HUXUBAR
MASALLACIN ANNABI (r)
JUMA'A, 8 /SHAWAAL/1436H
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI SALAH ALBUDAIR
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Yabo da godiya sun tabbata
ga Allah; mahaliccin rayuka, Wanda
yake rayar da qasussuwa bayan sun rududduge, wanda kuma yake gwavava kyautuka da rabo, Ina yin godiya a gare shi akan abinda ya
ke ta qaruwa na ni'imomi, da wanda ya ninku na daga falala da kyauta, Kuma ina shaidawa babu abun bauta da
gaskiya sai Allah; shaidawar da take kawar da bawa daga karkatan vata, ta kuma
tunkuxe masa azaba, kuma ina
shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa,
shine wanda aka turo shi ga dukkan talikai;
Larabawa da ajamawa. Allah ya yi daxin salati a gare shi da
iylanSa; salatin da yake wanzuwa, da
sallama a jejjere,
Bayan haka;
Ya ku musulmai !
Ku bi dokokin Allah, saboda kiyaye dokokin Allah (taqawah) shine
mafi girman abinda mutum ya samar,
Yin biyayya kuma a gare shi shine mafi girman nasaba, "Ya ku waxanda suka yi imani ku
kiyaye dokokin Allah iya kiyayewa, kuma kada ku mutu face kuna musulmai"
[Ali-Imraan: 102].
Ya ku musulmai !
Lallai duniya jin daxi ne
xan kaxan da zai tafi ya qare, da
kuma wata dukiya wacce daga qarshe za a kwace, da gidan da zai rushe, Da kuma ran da za a cire ta !
Saidai kuma;
Madalla da matafiyin da a cikin
taron matafiya yayi ta zaburar da abun hawanSa,
Ya kuma riski damar lokaci
na rayuwa da ya samu; gabanin yayi qaura (ya mutu).
Har ya zama kamar mutumin
nan da a qissarSa;
1. Bai
gushe ba yana ambaton zai mutu yana kuma
tuna haka
Har zuwa lokacin da mai raqumi
ya tsaya a qofar gidanSa
2. Sai ya
same shi a faxake, cikin shiri
Da tanadi, yana wanda
burace-burace basu shagaltar da shi ba.
Ya kai wanda ya manta
makomarSa, Ya kuma doge cikin
nau'ukan vata !!!
(1) Ka
riski rayuwarka ka gyara ta; saboda
zama a duniya gajere ne
Mutuwa kuma tana dufafar
mai rai kwatsam, tana kuma kawo masa farmaki.
(2) Idan
kuma ka sava wa haka, to lallai zaka shiga cikin ramin qabari
Kuma lallai Mala'ikun;
Munkar da Nakiru zasu yi tambayoyi a gare ka.
(3) Lallai
kuma zaka yi kuka, cikin qunar rai, tare da bayyanar da yin hasara
Lallai hisabi ga masu savo
abu ne mai wahala
(4) Saboda
masu zunubai zuwa: Wutar SA'IRA makomarsu take
Sune; Waxanda suka yi
sakaci, Sai sakacinSu ya kai su cikin
bala'i da kunyata
Ya kai wanda ya kame daga
abubuwan da suke karya azumi a cikin watan ramadhana, Ya kuma kiyaye dokokin Allah; abun
bauta! Ya wanda ya yanke dararenSa
da yin tasbihi da tilawa da ruku'i da sujjada !! Ya wanda ya bada dukiyarsa a matsayin
bauta da kuma kyautatawa bayin Allah !!!,
Ya wanda ya yi yaqi da kanSa, sai ya kiyaye ta daga wuta, sannan ya
xaukaka da ita !!!!,
Kada ka zama daga cikin
bayin da suka yi aikin biyayya da xa'a, sa'annan suka yanke,
Kada kuma ka kasance daga
cikin waxanda suka bada kaxan,
sa'annan suka qaranta; kuma suka hana,
Kada kuma ka kasance daga
cikin waxanda suka qaurace wa savo,
sa'annan suka koma cikinsa,
Ya wanda ka kasance zuwa ga
aiyukan alkhairi mai aikatawa,
Mai kuma nisantar sharri,
Mai tausasa wa faqiri da
talakawa,
Mai yin tilawar alqur'ani,
Mai kusantar masallatai,
A cikin dare kuma, kana yin
tsayuwa, da addu'oi,
kana yin sallah, kana
khushu'i, kana ta kuka,
To, kada ka koma cikin savo
bayan wucewar watan ramadhana,
Mai yin gaba da bayin
Allah,
Mai yin rafkanuwa dangane
da farillah,
Saboda
1- Lallai
ka tsayu wajen yin bauta na wani lokaci
Wanda kuma kwanakin suka
kasance albarka a gare ka da cin nasara
2- Kada ka
dena yin tsayuwa cikin darenka (wato: sallah), bayan kuma
Samman dararenka sun
xaukaka da tilawar al'qur'ani, da yin sujjada,
3- Kada
kuma ka dena yin azumin yininka,
bayan kuma
An karya lagon yin azumi,
cikin haquri, da juriya
4- Lallai
wanda ya munana aiki idan har ya so ya tsira,
To sai yayi tuba ta
gaskiya, ya kuma ninnika aiyuka
5- Kuma
bawa yana kwaxayin a rududdugar da qasussuwanSa rududdugarwa
Sai kuma a dawwamar da shi
a cikin aljannonin ni'imah dawwamarwa.
