MUHIMMAN MAS'ALOLIN DA
HUKUNCINSU KE IYA VUYA
DANGANE DA AZUMI
Amsawar Shehin Malami, Abdul'aziz xan Abdullahi Ibnu-baaz, Allah yayi masa rahama, amin
NA XAYA DA NA BIYU:
YIN MAFARKI BAYA KARYA AZUMI,
HAKA KUMA JINKIRTA YIN WANKAN
JANABA
Tambaya:
Idan
mai azumi ya yi mafarki a cikin yinin ramadhana Shin azuminsa yana lalacewa, ko
a'a? kuma shin wajibi ne akansa ya yi gaggawan yin wanka? Kuma shin ya halatta
a jinkirta wankan janaba dana haila da kuma na biki? ([1])
Amsa: Shi dai mafarki baya lalata azumi;
saboda ya kan kasance ne ba da zavin Shi mai yin azumin ba, Amma kuma wajibi ne
akansa ya yi wanka matuqar ya ga ruwan maniyyi, da kuma zai yi mafarki bayan
sallar asubah, amma sai ya jinkirta wankansa har zuwa lokacin sallar azahar to
da babu laifi cikin hakan, haka kuma da zai yi jima'i da matarsa cikin dare
amma sai ya jinkirta wankansa zuwa bayan fudowar alfijir to babu qunci akansa
cikin hakan, saboda ya tabbata daga Annabi (صلى الله
عليه وسلم) cewa:
«كَانَ يُصْبِحُ جُنُبًا مِنْ جِمَاعٍ ثُمَّ يَغْتَسِل ويَصُومُ».
"Lallai Shi ya kasance yana wayan gari da janaba sakamakon
jima'i, sannan sai ya yi wanka ya kuma yi azumi"([2]).
Haka
itama mace mai haila da mai jinin biqi (haihuwa), da za su yi tsarki da daddare
saidai kuma basu samu su ka yi wanka ba sai bayan ketowan alfijir to basu da
wata matsala; kuma azuminsu ingantacce ne. Saidai kuma baya halatta a gare su,
haka Shima mai janaba su jinkirta wankan zuwa futowar rana, saboda wajibi ne
akansu su yi gaggawar yin wanka gabanin fudowar rana; domin su samu su yi
sallah a cikin lokacinta, kuma wajibi ne ga namiji ya yi gaggawan yin wanka don
ya riski sallar asuba a cikin jam'i([3]). Kamar yadda wajibi ne ga mai haila da
mai jinin biqi su yi gaggawan yin wanka idan suka ga alamun tsarki a cikin dare
domin su sallaci sallar magriba da ishah na wannan daren, kamar yadda jama'a
daga cikin sahabban Annabi (صلى الله عليه وسلم) su ka yi fatawa da haka, lamarin kuma
haka ya ke da za su yi tsarkin a lokacin la'asar dole ne su yi gaggawan wanka
domin su samu su sallaci azahar da la'asar gabanin faxuwar rana. Allah ne
majibincin dacewa!
NA UKU DA NA HUXU:
AZUMI BAYA LALACEWA DA YIN MAFARKI
HAKA BAYA LALACEWA DA FITAR
JINI KO AMAI:
Tambaya: Na kasance mai azumi sai na yi barci a masallaci, dana tashi
sai na samu cewa na yi mafarki, Shin mafarkin yana da tasiri ga azumina? Tare
da cewa banyi wanka ba sai kawai na yi sallah ba tare da nayi wankan ba.
Wata rana kuma dutse ya rotse min kai sai jini
ya kwarara, Shin azumina ya lalace saboda fitan jini?
Amsa: Lallai mafarki baya lalata azumi, kuma baya yi masa tasiri;
saboda kasancewarsa yana fita ne ba a cikin zabin mutum ba, Sai dai kuma wajibi
ne akansa ya yi wankan janaba idan har maniyyi ya fita daga gare shi, saboda Annabi
(صلى الله عليه وسلم) yayin da aka tambaye shi kan haka, sai ya amsa da cewa mai
mafarki zai yi wanka ne; idan har ya ga ruwa (maniyyi).
Sallar da ka aikata ta kuma ba tare da ka yi
wanka ba wannan jahilci ne daga gare ka, abun kyama, kuma dole ne akanka ka
sake sallah bayan ka yi wanka, kana mai tuba zuwa ga Allah (سبحانه وتعالى).
