HUXUBAR
MASALLACIN ANNABI (r)
JUMA'A, 15 /SHAWAAL/1436H
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI ALIYU XAN ABDURRAHMAN AL-HUZAIFIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
Yabo ya tabbata ga Allah Mabuwayi Mai
baiwa, Mai gafarta zunubai, Mai karvar tuba, Mai tsananin aquba, Ma'abocin ni'imah da falala, Babu abun bautawa da gaskiya sai
shi, Makoma zuwa gare shi take, Ina yabo wa Ubangijina kuma ina gode masa, Ina tuba zuwa gare shi, Ina kuma neman gafararSa, Ina kuma shaidawa babu abun bautawa da
gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya, Maxaukaki Mai girma. Kuma ina shaidawa lallai Annabinmu
kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa, Mai yin bushara da gargaxi. Allah ka yi qarin salati da sallama da
albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammadu, da iyalanSa, da sahabbanSa, Waxanda suke rigaye zuwa ga kowace falala
da alkhairi.
Bayan haka:
Ku ji tsoron Allah ta hanyar yin aiki da abinda
yayi umurni, da kuma nisantar abubuwan da ya yi hani akansu ya tsawatar,
Ya ku bayin Allah!
Ku aikata aiyuka na kwarai don gyara
lahirarku, kuma kada ku vata
aiyukan; Sai ku yi asarar
kayukanku, Allah maxaukaki yana cewa:
"Kace: kuma ku yi aiki, da sannu Allah
zai ga aikinku, da ManzonSa, da Muminai,
Kuma za a mayar da ku zuwa ga masanin abinda ke fake, dana bayyane, Sa'annan ya baku labari kan abinda kuka
kasance ku ke aikatawa", [Taubah,
105].
Har ila yau Allah ta'alah yana cewa:
"Ya ku waxanda suka yi imani ku yi
biyayya ga Allah, kuma ku yi biyayya ga wannan Manzon, kuma kada ku vata aiyukanku", [Muhammadu,
33].
Allah ta'alah yana cewa:
"Kace, Lallai waxanda suka yi hasara sune
waxanda suka yi hasarar rayukansu da iyalansu, ranar qiyamah, Lallai wancan itace hasara mabayyaniya",
[Zumar, 15].
Kuma –Musulmai- ku gyara duniyarku ta
hanyar neman halal, da kuma ciyar da
shi ta qofofin alkhairi na wajibi, dana mustahabbi, da na halal, Ita kuma wannan duniyar ku sanya ta ta
zamto wurin yin guzurinku zuwa gidan ni'imah, Kuma kada ku bari duniya ta ruxe ku da
abubuwan qyalqyalin da suke cikinta,
Kuma kada ta fitine ku kan lahirarku,
Sai ka yi aiki –Ya kai musulmi- don gyara
duniyarka, ka kuma yi aiki tuquru don gyara
lahirarka, Ya zo a cikin wani hadisi:
"Ba shine mafi
alherinku ba Wanda ya bar lahirarsa don duniyarsa, Ko kuma wanda ya bar duniyarsa don
lahirarsa".
An rawaito daga Almustaurid xan Ash-shaddad (رضي الله عنه) yace:
"Wata rana mun kasance a wajen Manzon
Allah (صلى الله عليه وسلم) sai muka tattauna akan duniya da
lahira, Sai wassu suka ce: Kawai
duniya guzuri ce na lahira; A
cikinta akwai aiki, akwai sallah, akwai zakkah. Sai wassu kuma suka ce: Lahira a cikinta akwai aljannah, Suka faxi abubuwan da Allah ya nufe su da
faxa. Sai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace: Duniya ba
komai ba ce idan aka kwatanta da lahira,
Sai kamar yadda xayanku zai tafi zuwa kogi, Sai ya tsoma yatsarsa a
cikinsa, Duk abinda ya fita a
cikinsa shine misalin duniya", [Alhakim ya rawaito shi a cikin littafin
Almustadrak].
Kuma Alhakim ya sake ruwaitowa daga Sa'ad xan
Xariq, daga BabanSa, daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Madalla da gidan duniya ga mutumin
da yayi guzuri a cikinta ga lahirarsa,
har UbangijinSa ya yarda da shi. Tir da gidan duniya ga wanda ta hana shi
neman lahirarSa, Har ya kasa samun
yardar UbangijinSa".