Kuma –wallahi- tir da bawan da a cikin watan ramadhana zai yi
ta yin bautar UbangijinSa, Amma
idan watan ya fice sai yayi nauyin
jiki kan ibada, Sannan ya sanya rigar
qaranta bayan ta qari, Sannan yayi
biyayya wa shexanu, harma da masu taurin kai,
Ya kai bawan Allah
Kada ka kasance daga cikin waxanda suka koma bayan qeyyarsu, Suka kuma canza alqiblar
tafiyarsu, Sannan suka warware
abinda hannayensu suka qulle shi da kyau,
Suka kuma rusa abinda suka qawata; suka kuma kyautata gininsa,
Ya kai bawan Allah!
Kayi azamar aikata
alkhairi, iya azama, ka kuma tabbatu
akan aiyukan, tabbatuwa; saboda
Duk wanda aka azurta shi da
yin azama, tare da dogewa, Sai alkhairori da albarkoki su nufo shi, Wanda kuma aka yi masa baiwar
tabbatuwa kan aiyukan alkhairi to sai buxi da kyaututtuka su fiskance shi, Saboda ita azama tana umurtar mutum ne
da aikata abinda yafi amfani, Shi
kuma tabbatuwa da sabati yana xaukarsa zuwa ga aiki da abinda yafi xaukaka da
girma, Hadisi yazo daga Shaddad xan
Aus (رضي الله عنه) yace, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya
gaya mini cewa:
"Ya kai shaddad xan
Aus! Idan har kaga Mutane suna yin taskar zinari da azurfa To sai ka yi taskar WAXANNAN
KALMOMIN:
Ya Allah lallai ni ina
roqonka neman tabbatuwa cikin lamari (n addini), da azama akan aiyuka na
shiriya,
Kuma ina roqonka ka bani
abubuwan da suke hukunta samun rahamarka, da sabbuban gafararka,
Kuma ina rokonka ka bani
yin godiya kan ni'imominka, da kyautata yin bauta a gare ka,
Kuma ina roqonka zuciya
kuvutacciya, da harshe mai gaskiya,
Kuma ina roqonka ka bani
alherin da ka sani, sannan ka kare
ni daga sharrin da ka sani, kuma ina
neman gafararka kan abinda ka riga ka sani,
Lallai kai ne masanin
abinda ya vuya (na gaibu)" Axxabaraniy ya
rawaito shi.
Don haka, Ya kai bawan Allah,
Ka tafi akan siffar
tabbatuwa da kuma yin azamar aikata aiyukan alkhairi, kan halinka mai kyau, da kuma hanyarka mai kyau
miqaqqiya, Sannan aikinka ya zama
wanda ake tabbatuwa ne a dawwama akansa, Hadisi ya zo daga Alqamah, yace: Nace
ya ke Uwar-Muminai, Yaya aikin Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم);
Shin ya kasance ya kan keve wassu yinin?
A nan sai A'isha (رضي
الله عنها) tace:
A'a ; Aikinsa ya kasance wanda yake dawwama ne
akanSa, Wanene daga cikinku zai iya irin abinda Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yake
aikatawa. Muslim ne ya rawaito
shi.
Kuma lallai mafi soyuwan
aiyuka a wurin Allah shine wanda aka dawwama akansa; koda kaxan ne, Shi kuma aiki xan kaxan dawwamamme yana
girma yana tsarkaka yana qaruwa, Yayin
aiki mai yawa, mai wahalarwa ya ke gadar da/ qosawa, da gajiyawa, da kuma yanke
aikata shi, da gaza ci gaba. Ya
Allah ka arzurta mu da tabbatuwa akan aikata xa'a, da kuma gaggawa cikin
aiyukan alkhairori, da kuma tabbatuwa akan gaskiya har zuwa mutuwa, Ya mai ji,
ya mai karamci, ya mai amsa addu'oi !
A nan huxubar farko ta
qare!
