HUXUBAR MASALLACIN ANNABI (r)
JUMA'A, 23/RAMADHAN/1436H
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI ABDULBARIY XAN AWWADH AS-SUBAITIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya
cike watan ramadhana da qarin falala da lada,
Ina gode masa (سبحانه) kuma ina yaba masa, akan abinda yayi
na kevance mu da waxannan kwanakin guda goma, Ina kuma shaidawa babu abun bautawa da
gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokan tarayya, Halitta nasa ne, kuma shari'a itama tasa ce.
Sannan ina shaidawa cewa lallai shugabanmu
kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa, Shine wanda ya qara zage damtse don neman
dacewa da lailatul qadari
Allah ya yi daxin salati a gare Shi, da kuma
iyalansa da sahabbansa, duk lokacin da wata ta haskaka, ko kuma alfijir ya keto.
Bayan haka;
Ina yi muku wasici, da Ni kaina da jin tsoron
Allah, Allah yana cewa:
"Ya ku waxanda suka yi imani ku
ji tsoron Allah ku ji tsoron Allah iyakar jin tsoronsa, Kuma kada ku mutu face kuna musulmai", [Ali-imran:
102].
Mahaxar mahaxoxi, lokacin taskance falaloli, kana lokacin da ake komowa da ribobi da
ganima, Duka; a Waxannan kwanaki goman da suka sauko
mana, Kyaututtuka masu qamshi da
gamsarwa suke samun tsarkakan zukata,
Zunubai kuma suke zovewa daga jikin waxanda duk suka qanqan-da kansu ga
Allah, Addu'oi suna hauhawa, Rahamomi kuma suna sassauqa, Yayin da aljannonin Allah su kuma suke ta
yin shiri ga salihan bayi.
A cikin waxannan darare guda goma ake yin rige
don samun yardar Allah, da yin gasa
cikin fagagen yi masa biyayya, Su
kuma masu hankali sun san cewa lokacin da aka xibar wa wannan rayuwar gajeru ne
(basu da tsayi), Ajalin mutane kuma ba sanannu ba ne, Kamar yadda shiga cikin fagen tsere shi
kuma yake sanya musulmi ya riqa zaton
riskar waxanda suka fi shi gudun duniya da yawan bauta, da yin da'awa, Allah maxaukaki yana cewa:
"Waxanda suka yi rigaye (wajen aiki) sune masu yin
rigaye (wajen samun sakamako) * Waxannan sune makusanta"
[Waqi'ah: 10-11].
Ya kuma ce:
"Sai kuyi gaggawan aikata alkhairi"
[Baqarah: 148].
Kuma lallai duk wanda yayi rigaye zuwa ga
aikata alkhairi a duniya to
shine mai yin rigaye a lahira zuwa ga
ajannoni.
Mutumin
da yayi sakaci a farkon watan ramadhana, sai kuma ya kyautata aiyuka a kwanakin
qarshensa yafi alheri fiye da wanda ya kyautata aiki a farkon kwanakin amma sai
yayi sakaci a qarshensu; wannan kuma
saboda faxin Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم):
"Lallai aiyuka su kan samu fifiko ne ko qaranta da
abubuwan da suka kasance a qarshensu", Bukhariy ya rawaito
shi. Su kuma darare guda goman
qarshe na ramadhana sun fi girmar falala akan kwanaki ashirin da suka rigaye
su, a dunqule.
Annabi
(صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana qarin qoqari ta fiskar bauta, a cikin darare
goman qarshe na ramadhana, irin abinda baya yin makamancinsa a waninsu, kuma ya kasance yana yin i'itikaafi a
cikinsu, yana neman dacewa da
lailatul qadari.
A'ishah
(رضي الله عنها) tana cewa:
"Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kasance idan kwanakin nan guda goma suka shiga, sai ya tamke kwarjallensa, ya raya darensa, ya kuma tayar da iyalansa",
Bukhariy ya rawaito shi.
(Hadisin nan) jumloli ne guda uku gajeru da
suke yin cikakken bayani kan shiriyar annabinmu a cikin waxannan kwanaki ko
darare guda goma, Saboda tare da
manya-manyan aiyukan annabinmu mai karamci, da kuma nauyin da ya rataya a
wuyansa dangane da al'ummarsa, da wajibabbun addininsa, da haqqoqin
iyalansa, to kuma yana da wani
sha'anin na-daban a cikin dararen nan guda goma, ta fiskar tsayuwa a cikin sallah da zama, da
sujjada, da yin zikiri da tasbihi,
Kuma –kunga- yana aikata hakan tare da cewa an gafarta masa duk abinda
ya gabata na zunubansa!
Cewa kuma da aka yi (Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya kasance yana tayar da iyalansa daga barci) don yin sallah,
A farko: Munga tsayuwarsa wajen aikata
abinda yake wajibi akansa dangane da iyalansa da mutanen gidansa, Wannan kuma jan hankali ne a tarbiyyance
da yake hukunta cewa Iyaye su himmantu wajen qara kwarin guiwa da kuma bunqasa
himmar 'ya'yansu, da qara cike himma ko azamar sauran iyalansu, wajen bautansu ga Allah, Saboda kamar yadda muke kwaxayin ganin
duniyarsu ta yi kyau, To muyi kwaxayi
wajen ganin lahirarsu tayi kyau shine yafi zama wajibi kuma shi yafi dacewa.
