2015/07/16

AIYUKAN AZUMI (رمضانيات)








AIYUKAN RAMADHANA
KYAUTA ZUWA GA MASU AZUMI MAZA DA MATA
DAGA MAGANGANUN SHEIKH MUHAMMADU XAN SALIHU AL-USAIMIN,  DA SHEIKH ABDULLAHI XAN JARU-LLAHI




TANADAR
ABDULLAHI XAN AHMAD AL-ALLAF







FASSARAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم

Yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya isa a yi masa godiya,   Salati da sallama su qara tabbata ga bayinSa da ya zava.

Bayan haka:

Wannan 'yar takarda ce, taqaitacciya mai sauqaqewa, wacce na tara dalilanta daga littafin Allah, da sunnar AnnabinSa (صلى الله عليه وسلم), da kuma zantukan maluma na jiya da na yau. Wacce na sanya mata suna: "AIYUKAN RAMADHANA" Ina bada kyautar abinda ta qunsa zuwa ga kowani musulmi namiji da musulma, mai azumi namiji, da mai azumi mace. Kuma ina fatan Allah ya sanya ta a cikin ma'aunin aikina, a ranar da zan sadu da shi, sa'annan daga cikin sabbuban tsira a wajensa da samun aljannar ni'imah. Amin.
Kuma ina roqon duk wanda yake da gyare-gyare ko shawari da ya amfanar da ni da Su, don kaucewa aukawa cikin kura-kurai a fitowar takardar ta gaba.
   
WALHAMDU LILLAHI RABBIL ALAMINA.