Alhasan
Albasariy (رحمه الله) yace:
"Madalla da gidan duniya ga bawa
mumini; saboda mumini yayi aiki a
cikinta xan kaxan, ya kuma xauki guzurinsa daga cikinta zuwa ga Aljannah. Tir
da wannan duniyar ga kafiri da munafiqi;
saboda ya tozarta dararenSa,
Sannan yayi guzurinsa daga cikinta zuwa gidan wuta", [Ahmad ya rawaito shi a cikin littafinsa: Azzuhud].
Kuma
lallai kowani mutum ya sani ilimi na yaqini; cewa zai qaura ya bar wannan gida
na duniya, yana mai barin duk
abinda Allah ya bashi a cikin wannan gida, a bayan bayansa, Ta yadda babu wani abu da zai kasance tare da shi, sai aikinsa
kawai, Idan na alheri ne ya ga
alheri, In kuma na sharri ne to
sai ya ga sharri, Kuma idan har
ya zama halin mutum zai qare ne zuwa ga haka, kuma zai tafi zuwa ga wannan
makomar To, ya zama wajibi mutum yaje wajen UbangijinSa da mafi girman
abinda bawa zai iya aikatawa na aiyukan kwarai, Saboda babu wata hanya da bawa zai
tsira a wajen UbangijinSa sai ta hanyar
aiyuka na kwarai, Allah ta'alah yana
cewa:
"Kuma dukiyoyinku da 'ya'yanku basu
kasance za su kusantar da ku da wani kusanci ba a wurinmu, Saidai wanda ya yi imani, ya kuma yi aiki
na kwarai, To waxannan kam suna da
sakayya na ninki saboda abinda suka aikata,
kuma Su suna cikin banaye suna amintattu",
[Faxir, 37].
Kuma
–ya kai musulmi- damuwarka –a ko yaushe- ta kasance kan rabauta da sha,
daga dausayin Annabi Muhammadu; shugaban 'ya'yanAdam (صلى الله عليه وسلم) ; Saboda shine farkon
abun shan 'yan aljannah. Kuma duk
mutumin da Allah ya datar da shi; ya yi baiwa a gare shi da samun sha daga
wannan dausayin to lallai bashi da wani tsoro a bayan haka. Kuma duk waxanda zasu sha daga wannan
dausayin to lallai Allah ya sauqaqe musu wahalhalun da suke a gabanin
haka, Kuma lallai yin imani da wannan dausayin
yana cikin imani da ranar qarshe,
Saboda haka; Duk wanda bai yi imani da wannan dausayin ba to ba shi da
imani kwata-kwata; Wannan kuma
saboda rukunnan imani ba a rabe su;
Don haka, Duk wanda bai yin imani da rukuni guda xaya daga cikin
rukunnan imani ba, to lallai ya kafirce da su gabaxaya,
Kuma
shi wannan dausayin karramawar Allah ta'alah ne ga annabinSa
Muhammadu, Wanda al'ummarSa za su
sha daga gare shi, a filin da za a tattara halittu, da matsayar hisabi, ranar
qiyamah, a yinin da tsayinsa shine
gwargwadon shekara dubu hamsin, a wajen kafirai. Amma sai Allah ya taqaice tsayinsa ga
mumini.
Zai
lulluve mutane a cikin wannan yini, a filin hisabi irin abubuwan da ba za su
iya jure musu ba na baqin ciki, Kuma
ba don Allah ya bada qarfi a jikinsu na juriya, da wanzuwa ba = to da sun mutu
gabaxaya.
Kuma
a filin hisabi qishi mai tsananin gaske wanda ke qona hanta, irin wanda mutane
basu tava jinsa ba zai kama su, To
sai Allah ya karrama annabinSa Muhammadu (صلى الله
عليه وسلم) ya azurta shi da
dausayin ruwa, wanda al'ummarSa zata sha daga gare shi, Alhalin shi kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana tsaye a farkon wannan tafkin yana kallon al'ummarSa, yana kuma yin farin ciki da haka,
matsanancin farin ciki, kana kuma yana
kiran al'ummarSa don su sha daga wannan dausayin.
Kuma faxin wannann dausayin da siffar ruwansa
hadisan annabi masu yawa (mutawatirai) sun zo da bayaninsa, Kuma alqur'ani shima ya ambace shi a
cikin suratul kausar,
Kuma kowani Annabi yana da tafkinsa. Hadisi ya zo daga Samurah (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Lallai annabawa suna alfaharin wa yafi
yawan mabiya daga al'ummarSa, Ni ina
fatan a wannan yinin na kasance na fi su yawan masu gangarowa zuwa ga dausayi, Kuma kowani annabi a cikinsu a wannan
yinin yana kan wani dausayin da yake cike, a hannunsa akwai wata sanda, yana
kiran wanda ya sani daga cikin al'ummarSa, Kuma
kowace al'ummah tana da wani alama, wanda annabinta zai gane ta da shi", [Attirmiziy ya rawaito shi, da Axxabaraniy].