Kuma kwaxaitar da iyalai kan yin ibada, da
tayar da su daga barci don aikata ta,
yana neman qarin haquri kan tarbiyya,
da kuma qarin kwazo wajen faxakarwa,
tare da nuna cewa iyaye sun xauki nauyin da ya rataya a wuyansa, saboda
"Dukkanku
mai kiyyo ne, Kuma za a tambaye shi akan abin kiyyonSa".
Yana
cikin alamun rashin rabo, da rafkana:
Yadda sashin mutane suke ajiye lokacin alkhairi da ibada a gefe, tare da yawo kasuwanni, da yin wargi ko
kallon wargin, da yawaita barci.
Wannan kuma vangare ne na wasan da Shexan yake yi da mutane da kuma
vatar da su, Allah (تعالى) yana cewa:
"Lallai bayina baka da wani iko akansu na vatar da
su, Kuma Ubangijinka shine majivinci"
[Isra'i: 65].
Cewa
kuma da aka yi (Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya kan qara tamke kwarjallensa –a
cikin dararen nan guda goma): kinaya ce kan qarin shiri wa ibada, da yin xamara
don yin xa'a, tare da yin qoqari a
cikin dararen nan guda goma, qari akan
abinda Annabi ya saba.
Saboda
lokaci a cikin waxannan kwanaki goma yana da tsada, awoyinsa kuma suna da
muhimmanci, daqiqoqinsu kuma suna da
qima, kasancewar wata kyauta ko
rahama (daga Allah) zata iya sauka akanka a cikin kowace daqiqa sai ka rabauta
da ita, rabauta irin ta har abada,
Kuma ta yiwu a amsa maka wata addu'a da zata zama sababin jefa ka cikin
ni'imomin aljannah da qoramunta.
Ita
kuma ma'anar jumlar da take cewa: (Annabi yana raya darensa) tana nufin: Yana yin tsayuwar mafi yawancin sa'oin
daren, A'ishah (رضي الله عنها) tana cewa:
"Ban san cewa Annabi –صلى
الله عليه وسلم- ya tava karanta alqur'ani
gabaxayansa a cikin dare xaya ba, ko kuma ya yi sallar dare har zuwa
asuba, Kuma bai tava azumtar wata
cikakke ba in banda watan ramadhana"
[Muslim ya rawaito shi].
A
cikin waxannan dararen guda goma ganawa da Allah ta'alah a voye ta kan yi zaqi
ko daxi, nesa da ganin mutane ko jinsu,
Kuma a cikin wannan ganawar zuciya ta kan samu kevewa da Allah, ta bar
duk abinda ba shi ba, Zuciyar tana
siffanta da qasqanci irin na bauta,
tare da tsananta neman afuwa da gafara daga wajen Allah mai afuwa da
gafara, Kuma rai zai nuna kwaxayi da
fatan samun rahama daga Allah mai rahama mai jin qai, Kuma a cikin wannan ganawar ake godiya
wa Allah da yabonSa, da kuma yin addu'a, tare da tsarkake Allah,
Manzon Allah (صلى الله
عليه وسلم) yana cewa:
"Lallai Allah yana son bawa mai taqawa, mawadaci,
voyayye", [Sahihu Muslim].
Kuma
ba abu ne voyayye ba; Lallai
ginshiqin da ake gina karvar aiyuka akansa shine inganta niyyoyi, Kuma lallai yin aiki tuquru wajen gyaran
niyyah da kuma tsaftace ta, musamman a cikin waxannan kwanakin guda goma =
lamari ne mai girma, kuma yana da
tasiri babba, saboda aikata hakan ya
kan sanya sakamakon aiki ya zama maxaukaki mai girma.
Sufyan
(As-sauriy) yana cewa:
"Ban tava qoqarin magance wani abu ba; wanda yafi
tsanani akaina fiye da niyyata; saboda niyyata tana jujjuye mini, tana jirkita,
tana caccanzawa".
Ita
kuma niyya tana hukunta duk aikin da bawa zai yi, da sadakarsa, da sallarsa, da
karatunsa = su zama ga Allah tsantsa, ba
tare da neman wata ganima ko wani matsayi, ko neman mutane su ji shi ba, ko
kuma wassu halayyan duniya na daban;
Kuma Allah baya karvar aiki sai wanda aka yi shi ga Allah tsantsa; shi
kaxai bashi da abokin tarayya, Allah
ta'alah yana cewa:
"Addini tsarkakakke na Allah ne"
[Zumar: 3].
Kuma koyan niyya yafi muhimmanci fiye da yin
aikin.
Manzon Allah (صلى الله
عليه وسلم) yace, Allah (تبارك وتعالى) yace:
"Duk wanda ya aikata wani aiki sai ya haxa ni da
wanina a cikinsa, Na kyale shi; shi da
shirkarsa" .
