FADAKARWA GA MAHAJJACI YAYIN ISOWARSA "MIKAATI"
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah ubangijin halittu.
Tsira da aminci su kara tabbata ga shugaban manzanni, annabinmu Muhammadu, da
iyalansa da sahabbansa gabadaya. Bayan haka;
Dan'uwana Mahajjaci!
Lallai muna taya ka murnar karramawar da Allah ya yi a gare ka, da saukake maka
isowa (kasar Saudia) don yin wannan da'a mai girma, da ibada mai matsayi;
hajjin dakin Allah mai alfarma, (Bawan Allah kuma Mahajjaci) Yau ga ka nan ka
riga ka iso wurin da ake kiransa "mikaati"; ma'ana: mafarin tafiya
zuwa ga wannan matafiya mai girma da karamci; wato zuwa ga dakin Allah
'yantacce. Muna rokon Allah ta'alah ya saukake maka tafiyarka, ya kuma karba
maka da'arka, sannan ya shiryar da kai hanya madaidaiciya.
Dan'uwana Mahajjaci!
A wannan dama ta kasancewarka a "mikati" mu ke tunatar da kai da
wassu fadakarwa masu muhimmanci; wadanda zai yi kyau ka rika tuna su a lokacin
da ka ke wannan wuri; MIKAATI:
1) Wajibi ne akanka –Dan'uwana mahajjaci- ka fara aikin hajjinka
da tuba zuwa ga Allah mabuwayi da daukaka, daga dukkan zunubai da kurakurai,
tuba ta gangariya.
2) Haka kuma wajibi ne a kanka ka nufi Allah da gidan lahira da
aikin hajjinka ko umrarka, kana mai kusantarsa (swt) da dukkan abubuwan da za
su yardar da shi na kyawawan zantuka da aiyuka.
3) Ya kai dan'uwana Mahajjaci (Dole ne) Ka koyi abubuwan da aka
shar'anta maka na aiyukan hajjinka da ibadar umrarka; domin aiyukanka
gabadayansu su kasance akan shiriyar (musulunci) da kuma basirah, don kuma kar
ka auka cikin abubuwan da za su lalata maka aikin hajjinka, ko kuma su rage
maka ladansa.
4) Ka yawaita ambaton Allah (zikiri) da addu'oi, da karatun
alkur'ani, da sauraron kasassuka masu amfani, da karanta littatafa masu
fa'idah.
5) Mustahabbi ne akanka –Dan'uwana Mahajjaci- gabanin ka yi
harama, ka cancada wankanka, ka kuma shafa turare, haka kuma ka aske gashin
bakinka dana gaba, da hammatanka guda biyu, tare da yanke farce gwargwadon
bukata, Yayin da shi kuma gashin gemu haramun ne aske shi.
6) Mustahabbi ne ga mutum namiji a yayin da zai yi haramarsa ya
yi cikin kwarjalle da mayafi guda biyu farare masu tsafta.
Amma ita kuma mace za ta yi haramarta ne cikin dukkan tufan
da ta so, sai dai kuma wajibi ne akanta ta nisanci tufa mai kawa (ado).
7) Sunnah dangane da abin da ake kiransa "ID-DIBAA'U"
(Wato: Bude kafadar hannun dama) shi ne ya kasance a lokacin yin dawafin dakin
Allah mai alfarma, Don haka; wajibi ne a kanka (Mahajjaci) ka lullube kafadunka
guda biyu tsawon lokacin da ka ke cikin tufafin haramarka, sai dai a lokacin
dawafin dakin Allah (nau'i biyu na dawafi kadai, dawafin "kuduum" ga
mai aikin hajjin ifraadi ko kirani, ko kuma na umrah) kadai.
8) Ya halatta a lokacin
da ka ke tsakiyan haramarka ka daura agogo, ko ka sanya zobe ko tabarau ko belt,
ko 'yar jakar ajiyar kudi ko makamancinsa, haka kuma za ka iya sanya takalma
silifas (banda takalmin kafa ciki) koda kuma dinkakku ne, sannan babu laifi ka
yi amfani da lema.
9) Baya halatta ga mutum namiji wanda ya yi haramar umrah ko aikin
hajji ya sanya wando ko riga 'yar ciki ko ta waje da tagiya (fula) da rawani.
10) Baya halatta ga 'ya mace da ta yi haramar aikin hajji ko
umrah ta sanya nikaabi ko safar hannaye guda biyu (ma'ana: dole ta bude
tafukanta biyu da fiska), Sai dai kuma wajibi ne akanta -a lokacin haramarta da
lokacin da ba na harama ba- ta suturce fiskarta a yayin tarayyarta da mazajen
da aure ya halatta a tsakaninsu (wadanda ba muharramanta ba).
11) Bayan an riga an yi haramar aikin hajji ko umrah baya halatta
ga mutum ya aske gashi, ko yanke farce, ko kuma shafa kowanni irin turare.
