2015/07/03

SUNNONIN HUXUBAR JUMA'A

SUNNONIN HUXUBAR JUMA'A:

Huxuba –a sallar juma'a- rukuni ne daga cikin rukunnan juma'ar; wanda sallar bata inganta idan ba a yi ta ba; saboda Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya dawwama wajen aikata ta, kuma bai tava barin aikata huxubar ba, ana yin huxubobi guda biyu ne, kuma an sharxanta cewa su rigayi sallar juma'a.
Yana daga cikin sunnoni huxuba:
        Na xaya: Yin addu'a: An sunnanta yin addu'a ga musulmai kan neman gyaruwan addininsu da kuma lamuransu na duniya, tare da yin addu'a ga shugabanninsu; da cewa Allah ya gyara su kuma ya musu dace "wato: taufiqi''; saboda Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance
"إِذَا خَطَبَ يَوْمَ الْجُمُعَةِ دَعَا فَأَشَارَ بِأُصْبُعِهِ وَأَمَّنَ النَّاسُ".
Ma'ana: (Idan yana huxuba sai ya yi addu'a, yana mai ishara da yatsarsa, mutane kuma suna cewa: aamin!).

Na biyu: Kuma yana daga cikin sunnonin huxuba: limami ya jeranta huxubobin guda biyu tare da sallah, yana mai xaga sautinsa da huxubobin biyu gwargwadon iko, ya kuma yi huxubar a tsaye; wannan kuma saboda faxinsa maxaukaki:
ﭿ ﮀ الجمعة: ١١
Ma'ana: (Sai su barka a tsaye).
Jabir xan Samurah (رضي الله عنه) ya ce:
"كَانَ رَسُول اللَّهِ r يَخْطُبُ قَائِمًا، ثُمَّ يَجْلِسُ، ثُمَّ يَقُومُ فَيَخْطُبُ قَائِمًا، فَمَنْ حَدَّثَكَ أَنَّهُ كَانَ يَخْطُبُ جَالِسًا فَقَدْ كَذَب"([1]).
Ma'ana: (Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya kasance yana yin huxuba a tsaye, sannan sai ya zauna, sa'annan ya tashi ya tsaya ya sake huxuba, Duk wanda ya baka labarin cewa yana yin huxubarsa ne a zaune to lallai ya yi qarya).

Na uku: Yana daga cikin sunnah: Huxubar ta zama akan minbari ko wani bagire mai tudu; wannan kuma saboda (Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya kasance yana yin huxuba ne akan minbarinsa), kuma yana da tudu. Kuma saboda yin hakan yafi kaiwa maqura wajen isar da saqo wa adadin mutane masu yawa, kuma ya fi kaiwa maqura wajen wa'azi.
Na fuxu: Mustahabbi ne limami ya zauna -xan kaxan- a tsakanin huxubobi guda biyu; wannan kuma saboda faxin Abdullahi xan Umar (رضي الله عنه):
"كَانَ النَّبِيُّ r يَخْطُبُ الْخُطْبَتَيْنِ وَهُوَ قَائِمٌ، وَكَانَ يَفْصِلُ بَيْنَهُمَا بِجُلُوسٍ"([2]).
Ma'ana: (Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya kasance yana yin huxuba guda biyu alhalin yana tsaye, ya kan kuma rabe tsakaninsu da zama).
Na biyar: Kuma an sunnanta gajerta huxubobi guda biyu, sa'annan an so ta biyun ta zama tafi ta farkon gajerta; wannan kuma saboda hadisin Ammar (رضي الله عنه) daga Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"إِنَّ طُولَ صَلاةِ الرَّجُلِ، وَقِصَرَ خُطْبَتِهِ مَئِنَّةٌ مِنْ فِقْهِه، فَأَطِيلُوا الصَّلاةَ، وَأَقْصِرُوا الْخُطْبَة"([3]).
Ma'ana: (Lallai tsawon sallar mutum, da gajarcin huxubarsa alama ce da take nuna zurfin fahimtarsa; don haka ku tsawaita sallah, kuma ku gajarta huxuba).
Na shida: Kuma an sunnanta wa mai huxuba da ya yi sallama ga mamunsa idan ya fiskance su; saboda faxin Jabir (رضي الله عنه) cewa:
"كَانَ رَسُولُ اللَّه r إِذَا صَعِدَ الْمِنْبَرَ سَلَّمَ".
Ma'ana: (Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya kasance idan ya hau minbari sai ya yi sallama).
Na bakwai: Kuma an sunnanta wa liman zama akan minbari har zuwa kammala kiran sallah; wannan kuma saboda faxin Abdullahi xan Umar (رضي الله عنه) ya ce:
"كَانَ النَّبِيُّ r يَجْلِسُ إِذَا صَعِدَ الْمِنْبَرَ حَتَّى يَفْرَغَ الْمُؤَذِّنُ، ثُمَّ يَقُومُ فَيَخْطُبُ".
Ma'ana: (Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya kasance yana zama idan ya hau minbari, har zuwa mai kiran sallah ya kammala kira, sa'annan sai ya tsaya ya gabatar da huxuba).
Wannan shine abinda ya sauwaqa a wannan matsayar.
Wallahu ta'alah A'alam.




([1]) Muslim ya rawaito shi (lamba: 862). 
([2]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 928), da Muslim (lamba:  861)
([3]) Muslim ya rawaito shi (lamba: 869).  

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...