2015/01/08

GOMA BIYU DON SAMUN NASARAR AURE DA MORIYARSA (سعادةُ الزوجين بتحصيل عَشْرَتَيْن)

GOMA BIYU; DON SAMUN NASARAR AURE DA MORIYARSA

(سعادةُ الزوجين بتحصيل عَشْرَتَيْن)
Gabatarwa:
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai! Bayan haka:
Allah ta'alah cikin hikimarsa da buwayarsa ya daidaita mazaje da matansu a babin "hakkoki", tare da bada daraja ta musamman ga maza akan su mata; a cikin fadinsa:
(وَلَهُنَّ مِثْلُ الَّذِي عَلَيْهِنَّ بِالْمَعْرُوفِ، وَلِلرِّجَالِ عَلَيْهِنَّ دَرَجَةٌ) [سورة البقرة: 228].
Ma'ana: (Kuma  su mata suna da kwatankwacin abin da ke kansu na hakkoki, da kyautatawa. Lallai kuma su mazaje suna da wata daraja mai girma akan mata).
Hadisi ya zo daga Anas dan Malik (RA), yace: Manzon Allah (SAW) yace:
"لاَ يَصْلُحُ لِبَشَرٍ أَنْ يَسْجُدَ لِبَشَرٍ، وَلَوْ صَلَحَ لِبَشَرٍ أَنْ يَسْجُدَ لِبَشَرٍ لأَمَرْتُ الْمَرْأَةَ أَنْ تَسْجُدَ لِزَوْجِهَا؛ مِنْ عِظَمِ حَقِّهِ عَلَيْهَا، وَالَّذِي نَفْسِي بِيَدِهِ ، لَوْ كَانَ مِنْ قَدَمِهِ إِلَى مَفْرِقِ رَأْسِهِ قُرْحَةٌ تَنْبَجِسُ بِالْقَيْحِ وَالصَّدِيدِ ، ثُمَّ اسْتَقْبَلَتْهُ تَلْحَسُهُ مَا أَدَّتْ حَقَّهُ".
Ma'ana: (Baya halatta ga wani mutum ya yi sujjada ga wani, da zai halatta mutum ya yi sujjada ga mutum to dana umurci mace da ta yi sujjada ga mijinta, saboda girman hakkinsa da ke kanta. Na rantse da Allahn da raina ke hannunsa! Da miji tun daga dugaduginsa har zuwa matsagar kansa za a samu raunin da ruwan diwa ke tultulowa daga cikinsa, sai matarsa ta fiskance shi tana ta lashe masa shi da harshenta, to da bata sauke hakkinsa da ke kanta ba!) [Ahmad ya rawaito shi, lamba: 12614, da Nasa'iy, lamba: 9102, Albaniy a cikin aikin da ya yi ma littafin JAMI'US SAGIR ya inganta shi, lamba: 13683].
Kuma wani hadisin ya zo cikin littafin Abu-dawud ta hanyar Mu'awiyah El-kushairiy (RA) yace: Nace:
(يَا رَسُولَ اللَّهِ! مَا حَقُّ زَوْجَةِ أَحَدِنَا عَلَيْهِ؟ قَالَ: «أَنْ تُطْعِمَهَا إِذَا طَعِمْتَ، وَتَكْسُوَهَا إِذَا اكْتَسَيْتَ، وَلاَ تَضْرِبِ الْوَجْهَ، وَلاَ تُقَبِّحْ، وَلاَ تَهْجُرْ إِلاَّ فِي الْبَيْتِ».
Ma'ana: (Ya ma'aikin Allah! Menene hakkin matar 'dayanmu akansa? Sai yace: Ka ciyar da ita idan ka ci, ka tufatar da ita idan kayi tufa, kada ka doki fiska, kada kuma ka ce mummuna, Ba zaka kaurace mata ba sai a cikin wannan gidan). [Ahmad, lamba: 20011, Abu-dawud, lamba: 2142, Albaniy a cikin "sahih Abu-dawud ya inganta shi, lamba: 1859].