Shi kuma dutsen da ya rotse kanka har ya
kwararar da jinni babu komai akan haka.
Shi kuma amai da ya fita maka ba tare da zavinka
ba, to ba zai vata maka azuminka ba; saboda faxin Annabi (صلى الله عليه وسلم):
«مَنْ ذَرَعَهُ الْقَيْءُ فَلَا قَضَاءَ عَلَيْهِ، وَمَنِ
اسْتَقَاءَ فَعَلَيْهِ الْقَضَاءُ».
Ma'ana: "Wanda amai
ya rinjaye shi to babu ramukon azumi akansa, duk kuma wanda ya janyo amai to
wajibi ne akansa ya yi ramuko"([5]), Ahmad da ma'abota littafan "sunan"
suka rawaito shi da isnadi ingantacce.
$&$
NA BIYAR:
FITAR MAZIYYI DA SHA'AWA BAYA
KARYA AZUMI
Tambaya: Idan mutum
ya yi sumba alhalin yana azumi, ko kuma ya kalli wassu finafinai na tsiraici
sai maziyyi ya fita masa, Shin akwai ramukon azumi akansa? Idan kuma hakan ya kasance a cikin kwanaki ne
mabanbanta shin ramukon dole su zama a jejjere, ko za a iya yinsu a rarrabe?
Amsa: Fitan
maziyyi baya lalata azumi a maganar da ta fi inganci daga cikin maganganun
maluma guda biyu, lamarin haka ya ke sawa'un ya fita ne saboda sunbantar mata,
ko kuma ta hanyar kallon finafinai, ko kuma makamantan haka daga abubuwan da su
ke tada sha'awa.
Saidai kuma baya halatta ga musulmi ya kalli
finanai tsiraici da batsa, ko kuma sauraron abinda Allah ya haramta na sauraron
waqoqi, ko kayan kaxe-kaxe.
Fitar
maniyyi kuma da sha'awa to shi yana lalata azumi; sawa'un hakan ya auku ne
sakamakon runguma ko sumbanta ko maimaita kallo, ko makamancin haka daga cikin
sabbuban da su ke tada sha'awa; kamar wasan fitar da maniyyi (istimna'i), da
makamancinsa.
Yayin
da mafarki ko yin tunani su kuma azumi ba ya vaci da su, koda kuwa maniyyi ya
fita da sababinsu.
Kuma ba dole ba ne jerantawa wajen ramukon
ramadhana, hasalima ya halatta a rarrabe hakan, saboda gamewan faxin Allah
ta'alah:
ﭽ ﭵ ﭶ
ﭷ
ﭸ ﭹ
ﭺ ﭻ ﭼ ﭽ ﭾ ﭿ ﭼ البقرة: ١٨٤
Ma'ana: "Duk
wanda ya kasance daga cikinku maras lafiya
ko akan tafiya to sai ya qididdigi wassu yinin na daban",
[Baqarah: 184].
NA SHIDA:
HUKUNCIN MUTUMIN DA RUWA YA SHIGA CIKINSA BA TARE DA ZAVINSA BA
Tambaya: Mutum ne yake azumi sai ya yi
wanka da shawa (fanfo), to saboda qarfin tunkuxowar ruwan sai ya shige masa
cikinsa ba tare da zavinsa ba, Shin akwai ramukon azumi akansa? ([7])
Amsa: Babu ramukon azumi akansa; saboda
bai yi gangancin aikata hakan ba, sai hukuncin ya zama kamar na mutumin da aka
tilasta masa, ko mutumin da ya yi mantuwa.
NA BAKWAI:
HUKUNCIN HAXIYE MIYAU GA MAI AZUMI:
Amsa: Yawu baya cutar da azumi, don haka
idan mutum ya haxiye shi ba komai, kamar yadda in ya tofar da shi ba komai.
Amma kaki da yake fitowa daga qirji ko daga hanci, wanda larabawa ke kira
(nukhamah), ko kuma (nukha'ah) wanda shi kuma shi ne kaki mai kauri da yake
fitowa daga qirji ko kuma daga kai, irin waxannan wajibi ne ga mutum namiji ko
mace, su tofar ko fitar da shi, tare da rashin haxiye shi. Yayin da shi kuma
yawu na al'ada babu matsala akansa, kuma
baya cutar da mai azumi; namiji ne ko mace.
