2015/07/10

BADA HASKE KAN IBADAR I'ITIKAFI

HASKAKAWA KAN IBADAR I'ITIKAAF

(إضاءات حول الاعتكاف)

Haske na farko: Bayani akan menene i'itikaaf, da hukuncinsa:
1-     Ta'arifinsa: Kalmar "I'itikaaf" a harshen larabci tana nufin: lazimtar abu, da killace kai akansa.
A shari'ar Musulunci kuma tana nufin: Musulmi wanda ake kira "mumayyiz –wato: wanda ya san fari-da-baqi, koda bai balaga ba-" ya lazimci wani masallaci daga cikin masallatai, don yin xa'a ga Allah mabuwayi da xaukaka.

2-     Hukuncin "I'itikaaf": Sunna ne, kuma kusanci ne i zuwa ga Allah ta'alah; saboda faxinsa mabuwayi da xaukaka:
(أنْ طهّر بيتي للطائفين والعاكفين والركع السجود) [البقرة: ١٢٥].
(Cewa ku tsarkake xakina ga masu xawafi, da masu I'itikaaf, da kuma masu ruku'i da sujjada –sallah-) [Baqarah: 125].
Wannan aya dalili ce da ta bayyana cewa "I'itikaaf" an shar'anta shi har ga al'ummomin da su ka shuxe, Da kuma saboda faxinsa maxaukakin sarki:
(ولا تباشروهن وأنتم عاكفون في المساجد) [البقرة: ١٨٧].
(Kuma kada ku taki matanku alhalin kuna aikata "I'itikaaf" a cikin masallatai) [Baqarah: 187]. Kuma ya zo daga A'ishah - رضي الله عنها- cewa:
"أَنَّ النَّبِيَّ r كَانَ يَعْتَكِفُ العَشْرَ الأَوَاخِرَ مِنْ رَمَضَانَ حَتَّى تَوَفَّاهُ اللَّهُ"([1]).
(Lallai Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya kasance yana yin "I'itikaafin" kwanaki goman qarshen ramadana, har Allah ta'alah ya karvi ransa).
Kuma dukkan musulmai sun yi "ijma'i" kan kasancewan "I'itikaaf" abu ne da shari'a ta zo da shi, kuma sunna ne, da bata wajaba akan mutum sai dai in ya wajabta ta akan kansa; kamar a ce ya yi bakancen aikata shi.
Don haka; kasancewar "I'itikaaf" shari'a ne ya tabbata da dalilai na alqur'ani, da sunna da kuma "ijma'i".

Haske na biyu: Sharuxan "i'itikaaf":
"I'itikaaf" ibada ne da yake da sharuxa, kuma lallai ba ya inganta sai da su, Kamar haka:

1-     Dole mai i'itikafin ya zama musulmi, mumayyizi, mai hankali: Saboda i'itkafin "kafiri" ba ya inganta, haka shima mahaukaci idan da zai yi, da kuma yaro qarami wanda bai kai shekarun banbance fari-da-baqi (mumayyizi) ba. Amma "balaga da mazantaka" su ba a sharxanta su; saboda haka; i'itikafin mutumin da bai balaga ba matuqar dai "mumayyizi" ne da ya kai shekaru bakwai (7) ya inganta, haka kuma i'itikaaf na inganta daga mace.

2-     Niyya: Wannan kuma saboda faxinsa (صلى الله عليه وسلم):
"إِنَّمَا الأَعْمَالُ بِالنِّيَّات"([2]).
Ma'ana: (Lallai dukkan aiyuka su kan inganta ne tare da niyya). Sai mai "I'itikaaf" ya niyyaci lazimtar gurbin "I'itikafinsa", da nufin xa'a da bauta wa Allah mabuwayi da xaukaka.

3-     Dole "I'itikafin" ya zama a masallaci ne: Wannan kuma saboda faxinsa maxaukakin sarki:
(وأنتم عاكفون في المساجد) [البقرة: ١٨٧].
Ma'ana: (… alhalin ku kuna aikata "I'itikaaf" a cikin masallatai) [Baqarah: 187]. Da kuma saboda aikinsa (صلى الله عليه وسلم); domin ya kasance ya kan yi "i'itikaaf" ne kawai a masallaci, kuma ba a "ruwaito" cewa wata-rana ya yi "I'itikaaf" a wanin masallaci ba.