Maluman musulunci sun nazarci nassoshin shari'a, sannan su ka yi bayanin hakkokin sashin ma'aurata akan sashi, Sheikh Hammaad dan Muhammad Al-ansaariy yana cewa dangane da hakkokin miji akan matarsa:
«أما حُقُوق الزوج على الزوجة فمنها: أنْ لا تُحنِث قسمه، ولا تَكفُر نِعَمَه، ولا تخرُج من بيته إلا بإذنه، ولا تصوم تطوُّعًا إلا بإذنه، ولا تأذن في رحله في شيء يكرهه، ولا تأكل وتلبس ما يؤذيه، ولا تكلم رجلا من غير محارمها إلا بإذنه، وعليها الرفق بأقاربه، والأدب مع إخوانه وأعمامه وأخواله، والرعاية لذريته بعد موته، ... ولها أنْ تأخذ من ماله ما تعلم رضاه به وأنه لا يغضب له ... ».
((Amma dangane da hakkokin miji akan mace, daga cikinsu akwai: Kar ta zama sababin yin azumin kaffara kan rantsuwarsa, kada kuma ta butulce ma ni'imominsa, kada ta fita daga cikin gidansa face ta samu izininsa, kada ta yi azumin nafila sai da izininsa, kada kuma ta yi izini a masaukinsa ga wani abinda yake kinsa, kada ta ci ko ta sanya duk wani abinda zai cutar da shi, kada kuma ta yi magana da wani mutum wanda baya cikin muharramanta sai bayan ta samu izininsa, kuma wajibi ne akanta ta tausasa ma danginsa, ta kuma yi zamantakewa da ladabi tare da 'yan'uwansa da baffanunsa da kawunansa, ta kuma lura da zurriyyar da ya bari bayan rasuwarsa, … kuma ya halatta ta dauki wani abu na dukiyarsa, gwargwadon abin da ta san zai iya yarda, kuma ransa ba zai baci ba…)) [Littafin/ Mukhtasarul hukuuk, shafi: 220].  Dangane da 'daya bangaren kuma sai Malam yace:
«وحقها على الزوج: أنْ يُحسن معاشرتها، ... ويحتمل عنها وإنْ تطاولت عليه، ويعفو عن زلتها، ويصبر عليها إنْ ضعُفَت. ويُعلِّمها ما تحتاج إليه من أحكام الوضوء والصلاة والصوم والحيض ونحو ذلك مما لا بد لها من معرفته. ويُطعمها من الحلال، ولا يظلمها شيئًا مما يجب لها من الحقوق المتقدمة. ولا يلبس ويأكل ما يؤذيها، ولا يمنعها زيارة والديها، ولا الخروج إلى المسجد إلا لخوف الفتنة ... ومن حُقُوقها على زوجها أنْ يتزيَّن لها كما يُحبُّ أنْ تتزيَّن له»([1]).
((Hakkin mace kuma akan miji Shine: Miji ya kyautata zamantakewarsa da ita… ya kuma shanye tare jure abinda ta yi masa, koda kuwa ta masa dagun-kai ko ta'addanci, sai ya mata afuwa kan kuskurenta, ya rinka yi mata hakuri, in ta gaza. Ya kuma ilmantar da ita abubuwan da ta bukace su na hukunce-hukuncen alwala da sallah da azumi da haila, da makamantan haka, na daga abinda ba makawa sai ta sanshi a ilmance. Ya kuma ciyar da ita daga halal, kada kuma ya zalunce ta wani daga cikin hakkokinta na wajibi da suka gabata. Kada ya sanya ko ya ci abinda zai cutar da ita, ko ya hanata ziyartar iyayenta guda biyu, ko fita don zuwa masallaci, sai dai in ya ji tsoron fitina. … yana kuma daga cikin hakkokin mace akan mijinta; ya rinka yi mata ado kamar yadda ya ke son ta rinka yi masa ado)) [Littafin/ Mukhtasarul hukuuk, shafi: 222].
Bayan haka:
Lallai kowanni mutum namiji ne ko mace MAFARKINSA a koyaushe shine: Ace yayi dacen aure, da samun nasarar yinsa, ta yadda zai ci moriyarsa a rayuwarsa ta duniya da kuma ta lahira.
