al'umma – bayan Annabinta – Shi ne Abubakar,
sannan Umar, Sannan su na ukuntawa da: Usmanu, Sannan su huduntar da: Aliyu (
Allah ya kara musu yarda); kamar yadda Hadisai su ka nuna, kuma kamar yadda aka
yi Ijma'I wajen gabatar da Uthman wajen bai'a. Duk da cewa Wassu sashe na Ahlus
sunna sun yi sabani wajen Uthman da Aliyu Wanne ne ya fi?, - bayan haduwarsu
wajen gabatar da Abubakar da Umar -, Wassu su ka gabatar da Uthman … su
ka ce kuma; Na hudun Shi ne Aliyu. Wassu kuma gabatar da Aliyu. Wassu kuma su
ka tsaya ( kenan; su ka ki fifita 'Dayan kan 'Dan'uwansa). Amma (daga karshe)
Al'amarin Ahlus Sunnah ya hadu ya kuma tabbata wajen kaddamar da Uthman sannan
sai Aliyu; = Duk da cewa Wannan mas'alar – mas'alar Uthman da Aliyu – Bata
cikin Tussa da ake cewa wanda ya saba cikinta batacce ne,a wajen yawa yawan
Ahlus Sunnah. (kai dai wacce ake cewa wanda ya saba mata bacecce ne ; Ita ce: Mas'alar
halifanci; saboda sun yi Imani cewa: Khalifa bayan Manzon Allah ( s a w) shi
ne: Abubakar, sannan Umar, sannan Uthman, sannan Aliyu; Wanda ya saba cikin khalifancin
Wani daga cikinsu to ya fi Jakin gidansu bata".
Sannan ya ambaci sonsu (su Ahlus sunnah) ga =
Iyalen gidan Manzon Allah (s a w), da kuma jibintarsu da taimakonsu, tare da
kiyaye wasiyyar Manzon Allah (s a w) akansu. Da kuma so da jibitar Matan Manzon
Allah (s a w); Iyayen Mu'uminai, da Imaninsu kan cewa su matansa ne a Lahira.
Sannan ya ce:
" Kuma su na barranta daga hanyar
'Yan shi'a; da ke kin Sahabbai, ke kuma zaginsu, da kuma hanyar (Nasiba);
wadanda ke cutar da Ahlul Baiti da fadi ko da aiki. Sannan su na kamewa dangane
da abin da ya gudana tsakanin Sahabbai; Su kuma ce: Wadannan Lallai Wadannan
Abubuwan da aka kawo mana na fadin munanansu: Daga ciki akwai abin da Karya ne,
daa ciki kuma akwai abin da aka kara a ciki, aka kuma rage, daga aka jirkita
shi ya bar fiskarsa. Ingancecce kuwa daga ciki; Su abun a musu uzuri ne a
cikinsa; saboda ko dai ya zama sun yi kokari ( Ijtihadi) su ka kuma dace, ko
sun yi kokari sannan su ka kuskure. Sannan du da haka su ( Ahlus sunnah) ba su
kudurta cewa: kowani 'daya daga cikin Sahabbai ma'asumi( wanda aka kare shi) ne
ga barin manyan laifi ko kanana ba; hasali ma (su Sahabbai) mai yuwuwa ne a
gare su su yi zunubi a dunkule, Amma dai su na rigaye (cikin duk aiyuka) da
kuma falala da zai wajabta gafarta musu abin da ya faru daga wajensu – in ya
farun – har ma za'a gafarta musu munanan da baza a gafarta ma Wadanda su ka zo
bayansu ba; saboda su na da kyawawan da ke goge munana wanda na bayansu basu da
su; saboda ya tabbata daga Manzon Allah (s a w) cewa su ne: mafificin karni,
kuma mudun 'Dayansu idan ya yi sadaka da shi ya fi Dutsen Uhudu na zinari daga
Wadanda su ke bayansu. Sannan idan ya zama an samu wani zunubi daga 'daya daga
cikinsu To zai zama ya tuba daga gare shi, ko kuma ya aikata kyawawa da za su
goge masa shi, ko kuma an gafarta masa saboda falalar rigayensa, ko da
ceton (Annabi) Muhammad ( s a w); wanda
su su ka fi Mutane cancantar ceton nasa, ko kuma an jarrabe shi da wata
jarabawa a Duniya wanda za'a kankare masa shi da shi. (Idan wannan fa shi ne
halinsu ga zunubai da ake da tabbacinsa; To yaya kuma dangane da abin da su ka
kasance a cikin masu: Ijtihadi; wanda in sun dace su na da lada biyu, in kuma
su ka kuskure su na da lada 'daya, Shi kuma kuskuren an yafe!.
