2015/06/27

TAMBAYOYI HUDU A QABARI








TAMBAYOYIN NAN GUDA HUXU
(الأسئلة الأربعة)




TANADAR
MUHAMMADU XAN AHMAD XAN MUHAMMADU AL-AMMARIY







FASSARAR
ABUBAKAR HAMZA


Yabo da godiya sun tabbata ga Allah; wanda ya ilmantar da halittunsa alqalami, ya sanar da mutum abinda bai sani ba. Godiya tana qara tabbata ga Allah wanda ya halicci mutum, kuma ya sanar da shi bayani.
Salati da sallama su qara tabbata ga wanda baya magana da son zuciya, face anyi masa wahayi, Bayan haka:
Babu wani daga cikinmu da zai mutu, sannan a bunne shi a cikin qabarinsa, face an dawo masa da ransa a cikin jikinsa bayan bunne shi kai-tsaye, Sai Mala'iku biyu su zo masa a cikin qabarisa, sai su zaunar da shi a cikin qabarinsa, su masa tambayoyi guda huxu:
Tambayar farko: Wanene Ubangijinka.
Tambaya ta biyu: Menene addininka.
Tambaya ta uku: Wanene annabinka.
Tambaya ta huxu: Daga ina ka samo waxannan amsoshin?
An rawaito hadisi daga Albara'u xan Azib (رضي الله عنه) lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم)  ya ambaci halin mutum mumini idan aka bunne shi a cikin qabarinsa. Sai yace:
"فَتُعَادُ رُوحُهُ فِي جَسَدِهِ فَيَأْتِيهِ مَلَكَانِ فَيُجْلِسَانِهِ فَيَقُولَانِ لَهُ: مَنْ رَبُّكَ؟ فَيَقُولُ: رَبِّيَ اللَّهُ. فَيَقُولَانِ لَهُ: مَا دِينُكَ؟ فَيَقُولُ: دِينِيَ الْإِسْلَامُ. فَيَقُولَانِ لَهُ: مَا هَذَا الرَّجُلُ الَّذِي بُعِثَ فِيكُمْ؟ فَيَقُولُ: هُوَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ. فَيَقُولَانِ لَهُ: وَمَا عِلْمُك؟ [أي: كيف عرفتَ أن ربَّك الله، وأنّ دينك الإسلام، وأنّ نبيَّك محمد صلى الله عليه وسلم] فَيَقُولُ: قَرَأْتُ كِتَابَ اللَّهِ فَآمَنْتُ بِهِ وَصَدَّقْتُ [أي: وجدتُ الإجابة فيه]".
Ma'ana: "Sai a dawo masa da ransa cikin jikinsa, Sai mala'iku biyu su zo masa, sai su zaunar da shi, sai suce masa: Wanene Ubangijinka? Sai yace: Ubangijina shine Allah. Sai suce masa: menene addininka? Sai yace: addinina shine musulunci. Sai suce masa: Me zaka ce akan wannan mutumin da aka turo muku? Sai yace: Shi manzon Allah ne (صلى الله عليه وسلم). Sai suce masa: Menene madogarar iliminka? (Ma'ana: Ta yaya ka san cewa: Ubangijinka shine Allah, kuma addininka shine musulunci, kuma annabinka shine annabi Muhammadu صلى الله عليه وسلم ), Sai yace:  Na karanta littafin Allah sai nayi imani da shi, na kuma gaskata shi" [Ma'ana: Na samu amsa a cikin littafin Allah].
Wannan hadisin Ahmad([1]) da Abu-dawud([2]) ne suka rawaito shi da isnadi "sahih ligairihi".

Kuma lallai duk wanda ya karanta littafin Allah ya san cewa lallai Ubangijinsa shine Allah, saboda Allah ta'alah yana cewa:
{إِنَّ رَبَّكُمُ اللَّهُ} [الأعراف: 54].
Ma'ana: "Kuma lallai Ubangijinku shine: Allah" [A'araf: 54].
Haka duk wanda ya karanta littafin Allah ya san cewa lallai addininsa shine musulunci, Allah ta'alah yana cewa:
{إِنَّ الدِّينَ عِنْدَ اللَّهِ الْإِسْلَامُ} [آل عمران: 19].
Ma'ana: "Lallai addini a wajen Allah shine musulunci" [Aali-imraan: 19].
            Kuma duk wanda ya karanta littafin Allah ya san cewa lallai Muhammadu xan Abdullahi shine manzon Allah (صلى الله عليه وسلم). Allah ta'alah yana cewa:
{مُحَمَّدٌ رَسُولُ اللَّهِ} [الفتح: 29].
Ma'ana: "Muhammadu manzon Allah ne" [Al-fat-hi: 29].