NA TAKWAS:
HUKUNCIN AMFANI DA NA'URAR FESA ISKA A CIKIN BAKI (INHALER) DON
MATSANANCIN BUQATA HAKA, A WAJEN MAI AZUMI:
Tambaya: Menene hukuncin amfani da na'urar maganin
da ake fesa iska a cikin baki (inhaler), ga mai azumi a cikin yini (wato: da
rana), ga mai ciwon quncin qirji da wahalar yin numfashi (Asma)? ([9])
Amsa: Hukuncinsa shine halacci; idan har
lalura ta buqatar da mutum zuwa ga hakan, saboda faxin Allah mabuwayi da xaukaka
a cikin "suratul an'aam":
ﭽ ﭚ ﭛ
ﭜ ﭝ ﭞ ﭟ ﭠ ﭡ ﭢ ﭣ ﭼ الأنعام: ١١٩
Ma'ana: "Kuma ya
muku dalla-dallan abubuwan da ya haramta su akanku, saidai wanda lalura ta buqatar
da ku zuwa gare shi", [An'aam: 119]. Kuma saboda kasancewarsa baya kama da ci da
sha, sai ya yi kama da jinin mutum da ake xauka
don aunawa ko bincike, ko kamar allurar da ba a sanya abinci a cikinta ba.
NA TARA:
HUKUNCIN CI KO SHA DA MANTUWA GA MAI AZUMI:
Amsa: Babu wata
matsala akansa kuma azuminsa ingantacce ne, saboda faxin Allah (سبحانه وتعالى) a qarshen suratul baqarah:
ﭽ ﯥ ﯦ ﯧ ﯨ
ﯩ ﯪ ﯫﯬ ﭼ البقرة: ٢٨٦
Ma'ana: "Ya Ubangijinmu kada ka kama mu idan muka yi mantuwa ko muka yi kuskure",
[Baqarah: 286]. Kuma ya inganta daga Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) cewa Allah ta'alah ya ce:
«قَدْ فَعَلْتُ».
Ma'ana: "Lallai na amsa"([11]). Da kuma saboda abunda ya tabbata daga
Abu-hurairah (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) lallai ya ce:
«مَنْ نَسِيَ وَهُوَ صَائِمٌ، فَأَكَلَ أَوْ شَرِبَ، فَلْيُتِمَّ
صَوْمَهُ، فَإِنَّمَا أَطْعَمَهُ اللهُ وَسَقَاهُ».
Ma'ana: "Duk wanda ya manta alhalin yana
azumi sai ya ci ko ya sha, to ya cika azuminsa; saboda Allah ne ya ciyar da
shi, ya kuma shayar da shi"([12]), Bukhariy da Muslim su ka rawaito shi.
NA GOMA:
HUKUNCIN ALLURAR JIJIYA DA TA DAMTSE KO GAVVAI
GA MAI AZUMI
Tambaya:
Menene
hukuncin amfani da allurar da ake yinta a jijiya, da wacce ake yi damtse ko a
gabbai ga mai azumi, menene kuma banbacinsu? ([13])
Amsa: Ingantaccen
magana shi ne: Gabaxayansu biyun (ta jijiya da ta damtse) basa vata azumi,
wanda kawai take vata azumi itace allurar da ake sanya mata abinci. Haka kuma xaukan
jini don bincike, shima azumi baya karyewa da shi, saboda akwai banbanci
tsakaninsu da yin qaho. Amma shi kuma qaho da wanda ya yi shi da wanda aka yi
masa dukkansu azuminsu ya karye, a maganar maluma da ta fi inganci, wannan kuma
saboda faxinsa (صلى الله عليه وسلم):
«أَفْطَرَ الحَاجِمُ وَالمَحْجُومُ».
