2015/07/18

DARRUSA GUDA HUDU DAGA WATAN AZUMI (العبرة من شهر الصوم)





IZNA (DARRUSA) DAGA WATAN AZUMI
(العبرة من شهر الصوم)








NA
SHEHIN MALAMI  ABDULMUHSIN BN HAMAD AL-ABBAAD,











FASSARAR
Abubakar Hamza




  Malam ya fara Lecture ([1]) rsa ne da fadinsa:
        Bismillahir rahmanir rahim.
        Yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Salati da sallama su qara tabbata ga Manzon Allah, da iyalanSa, da sahabbanSa,                    Bayan haka:
        Wannan "Muhadara" ce mai taken:    DARRUSA DAGA WATAN AZUMI (العبرة من شهر الصوم), Wanda a cikinta nake cewa:

DUNIYA GIDA NE NA JARABAWA
 
           Allah ya halicci bayinsa ne don su bauta masa shi kaxai; ba tare da sun haxa shi da wani cikin bauta ba, kuma Allah a cikin littafin da zuwa da irinsa ya gagari mutane yana cewa:
{وَما خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنْسَ إِلاَّ لِيَعْبُدُونِ} [الذاريات: 56].
Ma'ana: {Ban halicci Aljani da Mutum ba sai don su bauta min}Ni xaya [Azzariyaat: 56].
 Kuma ya turo Manzanninsa masu daraja don su zana musu hanyar da za su bauta masa, Sai ya ce:
{وَلَقَدْ بَعَثْنَا فِي كُلِّ أُمَّةٍ رَسُولًا أَنِ اعْبُدُوا اللَّهَ وَاجْتَنِبُوا الطَّاغُوتَ} [النحل: 36]
Ma'ana: {Kuma hakika mun turo (tayar) Manzo cikin kowace al'umma, don su bauta wa Allah, su kuma nisanci bautar duk wani abin bauta (Waninsa) } [Nahli: 36].
Kuma Allah ya sanya rayuwar Mutane ta duniya ta zama waje ne na jarrabarsu don ya ga wanene a cikinsu zai fi kyautata aiki; yana cewa:
{الَّذِي خَلَقَ الْمَوْتَ وَالْحَياةَ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلاً} [الملك: 2].
(Allah){Shi ne wanda ya halicci Mutuwa da Rayuwa don ya jarrabe ku; Wane ne daga cikinku zai fi kyautata aiki}, [Mulk: 2].

Sai kuma ya ce:
{وَهُوَ الْعَزِيزُ الْغَفُور}.
{Kuma shi ne Mabuwayi Mai gafara}, Don ya nuna cewa lallai Su Mutane da aka jarrabe su, daga cikinsu akwai: Wanda zai kyautata aiyuka; Sai a saka masa da abin da sunansa (AL-GAFUURU) ya ke hukuntawa na yin gafara da rahma a gare shi. Sannan daga cikinsu akwai Wanda zai munana aiki; Sai ya zama ya cancanci horo, wanda sunansa (AL-AZIZU) ya ke hukuntawa; (saboda babu wanda ya gagari Allah). Wannan kuma ya dace da faxin Allah:
{نَبِّئْ عِبادِي أَنِّي أَنَا الْغَفُورُ الرَّحِيمُ * وَأَنَّ عَذابِي هُوَ الْعَذابُ الْأَلِيم} [الحجر: 49-50].
Ma'ana: {Ka baiwa Bayina labari; Lallai ni Ni ne Mai gafara Mai rahama, Kuma lallai azabata itace azaba mai raxaxi} [Alhijir: 49-50].

(A dunkule; Duniya gida ne na Jarabtar Bayi; kuma Wani daga cikinsu za a datar da shi sai ya ci jarrabawar, Sai kuwa ya samu sakamakonsa na aljannah a gidan Lahira. Wani kuma zai tave ya faxi sai ya cancanci azabar Allah gobe qiyama).
Malam ya ci gaba da cewa:

MUHIMMIN LOKACI DAGA CIKIN LOKUTAN NEMAN LAHIRA
Kamar yadda Allah ya  fifita wassu Mutane da Wurare akan wassu, haka kuma ya fifita Wassu lokutan akan wassu, yana daga cikin haka; FIFITA WATAN AZUMI mai albarka AKAN SAURAN WATANNI  da kuma zaven watan don ya zama mahalli da aka wajabta azumi a cikinsa.
{وَرَبُّكَ يَخْلُقُ مَا يَشاءُ وَيَخْتارُ} [القصص: 68].
{Kuma Ubangijinka yana halittan abinda ya nufa, kuma sai yayi zavi (daga cikinsu)} [Alqasas: 68].
Haqiqa Allah ya fifita wannan watan kuma ya sanya shi ya zama lokaci daga cikin lokutan neman gidan Lahira, wanda masu tsere-re-niya wajen yawar bauta da kyautata ta su, ke ta tsere; don neman tsira, da kuma samun kusanci zuwa ga Allah.
Bayi (a cikin wannan watan) suna kusantar Ubangijinsu, ta hanyar azumtar yininsu da kuma tsayuwar darensu, tare da karanta littafinSa mabuwayin, wanda
{Varna bata zuwa masa ta gaba gare shi da kuma ta baya; saboda saukakke ne daga Mai hikima Abun yabo}.
Sannan su na qara yin bauta ta hanyar jin tsoro, tare da nisantar faxawa cikin sava wa Allah don fatan samun lada da riba cikin kasuwancin da babu asara a cikinta, wannan kuma saboda Allah zai cika musu ladan aiyukansu, kuma ya musu qari daga falalarsa, kasancewarSa shi Mai gafara ne kuma Mai sakayya tare da bada lada mai yawa, kan aiki kaxan tsarkakakke.