Idan har mumini ya amsa waxannan tambayoyin guda huxu to sai Allah ya yi umurnin cewa a sanar da shi sakamakon cewa ya ci nasara, Sannan sai ya yi umurnin cewa a bashi kyautuka guda shida tun daga qabarinsa.
Kyautar farko: Shumfuxi daga aljannah.
Kyauta ta biyu: Tufatarwa daga aljannah.
Kyauta ta uku: A buxe masa qofa daga qabarinsa har zuwa aljannah, wacce ta wannan qofar qamshin aljannah da daxinta zasu riqa zuwa masa, kuma ta wannan qofar ce zai ga iyalansa, da duk abinda ya ke da su a cikin gidan aljannah.
Kyauta ta huxu: Za a yi masa bushara da shiga aljannah, alhalin yana cikin qabarinsa.
Kyauta ta biyar: Za a yalwata masa qabarinsa iya ganinsa.
Kyauta ta shida: Za a haskaka masa qabarinsa.
 فَيَقُولَانِ لَهُ: وَمَا عِلْمُك؟  فَيَقُولُ: قَرَأْتُ كِتَابَ اللَّهِ فَآمَنْتُ بِهِ وَصَدَّقْتُ. فَيُنَادِي مُنَادٍ فِي السَّمَاءِ أَنْ صَدَقَ عَبْدِي فَأَفْرِشُوهُ مِنْ الْجَنَّةِ، قلت: هذه الجائزة الأولى.
وَأَلْبِسُوهُ مِنْ الْجَنَّةِ، قلت: هذه الجائزة الثانية.
وَافْتَحُوا لَهُ بَابًا إِلَى الْجَنَّةِ؛ قَالَ: فَيَأْتِيهِ مِنْ رَوْحِهَا وَطِيبِهَا، قلت: هذه الجائزة الثالثة.
وَيُفْسَحُ لَهُ فِي قَبْرِهِ مَدَّ بَصَرِهِ، قلت: هذه الجائزة الرابعة.
وللترمذي([3]): عن أبي هريرة رضي الله عنه: ثُمَّ يُنَوَّرُ لَهُ فِيهِ، قلت: هذه الجائزة الخامسة.
قَالَ: وَيَأْتِيهِ رَجُلٌ حَسَنُ الْوَجْهِ حَسَنُ الثِّيَابِ طَيِّبُ الرِّيحِ فَيَقُولُ: أَبْشِرْ بِالَّذِي يَسُرُّكَ؛ هَذَا يَوْمُكَ الَّذِي كُنْتَ تُوعَدُ، قلت: هذه الجائزة السادسة.
فَيَقُولُ لَهُ: مَنْ أَنْتَ؟ فَوَجْهُكَ الْوَجْهُ يَجِيءُ بِالْخَيْرِ، فَيَقُولُ: أَنَا عَمَلُكَ الصَّالِحُ، فَيَقُولُ: رَبِّ أَقِمْ السَّاعَةَ؛ حَتَّى أَرْجِعَ إِلَى أَهْلِي وَمَالِي".
Ma'ana: "Sai suce masa: Menene madogarar iliminka? Sai yace:  Na karanta littafin Allah sai nayi imani da shi, na kuma gaskata shi. Sai mai kira a cikin sama yayi kira cewa: Lallai bawana yayi gaskiya. Kuyi masa shumfuxi daga gidan aljannah, Nace: Wannan itace kyautar farko.
Kuma ku tufatar da shi daga gidan aljannah, Nace: Wannan itace kyauta ta biyu.
Ku buxe masa wata qofa zuwa gida aljannah, Yace: Sai qamshinta da daxinta ya riqa zuwa masa, Nace: Wannan itace kyauta ta uku.
Sai kuma a yalwata masa a cikin qabarinsa iyakar ganinsa, Nace: Wannan itace kyauta ta huxu.