RUBUTUN:    Abdullahi xan Ahmad al-allaf Algamidiy
Garin Xa'ifa: p.o. box  2579



AYOYIN DA SUKE MAGANA AKAN AZUMI
Bismillahir rahmanir rahim
{يا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُتِبَ عَلَيْكُمُ الصِّيامُ كَما كُتِبَ عَلَى الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ (183) أَيَّاماً مَعْدُوداتٍ فَمَنْ كانَ مِنْكُمْ مَرِيضاً أَوْ عَلى سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِنْ أَيَّامٍ أُخَرَ وَعَلَى الَّذِينَ يُطِيقُونَهُ فِدْيَةٌ طَعامُ مِسْكِينٍ فَمَنْ تَطَوَّعَ خَيْراً فَهُوَ خَيْرٌ لَهُ وَأَنْ تَصُومُوا خَيْرٌ لَكُمْ إِنْ كُنْتُمْ تَعْلَمُونَ (184) شَهْرُ رَمَضانَ الَّذِي أُنْزِلَ فِيهِ الْقُرْآنُ هُدىً لِلنَّاسِ وَبَيِّناتٍ مِنَ الْهُدى وَالْفُرْقانِ فَمَنْ شَهِدَ مِنْكُمُ الشَّهْرَ فَلْيَصُمْهُ وَمَنْ كانَ مَرِيضاً أَوْ عَلى سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِنْ أَيَّامٍ أُخَرَ يُرِيدُ اللَّهُ بِكُمُ الْيُسْرَ وَلا يُرِيدُ بِكُمُ الْعُسْرَ وَلِتُكْمِلُوا الْعِدَّةَ وَلِتُكَبِّرُوا اللَّهَ عَلى مَا هَداكُمْ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ (185) وَإِذا سَأَلَكَ عِبادِي عَنِّي فَإِنِّي قَرِيبٌ أُجِيبُ دَعْوَةَ الدَّاعِ إِذا دَعانِ فَلْيَسْتَجِيبُوا لِي وَلْيُؤْمِنُوا بِي لَعَلَّهُمْ يَرْشُدُونَ (186) أُحِلَّ لَكُمْ لَيْلَةَ الصِّيامِ الرَّفَثُ إِلى نِسائِكُمْ هُنَّ لِباسٌ لَكُمْ وَأَنْتُمْ لِباسٌ لَهُنَّ عَلِمَ اللَّهُ أَنَّكُمْ كُنْتُمْ تَخْتانُونَ أَنْفُسَكُمْ فَتابَ عَلَيْكُمْ وَعَفا عَنْكُمْ فَالْآنَ بَاشِرُوهُنَّ وَابْتَغُوا مَا كَتَبَ اللَّهُ لَكُمْ وَكُلُوا وَاشْرَبُوا حَتَّى يَتَبَيَّنَ لَكُمُ الْخَيْطُ الْأَبْيَضُ مِنَ الْخَيْطِ الْأَسْوَدِ مِنَ الْفَجْرِ ثُمَّ أَتِمُّوا الصِّيامَ إِلَى اللَّيْلِ وَلا تُبَاشِرُوهُنَّ وَأَنْتُمْ عاكِفُونَ فِي الْمَساجِدِ تِلْكَ حُدُودُ اللَّهِ فَلا تَقْرَبُوها كَذلِكَ يُبَيِّنُ اللَّهُ آياتِهِ لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمْ يَتَّقُونَ(187)}، [البقرة].
Ma'ana: "Ya ku waxanda suka yi imani an wajabta  azumi akanku kamar yadda aka wajabta shi ga waxanda suka kasance gabaninku, tsammaninku zaku samu taqawa  (183)   Kwanaki ne qididdigaggu, Duk wanda a cikinku ya kasance maras lafiya ko yana kan tafiya (sai ya karya azumi), to sai ya qirgi wassu kwanakin na daban (ya rama). Kuma wajibi ne akan waxanda azumin yake wahalar da su, bada fansar ciyarwa ga matalauci. Wanda kuma ya qara alkhairi to yin hakan alheri ne a gare shi.   Kuma ku yi azumi (da wahala) shine yafi alkhairi a gare ku, idan kun kasance kuna sani   (184)   Watan ramadhana wanda aka sauqar da alqur'ani a cikinsa, Shiriya ne ga mutane, da kuma hujjoji bayyanannu na shiriya, da rarrabewa (tsakanin gaskiya da varna).  Kuma duk wanda ya halarci watan to ya azumce shi.  Wanda kuma ya kasance maras lafiya ko akan tafiya to sai ya qididdigi wassu yinin na daban.  Allah yana nufin yi muku sauqi, baya nufin wahala a gare ku.  Kuma domin ku cike qidayar, kuma domin ku girmama Allah akan abinda ya yi na shiryar da ku, kuma tsammaninku zaku yi godiya   (185)   Kuma idan bayina suka tambaye ka dangane da ni, to lallai ni ina kusa, Ina amsa roqon mai roqo idan ya roqe ni, Sai su nemi amsawa ta, kuma su yi imani da ni, tsammaninsu zasu shiryu   (186)   An halatta muku a daren azumi jima'i da matanku, Su tufa ne a gare ku, kuma tufa ne a gare su, Allah ya sani lallai ku kun kasance kuna ha'intar kayukanku, sai ya karvi tubanku, ya kuma yi muku afuwa.  Yanzu ku rungume su, kuma ku nemi abinda Allah ya qaddara muku (na 'ya'ya), Kuma sai ku ci, ku sha har sai farin zare ya bayyana muku daga baqin zare daga alfijir, sa'annan sai ku cika azumi zuwa dare.  Kuma kada ku rungume su alhalin kuna yin i'itikafi a masallatai. Waxannan iyakokin Allah ne, kada ku kusance su.  Kamar haka ne Allah yake bayyana ayoyinsa ga mutane, tsammaninsu zasu yi taqawa  (187)",    [suratul Baqarah].
       
HIKIMAR SHAR'ANTA AZUMIN WATAN RAMADHANA
        RAMADHANA: Suna ne na watan tara, daga cikin watannin da ake qirgen kwanakinsu da ganin jinjirin wata, kuma shine wata guda xaya da aka kira sunanSa a cikin alqur'ani mai girma.
 ITA KUMA HIKIMAR SHAR'ANTA YIN AZUMI Itace: Tsarkake ran bawa, da kuma tanadar ranSa don ta zama ta samu taqawa, har ta wayi gari ta cancanci samun karramawar Allah a lahira, sai kuma ta tsira.

