2015/07/18

HUDUBAR MADINA (04)








HUXUBAR MASALLACIN ANNABI (r)
JUMA'A, 1 /SHAWAAL/1436H




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI ALIYU XAN ABDURRAHMAN AL-HUZAIFIY







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya halicci dukkan halittu da ikonSa;     Ya kuma yi baiwa ga wanda ya nufa daga cikinsu ya azurta shi da yin biyayya a gare shi,    Sannan ya tavar da wanda ya nufa da hikimarSa, 
Tsarki ya tabbata ga Allah wanda ya wadata baya buqatar komai;      Saboda haka; Xa'a ko biyayyar wanda yayi ta kusantar Allah da nau'ukan bauta a gare shi bata amfanar da Allah da komai,    Kuma aikata savon waxanda suka sava masa bata cutar da shi;      wannan kuma don cikar wadacinSa da girman izzarSa da buwayarSa,
Ina shaidawa babu abun bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokan tarayya a cikin UluhiyyarSa,
Ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa,    Shine kuma zavavve daga cikin halittunSa,   
Ya Allah ka yi daxin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka annabi Muhammadu,    da iyalansa da sahabbansa salati da sallama masu yawa.

Bayan haka:
Ku ji tsoron Allah ta hanyar dawwama kan yin biyayya a gare shi,    da kuma qauracewa abubuwan da Allah ya haramta,     Lallai wanda yayi riqo da bin Allah ya rabauta a duniya da lahira,     Kuma lallai ya tave yayi hasara Wanda ya bi son zuciyarSa.

Ya ku bayin Allah!
Ku tuna ni'imomin da Allah yayi akanku waxanda basa qirguwa,      Sannan ku bi su da godiya domin su wanzu; su kuma dawwama,     Allah ta'alah yana cewa:
"Ka ambaci lokacin da Ubangijinku ya bada shela; cewa Idan har kuka yi godiya to lallai zan yi muku qari.      In kuma kuka butulce to lallai azabata mai tsanani ce", [Ibrahim, 7].
Har ila yau Allah yana cewa:
"Ya ku mutane lallai ku faqirai ne zuwa ga Allah, Shi kuma Allah shine mawadaci abun godiya", [faxir, 15].
Allah yana cewa:
"Duk wanda yayi godiya to lallai ya yi godiya ne wa kansa, Wanda kuma ya butulce to lallai Allah mawadaci ne abun godiya", [Luqman, 12].
Kuma Allah a cikin hadisin "qudusiy" yace:
"Ya ku bayina!   Lallai waxannan aiyukanku ne nake qididdige su a gare ku, Sa'annan sai in cike muku sakayyarsu,   Duk wanda ya samu alheri to sai yayi godiya wa Allah,    Wanda kuma ya samu wanin haka to kada ya zargi kowa sai kansa" [Muslim ne ya rawaito shi, daga hadisin Abu-zarrin t].

        Ya ku musulmai!
        Jiya, a cikin watan ramadhana darare da yini sun yi kyau a gare ku,      kuma kun yi ta jin zaqin nau'ukan biyayya masu yawa a cikin awannin da suka shuxe,     Kuma Allah ya datar da ku kan qaurace wa abubuwan da ya haramta,       saboda tsoron uquba daga Allah mai girma maxaukaki.       Don haka;    Kada ku canza biyayya wa Allah mai rahama da yin savo a gare shi,       Kada kuma ku xauki rafkana a madadin ambaton Allah da yin karatun alqur'ani.      Kada kuma ku bari tawaya ta shiga muku cikin farillai; saboda sakaci a cikinsu, ko kuma kasala,    Saboda yin haquri wajen aikata biyayya, da kuma barin savo wa Allah = suna daga cikin siffofin bayin Allah muminai, kuma alama ce ta bayin Allah masu taqawa.     Allah yana cewa:
"Ubangijin sammai da qasa da abinda ke tsakaninsu,      Ka yi bauta a gare shi;  kuma ka jure wajen bauta masa,      Shin ka san wani da yake da irin sunanSa ?". [Maryam,,56].
Kuma Allah ta'alah yace:
"Kuma kayi umurni wa iyalanka da yin sallah,    ka kuma jure akan haka,      Ba za mu tambaye ka arziqi ba,    mune muke azurta ka,      Kyakkyawar makoma tana ga bin dokokin Allah", [Xaha, 132].
        Kuma kada wani ya canza ya daina aikata abunda Allah ya ke so daga wajenSa, zuwa ga aikata abinda Allah baya son bawa ya aikata su,        saboda kada Allah ya juya masa zuwa ga abinda yake qi.    
Kuma kada wani ya canza aiyukan da yake yi na daidaito akan addini da dacewa da kuma biyayya,     zuwa ga bin son zuciya da shexani da aikata munanan aiyuka,       Sai Allah  ya canza halin wannan bawa, sai kuma lamurransa su jujjuya a gare shi,      Allah ta'alah yana cewa:
"Lallai Allah baya canza abinda yake tattare da wassu mutane face sun canza Su da kansu" [Ra'ad, 11].
Har   ila yau Allah yana cewa:
"Haka ya kasance ne saboda Allah bai kasance zai jirkita wata ni'ima da yayi ga wassu mutane ba, har sai sun canza Su da kawunansu,     Kuma lallai Allah mai ji ne masani", [Anfaal, 53].
Kuma Allah ta'alah yana cewa:
"Yayin da suka karkace sai Allah ya karkatar da zuciyarsu,     Lallai Allah baya shiryar da mutane fasiqai", [Saffi, 5].

