2015/01/18

LADDUBAN HALARTAR MACE MASALLACI (آداب حضور المسلمة إلى المسجد)



LADDUBAN HALARTAR MACE MASALLACI



BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah ubangijin halittu. Tsira da aminci su qara tabbata ga shugaban manzanni, da kuma iyalansa da sahabbansa gabaxaya.
Yar'uwata musulma: Muna yi miki qyautar wannan 'yar takarda wacce a cikinta ta qunshi sashin ladduban da su ka qyautu ga 'ya mace musulma ta ladabta da su in za ta zo masallacin annabi (SAW), ko kuma za ta shiga RAUDHA.

NA FARKO: A lokacin shiga masallaci:
An so musulma ta fara gabatar da qafarta ta dama, sai kuma ta faxi addu'ar da aka rawaito daga manzon Allah (SAW); Ma'ana sai ta ce:
«أَعُوذُ بِاللَّهِ الْعَظِيمِ، وَبِوَجْهِهِ الْكَرِيمِ، وَسُلْطَانِهِ الْقَدِيمِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ»([1]). «بِسْمِ اللَّهِ وَالصَّلَاةُ والسَّلامُ عَلَى رَسُولِ اللَّهِ، اللَّهُمَّ افْتَحْ لَنَا أَبْوَابَ رَحْمَتِكَ»([2]).
A'UZU BILLAHIL AZIM, WA BI WAJHIHIL KARIM, WA SULDANIHIL QADIIM, MINASH SHAIDANIR RAJIIM. BISMILLAH, WAS SALATU WAS SALAMU ALA RASULIL LAH, ALLAHUMMA IFTAH LIY ABWABA RAHMATIK.
Ma'ana: Ina neman tsari daga Allah mai girma, da kuma fiskarsa mai karamci, da qarfin mulkinsa daxaxxe daga shexan tsinanne abun jefewa. (Ina shiga masallaci) da sunan Allah, tsira da aminci kuma su qara tabbata ga manzon Allah,Ya Allah! Ka bubbuxe min qofofin rahamarka!

NA BIYU: Idan ki ka isa zuwa wurin da za ki zauna:
To, sai ki yi sallama, kina mai cewa: ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATUL LAHI WA BARAKATUHU, da sautin da mutumin da ke kusa da ke zai iya jinsa, Sannan kada ki yadda ki zauna face kin sallaci raka'oi guda biyu, wannan kuma saboda faxin annabi (SAW):
«إِذَا دَخَلَ أَحَدُكُمُ الْمَسْجِدَ فَلْيَرْكَعْ رَكْعَتَيْنِ، قَبْلَ أَنْ يَجْلِسَ»([3]).
Ma'ana:"Idan xayanku ya shiga masallaci to sai ya sallaci raka'oi guda biyu, gabanin ya zauna".

NA UKU: Girmama masallaci da nisantar yin wasa da abubuwan da su ke cikinsa, ko kuma jejjefa dauxa da datti:
Saboda abu na wajibi shi ne kula da masallaci, tare da tsaftace shi fiye da yadda muke tsaftace gidaddajinmu; Ya zo daga A'ishah (RA) tace:
«أَنَّ النبي r أَمَرَ بِبِنَاءِ الْمَسَاجِدِ فِي الدُّورِ وَأَنْ تُنَظَّفَ وَتُطَيَّبَ»([4]).
"Lallai annabi (SAW) ya yi umurnin a gina masallatai a cikin unguwanni, ya yi kuma umurnin a riqa tsaftace su ana kunna musu ko fesa tirare".
Abun da ake nufi da "tsakanin gidaddaji" a cikin hadisin shi ne, abin da a yau ake kiransa: unguwanni.