SAMUN QARIN ALKHAIRI
Yayin da Allah ya farlanta azumtar watan ramadhana ga bayinsa, Sai Annabi (Yabo da tsira su qara tabbata a gare shi) ya kwaxaitar da su azumtar azumi guda shida cikin watan Shawwal; bayan Ramadhana; wannan kuma don ladansu ya girmama, su kuma kasance kamar waxanda suka yi azumin shekara gabaxayanta, An ruwaito daga Abu Ayyub Al'ansariy (Allah ya yarda da shi) Lallai Manzon Allah (Yabo da amincin Allah su qara tabbata a gare shi) yace:
"من صَامَ رَمَضَانَ ثُمَّ أَتْبَعَهُ سِتًّا مِنْ شَوَّالٍ، كان كصيام الدهر".
Ma'ana: [Duk wanda ya azumci Ramadhana Sannan ya bi-bi-ye shi da guda shida a cikin watan Shawwal To lallai kamar azumtar shekara ne] (wajen lada da fallala.)  ALHAFIZU ALMUNZIRIY Ya ce: Muslim, Abu Dawud, Tirmiziy, Nasa'iy, Ibn-Majah da Xabaraniy suka rawaito shi.
A riwayar Xabaranin akwai qarin tambayar (Abu Ayyub) wa Annabi (Yabo da amincin Allah su qara tabbata a kansa) Yace: Sai na ce:
"بِكُلِّ يَوْمٍ عَشَرَةُ؟ قَالَ: نَعَم".
Ma'ana: "Kowani yini yana daidai da Yini Goma? Sai Annabi ya ce: [E]. Kuma waxanda suka rawaito shi Maruwaitan su Bukhari da Muslim ne. intaha (maganarsa ta qare).
 Haka ya kasance ne  saboda Shekara a  Musulunci a yawaice Kwanakinta basa wuce kwana xari uku da sittin (360). (To) kaga in aka jingina kwana Shidan nan zuwa ga kwanaki Talatin na Ramadhana, Kuma azumin yini ya zama kamar na yini goma –saboda kyakkyawa guda xaya yana da kwatankwacinsa goma– Musulmi zai zama kamar ya azumci shekara ne gabaxayanta. Wannan kuma falala ce mai girma daga Allah. Yabo da godiya duk nasa ne; kan ni'imominsa da basa qirguwa, kuma basa qididdiguwa.

DAGA ALKHAIRI ZUWA GA WANI ALKHAIRIN
Yana daga cikin falalar Allah da kyautatawansa ga bayinsa; Sauqaqe musu samun sabbuban da zasu zama dalilin daukaka ga darajarsu, sannan su sanya su Su zama suna ganawa da saduwa madawwamiya da bautar Ubangijinsu; Don haka ne; Idan Yini da Dararen Ramadhana su ka shuxe –Wanda Allah yake kankare munanan aiyuka a cikinsu ya kuma daga darajan Bayi…- Sai Watannin aikin Hajji su biyo su; Saboda Ranar idin azumi itace rana ta farkon cikin ranakun watannin aikin Hajji – wanda Allah ya ke cewa a kansu:
{الْحَجُّ أَشْهُرٌ مَعْلُوماتٌ فَمَنْ فَرَضَ فِيهِنَّ الْحَجَّ فَلا رَفَثَ وَلا فُسُوقَ وَلا جِدالَ فِي الْحَجِّ وَما تَفْعَلُوا مِنْ خَيْرٍ يَعْلَمْهُ اللَّهُ وَتَزَوَّدُوا فَإِنَّ خَيْرَ الزَّادِ التَّقْوى وَاتَّقُونِ يا أُولِي الْأَلْبابِ} [البقرة: 197].
Ma'ana: {Aikin hajji Watanni ne sanannu; Duk wanda ya yi harama a cikinsu To babu saduwa da mata ko maganan da za ta kai zuwa ga hakan, kuma babu fasiqanci (wato fita daga xa'a wa Allah) kuma babu jayayya cikin hajji, Kuma duk abinda kuka aikata na alkhairi Allah ya san shi, Kuma ku yi guzuri, Lallai kuma mafi-ficin guzuri shine bin dokokin Allah (taqawa), Kuma ku ji tsorona ya ma'abota hankali} [Baqarah: 197]. 
Lallai idan kwanakin Ramadhana (waxanda Alqur'ani ya sauka a cikinsu (kwaco-kwam daga Lauhul mahfuz zuwa Saman Duniya) kuma a ke bubbuxe qofofin Aljannah a cikinsu, a kuma rurrufe qofofin Wuta tare da garqame Shexanu a cikinsu, Kwanakin da Allah –a cikin hadisin qudusi – ya ke faxi akansu:
"كُلُّ عَمَلِ ابنِ آدَمَ لَهُ، الْحَسَنَة بِعَشْرِ أَمْثَالِهَا، إِلاَّ الصَّومَ فَإِنَّهُ لِي وَأَنَا أَجْزِي بِهِ".
[Dukkan aiyukan Xan'adam nasa ne, Kykkyawa xaya yana da kwatankwacinsa guda goma, Saidai Azumi; Shi kam nawa ne kuma ni zan yi sakayya a kansa].
To idan Kwanakin Azumin suka qare, Sai kwanakin Hajji da Annabi (yabo da amincin Allah su qara tabbata a gare shi) yake cewa a kansu:
«مَنْ حَجَّ وَلَمْ يَرْفُثْ وَلَمْ يَفْسُقْ رَجَعَ كَيَوْمِ وَلَدَتْهُ أُمُّهُ».
[Duk wanda ya yi hajji bai yi Jima'i, ko duk abinda yake kaiwa zuwa gare shi ba, haka kuma bai yi fasiqanci ba To zai koma kamar ranar da Mahaifiyarsa ta haife shi] Bukhariy da Muslim ne suka rawaito shi.
Ya sake cewa:
«الْعُمْرَةُ إِلَى الْعُمْرَةِ كَفَّارَةٌ لِمَا بَيْنَهُمَا، وَالْحَجُّ الْمَبْرُورُ لَيْسَ لَهُ جَزَاءٌ إِلاَّ الْجَنَّةُ».
[Kuma yin umrah zuwa wata Umrar kankara ne na abinda ya kasance a tsakaninsu (na zunubi), Shi kuma kuvutaccen Hajji ba shi da wani sakamako sai Aljannah], Bukhariy da Muslim.
Don haka Musulmi yana yin bankwana da lokacin azumi -wanda kasuwa ne na neman Lahira– Zai kuma fiskanci Wani lokacin neman aljanna (wato lokacin Hajji) Da haka ne, zai zama yana cikin wata ganawa da saduwa ta din-din-din da bautar Mahaliccinsa da ya qagi halittarsa ya kuma samar da shi daga rashi, Sannan ya kwarara masa ni'imominsa bayyanannu da kuma voyayyu.