LADDUBAN AZUMI NA WAJIBI
1-          Tsayuwa wajen yin ibadodi na zance da kuma na aiyuka.
2-          Nisantar abubuwan da aka haramta na zantuttuka da aiyuka, waxanda ake kallo ko ji, ko makamantan haka.

LADDUBAN AZUMI NA MUSTAHABBI
Jinkirta yin sahur, da gaggauta buxa baki, da karatun alqur'ani, da yawaita ambaton Allah da addu'oi da yin sadaka.

FALALAR WATAN RAMADHANA
1.           Saukar alqur'ani a cikin wannan watan, Allah ta'alah yace:
{شَهْرُ رَمَضانَ الَّذِي أُنْزِلَ فِيهِ الْقُرْآنُ} [البقرة: 185].
Ma'ana: "Watan ramadhana wanda aka sauqar da alqur'ani a cikinsa",    [suratul Baqarah].
2.           Gafarta zunubai, Wannan kuma saboda Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
«مَنْ صَامَ رَمَضَانَ إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ».
Ma'ana: "Wanda yayi azumin ramadhana yana mai imani da neman lada an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa". [Bukhariy ya rawaito shi,  lamba: 1910].
3.           Amsa addu'ar mai addu'a, Wannan kuma saboda Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"ثَلَاثَةٌ لَا تُرَدُّ دَعْوتُهُمْ: الصَّائِمُ حَتَّى يُفْطِرَ، وَالْإِمَامُ الْعَادِلُ، وَدَعُوَةُ الْمَظْلُوم".
Ma'ana: "Mutune guda uku ba a mayar da addu'oinsu; Mai azumi har zuwa lokacin buxa baki, da shugaba adali, da kuma addu'ar mutumin da aka zalunta",  [Hadisi ne hasan, littafin: Assahihul musnad min azkaril yaumi wallailah].
4.           A cikin ramadhana akwai daren lailatul qadari.
5.           Ana sanya shexanu a cikinsa a cikin mari da sarqoqi.
6.           Ana kankare zunubai a cikin watan, Wannan kuma saboda faxinsa (صلى الله عليه وسلم):
"وَرَمَضَانِ إِلَى رَمَضَانَ مُكفِّرَاتٌ مَا بَيْنَهُنَّ مَا اجْتُنِبَتِ الْكَبَائِر".
Ma'ana: "Da watan ramdhana zuwa wani ramadhana, su kan kankare abinda ya auku a tsakaninsu, matuqar an nisanci manyan laifuka (alkaba'ira)",   [Muslim ya rawaito shi, lamba: 233].
7.           Yin umrah a cikin watan ramadhana yana daidai da yin aikin hajji, Wannan kuma saboda Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
«عُمْرَةٌ فِي رَمَضَانَ تَعْدِلُ حَجَّةً».
Ma'ana: "Yin umrah a cikin watan ramadhana tana daidai da yin aikin hajji",   [Sahihul jami'i, 4097].

YIN AZUMI
Yin azumi: Shine kamewa -tare da yin niyyah- daga barin cin abinci, da shan abin sha, da jima'i, da sauran abubuwan da suke karya azumi, tun daga fudowar alfijir na biyu, har zuwa faxuwar rana. Kuma yin azumin ramadhana rukuni ne daga cikin rukunnan Musulunci.
Kuma yinSa wajibi ne ga kowani: Musulmi, balagagge, mai hankali, wanda yake da iko akansa, mazaunin gari (ba matafiyi ba); Wajibi ne akansa ya azumci watan ramadhana idan aka ga jinjirin watansa, ko kuma idan watan sha'aban ya cika yini talatin, Wannan kuma saboda faxinSa (صلى الله عليه وسلم):
«صُومُوا لِرُؤْيَتِهِ، وَأَفْطِرُوا لِرُؤْيَتِهِ، فَإِنْ غُمّ عَلَيْكُمْ فَأَكْمِلُوا عِدَّةَ شَعْبَانَ ثَلاَثِينَ».
Ma'ana: "Kuyi azumi saboda ganin wata, kuma ku sha ruwa saboda ganinsa, Idan aka yi muku hazo to sai ku cika qidayar watan sha'aban zuwa kwanaki talatin" 

