SIFFAR HAJJI DA UMRAH:
Asali da dalili a wajen
ma'abota ilimi kan sifar hajji Shine: hadisin Jabir bn Abdullahi (RA)
shahararre([1]).
Kuma haqiqa
mun bibiyi riwayoyi ingantattu kuma tabbatattu daga annabi (SAW); a yayin da kuma
muka haxa su, sai muka isa i zuwa ga sifar da take tafe:
Idan mutumin da yayi nufin
aikin hajji ko umrah ya isa wurin da ake kiransa "mikaati" mustahabbi
ne a gare shi yayi wanka, ya kuma aske abin da ke buqatar
cire shi na gashi; wato kamar gashin hamata, gaba, da gashin-baki, ya kuma
yanke faratunsa. Daga nan sai mutum namiji ya tobe xinkakkun
kayansa, kana ya sanya turare a jikinsa gabanin yin niyyar shiga cikin aikinsa
(na hajji ko umrah), kuma an so namiji ya xaura
zani da mayafi guda biyu masu tsafta farare. Ita kuma mace tana da damar tayi
haramarta daga abinda ta so na tufa. Shi namiji zai lulluve
kafaxarsa
da mayafinsa. Sai kuma mahajjaci yayi harama da nau'in aikin da ya nufa (kamar
umrah, hajji ifradi, qiraani, tamattu'i).
Abinda kuma yafi shine mahajjaci
yayi haramarsa bayan ya daidaita akan dabbarsa (ko motarsa).
Idan mai harama yana tsoron
wani abu da zai iya hana shi kammala aikinsa; kamar rashin lafiya, ko 'yan
fashi, ko makamancin haka to a nan zai yi sharaxin
cewa: wurin warwarewan aikinsa shine wurin da wannan uzurin ya riqe
shi.
Mustahabbi ne mahajjaci ya
kasance a wajen da zai yi niyya yana fiskantar alqiblah,
ya kuma ce: Ya Allah! Na yi nufin hajjin da ba riya a ciki, babu kuma yi don a
ji (sum'ah).
Sai kuma ya fara
"LABBAIKAL LAHUMMA LABBAIKA, LABBAIKA LA SHARIKA LAKA LABBAIKA, INNAL
HAMDAH, WAN NI'IMATAH, LAKA WAL MULKA, LA SHARIKA LAKA". Sahabbai kuma sun
kasance suna karawa akan haka; Suce: "LABBAIKA ZAL MA'AARIJ, LABBAIKA ZAL
FAWAADIL".
Kuma sunnah ne namiji ya xaga
sautinsa lokacin yin "talbiyyah".
Idan ya isa garin makkah
mustahabbi ne mahajjaci ko mai umrah yayi wanka, idan kuma ya zo zai fara xawafi
sai yayi abinda ake kiransa "id-xiba'i"
ma'anarsa kuma shine: mahajjaci namiji ya buxe kafaxarsa
ta dama, sai kuma ya lulluve kafaxarsa ta hagu da "haraminsa". Kuma sharaxi
ne mahajjaci ya kasance yana da alwala a lokacin da yake yin xawafi.
Mustahabbi ne kuma ya tava "hajarul aswad" da hannunsa, tare da kuma sumbantarsa
da bakinsa, idan kuma hakan ya gagara sai ya tava
shi da hannunsa, tare da sunbantar hannun, idan hakan kuma bai yiwu ba; to zai
yi nuni ne i zuwa ga dutsin (hajarul aswad) da hannunsa, ba tare da ya sumbanci
hannun nasa ba. Zai kuma aikata haka a kowani zagaye, kuma zai fara kowani
zagaye da kabbara. In kuma ya fara xawafin
nasa da faxin "BISMILLAHI WALLAHU AKBAR" to hakan ya yi kyau.
