ZAKKAR KONO SA'IY NE GUDA XAYA DAGA ABINCIN GARI
Amsa fatawa daga Shehin malami,
Abdul'aziz xan
Abdullahi Ibnu-baaz
-Allah yayi masa
rahama-
Yabo ya tabbata ga Allah, salati da sallama su
qara tabbata ga Manzon Allah, da kuma iyalansa da sahabbansa, da duk wanda ya
shiryu da shiriyarSa, Bayan haka:
Tambayoyi
sun
yi yawa kan fitar da shinkafa a matsayin zakkar fidda kai (fixr), da kuma fitar
da kuxi a madadin abincin? ([1])
Amsa: Haqiqa ya
tabbata daga Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) cewa lallai shi:
«فَرَضَ زَكَاةَ الْفِطْرِ عَلَى الْمُسْلِمِينَ صَاعًا مِنْ
تَمْرٍ، أَو صَاعًا مِنْ شَعِيرٍ، وَأَمَرَ بها أَنْ تُؤَدَّى قَبْلَ خُرُوجِ
النَّاسِ إِلَى الصَّلَاةِ».
Ma'ana: "Ya wajabta zakkar kono akan
musulmai, sa'iy guda na dabino, ko sa'iy na alkama (sha'ir), kuma ya yi umurnin
cewa a bada ita gabanin fitan mutane zuwa ga sallah"([2]). Yana nufin: sallar idi.
Ya zo a cikin sahihul Bukhariy da Muslim daga
Abu-said alkhudriy (رضي الله عنه) yace:
«كُنَّا نُخْرِجُ زَكَاةَ الْفِطْرِ فِي زَمَنِ النَّبِي صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّم صَاعًا مِنْ طَعَامٍ، أَوْ صَاعًا مِنْ شَعِيرٍ، أَوْ
صَاعًا مِنْ تَمْرٍ، أَوْ صَاعًا مِنْ أَقِطٍ، أَوْ صَاعًا مِنْ زَبِيبٍ».
Ma'ana: "Mun kasance muna fitar da zakkar
fidda kai a zamanin Annabi (صلى الله عليه وسلم): sa'in abinci, ko sa'in sha'ir, ko
sa'in dabino, ko sa'in cukui, ko sa'in busasshen inabi (zabib)". ([3])
Kuma mutane da dama sun fassara lafazin abinci
(xa'am) da ya zo a cikin wannan hadisin; da cewa shine: Acca (al-burru), wassu
kuma suka fassara shi da: duk wani abin da mutane suka riqa a matsayin abinci;
koma-menene shi; accan ne ko masara ko dawa ko wassunsu.
Wannan kuma shine daidai, saboda zakka yalwatawa
ce daga mawadata ga talakawa, kuma ba wajibi ba ne akan mutum ya yalwata daga
abin da ba shine abincin garinsu ba. Kuma babu shakka lallai shinkafa abu ne da
aka riqa a matsayin abinci a qasar Saudiyya, kuma abinci ne mai kyau mai tsada,
kuma harma (shinkafa) ta fi sha'ir xin da hadisai suka nuna cewa yana iya isarwa,
ta fi shi daraja da falala, saboda haka za a fahimci cewa babu laifi a fitar da
shinkafa a matsayin zakkar fidda kai (fixr).
Wajibin kuma shine a bada sa'iy xaya a duk
dangogin abinci, da irin sa'in Annabi (صلى الله
عليه وسلم), wanda kuma shine
kamfata guda huxu da hannaye guda biyu matsaikata (ba manya ba, ba kuma qanana
ba) da aka cika su, kamar yadda wannan bayanin ya zo a cikin littafin "qamus"
da wassunsa. Shi kuma (sa'iy) da lissafin ma'auni shi ne: kusa da kilogiram
uku. Don haka; Idan musulmi ya fitar da "sa'iy xaya" na shinkafa ko
waninsa na abincin qasarsa: hakan ya isar masa, koda kuwa baya cikin dangin
nau'ukan abinci da aka ambata a cikin wannan hadisin, a mafi ingancin zance
biyu na maluma. Kuma babu laifi in ya fitar da kwatankwacin sa'iy xaya da
ma'aunin kilo, wanda shi ne: kusan kilo uku.
Kuma wajibin shine a fitar da "zakatul fixr"
ga yaro da babba, da namiji da mace, da xa, da kuma bawa daga cikin musulmai.
Abun da yake cikin uwar mahaifa shi kuma ba
wajibi ba ne a fitar masa da zakkar kono, da ijma'in maluma, Saidai kuma
mustahabbi ne a cire masa, saboda Usman xan Affan (رضي الله عنه) ya aikata hakan.
Kuma wajibi ne a fitar da ita (zakatul fixr)
gabanin sallar idi, baya kuma halatta a jinkirta har sai bayan sallah, Saidai
kuma babu laifi a fitar da ita gabanin idi da yini xaya ko da yini biyu; Kuma
da haka ne za a san cewa lallai farkon lokaci na halaccin fitar da ita a mafi
ingancin zancen maluma shine: daren ashirin da takwas (daren 28), saboda wata
yana kasancewa –a wassu lokutan- kwana ashirin da tara (29), ya kan kasance
kuma –a wassu lokutan- kwana talatin (30), kuma sahabban Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) sun kasance suna fitar da zakatul fixr gabanin idi yini xaya
ko da yini biyu.
Waxanda ake basu zakatul fixr su ne: fakirai
da miskinai, kuma ya tabbata daga Abdullahi xan Abbas (رضي الله عنه) ya ce:
«فَرَضَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ زَكَاةَ
الْفِطْرِ طُهْرَةً لِلصَّائِمِ مِنَ اللَّغْوِ وَالرَّفَثِ، وَطُعْمَةً
لِلْمَسَاكِينِ، مَنْ أَدَّاهَا قَبْلَ الصَّلَاةِ، فَهِيَ زَكَاةٌ مَقْبُولَةٌ،
وَمَنْ أَدَّاهَا بَعْدَ الصَّلَاةِ، فَهِيَ صَدَقَةٌ مِنَ الصَّدَقَاتِ».
Ma'ana: "Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya farlanta zakkar fidda kai, tsarki ga mai azumi daga wargi
da batsa, kuma abinci ne ga miskinai, duk wanda ya bada ita gabanin fita sallah
to wannan zakka ce karvavviya, wanda kuma ya bada ita bayan sallah to sadaka ne
daga cikin sadakoki"([4]).
Kuma
baya halatta a fitar da qimar wannan zakkah cikin kuxi a wajen mafi yawan
maluma, kuma wannan ra'ayin shine ya fi qarfin dalilai, don haka wajibi ne a
fitar da zakkar fidda-kai cikin abinci, kamar yadda Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya aikata hakan Shi da sahabbanSa (رضي الله عنهم). Kuma wannan ita ce mazhabar yawa-yawan maluma.
Allah shi ne abun roqo kan ya datar da mu da
musulmai gabaxayansu kan fahimtar addininsa, da tabbatuwa akansa.
Muna kuma roqonsa da ya gyara mana zukatanmu
da aiyukanmu, lallai shi mai kyauta ne mai karamci.
Yabo da sallama su qara tabbata ga Annabinmu
Muhammadu da iyalanSa da sahabbanSa.
$&$
Barakallahu fikha.
ReplyDeleteAllah ya saka da alkhairi.
Barakallahu fikha.
ReplyDeleteAllah ya saka da alkhairi.