SIFFAR UMRAH DA AIYUKANT A ([1])
Alhamdu lillah, Bayan haka: Wannan gajeren
bayani ne dangane da aikin umrah, Gashi kamar haka ga makaranci mai alfarma:
1.
Idan mutumin da ya ke nufin
yin umrah ya iso miqaati, mustabbi ne a gare shi ya yi wanka, ya tsarkaka, kuma
itama mace haka za ta aikata, koda kuwa tana da haila, ko jinin biqi (haihuwa),
sai dai kuma in ta isa garin Makka ba za ta yi xawafi ba har sai ta tsarkaka,
kuma ta yi wanka. Kuma mutum namiji zai sanya turarensa a jikinsa, in banda
tufan haramarsa, idan kuma bai samu damar yin wanka a miqaatin ba to babu komai
akansa. Kuma mustahabbi ne idan har Allah ya kai shi garin Makka ya yi wanka
gabanin ya yi xawafi, matuqar ya samu sararin yin hakan.
2.
Mutum namiji zai tove duk
wata tufa da aka xinka, sai kuma ya xaura gyauto da mayafi, kuma mustahabbi ne
su kasance farare, masu tsafta. Amma ita kuma mace to za ta yi harama ne a
cikin tufafinta da take xaurawa na yau da kullum (al'ada)([2]), waxanda ba su da ado, ba kuma tufafin
"shahara" ba.
3.
Sa'annan sai ya yi niyyar
shiga cikin aikin, da zuciyarsa, sai kuma ya yi lafazi yana mai cewa:
«لَبَّيْكَ عُمْرَةً».
Ma'ana: "Na amsa maka zan yi
umrah". Ko:
«اللَّهُمَّ لَبَّيْكَ عُمْرَةً».
"ALLAHUMMA LABBAIKA UMRATAN".
Idan kuma mai harama ya ji
tsoron cewa wani abin zai hana shi sauke aikinsa da kammala shi; kamar rashin
lafiya, ko kuma ya ji tsoron maqiya ko makamantansu, to an shar'anta masa ya
sanya sharaxi, Sai ya ce:
«فإِنْ حَبَسَنِي حَابِسٌ فمَحِلِّي حَيْثُ
حَبَسْتَنِي».
Ma'ana: "Idan wani abu mai
hanawa ya hana ni (kammala aiki na) to wurin warware harama ta shi ne wurin da
ka sanya uzuri ya riqe ni". Wannan kuma saboda hadisin Duba'ah 'yar
Az-zubair (رضي الله عنها)
([3]).
Sannan
kuma sai ya yi ta yin "talbiyyah" da irin talbiyyar Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم), yana mai cewa:
«لَبَّيْكَ اللَّهُمَّ لَبَّيْكَ، لَبَّيْكَ لاَ
شَرِيكَ لَكَ لَبَّيْكَ، إِنَّ الْحَمْدَ، وَالنِّعْمَةَ لَكَ وَالْمُلْكَ، لاَ
شَرِيكَ لَكَ».
"LABBAIKAL LAHUMMA LABBAIKA, LABBAIKA LA SHARIKA LAKA
LABBAIKA, INNAL HAMDA WAN NI'IMATA LAKA WAL MULKA, LA SHARIKA LAKA " ([4]).
Ana neman ya yawaita faxin wannan
talbiyyar, da kuma ambaton Allah (سبحانه
وتعالى), da roqonsa, har zuwa
ya isa ga xakin (ka'abah).
4.
Kuma idan ya isa zuwa ga
masallaci mai alfarma, sai ya fara gabatar da qafarsa ta dama a yayin shigansa,
ya kuma ce:
«بِسْمِ
اللهِ، وَالصَّلَاة وَالسَّلاَمُ عَلَى رَسُولِ الله... ». «أَعُوذُ بِاللَّهِ
الْعَظِيمِ، وَبِوَجْهِهِ
الْكَرِيمِ، وَسُلْطَانِهِ
الْقَدِيمِ، منَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ، اللَّهُمَّ افْتَحْ لِي أَبْوَابَ
رَحْمَتِك»
Ma'ana: "Da sunan Allah (na
ke shiga), Yabo da sallama su qara tabbata ga Manzon Allah…"([5]), Ina neman tsarin Allah mai girma, da
kuma fiskarsa mai karamci, da kuma mulkinsa daxaxxe daga Shexani jefaffe. Ya
Allah ka bubbuxe min qofofin rahamarka"([6]).
5.