        Sai musulmi yayi ta yaqi da kansa   don ya zama akan mafi kyan halaye,    ya kuma riqa roqon UbangijinSa taimako da dace,  akan ya taimake shi kan yin biyayya wa  Allah,      ya kuma kare shi daga yin savo a gare shi.

        Ya ku musulmai!
        Shin baku sani ba ne cewa;
Lallai mafi kyan halin mutum musulmi shine:    
YA KASANCE AKAN BIYAYYA BAYAN WATA BIYAYYAR,     YA KUMA BIYAR DA AIYUKA KYAWAWA BAYAN AIKATA WASSU KYAWAWAN, TARE KUMA DA NISANTAR MUNANAN AIYUKA,      Allah yana cewa:
"Lallai waxanda suka nemi shiriya sai Allah ya yi qarin wata shiriyar a gare su,     kuma sai ya basu taqawarsu",  [Muhammadu, 17].

        Sannan sai matakin da yake qasa da wannan, wanda kuma shine:     
MUTUM YA BIYAR DA AIKI MAI KYAU BAYAN MUMMUNAN DA YA AIKATA; DON YA KANKARE MASA SU,     Allah ta'alah yana cewa:
"kuma ka tsayar da sallah a geffan yini guda biyu, da kuma wani yanki na dare, Lallai kyawawan aiyuka suna tafiyar da munana,      Wannan kuma tunatarwa ne ga masu yin  tunawa", [Huud,  114].
A cikin hadisin Mu'azu da Abu-zarrin (رضي الله عنهما) Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Ka kiyaye dokokin Allah a duk wurin da kake,     Sannan ka biyar da aiki mai kyau bayan mummuna sai ya kankare shi,        Kuma kayi mu'amala da mutane da halayya masu kyau",       [Attirmiziy ya rawaito shi].

        Mafi munin halayyar mutum kuma shine:     
BAWA YA BIYAR DA AIYUKA MUNANA BAYAN WASSU MUNANAN DA YAYI, KO KUMA YA BIYAR DA MUNANA BAYAN KYAWAWA, WAXANDA ZASU VATA MASA SU,             Allah ta'alah yana cewa:
"Ya ku waxanda suka yi imani ku yi xa'a wa Allah kuma ku yi xa'a wa Manzo, kuma kada ku vata aiyukanku", [Muhammadu, 33].     Wannan kuma saboda aikata munanan aiyuka da kuma savo bayan aikata kyawawa da biyayya         yana iya rusa aikin mutum,    ko kuma ya rushe sashin aikin,      ko kuma ya tauye ladan kyawawan,

         
Kuma haqiqa an rawaito daga wassu daga cikin magabata cewa sun kasance suna roqon Allah na tsawon watanni shida (6) kan ya karva musu aiyukan da suka yi a cikin watan ramadhana, haka kuma suna roqonSa na sauran tsawon watanni shidan cewa Allah ya kai rayukansu  watan ramadhana.

