2015/01/04

صفة وضوء النبي صلى الله عليه وسلم

SIFFAR ALWALA (IRIN TA MANZON ALLAH SAW)([1])
            Samar da alwala sharaxi ne na ingancin sallah; wanda babu makawa sai an yi ta, Allah mabuwayi da xaukaka yana cewa:
(يا أيها الذين ءامنوا إذا قمتم إلى الصلاة فاغسلوا وجوهكم وأيديكم إلى المرافق وامسحوا برؤوسكم وأرجلكم إلى الكعبين) المائدة: ٦
Ma'ana: "Ya ku waxanda su ka yi imani idan za ku tashi zuwa ga sallah sai ku wanke fiskokinku da hannayenku zuwa guiwowi, kuma ku shafi kayukanku, kana ku wanke kafofinku izuwa ga idon sawu",             [Ma'idah: 6]. Haka Allah ta'alah ya umurci muminai a cikin wannan ayar. Kuma manzon Allah (saw) ya ce:
«لَا تُقْبَلُ صَلَاة بِغَيْرِ طُهُور».
Ma'ana: "Ba a karvar sallar da aka yi ba tare da tsarki ba"([2]). Har ila yau manzon Allah (saw) ya sake cewa:
«لَا يَقْبَلُ اللَّهُ صَلَاةَ أَحَدِكُمْ إِذَا أَحْدَثَ حَتَّى يَتَوَضَّأَ».
Ma'ana: "Allah baya karbar sallar xayanku; idan ya yi hadasi har sai ya yi alwala"([3]).
            Don haka, babu makawa sai an yi alwala.
            Shi kuma alwala, a farko akan gabatar da aiwatar da yin tsarki gabaninsa; matuqar dai mutum ya riga ya yi kashi ko fitsari gabanin haka; Sai ya yi tsarkin ruwa (istinja'i) saboda fitan kashi ko fitsari, ko kuma ya yi (istijmari) da bulo ko da duwatsu ko kuma da magogin dauxa (mindil) mai kurzunu-kurzuni, kuma masu tsarki, don ya tafiyar da abin da ya fita daga gare shi, zai aikata hakan har sau uku, don ya samu ya tsaftace wannan mafitan daga guntu ko alamun fitsari da wannan kashin. Kuma yin tsarki da ruwa (istinja'i) shi ne yafi falala (akan istijmari). Idan kuma da zai haxa tsakaninsu; ta fiskar ya fara da na dutse sa'annan ya yi na ruwa to hakan yafi kamala ya kuma fi burgewa.
            Sa'annan sai ya yi alwalarsa ta shari'a, yana mai fara alwalar da:
  Yin bismillah; ya ce: Bismillahi, a lokacin fara alwalar tasa.
Wannan shi ne abun da aka shar'anta. Wassu maluman kuma sun ce faxin bismillar wajibi ne, a farkon fara alwalarsa.
Sa'annan sai ya wanke hannayensa sau uku, yin haka kuma shi ne abun da yafi falala.
Sa'annan sai ya kurkuri bakinsa, ya kuma shaqa ruwa a hanci, sau uku, da kamfata guda uku.
Sa'annan sai ya wanke fiskarsa sau uku; wato daga matsirar gashi ta sama, zuwa havarsa ta qasa, faxinsa kuma zuwa kunnuwa guda biyu. Wannan shi ne wanke fiska.
Sa'annan sai ya wanke hannayensa guda biyu, daga kan 'yan yatsunsa har zuwa guiwowin hannu, shi kuma guiwar hannu na farawa daga kan gavar zira'i, kasa da damtse, kuma suma guiwowin hannayen guda biyu za a wanke su, Zai fara wanke hannun dama, sa'annan sai hannun hagu. Namiji ne ko mace.
Sa'annan bayan haka, sai mai yin alwala ya shafi kansa da kunnuwansa guda biyu; Namiji ne ko mace.
Sa'annan bayan haka, sai ya wanke qafarsa ta dama sau uku, tare da idanun qafarsa guda biyu. Sa'annan sai ya wanke ta hagu, sau uku, tare da idanun sawu. Zai fara haka har sai ya shiga wa qwabrinsa. Kuma suma idanun sawun guda biyu suna cikin wuraren da ake wankewa.
Sunna ita ce yi sau uku-uku wajen kurkuran baki, da shaqa ruwa a hanci, da fiska, da hannaye guda biyu, da qafofi guda biyu. Amma dangane da "kai" to shi kam shafa xaya ne, tare da kunnuwansa guda biyu. Wannan shi ne sunnah.
