SHIN DUKIYAR
MAGADANKA TAFI SOYUWA A GARE KA, KO TAKA?!
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, salati da sallama su kara
tabbata ga ma'aikin Allah annabi Muhammad (SAW) da iyalansa da sahabbansa gabadaya,
Bayan haka:
أورد
الإمام البخاري في صحيحه في (بَاب مَا قَدَّمَ مِنْ مَالِهِ فَهُوَ لَهُ) بسنده
إلى عَبْد اللَّهِ بن مسعود رضي الله عنه قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صلى الله عليه
وسلم: «أَيُّكُمْ مَالُ وَارِثِهِ أَحَبُّ إِلَيْهِ مِنْ مَالِهِ؟» قَالُوا: يَا
رَسُولَ اللَّهِ، مَا مِنَّا أَحَدٌ إِلا مَالُهُ أَحَبُّ إِلَيْهِ! قَالَ:
«فَإِنَّ مَالَهُ مَا قَدَّمَ، وَمَالُ وَارِثِهِ مَا أَخَّر».
Waccar tambayar ta zo cikin hadisin da Imamul Bukhariy ya
ruwaito shi [6442] a (babin da ke magana kan abin da mutum ya bayar daga
dukiyarsa to shi ne fa nasa) da "Isnadinsa" … zuwa ga Abdullahi bn
Mas'uud (RA) ya ce: Annabi (SAW) ya ce:
"Wanene daga cikinku dukiyar magadansa tafi soyuwa a
wajensa fiye da dukiyarsa?", Sai su ka ce: Ya ma'aikin Allah! Babu wani
mutum daga cikinmu face dukiyarsa ce ta fi soyuwa a wajensa! Sai ya ce:
"To lallai dukiyar mutum ita ce wacce ya gabatar, dukiyar magajinsa kuma
ita ce: wacce ya jinkirtar!".
Shi kuma wannan hadisin ta wata fiskar zamu ga cewa ya yi kama
da sashin maganar da maluma ke fada; cewa: Abincinka shi ne wanda ka bayar, shi
kuma wanda ka riga ka cinye to ya zama kashi!
MUHIMMIN DARASI DA HADISIN KE KOYARWA: Lallai
wannan hadisin na daga hadisan da su ke kwadaitar da mutane kan yin aiyukan
alkhairi da ciyarwa, ko tufatarwa, ko bada agajin gina masallatai, ko aji
(dakin karatu), ko wakafin gidan zama ga talakawa ko ga dalibai, ko rijiyoyi,
da sauransu, da dukiya; domin mutum ya amfana da shi a gidan lahira!
JAN HANKALI GA MAWADATA: Allah ta'alah ya kan
jarrabi bayinsa da talauci, wassu kuma da dukiya ko wadata, ya kuma shar'anta
mana cewa in za a nemi dukiya to a neme ta (dukiyar) ta hanya guda daya tak;
hanyar "halal", kamar yadda ya sanya tambayoyin da za a yi ma bayi a
kiyamah dangane da abin da ya azurta su da shi na dukiya suka zamto "guda
biyu", su ne: Ta yaya ka same ta?
sa'annan
ta yaya ka kashe ta?
Hakan
kuma ya zo cikin hadisi ingantacce da ke magana kan abubuwa guda biyar da ba
zai taba yiwuwa dugadugan bawa su gota daga gaban ubangiji Allah ba har sai
bawan ya amsa su, hadisin yana cewa:
عَنْ
أَبِي بَرْزَةَ الأَسْلَمِيِّ رضي الله عنه، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لاَ تَزُولُ قَدَمَا عَبْدٍ يَوْمَ القِيَامَةِ حَتَّى
يُسْأَلَ عَنْ: عُمُرِهِ فِيمَا أَفْنَاهُ، وَعَنْ عِلْمِهِ فِيمَ فَعَلَ، وَعَنْ
مَالِهِ مِنْ أَيْنَ اكْتَسَبَهُ وَفِيمَ أَنْفَقَهُ، وَعَنْ جِسْمِهِ فِيمَ
أَبْلاَهُ»
Ma'ana:
((Ya zo daga Abu-barzatal aslamiy –RA- ya ce: Manzon Allah –SAW- ya ce:
Dugadugai guda biyu na bawa ba za su gushe ba a ranar kiyamah har sai an
tambaye shi kan: Rayuwarsa ta yaya ya karar da ita, iliminsa kuma mai ya aikata
da shi, ita kuma dukiyarsa; ta ina ya same ta, ta yaya kuma ya ciyar da ita,
kana kuma sai jikinsa da kuruciyarsa ta yaya ya tafiyar da ita?!)). [Tirmiziy
ya ruwaito shi, ya kuma ce: hadisi ne mai kyau, ingantacce, lamba: 2417, ya
kuma sake ruwaito shi ta hanyar Abdullahi bn Mas'uud –RA-, lamba: 2416, Albaniy
ya ce wannan hadisin ta wannan hanyar "hasan" ne, Duba: As-silsilatus
sahihah, lamba: 946].