        Kuma yana daga cikin kaidin Shexan yayi ta qawata wa mutum sakaci kan biyayya wa Allah,    da kuma raunin kasa bari ko nisantar aiyukan haramun a wajen watan ramadhana,      Wannan kuma domin shexan ya samu   ya rabauta da abinda ya kufce masa a cikin watan ramadhana,      saboda kasancewarsa a xaxxaure a cikin watan ramadhana.

        An ce wa mai suna ALBISHIR ALHAFIY Me zaka ce kan mutanen da suke yin ijtihadi wajen bautar Allah a cikin watan ramadhana,      Idan kuma ramadhanan ya fice sai su dena.      Sai yace:    Tir da mutanen da basu san da Allah ba sai a cikin watan azumi.

        Yana daga cikin manya-manyan karama, Allah yayi baiwa ga bawa da tsayuwa akan addini a dukkanin lokacin rayuwarSa,       da kuma cikakken jin daxi.     Allah yana cewa:
"Lallai waxanda suka ce Ubangijinmu shine Allah,     Sannan suka tsayu: babu tsoro a gare su, kuma ba za su yi baqin ciki ba    **    Waxannan sune ma'abota aljannah, suna masu dawwama a cikinta, sakamakon abinda suka kasance suke aikatawa" [Ahqaaf, 13-14].  
Kuma an rawaito daga Sufyana xan Abdullahi (رضي الله عنه) yace:
"Na ce ya ma'aikin Allah! Ka gaya min wata magana a cikin musulunci, wanda ba zan tava tambayar wani in banda kai ba, Sai yace: Kace: Nayi imani da Allah, sa'annan ka tsayu", Muslim ya rawaito shi.

        Kuma shi Ubangijinmu shine ake yin bauta a gare shi a kowani zamani da kowani wuri,      Kuma shine ya zama wajibi ayi masa biyayya; kada a sava masa,      Allah ta'alah yana cewa:
"kuma ka bauta wa Ubangijinka har sai mutuwa ta zo maka", [Hijri,  99].
        Maluman tafsiri suka ce:     Ka yi ta bautawa Ubangijinka ko-yaushe,    har mutuwa ta zo maka.
        Alhasan albasariyرحمه الله- yace:
"Mutum mumini bashi da wani lokaci da zai yanke yin bauta, har sai mutuwa ta zo masa".

        Kuma duk wanda ya fahimci waccar ayar da cewa: WAI SHARI'OI SUNA SAUKA GA BAWA, BAYAN YA ISA MARTABAR SAMUN YAQINI, wanda kuma shine: koruwar shakka a gare shi, to lallai yana cikin zindiqai mulhidai masu rushe addini da bidi'oi,     kuma addininSa ba musulunci ba ne.

         Kuma idan har watan ramadhana wajabcin azumtarsa ya kare, tare da abubuwan biyayya mabanbanta da aka shar'anta a cikin watanSa,     To lallai Allah ya shar'anta wassu aiyukan na alkhairi a bayan watan ramadhana,    ya kuma wajabta farilloli,   yayi hani kan abubuwa na haramun,    
Saboda an shar'anta yin azumi guda shida (6) a cikin watan shawwal,   Hadisi yazo daga Abu-Ayyub   (رضي الله عنه) yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Duk wanda ya yi azumi watan ramadhana sa'annan sai ya biyar da wassu guda shida (6) a cikin watan shawwal, to kamar yayi azumin shekara ne", Muslim ya rawaito shi.

        Kuma an shar'anta azumtar kwanaki guda uku (3) daga kowani wata, Wannan shima kamar yin azumin shekara ne.    kamar yadda hadisi ya nuna haka.

        Kuma an shar'anta yin azumin ranar litinin da alhamis, da azumin arafah, da ashurah, da yin azumin kwana goma na farkon watan zulhijjah.

        Kuma an shar'anta ambaton Allah, tare da yin karatun alqur'ani.

        Kuma mafificin nafila shine yin sallah a cikin tsakar dare.

        Kuma an shar'anta yin sadaka, da nau'ukan ciyarwa mabanbanta.

        Kuma lallai watan shawwal shine farkon jerin watanni aikin hajji guda uku,      Don haka, Aiyuka na-gari kamar yadda suke a cikin watan ramadhana, to lallai an shar'anta su a sauran watannin na bayan ramadhana.       Kuma lallai su bayi masu rigaye wajen aikin alkhairi sune masu yin waxannan ibadun dayawa.