ABUBUWAN DA AKA HALATTA AIKATA SU GA MAI AZUMI
(1)        Yin aswaki a tsawon yinin azumi.
(2)        Yin tafiye-tafiye saboda wata buqata ta halal.
(3)        Yin wanka da ruwa don jin sanyi saboda tsananin zafi.
(4)        Amfani da magani na halal, kamar yin allurar da ba a  sanya mata abinci a cikinta ba.
(5)        Sanya turare.
(6)        Sanya tozali.

ABUBUWAN DA SUKE LALATA AZUMI
1.            Yin jima'i.
2.           Cin abin ci, ko kuma na sha, ko abinda yake da irin ma'anarsu, wato kamar allurar da aka sanya mata abinci a cikinta.
3.           Fitar da jini ta hanyar yin qaho.
4.           Yin amai da-gangan.
5.           Fitan jinin haila da na haihuwa.
Abubuwan nan in banda jinin haila da na haihuwa basa karya wa mutum azumi sai sharruxan da suke tafe sun cika, (1) Sanin hukuncin haka, da lokaci. (2) Mutumin ya zama yana tune (ba cikin mantuwa ba). (3) Ya kuma kasance cikin zavinsa (ba wanda aka tilasta masa ba).

KARKASUWAN MUTANE DANGANE DA WAJABCIN AZUMI, AKANSU KO RASHIN HAKA (WAXANDA AZUMI BAI ZAMA WAJIBI AKANSU BA):
1-          Kashi na farko: Kafiri.
2-          Kashi na biyu: Qaramin yaro: Azumi baya wajaba akansa, har sai ya balaga, Kuma yaro namiji yana balaga ne, da tabbatuwan xayan lamura guda uku:
Na xaya: Fitan maniyyi ta hanyar mafarki ko waninsa.
Na biyu: Tsirowar gashin gaba.
Na uku: Cikar shekarun xa namiji goma sha biyar (15).
Ita kuma 'ya mace ta kan balaga ne da abinda xa namiji yake balaga da su, tare da qarin wani abun na huxu, wanda kuma shine: Haila.
3-          Kashi na uku: Mahaukaci.
4-          Kashi na huxu: Tsofo tukuf, wanda ya kai shekarun sunbatu da surutai, kuma ya zama baya tantance abubuwa.
5-          Kashi na biyar: Mutumin da ya gajiya, ya zama ya gagara yin azumi, gajiyawa na din-din-din, wanda ba a zaton gushewar hakan a gare shi, kamar tsoho, ko maras lafiyan da ba a zaton warakarsa. Saidai wajibi ne akan irin waxannan su ciyar a madadin azumi, wato miskini guda a madadin azumin kowani yini.
6-          Kashi na shida: Matafiyi, idan har bai yi nufin wayo don karya azuminsa da tafiyar da ya qirqiro ba.
7-          Kashi na bakwai: Maras lafiya, wanda ake fatan samun sauqi a gare shi. Wannan kuma yana da halaye guda uku
Na farko: Ya zama azumi ba zai wahalar da shi ba, haka ba zai cutar da shi ba, to wannan wajibi ne akansa yayi azumin.
Na biyu: Ya zama azumin zai cutar da shi, to wannan wajibi ne akansa ya karya azumi, kuma bai halatta ya yi azumin ba.
Na uku: Azumin ya zama zai wahalar da shi, saidai kuma idan ya yi shi ba zai cutar da lafiyarsa ba, to sai ya karya.
8-          Kashi na takwas: Mai haila, Wannan haramun ne akanta tayi azumi (idan kuma hailar ta bayyana mata, alhalin tana cikin azumi koda gabanin faxuwar rana ne da kamar daqiqa guda xaya to lallai azumin wannan yinin ya lalace. Haka idan ta yi tsarki a cikin yinin ramadhana, azumtar sauran yinin baya inganta. Amma idan har tayi tsarki a cikin dare koda kuwa gabanin ketowar alfijir ne da kamar daqiqa guda, to a nan azumi ya zama wajibi akanta).
9-          Kashi na tara: Mace idan ta kasance tana shayarwa ko tana xauke da ciki, sai kuma ta ji tsoron cutuwa ga kanta, ko kuma ga yaron, idan har ta yi azumi, to sai ta karya azumin.
10-      Kashi na goma: Wanda ya buqaci karya azumi don ya tunkuxe wata lalura, da makamancin haka, kamar don tsamar da musulmi daga nitsewa a cikin ruwa, ko gobara ko wanin haka.

