SIFFAR WANKAN JANABA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tambaya:
Yaya ake yin wankan janaba?
Amsa:
Wankan janaba tana da siffofi guda biyu;
(1) Yanayi da ke isarwa na wajibi,
(2) Da kuma siffa cikakkiya ta mustahabbi([1]).
(1) Yanayi da ke isarwa na wajibi,
(2) Da kuma siffa cikakkiya ta mustahabbi([1]).
Amma siffar da ta ke isarwa ga wanda yayi ta kuma ta wajibi:
Itace Bawa ya game jikinsa da ruwa tun daga farkon farawa tare da niyya; Ma'anar
wannan: Shine bawa ya game jikinsa da ruwa ta kowace fiska yaga dama tare da
niyya. Haka zai isar wa mutum; Yayi niyya sai yayi nitso cikin wani kududdufi
ko kuma kogi; ta yadda ruwan zai zama ya game jikinsa; Idan ya aikata haka tare
da niyya to ya tsarkaka daga janaba.
Amma ita kuma siffa ta biyu cikakkiya ta mustahabbi Itace:
Na farko:
Bawa ya wanke tafukansa guda biyu sau uku gabanin tsunduma su
cikin ruwa.
Na
biyu:
Sai ya sanya hannunsa cikin ruwa don ya wanke al'aurarsa da
duk wurin da dauxar janaba ta riga ta tava.
Na uku: Sannan sai ya wanke hannunsa
da qasa
ko da sabulu don gusar da dauxar janaba da ya tava da hannunsa.
Na
hudu:
Sai kuma ya yi alwalarsa cikakkiya irinta sallah; ma'ana: Ya
kurkuri baki, da shaqa ruwa a hanci, ya wanke fiskarsa, sau uku, da hannayensa biyu
zuwa guiwowinsu, sau uku, ya kuma shafi kansa da kunnuwa, sannan sai ya wanke qafofinsa
sau uku uku.
Na
biyar:
Sai kuma ya wanke kansa sosai, yana mai shigar da 'yan
yatsunsa cikin tushen gashin kansa; Idan har yayi zaton cewa ruwan ya shiga
tushensu to sai ya kwara ma kansa kamfata uku.
Na
shida:
Daga nan; Sai ya wanke sauran jikinsa da ruwa sau xaya,
yana mai farawa da saman jikinsa, har ya taho qasa.
Na bakwai: In
har kuma ya so zai iya jinkirta wanke qafarsa
a yayin alwalarsa har sai ya zo qarshen
wankarsa gabaxaya, sai ya koma gefe don wanke qafofinsa.
Waxannan
bayanan zasu bayyana cikin hadisan dake tafe:
Na
farko:
Hadisin Maimunah (RA), ta ce:
"وَضَعْتُ لِرَسُولِ اللهِ r
غُسْلاً وَسَتَرْتُهُ فَصَبَّ عَلَى يَدِهِ فَغَسَلَهَا مَرَّةً،
أَوْ مَرَّتَيْنِ -قَالَ سُلَيْمَانُ: لاَ أَدْرِي أَذَكَرَ
الثَّالِثَةَ أَمْ لاَ-، ثُمَّ أَفْرَغَ بِيَمِينِهِ عَلَى شِمَالِهِ فَغَسَلَ فَرْجَهُ،
ثُمَّ دَلَكَ يَدَهُ بِالأَرْضِ أَوْ بِالْحَائِطِ، ثُمَّ تَمَضْمَضَ وَاسْتَنْشَقَ،
وَغَسَلَ وَجْهَهُ وَيَدَيْهِ، وَغَسَلَ رَأْسَهُ، ثُمَّ صَبَّ عَلَى جَسَدِهِ، ثُمَّ
تَنَحَّى فَغَسَلَ قَدَمَيْهِ، فَنَاوَلْتُهُ خِرْقَةً فَقَالَ بِيَدِهِ هَكَذَا، وَلَمْ
يُرِدْهَا" ([2]).