NA SHA XAYA, DA SHA BIYU:
HUKUNCIN YIN AMFANI DA MAKILIN, DA MAXIGI
Tambaya:
Menene
hukuncin amfani da makilin xin goge haqora, da kuma maxigin kunne (magani),
dana hanci, dana ido, ga mai azumi? Kuma idan mai azumi ya ji xanxanonsu a cikin
maqogoronsa me zai aikata? ([15])
Amsa: Tsaftace haqora da makilin baya
karya azumin mai azumi, saboda hukuncinsa kamar yin aswaki ne, Saidai kuma
wajibi ne akansa ya kiyaye silalewan wani abu zuwa cikinsa, Amma inda wani abu
zai rinjaye shi ya shiga cikin cikinsa ba tare da nufi ba to babu ramuko
akansa.
Haka maganin xigawa a ido da kunne azumi baya
karyewa in an xiga su a zancen da yafi inganci daga zantukan maluma guda biyu,
Saidai kuma in har ya ji xanxanon abubuwan da ya xiga a maqogoronsa to ya rama
wannan azumin yafi tsentseni a gare shi, tare da cewa yin hakan ba wajibi ba ne
akansa, saboda kasancewar ido da hanci ba kafofi ne na shigar da abinci da abin
sha ba.
Amma
maganin da ake xigawa ta hanci to shi kam baya halatta; saboda kasancewar hanci
mashiga ne na abinci, don haka ne Annabi (صلى الله
عليه وسلم) ya ke cewa:
«وَبَالِغْ فِي الِاسْتِنْشَاقِ إِلَّا أَنْ تَكُونَ صَائِمًا».
Ma'ana: "Kuma ka kai maqura wajen shaqar
ruwa a hanci saidai in ka kasance mai azumi"([16]). Kuma wajibi ne ga mutumin da ya aikata
hakan ya rama azumi, saboda wannan hadisin da wadanda suke da ma'ana irin tasa,
matuqar ya ji xanxanon abun da ya xiga a cikin maqogoron nasa, Allah shi ne
majivincin dacewa.
NA SHA UKU:
HUKUNCIN SHAQAR TURARE (NA FESAWA DANA KONAWA)
Tambaya: Shin ya
halatta ga mai azumi ya shanshana qamshin turaren fesawa ko na gaushi da ake qonawa? ([17])
Amsa: Mai azumi ba zai shaqi turaren
wuta (Uud) ba, amma sauran turare waxanda ba na qonawa ba, to babu laifi
akansu, Amma turaren uud kam ba zai shanshane shi ba; saboda wassu maluma suna
ganin cewa wannan turaren yana karya azumi idan mai yinsa ya shake shi; saboda
ya kan tafi zuwa ga kwakwalwa, kuma tafiyat tasa ta kan zama da qarfi, Amma da
zai shaqe shi ba tare da nufi ba to ba zai karya masa azuminsa ba.
Tambaya: Shin a
cikin yinin ramadhana ya halatta ya yi amfani da tirare, misali: turaren uud na
mai da ake shafawa, da koloniya, da kuma turaren gaushi da ake qonawa? ([18])
Amsa: E, ya
halatta, da sharaxin kada ya shaqi turaren gaushi da ake qonawa.
NA SHA HUXU:
HUKUNCIN AMFANI DA TOZALI, DA KAYAN KWALLIYA A CIKIN YININ RAMADHANA
Tambaya: Menene
hukuncin amfani da tozali ko wassu kayan kwalliya ga mata a cikin yinin ramadhana,
kuma shin yana vata azumi ko a'a? ([19])
Amsa: Tozali
baya karya azumin 'ya mace, ko na namiji, a mafi ingancin zance guda biyu na
maluma, a kowani irin hali. Saidai kuma ayi amfani da shi da daddare shi ya fi
dangane da mai azumi mace ko namiji. Haka kuma abubuwan da mata ke ado da su na
sabulu ko mayuka, ko makamancin haka na dangin abubuwan da su ke alaqa da fata
kawai, misalin su qunshi (lalle), da kayan barbaxe-barbaxe da makamantan haka,
dukkan waxannan babu laifi ga mai azumi mace, ko namiji su yi amfani da shi,
tare da cewa baya halatta a yi amfani da kayan shafe-shafe matuqar zai cutar da
fiska (kamar canza mata kala), Allah shine majivincin dacewa!
