2015/07/10

ZAKKAR KONO (FIDDA KAI) صدقة الفطر

ZAKKAR FID-DA-KAI, KO SADAKAR FID-DA-KAI (AL-FIXR)

(إضاءات حول زكاة الفطر، أو صدقته)
     An sanya mata wannan sunan (na zakatu al-fixr) ne; kasancewar wannan zakkar ta kan wajaba ne saboda "shan ruwa" da za a yi na watan ramadhan, kuma wannan zakkar ba ta da alaqa da dukiya, a'a! wannan zakka ce da take da alaqa da ran mutum da jikinsa.

A nan akwai gavvai kamar haka:

Gavar farko: Hukuncin zakkar "fixr" da dalili akan haka:
Zakkar fidda kai ''wajibi'' ce akan kowane musulmi; saboda abinda aka ruwaito daga Abdullahi xan Umar رضي الله عنه-, ya ce:
"فَرَضَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم زَكَاةَ الفِطْرِ؛ صَاعًا مِنْ تَمْرٍ، أَوْ صَاعًا مِنْ شَعِيرٍ، عَلَى العَبْدِ وَالحُرِّ، وَالذَّكَرِ وَالأُنْثَى، وَالصَّغِيرِ وَالكَبِيرِ مِنَ المُسْلِمِينَ"([1]).
Ma'ana: (Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya wajabta zakkar fid da kai; sa'iy xaya na dabino, ko kuma sa'iy na sha'ir, akan bawa da xa, namiji da mace, da yaro da babba, daga cikin musulmai).

Gava ta biyu: Sharuxanta, da kuma ga wa take wajaba?
Zakkar fid-da-kai tana wajaba akan kowane musulmi; babba da qarami, namiji da mace, xa da bawa, saboda hadisin Ibnu-umar رضي الله عنهما- da ya gabata.
Kuma "mustahabbi" ne a fitar da ita ga xan-tayi da ke ciki; matuqar an busa masa rai; ma'ana: matuqar ya cika wata huxu, saboda magabata ''salaf'' sun kasance suna fitar da ita wa yaro, kamar yadda hakan ya tabbata daga Usman رضي الله عنه- da waninsa.
Kuma wajibi ne mutum ya fitar da ita ga kansa, da duk wanda ciyar da su yake wuyansa; kamar matarsa, xan'uwansa, haka kuma bawa; saboda ''sadakatu al-fixr" xinsa na kan shugabansa; dalilin haka shine: faxin Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم):
"لَيْسَ فِي الْعَبْدِ صَدَقَةٌ إِلا صَدَقَةُ الْفِطْر"([2]).
Ma'ana: (Ba a bada wata sadaka akan bawa in banda sadakatu alfixr).
Kuma ita wannan sadaka bata wajaba sai ga wanda ya ke da fiye da abinda zai ci –shi da iyalansa- da kuma buqatunsa na larura, ta ranar idi da darenta, wanda kuma da shi zai karya azuminsa. Don haka; ''zakatu al-fixr'' bata wajaba sai an samu cikar sharaxai guda biyu:
1-   Musulunci; saboda bata wajaba akan kafiri.
2-   Samuwar abinda ya fi qarfin abincinsa da abincin iyalansa, tare da samuwar abinda zai biya buqatunsa na asali, a ranar idi da kuma darensa.

Gava ta uku: Hikimar wajabta zakatul fixr:
          Yana daga cikin hikimomin da suka sanya aka wajabta ''zakatu al-fixr" abubuwan da ambatonsu ke tafe:
1-    Tsarkake mai azumi daga abinda ka iya aukuwa a cikin azuminsa na wargi ko batsa.

2-    Wadatar da fakirai da miskinai, wadatarwar da za ta hana su yin roqo a ranar idi, tare da shigar musu da farin ciki, domin idin ya kasance musu ranar farin ciki, kamar sauran vangarorin al'ummar musulmai; saboda hadisin Abdullahi xan Abbas رضي الله عنهما-:
"فَرَضَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم زَكَاةَ الْفِطْرِ طُهْرَةً لِلصَّائِمِ مِنَ اللَّغْوِ وَالرَّفَثِ،
وَطُعْمَةً لِلْمَسَاكِين"([3]).
Ma'ana: (Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya farlanta ''zakatu al-fixr" don ta zama tsarkaka ga mai azumi daga wargi da batsa, kana ta zama abinci ga miskinai).