Ma'ana: (Na sanya wa Manzon
Allah –SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA- ruwan wankansa, na kuma suturce shi, sai ya
zuba wa hannunsa sai ya wanke shi sau xaya ko sau
biyu, -Sulaiman Al-a'amash ya ce: Ban sani ba ya faxi
wanke hannu a karo na uku ko a'a-, Sa'annan sai ya zuba ruwa daga hannun
damansa i zuwa "hagu" xinsa
sai ya wanke "gabansa", sa'annan sai ya xauraye
hannunsa da qasa ko da katanga, sa'annan sai ya kurkuri baki ya kuma shaqa,
ya wanke fiskarsa da hannayensa, kana ya kuza ruwa a sauran jikinsa, sa'annan
ya koma gefe ya wanke qafofinsa guda biyu. Matar manzon
Allah Maimunah ta ce: Sai na miqa masa tsumma don
tsanar da jiki, amma sai ya karkaxe ruwa da
hannayensa; bai buqaci tawol ba).
A kwai kwatankwacin wannan
hadisin daga A'ishah (RA), wanda kuma shi ne:
Hadisi na biyu: Hadisin
A'ishah (RA) wanda Imamul Bukhariy da Muslim suka rawaito shi.
ta yadda ya zo a cikinsa:
عَنْ عَائِشَةَ، قَالَتْ: «كَانَ رَسُولُ اللهِ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا اغْتَسَلَ مِنَ الْجَنَابَةِ يَبْدَأُ
فَيَغْسِلُ يَدَيْهِ. ثُمَّ يُفْرِغُ بِيَمِينِهِ عَلَى شِمَالِهِ فَيَغْسِلُ
فَرْجَهُ، ثُمَّ يَتَوَضَّأُ وُضُوءَهُ لِلصَّلَاةِ، ثُمَّ يَأْخُذُ الْمَاءَ
فَيُدْخِلُ أَصَابِعَهُ فِي أُصُولِ الشَّعْرِ، حَتَّى إِذَا رَأَى أَنْ قَدْ
اسْتَبْرَأَ حَفَنَ عَلَى رَأْسِهِ ثَلَاثَ حَفَنَاتٍ، ثُمَّ أَفَاضَ عَلَى
سَائِرِ جَسَدِهِ، ثُمَّ غَسَلَ رِجْلَيْهِ» ([3]).
Ma'ana: (Manzon Allah –saw-
ya kasance idan ya zo yin wankan janaba; ya kan fara da wanke hannunsa guda
biyu, sannan sai ya kwara ruwa daga hannunsa na dama zuwa ga hagu don ya wanke
farjinsa, Sannan sai ya yi alwalarsa irinta salla, sannan sai ya xauki
ruwa sai ya shigar da 'yan yatsunsa cikin tushen gashin kansa, idan yaga cewa
ya isar da jiqajiqan ruwa to sai ya xibi
kamfata uku, Sannan sai ya kwara ruwa ga sauran jikinsa, Sannan sai ya wanke qafofinsa
guda biyu". Wannan hadisin da wanda ya gabace shi, sun yi bayanin siffar
wankan manzon Allah (sallallahu alaihi wasallama).
A dunqule;
dangane da cikakken yanayi ko siffar wanka: To shi ne, Bawa ya wanke hanayensa,
sa'annan ya wanke farjinsa, da duk gunda dauxa
ta tava,
sa'annan ya yi alwala alwalarsa irin ta sallah, sa'annan ya xauki
ruwa a hannunsa don ya tsettsefe gashin kansa da shi, yana mai shigar da
yatsunsa a cikin tushen gashin kansa; don ya jijjika fatarsa, sa'annan ya xebi
kamfata uku don wanke kansa, kana ya kwara ruwa a sauran jikinsa.
Kuma ba wajibi ne mace ta warware gashin kanta a wankan
janaba ba. Amma hakan wajibi ne akanta a wankan haila; saboda hadisin Ummu
Salamah (RA), ta ce: Na ce: Ya manzon Allah lallai ni mace ce da nake xaure
gashin kaina; Shin zan warware shi don wankan janaba? Sai ya ce:
"لا، إِنَّمَا يَكْفِيكِ أَنْ تَحْثِي عَلَى رَأْسِكِ
ثَلاثَ حَثَيَاتٍ، ثُمَّ تُفِيضِينَ عَلَيْكِ الْمَاءَ؛ فَتَطْهُرِينَ" ([4]).
Ma'ana: (A'a; Ai zai ishe ki
kawai ki xebi kamfata guda uku ki kwara akanki, sa'annan sai ki kwara ruwa
a jikinki; sai ki zama kin yi tsarki).
Walhamdu lillah!
Laraba/ 08/ Rabius saniy/1436h
Daidai da 28/01/2015m
No comments:
Post a Comment