Idan kuma ya iso setin dungun
da ake kira da "AR-RUKUNUL YAMANIY" to sai mai xawafi
ya tava
shi; ba tare da ya sumbance shi ba, idan cunkoso kuma ya hana tava
shi; to a wannan halin ba zai yi nuni i zuwa gare shi ba, haka kuma ba zai yi
kabbara ba.
Kuma mustahabbi ne mai xawafi
ya riqa
cewa –a tsakanin "RUKUNUL YAMANIY DA HAJARUL ASWAD"-:
(ربنا
ءاتنا في الدنيا حسنة وفي الآخرة حسنة وقنا عذاب النار) البقرة: ٢٠١
Kuma zai yi duk abin da ya sawwaqa
na addu'a a sauran xawafinsa. Mustahabbi ne mai xawafi
yayi sassarfa (ARRAMALU) a zagaye ukunsa na farkon xawafi.
Sai kuma ya yi tafiyarsa irin ta al'ada a sauran kewaye guda huxun.
Idan kuma ya kammala zagaye bakwai xinsa
to sai ya rufe duka kafaxunsa guda biyu da mayafinsa.
Sa'annan sai ya tafi i zuwa "MAKAAMU-IBRAHIMA" yana mai karanta:
(واتخذوا
من مقام إبراهيم مصلى) البقرة:
١٢٥
Sai kuma mutum ya sallaci
raka'a biyu a bayan wannan wuri "makaamu-Ibrahima"; yana mai karanta
(KUL YA AYYUHAL KAAFIRUUNA) bayan suratul fatihah, a raka'ar farko, A raka'a ta
biyu kuma sai ya karanta (KUL HUWAL LAHU AHADUN). Idan kuma bai samu damar yin
sallah a bayan (makaamu-Ibrahima) ba saboda cunkoso, ko makamancin haka; to sai
ya yi sallah a kowanne wuri a cikin wannan masallacin. Wannan xawafin
shi ake kira "xawaful quduum" ga mai hajjin "ifraadi", da "qiraani".
"dawafin umrah" kuma ga mai "tamattu'i".
Daga nan kuma; an shar'anta
masa ya sha ruwan zamzam, ya kuma kwara shi ma kansa.
Sa'annan sai ya dawo i zuwa
ga "hajarul aswad" ya tava shi -idan
hakan ya sauwaka masa.
Sa'annan sai ya fita zuwa ga
dutsen "safah", yana mai karanta fadin Allah ta'alah:
(إنّ
الصفا والمروة من شعائر الله) البقرة:
١٥٨
Daga nan kuma sai ya hau dutsen
"safah", har sai ya hango xakin
ka'abah, ya fiskanci alqiblah, ya daga hanayensa yana
cewa:
"ALLAHU AKBAR"; sau
uku,
(لاَ إِلَهَ إِلاَّ
اللهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ، وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى
كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، لا إِلَهَ إِلا اللهُ وَحْدَهُ، أَنْجَزَ وَعْدَهُ، وَنَصَرَ
عَبْدَهُ، وَهَزَمَ الأَحْزَابَ وَحْدَهُ).
LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU
LA SHARIKA LAHUW, LAHUL MULKU, WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADIIR.
LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAH, ANJAZA WA'ADAH, WA NASARA ABDAH, WA HAZAMAL AHZABA
WAHDAH.
Zai aikata wannan ne har sau
uku, tare kuma da yin addu'a mai tsayi a tsakanin zikiri da zikiri.
Sa'annan sai ya sauka yana
mai tafiya i zuwa dutsen "marwah". Idan ya iso tsakanin
"mil" guda biyu kwarra to sai ya yi gudu mai tsanani a tsakaninsu.
Wannan kuma ga mazaje ne kawai; banda mata. Dagan an kuma sai ya ci gaba da
tafiyarsa har sai ya hau dutsen "marwah". Zai kuma aikata akan wannan
dutsen kwatankwacin abinda ya aikata alhalin yana kan safah. Wannan kuma shine
kewaye ko zagaye xaya, sa'annan daga marwah idan har ya dawo safa to wani zagayen
na daban kenan, da haka har ya cika kewaye guda bakwai.