(Kuma duk abinda ya gabata kamar matashiya ce ga abubuwan da suke tafe)
MALAM SAI YA CE:

DARRUSA DAGA WATAN AZUMI

 Sannan ya fara maganarsa da cewa:

Wannan lokaci mai albarka kwanan nan Jama'ar Musulmi suka yi bankwana da shi, Don haka Madallan Mutumin da Allah ya datar da shi' ya yi kyawawan aiyuka a cikinsa, kuma ya ji tausayinsa ya karva masa su. Mamakin tavewar Mutumin da kwanakin suka shige ba tare da ya qaddamar da kyawawan aiyuka wa kansa ba; wanda zai ji daxinsu a ranar barin duniya (ranar haxuwa da Mahalicci) Mamakin girman musibarsa!! Tun da ya cike lokutansa da abinda zai yardad da Shaixan kuma ya yi daidai da son zuciyarsa mai Umurtarsa da mummuna. Allah ya kiyashe mu.
WANNAN LOKACI DA YA SHIGE YA QUNSHI MANYA-MANYAN FA'IDOJI DA GIRMAMAN DARRUSA DA SUKE MOTSA SON ALKHAIRI A CIKIN ZUCIYAR MUTUM, SU KUMA RATAYE TA DA YIN BIYAYYA WA ALLAH. HAKA KUMA SU KAN JEFA QIN SABO DA NISANTAR DUK ABINDA SUKE FUSATA ALLAH MAI GIRMA DA XAUKAKA.
  A NAN NE ZAN AMBATO DARRUSAN DA MUSULMI YA FITA DA SU DAGA WATAN RAMADANA. Ina kuma neman taimakon Allah da dacewarsa. SAI NA CE:

NA XAYA
        Idan kwanakin azumi suka riski Musulmi to fa dama ce ta samu a rayuwarsa na kusantar Ubangijinsa sosai, wanda za ta iya maimaituwa sau xaya ko biyu… zai iya yuwuwa kuma ajalinsa ya riske shi kafin wata damar; Don haka yana da matuqar muhimmanci ya zama an cike wannan damar da yin biyayya wa Allah da kuma nisantar yi masa sabo.
Abin da ya fi wannan muhimmanci kuwa shi ne: A dawwama a kan hakan.

 Malam ya ci gaba da wa' azi, ya ke cewa:

Saboda yana cikin sakamako da Allah yake yi wa Mutumin da ya kyautata a nan duniya kafin aje aljanna: Ya sa ke datar da shi zuwa ga wani kyakkyawan aikin na daban. Haka kuma horo na gaggawa ga mutumin da ya munana Sai a sa ke barinsa ya tave ya kuma sa ke aikata mummunan aiki a karo na biyu….
Kaga ashe Duk Musulmin da  ya san ciyon kansa –Idan ya dace har watan azumi ya riske shi– To zai cike lokutansa ne da abinda suke xa'a ne wa MahalliccinSa don bautarSa, wanda ya kewaye shi da ni'imomi bayyanannunsu da boyeyyu, Sai kaga zuciyarsa ta nitsu da yin kyawawan aiyuka, Tunaninsa kuma kawai shi ne Gidan Lahira; wanda shine qarshe kuma matabbata. Wanda ba abinda zai amfani Mutum a can sai abinda ya aikata … Tabbas Idan Mutum ya sabar wa ransa biyayya cikin waxannan yinin don kwaxayin abinda yake wajen Allah, sannan ya kame ga barin sava masa don tsoron horonsa … To Fa'ida da Darasi da ya kamata ya fita da shi daga wannan makaranta ta kwanaki Talatin Ita ce:
Mutum ya lazimta kuma ya dawwama wajen aikata dukkan biyayya tare da kuma nisantar savo, har Mutuwarsa. Kuma da aikata haka ne Allah ya bautar da mu a cikin faxinSa:
{وَاعْبُدْ رَبَّكَ حَتَّى يَأْتِيَكَ الْيَقِينُ} [الحجر: 99].
{Kuma ka bauta wa Ubangijinka har Mutuwa ta zo maka} [Alhijir: 99]
{يا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ حَقَّ تُقاتِهِ وَلا تَمُوتُنَّ إِلاَّ وَأَنْتُمْ مُسْلِمُونَ} [آل عمران: 102].
Ma'ana: {Ya ku wadanda ku ka yi Imani ku ji tsoron Allah iyaka jin tsoronsa kuma kada ku mutu face ku na Musulmi} [Ali-Imraan: 102].

