DAREN "LAILATUL QADARI" ITACE MAFI GIRMAN DARARE
Tambaya: Saboda
karatowar lokacin "lailatul qadari" za mu so malam ya yi magana wa xaukacin
musulmai akan wannan lamari? ([1])
Amsa: Lallai daren "Lailatul qadari"
shi ne mafificin darare, kuma Allah ya sauke alqur'ani ne xungurugum a cikinsa,
Sannan Allah ya bayyana cewa shi wannan dare ya fi watanni dubu, kuma dare ne
mai albarka, wanda a cikinsa ne kuma ake rabe lamurra masu hikima, kamar yadda
Allah (سبحانه وتعالى) ya ke faxa a farkon "suratud dukhan":
(حم * والكتاب المبين * إنا أنزلناه في
ليلة مباركة إنا كنا منذرين * فيها يفرق كل أمر حكيم * أمرا من عندنا إنا كنا
مرسلين * رحمة من ربك إنه هو السميع العليم) [الدخان: ١ – ٦].
Ma'ana: "Ina
rantsuwa da wannan littafi mabaiyani
* Lallai mu ne muka sauqar da shi
a cikin dare mai albarka, lallai mu mun kasance masu gargaxi * A
cikinsa ne ake rarrabe dukkan lamari mai hikima
* Lamari ne daga wurinmu, lallai
mun kasance masu tura manzanni * Rahama ce daga wurin Ubangijinka, lallai shi
mai ji ne masani" [Ad-dukhan: 1-6]. Allah (سبحانه وتعالى) ya ce:
(إنا أنزلناه في ليلة القدر * وما
أدراك ما ليلة القدر * ليلة القدر خير من ألف شهر * تنزل الملائكة والروح فيها
بإذن ربهم من كل أمر * سلام هي حتى مطلع الفجر) [القدر: ١ – ٥].
Ma'ana: "Lallai
mu muka sauqar da alqur'ani a cikin daren qaddara * Me
ya sanar da kai abinda ake ce: lailatul qadar?
* Daren qaddara ya fi alheri fiye
da watanni guda dubu * Mala'iku suna sassauka da Mala'ika jibrilu a
cikinsa * Da izinin Ubangijinsu, da kowani lamari * Aminci
ne wannan dare har zuwa fudowar alfijir" [Alqadar:
1-5].
Kuma
ya tabbata daga Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) lallai ya ce:
«مَنْ قَامَ لَيْلَةَ الْقَدْرِ إِيمَانًا
وَاحْتِسَابًا، غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ».
Ma'ana: "Duk wanda ya
yi tsayuwan lailatul qadari yana mai imani da Allah, da kuma neman lada to an
gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa". Bukhariy da Muslim
su ka rawaito shi([2]).
"Tsayuwan wannan dare" kuma na
kasancewa ne da yin salloli, zikiri, da addu'oi, da sadaka, da makamantan haka
na fiskokin alheri.
Kuma lallai "suratul qadari" ta yi
nuni cewa yin aiki a wannan dare ya fi alheri akan yin aiki a watanni dubu da
babu lailatul qadari a cikinsu. Wannan kuma falala ne mai girma, kuma rahama ce
daga Allah zuwa ga bayinsa, Don haka; ya dace ga musulmai su girmama wannan
dare, su kuma raya shi da bautar Allah.
Kuma haqiqa Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya bada labari cewa a cikin darare goman qarshen ramadhana
wannan daren ya ke, kuma a cikin dararen mara (wato; 21, 23, 25, 27, da 29) aka
fi fatan samu ko dacewa da wannan dare, a inda Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ke cewa:
«الْتَمِسُوهَا فِي الْعَشْرِ الْأَوَاخِرِ مِنْ
رَمَضَان، الْتَمِسُوهَا فِي كل وِتْرٍ».
Ma'ana: "Ku nemi
lailatul qadari a cikin goman qarshe na ramadhana, ku nemi shi a cikin kowani
dare na mara"([3]).
Kuma haqiqa hadisai ingantattu daga Manzon
Allah (صلى الله عليه وسلم) sun yi nuni cewa lallai wannan dare yana ciratuwa a cikin
kwanaki goman qarshe, ba wai da'iman har a bada a cikin dare ayyananne guda xaya
ya ke ba; don haka ta yiwu ya zama shi ne daren ashirin da xaya (21), wani
lokaci kuma daren ashirin da uku (23), wani lokacin kuma daren ashirin da biyar
(25), wani lokacin kuma ashirin da bakwai (27); wanda shi ne aka fi tsammanin
samunsa a cikinsa, haka kuma zai iya kasancewa shi ne daren ashirin da tara
(29), kamar yadda kuma zai iya yiwuwa a same shi a tsakanin dararen shafa'iy
(wato: 22, ko 24, ko 26, ko kuma 28), don haka; Duk wanda ya yi tsayuwar dare
na dukkan dararen goman qarshen ramadhana gabaxayansu yana mai imani da Allah
da kuma neman ladanSa to lallai babu makawa ya riski wannan dare mai albarka,
kuma ya rabauta da alherin da Allah ya yi alkawari ga wanda su ka aikata hakan.