Kuma dausayin Annabinmu (صلى الله عليه وسلم) yafi yawan mazowa, kuma ya fi girma, ya kuma fi zaqi, kamar
shari'arSa; An ruwaito daga
Abu-hurairah (رضي الله عنه)
daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Lallai tafkina yafi Ailah zuwa Adan
nisa, Kuma yafi nono fari, Yafi zuma zaqi, Yafi qanqara sanyi, Kofunan shansa sun fi adadin taurari yawa", [Muslim ya rawaito shi]. A wata riwayar da ba
ta Muslim ba, "Qamshinsa yafi turaren almiski daxi".
Daga Abu-zarrin (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Na rantse da wanda raina yake
hannunSa, Kofunan shan wannan tafki
sun fi taurarin sama yawan adadi, a cikin dare mai duhu, wanda bata da hazo ko
gajimare, daga cikin kofunan aljannah, Duk wanda ya sha daga wannan dausayi to ba
zai tava jin qishi ba, qarshen abinda ke kansa. Indaroro guda biyu ne suke tunkuxowa da
qarfi daga gidan aljannah don qara shi", [Ahmad da Muslim da Annasa'iy suka ruwaito
shi].
Daga Abu-Umamah (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Dausayina tsayinsa kwatankwacin
abinda ke tsakanin garin Adan da Amman ne,
Shi kuma yafi faxi sosai, A
jikinsa akwai vangarori guda biyu na zinari da azurfa –ma'ana:
indaroro guda biyu-, Abin shansa
yafi nono fari, yafi zuma zaqin
xanxano, yafi turaren almisku
qamshi, Duk wanda ya sha daga gare shi
ba zai tava jin qishi ba, kuma ba za a baqanta fiskarsa ba har abada" [Ahmad da Ibnu-Majah da Ibnu-Hibbana suka
ruwaito shi].
Daga
Zaid xan Khalid (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Shin kun san menene alkausara? Wani
kogi ne da Ubangijina ya bani shi a cikin gidan aljannah, A cikinsa akwai alheri dayawa, Al'ummata zata sha daga gare shi ranar
qiyamah, Yawan kofunansa kamar adadin
taurari ne, Wani bawan daga cikinsu za
a karkatar da shi, sai nace: Ya
Ubangijina! lallai yana daga cikin al'ummata? Sai ace: Lallai kai ba ka san abinda ya
qirqiro ba a bayanka" [Ahmad da
Muslim da Abu-Dawud suka ruwaito shi].
Saboda
waxannan dalilan shi Dausayi qasa ce mai faxi, a filin tsayuwar qiyama, Wanda
Allah zai cike ta da ruwa, daga kogin alkausara, Indararo guda biyu ne suke zuba a cikin
wannan dausayin, na zinari da
azurfa, daga kogin alkausara, kuma wannan tafkin ruwansa baya
raguwa, Kuma kowani mumini namiji da
mumina mace za su sha daga wannan dausayin,
alhalin suna kan matsanancin qishi mai girma, To daga nan kuma babu wani mutum da zai
ji qishi har abada, bayan shansa.
Kuma
lallai waxanda za su zo wa Annabi (صلى الله
عليه وسلم) akan tafkinsa sune: WAXANDA SUKE BIN SUNNARSA (عليه الصلاة والسلام) SUKE RIQO DA TAFARKINSA, SUNE KUMA MASU NISANTAR MANYAN
LAIFUKA (الكبائر) DAGA ZUNUBAI, Allah ta'alah yana cewa:
"Idan kuka nisanci alkaba'iran da
aka hane ku, to sai mu kankare muku
qananan laifukanku, kuma mu shigar da
ku mashiga mai karamci" [Nisa'i: ].
Kuma bayan riqonsu da sunnar Annabi (صلى الله عليه وسلم) da shiriyarsa, suna kiran mutane zuwa ga Allah (da'awah), akan ilimi da basira, Allah ta'alah yana
cewa:
"Ka ce: Wannan itace hanyata; ina
yin kira zuwa ga Allah, akan basira,
Ni da wanda ya bi ni, Kuma tsarki ya tabbata ga
Allah, Ni ban zama daga cikin mushirkai
ba" , [Nahli: ].
