WUCE GONA-DA-IRI CIKIN ADDU'A
(الاعتداء
في الدعاء)
Menene
wuce gona-da-iri cikin ADDU'A wadda Allah ya hane mu aikata shi? ya kuma
bayyana cewa baya son ma'abutansa, cikin fadinsa:
(ادعوا ربكم تضرعًا وخفية إنه لا يحب المعتدين) [سورة الأعراف،
55].
tare
da ambato surorinsa da nau'ukansa?
Bismillahir rahmanir raheem///
A ayar da ta gabata Allah (s w t) yayi umurni kuma yayi hani;
yayi umarni ya kuma kwadaitar kan: Yin addu'a da rokonsa a hali na
kankan-da-kai, da kuma yanayi dake kasa da bayyanawa (ma'ana: addu'ar bawa ta
kasance a boye; saboda yana rokon mai jine makusanci, ba kurma ko kuma wanda ba
ya halarce ba, kamar yadda yazo cikin Sahihul Bukhari, [lamba: 2992], Muslim, [2704].
(ادعوا ربكم تضرعا وخفية).
Sa'annan sai kuma Allah ta'alah yayi hani da tsawatarwa kan:
Ketare iyaka da wuce-gona-da-iri, ta hanyar bayyana rashin soyayyarsa ga
ma'abota hakan, a cikin fadinsa:
(إنه لا يحب المعتدين).
Maluma su ka ce: Duk da cewa ayar tana nuna: Gamemmen rashin son
Allah ga/ daukacin masu wuce iyaka a kowanni babi, (don haka: Duk mai ketare
haddin shari'a a kowanne ibada Allah baya sonsa) Sai dai kasancewar zuwan hanin
(wuce-gona-da-iri -a ayar-) yazo ne bayan umurni kan rokon Allah: Hakan na nuni
na musamman kan: HANI BISA GA KETARE HADDIN SHARI'A CIKIN ADDU'A
Shi
kuma
(الاعتداء).
Shine:
ketare iyakar da shari'a tace a tsaya akanta. Shi yasa a fassare- fassaren
hausa a ke fassara shi da: Wuce-gona-da-iri.
Zai yi kyau a sani cewa daga cikin wuce iyaka a babin addu'a (roko)
akwai wanda ke kaiwa izuwa ga kafirci, shirka (me fitarwa daga musulunci),
yayin da akwai wadda bai kai ga hakan ba (tare da cewa, Allah yaki mai aikata
shi; don haka haramun ne) kamar yadda zai bayyana daga nau'ukan wuce
gona-da-iri cikin addu'a.
NAU'UKAN
WUCE-GONA-DA-IRI CIKIN ADDU'AH:
Lallai kamar yadda ya gabata ketare iyakar Allah a cikin addu'a
mataki-mataki ne, akwai wanda yake fitar da ma'abucinsa daga musulunci, akwai
kuma wanda bai kai i zuwa ga hakan ba, A nan zan ambato wassu nau'uka na kowanne
daga cikinsu; Kamar haka:
1-
Yana
daga cikin wuce-gona-iri a cikin addu'a, kai shine ma yafi hatsari da
cutar da addinin bawa: Rokon wani Allah –ko shi wanene- rokonsa abinda ba wanda
zai iya baka shi sai Allah (s w t), kamar yaye bala'i, jawo wani amfani, warkar
da maras lafiya, bada arziki da 'ya'ya, neman dawowan batacce, d. s. Ya shiga
cikin wannan nau'in: Rokon Shehu da Bello da wassu daga cikin mutane a kasar
hausa-fulani ke yi a lokacin faduwa, a madadin komawa zuwa ga Allah tare da
cewa: Innah lillahi wa innah ilaihi raaji'una, ko makamancin hakan.