KARYA AZUMI:
Karya azumi na nufin: Mai azumi ya sha azuminsa bayan ya samu tabbacin faxuwar rana.

GAGGAUTA BUXA BAKI:
Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
«لاَ يَزَالُ النَّاسُ بِخَيْرٍ، مَا عَجَّلُوا الْفِطْرَ».
Ma'ana: "Mutane ba zasu gushe cikin alkhairi ba matuqar suna gaggauta buxa baki", [Bukhariy ya rawaito shi, lamba: 1856, da Muslim, lamba: 1098].

DA WANI ABU ZAI YI BUXA BAKI?
An rawaito daga Anas (رضي الله عنه) yace:
«كَانَ رسول الله صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُفْطِرُ قَبْلَ أَنْ يُصَلِّيَ عَلَى رُطَبَاتٍ، فَإِنْ لَمْ تَكُنْ رُطَبَاتٌ فَتمْرَاتٌ، فَإِنْ لَمْ تَكُنْ تمْرَاتٌ حَسَا حَسَوَاتٍ مِنْ مَاءٍ».
Ma'ana: "Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana yin buxa baki gabanin ya yi sallah, da dabinon da bai bushe ba, Idan bai samu xanyen dabino ba, sai ya yi da busassun dabino, Idan kuma bai samu busasshen ba, sai ya kwankwaxi wassu kwankwaxa na ruwa", [Sahihu Attirmiziy, 560 na Albaniy].

ADDU'AR BUXA BAKI
An rawaito daga Ibnu-Umar (رضي الله عنهما) yace:
«ذَهَبَ الظَّمَأُ وَابْتَلَّتِ الْعُرُوقُ، وَثَبَتَ الْأَجْرُ إِنْ شَاءَ اللَّهُ».
Ma'ana: "Qishi ya kau, jijiyoyi kuma sun jiqa, lada kuma ya tabbata insha Allahu", [Hadisi ne hasan, Sahihu Abiy-Dawud, lamba: 2066].

AMSA ADDU'A A LOKACIN BUXA BAKI
Wannan kuma saboda faxin Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم):
"ثَلَاث لَا تُرَدُّ دَعْوتُهُمْ: الصَّائِمُ حَتَّى يُفْطِرَ، ...".
Ma'ana: "Mutune guda uku ba a mayar da addu'oinsu; Mai azumi har zuwa lokacin buxa baki, … ",

LADAN MUTUMIN DA YA SHAYAR DA MAI AZUMI
Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
«مَنْ فَطَّرَ صَائِمًا كَانَ لَهُ مِثْلُ أَجْرِهِ، غَيْرَ أَنَّهُ لَا يَنْقُصُ مِنْ أَجْرِ الصَّائِمِ شَيْئًا».
Ma'ana: "Wanda ya shayar da mai azumi yana da kwatankwacin ladansa, ba tare da ladan Shi mai azumin ya tawaya da komai ba", [Sahihut Tirmiziy, lamba: 647].