HUXUBA TA BIYU
Yabo da godiya sun tabbata
ga Allah wanda ya xaukaka mu; da alqur'ani da sunnah, Kuma ya sanya mu daga cikin mafi
alherin al'ummai, Ina gode masa akan
ni'imominSa masu yawa, Kuma ina
shaidawa babu abun bautawa da gaskiya sai Allah; shaidawar da take kasancewa
mafi alherin kariya ga wanda yayi riqo da ita, Kuma ina shaidawa lallai annabinmu
kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa; UbangijinSa ya turo shi don ya zama rahama ga
talikai. Allah ya yi daxin salati da
sallama a gare shi, salati da sallaman da za su zama a haxe, a miqe, har zuwa
ranar sakamako!
Bayan haka!
Ya ku musulmai!
Ku
bi dokokin Allah, ku kiyaye shi, sannan ku yi masa biyayya; kada ku sava masa!
"Ya ku waxanda suka
yi imani ku bi dokokin Allah, kuma ku kasance tare da masu gaskiya"
[Taubah: 119].
Ya ku musulmai !!
Yin azumin yini shida a cikin watan shawwal sunnah ce
tabbatacciya, a mafi ingancin zancen maluma, Dalili kuma wanda jigajigan maluman
riwayar hadisi suka tabbatar da karvuwarsa; kana suka inganta shi = yayi nuni
akan wannan azumin, Hadisi yazo daga
Abu-Ayyub Al-ansariy (رضي
الله عنه) yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم )
yace:
"Duk wanda yayi
azumin watan ramadhana sa'annan ya biyar da guda shida daga shawwal to kamar ya
yi azumin shekara ne",
Muslim ne ya rawaito shi.
An kuma rawaito daga Sauban (رضي الله عنه ) daga
Manzon Allah (صلى
الله عليه وسلم), lallai yace:
"Duk wanda yayi
azumi guda shida bayan sallar azumi, to hakan shine cikon azumtar shekara (WANDA
YA ZO DA KYAKKYAWA GUDA XAYA TO YANA DA GUDA GOMA KWATANKWACINSA",
Ahmad da Ibnu-Majah suka rawaito shi .
Kuma cikin azumtar yini
guda shida na shawwal ##
Akwai falala, a wajen
ma'abota girma,
Kuma lallai azumtarsu bayan
idi yana daga cikin gaggawa zuwa ga alkhairi, da kuma saurin aikata ibada, Kuma ana samun falalar azumtarSu idan aka
yi su a jejjere, ko a rarrabe, A
farkon wata ne ko a qarshenSa,
Saidai kuma baya inganta ayi azuminsu da nufin haxa niyyarsu da kuma
biyan abinda ake bin bawa na bashin ramadhana da ya wuce, Duk kuma wanda ya aikata haka, to lallai
bashin da ake binsa bai sauka akansa ba.
Kuma haramun ne a riqi rana ta takwas na watan shawwal a matsayin ranar
idi ga mutumin da ya cika azuminsa guda shida na shawwal, harma ya yi abinci na murna irin na
idi, ayi masa gaisuwa irin ta idi, Har wassu jahilai su kira shi da sunan: IDIN
MASU BIYAYYA (عيد
الأبرار), Sai ka ji wanda ya
kammala azuminsa guda shida yana cewa: WANNAN SHINE IDINA, Duk wanda ya aikata wani abu daga cikin
haka; to lallai ya qirqiro bidi'a a cikin addini, kuma ya sava wa turbar salihan magabata, Sheikhul Islam Ibnu-Taimiyyah –Allah
ta'alah yayi masa rahama- yace:
"Amma yinin takwas
ga watan shawwal to ba ranar idi ba ne, a wajen mutanen kirki ko fajirai, Kuma baya halatta wani mutum ya qudurta
cewa wannan yinin na idi ne, Kuma bai
halatta a fari wani abu daga cikin alamomi ko aiyukan idi a cikin wannan yinin
ba".
Sai ku yi salati da sallama ga mai shiryarwa, wanda zai ceci
halittu gabaxaya, saboda duk wanda
ya yi masa salati guda xaya to Allah zai yi masa guda goma;
ALLAHUMMA SALLI WA SALLIM ALA NABIYYINA WA SAYYIDINA
MUHAMMADIN, wanda ke bishara da rahama da kuma lada, mai kuma yin gargaxi kan kamun Allah da
uquba, mai yin ceto, wanda kuma za a
ba shi ceton a ranar hisabi.
Ya Allah kuma ka yarda da dukkan iyalanSa da sahabbai, Ka haxa da mu Ya mai karamci, Ya mai yin baiwa!
Ya Allah ka xaukaka musulunci, kuma ka taimaki musulmai, kuma
ka qasqantar da shirka da mushirkai ….,,,,,,,,,,,,,,,,,,,
……………….
……………….
Addu'a ,,,,,,,,,,,
……………….
……………….
………,,,,,,,,,,,,
No comments:
Post a Comment