NA SHA BIYAR:
YI DA MUTUM (GIBA) DA
ANNAMIMANCI DA ZAGI SAVO NE
DA SUKE YIN MIKI GA AZUMI, TARE DA TAUYE LADANSA
Amsa:
Yi
da mutum (wato: giba) baya cikin abubuwan da su ke vata azumi, Shi ne kuma:
ambaton mutum da abinda ya ke qi, saboda faxinsa mabuwayi da xaukaka:
ﭽ ﭟ ﭠ ﭡ ﭢ ﭼ الحجرات: ١٢
Ma'ana: "Kada sashinku ya yi gibar
sashi", [Hujuraat: 12].
Haka kuma annamimanci da zagi da qarya dukkansu
basa cikin abubuwan da su ke vata azumi, Saidai manya-manyan savo ne da ya zama
wajibi a kiyaye su, mai azumi da wanda ba mai azumi ba su nisance su, kuma
lallai suna kawo givi ga azumi, su kuma rage masa ladansa; saboda faxin Manzon
Allah (صلى الله عليه
وسلم):
«مَنْ لَمْ يَدَعْ قَوْلَ الزُّورِ، وَالْعَمَلَ بِهِ،
وَالْجَهْلَ، فَلَيْسَ لِلَّهِ حَاجَةٌ أَنْ يَدَعَ طَعَامَهُ وَشَرَابَهُ».
Ma'ana: "Duk wanda bai bar zancen qarya
da aiki da ita, da wauta ba, Allah bashi da buqatar ya bar abincinsa da abin
shansa" ([21]). Bukhariy ya rawaito shi a sahihinsa.
Da kuma saboda faxinsa:
«الصِّيَامُ جُنَّةٌ، فَإِذَا كَانَ يَوْمُ صَوْمِ أَحَدِكُمْ،
فَلَا يَرْفُثْ، وَلَا يَصخَبْ، فَإِنْ سَابَّهُ أَحَدٌ أَوْ قَاتَلَهُ،
فَلْيَقُلْ: إِنِّي صَائِمٌ».
Ma'ana: "Azumi garkuwa ne, idan ranar
azumin xayanku ya zo to kada ya yi batsa balle jima'i, kada kuma ya yi shewa,
idan wani ya zage shi ko ya nemi faxa da shi to ya ce: Ni mai azumi ne" ([22]). Bukhariy da Muslim su ka rawaito shi.
Hadisai kan
wannan mas'ala suna da yawa.
NA SHA SHIDA:
HUKUNCIN GANIN MATA GA MAI AZUMI, DA GAISAWA DA WAXANDA BA MUHARRAMANSA BA
Tambaya:
Idan
mutum ya yi dubi da-gangan ga mace ajnabiyyarsa (wacce ba haramcin aure a
tsakaninsu), saboda kyanta, ko tufarta ko jikinta, -alhalin yana azumi- Shin
azuminsa ya lalace ko kuma hakan makruhi ne; Allah zai iya karvar azuminsa, Sai
kuma ya yi sakayya a gare shi akan kallonsa? Ku mana fatawa akan haka, da fatan
Allah ya baku lada?
([23])
Amsa:
Haramun
ne akansa ya kalli mata, idan kuma da sha'awa ne haramcin ya fi tsanani, saboda
faxin Allah (سبحانه وتعالى):
ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄﮅ ﭼ النور: ٣٠
Ma'ana: "Ka ce da muminai su rintse daga ganinsu,
kuma su kiyaye farjojinsu", [Nuur: 30].
Kuma saboda kasancewar sake ido yana daga
cikin hanyoyin aukuwar alfasha, don haka wajibi ne rintse ido tare da kiyaye
dukkan sabbuban aukuwar fitina, Saidai kuma azuminsa ba zai lalace ba matuqar
maniyyi bai fita ba, Amma wanda ya yi maniyyi to shi azuminsa ya vaci, kuma
dole ya yi ramuko. Allah shine mai datarwa!
Tambaya: Menene
hukuncin mutumin da ya yi musabaha da matar da bata halatta a gare shi ba, ko
ya yi magana da ita a cikin yinin ramadhana alhalin yana azumi, itama tana
azumi, Shin hakan yana vata azumi, ko kuma rage masa lada? Fatan za a faxakar
da mu, kuma shin akwai kaffara ne akansa?
([24])
Amsa: Musabaha
da matar da akwai aure tsakaninku (ajnabiyya) baya halatta, wannan kuma saboda Manzon
Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
«إِنِّي لَا أُصَافِحُ النِّسَاءَ».