Lalllai kuma wannan manufar, tare da bin dukkan hanyoyi don ganin tabbatuwanta suna da girman gaske, kuma idan miji da matarsa suka bi karantarwar alqur'ani da sunnar manzon Allah (SAW) sau-da-kafa, suna masu daukar shiriyarsu daga gidan annabta, cikin dukkan salon da ma'akin Allah kuma annabinmu Muhammadu (SAW) ya rayu da uwayen muminai (RA) lallai mutane zasu kai ga cimma hakan (nasarar aure da moriyarsa).
Kuma a wannan dama ta aure da abokaina guda uku masu suna Muhammadu suka yi; a kusan lokaci guda; NI ABUBAKAR HAMZA nayi tunanin bada gudumawata, amma kuma kash aljifun ba nauyi, Sai dai kuma nayi tunanin bada abin da yafi kudin ga kowanne daga cikinku; don ku yi bitarsa Ku da amarenKu, kana Ku yi iya kokarinKu wajen ganin kun gudanar da rayuwarku akan abin da wadannan wasiyyoyi da nasihu ke hukuntawa, wanda kuma da haka ne kawai za ku rabauta da cin nasara a duniya da lahira tare da samun moriya cikin aurataiyanku; Ku da kuma iyalanKu gabadaya, Allah ya tabbatar muku da haka, da dukkan mabiyin sunnar manzon Allah (SAW) a ko-ina yake.
Zuwa ga Muhammadu Muhammad Misau, Muhammadu Murtada Ya'akub, Muhammadu Salisu, Uwais Adamu, da masoyansu. TAKARDATA ZUWA GARE KU ZATA DAUKI TAKEN:
GOMA BIYU; DON SAMUN NASARAR AURE DA MORIYARSA
Wannan kuma saboda takaice bayanai kan wasiyyoyin nan guda biyu kan abu goma-goma da wassu iyaye biyu suka gabatar da su ga 'ya'yansu a lokacin aurensu, NA FARKO DAGA CIKINSU; Wasiyyoyi ne guda goma da wani mahaifi kuma mai ilimi a wannan zamani, ya yi su ga 'dansa, a lokacin aurensa. Yayin da NA BIYUN KUMA shahararriyar wasiyya ce da wata mata mai zurfin tunani da cikar hankali ta yi ma 'yarta a lokacin tarewarta zuwa gidan mijinta. Dukkan iyayen nan guda biyu a cikin wasiyyoyinsu sun kira "'ya'yansu" da "ya kai karamin dana!", "ya ke karamar 'yata!" har sau uku, a lokacin gabatar da wasiyyoyin, wannan kuma don sakwannin nasu su yi tasiri mai girma ga wanda aka yi masa nasihar, don kuma ya ji irin matsannancin tausayinsa da mahaifinsa ko mahaifiyarta take yi masa, ko take yi mata. Maganata kuma kan wadannan wasiyyoyin na kasa shi kashi biyu ne, kamar haka:
GOMAR FARKO: ZUWA GA MIJI (KO ANGO).
GOMA TA BIYU: ZUWA GA MATA (KO AMARYA). Kamar haka:
  

GOMAR FARKO: ZUWA GA MIJI (KO ANGO)
عشرُ وصايا قدّمها  والدٌ لولده عند زواجه:
Wadannan wasiyyoyin goma da ambatonsu zai zo a kasa, Na tsinto su ne a shafin internet mai suna SAIDUL FAWA'ID, Mutumin da ya gabatar da su kuma shine, M. Abdulladif Al-bariyjawiy. Ya fara da fadinsa:
أيْ بُنَيّ: أحمد الله جل في علاه أنْ أحياني حتى أراك يوم زفافك وقد اكتملتْ رجولتُك وتسعى لتحرز نصف دينك, وها أنت ستخرج من عالم عِشت فيه كالطائر الحرّ تسعى فيه بدون قيدٍ, تحلق عاليًا بلا قيود, وتقف على شطآن البحار دون همّ أو غمّ، إلى عالم جديد فيه من المسؤولية ما فيه([2]).