Lallai wannan hadisin na nuna cewa ita dukiya akan mata
tambayoyi har kashi biyu, tambayar farko: ta yaya aka same ta; shin ta hanyar
"halal" ne, ko kuma?
Tambaya
ta biyu: game da yadda aka ciyar da ita; "ga alkhairi ne ko ga
sharri"?
La'ilaha
illal lah!!! Kowanne bawa sai ya amsa wadannan tambayoyin dangane da dukiyarsa;
sawa'un dukiyar kadan ce ko mai yawa!! Allah ka tseratar da mu!!!
Wannan kalu-balen da ke jiran kowa; ya ke jirana, ya ke jiranka:
a filin kiyamah, a kuma gaban ubangiji mai girma, shi ne yasa na dauki alkalami
don na fadakar da 'yan'uwana musulmai, musamman wadanda talakawa ke ganin cewa
Allah ya tarfa ma garinsu nono; wato masu kudi; don mu gudu tare mu tsira tare!
Masu kudi da dukiya! Ga nasihata a gare ku:
NA FARKO: Lallai dukiyar da Allah ya baka taka
ce, matukar kana nan duniya; baka riga ka mutu ba, haka kuma taka ce a gidan
lahira idan ka yi aikin alkhairi da ita; saboda zaka je ka samu sakamakonka
cikakke a wajen Allah ta'alah! Wannan kuma saboda hadisin farko da na ambato,
mai nuna cewa, dukiyarka ta hakika bayan ka riga ka mutu ita ce: wacce ka riga
ka ciyar da ita gabanin rasuwarka. yayin da ita kuma wacce ka bari ga zuri'arka
da sauran magada to ta magadan ne, Kai ba za ta maka amfanin komai ba a
kiyamah; tare da cewa kai ne, ka tattara ta. Kamar yadda kuma za ta iya kasance
maka "Azaba" matukar ta shigo ne ta hanyar "haram", kamar
yadda (wailul likulli humazatin lumazah…. -Har karshen "surar" ta ke
nunawa).
Su kuma magada za su ci wannan dukiyar a matsayin
"halal", haka kuma ba za su samu kalu-balen amsa tambayar: ta yaya ta
shigo muku ba? Saboda kasancewar ta shigo musu ne ta hanya yardajjiya; ma'ana:
gado, Abin da kawai zai rage musu shine su yi kokarin su ga sun kashe ta ta
hanya mai kyau, wacce Allah ya yarda da ita.
Haka kuma Dukiyar zata iya zama asara ga bangarori biyun; wadda
ya tattara ta daga farko, da wadda ya kashe ta (magada); idan shi mai dukiyar
na asali ya tara ta ne ta mummuniyar hanya, ya kuma fitar da ita ta mummuniyar
hanya, ko kuma ya gadar da ita ga shashatun magada da su ka yi ma-sha'ansu da
ita!
Saboda wannan ne da makamancinsa maluma su ke bayyana cewa ya
halatta "mai kudi" a halinsa na lafiya; ba lokacin jinyan ajali ba:
ya halatta a gare shi ya yi aikin alkhairi da daukacin dukiyarsa gabadayanta;
in yaga dama. Amma In kuma ciyon ajali ya zama ya kama shi to a nan ma ya
halatta a gare shi ya yi wasici da daya bisa ukun daukiyar tasa daya bias uku (1/3)
ga wani aikin alkhairi, ko ga wani mutum, ko kuma ya kashe ta ga gina wani
alkhairin gabanin fitar ransa. Dalili kuma akan wadannan mas'alolin shi ne
hadisin da ke tafe:
عَنْ
سَعْدِ بْنِ أَبِي وَقَّاصٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: كَانَ رَسُولُ اللَّهِ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَعُودُنِي عَامَ حَجَّةِ الوَدَاعِ مِنْ وَجَعٍ
اشْتَدَّ بِي، فَقُلْتُ: إِنِّي قَدْ بَلَغَ بِي مِنَ الوَجَعِ وَأَنَا ذُو مَالٍ،
وَلاَ يَرِثُنِي إِلا ابْنَةٌ، أَفَأَتَصَدَّقُ بِثُلُثَيْ مَالِي؟ قَالَ: «لاَ»
فَقُلْتُ: بِالشَّطْرِ؟ فَقَالَ: «لاَ» ثُمَّ قَالَ: «الثُّلُثُ؛ وَالثُّلُثُ
كَبِيرٌ -أَوْ كَثِيرٌ- إِنَّكَ أَنْ تَذَرَ وَرَثَتَكَ [وفي لفظ: ذُرِّيَّتَكَ]
أَغْنِيَاءَ خَيْرٌ مِنْ أَنْ تَذَرَهُمْ عَالَةً يَتَكَفَّفُونَ النَّاسَ،
وَإِنَّكَ لَنْ تُنْفِقَ نَفَقَةً تَبْتَغِي بِهَا وَجْهَ اللَّهِ إِلا أُجِرْتَ
بِهَا، حَتَّى مَا تَجْعَلُ فِي فِي امْرَأَتِكَ [وفي لفظ: حَتَّى اللُّقْمَةَ
تَجْعَلُهَا...] ».