Sannan gwargwadon abin da ake ki daga aikin
sashensu kadan ne kuma bacecce ne a gefen falalan Mutanen da kyawawansu; na
daga Imani da Allah, da Manzonsa, da kuma jihadi a kan tafarkinsa, da hijira,
da taimakonsu, da kuma ilmi mai amfani, da aiki managarci (mai kyau).
Kuma duk wanda ya yi dubi cikin tarihin
Mutanen da ilimi da basira, da kuma abin da Allah ya yi musu baiwa da shi na
falala To zai sani yanke cewa: Su ne mafi alherin Halittu bayan Annabawa, ba a
yi kamar su ba kuma ba za ayi ba, kuma su ne zababbu wannan al'ummar; wacce ita
ce mafi alkhairin al'ummai kuma mafi daukaka da daraja a wajen Allah ".
Wadannan Misalai ne guda biyar daga zancen
Magabata na kwarai kan abin da ya wajaba a kudurta dangane da hakkin Fiyayyun
Halittu bayan Annabawa da Manzanni ( Yabon Allah da tsiransa ya kara tabbata a
gare su) ya kara ya yarda ga Sahabban dukkansu.
Sukan
sahabbai Sukan Qur'ani da Hadisi ne
Daga
cikin abin da ya dace a lura da shi; Lallai Sukan Wadannan fiyayyu zababbun ( r
anhum); Suka ne ga ( Wannan) Addinin; saboda ( addinin) ba isa ga na bayansu ba
face su ne tsani, kuma dai maganan Abu zur'ata ya gabata; in da ya ke cewa:
(( وإنما أدّى
إلينا هذا القرآنَ والسننَ أصحابُ رسولِ الله r،
وإنما يريدون أن يجرحوا شهودنا ليبطلوا الكتاب والسنة، والجرْح بهم أوْلى، وهم
زنادقةٌ)).
Ma'ana:
" kuma
(ka sani) Wanda kawai ya kawo mana
Wannan Qur'anin da Wadannan Sunnonin su ne Sahabban Manzon Allah ( s a w), (
Sannan su kuma) abin da kawai su ke nufi shi ne su soki SHAIDUNMU don su bata
Littafi (Alqur'ani) da Sunnah, To sukansu (su) shi ya fi, kuma su Zindikai ne
(Munafukai)".
Sukan
sahabbai ba zai cutar da su ba
Kuma sukan Sahabbai ba ya cutar da su komai, kai zai ma amfanar da su
ne; kamar yadda ya zo cikin hadisin Fallasheshshe da ya gabata; don shi mai
sukan ba zai cutar ba; sai kansa, duk wadda ya samu a cikin zuciyarsa; Sonsu da
kuma kubutuwa daga yi musu hassada, Sannan ya kiyaye Harshensa ga barin bijiro
musu sai da alkhairi To ya gode wa Allah akan Wannan ni'imar, ya kuma roki
Allah tabbatuwa kan Wannan shiriyar. Amma Wanda kuma a cikin Zuciyarsa akwai
hassada a gare su, sannan ya saki Baki ya ke ambato abin da bai dace da su ba;
To ya ji tsoron Allah akan kansa, ya kuma tobu ga barin Wa'dannan Laifuffukan,
Sannan ya tuba zuwa ga Allah; tun da dai kofar tuba a bude take a gabansa;
kafin ya yi nadama lokacin da nadama bata da amfani.
YA UBANGIJINMU KADA KA KARKATAR DA ZUCIYARMU BAYAN DA KA SHIRYAD DA MU,
KUMA KA MANA BAIWAR WATA RAHAMA DAGA WAJENKA; LALLAI KAI NE MAI YAWAN BAIWA , YA
UBANGIJINMU! KA GAFARTA MANA ( MU) DA 'YAN UWANMU DA SU KA RIGAYE MU DA IMANI,
KUMA KADA KA SANYA A CIKIN ZUCIYARMU: HASSADA GA WADANDA SU KA YI IMANI, YA
UBANGIJINMU LALLAI KAI NE MAI TAUSAYI MAI
RAHAMA.
No comments:
Post a Comment