A wajen At-tirmiziy kuma, daga Abu-hurarairah (رضي الله عنه): Sa'annan sai a haskaka masa qabarinsa, Nace: Wannan itace kyauta ta biyar.
Yace: Sai wani mutum mai kyan fiska, da kyakkyawar tufa, da daddaxan qamshi ya zo, sai yace masa: Ina maka albishir da abinda zai faranta maka rai, Wannan shine yininka da aka kasance ake alkawarta maka, Nace: Wannan itace kyauta ta shida.
To daga nan, Sai yace masa: Wanene kai; Fiskarka itace fiskar da take zuwa da alheri? Sai yace: NINE AIKINKA NA KWARAI.
Sai yace: Ya Ubangijina! Ka tashi qiyamah; don na koma cikin iyalaina da dukiyata" .
Ahmad ya rawaito shi([4]), da Abu-dawud([5]), da isnadi "sahih ligairihi".
Hadisi ya zo daga Anas xan Malik (رضي الله عنه) lallai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"إِنَّ الْعَبْدَ إِذَا وُضِعَ فِي قَبْرِهِ وَتَوَلَّى عَنْهُ أَصْحَابُهُ وَإِنَّهُ لَيَسْمَعُ قَرْعَ نِعَالِهِمْ أَتَاهُ مَلَكَانِ فَيُقْعِدَانِهِ فَيَقُولاَنِ: مَا كُنْتَ تَقُولُ فِي الرَّجُلِ لِمُحَمَّدٍ صلى الله عليه وسلم؟ فَأَمَّا الْمُؤْمِنُ فَيَقُولُ: أَشْهَدُ أَنَّهُ عَبْدُ اللهِ وَرَسُولُهُ. فَيُقَالُ لَهُ: انْظُرْ إِلَى مَقْعَدِكَ مِنَ النَّارِ قَدْ أَبْدَلَكَ اللَّهُ بِهِ مَقْعَدًا مِنَ الْجَنَّةِ، فَيَرَاهُمَا جَمِيعًا"([6]).
Ma'ana: "Lallai bawa idan aka sanya shi a cikin qabarinsa, kuma waxanda suka kawo shi suka juya suka bar shi, alhalin yana jin qarar takalmansu, Sai Mala'iku guda biyu su zo masa, su zaunar da shi, sai su ce: Me kake cewa dangane da wannan mutumin; Muhammadu (صلى الله عليه وسلم)? Shi mumini sai ya ce: Na shaida shi bawan Allah ne kuma manzonSa ne, Sai ace masa: Ka yi dubi zuwa ga mazauninka a cikin wuta, Allah ya canza maka da shi da wani mazaunin a gidan aljannah, Sai ya gansu gabaxaya", Bukhariy ya rawaito shi.