NA HUXU: Daidaita sahu, tare da cike kowacce kafa:
Wannan kuma saboda akwai wassu daga cikin mata waxanda basa bawa wannan lamari muhimmanci, shi yasa kike ganin sahun mata a karkace, a gurgunce, a kuma rarrabe, kai ka ce umurnin da aka yi kan kula da sahu ya taqaita ne ga maza banda 'yan-uwa mata, alhalin kuma annabi (SAW) yana cewa:
«أَلَا تَصُفُّونَ كَمَا تَصُفُّ الْمَلَائِكَةُ عِنْدَ رَبِّهَا؟» فَقال بعض الصحابة: يَا رَسُولَ اللهِ! وَكَيْفَ تَصُفُّ الْمَلَائِكَةُ عِنْدَ رَبِّهم؟ قَالَ: «يُتِمُّونَ الصّفَّ الْأولَ فالأول، وَيَتَرَاصُّونَ فِي الصَّفِّ»([5]).
Ma'ana: "Shin ba za kuna yin sahu kamar yadda mala'iku ke yin sahu a wajen ubangijinsu ba? Sai Wassu daga cikin sahabbai su ka ce: Ya ma'aikin Allah! Ta yaya mala'iku ke yin sahu a wajen ubangijinsu? Sai ya ce: suna ciccika sahun farko sai wanda ke biye da shi, kamar yadda kuma su ke hadewa; sashinsu zuwa sashi a cikin sahu".
Haka kuma wassu matan –Allah ya shirye su- su kan yi sallarsu a bayan sahu su kaxai, bayan kuma annabi (SAW) ya riga ya hana aikata hakan.