3-    A cikinta akwai bayyanar da godiya wa Allah ta'alah kan ni'imar  cika azumin Ramadhan, da kuma tsayuwa a cikin darensa, da horewarsa ga bayinsa kan aikata abinda ya sauwaqa na aiki na-gari a wannan wata mai albarka.

Gava ta huxu: Gwargwadon wajibin zakkar fid-da-kai, tare da bayanin abubuwan da ake fitar da zakkar daga cikinsu:
Abinda yake wajibi a "zakatu alfixr" shine "sa'iy xaya" daga mafi rinjayen abincin mutanen gari; na alkama ko sha'ir, ko dabino, ko zabib, ko cukui (aqid([4])), ko shinkafa, ko masara, ko wanin haka; saboda tabbatansa daga Annabi (صلى الله عليه وسلم)  a cikin hadisai ingantattu, kamar hadisin Abdullahi xan Umar رضي الله عنه-  da ya gabata.
Kuma ya halatta jama'a da yawa su bada ''zakatu alfixr" ga mutum xaya, kamar yadda ya halatta mutum xaya ya bada zakkarsa ga jama'a.
Kuma baya halatta a fitar da qimar abinci daga kuxi; saboda yin hakan ya sava wa umurnin manzon Allah (صلى الله عليه وسلم), kamar yadda kuma ya sava wa aikin sahabban annabi; saboda sun kasance suna fitar da "zakatu al-fidr" ne daga abubuwan ci, kuma saboda "zakatu al-fidr" ibada ce da aka farlanta wa mutane cewa su fitar da ita daga jinsi sananne; wanda kuma shine abinci; don haka idan aka fitar da ita ba daga wannan jinsin ba, to ba zata wadatar ba.

Gava ta biyar: Lokacin wajabcin "zakatu alfixr" da fitar da ita:
Zakkar fid-da-kai tana wajaba da faxuwar rana na daren idi; saboda daga wannan lokacin ake karya azumin watan ramadhan. Kuma dangane da lokacin fitar da ita, tana da lokaci biyu: Lokacin bada ita mai falala, da kuma lokacin halacci, Amma lokacinta mai falala shine: Daga fuxuwar alfijir na ranar idi har zuwa dab da lokacin yin sallar idi; saboda hadisin Abdullahi xan Umar رضي الله عنهما-:
"أَنَّ النَّبِيَّ صلى الله عليه وسلم أَمَرَ بِزَكَاةِ الفِطْرِ قَبْلَ خُرُوجِ النَّاسِ إِلَى الصَّلاَة"(


[5]).
Ma'ana: (Lallai Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya yi umurni cewa a fitar da "zakatu alfidr" gabanin mutane su fita i zuwa sallar idi).
Amma shi kuma lokacin halacci: shine, gabanin idi da yini xaya ko kuma biyu; saboda Abdullahi xan Umar رضي الله عنهما- da wassu sahabbai na-daban sun aikata haka.
Ba ya halatta a jinkirta zakatul fixr i zuwa bayan sallar idi; idan har ya jinkirta, to ta zama sadaka daga cikin sadakoki, kuma ya yi laifi (zunubi) saboda wannan jinkiri; Annabi (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"مَنْ أَدَّاهَا قَبْلَ الصَّلاةِ فَهِيَ زَكَاةٌ مَقْبُولَةٌ، وَمَنْ أَدَّاهَا بَعْدَ الصَّلاةِ فَهِيَ صَدَقَةٌ مِنَ الصَّدَقَات"([6]).
Ma'ana: (Duk mutumin da ya bayar da ita gabanin sallar idi to wannan zakka ce karvavviya, duk kuma wanda ya bada ita bayan sallah to sadaka ce daga cikin sadakoki).



([1]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 1503), da Muslim (lamba: 984).
([2]) Muslim ya ruwaito shi (lamba: 982).
([3]) Abu-dawud ya ruwaito shi (lamba: 1609), da Ibnu-majah (lamba: 1827), da Alhaakim (1/409), ya kuma inganta shi, An-nawawiy yace: hadisi ne hasan -a cikin (Almajmu'u, 6/85), Albaniy shima ya ce: hasan ne (Sahihu Ibni-majah, lamba: 1492).
([4]) Aqid shi ake kira cukui da harshen hausa, shine kuma: nono da aka busar da shi, mai tsami.
([5]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 1503), da Muslim (lamba: 984).
([6]) Abu-dawud ya ruwaito shi (lamba: 1609), da Ibnu-majah (lamba: 1827), daga hadisin Abdullahi xan Abbas (رضي الله عنهما), Albaniy yace: hadisi ne hasan (Irwa'ul galil, lamba: 843).

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...