2015/07/03

HUDUBAR MADINA (2)








HUXUBAR MASALLACIN ANNABI (r)
JUMA'A, 16/RAMADHAN/1436H




LIMAMI MAI HUXUBA
DR. ABDULMUHSIN XAN MUHAMMADU AL-QASIM







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah; muna gode masa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, muna kuma neman tsarinSa daga sharrin kayukanmu da kuma munanan aiyukanmu,     
Duk wanda Allah ya shiryar da shi to babu mai vatar da shi,     Wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi,
Kuma ina shaidawa babu abun bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokan tarayya,
Kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa ne,     
Allah ya yi daxin salati a gare shi; Shi da iyalansa da sahabbansa, ya kuma yi musu sallama mai tarin yawa.
Bayan haka:
Ku ji tsoron Allah –ya ku bayin Allah- iyakar jin tsoronsa,     Kuma kuyi riqo a musulunci da igiya mai qarfi.

Ya ku musulmai  
Lallai Allah ya fifita wassu darare da yini akan wassu,     ya kuma zavi wata xaya daga cikin watanni,     sai ya sanya shi ya zama  jagoran watannin shekara,     sa'annan ya keve shi da qarin falala da karramawa,      Yininsa ya zama lokacin yin azumi,     Darensa kuma lokacin yin sallar tarawihi,      Ayoyin littafin Allah a cikin wannan watan ana karanta su kuma ana tilawarsu,     A cikinsa kuma ake rurrufe qofofin wuta,     a kuma bubbuxe qofofin aljannah,     kuma a cikinsa ne ladan aiyuka suke ninninkuwa,       a kuma kankare kurakurai da zunubai,    Shine matattarar samun afuwa da gafara,     kuma shine watan alkhairori da albarkoki.
Saidai kash, Babu wani abun da zai gama cika      face ya juya zuwa ga gushewa.     Kuma lallai shuxewan zamani abu ne da yake faxakar da masu hangen nesa da basira = kan ribatar aiyukan alheri,      Ya kuma sanya su jin tsoron tuntuve, ko kasa isa.       
Lallai haqiqa mun kasance a kwanakin baya na kusa-kusa muna cikin matsanancin fata da jiran shiga cikin wannan wata mai girma,      Sai gashi a yau mun bada baya wa rabinsa,    tare da wassu aiyukan da ba a san wanene ya yi riba a cikinsu ba,   daga waxanda su ka yi hasara.
  A cikin watan ramadhana rayuka su kan fice daga cikin rafkana,    da kuma dabaibayin kasalar qin aiyukan alkhairi       =    zuwa:  Sararin ibadah, da kogin xa'a;     Saboda harsuna a cikin ramadhana suna qasqantattu (masu kamewa, da kuma yawaita tilawa),     Idanu kuma suna hawaye,    zukata kuma suna cikin tsoro, da nitsuwa,    Rayuka kuma sun fiskanci Allah,   Ibada kuma ta kan yi daxi,  tare da samun karvuwa a cikin rai,    Shi kuma lokacin rayuwa ya kan qara cika da albarka.
Kuma lallai Bawa ya kan samu wadata ne a cikin yin xa'a wa UbangijinSa, da kuma fiskantarSa,      Su kuma zukata basa samun nitsuwa sai sun koma zuwa ga Allah,     Shi kuma addinin gaskiya shine:  Tabbatar da yin bauta wa Allah, da kuma yin ikhlasin dukkan ayyuka waxanda suka haxa da yin azumi da waninsa ga Allah shi kaxai,    Kuma wannan shine tushen addini;    Don haka ne Allah ya umurci ManzonSa da yin ikhlasi (wato: kaxaita Allah cikin bauta), a cikin faxinsa:
"Kuma ka bauta wa Allah kana mai kaxaita shi da dukkan addini" [Zumar: 2].  
Kuma aka umurci Annabi (صلى الله عليه وسلم) da yin bayanin cewa lallai shi bautarsa ta tsayu ne kawai akan kaxaita Allah da addini (yin ikhlasi), A inda yace masa:
"Kace: Lallai ni an umurce ni da na bauta wa Allah ina mai kaxaita shi da dukkan addini" [Zumar: 11].
Kuma da aikata irin haka aka umurci dukkan al'ummomi, Allah mabuwayi da xaukaka yana cewa:
"Kuma ba a umurce su ba face da: Su bautawa Allah, suna masu kaxaita shi da addini, suna masu karkacewa shirka, Su kuma tsayar da sallah,    Su kuma bada zakkah,    Yin haka shine miqaqqen addini" [Albayyinah: 5].
           