NA BIYAR: Barin yin surutu, da xaga sauti:
Wassu matan su kan yi ta surutu da kuma yin maganganun da basu dace ba; na lamurran duniya, a masallacin annabi (SAW), Ta yiwu kuma; cikin maganganun nasu akwai cin nama (giba) ko haxa faxa; (annamimanci), alhalin kuma wajibi ne a nisanci aikata haka; saboda annabi (SAW) yayi hani a kansa a cikin shari'a.
Kamar yadda wassu matan su kan haifar da surutai, ta hanyar zuwa da 'yan yaran da ake shayar dasu, ko kuma su zo da yara masu qananan shekaru; waxanda basu san ladduban masallatai ba balle su yi aiki da su, don haka; sai su yi ta takura ma 'yan'uwansu masu sallah. Kai! wassu matan su da kansu ne su ke surutai marasa kan gado, ko su yi ta guxa, ko ihu, sai su yi ta takura ma 'yan'uwansu mata, Wannan kuma dukkansa baya halatta; saboda yana daga cikin abubuwan da aka yi hani akansu.
An tambayi shehin malami mai suna Salihu Alfauzan –Allah ya bashi lafiya- kan hukuncin yin guxa, (wanda kuma sauti ne da mace ke fitarwa a yayin bayyanar da farin ciki)?
Sai ya amsa da cewa: Baya halatta mace ta riqa xaga sautinta a wurin maza; saboda sautinta ya kan zama fitina, guxa ne ko waninsa. Sannan shi guxa ba abu ne sananne ba a wajen yawa-yawan musulmai, a zamanin da ko a na yanzu, don haka; yin guxa mummunan al'ada ce da ya dace a nisance ta.
Lallai kuma ba shakka, xaga sauti ko yin guxa da mata ke yi na daga cikin abubuwan qyama, sawa'un mace ta aikata hakan a cikin kasuwa ne ko akan hanya, kai koda a cikin gidanta ne matukar dai mazaje ajnabiyyanta za su ji sautinta, yaya kuma munin lamarin zai kasance idan ta aikata shi a masallacin manzon Allah (SAW)?!
Don haka –ya ke 'yar uwata musulma- ki kiyaye kanki daga aukawa cikin haka, ki kuma hana duk matar da take aikata shi daga cikin waxanda ba su san hukuncin aikata shin ba!
          Kuma yana daga cikin abubuwan da suka wajaba a aikata su: Fiskantar Allah mabuwayi da xaukaka da nufansa shi kaxai lokacin yin addu'oi, da kuma kauce ma rokon annabi (SAW) dangane da biyan bukatun bayi, wannan kuma saboda aikata hakan bai halatta ba, Allah ta'alah yana cewa:
(وَأَنَّ الْمَساجِدَ لِلَّهِ فَلا تَدْعُوا مَعَ اللَّهِ أَحَدًا ((18)).
Ma'ana: "Kuma lallai masallatai na Allah ne; kada ku roqi wani tare da Allah".
An tambayi shehin malami mai suna Abdul'aziz Ibnu-baaz –Allah ya yi masa rahama- kan hukuncin yin tawassali da "annabi (SAW)" kuma shin akwai dalilai ne kan haramcin nasa?
Sai ya amsa da cewa: Yin tawassali da addu'ar annabi (SAW) bayan mutuwarsa, da neman agajinsa, ko neman ya bada nasara kan maqiya, ko warkar da majinyata, waxannan dukkansu shirka ne babba, kuma yana cikin aiyukan ma'abota bautar gumaka. Haka kuma aikata irin wannan a hakkin sauran annabawa, da waliyyai, da aljanu, ko mala'iku, ko bishiyoyi ko duwatsu ko gumaka.
Akwai kuma nau'i na biyu wanda shima baya halatta, misalin mutum ya ce: Ya Allah ina roqonka domin annabinka Muhammadu (SAW); don matsayinsa, ko haqqinsa, ko zatinsa, ko don matsayin annabawa, ko waliyyai, ko salihan bayi, da makamantan haka; Dukkan waxannan bidi'oi ne, kuma suna cikin hanyoyin da suke kai mutane zuwa ga shirka, kuma lallai baya halatta a aikata hakan dangane da annabi (SAW) ko waninsa; saboda Allah ta'alah bai shar'anta mana aikata hakan ba; kamar yadda su kuma ibadodi mutum baya yin gaba-gaxi ko gamon kansa; wannan kuma saboda baya halatta bawa ya aikata wata ibada sai wacce shari'ar Allah mai tsarki ta yi nuni.
Amma abinda makahon nan ya aikata na yin tawassali da annabi (SAW) a zamaninsa (lokacin yana raye), Wannan aikin nasa tawassali ne da annabi don ya roqa masa Allah, ya kuma nema masa cetonsa wajen dawowar ganinsa zuwa gare shi, ba wai tawassali ne da zatin annabi (SAW) ko matsayinsa ko kuma haqqin da yake da shi a wurin Allah ba! kamar yadda maluman sunnah suka bayyana hakan a sharhin hadisin da suka yi.
Shi kuma aikata wannan nau'in dangane da annabi a lokacin yana da rai halal ne, kamar yadda hakan ya halatta dangane da waninsa, kamar ka ce ma dan'uwanka ko babanka ko dai duk wanda kake yi masa zaton alheri; ka ce da shi: Ka roqa min Allah ya warkar da ni daga cutar da ta matsa mini, ko ya mayar maka da ganinka da ka rasa, ko ya azurta ka da zurriya ta gari, ko makamancin haka, Wannan kuma halal ne da ijma'in dukkanin maluma.
An tambayi shehin malami mai suna Salihu Alfauzan –Allah ya qara masa lafiya cewa-: Wassu mata in su ka halarci masallaci su kan zauna su yi ta yin taxi da junansu, kan lamurran da ba na ibada ba, A wassu lokutan kuma basa yanke wannan taxin har sai lokacin da limami ya duqa zai tafi ruku'i, menene hukuncin aikata haka?
Sai ya amsa da cewa: Duk wanda ya halarci masallaci daga cikin mazaje ko mata, to wajibi ne akansa ya kula da alfarmar masallaci, da kuma alfarmar bauta (ibadah); akan haka; baya halatta ga mutum yayi ta kukkutsawa cikin zantukan duniya; saboda aikata hakan munanawa ne ga shi masallacin kansa, kuma yana shagaltar da masu yin bauta kan sababin zuwansu, tare da tafiyar da damar da aka samu a wannan wuri mai tsarki ga abin da ba shine ba, Abin da kuma ya fi muni da haramci shine shagaltuwar mutum (namiji ne ko mace) da hira ko yin taxi, alhalin limam ya riga ya fara sallah; saboda hakan zai sanya bawa ya rasa falalar da ake samu na riskar kabbarar harama, kai harma ya iya sanya bawa ya rasa raka'ar farko, kamar yadda kuma hakan ya ke cike kunnuwan limami da mamunsa ya sanya su cikin ruxani. Kamar yadda aikata haka ya kan zama sababin yin gangancin barin tsayuwa gabanin ruku'i wanda kuma yin tsayuwan rukuni ne a cikin sallah; ta yadda ita sallah bata inganta in har ba a yi shi ba.
Salati da sallama su qara tabbata ga annabinmu Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa gabaxaya.
20/01/1436h
wanda ya yi daidai da
 13/11/2014
A Madinar manzon Allah (SAW)



([1]) Littafin Sahihul jami'i, (lambar hadisi: 4591).
([2]) Littafin Sahihu Muslim, (lambar hadisi: 494).
([3]) Littafin Sahihul Bukhariy, (lambar hadisi: 425).
([4]) Ahmad a cikin littafin Musnad ya rawaito shi, (16/263).
([5])  Littafin Sunan An-nasa'iy, (lambar hadisi: 807), Kuma Imam Muslim shima ya rawaito shi, (lamba: 430).

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...