Idan da mai alwala zai wanke fiskarsa sau xaya; yana mai game shi da ruwa, tare da game hannayensa guda biyu da ruwa, sau xaxxaya, haka qafofinsa guda biyu; ya zamto ya game su da ruwa, sau xaxxaya, ko sau bibbiyu, hakan ya isar masa. Sai dai kuma mafificin lamari shi ne yin hakan sau uku-uku. Kuma lallai ya tabbata cewa annabi (saw) ya yi alwala sau xaxxaya, ya kuma yi sau bibbiyu, ya yi kuma sau uku-uku. Kuma ya tabbata cewa a wassu lokutan ya wanke wassu gavvan sau uku, wassu kuma sau biyu. Don haka; lamarin yana da sauqi, walhamdu lillah. Kuma wajibin shi ne a wanke kowace gava sau xaya; yana mai game shi da ruwa; ya game fiskarsa da ruwa tare da kurkuran baki da shaqa ruwa a hanci, ya kuma game hannunsa na dama da ruwa, har ya wanke guiwar hannu, haka hannun hagu shima zai game shi da ruwa, haka kuma zai shafi kansa da kunnuwansa guda biyu; yana mai game kansa da shafa, Sa'annan sai kafofi guda biyu; wanda zai wanke ta damarsa sau xaya, yana mai game ta da ruwa, itama kaqar hagu hakanan zai game ta da ruwa, tare da idanun qafa guda biyu. Yin wannan shi ne wajibi, idan da mai yin alwala zai maimaita alwalar sau biyu to yin hakan yafi falala, in kuma ya qara har ya zama sau uku, to hakan shine yafi falala. Kuma da haka alwala ta ke karewa.
      Sa'annan sai ya ce:
أَشْهَدُ أَنْ لا إِلَهَ إِلا اللَّهُ وَحْدَهُ لا شَرِيكَ لَهُ، وَأَشْهَدُ أَنْ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُه، اللَّهُمَّ اجْعَلْنِي مِنَ التَّوَّابِينَ، وَاجْعَلْـــنِي
مِنَ الْمُتَطَهِّرِين.
ASH'HADU AN LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, WA ASH'HADU ANNA MUHAMMADAN ABDUHU WA RASULUHU, ALLAHUMMA IJ'ALNIY MINAT TAWWABINA, WAJ'ALNIY MINAL MUTAXAHHIRA.
Haka nan annabi (saw) ya ilmantar da sahabbansa (ra). Kuma lallai ya inganta daga gare shi; cewa:
"مَا مِنْكُمْ مِنْ أَحَدٍ يَتَوَضَّأُ فَيُسْبِغُ الْوَضُوءَ ثُمَّ يَقُولُ: أَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُ اللهِ وَرَسُولُهُ إِلَّا فُتِحَتْ لَهُ أَبْوَابُ الْجَنَّةِ الثَّمَانِيَةُ يَدْخُلُ مِنْ أَيِّهَا شَاءَ".
Ma'ana: "Babu wani daga cikinku da zai yi alwala sa'annan sai ya qyautata alwalar, sannan ya ce: Ash'hadu an la ilaha illal lahu, wa anna Muhammadan abduhu wa rasuluhu, face an bude masa qofofin aljannah guda takwas; don ya shiga ta wanda ya ga dama daga cikinsu"([4]). Muslim ne ya rawaito shi a cikin littafinsa (sahihi), Imam At-tirmiziy ya zo da wannan qarin a cikin hadisin bayan abin da ya gabata da isnadi mai kyau (hasan):
اللَّهُمَّ اجْعَلْنِي مِنَ التَّوَّابِينَ، وَاجْعَلْنِي مِنَ الْمُتَطَهِّرِين.
Ma'ana: "Ya Allah ka sanya ni daga cikin masu yawan tuba, ka sanya ni daga cikin masu neman tsarkaka"([5]).
Wannan zikirin ana faxansa ne bayan kammala alwala; namiji zai faxe shi, mace itama za ta faxe shi, a wajen banxaki (ba a ciki ba).
           Da haka aka san alwala ta shari'a. Kuma ita alwala ita ce mabuxin sallah; saboda faxin annabi (saw):
«مِفْتَاحُ الصَّلَاةِ الْوُضُوءُ، وَتَحْرِيمُهَا التَّكْبِيرُ، وَتَحْلِيلُهَا التَّسْلِيمُ».
Ma'ana: "Mabuxin sallah shi ne alwala, shiga cikinta kuma ya kan kasance da yin kabbara, ficewa daga gare ta kuma da yin sallama"([6]).
$/&/$



([1]) MAJMU'U FATAWA IBN BAAZ, (11/ 21-24).
([2]) Muslim ya rawaito shi, (lamba: 224).
([3]) Bukhariy ne ya rawaito shi, (lamba: 135), da Muslim (lamba: 225) daga hadisin Abu-hurairah (ra).
([4]) Muslim ya rawaito shi, (lamba: 234) daga hadisin Uqbah xan Amir daga Umar bn Al-khaxxab.
([5]) Tirmiziy ya rawaito shi, (lamba: 55) daga hadisin Umar (ra).
([6]) Tirmiziy ya rawaito shi, (lamba: 3) daga hadisin Aliyu (ra).

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...