            Ita kuma SALLAH matsayinta a cikin addini yana zuwa ne bayan kalmomin shahada guda biyu,      Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana yin umurni da aikata ta, tun a farkon da'awarsa,       Sarki Hiraqlu yace wa Abu-sufyan:
"Da wani abu yake umurtarku? –yana nufin: Annabi Muhammadu  (صلى الله عليه وسلم),      Sai yace:  "Yana umurtarmu da yin sallah, da bada zakkah, da kuma kamewa, tare da sada zumunci",   [Bukhariy da Muslim suka rawaito shi].
            Kuma (sallah) itace: mafi soyuwan aiyuka a wajen Allah ta'alah;    Saboda an tambayi Annabi (صلى الله عليه وسلم) cewa: Wani aiki ne yafi soyuwa a wurin Allah? Sai yace: "Yin sallah akan lokacinta, Sa'annan sai biyayya wa iyaye",  [Bukhariy da Muslim suka rawaito shi].
            Kuma an keve sallah da qarin falala akan sauran ibadodi, sakamakon ita sallah an farlanta ta ne a sama (lokacin mi'iraji).

            Ita kuma ZAKKAH an ambace ta tare da sallah a cikin ayoyin alqur'ani masu yawa,      kuma itama ginshiqi ne daga cikin ginshiqan addinin msulunci,      kuma tana tsarkake rai daga xabi'ar rowa,     tana kuma bunqasa dukiya, sannan tana kare shi,     Tare da sanya mai bada zakkah cikin sahun mutanen kirki masu kyauta,     Allah yana cewa:
"Ka karvi zakkah daga dukiyarsu, kana mai tsarkake su da ita" [Taubah: 103].
            Kuma ita zakkah tana kare mutum daga uqubar zunubai,    ta kuma tunkuxe masa manya-manyan masifofi, da baqin ciki,   Sannan ta sauqaqe masa al'amura,     Allah yana cewa:
"Amma wanda ya yi kyauta, ya kuma yi taqawa   *   Ya kuma gaskata lamarin aljannah   *   Lallai zamu sauqaqe masa har ya kai ga sauqi   *   Amma wanda yayi rowa, ya kuma wadatu da kansa   *   Ya kuma qaryata lamarin aljannah   *   To da sannu zamu sauqaqe masa har ya kai ga tsanani " [Al-laili: 5-10].  

            Shi watan RAMADHANA lokaci ne na ciyarwa da kyauta,        Kuma lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) yafi yawaita yin kyauta a cikin watan ramadhana.     Kuma dukkan wata ciyarwa da bawa ya aikata to lallai za a bashi mayewa a wurin Allah, kuma tamkar bashi ne da za a mayar masa da shi,      Kuma ita dukiya tana qaruwa ne da yin sadaka ko zakkah, ba tawaya ba.       Sannan mutum yana cikin sadakarsa ne a ranar tashin alqiyamah.

            A cikin watan ramadhana akwai ibadodi da suke kankare zunubai masu yawa;      Saboda azumtar wannan watan yana gafarta laifuka da zunubai,       Annabi (عليه الصلاة والسلام) yace:
"Duk wanda yayi azumin watan ramadhana da imani yana mai neman lada, to an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa", [Bukhariy da Muslim suka rawaito shi].
            Kuma duk wanda ya kiyaye azumtar watan to lallai hakan zai kasance kariya a gare shi daga faxawa cikin wuta, Annabi (عليه الصلاة والسلام) yace:
"Azumi garkuwa ne", [Bukhariy da Muslim suka rawaito shi].       
Ibnu-hajar –Allah yayi masa rahama- yace:
"Idan har mutum ya katange kansa daga aukawa cikin sha'awarsa a nan duniya, Sai hakan ya zame masa kariya daga faxawa wuta a lahira".
            Kuma duk wanda ya yi sallah a cikin dararen watan to sai a gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa, Annabi (عليه الصلاة والسلام) yace:
"Duk wanda ya yi tsayuwar ramadhana –sallar dare- da imani tare da neman lada, to an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa", [Bukhariy da Muslim suka rawaito shi].
An-nawawiy –Allah yayi masa rahama- yana cewa:
"Abunda ake nufi da  قيام رمضان cikin hadisin shine: Sallar tarawihi".
           
            [Watan azumi] wata ne mai albarka,     Yin umrah a cikinsa yana daidai da yin aikin hajji,        Annabi (عليه الصلاة والسلام) yace wa wata mata daga cikin mutanen garin Madina (Al'ansaar):
"Me ya hana ki kiyi aikin hajji tare da mu? Sai tace:   Mun kasance muna da raqumi guda xaya, Sai baban wane da xansa suka hau shi –tana nufin: mijinta da xanta-, Sai kuma ya bar mana raqumi xaya da zamu riqa xebo ruwa da shi. Sai Annabi yace: Idan watan ramadhana ya zo to sai kiyi umrah a cikinsa; saboda yin umrah a watan ramadhana yana daidai da yin hajji", [Bukhariy ya rawaito shi].
Ibnul-jauziy –Allah yayi masa rahama- yace:
"A cikin wannan hadisin an fahimci cewa: Lallai ladan yin aiki ya kan qaru;     saboda darajar lokacin da aka aikata shi a cikinsa,    kamar yadda ladan ke qaruwa idan aka halarto da zuciya a cikin aiki, ko aka yi ikhlasi da tace niyyah".   