HADISAI AKAN AZUMI WAXANDA BASU INGANTA DAGA ANNABI BA:
1-  Hadisin
"صوموا تَصِحُّوا".
Ma'ana: "Kuyi azumi ku samu lafiya" [Assilsilatu Adda'iyfah, 253].
2-  Hadisin
«إِذَا صُمْتُمْ فَاسْتَاكُوا بِالْغَدَاةِ وَلَا تَسْتَاكُوا بِالْعَشِيِّ؛ فَإِنَّ الصَّائِمَ إِذَا يَبِسَتْ شَفَتَاهُ كَانَ لَهُ نُورٌ
يَوْمَ الْقِيَامَةِ».
Ma'ana: "Idan kuna azumi ku yi aswaki da safe, kada ku yi aswako yamma, saboda mai azumi idan levvansa biyu suka bushe, to haske ne a gare shi a ranar tashin alkiyamah".
3-  Hadisin
«لِيَتَّقِهِ الصَّائِمُ».
Ma'ana: "Mai azumi ya nisanci sanya shi (yana nufin kwalli)" [Assilsilatu Adda'iyfah, 1014].
4-  Hadisin
«تُحْفَةُ الصَّائِمِ الدُّهْنُ وَالمِجْمَرُ».
Ma'ana: "Tsarabar mai azumi sune man shafawa da garwashin turaren wuta", [Da'iful jami'i, 2402].
5-  Hadisin
«شهر رمضان معلقٌ بين السماء والأرض، ولا يرفع إلى الله إلا بزكاة الفطر».
Ma'ana: "Watan ramadhana akan rataye shi tsakanin sama da qasa, ba za a xaga shi zuwa ga Allah ba sai an bada zakkar fidda kai (fixir)" [Assilsilatu Adda'iyfah, 43].

TSAYUWAN DARE (SALLAR TARAWIHI)
Wannan shine raya dararen watan ramadhana da yin salloli tare da yin karatu mai tsayi a cikinsu. An sanya masa sunan (tarawihi) ne saboda mutane sun kasance suna hutawa duk bayan sallama guda biyu.
Kuma yin tarawihi sunnah ne, Yawan raka'ointa kuma goma sha xaya ne, Amma wassu malaman sun ce za a iya wani adadin ba wannan ba; Saidai kuma zancen da yake dacewa da shiriyar Annabi (صلى الله عليه وسلم) shine: Lallai tarawihi raka'oi ne guda takwas, in banda raka'oin witiri, saboda hadisin A'ishah (رضي الله عنها) wanda ya zo a cikin littafin sahihul-Bukhariy, tace:
«مَا كَانَ يَزِيدُ فِي رَمَضَانَ وَلاَ فِي غَيْرِهِ عَلَى إِحْدَى عَشْرَةَ رَكْعَةً».
Ma'ana: "Annabi bai kasance yana yin qari ba, a cikin watan ramadhana ko a waninsa akan raka'oi guda goma sha xaya"

TSAYUWAN DARE
An rawaito daga A'ishah (رضي الله عنها) lallai tace:
إنّ النبي صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، «كَانَ إِذَا دَخَلَ الْعَشْرُ الْأَوَاخِر، أَحْيَا اللَّيْلَ، وَأَيْقَظَ أَهْلَهُ، وَجَدَّ وَشَدَّ الْمِئْزَرَ».
Ma'ana: "Lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kasance idan kwanaki goman qarshe suka shiga, ya kan raya dare, ya kuma tada iyalanSa, ya kuma tamke kwarjalleSa", [Bukhariy ya rawaito shi, lamba: 1920, da Muslim, lamba: 1174].