Idan ya isa jikin xakin
ka'abah sai ya yanke faxin "talbiyyah", sai kuma ya nufi
"al-hajarul aswad" ya fiskance shi, sannan ya shafe shi da hannun
damansa, ya kuma sumbance shi; -idan har ya samu dama, kada kuma ya cutar da
mutane ta hanyar matse su cikin cunkoso, yana mai cewa a lokacin tava shi:
BISMILLAHI, ALLAHU AKBAR. Idan kuma sunbantar dutsen ya wahalar to sai ya shafe
shi da hannunsa, ko da wata sanda da take hannunsa ko makamancinsa, sai kuma ya
sunbanci abinda ya tava dutsen da shi, Idan kuma tava dutsen da hannu zai
wahalar to sai ya yi nuni zuwa gare shi (ishara da hannu), yana mai cewa:
"Allahu akbar", saidai kuma ba zai sunbanci abinda ya yi nunin da shi
ba. Kuma ana sharxantawa gabanin ingancin xawafi mai xawafin ya aiwatar da shi
cikin tsarki daga qaramin hadasi da kuma babbansa; saboda xawafi kamar sallah
ne, saidai kuma an yi rangwamen yin magana a cikinsa.
6.
Zai sanya xakin ka'abah ta
hannunsa na hagu, sai ya kewaya shi har kewaye bakwai, idan ya iso wurin
"Ar-ruknul yamaniy" sai ya shafe shi da hannunsa, idan hakan ya sauwaqa
masa, yana mai cewa: "Bismillahi, wallahu akbar", saidai kuma ba zai
sunbance shi ba, idan kuma babu sararin tava shi to sai ya kyale shi ya yi
tafiyarsa, ba tare da ya yi nuni ba, haka kuma ba tare da ya yi kabbarar ba,
saboda ba a rawaito hakan daga Annabi (صلى الله
عليه وسلم) ba. Amma shi
"hajarul aswad" kuma duk lokacin da ya zo wurinsa ana son ya tava shi
ya sunbance shi, kamar yadda muka ambata a baya, in kuma ba haka ba to sai ya yi
nuni zuwa gare shi, yana mai yin kabbara.
Kuma mustahabbi ne yin
"ramalu"; wanda kuma shine: Sauri a cikin tafiya a lokacin kewaye uku
na farko cikin xawafin da ake ce masa "xawaful qudum", tare da
kusantar da taku sashinsa zuwa sashi, wannan kuma ga namiji ne kawai banda
mata. Kamar yadda kuma "mustahabbi" ne, ga namiji ya yi "ix-xiba'i";
Shi kuma ma'anarsa shi ne: mai umrah ya sanya tsakiyar mayafinsa a qarqashin
hamatarsa ta dama, hancinsa guda biyu kuma akan kafaxarsa ta hagu.
Kuma mustahabbi ne ya
yawaita ambaton Allah da kuma addu'oi, gwargwadon abunda ya sawwaqa, a dukkan
kewaye, kuma babu wata addu'a ta musamman ko wani zikiri kevantacce da aka ware
cewa za a riqa yinsa a cikin xawafi, kawai dai ana son mai umrah ya yi ta yin
addu'a da zikirori gwargwadon abun da ya sawwaqa, saidai kuma ana son a
tsakanin "ruknul yamaniy" da "hajarul aswad" a cikin kowani
kewaye ya yi ta maimaita:
ﭽ ﯜ ﯝ ﯞ ﯟ ﯠ ﯡ ﯢ ﯣ ﯤ ﯥ ﯦ ﭼ البقرة: ٢٠١
RABBANA ATINA FID DUNYAH HASANATAN
WA FIL AKHIRATI HASANATAN WA QINA AZABAN NAARI.
Ma'ana: "Ya ubangijinmu ka
bamu abu mai kyau a duniya, a lahira itama abu mai kyau, ka kare mu daga azabar
wuta".
Saboda yin hakan ya tabbata daga Annabi
(صلى
الله عليه وسلم) ([7]). Kuma zai gama kewaye na bakwai ne da shafar
"hajarul aswad" da kuma sunbantarsa –idan hakan ya sauqaqa, ko kuma
ya yi nuni zuwa gare shi yana mai yin kabbara, kamar yadda bayanin hakan ya
gabata a baya.
Bayan ya gama wannan xawafin sai ya
mayar da mayafinsa saman kafaxunsa guda biyu.
7.
Sannan sai ya yi raka'oi
guda biyu; a bayan "maqaamu Ibrahima" idan ya samu sukunin yin hakan,
in kuma bai samu ikon yi a bayansu ba to sai ya yi waxannan raka'oin guda biyu
a kowani wuri a cikin masallacin. Yana mai karanta –bayan fatiha- a raka'ar
farko: QUL YA AYYUHAL KAFIRUNA, a raka'a ta biyu kuma –bayan fatiha- QUL HUWAL
LAHU AHAD, Yin haka shine mafifici, Amma da zai karanta wassu surorin ba
waxannan ba to babu laifi akansa. Sannan bayan ya yi sallama sai ya koma ya
sake sunbantar "hajarul aswad", idan ya samu zarafin aikata hakan.
8.