4-     Sa'annan masallacin da ya ke "I'itikafin" a cikinsa dole ya kasance ana tsayar da sallar "jam'i" a cikinsa: Wannan kuma an sanya shi ne a matsayin sharaxi saboda idan har lokacin da ya yanka ma kansa na "I'itikafin" sallar farilla za ta riqa samuwa a cikinsa, kana kuma shi mai "I'itikafin" yana daga cikin waxanda halartar sallah cikin jam'i yake wajibi akansu; saboda yin I'itikafi a masallacin da ba a tsayar da jam'i a cikinsa zai hukunta qauracewa "sallah cikin jam'i" ga wannan bawan, alhalin kuma halartarta wajibi ne akansa, ko kuma ya rika fita i zuwa ga "jam'in" akai-akai; wanda hakan na baran-baran da "maqasudin" I'itikaaf". Amma mace kam yana inganta a gare ta da ta yi "i'itikaafinta" a kowani masallaci; sawa'un ana yin sallah cikin jam'i ko a'a. Wannan kuma idan ba wata fitinar da za ta haifu sakamakon "I'itikaafinta"; Amma idan "I'itikaafin" nata zai janyo wata fitina to anan kam wajibi ne a hana ta. Abun da ya yi fi falala kuma shine masallacin da za a yi "i'itikaafin" ya zama ana tsayar da sallar "juma'a" a cikinsa, sai dai hakan ba sharaxi ne na "i'itikaafi'' ba.

5-     Tsarkakuwa daga "babban hadasi": Don haka; i'itikafin "mai janaba da mai haila da mai jinin haihuwa" ba ya inganta; saboda bai halatta waxannan su zauna a masallaci ba.
Lallai "yin azumi" ga mai "i'itikaafi" ba sharaxi ba ne, wannan kuma saboda abinda aka ruwaito daga Abdullahi xan Umar رضي الله عنه- cewa lallai Umar رضي الله عنه-, ya ce:
"يَا رَسُولَ اللهِ إِنِّي نَذَرْتُ فِي الْجَاهِلِيَّةِ أَنْ أَعْتَكِفَ فِي الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ لَيْلَةً، فَقَالَ: أَوْفِ بِنَذْرِك" ([3]).
Ma'ana: (Ya Manzon Allah! Lallai ni na yi bakancen zan yi "I'itikaafin" dare guda a masallaci mai alfarma –makka-, a jahiliyya? Sai ya ce: Ka cika bakancenka). A nan da yin azumi sharaxi ne na "I'itikaafi" to da Annabi ba zai halatta a yi I'itikafi da daddare ba; saboda ba a yin azumi a cikin dare. Daxin-daxawa kuma "I'itikaafi, da yin azumi" ibadodi ne guda biyu mabanbanta; don haka ba a sharxanta samar da xayansu gabanin ingancin xayan.

Haske na uku: Zamanin I'itikaaf, da mustahabbobinsa, da bayanin abubuwan da aka halatta ga mai i'itikaaf:
1.     Lokacin yin i'itikaafi da zamaninsa: Zama a cikin masallaci na wani gwargwado ko yanki na lokaci ko zamani shine rukunin I'itikaaf, saboda da za a rasa zama a cikin masallaci na wani yanki daga cikin lokaci to da I'itikafin bai qullu ba.
Amma dangane da mafi qarancin lokacin I'itikaafi kuma akwai savanin maluma akansa, amma ingantacciyar magana –in sha Allah- itace: bashi da iyaka ta fiskar mafi qarancin lokacinsa; don haka I'itikaafi yana inganta idan aka yi shi cikin xan wani gwargwado na daga lokaci, koda kuwa kaxan ne, Sai dai kuma mafificin lamari shine kada I'itikaafin ya zama qasa da yini xaya da kwana; saboda Annabi (صلى الله عليه وسلم) da sahabbansa ba a ruwaito cewa sun yi I'itikafin qasa da haka ba.
Kuma mafificin lokatan I'itikaafi shine: kwanaki goman qarshen ramadana; saboda hadisin A'ishah - رضي الله عنها- da ya gabata:
"أَنَّ النَّبِيَّ r كَانَ يَعْتَكِفُ العَشْرَ الأَوَاخِرَ مِنْ رَمَضَانَ حَتَّى تَوَفَّاهُ اللَّهُ"([4]).
Ma'ana: (Lallai Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya kasance yana yin "i'itikaafin" kwanaki goman qarshen ramadana, har Allah ta'alah ya karvi ransa).
Amma da mutum zai yi i'itikaaf ba a wannan lokacin ba, to i'itikafinsa ya halatta, sai dai ya aikata savanin abinda ya fi falala.
Duk wanda ya yi niyyar ya yi i'itkaafin kwanaki goma na qarshen watan ramadana to zai yi sallar asubar ranar ashirin da xaya (21) a masallacin da ya niyyaci aikata i'itikafi a cikinsa, sa'annan sai ya shiga cikin bautarsa (i'itikafinsa). Kuma i'itikafinsa zai qare ne idan rana ta faxi, na yinin qarshen a watan azumi (ramadana).