            Idan kuma bawa bai amsa tambayoyin nan guda huxu ba to sai Allah ya yi umurnin a sanar da shi sakamakon faxuwarsa, Sannan ya yi umurnin a yi masa abubuwa guda huxu, Me ya sanar da kai waxannan abubuwan guda huxu?
            Na farko: Tufatarwa daga wuta.
            Na biyu: A buxe masa qofa daga qabarinsa, zuwa gidan wuta, Sai zafin wuta da tiririnta ya riqa zuwa masa.
            Na uku: A sanya qabarinsa ya matse shi.
            Na huxu: Sannan a yi masa albishir da shiga wuta alhalin yana cikin qabarinsa.
An rawaito hadisi daga Albara'u xan Azib (رضي الله عنه) lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم)  ya ambaci halin mutum kafiri idan aka bunne shi a cikin qabarinsa. Sai yace:
"فَتُعَادُ رُوحُهُ فِي جَسَدِهِ فَيَأْتِيهِ مَلَكَانِ فَيُجْلِسَانِهِ فَيَقُولَانِ لَهُ: مَنْ رَبُّكَ؟ فَيَقُولُ: هَاهْ هَاهْ لاَ أَدْرِي، فَيَقُولاَنِ لَهُ: مَا دِينُكَ؟ فَيَقُولُ: هَاهْ هَاهْ لاَ أَدْرِي، فَيَقُولاَنِ لَهُ: مَا هَذَا الرَّجُلُ الَّذِي بُعِثَ فِيكُمْ؟ فَيَقُولُ: هَاهْ هَاهْ لاَ أَدْرِي، فَيُنَادِي مُنَادٍ مِنَ السَّمَاءِ أَنْ كَذَبَ، فَافْرِشُوا لَهُ مِنَ النَّارِ، وَافْتَحُوا لَهُ بَابًا إِلَى النَّارِ، فَيَأْتِيهِ مِنْ حَرِّهَا وَسَمُومِهَا، وَيُضَيَّقُ عَلَيْهِ قَبْرُهُ حَتَّى تَخْتَلِفَ فِيهِ أَضْلاَعُهُ، وَيَأْتِيهِ رَجُلٌ قَبِيحُ الْوَجْهِ، قَبِيحُ الثِّيَابِ، مُنْتِنُ الرِّيحِ، فَيَقُولُ: أَبْشِرْ بِالَّذِي يَسُوءُكَ".
Ma'ana: "Sai a dawo masa da ransa cikin jikinsa, Sai mala'iku biyu su zo masa, sai su zaunar da shi, sai suce masa: Wanene Ubangijinka? Sai yace: Hah, Hah, Ban sani ba. Sai suce masa: menene addininka? Sai yace: Hah, Hah, Ban sani ba. Sai suce masa: Me zaka ce akan wannan mutumin da aka turo muku? Sai yace: Hah, Hah, Ban sani ba. Daga nan sai mai kira daga sama ya yi kira, cewa: Yayi qarya, Ku masa shumfuxi daga wuta, kuma ku buxe masa qofa zuwa gidan wuta, Sai zafinta da tiririnta ya riqa zuwa masa, Sai kuma a quntace masa qabarinsa akansa, har sai qasussuwansa na qirji sun shige wa junansu. Daga nan sai wani mutum mai mummuniyar fiska, da mummunan tufafi, da xoyi ya zo masa sai ya ce: Ina maka albishir da abinda zai baqanta maka rai".
Ahmad ya rawaito shi([7]), da Abu-dawud([8]), da isnadi "sahih ligairihi".
Hadisi ya zo daga Anas xan Malik (رضي الله عنه) lallai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"إِنَّ الْعَبْدَ إِذَا وُضِعَ فِي قَبْرِهِ وَتَوَلَّى عَنْهُ أَصْحَابُهُ وَإِنَّهُ لَيَسْمَعُ قَرْعَ نِعَالِهِمْ أَتَاهُ مَلَكَانِ فَيُقْعِدَانِهِ فَيَقُولاَنِ: مَا كُنْتَ تَقُولُ فِي الرَّجُلِ لِمُحَمَّدٍ صلى الله عليه وسلم؟ فَأَمَّا الْمُنَافِقُ وَالْكَافِرُ فَيُقَالُ لَهُ: مَا كُنْتَ تَقُولُ فِي هَذَا الرَّجُلِ؟ فَيَقُولُ: لاَ أَدْرِي كُنْتُ أَقُولُ مَا يَقُولُ النَّاسُ، فَيُقَالُ: لاَ دَرَيْتَ، وَلاَ تَلَيْتَ، وَيُضْرَبُ بِمَطَارِقَ مِنْ حَدِيدٍ ضَرْبَةً؛ فَيَصِيحُ صَيْحَةً يَسْمَعُهَا مَنْ يَلِيهِ غَيْرَ الثَّقَلَيْن"([9]).
Ma'ana: "Lallai bawa idan aka sanya shi a cikin qabarinsa, kuma waxanda suka kawo shi suka juya suka bar shi, alhalin yana jin qarar takalmansu, Sai Mala'iku guda biyu su zo masa, su zaunar da shi, sai su ce: Me kake cewa dangane da wannan mutumin; Muhammadu (صلى الله عليه وسلم)? Amma shi kuma munafiki da kafiri sai ace musu: Me za ku ce akan wannan mutumin? Sai yace: Ban sani ba, na kasance ina faxan abinda mutane ne kawai suke faxa, Sai ace: Baka sani ba, kuma baka karanta ba, Sai a doke shi da gudumomin qarfe mummunan duka, sai ya yi wani irin ihun da duk abinda ke kusa da shi zai ji, in banda mutum da aljani", Bukhariy ya rawaito shi.