Sai suke kira zuwa ga/ Shari'ar Annabi Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) , suke kuma nisantar bidi'oi da qirqirarrun abubuwa a cikin
addini, da abubuwan da shari'a ta
kyamata, Tare da lazimtar yin ikhlasi
wanda yake kore RIYA DA YI DON MUTANE SU JI (SUM'AH).
Kuma yana
daga cikin sabbuban sha daga dausayin Annabi (عليه
الصلاة والسلام) yawaita
yin salati da sallama ga Manzon Allah (صلى الله
عليه وسلم).
Allah
ta'alah
yana cewa:
Bimillahir rahmanir rahim:
(إنا أعطيناك الكوثر فصَلِّ لربك وانحر،
إنّ شانئك هو الأبتر ).
"Lallai mune
muka baka tafkin alkausara, Sai kayi
sallah wa Ubangijinka, kuma ka yi suka
-a
gare shi-, Lallai wanda ke aibanta ka shine mai yankakkiyar albarka" [Alkausar, 1-3].
ALLAH YA YI MINI ALBARKA NI DA KU CIKIN
ALQUR'ANI MAI GIRMA.
….
….
HUXUBA TA BIYU
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah; ma'abocin
girma da karramawa, da mulkin da ba a
cimmasa, da kuma buwayar da bata
qasqanta , Ina yin godiya ga
Ubangijina akan ni'imomi dayawa,
Kuma ina shaidawa babu abun bautawa da gaskiya
sai Allah shi kaxai yake bashi da abokin tarayya, Mamallaki Mai tsarki da Kamala,
Ina kuma shaidawa lallai annabinmu kuma
shugabanmu Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa, Mafificin salati da sallama su qara
tabbata a gare shi. Da kuma iyalanSa
da sahabbanSa masu karamci.
Bayan haka,
Ku kiyaye dokokin Allah iya kiyayewa, Kuma ku yi riqo a musulunci da igiya
mai qarfi,,,
Ya ku bayin Allah!
Mamakin girman rabon mutumin da Allah ta'alah ya masa kyautayin
zuwa tafkin Annabinmu Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) ; ya kuma sha daga gare shi, don ya rabauta da rashin jin
qishi har abada.
Sai kuma ku yi mamakin girmar hasarar mutumin da aka haramta
shan ruwan wannan tafkin a gare shi, sannan aka kore shi, Kuma Ubangijinka baya zaluntar
kowa!
Ya ku musulmai!
Lallai yana daga cikin sabbuban hana gangarowa zuwa ga tafkin
Annabi (صلى الله عليه وسلم) YIN BIDI'OI DA AIKI DA QIRQIRARRUN ABUBUWA
A CIKIN ADDINI, DA KANGE MUTANE DAGA MUSULUNCI, DA ZANCE KO DA AIKI, KO FATAWA.
Kamar yadda hakan ya zo a cikin hadisan da aka ruwaito, kan sabbuban da
suka sanya aka kori wassu mutane daga cikin wannan al'ummar. A cikin waxannan hadisan ance: LALLAI KAI BA KA SAN ME SUKA QIRQIRO BA
a bayanka, Sai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"A
nisanta wanda ya canza addini a bayana mafi nisan nisantawa".
Kuma yana daga
cikin sabbuban da suke hana zuwa tafkin Annabi (صلى
الله عليه وسلم): Aikata manyan zunubai, saboda
zunubai abubuwa ne da suke vata zukata.
Kuma Riya da yi don
mutane su ji (sum'ah) suma suna cikin abubuwan da suke hana sha daga wannan
dausayin.
Haka kuma
zaluncin da ke kasancewa a tsakanin bayi, Shima sababi ne mai girma na hana sha
daga dausayinSa.
Kuma alaqa da
take tsakanin yin sakayya da hana shan ruwa daga dausayinSa, da waxannan
aiyukan (da suka zama sababin haka), a fili take ga wanda yayi tunani akan haka; Saboda
Duk wanda a duniya ya bi shari'ar Annabi (صلى
الله عليه وسلم), ya kuma yi riqo da
shiriyarSa to sai ya gangara tafkinSa a lahira, ya kuma sha daga gare shi.
Wanda kuma ya canza, ya qirqiro abubuwa a cikin addininSa sai a
hana shi; saboda ya kange mutane daga
bin gaskiya.
"Lallai
Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani ku yi salati a
gare shi, da sallama mai yawa" [Ahzab: 56].
……………….
……………….
Addu'a ….
………………..
………………..