YIN SAHUR:
Shi sahur: Shine cin abinci, ko shan abun sha a qarshen dare, da niyyar yin azumi.
Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
«فَصْل مَا بَيْنَ صِيَامِنَا وَصِيَامِ أَهْلِ الْكِتَابِ أَكْلَةُ السُّحُورِ».
Ma'ana: "Abunda ya rabe tsakanin azuminmu dana ma'abota littafi shine: Cin sahur", [Muslim ya rawaito shi, lamba: 1096].

KWAXAITARWA KAN YIN SAHUR
Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
«تَسَحَّرُوا فَإِنَّ السَّحُورَ بَرَكَةُ».
Ma'ana: "Ku yi sahur; lallai a cikin abincin sahur akwai albarka", [Muslim, 1095].

LOKACIN YIN SAHUR:
An karvo daga Zaid xan Sabit (رضي الله عنه) yace:
«تَسَحَّرْنَا مَعَ رسول الله صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، ثُمَّ قَامَ إِلَى الصَّلاَةِ، فقُلْتُ: كَمْ كَانَ بَيْنَ الأَذَانِ وَالسَّحُورِ؟ قَالَ: «قَدْرُ خَمْسِينَ آيَةً».
Ma'ana: "Mun yi sahur tare da Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) sannan sai ya tashi zuwa ga sallah, Sai nace: Wane gwargwado ne ya kasance tsakanin kiran sallah da sahur? Sai yace: Gwargwadon karanta ayoyi hamsin", [Bukhariy ya rawaito shi, 1821].

AZUMI NA MUSTAHABBI (SUNNAH):
1.  Azumin yini shida a cikin watan shawwal, bayan watan ramadhana, wanda za a cika samun ladan azumtar shekara da su.
2.  Yin azumin ranar litinin da alhamis, saboda yini ne guda biyu da ake bijiro da aiyukan bayi a cikinsu wa Allah.
3.  Azumtar kwanaki uku a cikin kowani wata, wanda shima za a rubuta wa mutum ladan azumtar shekara, wannan kuma saboda aiki mai kyau guda xaya, yana daidai da guda goma kwatankwacinsa. Kuma abinda yafi shine wannan azumin ya zama an yi su ne a ranar goma sha uku, da goma sha huxu, da kuma goma sha biyar na kowani wata.
4.  Azumtar kwana taran farko na watan zulhijjah, Wanda kuma yafi muhimmanci shine yin azumin ranar tara, wanda kuma shine ranar arafah, ga wanda ba mahajjaci ba.
5.  Yin azumi a cikin watan almuharram, Wanda yafi muhimmanci kuma a ciki shine azumtar ranar tara, da ta goma.

AZUMIN DA AKA HANI AKAI:
1-  Azumtar ranar da ake shakka, wanda kuma shine yinin talatin na watan sha'aban.
2-  Yin azumin ranakun idi guda biyu, idin azumi da idi layya.
3-  Azumtar yini guda uku na bayan layya (ayyamut tashriq), wanda kuma sune ranar goma sha xaya, das ha biyu da sha uku, na watan zulhijjah, ga wanda ba mahajjaci mai yin tamattu'i ko qirani idan bai samu dabbar hadaya ba.
4-  Ware yinin jumu'a da azumi.
5-  Mace ta yi azumin nafila ba tare da ta samu izinin mijinta ba.

YIN I'ITIKAFI
Yinsa sunnah ne abun so (mustahabbi), kuma wanda yafi falala shine yin i'itikafi kwanakin qarshen wata mai karamci (ramadhana). An rawaito daga A'ishah (رضي الله عنه) tace:
«إنَّ رسول الله صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يَعْتَكِفُ العَشْرَ الأَوَاخِرَ مِنْ رَمَضَانَ حَتَّى تَوَفَّاهُ اللَّهُ».
Ma'ana: "Lallai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana yin i'itikafin kwanaki goman qarshe na ramadhana, har Allah ya xauki ransa", [Assilsilatu adda'iyfah, 401].