            Kuma littafin Allah mai karamci an sauqar da shi ne a cikin watan ramadhana:
"Watan ramadhana wanda aka sauqar da alqur'ani a cikinsa,    shiriya ne ga mutane,   da bayanin shiriya, da kuma rarrabewa (tsakanin gaskiya da varna)", [Baqarah: 185].
            Kuma ramadhana lokaci ne na yawaita tilawar alqur'ani,     Kuma mala'ika Jibrilu ya kasance (عليه السلام) yana yin darasunSa tare da Annabi (صلى الله عليه وسلم) a cikin wannan watan.    Kuma duk lokacin da musulmi yayi tilawar littafin Allah, sai ya qara hawa mataki na sama a cikin aljannah,      Annabi (عليه الصلاة والسلام) yace:
"Za a ce wa: ma'abocin alqur'ani: Ka yi karatu sai ka xaukaka, kuma ka kyautata karatunsa kamar yadda kake kyautata shi a duniya; saboda matsayinka (a lahira) yana nan ne a qarshen ayar da ka karanta ta".      [Ahmad ya rawaito shi].

            Shi kuma addu'a shi ne mabuxi daga qunci,     kuma matakalar da ake bi ta kanta don hauhawa zuwa ga alkhairori,      kuma lallai maxaukakin sarki Allah yayi baiwar amsa addu'a ga mai azumi,     Annabi (عليه الصلاة والسلام) yana cewa:
"Mutane uku ba a mayar da addu'oinsu;    Mai azumi har yayi buxa baki, da shugaba adali, da kuma addu'ar wanda aka zalunta;    Allah zai xaga ta har sama da girgije,     kuma za a bubbuxe mata qofofin sammai,    Sai Ubangiji yace:    Zan taimake ki koda bayan wani lokaci ne",                       [At-tirmiziy ya rawaito shi]. 

            Kuma yana daga cikin kyautar Allah:      Yadda yake qarin falaloli a cikin watan ramadhana,    ya kuma sanya goman qarshe (na watan) su ka zama haske a goshin watan azumi,      Kuma a cikinsu ne ake samun dare guda xaya;      wanda yin bauta a cikinsa yake daidai da yin ibadar watanni guda dubu,    kuma saboda matsayin wannan dare ne a wurin Allah: Saukar Mala'iku take yawaita a cikinsa; saboda yawan albarkansa,     Su kuma Mala'iku  (n rahama) suna sauka ne tare da saukar albarka da rahama.  

            Yin i'itikaafi a cikin watan azumi shi kuma yana daga cikin sunnonin Annabi (صلى الله عليه وسلم) domin tsarkake zuciya daga dauxa, da kurakurai,       da kuma saboda yin hisabi wa rai  daga sakacinta,      kuma domin  ran bawa ta qara fiskantar Allah; don darajojinta su qara xaukaka a wajensa,     
Sai kayi qoqarin sanya wa kanka wani rabo na i'itikaafi a cikin watan,       kuma Annabi (عليه الصلاة والسلام) ya kasance yana yin i'itikafin kwanaki goman qarshen ramadhana,  don qoqarin dacewa da lailatul qadari,      A'ishah (رضي الله عنها) tace:
"Annabi  (صلى الله عليه وسلم)  ya kasance yana yin i'itikafin kwanaki goman qarshe na watan ramadhana, har Allah ta'alah ya karvi ransa", [Bukhariy da Muslim suka rawaito shi].
Ibnu-baxxalin –Allah yayi masa rahama- yace:
"Wannan hadisin yana nuna cewa lallai yin i'itikaafi yana daga cikin sunnoni masu qarfi; saboda kasancewar i'itikaafin xaya daga cikin abubuwan da Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya doge akan aikata su;     kuma ya dace muminai su yi koyi da Annabinsu akan haka".
            Kuma lallai cikin yin i'itikaafi akwai yanke dukkan alaqoqi da halittu,     domin samun lokacin yin bauta wa Ubangiji ta'alah; mai halitta,        Kuma idan alaqar ibada tayi qarfi tsakanin bawa da Ubangijinsa sai Allah ya yarda da bawa.    
Ibnu-shihabin –Allah yayi masa rahama- yace:
"Abun mamaki musulmai sun bar yin i'itikaafi,     alhalin Annabi (صلى الله عليه وسلم) bai bar yinsa ba tunda ya shiga garin Madina, kowace shekara, a cikin kwanaki goma na qarshen ramadhana, har Allah ya karvi ransa".