Ma'ana:
((Hadisi ya zo daga Sa'ad bn Abiy-wakkas –RA- yana cewa: Manzon Allah –SAW-
da-kansa ya kasance yana ziyartata a shekarar hajjinsa na bankwana; saboda
matsanancin ciyo dake tare da ni, Sai na ce: Zafi da radadin wannan ciyon ya
kai yadda ya kai, gashi ni mutum ne ma'abocin dukiya, bani kuma da wanda zai
gaje ni in na mutu sai 'yata mace guda 'daya; Shin na yi sadaka ne da
biyu-bisa-ukun dukiyata -2/3-? Sai annabi –SAW- ya ce:
A'a! Sai na ce: To na sadakar da rabinta -1/2-? Sai ya
ce: A'a! Sa'annan sai ya ce: Sai dai daya-bisa-uku 1/3?
Shima 1/3 yana da girma, ko yana da yawa; Lallai ka bar
magadanka [a wani lafazin: zurri'arka] mawadata shi ne ya fi alkhairi fiye da
ka tafi ka barsu talakawa masu rokon mutane! Kuma lallai ba zaka yi wata
ciyarwa da ka ke neman ganin fiskar Allah da ita ba face an baka lada akanta,
koda kuwa abin da za ka sanya shi a cikin bakin matarka ne [a wani lafazin: koda
kuwa loma ne da zaka sanya ta a cikin bakinta])).
[Bukhariy ne ya ruwaito shi, lamba: 1295, da 3936, da 4409, da
6373, da Muslim, lamba: 1628].
Da kuma saboda fadinsa (SAW):
"إِنَّ اللَّهَ تَصَدَّقَ
عَلَيْكُمْ عِنْدَ وَفَاتِكُمْ بِثُلُثِ أَمْوَالِكُمْ، زِيَادَةً فِي
حَسَنَاتِكُمْ لِيَجْعَلَهَا لَكُمْ زَكَاةً فِي أَعْمَالِكُم".
Ma'ana:
(Lallai Allah ta'alah ya ba ku damar ku yi sadaka -a wajen rasuwarku- da
"daya-bisa-ukun 1/3 dukiyoyinku; domin karuwar
kyawawan aiyukanku; wadda Allah zai sanya shi ya zama tsarki cikin aiyukanku).
[Ibnu-majah ya ruwaito shi (2709), da Ahmad a cikin
"musnad" (lamba: 27482), da Ad-daraqudniy (5/263), da Al-baihaqiy
(6/264), hadisi ne hasan (duba: Irwa'ul galil, 6/77].
NA BIYU: Wata shawarar kuma a nan ita ce:
"Mai kudi da dukiya" ana son ya fifita ciyar da dukiyarsa ga abin da
zai dau lokaci talakawa ko daukacin jama'a suna amfana da shi, fiye da basu
abincin da za su cinye a lokaci guda, ko tufatar da su, ko kaisu umrah ko
hajji, tare da cewa wadannan suma alkhairori ne masu girma, sai dai kuma abin
da ya fi bayar da lada da yawa na tsawon lokaci ga wanda ya aikata shi shine
duk abin da zai dau shekara da shekaru ana amfana da shi; wannan kuma saboda
hakan ya zame masa "sadaka mai gudana" har bayan rasuwarsa, wato
kamar samar da gidaje na wakafai ma talakawa ko daliban ilimi, gina makarantu,
masallatai, tonon rijiyoyi, samar wa mutane hanyoyi a cikin garurrukansu, ko
izuwa ga kauyukansu, dasa bishiyoyi, da sauransu, saboda hadisin Abu-hurairah
(RA):
عَنْ
أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ قَالَ: "إِذَا مَاتَ الإِنْسَانُ انْقَطَعَ عَمَلُهُ إِلا مِنْ
ثَلاثٍ: صَدَقَةٍ جَارِيَةٍ، أَوْ عِلْمٍ يُنْتَفَعُ بِهِ، أَوْ وَلَدٍ صَالِحٍ
يَدْعُو لَه".
Ma'ana:
((Idan 'dan-adam ya mutu aikinsa ya yanke sai dai nau'I guda uku: sadaka mai
gudana, ko ilimi da ake amfana shi, ko kuma 'da salihi da ya ke yi masa
addu'a)). [Muslim ya ruwaito shi, lamba: 1631].