2.     Mustahabban i'itikafi: I'itikafi ibada ne da bawa ke kevewa a cikinsa da Ubangijinsa, tare da yanke alaqoqi da duk wanda ba shi ba, don haka "mustahabbi" ne mai i'itikafi ya kevanta da yin ibadodi; ta yadda zai yawaita yin salloli da zikiri (ambaton Allah), da addu'oi da karatun alqur'ani, da tuba da istigfaari, da makamantan haka; na nau'ukan xa'a da za su kusantar da shi i zuwa ga Allah ta'alah.

3.     Abubuwan da aka halatta ga mai I'itikaafi: An halatta masa fita daga masallaci don aikata abinda ba makawa a gare shi sai ya aikata shi; kamar cin abinci da shan abin sha; idan bashi da wanda zai halarto masa da su, haka kuma fita don biyan buqata, da kuma yin alwala idan ya yi hadasi, da kuma wankan janaba. Kuma an halatta masa yin magana da mutane, cikin abinda ke da fa'ida, da tambayan yaya halinsu? Amma maganganun da basu da amfani, ko kuma babu lalurar yinsu: waxannan kam suna baran-baran da maqasudin i'itikaafin, da kuma abinda aka shar'anta i'itikaafin don shi. Kuma an halatta  masa cewa wassu daga cikin iyalansa da danginsa su ziyarce shi, su kuma yi zance da shi na xan wani lokaci, haka kuma an halatta masa ya fita daga gurbin i'itikafin nasa don ya yi bankwana da su (ya musu rakiya); wannan kuma saboda hadisin Safiyyah - رضي الله عنها- ta ce:
"كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم مُعْتَكِفًا فَأَتَيْتُهُ أَزُورُهُ لَيْلا، فَحَدَّثْتُهُ ثُمَّ قُمْتُ فَانْقَلَبْتُ،
فَقَامَ مَعِي لِيَقْلِبَنِي"([5]).
Ma'ana: (Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya kasance yana i'itikaafi, sai na zo masa a cikin dare don na ziyarce shi, na kuma yi masa taxi, sa'annan sai na tashi zan koma, sai shima ya tashi don ya raka ni); ma'ana: ya mayar dani i zuwa xakina.
Kuma halal ne ga mai i'itikaafi ya ci abinci, ya sha abin sha, ya yi barcinsa a masallaci, tare da kula da tsaftar masallacin, da kuma alfarmansa.

Haske na huxu: Abubuwan da suke vata "i'itikafi":
I'itikaafi yana vaci da abubuwa masu zuwa:
1-     Ficewa daga masallaci ba tare da buqata ba; da-gangan; koda kuwa lokacin fitan ya yi qaranci; wannan kuma saboda hadisin A'ishah - رضي الله عنها-:
"وَكَانَ لاَ يَدْخُلُ البَيْتَ إِلا لِحَاجَةٍ؛ إِذَا كَانَ مُعْتَكِفًا"([6]).
Ma'ana: (Annabi ya kasance baya shiga gida sai don buqata, idan ya kasance yana i'itikaafi). Da kuma saboda kasancewar fitan yana sarayar da zama a gurbin i'itikaafi, alhali kuma shi zaman (a cikin masallaci) shine rukunin i'itikaafi.

2-     Yin jama'i: Koda kuwa a cikin dare ne, koda kuma a wajen masallaci ya yi shi; wannan kuma saboda faxinsa maxaukakin sarki:
(ولا تباشروهن وأنتم عاكفون في المساجد) [البقرة: ١٨٧].
Ma'ana: (Kuma kada ku taki matanku alhalin kuna aikata "i'itikaaf" a cikin masallatai) [Baqarah: 187].
Yana xaukar hukuncin "jima'i": fitar da maniyyi da sha'awa; ba tare da an samu yin jima'i ba; kamar ta hanyar wasa da al'aura har maniyyi ya fito "istimna'i", da rungumar mata da bai kai i zuwa ga saduwa ba.

3-     Fitar hankali: I'itikaafi yana lalacewa da samuwar hauka, da maye; saboda mahaukaci da wanda ke cikin maye sun fita daga cikin waxanda bauta ke wajaba a kansu.

4-     Haila da nifasi; Wannan kuma saboda baya halatta ga mai haila da mai jinin nifasi su zauna a cikin masallaci.

5-     Yin ridda: Wannan kuma saboda yin ridda na yayi hanun-riga da bauta, kuma saboda faxinsa maxaukakin sarki:
(لئن أشركت ليحبطن عملك) [الزمر: ٦٥].
Ma'ana: (Da zaka yi shirka to da ayyukanka sun ruguje)  [Zumar: 65].


Allah ne masani  !


([1])  Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 2020), da Muslim (lamba: 1172).
([2]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 1), da Muslim (lamba:  1907)
([3]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 2032), da Muslim (lamba:  1656)
([4])  Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 2020), da Muslim (lamba: 1172).
([5])  Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 2035), da Muslim (lamba: 2175).
([6])  Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 2029).

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...