        Yana kuma daga cikin makircin shexan Wassu mutanen kasala kan aikata sallar farilla sai ta same su,     Sai su yi sallah a cikin watan azumi,   su kuma dena yinta a bayan watan,     ko kuma suyi wassu sallolin su kuma bar wassu,      Wannan kuma kafirci ne babba,    saboda faxin Allah ta'alah:
"Kuma ku tsayar da sallah, kada kuma ku zama daga cikin mushirkai" [Ruum, 31].    Da faxinSa maxaukaki:
"Me ya shigar da ku cikin wutar saqara?    Sai su ka ce: Bamu kasance daga cikin masu yin sallah ba", [Muddasir, 42-43].
Da kuma saboda faxinSa (صلى الله عليه وسلم):
"Alkawarin da yake tsakaninmu da munafikai shine sallah, Duk wanda ya bar yinta to lallai ya kafirta", [Attirmiziy ya rawaito shi].
Kuma saboda ijma'in sahabbai kan kafirta mutumin da ya qi yin sallah.

        Wanda kuma ya yi barci bai yi sallah ba, Sai kuma ya tashi ya sallace ta, a ta fiskar al'ada,      ko ya jinkirta ta zuwa qarshen lokacinta,      ko ya bar yin sallah a cikin jama'a      To wannan zai mutu ba a kan tafarkin Manzo ba.

        Allah ta'alah yana cewa:
"ya ku waxanda suka yi imani ku kiyaye dokokin Allah iya kiyayewa kuma kada ku mutu face kuna musulmai" [Ali-imrana, 102].   

ALLAH YA YI MINI ALBARKA NI DA KU CIKIN ALQUR'ANI MAI GIRMA.


HUXUBA TA BIYU

Yabo da godiya sun tabbata ga Allah; ma'abocin girma da karramawa,    da mulkin da ba a cimmasa,    da kuma buwayar da bata qasqanta,  
Kuma ina shaidawa babu abun bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokan tarayya,    mamallaki mai tsarki da kamala,  
Ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa,  
Ya Allah ka yi daxin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka annabi Muhammadu,    da iyalansa da sahabbansa masu karamci.
       
Bayan haka,
Ku kiyaye dokokin Allah iyakar kiyayewa, Kuma ku yi riqo a musulunci da igiya mai qarfi,

Bayin Allah!
        Lallai maqiyinku shexan ya kasance a xaxxaure a cikin watan azumi, amma yanzu yana son ya xau fansa, don ya sanya aiyukanku su zama qura abar sheqewa,   Sai ku mayar masa da martani ta hanyar riqo da Allah, da kuma tabbatuwa akan hanyarSa miqaqqiya,

        Kuma ku sani lallai samun rabo na har abada yana nan ne cikin haqurtar da kai na xan wani lokaci, kan biyayya wa Allah, da barin yin savo a gare shi,

        Kuma ku sani lallai tavewa da yin hasara na har abada ya kan fara ne, da bin son zuciya na xan wani lokaci.

        Kuma da xan'adam zai yi tunani kan qarancin kwanakin rayuwa, da gushewar duniya,   to da ya shagaltu da yin aiyuka nagari,     kuma da burace-burace basu vatar da shi ba.

Allah ta'alah yana cewa:
"A ranar da zai tattara Su, kamar gabaxayansu basu zauna a cikin duniya ba sai kimanin wata sa'a a cikin yini,  da suke gane juna a cikinta.  Lallai waxanda suka kafirce da ayoyin Allah sun yi hasara, kuma basu kasance shiryayyu ba" [Yunus, 45].
Idan wannan shine lokacin dukkan halittu, To MENENE YAWAN SHEKARUN DA AKA BAKA DAGA WANNAR "SA'AR?

        Kuma hadisi ya zo daga Abdullahi xan Abbas Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Ni'imomi guda biyu an bugi hancin yawa-yawan mutane akansu, Lafiya da kuma faragar lokaci", Bukhariy ya rawaito shi.

        Kuma lallai wannan gidan ba gidan dawwama ba ce,   Gidanka na haqiqa itace gidan lahira, wanda ko ta zama ni'ima ce tabbatacciya, ko kuma azaba mai raxaxi.

Bayin Allah!
"Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan annabin…" [Ahzab: 56].

Addu'a ….
……………….
……………….
……………….


No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...