Malam ya yi kira da babbar murya ya ce:
Ba zai dace da Musulmin da ya xanxani zaqin biyayya wa UbangijinSa a cikin watan azumi, Ya canza wannan daxi\zaqin da xacin savo ba, haka kuma idan ya baqanta wa Shexan a cikin Ramadhana To bai kamata ya faranta masa rai a sauran watanni guda sha xayan nan ba. Kuma baya cikin siffofi mutum nagari wanda ya san ciyon kansa: Yin bankwana da kyawawan aiyuka tare da bankwanarsa wa watan azumi; don wanda a ke yi masa bauta a cikin Ramadhana shine kuma abun bauta cikin sauran watannin, yana da ransa baya mutuwa…….

NA BIYU
Babbar Fa'ida:
Azumi sirri ne da ke tsakannin Bawa da Ubangijinsa, ba wadda ke sanin haqiqaninsa sai Allah shi kaxai, wannan yasa ya zo cikin hadisin qudusi:
"كُلُّ عَمَلِ ابنِ آدَمَ لَهُ، الْحَسَنَة بِعَشْرِ أَمْثَالِهَا، إِلاَّ الصَّومَ فَإِنَّهُ لِي وَأَنَا أَجْزِي بِهِ، يَدَعُ شَهْوتَهُ وَطَعَامَهُ مِنْ أَجْلِي".
Ma'ana: [Allah yana cewa: Dukkan aikin xan-adam nasa ne, kyakkyawa xaya yana da kwatankwacinsa guda goma. Saidai azumi; shi kam nawa ne, kuma ni zan yi sakayya a kansa, ya kan bar buqatarsa (sha'awarsa), abincinsa da abin shan sa don ni ].
Sananne ne Bawa zai iya vuya -ga barin ganin Mutane- ya kuma rufe kofa ya ci, ya sha, Sa'annan ya fito -ya bayyana- wa Mutane cewa shi mai azumi ne; tare da cewa ba wanda zai san haqiqanin lamarin sai Allah. Saidai Musulmi ba zai yi hakan ba; saboda ya san Allah ya na tsinkaye da shi yana kuma ganinsa. Wannan kuma abin a yaba wa Mutum ne.
DARASI A NAN SHI NE:
Dole Mutum ya gane cewa Lallai wanda a ke jin tsoron kamunSa idan an tauye azumi To fa shi ya kamata a ji tsoron kamunSa idan aka tauye Sallah, Zakkah, da Hajji da xaukacin duk abubuwan da Allah ya wajabta … saboda wanda ya wajabta azumi Shine kuma ya wajabta Sallah. Wanda ita ko (sallah ita ce Mafi girmar Rukunan Musulunci bayan Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah da Shaidawa Annabi Muhammadu manzon Allah ne. Don ma girman sha'anin Sallah ne da kuma kasancewarta ganawar safiya da maraice tsakanin Bawa da Ubangijinsa, Allah bai farlanta ta wa Manzonsa ba Sai da Allah ya yi Mi'iraji da shi (aka hawar da shi sama). … kenan, Idan Musulmi ya gane cewa tauye azumi matsala ne mai girma, To ya zama wajibi ya riska kuma ya gane cewa matsalar ta fi muni da za a qaddara ya tauye Sallah …
Wannan yana daga cikin manya-manyan fa'idoji da musulmi zai tsinka daga watan Ramadhana.

NA UKU
Ya kan daxaxa wa dukkan musulmi rai ya kuma faranta masa: Ganin cikar Masallaci a watan Azumi, amma farin cikin zai fi girma ne Idan da musulmai za su dawwama kan tururuwa a Masallatai bayan tafiyan watan Ramadhana. Ke nan ya zama wajibi kowani Musulmi ya yi niyya kwakkwara don tabbatuwa kan wannan alkhairin don Mutum ya samu kansa cikin bakwai da Allah zai Inuwantar da su cikin Inuwarsa ranar da babu Inuwa sai ta Allah
[ … Da Mutumin da zuciyarsa ta ke rataye da Masallaci …]. Kamar yadda hakan ya tabbata a cikin littafin SahihulBukhariy, daga Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم).
NA HUDU
Abinci da abin Sha da sauran abubuwan da suke karya azumi asalinsu halal ne, amma sai a ka haramta su cikin yini (da rana) na watan Azumi. Sai ka ga Musulmi ya kame ya bar abinda a asalinsa halal ne saboda haramcin da ya bijiro masa. Ke nan Musulmi a cikin watan Azumi ya kan kame ne ga barin (abu biyu): Dukkan abu na haram, da kuma abin da ya ke halal kafin azumi da kuma bayansa; na abinci dana sha da kuma sha'awa. Amma kamewarsa ga barin haramun shi kam a rayuwa ne gabaxaya; Misali Kamewar Ido, Harshe, Kunne, Hannu da Farji ga barin abinda aka hana su faxawa cikinsa da aikata shi.