A farkon fari Uban cewa yayi: "Ya kai karamin 'dana! Ina gode ma Allah da ya rayar da ni, har naga ranar tarewarka, alhalin mazantakarka tana mai cika, sai gaka kana fita daga wata duniyar da ka riga ka rayu a cikinta, kamar tsuntsu mai 'yancin da ke yawonsa ba tare da dabaibayi ba, sannan ya je ya tsaya a gabar teku ba tare da wata damuwa ba, don ka shiga wata duniyar sabuwa fil ta daban, wacce take cike da dabaibayin hakkoki, da nauyace-nauyace". Sannan sai ya ci gaba da cewa:
أيْ بُنَيّ: إنّ أسعد ما يكون الأب يوم يرى فلذة كبده قد صار رجلاً, وإنّك ستَقدَم على عالَمٍ جديدٍ وحياةٍ جديدة, فيها مِن الجمال الكثير؛ إنْ أنتَ أحسَنْتَ التنقيب عنه واستخراجَه, وفيها مِن التنغيص ما يُودِي بك إلى شقاءِ الحياة وتعْسِ الرّفادة. فاحرص على الانتقاء ترتقي، واحرص على حسن المعاملة تتقي. وإيّاك وسوءَ الظنّ في زوجِك فهو الجحيمُ بعَينه، وهو المهلكة بذاتها.
"Ya kai karamin dana! Lallai lokacin da uba ke cike da jin dadi tare da annashwa shine lokacin da 'dansa ya zama cikakken mutum, don haka; lallai kai zaka tsunduma cikin wata duniyar ta daban, da kuma sabuwar rayuwa; wacce a cikinta akwai abubuwa masu kyan gaske dayawa; matukar ka kyautata bin hanyar zakulo su, kamar yadda kuma akwai abubuwan da ka iya gurbata rayuwar mutum tare da kawar masa da jin dadinsa, Akan haka; Sai ka tsananta kwadayinka wajen zakulo su; don ka daukaka, in kuma ka kai makura wajen kyautata mu'amalah; sai ka samu kariya. Ina kuma yi maka kashedi kan munana zato ga matarka saboda yin haka shine wuta mai saurin kunnuwa, kuma shine halaka ta hakika". Sannan sai wannan mahaifin ya ci gaba da cewa:
أيْ بُنَيّ: إنّك لن تنال السعادة في بيتِك إلا بعشر خصال تمنحها لزوجِك فاحفظها عني واحرص عليها: أما الأولى والثانية: فإنّ النّساء يحببن الدّلال، ويحببن التصريح بالحب، فلا تبخل على زوجتك بذلك، فإنْ بخلتَ جعلت بينك وبينها حجابًا من الجفوة ونقصًا في المودة.
"Ya kai karamin 'dana! Lallai kai baza ka taba samun nasara da rabauta ba a cikin gidanka har sai kayi riko da wassu sifofi guda goma da zaka rika bada su ga matarka, Sai ka saurara musu daga gare ni, kana mai kwadayin aiki da su da kiyaye su; amma NA FARKO DA NA BIYU: Ka sani! lallai dukkan mata suna son a shagwaba su, suna kuma son a rinka bayyana musu/ ana son su cikin lafazi karara, Kada ka yadda ka yi rowar abubuwan nan guda biyu ga matakarka, in kuma ka kuskura ka hana mata su, to hakika ka sanya shamakin nisantawa ne tsakaninka da ita, tare da kawo tasgaro da karanta soyayya". Sai ya ci gaba da cewa:
وأما الثالثة: فإن النساء يكرهنَ الرجلَ الشديدَ الحازمَ، ويستخدمْن الرجلَ الضعيفَ الليّن؛ فاجعل لكل صفةٍ مكانَها؛ فإنه أدعَى للحُبّ،وأجلب للطمأنينة.
Amma sifa ta UKU KUMA: Ka sani! Lallai su mata suna kin mutumin da ked a tsanani, da hazama, (wanda baya sassautawa, ko-yaushe), suna kuma neman hidimtawar namiji mai rauni da tausayi, Yi kokarin sanya kowacce sifa a gurbinta, don yin hakan ne kawai zai jawo muku soyayya, tare da samar da nitsuwa!". Sannan yace: 
وأما الرابعة: فإنّ النساء يُحببن مِن الزوج ما يحب الزوج منهنّ؛ مِن طيب الكلام، وحُسن المنظر، ونظافة الثياب، وطيب الرائحة؛ فكن في كل أحوالك كذلك.