            Sai ka nisanci duk abubuwan da suke tauye azumi ko lalata shi,      Ka kuma kiyaye aukawa cikin mutuncin musulmai,    Sannan ka kiyaye harshenka, da jinka, da ganinka daga dukkanin abubuwan da Allah ya haramta,   
Imam Ahmad –Allah yayi masa rahama- yana cewa:
"Ya dace mai azumi ya himmatu wajen kiyaye azuminsa daga harshensa,      kuma kada yayi jayayya a cikin maganarsa,     (magabata) Sun kasance idan suna azumi su kan zauna a cikin masallatai, Sai su riqa cewa:    Mun zauna muna kiyaye azuminmu, ba zamu ci naman wani ba".

            Wanda kuma aka jarrabe shi da wautar wani jahili to kada ya fiskance shi da irin wautar tasa,        Annabi (عليه الصلاة والسلام) yana cewa:
"Idan yinin azumin xayanku ya zo to kada yayi kwarkwasa,    kada kuma yayi shewa,     Idan wani ya zage shi to sai ya ce: Lallai ni ina azumi",    [Bukhariy ya rawaito shi].

            A'UZU BILLAHI MINASH SHAIXANIR RAJIM
"Kuma kuyi gaggawa zuwa ga rahama daga Ubangijinku, da wata aljannah wacce faxinta shine kamar faxin sammai da qasa,      An tanade ta ne ga masu taqawa" [Ali-imraan: 133],

Allah ya muku albarka Ni da Ku cikin alqur'ani mai girma.  …..


HUXUBA TA BIYU
            Yabo da godiya sun tabbata ga Allah akan kyautatawarSa,       Ina gode masa kan datarwanSa, da ni'imominSa,
Ina shaidawa babu abun bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokin tarayya, tare da girmama sha'aninSa.
            Kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa ne,
            Ya Allah kayi qarin salati a gare shi,    da iyalansa da sahabbansa , ka kuma yi musu sallama mai qaruwa.
           
Ya ku musulmai!
            Maganin cutukan zuciya yana nan cikin abubuwa guda biyar:
(1)            Yin karatun alqur'ani da fahimta.
(2)            Da qin cin abinci (wato; yin azumi).
(3)            Da yin sallar dare.
(4)            Da yin addu'a a lokacin sahur.
(5)            Sai zama da salihan mutane.
Ya kasance a watan azumi kana da wani aiki, tare da yin sallar tahajjud, da karatun alqur'ani,      Sai ka sanya watan azuminka ya zama yaqi ne da baya yankewa tsakaninka da sha'awar ranka,     da kuma kevanta da Allah don yi masa bauta da xa'a,      da yin darasun ayoyin alqur'ani,       da kuma sallolin dare da ikhlasi,      Saboda ramadhana lokaci ne na tuba da kuma mayar da lamura zuwa ga Allah,
Kuma qofar tuba a buxe take,
Sa'annan kyautuka Ubangijinka ababen bayarwa ne,
Kuma yaushe ne, mai qetare iyaka cikin savo, da yawaita kurakurai zai tuba idan har bai tuba a cikin watan ramadhana ba?!
Kuma yaushe zai koma ga Ubangijinsa idan har bai aikata hakan ba a cikin watan rahama da gafara?!
Sai kayi gaggawan komawa zuwa ga Allah,      kana mai kwankwasa qofarSa,      da yawaita neman gafararSa.
Kuma ku ribata da lokacin samun manya-manyan riba,     Saboda kwanakin samun hakan qididdigaggu ne,     kuma lokuta masu falala abun halarta ne daga Mala'iku,     kuma a cikin watan ramadhana akwai taskoki masu tsada,      Kar ku tozarta su, da aikata wargi ko wasa, ko kuma abubuwan da basu da wata fa'idah a cikinsu.
Shi kuma mai hankali shine wanda yayi nazarin halinsa,      ya kuma yi nazari da tunani cikin aibukansa,    Sannan ya yi qoqarin gyara kansa gabanin lokacin mutuwarsa ya dufafe shi kwatsam, sai aikinsa ya qare,     ya kuma tafi zuwa barzahu,    Sa'annan zuwa gidan hisabi!

Sannan, ku sani!
Lallai Allah ya yi muku umurnin yin salati da sallama ga AnnabiSa, a inda yake faxa a cikin alqur'ani:
"Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani kuyi masa salati, kuma kuyi masa sallama…" [Ahzab: 56].

Addu'a ….  ……………….

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...