Malam ya ci gaba da ambato ni'imomin Allah ga Mutane, da kuma yadda yanayin gode masa da su, ko butulce masa yake, A inda yace:

Allah ya yi baiwa wa Mutum da waxannan ni'imomi wanda Mutum bai isa ya wadata ga barin su ba, Saidai kamar yadda ya yi baiwa da su To ya wajaba a yi amfani da su wajen duk abinda zai yardad da shi, Ya kuma haramta a yi amfani da su wajen duk abinda ke baqanta masa. Yana  kuma daga cikin manyan godiya wa Allah kan ni'imomin Musulmi ya zamo ya na amfani da su a inda aka umurce shi, yana kuma kamewa ga barin sava masa da su; tun da shi ya yi baiwa da su.
 - IDo An shar'anta yin amfani da shi cikin halal, kuma an hana amfani da shi wajen kallon haram, To hanuwansa Shi ne azuminsa, Lokacin aikata hakan kuma rayuwa ne gabaxaya.
 - KUNNE An shar'anta amfana da shi wajen sauraron abinda yake halal, aka kuma haramta wa bawa amfana da shi wajen sauraron haramun, kamewansa ga barin hakan shi ne azuminsa. Hukuncin hakan kuwa na nan tsawon rayuwa.
 - HANNU An shar'anta yin amfani da shi wajen tava abu na halal, sannan an hana amfani da shi wajen dukkan haram, hanuwansa shine azuminsa, kuma hakan hukuncinsa tsawon rayuwa ne.
 - QAFA An shar'anta amfani da ita wajen tafiya zuwa ga dukkan alkhairi, sannan aka kuma haramta tafiya da ita zuwa ga haram. Hanuwa ga barin hakan shi ne azuminta, Lokacin wannan kuma Duk kan rayuwar Baligi ne.
 - FARJI An halalta amfani da shi wajen halal (Mata, Baiwa), a ka kuma haramta amfani da shi a wanin haka. Kamewarsa ga barin hakan shi ne azuminsa. Hukuncin kuma na nan tsawon rayuwar Baligi.
Akwai kuma sakamako mai kyau da Allah ya tanada ga duk Mutumin da ya kiyaye gavvansa kuma ya yi amfani da su a wuraren da suka dace. Haka kuma ya tanadi narkon azaba ga Mutumin da bai kiyaye su ba. Kuma ya bada labari cewa su waxannan gavvan abun tambaya ne ranar tashin alkiyama;
{وَلا تَقْفُ مَا لَيْسَ لَكَ بِهِ عِلْمٌ إِنَّ السَّمْعَ وَالْبَصَرَ وَالْفُؤادَ كُلُّ أُولئِكَ كانَ عَنْهُ مَسْؤُلاً} [الإسراء: 36].
{Kar ka faxi abin da baka da sani kansa; don Ji da Gani da Zuciya dukkan su abun tambaya ne akan su} [Isra'i: 36].
{الْيَوْمَ نَخْتِمُ عَلى أَفْواهِهِمْ وَتُكَلِّمُنا أَيْدِيهِمْ وَتَشْهَدُ أَرْجُلُهُمْ بِما كانُوا يَكْسِبُونَ} [يس: 65].
Allah ta'alah har ila yau yana cewa: {A Yau zamu yi rufi ga Bakunansu sai Hannayensu su yi Magana da mu, Kafofinsu su bada Shaida kana bin da su  ka kasance su ke aikatawa} [Yasin: 65].
{وَيَوْمَ يُحْشَرُ أَعْداءُ اللَّهِ إِلَى النَّارِ فَهُمْ يُوزَعُونَ * حَتَّى إِذا مَا جاؤُها شَهِدَ عَلَيْهِمْ سَمْعُهُمْ وَأَبْصارُهُمْ وَجُلُودُهُمْ بِما كانُوا يَعْمَلُونَ * وَقالُوا لِجُلُودِهِمْ لِمَ شَهِدْتُمْ عَلَيْنا قالُوا أَنْطَقَنَا اللَّهُ الَّذِي أَنْطَقَ كُلَّ شَيْءٍ وَهُوَ خَلَقَكُمْ أَوَّلَ مَرَّةٍ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ} [فصلت: 19-21].
Ma'ana: {Ranar da za a tara Maqiya Allah zuwa ga Wuta alhali ana tunkuxa su, ana jan su zuwa wajen hisabi * Har lokacin da za su zo mata, Sai Jinsu da Ganinsu da Fatunsu su yi shaida akansu kan abinda suka kasance suke aikatawa * Sai su ce wa Fatunsu; Don me kuka yi shaida a kanmu?! Sai su ce: Allah ne ya nufe mu da yin magana; wanda shi ke nufan kowani abu da hakan, wanda kuma shi ya halicce ku farkon al'amari, kuma zuwa gare shi za a mayar da ku} [Fussilat: 19-21].
Annabi (yabo da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ya ce wa Mu'azu (Allah ya yarda da shi) bayan ya umurce shi da kiyaye harshe, sai Mu azu yace: Ya ma'aikin Allah! Shin mu abin kamawa ne da abinda muke magana da shi?! Sai Annabi ya ce:
"ثَكِلَتْكَ أُمُّكَ يَا مُعَاذُ، وَهَلْ يَكُبُّ النَّاسَ فِي النَّارِ عَلَى وُجُوهِهِمْ، أَوْ قَالَ: عَلَى مَنَاخِرِهِمْ، إِلَّا حَصَائِدُ أَلْسِنَتِهِمْ؟".
