SALLAR TARAWIHI ([1])
Yana daga
cikin lamurran da hukuncinsu ka iya vuya ga sashin mutane; Shi ne zaton wassu
mutane cewa bai halatta a yi sallar tarawihi qasa da raka'oi ashirin (20) ba,
Wassu kuma sai su ka yi zaton cewa bai halatta a yi qari akan raka'oi goma sha xaya
(11), ko sha uku (13) ba, Waxannan kuma dukkansu zato ne da aka yi shi ba a
mahallinsa ba, kuma zato ne na kuskure; da ya sava wa dalilai.
Saboda
hadisai ingantattu daga Annabi (صلى الله
عليه وسلم) sun yi nuni cewa lallai
sallar dare abu ne da aka yalwata yanayinta ga mutane; saboda ba a sanya mata
wani iyaka da bai halatta a qetare shi ba, saboda ya tabbata cewa Annabi (صلى الله عليه وسلم) yana yin raka'oi goma sha xaya (11), a wassu lokutan kuma sai
ya yi raka'oi goma sha uku (13), a wassu lokutan kuma ya kan sallaci qasa da
haka; a watan ramadhana ne ko a waninsa, Da kuma aka tambaye shi kan sallar
dare sai ya ce:
«صَلَاةُ اللَّيْلِ مَثْنَى مَثْنَى، فَإِذَا خَشِيَ
أَحَدُكُمُ الصُّبْحَ صَلَّى رَكْعَةً وَاحِدَةً تُوتِرُ لَهُ مَا قَدْ صَلَّى».
Ma'ana: "Sallar dare
raka'oi bibbiyu ne, Idan xayanku ya ji tsoron riskar asuba to sai ya sallaci
raka'a guda xaya; da za ta zama wutirin abin da ya sallata"([2]).
Hadisi ne da aka yi ittifaqi kan ingancinsa.
Don
haka; ba a iyakance raka'oi aiyanannu ba, a ramadhana ne ko a waninsa; wannan
ya sanya sahabban Annabi (صلى الله عليه وسلم) -Allah ya qara yarda da su-, a lokacin
khalifancin Umar su ke sallatar raka'oi ashirin da uku (23) a wassu lokuta, a
wassun kuma raka'oi goma sha xaya (11), Dukkan wannan sun tabbata daga Umar (رضي الله عنه), da kuma sahabban Annabi (رضي الله
عنه) a zamanin khalifancinsa. Wannan yasa
wassu daga cikin magabata a cikin watan ramadhana su ke sallatar raka'oi
talatin da shida (36), sai kuma su yi wutri da raka'oi guda uku (3). Wassun
kuma su ke sallatar raka'oi arba'in da xaya (41), Shekhul islam Ibnu-taimiyyah
da wassunsa daga cikin ma'abota ilimi (maluma) sune su ka hakaito hakan daga
gare su. Kamar yadda shi Ibnu-taimiyyar ya bayyana cewa lamarin adadin raka'oi
abu ne da ke da yalwa; kuma ya ce: Duk mutumin da ya tsawaita tsayuwarsa na
karatu da ruku'i da sujjada to mafifici a gare shi shine ya qaranta adadin
raka'oi, Shi kuma wanda ya sassauta karatunsa da ruku'i da sujjada to sai ya qara
adadin raka'oi. Wannan shi ne ma'anar maganarsa.
Amma
duk wanda ya yi nazari kan sunnar Annabi (صلى الله
عليه وسلم) da ya doge a kanta zai
gani cewa yin raka'oi goma sha xaya (11), ko sha uku (13) shi ne mafificin
lamari; a ramadhana ne ko a waninsa, saboda yin haka shi ne abun da ya dace da
aikin Annabi (صلى الله عليه وسلم) a mafi rinjayen lokacinsa, kuma hakan
ya fi tausasa wa masu sallah, kuma shi yafi kusa da samun kushu'in gabbai da
nitsuwarsu (da rashin gaggawa). Amma shi kuma wanda ya yi qari akan haka to babu
laifi akansa, kuma bai aikata makaruhi ba, kamar yadda ya gabata.
Kuma
abun da yafi ga mutumin da ya yi sallah tare da limami a cikin sallan dare a
watan ramadhana shi ne: kada ya tafi har sai liman ya idar; wannan kuma saboda
faxin Annabi (صلى الله عليه وسلم):
«إِنَّ الرَّجُلَ إِذَا قَامَ مَعَ الْإِمَامِ حَتَّى
يَنْصَرِفَ كُتِب لَهُ قِيَامُ لَيْلَةٍ».
Ma'ana: "Lallai mutum
idan ya yi tsayuwan dare tare da liman har ya idar, to akan rubuta masa ladan
tsayuwan dare"([3]).
$&$
No comments:
Post a Comment