2015/07/04

YIN UMRAH A WATAN RAMADHANA

YIN UMRAH A WATAN RAMADHANA

Tambaya: Shin ya tabbata cewa umrah a cikin watannin aikin hajji tana da wata falala ta musamman, wanda ya banbanta da sauran watannin? ([1])
Amsa: Mafificin zamani da ake aiwatar da umrah a cikinsa shi ne watan azumi, saboda faxin Annabi (صلى الله عليه وسلم):
«عُمْرَةٌ فِي رَمَضَانَ تَعْدِلُ حَجَّةً».
Ma'ana: "Yin umrah a cikin ramadhana yana daidai da yin aikin hajji" ([2]). Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi, a wani lafazin na Imam Albukhariy:
«تَقْضِي حَجَّةً مَعِي».
Ma'ana: "Tana daidai da yin hajji tare da ni" ([3]). A cikin sahihu Muslim kuma: 
«تَقْضِي حَجَّةً أَوْ حَجَّةً مَعِي».
Ma'ana: "Tana daidai da yin hajji, ko kuma yin hajji tare da ni" ([4]). Haka lafazin ya zo da shakka –daga maruwaita-.
Lafazin "tare da ni" na nufin: tare da Annabi (صلى الله عليه وسلم).
Sa'annan bayan umrar ramadhana sai kuma yin umrah a cikin watan "zulqi'idah" ([5]); saboda dukkanin umrarsa (صلى الله عليه وسلم) sun kasance ne a cikin wannan watan, Allah ta'alah kuma yana cewa:
(لقد كان لكم في رسول الله أسوة حسنة) [الأحزاب: ٢١].
Ma'ana: "Lallai kuna da abun koyi mai kyau daga rayuwar Manzon Allah" [Ahzaab: 21].



([1]) A duba/ FATAWA ISLAMIYYAH, (2/303), tattarawar: Sheikh Muhammad Al-musnid, da littafin MAJMU'U FATAWA WA MAQAALAAT MUTANAWWI'AH, (17/ 431).
([2]) Hadisin Abdullahi xan Abbas (رضي الله عنه), Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 1782), da Muslim (lamba: 1256).
([3])  Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 1863), wajen Muslim kuma hadisin ya zo da lambar da ta gabata.
([4])  Riwaya ce na hadisin da ya gabata.
([5])  Bayani akan yawan "umrar" da Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya aikata, da kuma lokutansu = ya zo daga Anas (رضي الله عنه), Kamar yadda Imamu Bukhariy ya kawo a cikin sahihinsa (lamba: 1778-1781), da Muslim (lamba: 1253).

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...