ZAKKAR FIDDA KAI (FIXIR):
Abdullahi xan Abbas (رضي الله عنهما) yace:
«فَرَضَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ زَكَاةَ الْفِطْرِ طُهْرَةً لِلصَّائِمِ مِنَ اللَّغْوِ وَالرَّفَثِ، وَطُعْمَةً لِلْمَسَاكِينِ، فَمَنْ أَدَّاهَا قَبْلَ الصَّلَاةِ فَهِيَ زَكَاةٌ مَقْبُولَةٌ، وَمَنْ أَدَّاهَا بَعْدَ الصَّلَاةِ فَهِيَ صَدَقَةٌ مِنَ الصَّدَقَاتِ».
Ma'ana: "Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya farlanta zakkar fidda kai, don ta zama tsarki ga mai azumi daga wargi da batsa, abinci ga miskinai. Duk wanda ya bada ita gabanin yin sallar idi to wannan zakka ce karvavviya, Wanda kuma ya bada ita bayan idar da sallah to sadaka ce daga cikin sadakoki", [SahihuAbiydawud].
        Kuma ana fitar da zakkar fidda kai ga mutum da waxanda yake ciyar da su, qanana ne ko manya, namiji ko mace, xa ne ko kuma bawa.

FAXAKARWA      ((GUDA 25))
        'XAN UWANA MUSULMI!
(1)        Ka yi azumin watan ramadahana kana mai imani da neman lada, a wajen Allah ta'alah, domin ya gafarta maka abinda ya gabata na zunubanka.
(2)        Ka kiyaye karya azumi yini xaya daga cikin yinin ramadhana ba tare da wani uzuri ba, saboda aikata hakan yana daga cikin manya-manyan zunubai.
(3)        Ka tashi ka yi salloli cikin dararen ramadhana, sallolin tarawihi da tahajjud, musamman lailatul qadari, cikin imani da neman lada; domin a gafarta maka duk abinda ya gabata daga zunubanka.
(4)        Yi qoqarin abincinka da abin shanka da tufafinka su kasance na halal, domin a karvi aiyukanka, a kuma amsa maka addu'oinka. Kuma ka kiyaye kar ya zama ka kame daga halal, amma sai ka buxa baki kan haram.
(5)        Ka shayar da wassu masu azumi a wurinka, domin ka samu kwatankwacin ladansu.
(6)        Ka kiyaye aiwatar da salloli guda biyar a cikin lokutansu, a cikin jam'i, domin ka samu ladan hakan, sannan Allah ya kiyaye ka da su.
(7)        Ka yawaita yin sadaka, saboda mafificin sadaka itace sadakar da aka yi ta a cikin watan ramadhana.
(8)        Ka kiyaye vata lokaci ba tare da yin aiki managarci ba, saboda za a tambaye ka akansu, kuma za a yi hisabi akan haka, kuma za ka ga sakayyar abinda ka aikata a cikinsu.
(9)        Ka yi umrah a cikin watan ramadhana, saboda yin umrah a cikin watan ramadhana yana daidai da aikin hajji.
(10)    Ka nemi taimakon iya yin azumtar yini da yin sahur a qarshen yankin dare, matuqar baka ji tsoron ketowar alfijir ba.
(11)    Ka gaggauta buxa baki, bayan ka tabbatar da faxuwar rana, domin ka dace da samun soyayyar Allah a gare ka.
(12)    Ka yi wankan janaba gabanin ketowar alfijir, domin kayi ibadar sallah cikin tsarki da tsafta.
(13)    Ka mori damar samun kanka da kayi a cikin watan ramadhana, ka kuma cike lokutansa da karatun mafi alherin abinda ya sauka a cikinsa, wanda kuma shine tilawar alqur'ani da tunanin ayoyin, domin ya zama hujja a gare ka a wajen Ubangijinka, mai ceto a gare ka ranar qiyamah.
(14)    Ka kiyaye harshenka daga qarya, da tsinuwa, da cin nama da annamimanci, saboda waxannan suna tauye ladan azumi.
(15)     
(16)     
(17)     


No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...