12) Baya halatta ga mutumin da ya nufi shiga Makkah don yin aikin
hajji ko umrah ya shige mikaati ba tare da ya yi harama (niya) ba.
13) Nau'ukan aikin hajji da aka shar'anta kala uku ne; Na farko:
Tamattu'i, Na biyu: Kiraani,
Na uku:
Ifraadi. Mafifici a cikinsu kuma shi ne: tamattu'i, Don haka;
(Idan) ka yi nufin yin harama da: "tamattu'i" za ka yi niyyar
yin umrah ita kadai sai ka ce: "Labbaikal lahumma umrah",
In kuma ka nufi yin "kiraani" to za ka yi
niyyar umrah da hajji su biyu a tare sai ka ce: "Labbaikal lahumma
umratan wa hajjah", Idan
kuma "ifraadi"
ne to shi kuma sai ka yi niyyar hajji shi kadai sannan ka ce: "Labbaikal lahumma
hajjan".
14) Ana shar'antawa ga mutumin da zai yi aiki hajji ko umrah sai
kuma ya zama yana tsoron wani lamarin da zai iya hana shi cika aikinsa, kamar
rashin lafiya ko waninsa, an shar'anta masa ya sanya sharadi, wannan kuma zai
kasance bayan ya kulla niyyarsa ne; Dagan an sai yace: "KUMA IDAN WANI ABU
MAI HANAWA YA HANA NI, TO WAJEN WARWARE NIYYATA SHINE WURIN DA KA KAWO LAMARIN DA
ZAI HANA NI".
Fa'idar fadin wannan shine: Halaccin warware niyyar da aka
kulla, idan aka samu sababin da ya hana karisa aiyukan, Sai kawai mahajjaci ya
warware haramarsa, kuma babu komai akansa.
15) Ka nisanci –Ya kai 'dan'uwana Mahajjaci- duk abin da Allah ya
hana aikatawa na jima'i da fasikanci da jayayya da laifuka, sannan ka kiyayi
cutar da 'yan'uwanka musulmai; da zance ko a aikace.
16) In ka kasance wanda aka jarrabe shi da shan taba To yin
haramarka da aikin hajji ko umrah dama ce a gare ka na yin bankwana -na karshe-
da ita tabar, ('Dan'uwana) har yaushe ne zaka ci gaba da shanta (taba) alhalin
ba ka fa'idanta da komai ba; sai fadawarka cikin zunubi, da lalata dukiya, tare
da cutar da lafiyarka, da kuma ta 'yan'uwanka?!
17) Ka nisanci –Allah ya maka dace- shagaltuwa -a halin
haramarka- da dauke-dauken hotuna na tarihi, ka kuma tuna cewa annabi (saw) a
yanayin hajjinsa ya fada cikin abin da ya inganta daga gare shi:
"اللَّهُمَّ حَجَّة لاَ
رِيَاءَ فِيهَا، وَلاَ سُمْعَة".
Ma'ana: "Ya Allah wannan hajji ne da babu yi don mutane
su gani (riya) a cikinsa, babu kuma yi don su ji;(sum'ah)"([1]).
18) 'Dan'uwana Mahajjaci! A hanyarka ta zuwa garin Makkah an so ka
yawaita yin "talbiyyah";
«لَبَّيْكَ اللَّهُمَّ
لَبَّيْكَ، لَبَّيْكَ لاَ شَرِيكَ لَكَ لَبَّيْكَ، إِنَّ الْحَمْدَ، وَالنِّعْمَةَ
لَكَ وَالْمُلْكَ، لاَ شَرِيكَ لَكَ».
"LABBAIKAL LAHUMMA LABBAIKA, LABBAIKA LA SHARIKA LAKA
LABBAIKA, INNAL HAMDA WAN NI'IMATA LAKA WAL MULKA, LA SHARIKA LAKA".
19) Sunna dangane da "talbiyyah" ita ce kowanni Mahajjaci
yayi "LABBAIKAL LAHUMMA LABBAIKA" wa karan-kansa, Amma yin
"talbiyyah" a jama'ance kam baya cikin shiriyar annabi (saw).
20) 'Dan'uwana mahajjaci! Ka tuna cewa a "mikaati" da
ake da su (guda biyar) akwai wurare da aka kebe su, domin fadakar da alhazai,
da kuma basu kananan rubuce-rubuce da su ke da alaka da aikin hajji, tare da
amsa musu tambayoyinsu tare da amsa musu duk abin ya zo daga wajensu na neman
bayanai.
Allah ta'alah ya azurta mu; gabadayanmu da dacersa, tare da
karbar aiyuka, ya kuma nusar da mu shiriyarmu.
Salatin Allah da sallamarsa su kara tabbata ga annabinmu
Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa gabadaya.
Na
Shehin malami
Prof. Abdurrazak bn Abdulmuhsin Albadr
Fassarar: Abubakar Hamza
Hajji: 1435h-2014m
No comments:
Post a Comment