«وَاللهِ مَا مَسَّتْ يَدُ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ يَدَ امْرَأَةٍ قَطُّ، ما كان يُبَايِعُهُنَّ إلا بِالْكَلَامِ».
Ma'ana: "Ina rantsuwa da Allah! Hannun Manzon
Allah (صلى الله عليه وسلم) bai tava tava hannun wata mace ba, saboda bai kasance yana yi musu
mubaya'a ba sai da magana"([26]).
Wannan kuma tana nufin: Matar da akwai
halaccin aure a tsakaninsu, waxanda ba muharramai suke a gare shi ba. Amma ita
kuma wacce ta haramta ga mutum kamar yar'uwarsa, ko babarsa to babu laifi ya yi
musabaha da su.
Amma
dangane da yin magana da matar da akwai halaccin aure a tsakani: Idan har
magana ce ta halal wacce babu tuhuma ko kokonto akanta; kamar ace ya tambaye ta
kan 'ya'yanta, ko kan mahaifinta, ko kan wata buqata daga cikin buqatun
makwabta ko dangi to wannan babu komai, amma in kuma maganar ta kasance zance
ne da ya ta'allaqa da varna ko zina, ko sanya lokutan zina, ko mai tada
sha'awa, ko neman ta buxe wani vangare na jikinta dukkan waxannan basa halatta.
Yayin
da idan zancen ya zama tare da cikakken sitira da hijabi, babu kuma kokonto a
cikinsa da tuhuma, ba kuma akan sha'awa ba ne, to babu laifi akansu cikin irin
wannan maganar, saboda kasancewar Annabi (صلى الله
عليه وسلم) ya yi magana da mata,
kuma mata sun yi magana da shi, don haka babu qunci akan haka.
Azumin
kuma ya inganta; musabaha bata lalata shi, haka kuma zance yake, matuqar
maniyyi bai fita ta sanadiyyarsa ba, In kuma maniyyi ya fita to wajibi ne
akansa ya yi wanka, kuma azumin ya lalace, dole akansa ya biya shi –in har
azumin na wajibi ne.
Kuma
wajibi ne akan musulmi ya kiyayi abubuwan da Allah ya haramta masa, kada kuma
ya yi musabaha da matar da bata halatta ba a gare shi, kada kuma ya yi magana
da ita da sha'awa, ko ya kalli kyanta, saboda Allah yana cewa:
ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄﮅ ﮆ ﮇ ﮈﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍ ﮎ ﭼ النور: ٣٠
Ma'ana: "Ka ce da muminai su rintse wani
abu na ganinsu, kuma su kiyaye farjojinsu, yin haka shine yafi tsarki a gare
su, lallai Allah mai bada labari dangane da abinda suke aikatawa", [Nuur:
30]. Don haka; Kiyaye abubuwan da suke sabbaba sharri wajibi ne akan mumini a
duk inda ya ke. Muna roqon Allah ya kare mu tare da sauran musulmai daga dukkan
mummuna. Yabon Allah da sallamarsa su qara tabbata ga Annabinmu Muhammadu da
iyalansa da sahabbansa gabaxaya.
$&$
Allah ne masani, Wannan shine abinda na tato
mana daga littatafan Shehin Malami, Abdul'aziz xan Abdullahi Ibnu-baaz. Allah
yayi masa rahama.
Wallahu
a'alam ! ! !
([14]) An rawaito wannan lafazin
daga adadi da yawa na sahabban Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) Daga cikinsu akwai: Sauban (رضي الله عنه) Imam Ahmad ya rawaito hadisinsa (5/276), kuma an rawaito cewa
Imam Ahmad ya ce: Hadisin Sauban shine mafi ingancin abinda aka ruwaito a
wannan babin. Kamar yadda Imam Ahmad ya sake rawaito shi daga hadisin: Rafi'i xan
Khadij (رضي الله عنه) (3/465), da Abu-dawud
(lamba: 2367-2371), da Tirmiziy (lamba: 774) ya kuma inganta shi, da Alhakim a
cikin "Almustadrak", (lamba: 1561), ya inganta shi, kuma Imam Zahabiy
yayi masa muwafaqah (1/591).
Allah ya saka da alkhairi
ReplyDelete