Ya kai bawan Allah,            Ya ke baiwar Allah!
Lallai duk mutumin da ya xauki ilimin sanin Allah, da addininsa, da annabinsa daga littafin Allah da kuma sunnar Manzon Allah  (صلى الله عليه وسلم ) to zai iya amsa waxannan tambayoyin, Hadisi ya zo daga Albara'u xan Azib (رضي الله عنه) lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"فَيَقُولَانِ لَهُ: وَمَا عِلْمُك؟  فَيَقُولُ: قَرَأْتُ كِتَابَ اللَّهِ فَآمَنْتُ بِهِ وَصَدَّقْتُ. فَيُنَادِي مُنَادٍ فِي السَّمَاءِ أَنْ صَدَقَ عَبْدِي".
Ma'ana: "Sai suce masa: Menene madogarar iliminka? Sai yace:  Na karanta littafin Allah sai nayi imani da shi, na kuma gaskata shi. Sai mai kira a cikin sama yayi kira cewa: Lallai bawana yayi gaskiya" Ahmad ya rawaito shi([10]), da Abu-dawud([11]), da isnadi "sahih ligairihi".  
Kuma Allah ta'alah yace:
{فَمَنِ اتَّبَعَ هُدَايَ فَلَا يَضِلُّ وَلَا يَشْقَى} [سورة: طه، آية رقم: 123].
Ma'ana: "Duk wanda ya bi shiriyata to lallai ba zai vata ba kuma ba zai tave ba", [Xaha: 123].
An rawaito hadisi daga Jabir (رضي الله عنه) yace: Naji Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"وَقَدْ تَرَكْتُ فِيكُمْ مَا لَنْ تَضِلُّوا بَعْدَهُ إِنِ اعْتَصَمْتُمْ بِهِ، كِتَابُ اللهِ"([12]).
Ma'ana: "Kuma na bari a cikinku abinda ba za ku tava vata idan kuka yi riqo da shi ba: Littafin Allah", Muslim ya rawaito shi.