[Mahaifiyarka ta yi asararka Ya kai Mu'az! Ai ba komai ke tuntsurar da Mutum cikin wuta kan Fiskarsa \Ko a kan Hancinsa ba Sai abinda harshensa ya girba masa]. Tirmiziy ne ya ruwaito shi.
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya sake cewa:
«مَنْ يَضْمَنْ لِي مَا بَيْنَ لَحْيَيْهِ وَمَا بَيْنَ رِجْلَيْهِ أَضْمَنُ لَهُ الْجَنَّةَ».
Ma'ana: [Duk wanda ya lamunce mini abin da ke tsakanin Lebbansa(wato Harshe) da kuma abinda ke tsakanin qafofinsa (wato Farji) To Na lamunce masa shiga aljannah] Bukhari ya ruwaito shi daga hadisin Sahal xan Sa'ad Allah ya yarda da su.
Shi kuma Tirmiziy ya rawaito shi ne daga hadisin Abu-Huraira (Allah ya yarda da shi), kuma yace hadisi ne "hasan", da Lafazin;
«مَنْ وَقَاهُ اللَّهُ شَرَّ مَا بَيْنَ لَحْيَيْهِ وَشَرَّ مَا بَيْنَ رِجْلَيْهِ، دَخَلَ الجَنَّةَ».
[Wanda Allah ya kare shi daga sharrin abinda yake tsakanin  Levvansa guda biyu da tsakanin qafofinsa ya shiga aljannah].
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
«مَنْ كَانَ يُؤْمِنُ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ فَلْيَقُلْ خَيْرًا أَوْ لِيَصْمُتْ» .
Ma'ana: [Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar qarshe To ya faxi alkhairi ko ya yi shiru], Bukhariy da Muslim suka rawaito shi.
Ya zo cikin hadisin Abu Musa (Allah ya yarda da shi) faxin Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم):
«الْمُسْلِمُ مَنْ سَلِمَ الْمُسْلِمُونَ مِنْ لِسَانِهِ وَيَدِه».
Ma'ana: [Musulmi shi ne wanda Musulmai su ka kuvuta daga sharrin Harshensa da Hannunsa].
Daxin daxawa kuma ya na cewa:
«إِنَّ الْمُفْلِسَ مِنْ أُمَّتِي مَنْ يَأْتِي يَوْمَ الْقِيَامَةِ بِصَلَاةٍ وصيام وزكاة، وقد شَتَمَ هَذَا، وَقَذَفَ هَذَا، وَأَكَلَ مَالَ هَذَا، وَسَفَكَ دَمَ هَذَا، وَضَرَبَ هَذَا، فَيعطى هَذَا مِنْ حَسَنَاتِهِ وَهَذَا مِنْ حَسَنَاتِهِ، فَإِنْ فَنِيَتْ حَسَنَاتُهُ قَبْلَ أَنْ يَقْضِيَ مَا عَلَيْهِ أُخِذَ مِنْ خطاياهم فطرحت عليه ثم يطرح في النار».
Ma'ana: [Lallai fallashasshe daga cikin al'ummata shine wanda zai zo ranar kiyama da tarin Sallah da Azumi da Zakka, Sai ya zo alhali ya zagi wannan, ya yi qazafi wa wannan, kuma ya ci dukiyar wannan, ya zubar da Jinin wannan, ya kuma doki wannan, Sai a baiwa wannan daga kyawawansa, wannan ma daga kyawawansa, Idan kyawawan suka qare kafin a gama biyan abinda yake kansa Sai a xauko daga munanansu sai a zuba masa, Sai kuma a jefa shi a Wuta] Muslim ne ya ruwaito shi.
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
«حُفَّتِ الْجَنَّةُ بِالْمَكَارِهِ وَحُفَّتِ النَّارُ بِالشَّهَوَاتِ».
[An kewaye aljanna da abinda rai ke qi, An kuma kewaye Wuta da abinda rai ke sha'awa].Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi daga hadisin Abu-Hurairah (رضي الله عنه).    awa.nsa na abin ci da  ya in  
    A dunqule Allah ya wajabta wa Bawa kiyaye Harshensa, Farjinsa, Jinsa, Ganinsa, Hannunsa da qafarsa ga barin haram, kuma wannan ma a harshen Larabci a na kiransa azumi; don ma'anar SIYAM a wajensu shine: Kamewa. Kuma wannan azumin bai kevanci wani lokaci banda wani ba, kai hasalima shi lokacinsa; Rayuwar Mutum ne har mutuwa, don Bawa ya rabauta da yardar Ubangijinsa ya kuma tsira daga Fushinsa tare da azabarsa.
Idan Musulmi ya riski Azumi ya kan hanu ya kuma bar abubuwa waxanda gabanin haka Allah ta'alah ya halatta masa su, zai bar yin amfani da su na tsawon kwanakin watan (ramadhana); wannan kuma saboda haramci da ya bijiro mu su;
To DARASI A NAN; SHINE: Riskar cewa akwai abubuwan da dama haramun ne Mutum ya aikata su a gabaxayan rayuwarsa, Don haka WAJIBI ne akansa ya kame ya kuma bar auka musu har abada; don tsoron kar Allah ya masa horo.