Lallai wannan nau'i na wuce
iyaka ya kai yadda ya kai wajen muni, kuma ubangiji ta'alah ya kafirta
ma'abocinsa a wurare da dama, daga cikinsu akwai fadinsa:
(ومَن أضل ممن يدعو من دون الله مَن لا
يستجيب له إلى يوم القيامة وهم عن دعائهم غافلون. وإذا حُشر الناس كانوا لهم أعداء
وكانوا بعبادتهم كافرين) [سورة الأحقاف: 5-6].
Wannan mas'alar saboda
girmanta tana bukatan wassu zamanmaki. Allah ya bamu ikon fadakar da duk wadda
mu ka ji yana aukawa cikin hakan, musamman tsofaffi da jahilai. Allah shi
kyauta.
2-
Yana daga cikin wuce-gona-da-iri a cikin addu'a: Bawa ya roki abubuwan da Allah ya kebanta da su a
rububiyyarsa ko sifofinsa, kamar ya nemi: Taskokin Allah su kasance a wajensa;
don ya rinka bawa wanda yaso abinda ya so, ya kuma hana wani abinda yaso, ko
kuma ya roki sanin gaibu, da sauransu.
3-
Yana daga cikin wuce-gona-da-iri a cikin
addu'a: Bawa ya roki abubuwan da basu dace da shi ba, kuma Allah ba zai ba
shi su ba; kamar ya roki a bashi matsayi da daraja irin ta annabawa da
manzanni, ko ya nemi a mayar da shi mala'ika; da zai wofanta ga barin bukatar
abinci da abin sha, da biyan bukata. ko ya roke shi ya kasantar da shi ma'asumi
kamar mala'iku ko annabawa da sauransu.
4-
Yana daga cikin wuce-gona-da-iri a cikin addu'a: Bawa ya roki abinda aka sani cewa Allah cikin hikimarsa
ba zai aikata su ba; kamar ya roki Allahn ya dawwamar da shi ba mutuwa har zuwa
kiyama; (ma'ana: kar ya dauki ransa), ko ya nemi a kawar masa da halayya da
bukatu na 'dan adamtaka kamar ci, sha, barci, mantuwa, ko ya musuluntar da duk
duniya, ko yasa kowa-da-kowa cikin aljanna, ko ya bashi 'da ba tare da mace ba,
da sauransu.
5-
Yana daga cikin wuce-gona-da-iri a cikin addu'a: Bawa ya roki abinda Allah ya hane shi, kamar mai neman
taimakon Allah kan aikata haramun, misali: ya roke shi ya saukake masa hanyar
alfasha ko magudi da zalunci da handama, ko ya taimake shi kan wani tafiyar da ya shirya don yin barna da zunubi a cikinta;
kamar sata, fashi, d. s.
6-
Yana kuma daga cikin wannan nau'in: Bawa ya nemi Allah yayi gafara ga wadda ya mutu yana
kafiri ko shi wanene; saboda Allah ya hana hakan, Lallai kuma wannan na faruwa
da yawa musamman a zamaninmu; zamanin fitintinu da kashe-kashe, ta yadda sau da
dama akan samu masu kashe mutanen da basu san me yasa suka kashe ba, kamar
yadda mutane da-dama da aka da dama daga wadanda ake kashewan suma basu san
dalilin da yasa aka kashe su ba. To a irin wannan hali in har labarin irin
wannan mutuwa mai abun tausayi yazo maka sai kace: Allah ya jikan musulmi. Amma
bai halatta kayi addu'ar gafara, rahama da jin kai ga wanda ba musulmi ba koda
kuma wanene shi; mahaifi ne, mahaifiya, 'da, balle waninsu; saboda Allah (s w t)
ya ce:
(وَلَا تُصَلِّ عَلَى
أَحَدٍ مِنْهُمْ مَاتَ أَبَدًا وَلا تَقُمْ عَلَى قَبْرِهِ؛ إِنَّهُمْ كَفَرُوا
بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ وَمَاتُوا وَهُمْ فَاسِقُونَ) [سورة التوبة، 84]
Ma'ana: "Kada kayi addu'a ko sallah, ga 'daya
daga cikinsu da ya mutu, har abada, kuma kada ka tsaya kan kabarinsa; lallai su
sun kafirce ma Allah da Manzonsa, kuma sun mutu suna fasikai (da suka fice daga
'da'a ma Allah; kafirai.