Kuma
haqiqa Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kasance ya kan keve waxannan darare
goman da qarin zabura da himma wajen bautar Allah da irin abinda baya aikata
shi a cikin sauran kwanaki ashirin na farkon, A'ishah (رضي الله عنه) ta ce:
«كَانَ النبي صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
يَجْتَهِدُ فِي الْعَشْرِ الْأَوَاخِرِ مِنْ رَمَضَان، مَا لَا
يَجْتَهِدُ فِي غَيْرِهِ».
Ma'ana: "Lallai Annabi
(صلى الله عليه وسلم) yana qara qoqarin ibada a cikin kwanaki goman qarshen ramadhana
irin qoqarin da baya yinsa a cikin wassunsu"([4]). Ta sake cewa:
«كَانَ النبي صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا دَخَلَ
الْعَشْرُ أَحْيَى لَيْلَه وَأَيْقَظَ أَهْلَهُ وَجَدَّ وَشَدَّ الْمِئْزَرَ».
Ma'ana: "Lallai Annabi
(صلى الله عليه وسلم) ya kasance idan goman qarshe suka shiga ya kan raya darensa,
ya kuma tayar da iyalansa daga barci, ya zage damtse ya qara xaure kwarjallensa"([5]).
Kuma
ya kasance ya kan yi i'itikafi a cikinsu a mafi rinjayen lokaci, Allah mabuwayi
da xaukaka kuma yana cewa:
(لقد كان لكم في رسول الله أسوة حسنة)
[الأحزاب:
٢١].
Ma'ana: "Kuma haqiqa
ya kasance a gare ku dangane da rayuwar Manzon Allah abun koyi mai kyau"
[Ahzab: 21].
Kuma A'ishah (رضي الله عنه) ta tambaye shi ta ce:
«إِنْ وَافَقْتُ لَيْلَةَ الْقَدْرِ فَمَا أَقُولُ فيها؟ قَالَ:
"قُولِي: اللَّهُمَّ إِنَّكَ عَفُوٌّ تُحِبُّ الْعَفْوَ فَاعْفُ عَنِّي».
Ma'ana: "Idan na yi
dacen lailatul qadari to me zan riqa faxa a cikinsa? Sai yace: Ki ce: Ya Allah
lallai kai mai afuwa ne, kana son afuwa; to ka yi min afuwa"([6]).
Kuma
sahabban Annabi (صلى الله عليه وسلم) Allah ya qara yarda a gare su da kuma
magabatan kwarai bayansu sun kasance suna girmama waxannan darare guda goma,
kamar yadda kuma suke qoqarin aikata dangin alkhairi nau'i-nau'i a cikinsu.
Don
haka abunda aka shar'anta wa musulmai a ko-ina suke shine su yi koyi da Annabinsu
(صلى الله عليه وسلم), da kuma sahabbansa masu karamci Allah ya qara yarda a gare
su, tare da kuma magabantan wannan al'umma mutanen alkhairi, Sai su riqa raya
waxannan dararen da yin sallah, da yin karatun alqur'ani, da kuma nau'ukan
zikirori da ibadu, suna masu imani da Allah da kuma neman lada, saboda su
rabauta da gafarar zunubansu, tare da 'yantawa daga shiga wuta, a matsayin
falala daga gare shi (), da kyauta mai karamci.
Kuma
lallai dalilan alkur'ani da sunna sun yi nuni cewa lallai wannan falala mai
girma ana samunta ne idan aka nisanci manyan laifuka da ake ce da su:
alkaba'ir, kamar yadda Allah (سبحانه وتعالى) ya ke cewa:
(إنْ تجتنبوا كبائر ما تنهون عنه
نكفِّر عنكم سيئاتكم وندخلكم مدخلا كريما) [النساء: ٣١].
Ma'ana: "Idan ku
ka nisanci manya-manyan laifukan da aka hane ku za mu kankare mu ku kananan
laifukanku, mu kuma shigar da ku mashiga mai karamci",
[Nisa'i: 31]. Annabi (صلى الله عليه
وسلم) kuma ya ce:
«الصَّلَوَاتُ الْخَمْسُ، وَالْجُمْعَةُ إِلَى الْجُمْعَةِ،
وَرَمَضَانُ إِلَى رَمَضَانَ، مُكَفِّرَاتٌ لمَا بَيْنَهُنَّ إِذَا اجْتَنَبَ
الْكَبَائِرَ».
Ma'ana: "Salloli guda biyar, da juma'a
zuwa juma'a, da ramadhana zuwa ramadhana, masu kankare abunda ya kasance a tsakaaninsu
ne matuqar an nisanci manya-manyan laifuka". Muslim ne ya ruwaito shi a
cikin "sahihinsa"([7]).