Malam ya rufe wannan Fa'idar da ambato sakamakon mai azumi; Ya ce:
Haqiqa Manzon Allah ya bada labari daga Mahaliccinsa – kamar yadda ya zo cikin hadisin qudusi – cewa:
[Lallai Mai azumi yana da farin ciki guda biyu da zai yi su; Farin ciki xaya lokacin shan ruwansa, Xayan kuma lokacin ganawa da Ubangijinsa].
Don haka mai azumi zai yi farin ciki lokacin shan ruwansa saboda zai bawa ransa abinda aka hana ta alhali abun so ne da sha'awa a wajenta; daxin–daxawa; yana jin an datar da shi ya kammala ibadarsa cikin lafiya, wanda sakamakonta mai girma ne a wajen Allah. Sa'annan zai kuma yi asalin babban farin cikin ne Lokacin ganawa da Allah; ta yadda zai saka masa a kan azuminsa sakamako cikakke.

 A nan Malam zai gaya mana sakamakon azumin Gabbai, Inda yace:
Duk Mutumin da ya kame Harshensa ga barin alfasha da faxin zur (qarya), ya kuma kiyaye Farjinsa ga barin abinda a ka haramta masa, sannan ya kiyaye Hannayensa ga barin tava abinda ba a halatta masa ba, haka ya kiyaye Jinsa ga barin abinda jinsa haramun ne, sannan ya kiyaye Ganinsa ta yadda ya bar ganin abinda Allah ya haramta ganinsa … Sannan kuma ta gefe guda ya yi amfani da waxannan Gavvan ta wurin da aka halatta masa… Duk wanda ya yi haka har Ubangijinsa ya xau ransa To zai yi buxa baki ne – Bayan dogon azumi da ya yi da Gabbensa – da abinda Allah ya tanada wa wanda ya masa biyayya na ni'imomi; wanda Farkon abinda zai fara samu kuwa shine abinda Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya bayyana na abinda zai gudana wa Mumini lokacin mutuwa; Lokacin qaura daga wannan gidan (na duniya) zuwa gidan qarshe (Lahira) Na zuwan Mala'ikun Allah; Kai ka ce rana ce a fuskar su saboda haske, tare da su akwai likkafanai da kuma turare  na aljannah, A gaba gare su Mala'ikan Mutuwa yana jagorantarsu; sai ya ce: Ya ke wannan rai ta gari! ki fita zuwa ga gafara daga Allah da kuma yarda … Sai ta fita da tsanaki kamar yadda ruwa ke xiga daga bakin abin shayarwa … ] har zuwa qarshen abin da Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya bayyana cikin wannan dogon hadisin na abubuwan da za su gudana bayan fitar da ran bawa.
Kuma lallai abinda ya zo cikin wannan hadisin yana cikin albishir masu daxi waxanda mutumin da ke fatan samun tsira, ya kuma yi ta qoqarin tsamar da ransa daga halaka, zai same su a gaba (wato tun daga lokacin mutuwa).
Kuma don Ran bawa ta tsira ne Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya SHIRYAD da Mutumin da ya tambaye shi dangane da tashin kiyama, ya shiryad da shi ZUWA GA ABIN DA YA FI MUHIMMANCI A KAN TAMBAYAR YAUSHE NE TASHIN NATA, wanda shi ne: YI MATA TANADI NA AIYUKA NAGARI kamar yadda ya ce masa:
«وَمَاذا أَعْدَدْتَ لها؟».
Ma'ana: [To me ka tanadar mata?!] Yana mai baiyana cewa lallai ya wajaba a kan Mutum ya yi tanadi wa Lahira tun a nan gidan Duniya; saboda Allah yana cewa:
{وَتَزَوَّدُوا فَإِنَّ خَيْرَ الزَّادِ التَّقْوى وَاتَّقُونِ يا أُولِي الْأَلْبابِ} [البقرة: 197].
Ma'ana: {Kuma ku yi guzuri, amma mafi alkhairin guzuri shi ne tsoron Allah, kuma ku ku kiyaye dokokina ya ku ma'abota Hankali} [Baqarah: 197]. Wannan kuma saboda kowace tafiya akwai guzurin da ya dace da ita; Ita kuma tafiya zuwa Gidan qarshe (Lahira) guzurinta shine: Tsoron Allah da aikata biyayyarsa tare da tafiya kan Turbar da Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya zo da ita.

Malam ya gama Lecture-rsa da yin KEVANTACCIYAR NASIHA WA MAZAUNA WANNAN GARI mai albarka MADINAR MANZON ALLAH (صلى الله عليه وسلم). Yace:

KALMA TA QARSHE
Zan qarisa nasihata da yin fadakarwa da ta kevanci Waxanda Allah yayi musu baiwa da zama a cikin garin Madina.
Ya ce:
Watan Ramadhana wata ne mai albarka da Allah ya keve shi da wassu kevantattun abubuwa da ba a samu a wassunsa (Haka ma Garinku). To Mu da sauran Musulman Duniya duk Mun yi ban kwana da shi kwanan nan, Muna kuma fatan Mu zama duk Mun  rabauta da yardar Allah mai girma da daukaka (a cikinsa).
Abinda na ke so na ambata a nan shi ne: Idan wannan lokaci mai falala da albarka ya zama ya tafi ya barmu da ma sauran Musulmai, To – Alhamdu lil lah – Allah ya barmu da Wuri madaukaki; wato Shi ne Madina. Wato a Ramadan Allah ya hada mana Falalan Lokaci da Wuri, To yanzu da Falalan Lokaci ya tafi ya bar mu da Falalan Wuri; Don haka; Ga kasuwa daga cikin Kasuwannin da ake sayen Lahira a gabanmu (Wato: Masallacin Manzon Allah Yabo da amincin Allah su kara tabbata a kansa) wanda ya ke cewa a kansa:[ Salla a wannan masallacin nawa ya fi salla dubu a waninsa, banda Masjidul haram). Lallai ko wannan falala ne mai girma.
 Kuma Lallai yan Kasuwa na Duniya kirdadon Lokaci  da Wuri da kayansu zai fi ja sosai don neman riba mai yawa, TO YAYA MUTUMIN DA YA KE KASUWANCI DA ALLAH KUMA YA AJIYE SHI A GARIN DA KASUWANCIN AKWAI RIBA SOSAI?! … Ka yi mamakin Falalar Allah akanmu da kyautarsa da kyautatawansa. Godiya da yabo duka nasa ne akan ni imominsa gaba daya.

Ya ci gaba da cewa:

Ba zai wuce ni ba Na tunatar da mu kamar yadda ni'imar Allah da ya yi mana na zama a garin Fiyeyyen halitta take da girma, TO MU SANI GWARGWADON NI'IMA GWARGWADON TAMBAYA. Kuma kamar yadda kyautatawa a garin nan Ladansa na da girma a wajen Allah, haka kuma Munanawa da sabo a garin ba kamar sauran Wurare ba ne; Don haka wanda ke saba wa Allah a nesa da Haram ba dai – dai ya ke da Mutumin  da ke aukawa wa Haramun a Haramin Makka ko Madina ba, saboda akwai banbanci mai nisa tsakaninsu.

Malam ya ci gaba da fadin Falalar Madina Yace:

  - Ita Madina itace mafi xaukakan gurbi da tsarki a dukkan Duniya bayan garin Makka. Masallacin kudus Kuma na biye dana Madina.
  - Kuma itace Tushe da Mabubbugan Annabci, sannan daga ita ne haske ya tsinkaya ya shiga dukkan yankuna na Duniya.
  - Kuma ita ce Cibiyar Musulunci na farko a zamanin Annabi  (Yabo da amincin Allah su kara tabbata a kansa) Tun daga hijirarsa zuwa gare ta, da kuma zamanin Abubakar da Umar da Usman da kuma sashe na Khalifancin Aliyu( Allah ya kara musu yarda gaba daya).
  - Kuma a cikinta aka bunne Manzon Allah (Yabo da amincin Allah su qara tabbata a gare shi) da Abubakar da Umar da Usman, da kuma mutane dadama daga cikin Sahabban Annabi (Yabo da amincin Allah su qara tabbata a kansa).
  - Sannan a kan Wannan qasar Mala'ika Jibrilu ya yi ta sauka da wahayi daga Allah zuwa ga annabi Muhammadu (Yabo da amincin Allah su qara tabbata a kansa).
  - Kuma Itace farkon qasar da ta qunshi farkon Jami'ar Musulunci da matattararsa; wanda Abubakar (Allah ya yarda da shi) Xaya ne daga cikin Fitattun xalibanta, Haka Umar da Usman da Aliyu (Allah ya yarda da su).
  - Kuma Itace qasar da duga–dugin Zavavvun halittu bayan Annabawa (Wato: Sahabbai) Su ka yi ta tafiya akanta.
 
  Sai kuma ya qarisa nasiharsa da faxinsa:

        To fa ya dace da mu –bayan Allah ya karrama mu da zama a cikinta- Mu yi guzuri da kyawawan aiyuka da za su amfane mu bayan Mutuwa. Kuma mu zama mu na tsoron aukawa cikin sabon Allah a cikinta; saboda hakan zai fusatar da shi a kanmu.

Malam ya kammala Laccarsa da yin addu'a yake cewa:

Ina rokon Allah ya sanya mu – gaba dayanmu – daga cikin wanda ya karbi azuminsu, da Sallansu, Kuma ya azurta mu da kyakkyawan zama a wannan da kuma ladabi mai kyau, sannan ya kyautata karshenmu. Kamar yadda na ke fatan Allah ya yi baiwa wa Musulmai – gaba daya – da komawa zuwa ga Littafin Ubangijinsu da Sunnar Manzonsu a fadin Duniya gaba daya don su rabauta datsirar Duniya da Lahira, Lallai Shi Mai ji ne kuma Mai amsawa.

  Yabo da tsira da albarka su kara tabbata ga Bawansa kuma Manzonsa, kuma Masoyinsa, Zabebbensa cikin Halittunsa; Muhammad bn Abdullahi, da Iyalensa da Abokansa da ma Wadanda su ka bi hanyarsu, kuma su ka Shiriya da shiriyarsu har zuwa ranar sakamako.



(Alhamdu Lil lah)
27\ Ramadan\ 1428 h.



[1]   Wannan Lecture Ce Da Malam Ya Yi Ta A Makaranta Mai Suna(Sanawiyyatu Daiba) A Nan Madina, Sannan An Yada Ta A Jaridar Jami Ar Musulunci A Shekara Ta 1390 Na Hijirar Manzon Allah(Yabo Da Amincin Allah Su Kara Tabbata A Gare Shi) A Watan Shawwal

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...