"Amma sifa ta HUDU KUMA: Sani cewa mata suma suna so daga mazajensu irin abinda miji ke so daga gare su; na daddadar magana, da cancada ado, da tsaftace tufa, da kuma tashin kamshi, Sai ka zamto a dukkan halayenka akan haka! Sannan yace:
أما الخامسة: فإنّ البيتَ مملكة الأنثى وفيه تشعر أنّها متربعةٌ على عرشها وأنها سيدة فيه، فإيّاك أنْ تهدم هذه المملكة التي تعيشها، وإياك أنْ تحاول أن تزيحها عن عرشها هذا، فإنّك إنْ فعلت نازعتَها مُلكها، وليس لملكٍ أشدّ عداوةً ممن ينازعه ملكه وإنْ أظهر له غيرَ ذلك.
"Amma sifa ta BIYAR KUMA: Gidan aure shine wurin sarautar 'ya mace, kuma a nan ne take ji a jikinta cewa tana zaman watayawa (da nade kafa) akan gadon mulkinta, kuma lallai ita jagora ce a cikin wannan gida, Ina gargadarka kan rushe mata masarautar da take rayuwa a cikinta, ko kuma ka yi kokarin angaje ta daga gadon mulkinta; in kuma ka aikata haka; to kayi husuma ne da ita ko fito-na-fito akan abin da take mulka, Babu wata adawa kuma da tafi tsanani fiye da ta mai mulkin da ake fito-na-fito da shi akan mulkinsa, koda kuwa a zahiri yana nunar da sabanin haka! Sannan sai ya ci gaba da cewa:
أما السادسة: فإنّ المرأة تحب أنْ تكسب زوجها ولا تخسر أهلها، فإيّاك أنْ تجعل نفسك مع أهلها في ميزان واحد، فإمّا أنت وإمّا أهلها، فهي وإنْ اختارتك على أهلها فإنّها ستبقى في كمدٍ تُنقل عَدْواه إلى حياتك اليومية.
"Amma sifa ta SHIDA KUMA: Lallai mace tana son ta rabauta da samun mijinta, ba tare da kuma tayi hasarar iyalanta ba; don haka; Kada ka sanya kanka da danginta a ma'auni guda daya, har kace: Ta zabi ko kai, ko kuma danginta; saboda koda ta zabe ka akan danginta to ka sani; cewa zata wanzu ne cikin mummunan bakin-cikin da muninsa zai shigo rayuwarka ta yau da kullum! Sannan yace:
والسابعة: إنّ المرأة خُلِقت مِن ضِلعٍ أعوج، وهذا سرّ الجمال فيها، وسرُّ الجذب إليها، وليس هذا عيبًا فيها؛ "فالحاجب زيّنه العِوَجُ"، فلا تحمل عليها إنْ هي أخطأتْ حَملةً لا هوادة فيها تحاول تقييم المعوج فتكسرها وكسرها طلاقها، ولا تتركها إنْ هي أخطأت حتى يزداد اعوجاجُها وتتقوقع على نفسها؛ فلا تلين لك بعد ذلك ولا تسمع إليك، ولكن كن دائمًا معها بين بين.
"Amma sifa ta BAKWAI KUMA: Lallai 'ya mace an halicce ta ne daga kashin-hakarkari karkatacce, kuma karkatar mace shine sirrin kyanta, haka kuma shine sirrin da ke jan maza zuwa gare ta (har su fitinu da ita), wannan kuma ba aibi ba ne a gare ta, saboda gira (namarsa da gashinsa) ba komai ya kawata shi ba sai karkatarsa, don haka; idan mace tayi kure kada ka tasa ta a gaba; ba tausasawa ko rangwantawa, da nufin kokarin mikar da karkatarta; in kayi haka, sai ka karya ta; wanda kuma karyatan shine sake ta (rabuwar aure), Kada kuma ka kyale ta sakaka –in ta yi kuskuren- sai karkatarta ta karu, har ta riga ta kangare; ta yadda ba zata zama da taushi ko taji maganarka daga baya ba; A'a dole ne koyaushe idan tayi kuskure ka kasance tsakanin abubuwan nan guda biyu tare da ita. Sannan yace:
أما الثامنة: فإنّ النّساء جُبلن على كُفر العشير وجُحدان المعروف؛ فإنْ أحسنتَ لإحداهنّ دهرًا ثم أسأت إليها مرة قالت: ما وجدت منك خيرًا قط؛ فلا يحملنّك هذا الخلُق على أن تكرهها وتنفر منها، فإنّك إنْ كرهت منها هذا الخلُق رضيتَ منها غيرَه.