…
…
HUXUBA TA BIYU
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai,
mai rahama mai jin qai, mamallakin ranar sakamako, Ina shaidawa babu abun bautawa da gaskiya
sai Allah, Ubangijin halittun farko
da na qarshe, Kuma ina shaidawa
lallai annabi Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa ne, Shugaban masu taqawa, Allah yayi qarin salati a gare shi, da
kuma iyalansa da sahabbansa, gabaxaya,,,
Bayan haka:
Ina
yi muku wasici da kuma ni kaina, da jin tsoron Allah, Allah yana cewa:
"Ya ku waxanda suka yi imani ku
ji tsoron Allah, kuma ku kasance tare da masu gaskiya", [Taubah: 119].
Bayan 'yan kwanaki kaxan al'ummar musulmai
zasu yi bikin ni'imar cikan watan ramadhana, Kuma zasu yi farin ciki ta hanyar yin
idi; wanda aka shar'anta Yin KABBARA a cikinsa tun daga faxuwar ranar daren idin, har zuwa lokacin da zasu yi
sallar idin, Allah yana cewa:
"Kuma domin ku cika qirge, kuma domin ku girmama
Allah akan shiriyarSa da yayi muku.
Kuma tsammaninku zaku gode" [Baqarah: 185].
Abdullahi xan Mas'ud (رضي الله عنه) ya kasance yana cewa:
ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL
LAHU, WALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMDU.
An rawaito daga Abdullahi xan Abbas (رضي الله عنهما) yana cewa:
ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA
LILLAHIL HAMDU, ALLAHU AKBAR WA AJALLU,
ALLAHU AKBAR ALA MA HADANA.
[Albaihaqiy ya rawaito
shi].
Salmanu
–Alfarisiy- (رضي الله عنه) ya kasance yana karantar da mutune
wannan kabbarar, Sai yace:
Ku yi kabbara da yin ALLAHU AKBAR, ALLAHU
AKBAR, ALLAHU AKBAR KABIRAN,
[Albaihaqiy].
Kuma
an sunnanta wa maza suyi ta xaga sautinsu da kabbarori a cikin masallatai da
gidaddaji da kasuwanni, suna masu
shelanta girmama Allah, tare da
bayyanar da yi masa bauta, da gode masa.
Kuma
Allah ya shar'anta mana bada zakkar fid-da-kai (fixr), kuma lallai ita tsarkaka ce ga mai azumi,
daga wargi da kwarkwaso, kuma abinci
ne ga miskinai, Zakkar ta kan kasance
sa'iy guda xaya na alkama da dabino da zabib (busasshen inabi), ko shinkafa da
makamancinsa daga jinsin abubuwan ci,
Ana bada ita a madadin yara da manya, da namiji da mace, da xa da bawa,
daga cikin musulmai. Mafificin lamari
shine a bada ita gabanin yin sallar idi,
Amma ya halatta a fitar da ita gabanin idi da kwana xaya ko biyu.
Kuma
mustahabbi ne yin wanka, da fesa turare ga maza, gabanin fitansu zuwa ga
sallar, saboda ya tabbata daga Sa'idu
xan Jubair (رضي الله عنه) lallai shi yace:
"Sunnar idi abubuwa ne guda uku: Yin tafiya da
qafa, da yin wanka, da kuma cin abinci gabanin fita izuwa ga sallah".
Haka
kuma yin ado da mafi kyan tufa (shima sunnah ne), Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana da wata alkebba (ta musamman) wacce yake sanya
ta ranar idi da ranar juma'a, Kuma ya
inganta cewa Abdullahi xan Umar, ya kasance yana sanya mafi kyan tufafinsa a
lokacin idi.
Amma
su kuma mata zasu nisanci yin ado idan zasu fita, saboda an hana su bayyanar da
adonsu ga mazajen da ba muharramansu ba.
Haka kuma yana haramta ga matar
da zata fita waje ta shafa turare, ko tayi irin bijirowar da zata fitini
mazaje.
Da
kuma cin dibino witiri, gabanin ya fita zuwa filin sallar idi (shima wannan
sunnah ne), saboda abinda Albukhariy
ya rawaito daga Anas (رضي الله عنه) yace:
"Manzon Allah –صلى
الله عليه وسلم- ya kasance a sallar azumi
baya fita wurin sallah har sai yaci dabino", A wani lafazin kuma
"yana
cinsu witiri".
Kamar
yadda yin gaisuwar idi itama mustahabbi ce,
saboda hakan ya tabbata daga sahabbai (رضي الله
عنهم), Misalinsa kuma shine kamar kace: ALLAH YA KARVA MANA MU DA KU (تقبل الله منا ومنكم), Da wassun wannan daga
cikin laffuzan gaishe-gaishen idi na halal.
Allah
(تعالى) yana cewa:
"Kuma domin ku cika qirge, kuma domin ku girmama
Allah akan shiriyarSa da yayi muku.
Kuma tsammaninku zaku gode" [Baqarah: 185].
Huxubar ta qare,,, ,,, ,,,
………………
Salati wa Annabi, da addu'oi
………………
No comments:
Post a Comment