Wannan sa'ayin ga mai aikin
hajjin "ifraadi ko kiraani" shine sa'ayinsa na aikin hajji, kuma waxannan
mutum biyu ba za su yi abinda ake kiransa "tahalluli" ba; a bayan
wannan sa'ayin, hasali ma za su wanzu ne a cikin haramarsu. Ga mai hajjin
"tamattu'i" kuma shine sa'ayin umrarsa.
Shi mai tamattu'i zai yi
tahalluli ya warware daga umrarsa daga zarar ya aske gashin kansa, sai kuma ya
sanya tufafinsa.
Idan ranar takwas ga watan 12
ta zo (ma'ana: yinin da ake kiransa yinin tarwiyyah), To sai mai tamattu'i ya
yi haramar aikin hajjinsa, daga wurin da ya ke zaune.
Haka suma mazauna garin
makka, da waxanda su ke kusa da ita daga cikin waxanda
ba su yi harama ba.
Kuma mustahabbi ne mahajjaci
–a wannan yinin- ya aikata irin abin da ya aikata a "mikaatinsa"; na
yin wanka, da shafa turare, da tsafta. Daga nan kuma sai xaukacin
mahajjata su xunguma su nufi qauyen
"minah" suna masu "talbiyyah", suna masu sallatar azahar,
la'asar, magriba, ishah, da asuba, kowacce daga cikinsu ita xayanta
ba tare da an yi jam'inta da 'yar'uwatta ba, gami da yin kasarun sallah mai raka'a
huxu
daga cikin sallolin guda biyar.
A safiyar yinin tara (9) mahajjata
zasu tafi zuwa filin "arfah", In har kuma da zasu samu damar sauka a
wajen masallacin "Namirah" zuwa lokacin da rana zata yi zawali to
hakan yana da kyau. Idan ranar ta yi zawali sai shugaba ko mai na'ibtarsa ya yi
huduba gajeruwa, sa'annan ya sallaci azahar da la'asar "kasaru kuma a tare",
a lokacin sallar azahar. Kana kuma sai ya shigo yankin filin arfah. Kuma wajibi
ne akan mahajjaci ya tabbatar cewa yana cikin kewayen arfah. Sai ya fiskanci alqiblah,
ya daga hannayensa yana mai addu'a da kuma "labbaikal lahumma
labbaika", ya yi ta hamdalah, ya yi ijtihadi sosai wajen kan-kan-da-kai da
zikirori da addu'a a wannan yini mai girma. Kuma mafificin abin da ake faxa
a wancan yinin shine:
"لا إِلَهَ إِلا اللَّهُ وَحْدَهُ لا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ
الْمُلْكُ، وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ".
LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU
LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU, WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADIIR.
Kuma mustahabbi ne mahajjaci
ya zamto ba ya cikin yanayi na azumi a tsawon wannan yinin; saboda hakan zai fi
bashi karfi wajen bauta. Mahajjaci ba zai gushe ba yana tsaye yana mai
kan-kan-da-kai, tare da bayyanar da kaskancinsa i zuwa ga Allah, har rana ta faxi.
Idan rana ta faxi
sai mahajjaci ya gangara daga "arfah" cikin nitsuwa, yana tafiya yana
"talbiyyah" har ya isa filin "muzdalifah"; sai ya sallaci
sallar magriba da ishah a tare, gami da yin kasarun ishar. Kuma an yi rangwame
ga masu rauni su fice daga muzdalifah cikin dare. Shi kuma mai karfi dole ne
akansa ya wanzu a muzdalifan har sai bayan yayi sallarsa ta asubah.