Allah ya sake cewa: "Bai halatta ba ga
wannan Annabi da wadanda suka yi imani da shi: Su nemi gafara wa mushirkai,
koda kuwa dangi ne makusanta, bayan ya bayyana musu cewa su 'yan wuta ne".
Kamar yadda Annabi Ibrahimu (a s) da lamarin ya bayyana masa cewa mahaifinsa ya
mutu akan kafirci barranta yayi daga gare shi:
(مَا كَانَ لِلنَّبِيِّ
وَالَّذِينَ آَمَنُوا أَنْ يَسْتَغْفِرُوا لِلْمُشْرِكِينَ وَلَوْ كَانُوا أُولِي
قُرْبَى مِنْ بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمْ أَنَّهُمْ أَصْحَابُ الْجَحِيمِ ***
وَمَا كَانَ اسْتِغْفَارُ إِبْرَاهِيمَ لِأَبِيهِ إِلَّا عَنْ مَوْعِدَةٍ
وَعَدَهَا إِيَّاهُ فَلَمَّا تَبَيَّنَ لَهُ أَنَّهُ عَدُوٌّ لِلَّهِ تَبَرَّأَ
مِنْهُ إِنَّ إِبْرَاهِيمَ لَأَوَّاهٌ حَلِيمٌ) [سورة التوبة: 113-114].
Wannan kuma shine dalilin da yasa Allah bai bada
izini ga manzonsa annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su kara tabbata a
gare shi) a lokacin da ya nemi izinin neman gafara wa mahaifiyarsa. Sannan sai
aka bashi izinin ya je ziyartar kabarinta, kamar yadda Muslim ya ruwaito [lamba:
976]:
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ قَالَ: زَارَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى
اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَبْرَ أُمِّهِ فَبَكَى وَأَبْكَى مَنْ حَوْلَهُ،
وَقَالَ: "اسْتَأْذَنْتُ رَبِّي عَزَّ وَجَلَّ فِي أَنْ أَسْتَغْفِرَ لَهَا
فَلَمْ يُؤْذَنْ لِي، وَاسْتَأْذَنْتُ فِي أَنْ أَزُورَ قَبْرَهَا فَأَذِنَ لِي؛
فَزُورُوا الْقُبُورَ فَإِنَّهَا تُذَكِّرُكُمْ الْمَوْتَ".
Tun da ko haka ne; To akwai wani mushirki, kafiri
da zai mutu akan kafirci ko shirkarsa, ko wanene shi? wanda zaka nema masa
gafara! Amsar itace: Babu!
Za dai ka ji tausayinsa, ko ka jiye masa, shi
da kuma sauran kafirai irin yadda suka yi asarar rayuwarsu; asara ta
din-din-din.
Amma addininmu ya hana nema musu gafarar
Allah. Kuma saba wa hakan na daga cikin nauoin wuce gona-da –iri cikin addu'a.
Kuma wannan mas'alar don ita nayi takaitaccen
rubutun nan nawa, saboda na tunatar da 'daukacin musulmai shari'ar mahaliccinsu,
da fatan kuma Allah ta'alah ya taimaki masu aukawa cikin wannan laifi, su gyara.
7-
Yana daga cikin wuce-gona-da-iri a cikin addu'a: Bawa ya nemi Allah ya la'anci muminai, ko ya musu addu'an
tabewa, kaskanci wai don ransa ya baci, Said bn Jubair daga cikin salaf yana
cewa:
"لا تدعوا على
المؤمن والمؤمنة بالشر؛ اللهم اخزه، والْعَنْه، ونحو ذلك؛ فإنّ ذلك عدوان".
Yace saboda yin hakan wuce-gona-da-iri ne.
