SAUKAR ALQUR'ANI A RAMADHANA
Tambaya: Shin za a iya koya daga
"muraja'ar qur'ani da Mala'ika jibrilu yayi ta yi da Annabi Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) a ramadhana "falalar sauqar alqur'ani" a cikin watan azumi? ([1])
Amsa: Daga bitar da mala'ika jibiru (عليه السلام) ya yi ta yi tare da Annabi Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) ana fa'idanta cewa yin hakan yana da falala, kuma mustahabbi
ne ga musulmi ya riqa bitar alqur'ani tare da wanda zai fa'idantar da shi ya
kuma amfanar da shi (malami), saboda kasancewar Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya aikata hakan tare da Mala'ika Jibrilu (عليه السلام) don ya fa'idanta, kasancewar shi Jibrilu shi ne yake zuwa masa
da alqur'ani daga wajen Allah mabuwayi da xaukaka, kuma shi ne jakada (dan
aika) tsakanin Allah da dukkan Manzanninsa, don haka Mala'ika Jibrilu babu makawa
zai amfanar da Annabi (صلى الله عليه وسلم) wassu abubuwa daga wajen Allah
ta'alah, ko ta fiskar harrufan alqur'ani, ko ta fiskar ma'anoninsa da Allah ya
ke nufi da shi. A kan haka idan mutum ya yi bitar alqur'ani tare da wanda zai
taimake shi wajen fahimtar saqon da alqur'anin ke xauke da shi, ko ya taimake
shi wajen iya tsayar da harrufansa to lallai hakan abun nema ne, kamar yadda Annabi
(صلى الله عليه وسلم) ya yi muraja'rsa tare da Jibrilu. Wannan kuma ba wai yana nuna
cewa Mala'ika Jibrilu ya fi Annabi Muhammadu (صلى الله
عليه وسلم) falala ba, Saidai yana
nuna cewa Mala'ika Jibrilu shi ne ya zo daga wajen Allah ta'alah a matsayin
jakadan da ke isar wa Manzon Allah (صلى الله
عليه وسلم) abin da Allah ya yi
umurni da shi na wahayin alqur'ani, ta fiskar lafazi da ta fiskar ma'ana, Don
haka; Shi kuma Annabi Muhammadu (صلى الله
عليه وسلم) yana amfana da Jibrilu
ta waxannan fiskokin. Baya nuna cewa Jibrilu ya fi Annabi Muhammadu falala;
A-a, Annabi (صلى الله عليه وسلم) shi ne fiyayyen 'yan Adam, kuma ya fi
dukkan Mala'iku falala, yabon Allah da sallamarsa su qara tabbata a gare shi.
Kuma
lallai wannan bitar tana da alheri da dama ga Shi Annabi (صلى الله عليه وسلم) da kansa, da kuma al'umma, saboda kasancewarta bita ce na abin
da Mala'ika Jibrilu ya zo masa da shi daga Allah, don Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya amfana da abinda ya zo daga Allah buwayi gagara misali.
Kuma
a cikin yinta akwai wata fa'idar ta daban; Wacce itace: Yin bitar alqur'ani
cikin dare shine mafifici akan bitarsa da rana; saboda bitar da Mala'ika
Jibrilu ya ke yi da shi ta kasance a cikin dare, kuma sananne ne lallai shi
dare zuciya da tunani sun fi tattaruwa wuri guda a cikinsa fiye da rana, don
haka; za a fi fa'idantuwa idan bitar qur'ani ta zama da daddare.
Yana
daga cikin fa'idodin hadisin: Bayani kan kasancewar bitar alqur'ani abu ne da
shari'a ta zo da shi, kuma yinsa yana daga cikin kyawawan aiyuka, koda kuwa ba
a cikin watan ramadhana ba ne, saboda kasancewar mutane biyu da suke yinsa za
su amfana. Da kuma za su zama fiye da mutane biyu to babu laifi ga hakan,
saboda babu laifi kowanne ya amfana da xan'uwansa, ya kuma qarfafa shi akan
karatun alqur'ani, ya sanya masa nashaxi; saboda ta yiwu ba zai samu nashaxi idan
ya zauna yana karatun shi kaxansa ba, savanin idan bitar ta zama tare da
abokinsa ne, ko kuma abokansa da yawa, sai hakan ya qarfafe shi ya kuma bashi
nashaxi, tare da fa'ida mai girma da za ta kasance; na warware wani abun da zai
iya kulle wa sashi masu bita kai, don haka; a cikin yin muraja'a akwai alheri
da yawa.
Kuma
za a iya fahimta cewa karanta alqur'ani gabaxayansa daga bakin liman ga jama'ar
masallaci a cikin watan ramadhana nau'i ne na wannan bitar. Saboda cikin yin
hakan akwai fa'idantar da mamu littafin Allah; alqur'ani gabaxayansa, Shi yasa
Imam Ahmad xan Hanbal ya ke so ga mutumin da ya limanci mutane a ramadhana ya
sauke alqur'ani gabaxayansa tare da su, yace hakan mustahabbi ne, wannan kuma
yana faxawa cikin dangin aikin magabatan kwarai na son sauraron karatun alqur'ani
gabaxayansa. Saidai kuma wannan baya hukunta a yi ta saurin karatu, ta yadda
limami ba zai nitsu a cikin karatu da sallarsa ba; Hasalima neman samun
nitsuwar shi ne mafifici akan wai dole sai an yi saukar alqur'ani.
$&$
No comments:
Post a Comment