"Amma sifa ta TAKWAS KUMA: Lallai su mata a lokacin halittarsu an dabi'antar da su kan butulce ma abokin zama (miji), da kuma musanta kyawawan abubuwan da yayi; kai da za ka kyautata ma 'daya daga cikinsu na tsawon zamani, sannan kuma sai ka munana mata sau daya; sai tace: Da dai ban taba samun wani abun alheri ba a wurinka; don haka; kada wannan dabi'ar tata ta daukeka kan kyamarta gabadaya, ko kuma kaurace mata; saboda in ka ki wannan dabi'ar to ai ka gamsu da wassu dabi'un nata! Sannan yace: 
أما التاسعة: فإنّ المرأة تمر بحالات من الضعف الجسدي والتعب النفسي، حتى إنّ الله سبحانه وتعالى أسقط عنها مجموعةً من الفرائض التي افترضها في هذه الحالات؛ فقد أسقط عنها الصلاة نهائيًا في هذه الحالات، وأنسأ لها الصيام خلالهما حتى تعود صحتها ويعتدل مزاجها، فكن معها في هذه الأحوال ربانيًّا؛ كما خفف الله سبحانه وتعالى عنها فرائضه أنْ تُخفف عنها طلباتِك وأوامرَك.
"Amma sifa ta TARA KUMA: Lallai mace ta kan samu kanta a wassu lokutan cikin yanayi na raunin jiki, da kunci a rai, wanda kuma har Allah (SWT) a cikin wadannan hali (na haila da jinin haihuwa) ya dauke mata wassu daga cikin farillan da ya farlanta mata; ma'ana: ya dauke mata yin sallah gabadaya, tare da jinkirta mata lamarin azumi, har sai lafiyarta ta dawo mata, dabi'arta kuma ta daidaita, A don haka; kaima a cikin halin jinin hailarta ko na haihuwa sai ka yi koyi da Allah a lamarinta; ma'ana: kamar yadda Alah (SWT) ya dauke mata farillansa, kai kuma sai ka rangwanta mata cikin abubuwan da ka ke neman ta zartar, da kuma takaita yawa-yawan umurninka! Sannan a karshe yace:
أما العاشرة: فاعلم أن المرأة أسيرة عندك، فارحم أسرها وتجاوز عن ضعفها؛ تكن لك خير متاع وخير شريك. والسلام.
"Amma sifa ta GOMA KUMA: Ka sani! Mace a wurinka kamar daurarren bawanka ne (ba fita sai da izininka…); sai ka tausaya ma rashin 'yancinta, zata zame maka mafi alherin abun jin dadi, kana kuma mafi alherin wanda ake tarayya da shi!! Aminci ya tabbata a gare ka, Sannan yace: Mahaifinka/
Abdulladif Al-bariyjawiy.
Lallai wadannan wasiyyoyin idan har miji ya bi su sau-da-kafa wajen samar da su ga matarsa to lallai zata rayu da shi cikin nasara da aminci, kuma za ta kasance cikin matan da suka ci ribar aure da more masa –tun daga nan duniya, Ana kuma yi matan fatan dace a lahira-. Allah ya azurta mu da kyawawan halayyan musulunci da zamu zama mafiya alherin maza ga matanmu, amin!
Sai kuma bangare na biyu, wanda shi kuma yake da alaka da yadda ya kamata mace ta zama a wajen mijinta; gabanin ace yayi dace, ya kuma yi sa'a!
kamar haka:

GOMA TA BIYU: ZUWA GA MATA (KO AMARYA)
عَشرُ وصايا قدّمتْها  أمّ لابنتِها يومَ زفافها:
Ya zo cikin littatafa da yawa, daga cikinsu littafin DA'IRATU MA'ARIFIL USRATIL MUSLIMAH (vol. 54/ shafi: 180) cewa lallai Umamah yar Al-haris ta yi wasiyya ga 'yarta a lokacin da aka aurar da ita.