Sa'annan kuma sai ya fiskanci
alqiblah,
ya gode ma Allah ta'alah (alhamdu lillahi), ya girmama shi (Allahu akbar), yana
mai yin "la'ilaha illal lahu", da sauran zikirori, har sai gari ya yi
haske sosai. Sa'annan sai mahajjaci ya bar muzdalifah gabanin fudowar rana. Kuma
wajibi ne akansa ya tafi a nitse, yana mai yin "talbiyyah". Daga nan
kuma sai ya tsunci duwatsu (tsakuwa) guda bakwai akan hanyarsa. Har idan ya iso
"jamratul akabah" sai ya jefe ta da tsakuwan nan guda bakwai, yana
mai yin kabbara tare da kowanne tsakuwa. daga nan kuma sai ya yanke
"talbiyyah"; yana kuma mai tsayar da yinta kwata-kwata. Sa'annan sai
ya yanka ko soke abun hadayarsa, kuma mustahabbi ne ya ci wani abu daga cikin
naman. Sa'annan sai ya aske gashin kansa. Sai ya yi xawafinsa
na ifadha, tare da yin sa'ayi na aikin hajjinsa in aikin hajjin
"tamattu'i" ya ke yi. Ko kuma "ifraadi ko kiraani" amma sai
ya zama bai yi "sa'ayin" ba a lokacin da ya yi "xawaful
quduum"
dinsa.
Kuma sunnah ita ce a jera waxannan
aiyukan: jifa, sai yanka ko sukar raqumi,
sai kuma aski ko saisaye. Idan kuma mahajjaci ya kauce ma hakan; ya kuma gabatar
da wani aikin daga aiyukan ranar goma akan wani, to babu laifi. Kuma idan mahajjaci
ya aikata abu biyu daga cikin aiyuka uku –jifan jamratul akabah, aski ko
saisaye, da kuma xawafi tare da sa'ayi; in har akwai sa'ayin akansa- to ya samu
"tahallulin farko", daga nan kuma kowanne abu ya halalta a gare shi
wanda "ihrami" ya haramta masa, in banda kwanciya da matarsa. Idan
kuma ya aikata ukun gabaxaya to ya yi "babban
tahalluli"; sai kowanne abu ya zama ya halatta masa; harma kusantar matar
tasa.
Kuma mahajjaci zai kwana a
"minah" daren goma sha xaya da sha
biyu (11, 12) a matsayin wajibi, sai
kuma ya yi jifan "jamaraat guda uku" ranar goma sha xaya;
yana mai farawa da "qaramin", sannan sai "alwusxah",
sa'annan sai na karshen (babba). Haka nan zai aikata a rana ta goma sha biyu
(12). Lokacin jifan kuma na farawa ne daga "zawalin rana" har zuwa
asubahi. Idan mahajjaci ya jefi "jamrah qarama"
an sunnanta masa ya matsa kaxan ta dama gare
shi, ya tsaya yana mai fiskantar alqiblah,
ya xaga
hannayensa yana addu'a. haka nan idan ya jefi "jamrah ta tsakiya" nan
ma an sunnanta masa ya matsa gaba kaxan
ta vangaren
hagu, ya fiskanci alqiblah, ya tsaya ya jima yana
addu'a, hannayensa sama. Sai dai kuma ba zai tsaya ba bayan ya yi jifan
"jamratul aqabah". Idan kuma ya yi nufin gaggawa to wajibi ne akansa ya
fita daga minah ranar goma sha biyu (12), kafin rana ta faxi.
Yayinda idan da ranar zata faxi masa alhalin
yana "minah", a cikin zavinsa
to wajibi ne akansa ya kwana zuwa ranar goma sha uku (13).
Idan kuma mahajjaci ya so ya
fice daga garin makka to wajibi ne akansa yayi xawafin
bankwana, don ya sanya aikinsa na qarshe
ya zamo xawafin xakin Allah. Shi kuma wannan xawafin
na faxuwa
ga mace mai haila ko kuma mai jinin nifasi.
WALHAMDU LILLAH
!
No comments:
Post a Comment