Yana
daga abinda ya kamata a fadakar: Lallai wassu musulmai su kan yi iya qoqarinsu
wajen bautar Allah a cikin watan azumi na ramadana, su kuma tuba zuwa ga Allah
(سبحانه وتعالى) daga abinda ya gabata na dukkan zunubansu, sannan bayan fitan
watan ramadhana sai su koma zuwa ga aiyukansu munana, to lallai akwai hatsari
mai girma a cikin haka, kuma wajibi ne ga musulmi ya nisanci hakan, ya kuma yi
niyya ta gaskiya cewa zai doge kan biyayya ga Allah, ya kuma bar yin savo a
gare shi, kamar yadda Allah mabuwayi da xaukaka yake faxa wa Annabinsa (صلى الله عليه وسلم):
(واعبد ربك حتى يأتيك اليقين) [الحجر:
٩٩].
Ma'ana: "Kuma ka
bauta ma Ubangijinka har mutuwa ta zo maka",
[Hijri: 99]. Ya kuma ce:
(يا أيها الذين ءامنوا اتقوا
الله حق تقاته ولا تموتن إلا وأنتم مسلمون) [آل عمران: ١٠٢].
Ma'ana: "Ya ku
wadanda su ka yi imani ku ji tsoron Allah iyaka tsoronsa, kada ku mutu face
kuna musulmai", [Ali-imraan: 102]. Allah (سبحانه وتعالى) yana cewa:
(إن الذين قالوا ربنا الله ثم استقاموا
تتنزل عليهم الملائكة ألا تخافوا ولا تحزنوا وأبشروا بالجنة التي كنتم توعدون *
نحن أولياؤكم في الحياة الدنيا وفي الآخرة ولكم فيها ما تشتهي أنفسكم ولكم فيها ما
تدعون * نزلا من غفور رحيم) [فصلت: ٣٠ – ٣٢].
Ma'ana: "Lallai
waxanda suka ce Ubangijinmu shi ne Allah, sannan suka tsayu, Mala'iku suna
sassauka akansu cewa kada ku ji tsoro, kuma kada ku yi baqin ciki, ana kuma yi
muku albishir da aljannar da aka kasance ake muku alkawari * Mune majibintanku
a rayuwar duniya da kuma a lahira, kuma a cikinta kuna da abin rayukanku suke
sha'awa, kuma kuna da duk abinda kuka nema * Liyafa ne da mai gafara mai rahama",
[Fussilat: 30-32].
Ma'anar wannan ayar shi ne: Lallai waxanda su
ka tabbatar da cewa Ubangijinsu shi ne Allah, suka yi kuma imani da shi, suna
masu ikhlasin bauta a gare shi, sannan suka tsayu akan haka, to Mala'iku suna
yi musu albishir a lokacin mutuwarsu da cewa kada su ji tsoro, kada kuma su yi
baqin ciki, kuma lallai makomarsu itace aljannah; saboda imaninsu da Shi Allah
(سبحانه وتعالى) da kuma tsayuwarsu akan addininSa, ta fiskar yi masa biyayya
da barin sava masa, tare da kevance Shi da yin bauta.
Kuma ayoyin alqur'ani da suke nuna irin wannan
ma'anah suna dayawa; dukkansu kuma suna nuna wajabcin tabbatuwa a kan gaskiya,
tare nisantar savon Allah ta'alah da kiyayanSa.
Yana
kuma daga cikinSu faxinsa maxaukakin sarki:
(وسارعوا إلى مغفرة من ربكم وجنة عرضها
السموات والأرض أعدت للمتقين * الذين ينفقون في السراء والضراء والكاظمين الغيظ
والعافين عن الناس والله يحب المحسنين * والذين إذا فعلوا فاحشة أو ظلموا أنفسهم
ذكروا الله فاستغفروا لذنوبهم ومن يغفر الذنوب إلا الله ولم يصرّوا على ما فعلوا
وهم يعلمون * أولئك جزاؤهم مغفرة من ربهم وجنات تجري من تحتها الأنهار خالدين فيها
ونعم أجر العاملين) [آل عمران: ١٣٣ – ١٣٦].
Ma'ana: "Kuma ku yi gaggawa zuwa ga wata
gafara daga Ubangijinku, da kuma aljannar da faxinta shine kamar faxin sammai
da qassai; an tanade ta ga masu taqawa * Waxanda suke ciyarwa a halin wadaci da
qunci, da kuma masu haxiye fushi, da masu afuwa ga mutane, Kuma lallai Allah
yana son masu kyautatawa * Kuma sune waxanda idan suka aikata alfasha ko suka
zalunci kansu suke tuna Allah Sai su nemi gafara ga zunubansu, Kuma wanene ke
gafarta zunubai in banda Allah, kuma basa dogewa akan abunda suke aikatawa
alhalin suna sani * Waxancan sakamakonsu shine gafara daga Ubangijinsu da
aljannonin da qoramu suke gudana a qarqashinsu, suna masu dawwama a cikinSu,
Madalla da sakayyar masu aiki!", [Ali-imraan: 133-136].
Daga
qarshe muna roqon Allah da ya datar da mu da sauran musulmai a cikin waxannan
dararen da wassunsu, zuwa ga abinda ya ke so ya kuma yarda da shi, ya kuma
tsare mu gabaxaya daga sharrin kayukanmu da kuma munanan aiyukanmu; Lallai shi
mai kyauta ne mai karamci.
$&$
No comments:
Post a Comment