            Wanda kuma ya xauki ilimin sanin Allah, da addininSa, da AnnabinSa ba daga littafin alqur'ani da sunnah, to lallai ba zai amsa tambayoyin nan ba;
Wanda ya xauki ilimin sanin Allah, da addininSa, da AnnabinSa daga zantukan mutane to sai su vatar da shi daga amsa tambayoyin da suka gabata, Hadisi ya zo daga Anas xan Malik (رضي الله عنه) lallai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"فَأَمَّا الْمُنَافِقُ وَالْكَافِرُ فَيُقَالُ لَهُ: مَا كُنْتَ تَقُولُ فِي هَذَا الرَّجُلِ؟ فَيَقُولُ: لاَ أَدْرِي كُنْتُ أَقُولُ مَا يَقُولُ النَّاسُ، فَيُقَالُ: لاَ دَرَيْتَ، وَلاَ تَلَيْتَ، وَيُضْرَبُ بِمَطَارِقَ مِنْ حَدِيدٍ ضَرْبَةً؛ فَيَصِيحُ صَيْحَةً يَسْمَعُهَا مَنْ يَلِيهِ غَيْرَ الثَّقَلَيْن"([13]).
Ma'ana: "Amma shi kuma munafiki da kafiri sai ace musu: Me za ku ce akan wannan mutumin? Sai yace: Ban sani ba, na kasance ina faxan abinda mutane ne kawai suke faxa, Sai ace: Baka sani ba, kuma baka karanta ba, Sai a doke shi da gudumomin qarfe mummunan duka, sai ya yi wani irin ihun da duk abinda ke kusa da shi zai ji, in banda mutum da aljani", Bukhariy ya rawaito shi.
            Wanda ya xauki ilimin sanin Allah, da addininSa, da AnnabinSa daga Shaidani to sai  ya vatar da shi; ya kasa amsa tambayoyin da suka gabata; Allah ta'alah yana cewa:
{وَيَتَّبِعُ كُلَّ شَيْطانٍ مَرِيدٍ * كُتِبَ عَلَيْهِ أَنَّهُ مَنْ تَوَلاَّهُ فَأَنَّهُ يُضِلُّهُ وَيَهْدِيهِ إِلى عَذابِ السَّعِيرِ} [الحج: 3-4].
Ma'ana: "Kuma yake bin dukkan shexani mai taurin kai * An hukunta masa cewa duk wanda ya jibince shi to lallai zai vatar da shi, kuma zai shiryar da shi zuwa ga azabar wuta mai huruwa" [Alhajji: 4].
Kuma duk wanda ya xauki ilimin sanin Allah, da addininSa, da AnnabinSa daga hankalin da ya ke bin wani abun da littafin Allah da sunnar Manzo ba, to lallai zai vatar da shi; ya kasa amsa tambayoyin da suka gabata; Allah ta'alah yana cewa:
{وَمِنَ النَّاسِ مَنْ يُجَادِلُ فِي اللَّهِ بِغَيْرِ عِلْمٍ وَلَا هُدًى وَلَا كِتَابٍ مُنِيرٍ * ثَانِيَ عِطْفِهِ لِيُضِلَّ عَنْ سَبِيلِ اللَّهِ لَهُ فِي الدُّنْيَا خِزْيٌ وَنُذِيقُهُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ عَذَابَ الْحَرِيقِ} [الحج: 8-9].
Ma'ana: "Akwai daga cikin mutane wanda yake jayayya kan Allah, ba tare da ilimi ba, ko shiriya, ko littafi mai haske ba * yana mai karkatar da wuyansa (don girman kai), saboda ya vatar, daga hanyar Allah, A duniya yana da wulaqanta, kuma zamu xanxana masa a ranar lahira, azabar gobara" [Alhaji: 8-9].
            Kuma duk wanda ya xauki ilimin sanin Allah, da addininSa, da AnnabinSa daga son zuciyarsa, to lallai zai vatar da shi; ya kasa amsa tambayoyin da suka gabata; Allah ta'alah yana cewa:
{وَلا تَتَّبِعِ الْهَوى فَيُضِلَّكَ عَنْ سَبِيلِ اللَّهِ} [ص: 26].
Ma'ana: "Kuma kada ka bi son zuciya, sai ya vatar da kai daga hanyar Allah" [Saad: 26].  Har ila yau Allah ta'alah yana cewa:
{وَإِنَّ كَثِيرًا لَيُضِلُّونَ بِأَهْوَائِهِمْ بِغَيْرِ عِلْمٍ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ بِالْمُعْتَدِينَ} [الأنعام: 119].
Ma'ana: "Kuma lallai mutane dayawa suna vatarwa da son zuciyarsu ba tare da ilimi ba, Lallai Ubangijinka shine yafi sanin masu qetare iyaka" [Al'an'am: 119].  
            Kuma duk wanda ya xauki ilimin sanin Allah, da addininSa, da AnnabinSa daga ra'ayoyi, to lallai zai vatar da shi; ya kasa amsa tambayoyin da suka gabata; Allah ta'alah yana cewa:
{إِنْ يَتَّبِعُونَ إِلاَّ الظَّنَّ وَما تَهْوَى الْأَنْفُسُ وَلَقَدْ جاءَهُمْ مِنْ رَبِّهِمُ الْهُدى} [النجم: 23].
Ma'ana: "Ba komai su ke bi ba face zato, da abubuwan da rayuka suke so. Kuma haqiqa shiriya ta zo musu daga UbangijinSu" [An-najmi: 23]. Kuma Allah ta'alah yana cewa:
وَما يَتَّبِعُ أَكْثَرُهُمْ إِلاَّ ظَنًّا إِنَّ الظَّنَّ لا يُغْنِي مِنَ الْحَقِّ شَيْئًا، إِنَّ اللَّهَ عَلِيمٌ بِما يَفْعَلُون} [يونس: 36].
Ma'ana: "Ba komai mafi yawansu suke bi ba face zato, lallai zato baya wadatar da komai daga gaskiya, Lallai Allah masani ne dangane da abinda suke aikatawa" [Yunus: 36]. Kuma hadisi ya zo daga Abdullahi xan Amru (رضي الله عنه) yace: Na ji Annabi (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"إِنَّ اللَّهَ لاَ يَنْزِعُ الْعِلْمَ بَعْدَ أَنْ أَعْطَاهُمُوهُ انْتِزَاعًا، وَلَكِنْ يَنْتَزِعُهُ مِنْهُمْ مَعَ قَبْضِ الْعُلَمَاءِ بِعِلْمِهِمْ فَيَبْقَى نَاسٌ جُهَّالٌ يُسْتَفْتَوْنَ فَيُفْتُونَ بِرَأْيِهِمْ فَيُضِلُّونَ وَيَضِلُّونَ"([14]).
Ma'ana: "Lallai Allah xauke ilimi bayan ya baku shi xaukewa, Saidai zai cire shi ne daga cikinsu ta hanyar xauke maluma da iliminsu, Sai mutane jahilai su saura; ana riqa neman fatawa a wurinsu, Sais u bada fatawa da ra'ayinsu, sai su vatar, kuma su vata ", Bukhariy ya rawaito shi.
            Kuma duk wanda ya xauki ilimin sanin Allah, da addininSa, da AnnabinSa daga maganganu ko aiyuka ko rayuwar fasiqan maluma, da vatattun masu bauta, to lallai zasu vatar da shi; ya kasa amsa tambayoyin da suka gabata; Allah ta'alah yana cewa:
{يا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ إِنَّ كَثِيرًا مِّنَ الأَحْبَارِ وَالرُّهْبَانِ لَيَأْكُلُونَ أَمْوَالَ النَّاسِ بِالْبَاطِلِ وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ اللَّهِ} [التوبة: 34].
Ma'ana: "Ya ku waxanda suka yi imani lallai dayawa daga cikin maluma da masu bauta suna cin dukiyar mutane da varna, kuma suna tunkuxewa daga hanyar Allah", [Taubah: 34].
            Kuma duk wanda ya xauki ilimin sanin Allah, da addininSa, da AnnabinSa daga zallan maganganu ko aiyuka, ko kuma rayuwar salihai daga cikin maluma, ko masu bauta, to sai su vatar da shi; ya kasa amsa tambayoyin da suka gabata;wannan kuma saboda su ba ma'asumai ba ne; Allah ta'alah yana cewa:
{اتَّخَذُوا أَحْبَارَهُمْ وَرُهْبَانَهُمْ أَرْبَابًا مِنْ دُونِ اللَّهِ} [التوبة: 31].
Ma'ana: "Sun riqi malumansu da masu bauta a cikinsu abubuwan bauta koma bayan Allah" [Taubah: 31].
            Kuma duk wanda ya xauki ilimin sanin Allah, da addininSa, da AnnabinSa daga abinda mafi yawan mutane suke a kansa to sai su vatar da shi; ya kasa amsa tambayoyin da suka gabata; Allah ta'alah yana cewa:
{وَإِنْ تُطِعْ أَكْثَرَ مَنْ فِي الْأَرْضِ يُضِلُّوكَ عَنْ سَبِيلِ اللَّهِ إِنْ يَتَّبِعُونَ إِلاَّ الظَّنَّ وَإِنْ هُمْ إِلاَّ يَخْرُصُون} [الأنعام: 116].
Ma'ana:  "Kuma idan ka yi xa'a wa mafi yawan waxanda suke bayan qasa, sai su vatar da kai ga barin hanyar Allah, Ba komai suke bi ba face zato, kuma ba komai suke yi ba face qarya" [Al'an'am: 116].
            Kuma duk wanda ya xauki ilimin sanin Allah, da addininSa, da AnnabinSa daga abinda mafi yawan musulmai suke kansa to sai su vatar da shi; ya kasa amsa tambayoyin da suka gabata; Allah ta'alah yana cewa:
{وَمَا يُؤْمِنُ أَكْثَرُهُمْ بِاللَّهِ إِلَّا وَهُمْ مُشْرِكُونَ} [يوسف: 106].
Ma'ana: "Kuma mafi yawansu basa yin imani da Allah, face sun kasance suna yin shirka" [Yusuf: 106].

