YIN I'ITIKAFI
Tambaya: Menene
hukuncin i'itikafi ga namiji da mace?
Kuma shin sharaxi ne sai i'itikafin ya zama tare da azumi?
Sannan da waxanne abubuwa ake son mutum mai i'itikafi ya
shagalta da su?
Yaushe ne kuma zai shiga wurin i'itikafinsa?
Amsa: I'itikafi
sunnah ne ga maza da mata, saboda abun da ya tabbata daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) na cewa ya yi i'itikafi a watan ramadhana, kuma daga qarshe
sai lamarinsa ya tabbata akan i'itikafin kwanaki goman qarshen ramadhana, kuma
sashin matansa sun kasance suna yin i'itikafi tare da shi (صلى الله عليه وسلم), haka kuma matansa sun ci-gaba da yin i'itikafi a bayansa([2]).
Kuma mahallin da ake yin i'itikafi shi ne: masallacin da ake
yin sallar jam'i, kuma idan a kwanakin i'itikafinsa juma'a za ta gitta to an so
ya aiwatar da i'itikafinsa a masallacin juma'a.
Kuma a mafi
ingancin magana daga zantukan maluma; i'itikafi bashi da wata iyaka da aka
iyakance masa, kuma ba a sharxanta yin azumi tare da i'itikafi, saidai kuma yinsa
tare da azumin shine ya fi.
Kuma sunnah ga i'itikafi shine mai yinsa ya shiga wurin i'itikafinsa
a lokacin da ya niyyaci haka, ya kuma fita daga wurin bayan qarewar lokacin da
ya diba wa kansa; (ko ya niyyata), amma ya samu damar ya yanke i'itikafinsa (ya
fita daga masallaci) idan akwai buqatar hakan, saboda kasancewar i'itikafi
sunnah ne, da baya wajaba akan mutum don shiga cikinsa ko fara shi, matuqar dai
ba na bakance ba ne.
Kuma
mustahabbi ne a yi i'itikafin kwanaki goman qarshen watan ramadhana, a matsayin
koyi da Annabi (صلى الله عليه وسلم), kuma duk wanda zai yi i'itikafinsa to
mustahabbi ne ya shiga wurin i'itikafin bayan sallar asubah, a yinin ashirin da
xaya (21), yana mai koyi da Annabi (صلى الله
عليه وسلم), sai kuma ya fita idan
kwanaki goman suka qare, idan kuma ya yanke shi gabanin cikar kwanaki goman to
babu laifi akansa, matuqar dai ba bakance ya yi ba, kamar yadda ya gabata. Kuma
abun da ya fi shine ya kama wuri aiyananne a masallaci –in hakan ya sauqaqa masa-,
kuma an shar'anta wa mai i'itikafi cewa ya yawaita ambaton Allah, da karatun alqur'ani
da neman gafara, da addu'oi, da kuma salloli matuqar dai ba a lokutan hani ba
ne. Kuma babu laifi wassu daga cikin abokansa su ziyarce shi, haka kuma babu
laifi ya yi taxi da su, kamar yadda Annabi (صلى الله
عليه وسلم) wassu daga cikin
matansa su ke ziyartarsa, su ke kuma yin taxi da shi, harma a wata rana matarsa
Uwar muminai Safiyyah ta ziyarce shi alhali yana i'itikafi a cikin watan azumi,
a yayin da ta tashi za ta koma sai ya tashi tare da ita ya raka ta bakin kofar
masallaci([3]), Sai hakan ya nuna cewa babu laifi kan
aikata irin wannan.
Kuma wannan aikin nasa ya qara fito da cikar qanqan-da-kan Manzon
Allah (صلى الله عليه وسلم) da tawali'unsa, da kuma kyakkyawar mu'amalarsa tare da
matansa, Allah ya yi daxin yabo da salati a gare shi.
$&$
No comments:
Post a Comment