NA UKU: Gabanin na rufe maganata kan fadakar
da mawadata bisa aikata aiyukan alkhairi da dukiyar da Allah ta'alah ya basu
kula da ita na 'dan wani lokaci, zai yi kyau na Ambato koda wassu daga cikin
ayoyin alqur'ani mai girma da suke kwadaitarwa kan wannan lamarin, Allah yana
cewa:
(وَأَنْفِقُوا مِنْ مَا
رَزَقْنَاكُمْ مِنْ قَبْلِ أَنْ يَأْتِيَ أَحَدَكُمُ الْمَوْتُ فَيَقُولَ رَبِّ
لَوْلا أَخَّرْتَنِي إِلَى أَجَلٍ قَرِيبٍ فَأَصَّدَّقَ وَأَكُنْ مِنَ
الصَّالِحِينَ * وَلَنْ يُؤَخِّرَ اللَّهُ نَفْسًا إِذَا جَاءَ أَجَلُهَا
وَاللَّهُ خَبِيرٌ بِمَا تَعْمَلُونَ}. [المنافقون: 10-11].
Ma'ana:
((Kuma ku ciyar daga abin da muka azurta ku, gabanin mutuwa ta zo ma daya daga
cikinku, sai ya ce: Ya ubangijina! Da dai ka jinkirta min zuwa wani dan lokaci
na kusa; don na samu na yi sadaka, na zama daga cikin mutane salihai ** Kuma
Allah baya jinkirta ma rai idan ajalinta ya zo, kuma Allah shi ne mai bada
labari kan abin da kuke aikatawa)). [Munafiquna: 10-11].
NA HUDU: Amma dangane da tsarkin dukiya da
kasancewarta ta halal gabanin sadaka da ita, to wannan ma abun lura ne; matukar
ana son a more ta a kiyamah; saboda hadisi yana nuna cewa: "Lallai Allah
mai tsarki ne, baya kuma karba sai mai tsarki", a wani hadisin kuma:
عَنْ
أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ تَصَدَّقَ بِعَدْلِ تَمْرَةٍ مِنْ كَسْبٍ
طَيِّبٍ، وَلاَ يَقْبَلُ اللَّهُ إِلا الطَّيِّبَ، وَإِنَّ اللَّهَ يَتَقَبَّلُهَا
بِيَمِينِهِ، ثُمَّ يُرَبِّيهَا لِصَاحِبِهِ، كَمَا يُرَبِّي أَحَدُكُمْ
فَلُوَّهُ، حَتَّى تَكُونَ مِثْلَ الجَبَلِ».
Ma'ana:
((Daga Abu-hurairah –RA- ya ce: manzon Allah –SAW- ya ce: Duk mutumin da ya yi
sadaka, da gwargwadon girman dabino guda daya, daga dukiyarsa tsarkakakkiya ta
halal, -Allah kuma baya karba sai tsarkakakke- to lallai Allah zai karba masa
da hannun damansa, sa'annan sai ya yi ta bunkasa masa shi har sai ya zama kamar
dutse mai girma, kamar yadda 'dayanku yake girmar da 'yar rakumarsa ta-mace
karama)).
[Bukhariy
ne ya ruwaito shi, lamba: 1410, da 7430, da Muslim, lamba: 1014].
NA BIYARr: Rufewa da addu'a ga duk mawadacin
da ya ke ciyar da dukiyarsa don daukakar addinin Allah, ko taimakon mutane,
tare da fatan Allah ya sanya shi cikin mafifitan mutane, ya kuma bashi ninkin-baninkiya
tare da bashi mayewar abin da ya fitar don ciyarwa. Shi kuma mutumin da ya yi
mammako, ya hana hakkokin da suke kansa, Allah ya kawo masa asara. Amin!!
Wannan "makalar" fadakarwa ce ga masu dukiya; saboda
me Allan yawan mutanen da Allah ta'alah ya basu tarin dukiya, musamman a wannan
zamanin sai dai kuma kash, basu gabatar da komai wa kansu, da za su je su same
shi a lahirarsua, da dama kuma daga cikinsu sukan gadar da ita ga zuri'arsu
'yan sharholiya da lalaci da aikin kawai; sai dukiyar daga karshe ta zama asara
ga bangaren wanda ya wahala wajen tara ta, da su wadanda su ka gaje ta ta
hanyar lalatar da ita ta fiskar aikin tsiya, da su ka ga-dama. Allah ka shiryad
da mu hanya madaidaiciya.
Ya Allah ka yi dadin salati da sallama ga manzonmu annabi
Muhammad da iayalansa da sahabbansa, amin.
Abubakar Hamza Zakariyya
09/05/1435h, daidai da 10/03/2013
No comments:
Post a Comment