[Allah ne masani]

Al-madinah, 10/Ramadhan/ 1436h
Daidai da 27/06/2015m




([1]) Ahmad ya rawaito shi (حديث البراء بن عازب).
([2]) Abu-dawud ya rawaito shi a cikin sunan (باب في المسألة في القبر).
([3]) Attirmiziy ya rawaito shi a cikin sunan xinsa (lamba: 1071, juzu'I 3, shafi: 383).
([4]) Ahmad ya rawaito shi (حديث البراء بن عازب).
([5]) Abu-dawud ya rawaito shi a cikin sunan xinsa (باب في المسألة في القبر).
([6]) Bukhariy ya rawaito shi a cikin sahihinsa (باب ما جاء في عذاب القبر).
([7]) Ahmad ya rawaito shi (حديث البراء بن عازب).
([8]) Abu-dawud ya rawaito shi (باب في المسألة في القبر).
([9]) Bukhariy ya rawaito shi a cikin sahihinsa (باب ما جاء في عذاب القبر).
([10]) Ahmad ya rawaito shi (حديث البراء بن عازب).
([11]) Abu-dawud ya rawaito shi (باب في المسألة في القبر).
([12]) Muslim ya rawaito shi a cikin sahihinsa (باب حجة النبي صلى الله عليه وسلم).
([13]) Bukhariy ya rawaito shi a cikin sahihinsa (باب ما جاء في عذاب القبر).
([14]) Bukhariy ya rawaito shi a cikin sahihinsa (باب ما يذكر من ذم الرأي). 

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...