Sannan sai ya fita zuwa ga
dutsen "safah"; sai ya hau kansa, ko ya tsaya a wurinsa, amma ya hau
kan na dutsen shine ya fi –in har ya samu dama-, sai ya karanta faxinsa maxaukakin
sarki:
ﭽ ﮅ ﮆ ﮇ ﮈ ﮉ ﮊ ﭼ البقرة: ١٥٨
INNAS SAFAH WAL MARWATA MIN
SHA'AIRIL LAHI .
Ma'ana: "Lallai safah da
marwah suna daga wuraren bauta wa Allah", [Baqarah: 158].
Kuma
mustahabbi ne ya yi ta godiya wa Allah yana kabbara, ya ce:
«لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ،
لَهُ الْمُلْكُ، وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، لَا
إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ،
أَنْجَزَ وَعْدَهُ، وَنَصَرَ عَبْدَهُ، وَهَزَمَ الْأَحْزَابَ وَحْدَهُ».
"LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAH , LAHUL
MULKU WA LAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADIIR, LA ILAHA ILLAL LAHU
WAHDAH, ANJAZA WA'ADAH, WA NASARA ABDAH, WA HAZAMAL AHZABA WAHDAH"([8]). Sa'annan sai ya yi abinda ya sauwaqa
na addu'a. Daga nan sai ya maimata zikiri da addu'an har sau uku.
Daga
nan sai ya sauka, ya kuma xau hanyarsa ta tafiya dutsen marwah, har ya iso
koriyar alama ta farko, sai mutum namiji ya qara sauri har ya kai ga koriyar
alama ta biyu. Ita kuma mace ba a shar'anta mata yin sauri ba; saboda
kasancewarta al'aura ce. Sai ya hau dutsen Marwah ko kuma ya tsaya a wurinsa,
amma ya hau kan duten shine abinda ya fi matuqar ya samu dama, zai kuma faxi tare
da aikata -akan dutsen Marwah- kamar yadda ya fada, ya kuma aikata akan dutsen
Safah. Sannan sai ya sauqa daga kan marwah yana mai tafiya a wurin da ake
tafiya, yana sauri idan ya iso wurin da ake sauri, har sai ya iso dutsen Safah,
zai aikata hakan har sau bakwai; tafiyarsa daga safah zuwa marwah xaya,
dawowansa zuwa safah biyu.
Da
kuma zai yi "sa'ayinsa" na safah da marwah akan abun hawa to babu
komai, musamman kuma idan akwai buqatar hakan. Kuma mustahabbi ne a cikin sa'ayinsa
ya yawaita zikiri da addu'oi, da abun da ya sauwaqa. Kuma dole ya yi safah da
marwansa alhalin yana da tsarki daga hadasi babba da qarami, amma da zai yi
sa'ayinsa ba tare da alwala ba, to ya isar masa.
Idan
ya kammala aikinsa na sa'ayi to sai ya aske gashinsa gabaxaya, ko ya rage shi,
saidai kuma aske gabaxayan gashin shi ya fi falala. Idan kuma isowarsa Makkah ta
kasance dab da fita aikin hajji ne, to a wannan halin ya rage gashin nasa shi
ya fi falala; don ya samu wanda zai sake askewa a lokacin da ya gama aikin
hajjinsa. Amma ita kuma mace sai ta tattara gashinta a wuri guda sai kuma ta
yanke kamar kan xan yatsa, ko qasa da haka.
Idan
mai umrah ya aikata abubuwan da suka gabata to lallai umrarsa ta cika, walhamdu
lillah. Kuma dukkan abubuwan da suka riga suka haramta a gare shi, sun halatta
a gare shi.
Allah
ya datar da mu da sauran 'yan'uwanmu musulmai da bamu fahimta a cikin addini, da
tabbatuwa akansa. Ya kuma karva mana aiyuka gabaxaya, lallai shi Allah mai
kyauta ne mai karamci.
Yabon
Allah da sallamarsa su qara tabbata ga bawansa kuma manzonsa Annabi Muhammadu (صلى الله عليه وسلم), da iyalansa da sahabbansa, da wadanda suka bi su da
kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
$&$
([2]) Amma ba za ta sanya NIQABI,
da BURQU'I, da SAFAR HANNU ba, waxannan za ta cire su, sai kuma ta riqa lulluve
fiskarta da tafukan hannunta da wassu tufa waxanda ba waxannan xin ba, a
lokacin da take karaskiya da mazajen da ba muharramanta ba. A duba/ HASHIYAR
MAJMU'U FATAWA na Ibnu-baaz, na Dr. Muhammad xan Sa'ad As-shuwai'ir (17/426).
([7]) Ya tabbata ne a cikin
hadisin da Abu-dawud ya rawaito shi, daga Abdullahi bn As-sa'ib (رضي
الله عنه) (lamba: 1892), da Nasa'iy a cikin
as-sunanul kubrah, (lamba: 3934), da Ibnu-khuzaimah (2721), da Alhakim a cikin
"Mustadrak" (lamba: 3098), ya kuma inganta shi, Imam Az-zhabiy kuma
ya masa muwafakah.
No comments:
Post a Comment