Ita kuma wannan uwar (Umamah) -'yar kabilar baniy shaiban- ta shahara da fasaha, tare da cikar hankali.
Kuma ta yi rayuwarta ne gabanin turo manzon Allah (SAW) –zamanin jahiliyyah-.
Kuma mijinta mai suna Aufu dan Muhallam as-shaibaniy ya kasance shugaba ne a cikin mutanensa kuma jagora.
Sai sarkin kinda mai suna Alharis dan Amru ya nemi auren 'yarsu mai suna Ummu-iyaas, sai kuma aka aurar masa ita, to a nan ne mahaifiyar wannan amarya ta yi mata wasiyyar da take tafe, wacce kuma maluma su ke daukanta daga cikin mafifitan wasiyyoyi da aka yi ma 'ya mace lokacin aurar da ita, WACCE TA KUNSHI BAYANAI AKAN GINSHIKAN DA AKE GINA RAYUWAR AUREN DA ZAI CI NASARA, DA KUMA ABUBUWAN DA SUKA WAJABA 'YA MACE TA BADA SU GA MIJINTA.
Ga wasiyyar kamar haka:
أيْ بُنيّة: إنَّ الوصية لو تُركت لفضلِ أدبٍ تُركت –لذلك- منكِ، ولكنها تذكرةٌ للغافل، ومعونةٌ للعاقل.
ولو أنَّ امرأةً استغْنَت عن الزوج لغِنَى أبَويها، وشدّةِ حاجتهما إليها كنتِ أغنى الناس عنه، ولكنَّ النساء للرجال خُلقن، ولهنّ خُلق الرجال.
"Ya ke karamar 'yata! Lallai wasiyya da za a bar gabatar da ita ga mutum don cikar ladabinsa to da baza a yi miki ita ba; saboda haka, sai dai ita (wasiyya) tunatarwa ce ga wanda ya gafala, taimako ne ga mai hankali.
Kuma da akwai wata matar da zata wadata ba sai ta yi aure ba; saboda kasancewar iyayenta mawadata, da kuma matsananacin bukatarsu gare ta; To ke ce kika fi dukkan mata bukatar barinsa (aure); sai dai kuma su mata an halicce su ne don maza, kamar yadda don su (matan) aka halicci maza!
Ta ci gaba da cewa:
أي بُنَيّة: إنّكِ فارقتِ الجوَّ الذي منه خرجتِ، وخلّفتِ العُشَّ الذي فيه درجْتِ. إلى وَكرٍ لم تعرفيه، وقرينٍ لم تألفِيْه، فأصبح -بملكه عليك-، رقيبًا ومَليكًا؛ فكوني له أمَةً يكن لكِ عبدًا وشيكًا.
"Yak e karamar 'yata! Lallai ke kin riga kin rabu da wannan yanayin da kika fito daga cikinsa, kin kuma bar sabbon da kika fito daga cikinsa (ma'ana: kin bar gidan da aka haife ki, sannan kika girma a cikinsa; gidan iyaye), kin tafi zuwa gidan da baki sanshi ba, zuwa kuma ga abokin zaman da baki saba da shi ba, wanda ya wayi gari –da daura muku aure- mai kula da ke, da ya mallake ki; Ki zame masa baiwa (mai bin umurni) zai zame miki bawa mai sauri amsawa! Sannan ta ci gaba:
أيْ بُنَيّة: احملي عني عشرَ خِصالٍ تكن لك ذُخرًا وذكرًا:
"Yak e karamar yata! Ki ji sifofi goma daga gare ni; za su zame miki guzuri, kuma abun ambato;
فأما الأولى والثانية: الصحبةُ له بالقناعة، والمعاشرةُ بحسن السمع والطاعة.
Amma NA FARKO DANA BIYU: Ki yi abota da mijinki da wadatar zuci, ki kuma yi zamantakewa da shi cikin ji da biyayya.
وأما الثالثة والرابعة: التعهد لموقع عينيه، والتفقد لموضع أنفه؛ فلا تقع عيناه منكِ على قبيحٍ، ولا يشمَّ منكِ إلا أطيبَ الريح.