Wani daga cikinsu kuma yace a lokacin da yake bayyana ma'anar ayar da nake
rubutu don amsa tambayar da ta zo akanta:
"هم الذين يدعون على
المؤمنين فيما لا يحل، فيقولون: اللهم اخزِهم، اللهم الْعَنْهم"
Wadanda Allah ta'alah ya bayyana mana cewa baya
sonsu; wadanda su ke wuce gona-da-iri cikin addu'a sune: masu yi munanar addu'a
ga muminai; Allah ka tozarta su, su ce: Allah ka la'ance su. Don haka wannan
nau'in ma ya shiga cikin wuce iyaka da aka hana a babin addu'a. Sai mu kula!
8-
Yana daga cikin wuce-gona-da-iri a cikin addu'a: Bawa ya yawaita maganan da ba a bukatar ta a lokacin
addu'arsa, kamar yace ya Allah in ka shigar dani aljanna ka bani: farin-gida
(white house), ta hanun damanta, Shi yasa wani daga cikin salaf da yaji 'dansa
yana addu'a
yana fadan irin haka sai ya kwabe shi, sannan ya gaya masa cewa Manzo (s a w)
yace: Za a samu wassu da zasu rika wuce gona-da-iri a cikin addu'a da tsarki, A
hir dinka ka kasance daga cikinsu! Kamar yadda Abu dawud [lamab: 96] ya rawaito
shi, kuma hadisin ingantacce ne, Ga lafazinsa:
عَنْ أَبِي نَعَامَةَ أَنَّ عَبْدَ اللَّهِ بْنَ مُغَفَّلٍ
سَمِعَ ابْنَهُ يَقُولُ: "اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْقَصْرَ
الْأَبْيَضَ عَنْ يَمِينِ الْجَنَّةِ إِذَا دَخَلْتُهَا، فَقَالَ: أَيْ بُنَيَّ!
سَلْ اللَّهَ الْجَنَّةَ، وَعُذْ بِهِ مِنْ النَّارِ؛ فَإِنِّي سَمِعْتُ رَسُولَ
اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: "سَيَكُونُ قَوْمٌ
يَعْتَدُونَ فِي الدُّعَاءِ".
Don haka; abinda ake bukata ka nemi shiga
aljanna, da kuma tsari daga fadawa wuta.
9- Yana daga cikin wuce-gona-da-iri a
cikin addu'a: Bawa ya rika daga sauti a cikin
addu'arsa, shi yasa yazo a cikin ayar cewa: Ku roki Allah a boye; lallai Allah
baya son masu wuce iyaka, Abdulmalik bn Abdul'aziz bn Juraij yace: "Lallai
a cikin addu'a akwai wuce iyaka: An ki daga sauti, ihu da hauragiya a cikin
addu'a, ana kuma umurni da Kankan-da-kai, da kuma nitsuwa, Ga lafazin nasa a
larabce:
(إنّ من الدعاء
اعتداء: يكره رفع الصوت والنداءُ والصياحُ بالدعاء، ويؤمر بالتضرع والاستكانة).
Daga
karshe: Wannan wassu ne daga cikin nau'ukan wuce gona-da-iri, da ketare iyakar
shari'a a babin addu'a, akwai kuma wassu nau'ukan da ban Ambato su ba; saboda
duk wani saba wa turbar manzon Allah (s a w) cikin addu'oi, da kuma nisantar
shiriyarsa yana fadawa
cikin: I'ITIDA' A ADDU'A. Don haka wajibi ne mu san yaya Manzon Allah (s a w)
yake addu'arsa don mu kubuta daga fadawa cikin ketare haddin musulunci.
Kuma –in
sha Allah- makala ta gaba in da rai da lafiya za ta kasance ne da taken: WASSU
DAGA CIKIN SHIRIYAR MANZON ALLAH (S A W) A BABIN ZIKIRI DA ADDU'OI.
Rubutawar
Abubakar Hamza
03/02/2012m
No comments:
Post a Comment