Amma NA UKU DANA HUDU: Ki kiyaye mai idanunsa biyu zasu gani, da wanda hanci zai ji; kar ki yarda idanunsa su ganki kina aikata mummuna, kada kuma hancinsa ya shanshani wani abu face mafi dadin iska!
وأما الخامسة والسادسة: فالتفقد لوقت طعامه، والهدوء عند منامه. فإنَّ حرارة الجوع مَلْهَبَة، وتنغيصَ النوم مَغْضَبَة.
Amma NA BIYAR DANA SHIDA: Kiyaye lokacin cin abincinsa, da kuma nitsuwa a yayin barcinsa; saboda tsananin yinwa na kunna bakin-wuta, yayin da shi kuma yanke barci ke sanya bacin rai!
أما السابعة والثامنة: فالاحتفاظ بماله، والإرعاء على حشمه وعياله؛ لأنّ الاحتفاظَ بالمال مِن حسن الخلال، ومراعاةَ الحشم والعيال مِن الإعظام والإجلال.
Amma NA BAKWAI DANA TAKWAS: Ki kiyaye masa dukiyarsa, ki kuma kula masa da danginsa da iyalansa; saboda kiyaye masa dukiya na daga kyawawan sifofi, shi kuma lura da danginsa da iyalansa yana daga girmamawa!
أما التاسعة والعاشرة: فلا تُفشي له سرًّا، ولا تعصي له أمرًا؛ فإنّك إنْ أفشيتِ سِرَّه لم تأمني غَدْرَه، وإنْ عصيتِ أمرَه أوغرْتِ صدرَه.
Amma NA TARA DANA GOMA: Kada ki yada sirrinsa, kuma kada ki saba ma umurninsa; saboda idan har kika yada sirrinsa to baza ki taba amintuwa da shi ba, in kuma ki ka saba umurninsa to kin tafasa kirjinsa!
Sai kuma ta cike wasiyyarta da fadinta:
ثم اتقي مِن ذلك: الفَرحَ إنْ كان تَرِحًا، والاكتئابَ عنده إنْ كان فَرِحًا؛ فإنّ الخَصلة الأولى مِن التّقصير، والثانية مِن التَّكْدير.
Ki kuma kiyayi yin farin ciki a yayin da mijinki ke cikin bacin rai, da bayyanar da bacin rai yayin da yake farin ciki; saboda yin farin cikin mace yayin bacin ran mijinta na daga sakaci da jafa'i, yayin da shi kuma bata ranta a halin farin cikinsa zai gurbata masa farin ciki!    
وكوني أشدَّ ما تكونين له إعظامًا يكن أشدَّ ما يكون لكِ إكرامًا، وأشدَّ ما تكونين له موافقة يكن أطول ما تكونين له مرافَقةً.
Kuma gwargwadon yadda kika kasance kike girmama shi, gwargwadon yadda zai yi ta karrama ki (da kyautuka), kamar yadda gwargwadon yadda kike masa muwafaka (ba gardama) gwargwadon jimawanki a wajensa!
واعلمي أنك لا تَصلين إلى ما تحبّين حتى تُؤْثري رضاه على رضاك، وهَواهُ على هواكِ فيما أحببتِ وكرهتِ! والله يَخيرُ لكِ.
Kuma ki sani! Ba za ki isa ga samun abinda kike so ba; har sai kin fifita yardarsa akan yardarki, da abinda yake karkata zuwa gare shi akan naki; cikin duk abin da kika so, ko kika ki!   ALLAH YA YI MIKI ZABIN ALKHAIRI !!!
          Madalla da wannan uwa! Nan ne kuma karshen wasiyyarta, Idan har kuma mace ta yi aiki da su sau-da-kafa to lallai mijinta zai ji dadin zama da ita, kuma za su rabauta a rayuwarsu ta aure.
Allah ya taimake ku wajen aiki da wadannan nasihohi. WASSALAMU ALAIKUM.
                                                          'Dan'uwanku amini Abubakar Hamza
                                                               Madinah:17/03/1436h=08/01/2015m.


([1]) مختصر الحقوق، تأليف: الشيخ حماد الأنصاري، ص220 (ضمن رسائله الفقهية).
([2]) موقع صيد الفوائد،

1 comment:

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...